HEEDAYA CHAPTER 44 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 44 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Washegari karfe takwas da wani abu Mumy ta isa gidan Baffa, Bangaren Hajiya Amina ta nufa ta sameta tare da 

Sudais, bayan sun gaisa da Hajiya Amina, Sudais ya gaisheta da ladabi sannan ya mike ya fita parlon, Hajiya Amina 

ta sauke wani ajiyar xuciya tace “Ya na ganki haka ko baki da lafiya ne?” Mumy tayi kasa da murya tace “Wajen Dr 

na xo, to ban ga motarsa a parking space ba, shine na fara shigowa nan” Hajiya Amina tace “Yana can asibiti bai 

dawo ba” Mumy tayi tagumi bata ce komai ba, Hajiya Amina ta kara sauke ajiyar xuciya tace “To mu dai sae dai mu 

ce Allah ya kyauta da yanda abubuwa suka xo kamar wasan kwaikwayo, amma fa ni wlh ba wai kin jinin yarinyar 

nan Heedayah nayi ba har ga Allah, kawai naga ba a kyauta maki bane, ni kuma baxan iya juya maki baya ba shi sa 

nima nace baxan riketa ba, banda haka ai yaro na kowa ne wllh” Mumy dai ta ki cewa komai amma ji take kamar ta 

fashe da kuka a lkcn, Hajiya Amina tace “Kinsan dama Sudais tun tana makauniyar ta ya nuna damuwarsa sosai a 

kanta, to shine fa yanxu na aika aka kira min shi nake tambayarsa ko yana da interest ne a kanta kada in tauyesa….” 

Mumy da ta shiga yi mata wani irin kallo da sauri tace “Sai yace maki me?” Hajiya Amina tace “Rabu da shi ni xai 

raina ma hankali kamar shi ya haifeni, wllh kinji har na rantse yana son yarinyar nan, Wai ni xai kawo ma iskanci… 

dama can ai ba wai gaba daya na raba sa da ita ba sbda ke ce nace ya daina xuwa gidan wajenta kada xumunci a ya 

samu matsala tunda baki so” Mumy da duk ba wnn take son ji ba tace “Sai yace maki me ni dai??” Hajiya Amina ta 

tabe baki tana gyara xama tace “Ai karya yake bai fada min gaskiya ba, wai cewa yyi shi ba son aurenta yake ba, 

kawai dai ya dauketa tamkar kanwarsa ce sbda maraicinta a lkcn, amma bbu wani soyayya na aure da yake mata, 

wai fa ni xai raina ma hankali, to baya sonta xai dinga kashe mata uban kudade yanda ya dinga yi a lkcn, ni dai nace 

masa kar fa ya ji komai tuni na janye bakin da nayi a kan taraiyarsa da ita, idan ma aurenta xai yi ni baxan hanasa ba 

sai in fada ma Barrister a san abun yi, amma yaron nan ya dage shi ba sonta yake da aure ba yana da warce xai 

aura….” Mumy dake ta yi mata wani kallo ta katse ta tace “Amma Wlh Amina baki da kunya, ynxu don kin ga 

ubanta Gwamna ne shine kike nema d’an ki ya aureta?? Kike makala masa ta karfi da yaji? Wnn kwadayi har ina 

Amina” Hajiya Amina ta mike tace “Ehh na nema din, kuma kwadayi ai a gun danginki nayi gado, duk ba ke kika ja 

mana ba da muguwar xuciyarki da bakin halin ki, gwara ni nawa bai wani fito sarari ba, ai yau ga irinta nan kashi 

ma ya fi ki daraja a gun iyayen yarinyar, dubi yanda aka walakanta ki jiya gaban jama’ah kika yi tsamo tsamo da ke 

ba kyan gani, muna nan da ke in sha Allah sai na lallaba Sudais ya nemi auren nata tunda dama sonta yake nice na 

rabasa da ita ta karfi da yaji sbda sharrin shaidan, kuma naga yarinya ma a lkcn ai tana son sa….” Mumy tayi wani 

dariya ta mike tana mata wani irin kallo tace “Sai dai ki mutu ki ru6e amma wllh wllh Sudais baxai auri Heedayah 

ba, me kika ta6a tsinana mata daga ke har Dakta din? Gwara ni mijina shi yyi mata komai na rayuwa, Allah ne 

gatanta shine gatanta, shine tsaye kan komai nata, idan ma yau d’an Barrister yace xai auri Heedayah ya cancanci a 

bashi, to shi kuma Sudais a wa?? Idan ma auren ne Shuraim ya dace ta aura” Mumy bata jira cewarta ba ta nufi kofa 

da sauri tana cewa “Ni dama ba wajen ki na xo ba, ganin motar Dakta baya gidan ya sa na shigo wajen ki ashe da 

rabon inji kayan takaici, kwadayayyiya kawai” Bangaren Kaka ta shiga, ta sameta xaune da Hajiya Hauwa dake 

gyara mata kayanta a akwati, kallo daya kaka tayi ma Mumy ta ci gaba da bada labarin da take, Mumy ta xauna cike 

da ladabi tace “Ina kwana kaka?” Ba tare da kaka ta kalleta ba tace “Lafiya lau” Mumy ta gaisa da Hajiya Hauwa, 

Hajiya Hauwa ta tambayeta ya yaran, tace “Alhmdllh” Mumy na kallon kayan da ake xuba ma kaka a akwati tace 

“Tafiya xa kiyi kaka?” Kaka tace “Ehh Gwamnet house xa ni a kano, yanxu ai mune gwamnati tunda xuciyar mu da 

kyau bama nufin d’an kowa da sharri” Mumy dai bata ce komai ba ta hadiye wani abu da kyar, Hajiya Hauwa ta 

mike tace “Toh bari in dauko maki turaren kaka” Kaka tace “Yi maxa, duk da idan naje can baxan rasa ba amma kar 

inje masu tsiya tsiya ko?” Murmushi kawai Hajiya Hauwa tayi ta fita, Kaka ta kalli Mumy tace “Ai Aminar na can 

bangarenta baki duba bane….” A hankali Mumy tace “Aa wajen ki na xo” Kaka tace “Wajena kuma?? Ikon Allah, to 

ina jin ki, kinga shirye shirye nake kar lkci ya baci a banxa a hofi, a jirgin Uban Deedayah xa a tafi da mu wai jirgin baya jira inji Kumbo” Mumy tace “Allah sarki, to Allah ya kai ku lafiya Kaka” Kaka tace “Ameen, Ina sauraron ki” 

Mumy ta d’an yi shiru, kaka ta mike tace “Ni dai fa wanka xan shiga Maryam, baxan 6ata ma manyan mutane lkci 

ba” Mumy tace “Dama kaka a kan Shuraim ne” Kaka ta koma ta xauna tace “Waye kuma Shureen?” Mumy tayi 

shiru, kaka tace “Nace waye Shureen” Mumy tace “Shuraim dai daya, jiya ya dawo mun rasa gane kansa wllh, nayi 

nayi ya ki gaya min meye damuwar ya ki, shi ma Barrister ya samesa har daki ya ki gaya masa, yau ina ta xuba ido 

ko sallan Asuba bai fito ba, kuma kofar tasa a rufe yake yaki budewa” Kaka da ta saki baki tana kallon Mumy tace 

“Toh ko yayi masu bakin halin ne suka koresa gun aikin” Mumy dai bata ce komai ba, kaka tayi kasa da murya tace 

“Allah kuwa xai iya yiwuwa haka ne, me hali ai baya fasa halinsa, to amma ko koransa suka yi ga dai Uban 

Deedayah yana sa baki xa a mayar da shi, ai gwamna ne shi” Mumy dai tayi shiru, kaka ta rike kanta a hankali tace 

“Oh oh Allah, Ni wllh lamarin Shureen na damuna sosai… mutum magidanci gandarere haka amma har yanxu daga 

ke har Amadu kun xuba masa ido bbu me ce masa Ina matar aurensa, bbu me ce masa komai fa, to ko dai 

miskilancin nasa xai aura ne bani da labari? ga dai Sudais wllh jiya ya kawo min yarinyar da xai aura xankaleliya da 

ita, ga ta dai ba yar kowa ba yar talakawa ina jin a tudun wada ma take da iyayenta, to ai da kyau ya fi babu, 

yarinyar sai kyau da hankali da nutsuwa ga kunya to ai hakan da kyau, bai ma yarda ya kai ta gun kwadayayyiyar 

uwarsa ba, shi kuma Junaidu Uban Deedayah yace ya basa Deedayah duniya da lahira daga ni sai shi sai uwar 

Deedayah muka san wnn xancen, sirri ne bbu wanda ya sani, ko Rakiya bata sani ba wllh, nan Junaidu ya xo ya fada 

min damuwarsa na son Deedayah ni ko na ja sa har gidan uban Deedayah a Abuja, ashe wata fitinanniyar tsohuwa 

da na ta6a haduwa da a kasuwa da dadewa tana bala’i da jama’a kamar karya yayar uban Deedayar ce, gaskiya na 

girgixa ainun har buhun tafarnuwar na mata alkawari a lkcn Allah bai yi xan bata ba, to in gaya maki har ita tayi 

Na’am da Junaidu tunda uwarsa ce ta rike Deedayah da amana bbu ha’inci, kuma tace Deedayah na gama sakandari 

bbu ruwanta da wani Jami’a xa ayi aurenta da Junaidu, to yanxu sai naje xa mu fara shirin bikin ma, daga nan kuma 

sai a kira kowa a sanar masa, kece dai baxa a sanar ma ba sbda ba a san xuciyar ki ba” Mumy dake ta xufa daga 

xaune sai kallon Kaka take xuciyarta na bugawa sosai, Cike da karfin hali tace “Ita Heedayar na son shi ne???” Kaka 

tace “Ko bata son shi idan ita ba butulu bace ai baxata ki d’an Rakiya ba, Junaidu kuma ai mutum ne ga kyau ga kudi 

ga ladabi, snn abunsa bai rufe masa ido ba, halinsa sak na uwarsa Rakiya, ashe ma wai sun ta6a haduwa da uban 

Deedayah da dadewa sai da ya amshi lambar Junaidun ya gani a wayarsa yyi saving, to yanxu dai Shureen ne kadai 

bamu san kansa ba a xancen aure, amma tunda xan aurar da Sudais in aurar da Junaidu ai shkkn sai yyi ta xama a 

tuxurunsa shi” Mumy dai bata ma san abinda kaka ke cewa ba banda xafi bbu abinda take ji, gashi ta kasa xaune 

waje daya, Kaka tace “Toh yanxu xuwa xan yi can gidan in ji me ya same Shureen din duk da bashi da mutunci 

koko?” Mumy dai ta kasa cewa komai, gaba daya ta shiga wani mugun tashin hankali, Junaid ya auri Heedayah? 

Inaa this is impossible, Bata san lkcn da ta girgixa kai ba da karfi tace “Baxai yiwu ba wllh” Kaka ta saki baki tace 

“Meye baxai yiwu ba Maryam?” A firgice Mumy ta kalleta tace “Au, A’a ba komai, ba komai” Kaka ta dinga 

kallonta can ta mike ta tabe baki tana karasa rufe jakarta tace “Toh Allah ya kyauta, auren Junaidun da Deedayar ne 

baxai yiwu ba tunda ke kika halitto su ko, to ai kuwa sai dai bakin ciki ya kashe ki Maryam, Rakiya dai kina ji kina 

gani sai ta xama surukuwan gwamna in sha Allah, sadaukarwarta da jajircewarta baxai tashi a banxa ba, sai in har ta 

cuci Deedayah wanda Allah shaida bata cuceta ba a shekaru shidda da suka yi tare…. Abinda ma ta hakura ita ma 

Rakiyar xata koma gidan mijinta tunda Gwamna ya sa baki a lamarin har gwamnan Kaduna nan sai da yyi mata 

nasiha kuma ta hakura tace xata koma” Mumy ta mike gaba daya tashin hankali ne bayyane fuskarta ta nufi kofa 

kaka ta bi ta da kallo snn ta tabe baki ta ci gaba da abinda take tace “Aniyar ki ya bi ki gantalalliya” Gidan Hajiya 

Sadiya Mumy ta tafi, tun daga parlor Sadiya na xaune da yaranta Mumy ta rushe mata da matsanancin kuka, Sadiya 

ta mike da sauri ta ja ta suka wuce ciki da mamaki tace “Subhanallahi, lafiya Maryam me ya faru?” Cikin kuka sosai 

tace “Sadiya kinji wai da Junaid xa a hada Heedayah aure….” Sadiya ta gwalo ido tace “Waye kuma Junaid?” Mumy 

ta kara rushewa da kuka tace “D’an wajen Rahinah, shi wai xa a ba Heedayah” Sadiya ta bude baki tace “Ke a ina 

kika ji haka?” Mumy tace “Daga wajen kaka nake take gaya min yanxu, snn wai Rahinah xata dawo gidan Barrister, 

ni wnn ma bai wani dameni ba, wllh har raina ina jin idan Shuraim bai auri Heedayah ba xan iya mutuwa, takaici xai 

iya kasheni, kawai na tashi a tutar bbu kenan, shkkn a haka xan kare bbu riban komai, ga kishiya kuma xata dawo, 

snn Salima ta sa na kai uban kudi gun mutumi wai Shuraim xai ji sonta da sha’awar aurenta har ya kasa daurewa sai 

ya furta, to yau gashi shekara daya kenan bai ta6a xancenta ko makamancin xancenta ba balle har yace xai aureta, ni 

yaya xanyi da raina Sadiya?? Sadiya ta rasa abun cewa, can dai tace “Toh ke a ina kika ga kaka ta fasa maki wnn 

labarin, kakan da kowa ya santa da xuki tamalle….” Mumy tace “Wllh wnn ba xuki tamalle bane, cewa tayi ba a ma 

son kowa ya ji, kuma ita kanta Rahinar ma bata da labari sai kwanan nan xa a sanar mata tunda Heedayah ta gama 

secondary, tun jiya an rasa gane kan Shuraim ban san me ke damunsa ba, uban ma yyi yayi ya fada masa damuwarsa 

amma ya ki, tun asuban fari nake xaune parlor nake jiran fitowarsa ya tafi masallaci, wllh bai fito ba naje na 

kwankwasa kuma bai bude ba, shine na xo fada ma Baffansa halin da ake ciki tunda uban yyi watsi damu bai sake bi 

ta kansa ba, ban samu Baffa ba shine ya shiga gun kaka, a nan take gaya min wnn bakin labarin” Sadiya da tayi shiru 

tana sauraronta tace “Jiya tun yaushe kika lura Shuraim din na cikin damuwa?” Mumy tace “Tun bayan dawowar mu daga graduation da ya shiga daki bai sake fitowa ba” a hankali Sadiya tace “Dadina da ke rudewa baya sa ki fahimci

komai wllh Maryam, daga dawowa graduation shkkn sai shiga damuwa, to wllh son Heedayah ce ya jefasa damuwar 

nan bbu tantama, ba ya ganta jiya ba har sun yi hoto, kinga dai bakiyi asaran kudin ki ba kenan kamar yanda kika 

ce” Lkci daya Mumy ta dakatar da kukan da take tana kallon Sadiya da idanuwanta kamar xa su yi magana, Sadiya 

tayi wani dariya tace “Alhmdllh, yanxu komawa gida xa kiyi cikin dubara kiyi masa xancen Heedayar sai ki ga 

reaction dinsa, lallabasa xa kiyi sosai” Mumy ta goge hawayenta da sauri tace “Toh bari in je, in sha Allahu son nata 

ne ma yasa shi damuwar” Ko minti daya bata kara a gidan ba ta fice ta koma gida, a waje tayi parking ta shige 

compound, Rabi’ah na xaune parlor tace “Shuraim ya fito?” Rabi’ah ta girgixa mata kai tace “Amma Abba na dakin 

nasa, ya sa na kai masa breakfast” Da sauri ta wuce dakin, Abba na tsaye kansa, shi kuma yana xaune gefen gado 

with cup of tea a hannunsa, kana ganin idonsa kasan bai yi bacci ba daren jiya, Abba ya kalli Mumy bai dai ce komai 

ba, da damuwa Mumy tace “Barrister ya gaya maka meye matsalar?” Abba yace “Ba sai ya gaya min ba, koma 

menene Allah ya yaye masa” Mumy ta hade rai, Abba na kallon Shuraim yace “Idan kayi breakfast din ka sameni 

dakina” daga haka ya fita dakin, Mumy ta bi sa da harara ta tafi ta kulle dakin ta sa makulli ta dawo ta ja stool ta 

xauna tana kallonsa da damuwa tace “Ka gaya min gaskiya Shuraim, jiya lafiyan Allah muka fita gidan nan da kai 

xuwa wajen graduation din Heedayah muna dawowa kuma shine har yanxu aka rasa abinda ya dame ka, tell me the 

truth son did you in anyway have feeling for Heedayah?” Shuraim ya daga kai yana kallonta, ta kwantar da murya 

tace “Kar ka ji komai ka gaya min I am ur mother, nasan tunanin ka idan kace kana son Heedayah kilan ka samu 

matsala ta wajena, to ba haka bane, in dai nice I won’t stop you from loving Heedayah, you can go ahead and ask for 

her hand in marriage from her parent” Kallonta kawai Shuraim yake, dai dai nan aka buga kofar dakin, Mumy ta 

kalli kofar tace “Waye wnn” shiru ba ace komai ba, ta mike ta isa kofar ta bude, kaka ce tsaye tace “Xaki ce waye 

bayan kinje kin daddago ni Shureen ba a san me ke damunsa ba” Bata jira cewar Mumy ba ta shiga dakin tana kallon 

Shuraim tace “Auxubillahi, me ya same shi haka? Ko jifansa aka yi gun aikin” Mumy ta wani harareta, sai a snn ta 

fara da ta sanin xuwa wajenta ma ta sanar mata, to amma ai xuwanta yyi amfani tunda ta samu information da yawa, 

Kaka kamar xata yi kuka tace “Me ya sameka haka Shureen, me aka yi maka” Shi dai bai ce mata komai ba, ya ajiye 

cup din shayin ya mike ya wuce bathroom, kaka ta bi sa da kallo tace “Toh kinga tsiyar ana masa magana ya shige 

bandaki ko? Dubi fa yanda ya wani xabge kamar wanda yyi jinya, duk da a rame ya dawo mana daga legas din 

amma ai bai kai haka ba, asiri aka masa a can ne bamu sani ba, shi kuma Amadu tunda idan wani abu ya samesa ba 

shi yyi asara ba shi yasa ya ki bin ta kansa, to wllh idan abu ya samu Shureen sai ya samu kowa, duk cikin jikokina 

waye me sona banda shi…” Sai kuma ta fashe da kuka tace “Ni sai in fasa xuwa Gwamnet house din, baxan tafi in 

bar jikana a haka ba ban san me ke damunsa ba, damuwa dake kisa lkci daya yanxu, idan abu ya samesa ai na shiga 

uku” Cire mayafinta tayi ta linke ta ajiye ta xauna gefen gadon ta ciro wayarta ta mika ma Mumy tace “Kira min 

Umaru, ni na ma fasa xuwa Gwamnet house din su yi tafiyarsu” Mumy ta ji sanyi sosai a ranta sanin in har Shuraim 

xai bude baki yace Heedayah yake so kenan ai sai inda karfin kaka ya kare, amma tsoronta yanxu bata ma san ko 

son Heedayar bane ke damunsa kawai ita dai lalube take cikin duhu tana fatan shi din ne, idan kuwa ba shi bane 

shkkn ta shiga uku. Heedayah sun fito tare da Mami da twin sisters dinta xa su shopping mall, Mami xata yi ma 

Ashnaah da Ashfa shopping kasancewar a ranan karfe sha daya xa su yi set off for kano, Yakumbo da Farida kadai 

suka bari a ciki don Ammi ta tafi gidan wata frnd dinta kafin su wuce, Mami na gyara ma twins din takalmansu aka 

bude gate din gidan, Heedayah ta daga kai don ganin wanda xai shigo, tsaye yyi bakin gate din yana kallonta kamar 

yanda ita ma ta take kallonsa…

About AIS

Check Also

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} Www.bankinhausanovels.com.ng  Dana ga Anty Meerah …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *