HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 2 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 2 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Suna na meerah sadau Dan maliki, tafada yayinda take juya fararen Ida nuwanta, Akwai wani Abu da kike bukata yafada Yana fuskantarta,shiru tayi can tace dama nakawo c.v Dina ne ko zansamu aiki A asibitinka Amma ni badan kudi zanyi wannan aikiba saboda ni Ina tausayin talakawa, da marasa karfi,

Shiru yayi Yana tunani Amma yar’me kudi Kamar sadau Danmaliki mezesa tayi aiki anan, katse Mai tunani tayi da fadin Dan Allah karkace A ah taimakone da ceton rayukan Al’umma,  Ajiyar zuciya yayi me karfi sannan yace” Wana bangare kikeso dadine yakashe meerah batasan sanda tasaki murmushiba harsaida fararan hakoranta suka bayyana,

Ina sauraranki, yace Mata Dan Kuma murmusawa tayi sannan tace, so samu muyi Aiki tare dakai Abin Alfaharine Agareni nayi Aiki tareda kwararran likita Kuma jajir tacce SHURIEM Ismail Mai dala.

Kallan ta yayi tayi matukar burgeshi Azamaninnan balallai bane Asamu Yar’ me kudi irin Haka ta damu da Rayuwar talakawaba, Kinga dai office din nawa baida girman da mutum 2 zasu zauna, zansa Abaki wani office Din daban Kinga saikinfi sakewa, Kuma aikinmu Yana bukatar jajircewa da Ayki tukru, Ay merah Bata barshi yakarasa maganarba tai zaraf tace, Dr. Nanma yayi office dinma yanada girma kujera da table kawai za’ a samun tacan taununa dannesa dashi, shikenan badamuwa tunda kinfisan hakan, yanzu yaushe Zaki Fara aikin, yanzuma ta fada tareda mikewa inason Naga majinyatan  da suke kwance, babu damuwa ya’amsa Mata, waya yakira saiga wata staff tashigo Dan rissinawa tayi tareda gaisheshi, amsawa yayi tareda Yi Mata Umarnin tazagaya da meerah cikin Asibin,. Toh ranka yadade, muje koh tafadawa merah binta tayi Abaya suka fita.

Shi kuwa shriem bayan fitarsu waya yayi Aka kawo mai kuje da Table da duk Abinda merah zata bukata, Amma haryanzu datunani fal zuciyarsa shidai yarinya tabirgeshi, Akalla wannan tayi sa’rsa, Amma shekarun Basu nuna Ajikntaba, murmushi yayi yacigaba da Aykin gabansa bayan wasu lokuta yatashi yafara shiri domin zai shiga tearter. 

Bayan dawowar meerah batsamu Dr. SHURIEM ba karewa office din kallo tayi Kamar tana nazarin wani Abun sannan tanemi guri tazauna, tareda dauko wayarta ta Fara chat.

Bayan yadawone yasameta zaune sannu tai masa, Amsawa yayi lokaci guda Kuma Yana hada kayansa nawuce saidasafe saboda inada wani uzurinda zanyi, meerah itama saurin mikewa tayi tareda Fadi” Dan Allah ko zaka Ajiyeni Dan bada mota nazoba badamuwa yay hanyar fita da sauri tabi bayansa.

Tafe suke Amota kowa da Abinda yake tunani meraah ce tai karfin halin cewa Dr. Kozan iya samun numbernka meyasa kikeson numberta yafada hankalinsa nakan tuki, saboda ka girmani ka karbi bukatar danazo maka daita inasone nahadaka da mamana tai maka godiya ta fada tanamai karkada idanu, basai angodeminba ni Dan Allah nayi, Dan Haka bana bukatar Sai angodemin da merah taga wannan shawarar bataiba saitai zaraf tace to kodan gaisawa muringayi Mana, murmushi yayi tare da fadin “dama Haka kikace dayafi ni arayuwata banasan mutum me kwanana inkinasan Abu Awurina kitambayeni kawai, murmushi nasara tayi tafito dawayar Yana gaya Mata numbern dialing tayi dataji tashi sannan takashe, murna fal zuciyarta.

Bayan ya Ajiyeta a  gidane yadawo part dinsa yawuce direct Dan yau ko momi bai nemaba saboda Agajiye yake, wanka yayi tareda sa farar jallabiya, yay sallah sannan yadan rintsa.

A bangaren meerah kuwa da gudu tashiga gida cin karo tayi da mamanta nafitowa daga falonsu Aybatasan sanda ta rungumetaba tana fadin mama munyi nasara wannan bazai wahalar shigowa Hannuba mamanta tace takuma rungumeta nayi murna sosai ya’ta Allah dai yacika Mana burinmu Amma saikin zage dantse sosai, Aidan jin Kai ne mama da ganinsa, Amma tunda yazo hannuna zaiyi laushi, mama bari naje ciki indan kwanta Dan har kaina yafara ciwo, dato maman ta amsa tana maiwucewa, itama meeran tawuce.

Hankalina Amugun tashe yake wayata gurin Yaya kar Akuma kirana Ina daki nakasa nutsuwa nadawo falo waiko zanga yashigo gurin momy na rokeshi, shiru shiru hardare babushi shahada nayi Mike dannaci Alwashin kozai dakeni yau saiyaban wayata hanyar part dinsa nanufa gurinnan shiru bakowa Haka nadake nwuce nashiga falonsa bakowa Afalon hkn yasa nashiga bedroom din nanma Naga bayanan  dasauri nakama dube duben inda zanga wayata nice hadda Bude wardrobe dinsa inata nema jinayi anbude kofar toilet Ina waigawa Naga yayanmu, Aibasan sanda nai mutuwar tsayeba…….

Firgita nayi sakamakon ganin Yaya danayi ba riga dagashi Sai tawul akungunsa dawani karami Yana goge Kai.

Kwanjinsane kawai yafirgatani lallai shiyasa inya   dakeni nake jin jiki da mamaki yake kallona, mekikeyi anan, sanin cewa yayanmu baya San karya, hakan yasani fadar gaskiya, muryata na rawa nace nazo karbar waya tane.

Shiru yayi Yana nazarina ni kwa na shagala da Kare masa kallo daya fahimci nazubawa kirjinsa ido sakamakon gashin Dana gani kwance, tsawa yadakamin tareda fadin”mekike kallone a jikina,  jikina    narawa na sunkuyar da kaina.

Hannu yasa yadago fuskata, tareda yarfamin zafafan maruka guda 2 kawai ganin wuta nayi ta gilma ta idona tsabar na Maru.

Dorawa yayi da fadin “wato ke rashin kunyar taki har takai Haka koh?, To Bari kiji ingaya Miki ni shuriem yanuna kansa nafi karfinki heedaya, yafada Yana nuna ni, ke yacigaba da nunani da yatsansa saidai sadaka Amasallaci,

Kuma ni Zan bada ke saboda wannan in muka barki saikija Mana Abun kunya, kukane yakwacemin nafice da gudu daga dakin Ina maijin kuna A zuciyata, 

Direct dakinmu nawuce  ko momy kasayi Mata Saida safe nayi saboda halin danake ciki, tararwa nayi sadiya tayi barci Haka nazauna naita kukana bame lallashina. 

Washe gari Haka natashi Kamar Mara lafiya saboda naji zafin zagin da yayanmu yaymin, momy taimin tambayar duniya nace Mata bakomai.

Bangaren meerah kuwa yau dawuri taje Ayki bayan ta can cada Ado, lokacin data isa  shuriem ma be zo aykiba, wayarta tadauko takira shuriem, tajima tana ringing sannan yadaga yace Mata Yana Hanya, cikin mintuna kalilan yaiso.

Cinkin kissa ta tarbeshi tareda Yi Masa  sannu da zuwa, Amsawa yayi cikin jindadi yanuna Mata Ayyukan dazatayi yafice Dan Yana ayki sosai, yauma Haka taribace shuriem da kalamant yakaita gida.

Yau yakasance Asabar bamuda school misali karfe 11:15am  Muna zaune A falon nida sadiya kawai Sai mukaji sallamar iya ai da gudu natashi naje narungumeta, inai Mata oyoyo dariya taketayi, nima ita nakeyi saboda munasan junanmu nida iyata, karasowa tayi ta kalli sadiya tareda rike haba tace, iye yar’ nema tabdi  wato ke bazakiyi min oyoyon ba to aniyarki tabiki malam yace nashe Kara guda gurin Dana isma’il sadiyace tayi murmushi tare da fadin, kece iya, zuwa ba sanarwa,  kawai saimu ganki.

Bazan sanarba tunda gurin Dana nazo Ismail ba girinkuba, nice nace iyata kizauna Mana nakira momy, zama tayi tana fadin hedayata Wai meyasa mi wayarkine bana samunki, sadiyace ta kyaftamin Wai Kar nagaya mata.

Nikuwa tabare fuska nayi nace ba yayanmu bane yakwace Ai Sai ganin iya mukayi ta Mike warware mayafinta tayi tana fadin “kan bala’i yaufa Akeyinta kiramin uwarsa Aida gudu naruga nasamu momy adaki nashaida Mata Kiran iya, momy da murnata tazo falon.

Turus tayi ganin iya taci damara wata harara ta gallamin Ashe iya taga momy Aikwa tace Ina wuta insakaki nagaji da Abinda kukewa yarinyar keda danki kunsata Agaba, kun hanata Shan ruwa, yarinya tarame ta kanjame to kiyiwa danki waya duk inda yake yakawowa Heedaya wayarta in bahakaba yau za’ayi karamin yaki Agidannan.

Momyce ta sassauta murya tace “karya take Masa iya shi shuriem ma me zaiyi da wayarta, iyace takuma harzuka tace “wato ita heedayance ke karya ba mugun dankiba to tunda bazaki kirashiba Heedaya zo muje kirakani Asbitin keeey taja hannuna mukayi hanyar fita…….

Ummice tayi saurin Shan gaban iya, ciki gimamawa tace Bari nakirashi zezo yanzu yakawo, base kinje bama, iyace ta murmusa tareda fadin nazata bazaki, kirashinba naje harcan  nakare Masa tanadi Kuma yabamu wayar Dan dole, hakuri momy taci gaba da bata, sannan ta juya da sauri tashige dakinta Sai gata tafito da waya dauke ahannunta.

Bugu daya shuriem yadaga sallama kawai momy ta amsa Masa tadora dacewa “shuriem duk inda kake Kuma duk Abinda kake kabari kazo gida Ina nemanka yanzu wannan umarnina ne.

Duk komawa mukayi muka zauna jiran yayanmu, jimawa kadan saigashi yashigo Arude, da sauri ya Isa gaban momy ya tsugunna tareda Kama kafafunta Yana fadin” momyna me yafaru,  shafa kansa tayi tareda fadin son dama iyace take nemanka.

Sai asannan yasan dawasu mutane A falon kallanta yayi yace “matar yaushe agari” iyace ta karbe dama yaushe zaka ganni, dama maganar wayar heedayace kadakkota yanzu kabani, Sosa Kai yayi tareda fadin hajiya iya bakisan Abinda yarinyarnan tayiba hannu tadaga Masa tareda fadin banaso nasani, kallon  momy iya   tayi kigayawa danki idan be bada wayarnan ba Akwai karamin yaki Agidannan ummice takalli shuriem tace “son dakkomin wayarnan yanzunnan wannan umarnina nabaka, tashi yayi batareda yace komaiba yanufi bangaransa.

Dawowa yayi ya mikawa momy wayar karba tayi ta mikawa iya murmushi nayi tareda rungume iyata Ina murna, yayane ya Mike tareda fadin ninawuce Zan koma wurin Ayki nikwa Araina nace Ala Rakata ki gona, cewa nayi musu inazuwa, domin nakagu naji muryar hayatyna Dan kwana 2 nayi kewarsa.

Da farin cikina na kunna wayar Ina kokarina Kira kawai Naga ba sim card lallai Yaya yaraina minhankali wani tunani nayi nace hmm inyasan wata besan wataba toilet nashiga nasheka wankana nafi falo,..

Natarar bakowa kitchen nanufa natarar momy da sadiya har sun kammala girki sannu naimusu tareda tambayar momy hajiya iya.

Kallona tayi shekeke tace “tatafi bangaranta saura Kuma kije kiyi Abinda Kika Saba kinda San halin shuriem ai zata tafi ba anan zata zaunaba.

Matsowa nayi kusada ita  nace kiyi hakuri momyna nida Yaya yanzu Ai bafada tsakaninku, Allah yasa dagske me tafada tana cigaba da aykinta, Kuma matsawa nayi nace Mata momy dama Naga Yaya Kamar dazu yanajin yunwa ko Zaki bani Abinci nakai Masa gurin Ayki, ba momyba hatta sadiya saidata kalloni, momyce tace “yau Kuma Heedaya caraf na’amshe eh aibanasan wannan fadan momyna, dariya tayi dakyau sannan tace ” Allah yasa da gaskene dama ke kike janyo muku sabani, Abinci tahadamin cikin basket tacemin nabari Abba ya Aiko mudi drivernsa ze karbar masa Abinci, kibari saiya saukeki.

Da fara’a ta na amsa dato inayi kamar Abun kirki zai kaini bayan wasu mintuna idi ya iso, fita nayi muka tafi ni kadai nake wani murmushiba mugunta idine yalura Dani yace “ranki yadade kikace Asibitin megida shuriem zankaki, da eh na amsa Masa jin jina Kai yayi nasan me yake tunani yasan bama taba hada Hanya da juna, Muna Isa nafita tareda ce Masa nagode malam idi, cewa yayi ranki yadade ko inkin Gama zakiyimin waya nadawo nadaukeki. Nagodema daka kawoni malam idi base kadawoba kwandona nadauka nayi ciki  gaisawa nayi da staff din da muka Saba dasu direct nawuce office dinsa Ina budewa Naga bayanan Sai wani sabon table din nagani dawata mace Akai,  gadama tasamu hedaya Yi Amfani da damarki nafada cikin raina.

Kallan banza nai Mata tareda fadin kekuma wane matsayi gareki daza’a baki wuri anan office din kallona kawai tatsaya tanayi nikuwa Allah, Allah nake takulani.

Wucewa nayi natafi kan kujerar da yayanmu ke zama nazauna merah kuwa da kishi yaturniketa Afusace tataso tazo gaban table din tasaya kewacece da Zaki zo kishigowa mutane office Kai tsaye be ishekiba harda zama man kujerar Dr. Shriem kallan banza nayi Mata tare fadin matarsa ni matarsace.

Wani zabura meerah tayi race ” kije kinemi mijinki can Amma shuriem yafi karfinki Yar’ mitsiyata danne fushina nayi nace Mata Ansa ranar aurena dashi to me kuwa Ake jira shaidu. Merah ce ta haukace takama zage zage nikuwa Abinda ke gabana nacigaba dayi drowern table din najanyo key din motarsa nagani hamdala nayi nadauka NASA ajakata nayi hanyar  fita merah kuwa Kamar zata haukace Dan masifa hanyar fita nayi Gam naji nayi karo da mutum……

Gam naji nayi karo da mutum dagowa nayi A furgece tunanina yayanmune saina ga nurse umaima don munsaba da ita sosai hargida Yaya yake kiranta ta duba mu in rashin lafiyarmu ta Mata ta tashi, murmushi taimin Nima namayar Mata gaisheta nayi ta amsa da fara’arta kin hadu da Dr. Din Dan nabarshi Yana duba wani patient Aida saurina nace ai sauri nakeyi dama Abinci nakawowa yayanmu na fada Ina nuna Mata kwandon Hanya tabani nawuce tareda ce Mata Sai Anjima.

Ai Ina fita natari napep nagaya Masa inda zai Kaini nashige, tunanine fal zuciyata yanzu idan Yaya yadawo yaji Abinda nayi nashiga 3, Dan dagani matarnan Dana gani bazatayi mutunciba, jinayi me napep din Yana cewa hajiya mun iso, sauka nayi tareda Bude jakar hannuna naciro kudinsa nabashi, get nabude nasamu bakowa A harabar gidan, falo nawuce  natadda momy nawaya jira nayi tagama, sannan nace mata nadawo momy, Allah yay Miki Albarka tacemin  na amsa da Ameen, momy Bari naje gurin iya nafada Ina mikewa, Ina zuwa dakin iya tarar da Abinci kala kala ita Kuma tanata faman barci, zama nayi naci nakoshi nasha ruwa nadauko wayata saboda takaici game nakamayi Nan barci Yayi Awon gaba Dani.

Bangaran meerah kuwa tana ganin nurse umaima tatareta da sauri tareda cemata sister Dan Allah wannan data fita wacece tacemin Wai it’s zata auri Dr. Nurse umaima kuwa dama ta tsani meerah saboda yadda take amsa musu gaisuwa a wulakance, ankusa bikinma tafada tareda Ajiye files dinta tafice meerah kuwa Kuma haukacewa tayi mamanta takira tagaya Mata yadda sukayi Ai kuwa itama mamanta ranta back matuka   ce Mata tayi duk yadda zatayi kartadawo gida Sai yay Mata Alkawarin Aure Kuma Nan bada dadewaba kikieso Ayi bikin cikin murna ta kashe wayar tacigaba da Aykinta.

Shuriem kuwa Yana dawowa office yatadda  kwandan Abincin  da Heedaya ta kawo budewa yayi yay murmushi tareda fadin idi driver yazo kenan, ruwa yadauko yazauna yazuba Abincinsa hankalinsa kwance yakeci Yana Danna wayarsa meerah kuwa takai har wuya ganin be kulataba.

Ai Yana Kai spoon din karshe ta fashe da wani irin kuka, ido yabita dashi, danshi Yama manta da ita awurin lafiya dai meerah meyake damunki, cikin kuka ta Fara magana Kaine Kaine damuwata shuriem kasan yaushe nadauka Ina dakon soyayyarka, soyayyarkace tasa nazonan Asibintin neman Ayki bakamar yadda nagaya maka bane inasonka shuriem, dazu wata yarinya tazo office dinnan tagama cimun mutunci Wai itace wadda zaka aura Wai har ansa muku Rana dawani kukan tasake rushewa tasowa yayi yazo Dede kanta yatsaya yace Mata “meerah goge hawayanki kiyimin bayani dalla dalla naji, goge hawayenta tayi tagaya Masa karya da gaskiyar Abinda sukayi da Heedaya harda cewa Heedaya ta falla Mata Mari, takarashe da fadin Amma na  yafe Mata saboda Kai my shuriem nidai burina ka Amince da soyayyata, shiru yayi Yana nazarin wacece,  wannan me karfin hali Haka, tace Kuma ita takawomai Abinci waya yadauka yakira momy bayan sungaisa yatambayeta dawa idi sukazo Dan lokacin dayazo  bayanan Yana wani Aiki  momyce tayi murmushi kana tace “Yar’ gidankace Heedaya Ashe bata samekaba da eh ya amsa ransa ya baci sallama yay Mata yakashe Kiran hakuri yashiga bawa meerah tareda Yi Mata Alkawarin zuwa dare ze gaya Mata hukuncin da yayanke ,

Murnace takamata jin sunkusa samun nasara, lokacin tashinsa yayi yaduba baiga mukullinsa na motaba meerah yatambaya bayan Heedaya waya shigo, um to sister umaima tashigo takawo wasu files Amma ko zama batayiba da tatarar bakanan ta juya.

Murmushin mugunta yayi yace Mata Saida safe taupiq yakira yace yazo yakaishi gida cikin lokaci kalilan saiga taufiq kallan taufiq yay yace mujeko, sun Fara tafiya Ahanya yake tambayrsa meyasamu motar, Yar’ takurar nance ta biyoni har office tadaukemin key din shi kuwa taufiq mezeyi inba daryaba,Haka suka iso gida Yana tai Masa tsiya shikuwa shurem shiru yayi saboda ransa Abace yake.

Koda suka iso ko kallonsa banyiba nagaida yaya taufiq natashi natafi gun iyata shima taufiq biyoni yayi bayan sun gaisa da momy.

Shi kuwa gogan naku kusada momy yakoma tareda fadin” momy inason zamuyi wata magana dato ta amsa Masa tareda tashi tayi daki shi Kuma ya mara Mata baya.

Momyce zaune gefen gadonta shi Kuma ya zaune Akasa Sosa Kai yakamayi momy tace son yadai nisawa yayi yafara magana cikin kunya yace ” momy nasamu wadda Zan aura Kuma har mun shirya kanmu………¹⁵ ¹⁶

About AIS

Check Also

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 14 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

Www.bankinhausanovels.com.ng             D’aukan papern Yaya Shuriem Yayi ya kekke Tata, Ni …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *