HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 3 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 3 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Momyce takalli shuriem cikin farin cikin tace iye yaronnawa yagirma shi kuwa shuriem kunyace takara kamashi Kamar yanutse yakeji, 

Momyce tacigaba da cewa Yar’ gidan waye dafatan Yar’ manyan mutane ce masu mutumci gyara zama yakukayi yakorowa momy bayanin haduwarsu da kuma mahaifinta Amma yaboye Mata Abunda sukayi da Heedaya yau A Asibitinsa.

Dadi taji tace ” insha Allahu yau Zata sanar da Abbansa, tashi yay yafita Yana godiya.

Nida Yaya taufiq ne muketa Shan Hira, iya na jefa Mana baki kadan kadan, sallamar yayanmu naji Amsawa nayi tareda mikewa Zan fice,  iyace tace ikon Allah yanzu shuriem har kazamarwa Yar’ uwarka dodo duk inda taganka taringa zabura Kamar sabon kamu, iya aidama turu kikasa Abba yakaita canne yafi dacewa da ita, cewar yayanmu, 

Iya kwa me zatayi Banda fada Kamar ta aro baki Haka takeji taufiq ne yaja hannunsa suka fice suna dariya Ai danaga sun fita dawowa nayi nazauna na lallaba iyata muka cigaba da hirarmu.

Misalin karfe 9:30pm merah keta Kiran Yaya yaki dayawa candai ya daga daya gaji da jin karar wayar daukar wayar yayi yakara Akunne batareda yayi maganaba, cikin kirsa da shwagwaba meerah ta fara magana Kamar Haka,  “my shuriem najika shiru shiyasa nace Bari na kiraka naji ko lafiya, Ajiyar zuciya yayi saboda ta da meshi gashi bacci zeyi ta hanashi, merah yakira sunanta sannan yadora da fadin na Amince dan Haka kisanar Agida Nan bada jimawaba Abbana zezo yasamu mahaifinki suyi magana, Ay wani ehu da meerah tasaki jiyayi Kamar zata cire Masa dodon kunne, katse kiran yayi, sannan yakira layin Momy yace taturo Masa heedaya tace Masa anbasu Assignment yasan inbece hakaba bazata barta tazoba cewa zatayi dare yayi shikuwa shuriem mugunta ya shiryawa Heedaya.

Jinayi  Ana tashina cinkin barcin daya Fara daukata, tashi nayi tareda fadin momy kece, eh tacemin tadore da cewa ki maza kije yayannaku yana jiranki kince zeyi miki Assignment Kuma kin Kama barci ta fad  tareda ficewa daga dakinmu nikuwa nasan kwanan zancan yanzu inbanjeba ze iya zuwa yasameni har dakin Kuma se kashina yabushe, gashi banasan momy tasan Abinda nayi A asibitin yaya, tashi nayi na nufi part din yayanmu yauma baya falo Kai tsaye nawuce dakin Danni Akwai daukar kasada kowace irice .

Bedroom din duhu din dim  ko tafin hannu na bana gani wucewa nayi nakama laluban switch din kawai Sai jinayi nayi tuntube da mutum Tim naji nafada Masa Aka baki na kware na  kurma ihu dokemin baki yayi yace banason kitaramun mutane fitilar wayarsa yakunna nakare Masa kallo daga kwancen danake,. Jallabiyace Fara Sol Ajikinsa Sai wani Dan ubansun kamshi dake tashi Ajikinsa Zaune yake kan dadduma da carbi Ahannusa yanaja da Alama sallah ya idar domin naji danshin ruwan dayay Alwala Ahannunsa, tunda nake Arayuwata bantaba samun kusanci da wani namijiba irin Haka,

Yau saigani ringingine kaina da kafadata acinyar yayanmu ya ilahi na

Furta Araina saka makon wani kwarjini da yayanmu yaymin kallon juna muka shigayi ba kakkautawa, kowa da Abinda yake sakawa Aransa,

Abbane yajiyo Kara bangaren Yaya tunaninsa ko barayine suka shigo gidan lokacin momy tagama gaya  Masa Masa maganar Auran shuriem kenan suka jiyo karar dukkansu suka Mike Abbane yay karfin halin cewa Bari yaje yaduba.

Ai har Abbanmu yashigo bamusan yashigoba munata faman Kallon kallo nida Yaya Afirgice Abba yace” shuriem Heedaya mezan gani Haka…….

Mikewa mukayi Afirgice, Abba yakama yimana duban tuhuma, Zoki wuce Heedaya yafada ransa Yana kuna bayan na fitane yadawo kan yayanyanmu, shuriem yakira sunansa, shikuwa Kara kasa da kansa yayi, kazama butulu Arayuwarka, matar data reneka atafin hannunta tahakura da komai Dan farin cikinku Kai Yar’ uwarka yau Abinda zaka saka Mata dashi kenan, yayane yabude baki zaiyi magana Abba yadaga Masa hannu, tareda fadin “bakada Abinda zaka gayamin nayarda da idona naganka.

Daga Nan Abba baikara cewa komaiba yajuya yafice ransa na suya bezame ko inaba Sai part din Iya, kofa ya kwankwasa Mata, baiwar Allah iya Nene har Anfara bacci, ta jiyo Ana buga Mata kofa tasowa tayi tanacewa nikuwa waye da tsohon darennan heedayata lafiya daiko? tana budewa taga Abba Atsaye hanya tabashi yawuce tareda fadin isma’ila  lafiya daiko.

Abbane yace iya kedai samu guri kizauna, Abunda na gani yau yafi karfin tunanina, iya kam shigowa tayi tazauna tana fuskantar Abba tareda fadin Ina sauraranka, Abbane ya gyara zama yace ” iya yarannan ne Heedaya da shuriem Nan ya zaiyyane Mata Abinda ya faru sannan yadora da cewa iya hankalina yayi matukar tashi gashi nagayawa momynsa yasami yarinyar daya keso zai aura yanzu, iya yaza muyi da wannan Abun kunya har gida iyace tanisa bayan zurfin tunani datayi tace “isma’ila yarannan duk akarkashin ikonka suke Abinda nakeso kayi yanzu shine gobe da sassafe kaje gurin Alh Usman kanin mahaifin Heedaya kasamu Abokinka guda daya kutafi tare sonake Asafiyar gobe Adaurawa shuriem da Heedaya aure nasan Alh. Usman bazai kiba dubada yadda muke mutunta juna, daga Nan kuwuce gidan ita wadda takeso din kuje ku nema Masa auranta duk ranar da iyayanta suka sa mu amsa kawai bashi yajiyoba.

Abbane yakarbe zancan da fadin kinyi dai dai iya Kuma bazan taba kaucewa maganarkiba, Allah yay maka Albarka kaje kayi barcinka harda minshari Kar tunanin shuriem yadaga maka hankali cewar iya Nene Da Amen ya amsa yatashi yakama hanyar part dinsa.

Koda yakoma momy yasamu hankalinta Atashe domin tunda yafita gabanta yaketa faduwa dasauri ta nufoshi tana fadin “Abban Yara lafiya daiko najika shiru baka dawoba, kamata yayi yazaunar da ita tareda Kiran sunanta yace “ki kwantar da hankalinki ba Abunda muke tunani bane Amma Akwai maganar danakeso muyi

Ina bukatar ki nutsu, Ajiyar zuciya momy tayi tace Ina sauraranka Koro Mata bayani yashigayi tiryan tiryan har yadda sukayi da iya yagaya mata.

Sannan yace Amma ke meye shawararki, fasalta halinda take cikima Bata bakine Amma dayake macace me ilmi Sai Bata nunaba, kallansa tayi tace wannan matakin shiya dace dasu Kuma kaida iya kunyi daidai, Albarka Abba yay tasa Mata tareda cewa nayi dacen Mata tagari nasan Kuma wannan wata baiwace da ubangiji yaymin tashi yayi yadauro Alwala yakama nafilfili itama ummi tashi tayi tabi bayansa Haka suka Raya wannan dare suna ibada acinkinsa tareda rokon Allah yasa wannan aure yazama Abin Alfahari ga zuri’arsu baki daya.

Bangaran yayama Haka ya kwana sallah tareda Kai kukansa ga Allah madaukaki.

Ni kuwa kwana nayi kuka danaji kukan bazemunba Nima Alwalar nayi naxo naitagayawa ubangiji yasamomin mafitar wannan Al’amari.

Washe gari da safe gidan shiru kakeji bawani me kwakwkwaran motsi Koda mukazo Karin kumallo yayakin fitowa yayi Nima sadiyace talallabani nafito Ina fitowa Naga ummy nabina da kallon banza nikuwa Araina nace niba take nakeyiba kibarni naji Da Abinda ke damuna.

Zuwa nayi nagaida momy da Abba bayabo ba fallasa suka amsamin wuri nanema nazauna kasacin Abincin nayi saboda Ina cikin damuwa, bayan mungama Abbane yafara mikewa tareda fadin nizan fita saina dawo yafada tareda yin hanyar waje Abokinsa yakira awaya yace inbaya komai zairakashi wani waje dagacan bangaran, Abokin Abban ya amsa Masa cewa Yana free yagaya Masa inda zasu hadu Abbane yace su hadu Asaban titi, Aikuwa cinkin mintuna kalilan suka hadu Abbane yaywa Abokinsa Alh.sagir bayanin indazasu Aida fara’arsa yasawa Auran Albarka.

Cikin kankanin lokaci suka Isa gidan kawun Heedaya yaro suka samu yay musu sallama da malam usman bayan yaran yafito yashaida musu yace gashinan zuwa sun Dan jira kadan saiga malam usman yafito ganin Abbane yakoma da sauri yadauko musu irin babbar dar dumar nan yashimfida musu Azauran gidan, iso yay musu, suka shigo suka zauna, gaisawa Akayi Abba yadubi Alh. Usman yace “Alh wani babban Al amarine ke tafe damu Ina nemawa shuriem Auran Yar’ ka Heedaya Kuma inaneman Alfarma kafin mubarnan kanemo  shaidu adaurq musu aure…..

Alh. Usman yakalli Abba sannan yayi murmushi tareda cewa ai Alhaji Heedaya Abar ikonkace Kaine Wanda zaka zaba Mata mijin daya dace da ita, saigashi Kuma wani Abun Karin farin cikin danmu yagani yanaso kaga Allah kawai zamuyiwa godiya, Kuma yanzu Abnda za’ayi.

Alh.ismai’il Kai zaka zama waliyyin Heedaya shikuma wannan da kukazo dashi yakarbarwa shuriem Auren, Abba najin Haka Dadi yalullubeshi yay taiwa kawun Heedaya godiya, daganan kawu Usman yakirawo makotansa guda 3 suka shaida daurin Auran,

Daganan Abba yaywa kawun Heedaya bayanin Auran shuriem na biyu kawun Heedaya Albarka yasawa Auran daga karshe sukayi Addu’a sukayi sallama suka tafi.

Daga Nan Basu zame ko inaba Sai gidansu meerah sukyi sa’a kuwa Abbanta Yana gari bayan sun zauna ne Abba yadubi Alh. Sadau Dan maliki yace ” dama yaro nane yaga Yar’ wajanka yanaso shine mukazo neman iri ko zamu samu Abban merah saidaya nisa sannan yace ni Alh. Sadau Dan maliki ya’ daya tilo Allah yabani Kuma ni bazanyi Mata Auran doleba Amma Abune nawaya Bari nakirawota NASA handsfree kuji da kunnanku.

Haka kuwa Akayi, Abban Meera yakirata ringing 2 ta daga tare da fadin daddyna, Alh. Sadaune yakatse ta fadin daughter Akwai wani yaro shuriem ya turo iyayansa gurina Akan maganar auranku, Amma Kuma nace sainaji tabakinki tukunna, daga can bangaran merah tace “daddy dama ni naturoshi Kuma na Amince dashi, Nan dai suka tsaida Rana wata 1 mezuwa, Dan Acewar Abban meerah bayaso Asa lokaci dayawa tunda yaran bawasu kananabane,. Abbane ya amsa Masa tareda Yi Masa godiya.

Bayan yadawo gida yakira momy suka tafi bangaran iya bayan sun zauna ne yay musu bayanin Andaura Auran Heedaya da shuriem da Kuma sa ranar auransa da merah Albarka suka sawa Abin sannan yadauki waya yakira shuriem awaya yace “yazo yanasan ganinsa bayan shuriem ya iso ya sunkuya yagaida momy da iya.

Sun amsa  fuskarsu asake  saboda Auransa da Heedaya ya wanke musu Abinda yayi, Abba yagaisar ya amsa bayabo ba fallasa.

Abbane yay gyaran murya sannan yafara magana Kamar Haka shuriem saka makon Abunda kayi jiya ko ince kukayi na daura auranka da Heedaya Asafiyar yau.

Sannan Ansa ranar auranka da yarinyar daka kawo kanaso, iyayanta sun nemi Asa wata 1 mezuwa Kuma na’amince sannan inada dokokin dazan kafa maka banaso Kuma katsallakeso indai kanaso Abunda kayi yagoge agurina.

Na Farko banasan katakurawa Heedaya A Rayuwar Auranka da ita saboda nasan ba kwa jituwa kariketa Amana kodan maraicinta.

Sannan na 2 duka matanka zaka Ajiyesu A part Dinka saboda yanada girma bazaka tare a sabon gidankaba har Sai Naga yanayin Zamanka dasu.

Sannan na 3 ni bazan cigaba da ciyarma da matarkaba kana nema Kuma kana samu ko ruwa zata Sha Kai zaka siya mata.

Sannan Abu nakarshe in yamma tatyi kadauko ATM kadauki mahaifiyarka kuje wani babban kantin Adanyi Mata siyayya kafin kayi musu lefe Dan Haka ku kusan Abinda zaku siya, Nina Gama magana zaka iya tafiya tunda shuriem yazauna kansa na sunkuye be dagoba  se asannan yadago yay wa Abba godiya, sannan yaywa su iya sallama yafita.

Shriem ne yakoma bangaransa hankalinsa Atashe yarasa wane hali yake cikima bakin ciki ko farin ciki, direct toilet yashiga ruwa yasakarwa kansa yanata tunane tunane ..

Momy kuwa Anty saudat takira tagaya Mata Abinda ya faru tayi murna sosai bayan sungama magana ne momy takira mahaifiyarta tagaya Mata tayi murna sosai sannan Abba yasha Addu’a shida zuri’arsa .

5:00pm Yaya shigo bangaramu Wanda yay dadai da fitowata daga kitchen kallo be isheniba Haka shima yawuce ko inda nake be kallah ba, dakin momy Naga ya shiga nikuwa nazauna A falo nakama cin indomie din Dana dafa can sainaga sun fito da momy, momy harda murmushinta Abin yabani mamaki Nita ki kulani tun safe shikuwa har fara’a take Masa da Alamu ma fita zasuyi dannaganta da mayafi Akanta Saida sukazo kusadani Naga ta Bata Rai tareda fadin zamuje unguwa ba dadewa zamuyiba kallanta nayi nace ” Momy meza adafa kafinki dawo, shuriem zakiyiwa wannan tambayar ba niba ta fada tanayin hanyar fita duban Yaya nayi nace me za’a dafa  Yaya shikuwa da mugunta yace, Masa nakeso damiyar Agushi, sannan kiyimin tuwan farar shinkafa, so samu inaso naci Amala, sannan da lemo Kamar kala 3 Yana Gama fada yajuya yabi bayan momy, momyma har takai bakin kofa tajuyo tace daga yau ko ruwan gidannan banyarda kishaba shuriem ze siyo sannan karki taba Mana kayan Abinci shima ze kawo miki Wanda Zaki dinga Amfani dasu daganan kawai Naga sunjuya sun fice wannan wace irin ukubace wato shi sha faffe damai ankiyin fushi dashi nikuwa har iyata ta juyamin baya Wai ni sakaryace tunda nayadda namiji ya tabani, rushewa nayi dawani irin kuka me tsuma zuciya, cikin kukan naringa maganganu nida wannan Rayuwar gwara na auri Hamza nahuta.

Mikewa nayi zumbur nayi hanyar dakinmu sadiya nasamu Zaune tana karatu wayarta data Ajiye gefenta nazara nayi waje dama na haddace numbern Hamza bugu daya naimai yadaga Ay yanajin nice yarikecemin shi bayasamun kwanciyar hankali shiso yake kawai yaganni ban bawa zuciyata damar wani yin tinaniba nace yazo bayan sallar magrib lokacin gari yayi duhu saboda nasan Abba dayayi magariba yake dawowa gida.

Magrib nayi, nayi sallah sadiya da ido kawai takebina saboda yanzu Abun yafi karfinta can naji wayar sadiya tafa ringing Aida sauri nadaga, cewa yay yazo Yana kofar gida tareda kashe Kiran powder kawai nashafa domin bana cikin halinda Zan iyayin kwalliya, hijabin sallara nazurma nafita.

Awajen get nasameshi Yana ganina yarude babyna naji Dadi yau dakika bani damar zuwa gidanku, murmushi nayi nace hayaty Albishir Zan maka na Amince da Auranka Aibanyi auneba naji yakamo hannayena yarikesu gam waishinan murna yake, bazato ba tsammani Naga fitilar mota na haskemu dubawar dazanyi Sai Naga motar yayanmuce…..²¹ ²²

About AIS

Check Also

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 14 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Www.bankinhausanovels.com.ng             D’aukan papern Yaya Shuriem Yayi ya kekke Tata, Ni …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *