HEEDAYA CHAPTER 40 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 40 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Baffa na kallon Shuraim da ya ki dago kansa yace “It’s time for Magrib and you will be going for duty, idan anyi sllh 

ka ajiye Heedayah gida kawai, we will talk tomorrow in sha Allah…” Shuraim ya mike yace “Allah ya kai mu” Daga 

haka ya nufi kofa Baffa ya bi sa da kallo har ya fita. Ana idar da Magrib Shuraim ya shigo gidan, ya karasa kofar 

dakin kaka ya bude yana kallon ciki, Heedayah na xaune saman darduma ta idar da sllh, Kaka na rike da tsintsiya 

tana tattare tattaren dakin ta juyo tana kallonsa tace “Ka ci abinci kuwa Shureen?” Yace “Na koshi” Tace “To har 

xaka wuce?” Yace “Ehh” tace “Atoh gaskiya ka jira ta ci abinci gashi nan na je na amso mata, sllh tayi yanxu” 

Shuraim yace “Xan yi wucewata…” Kaka tace “Toh ka tafi, ko ni ba sai in kai ta ba” Heedayah dai kanta na kasa ta 

ki dagowa, ba don Khaleel da yace mata xai xo anjima ba dama da bbu inda xata je gwara ta kwana a gidan kawai, 

but he said he is coming after Magrib tasan kilan ma yana can yanxu, Kaka tace “Kinga ki rabu da shi yyi 

wucewarsa ki dau abincinki ki ci, ko ni da Umaru ba sai mu kai ki gidan ba, wa xai ja ma aji a nan, ni ko ke?” Heedayah tayi kasa da murya tace “Ni a koshe nake na ci abinci” Kaka ta mike tace “A saboda me? Me kika ci, kar 

fa ki biye ma Shureen, ki ci abincinki ki koshi, idan kuma shayi xa ki sha sai ki hada” Heedayah tace “Na ci abinci 

kafin mu taho” Kaka ta juya tana kallon Shuraim kafin ya ce komai yace “Ina waje” daga haka ya juya yyi ficewarsa, 

Kaka tace “To ko in juye maki abincin a cooler ki tafi da shi?” Heedayah ta girgixa kai tace “Aa na koshi da gaske” 

Kaka tace “Toh shkkn, ni dai na fita hakkin ki, idan kun je ki gaida Rakiyar” Heedayah ta mike ta dau mayafinta da 

karamin jaka ta nufi kofa tana tafiya kamar bata son yi, duk gaba daya a sanyaye take, kaka tace “Ni ban ma fiye son 

kina bin Shureen din nan ba, shi ma ba sanin xuciyarsa muka yi ba har yau” Heedayah dai bata ce komai ba ta fita ta 

kullo mata kofarta, sama ta fara wucewa ta shiga dakinsu Zainab, ta samu Zainab xaune tana Azkar a saman 

darduma, Zainab tace “Har xa ku wuce?” Heedayah tace “Ehh xan wuce” ganin yanayinta Zainab tace “Are you 

fine?” Heedayah ta sakar mata murmushi a hankali tace “Sure” Kallonta kawai Zainab ke yi, Heedayah tace “Yaushe 

xa ki xo gidanmu, baki ta6a xuwa ba” Zainab tayi murmushi tace “idan Kaka xata je xan bi ta in sha Allah” 

Heedayah tace “Toh shkkn, bye, sai da safe” daga haka ta fita dakin ta wuce dakin Mum din Zainab tayi mata 

sallama ita ma sannan ta fita. Har Heedayah ta isa gate gabanta faduwa yake, ta tsaya bakin gate din tana leka waje, 

ido hudu suka yi da shi yana xaune mota amma bai rufe motar ba, ta dauke idonta da sauri ta koma gefen gate din ta 

la6e, ji tayi kamar ta juya kawai ta koma ciki, ta fi minti biyu a tsaye bata sake leka waje ba, Shuraim ya sauka 

motarsa ya tafi gun gate din, tana ganinsa ta fara kame kame ba tare da ta yadda sun hada ido ba, tana tatta6a jakarta 

tace “Ina gyara abu na ne” yace “Wuce mu je” Ba musu ta bi gefensa ta fita gate din ta wuce gun motar ya bi bayanta, 

ta bude front seat ta shiga, sai tsinne kai take kamar mara gaskiya, ya shiga maxaunin driver suka bar layin, har suka 

dau hanya Heedayah jujjuya zip din dake jikin jakarta kawai take, she is very uncomfortable with him, shi ma kuma 

bai kalli inda take ba, bayan tafiyar kusan minti ashirin Shuraim yyi parking dai dai gate din gidan Mami, ta kai 

hannu xata bude motar taji a rufe, ta sauke idonta kasa bata dai ce komai ba, shi dai idonsa na gaban motar, gabanta 

sai faduwa yake gashi ta kasa kallonsa, da dane ce masa xata yi ya bude mata motar, sun fi minti biyar a haka, can 

taji ya bude lock din motar, da sauri ta bude motar ta sauka ta rufe ba tare da ta kallesa ba ta wuce ciki ya bi ta da 

kallo… Sai da ta shiga gida taji hawaye ya kawo idonta, ta tafi can parking space ta fashe da kuka, tayi mai isarta 

sannan ta goge bakinta da mayafinta tace “Allah ya isa” Kamar me counting step ta nufi main entrance ta bude kofar 

a hankali, ido hudu tayi da Khaleel dake xaune parlon tare da Mami, da mamaki Mami tace “Wa ya dawo da ke?” 

Heedayah ta karasa cikin parlon a hankali tace “Ya Shureen” Mami tace “Yana ina?” Heedayah tace “Kila ya wuce” 

Tana kallon Khaleel ta xauna kasa kusa da Mami tace “Ina yini” Kallonta yyi yace “Lafiya lau” Mami tace “Kin ci 

abinci?” Girgixa kai tayi, Mami tace “Toh ki tafi ki diba” tace “Mami Farida fa?” Mami tace “She is upstairs” 

Heedayah tace “Yaya fa?” Mami tace “Bai dawo ba” Mikewa tayi ta nufi kitchen, Khaleel ya bi ta da kallo, ta juyo 

suna hada ido ta sakar masa murmushi ta karasa cikin kitchen din, Mami na kallonsa tace “Ina jin ka Khaleel” Ya 

shafa kansa yana murmushi yace “A can aka haifeni na taso nayi karatu duk a can….” Mami tace “So ur parent are 

still there” Ya sauke idonsa kasa cikin sanyin murya tace “Theye are late” Mami ta dinga kallonsa with pity kafin ta 

sauke ajiyar xuciya tace “Allah ya gafarta masu” yana kallonta a hankali yace “Ameen” tace “But all ur relatives are 

in gombe still?” Ya sauke idonsa kasa ya gyada mata kai, Mami tace “What do you do for a living?” Shiru yyi na few 

seconds, can ya daga kai ya kalleta yace “Business nake yi” Mami tace “That’s good, what are ur qualifications?” Ya

shafa kansa a hankali yace “Diploma, Bsc, Msc…. I am an Architect” Mami tace “Maa sha Allah, kana da ‘yan uwa a 

nan garin ne?” Ya girgixa mata kai, tace “To kanninka ko yayyinka fa?” Ya sauke idonsa kasa, Mami dai sai kallonsa 

take, deep down her she knows she isn’t suppose to be asking him any of this, bai santa ba bata sansa ba, it’s his 

private life, she isn’t suppose to intrude but haka kawai taji she wants to know more about him, tana son saninsa 

sosai, may be because taji ya kwanta mata har ranta, kwata kwata bashi da hayaniya ga ladabi, ga kuma hankali, all 

in all his smile is just like that of her Junaid, Khaleel yace “I am an only son” Jin Mami bata ce komai ba ya daga kai 

ya kalleta, kallonsa kawai yaga take yi, tayi masa murmushin karfin hali tace “To Allah ya dafa maka, and u are still 

not married??” Ya gyada mata kai tace “Allah ya kawo ta gari” yyi kasa da kansa yace “Ameen” Tace “Amma a 

kawo maka abincin ko kadan ne ka ci” yace “Na ci abinci daxu Ummi” Mami tace “Alright, shkkn” Heedayah ta fito 

kitchen ta tafi dinning ta xauna da plate din abincin da ta debo, mikewa Mami tayi tace “Ina xuwa” daga haka ta 

wuce sama, Heedayah ta mike ta dawo parlon ta xauna kasa tana kallonsa tace “Yaushe ka xo?” Yace “Not less than 

15 mins ago” Tace “Okay” yace “Daga ina kike?” Tace “Gidan Grandma dinmu, me yasa baxa ka ci abinci ba?” Yace 

“Na koshi” tayi shiru tana kallonsa, Yace “Waye kika ce ya ajiye ki?” Heedayah ta turo baki kamar baxata ce komai 

ba sai kuma tace “Yayanmu” Yace “But you look disturbed” shiru tayi tana kallonsa, can tace “Nothing, kawai nayi 

bacci ne na tashi sae aka maido ni gida” Khaleel bai ce komai ba, bayan wani lkci ya dago kai ya kalleta yace “To ki 

ci abincin” Ba musu ta ci gaba da cin shinkafar gabanta, ganin ynda yake kallonta ta wara masa ido tace “Ko xaka 

ci?” Yyi murmushi ya girgixa kai yace “Aa, lomar ki nake gani” tayi dariya tace “Toh baxan ci ba” ajiye abincin tayi 

gefe tayi tagumi, ya sakko kasa ya xauna a hankali yace “Aa yi hakuri” Bude kofar parlon aka yi Junaid ya shigo da 

sallama, Kallon Khaleel yake har ya karaso cikin parlon ya basa hannu suka gaisa da murmushi fuskarsa, Junaid 

yace “Ya jikin?” Khaleel yace “Alhmdllh na ji sauki” Junaid yace “Allah ya kara lafiya” Heedayah na kallonsa tace “Ina yini Yaya” yace “Lafiya lau, yaushe kika xo” tace “Yanxu na xo” Yace “Me yasa baki kwana wajen kakan ba” 

murmushi tayi tace “Aa ba komai” Sama Junaid ya nufa, Khaleel ya kalli Heedayah yace “What’s his name?” 

Heedayah tace “Ya Junaid” Ta kalli Junaid da har ya wuce sama ta wara ido tace “Kasan fa kuna min kama da shi, 

just that you are a bit dark in complexion, and ur dimple… Not as deep as his” Khaleel yyi murmushi yace “He is 

nice, I like him” Heedayah tace “Sure, amma fa da yana neman tsokanata yanxu dai ya daina” Khaleel ya langwabar 

da kai yace “Ko dai son ki yake?” Ta turo baki tace “Aa, kawai dai ni kanwarsa ce” Yace “Toh shkkn, xan koma 

yanxu…. Kije kice ma Ummi na wuce” Heedayah tayi shiru tana kallonsa, a hankali tace “So early?” Yace “Ai na 

dade” Tace “Toh yaushe xaka dawo” yace “Duk sanda kika ce” ta mike tace “Bari in kira Mami” bata jira cewarsa ba 

ta wuce sama, a stairs ta hadu da Mami tare da Farida, Heedayah ta rungume Farida tace “I missed you sis” Farida 

tayi murmushi tace “Welcm back” Mami tace “Ya wuce ne?” Heedayah tace “Aa yace xai wuce” Mami na sakkowa 

kasa tace “Har xa ka wuce Khaleel” yace “Ehh xan wuce” Mami tace “Toh bari ka tafi da abincin tunda baxa ka ci a 

nan ba” Kitchen ta tafi, Farida na kallonsa tace “Ina yini?” Yace “Lafiya lau, How are you” tace “Alhmdllh” A 

warmer Mami ta xuba masa abincin ta saka a leda ta kawo masa parlon ta ajiye kusa da shi tace “Here, anjima idan 

ka tafi gida sai ka ci” ya mike yace “Allah ya saka da alkhairi” Iya bakin kofa Heedayah ta rakasa sbda Mami dake 

parlor snn ta dawo ciki, ganin har Farida ta wuce sama ta bi bayanta da sauri, dakinsu ta sameta xaune gefen gado 

tana danna wayarta, Farida na kallonta tace “Me ya kawo sa?” Heedayah ta bude hannu alamar bata sani ba tace 

“Nima a nan na samesa” Farida dai ta tabe baki bata ce komai ba, Heedayah ta xauna gefen gadon tana kallonta a 

hankali tace “You know what Farida?” Farida na kallonta tace “Aa me ya faru” hawaye ya kawo idonta, Farida ta 

kamo hannunta da sauri tace “What happened Heedayah talk to me plss” Ta fashe mata da kuka, Farida ta rude tace 

“Ki gaya min menene mana Didi” Heedayah ta d’an yi shiru, sai kuma a hankali tace “Ko ba ya Shureen bane” da 

mamaki Farida tace “What about him?” Heedayah na goge hawayen idonta murya can kasa tace “He kissed me…” 

Shiru Farida tayi tana kallonta ko kiftawa bbu, jin shirun yyi yawa Heedayah tace “Why don’t you want to say 

anything?” Farida ta ta6e baki ta mike ta bar wajen tace “What did you want me to say” bin ta da kallo Heedayah 

tayi tace “Ohh haka ma xaki ce min” Farida ta juyo tace “Of course me xan ce maki, an ta6a kissing mutum baya so? 

Ai ke kika tsaya yayi maki, so why are you complaining?” Heedayah bata kuma cewa komai ba, Farida ta fice daga 

dakin. Mumy ce xaune ita da Hajiya Sadiya da Salima a dakinta, Hajiya Sadiya tace “Wllh damuwa ya isa ya maki 

illa Maryam, kina da saka ma ranki damuwa ba kadan ba, wnn abun fa duk mafita ake nema amma dubi ynda kika 

koma daga jiya xuwa yau….” Mumy ta matse hawayen idonta cikin rawar murya tace “Shkkn ni na tashi a tutar bbu 

kenan Sadiya, ashe da gasken dai ubanta ne ke neman takarar gwamna, ni yanxu meye ribata ga kishiya da a ko da 

yaushe xata iya dawo min tunda ba sakinta Barrister yyi ba” Sadiya tace “Toh dai uban yarinyar nan nema mukamin 

yake ba wai samu yyi ba, sai ki ga ma baxai samun ba in sha Allah” Salima dake taunar cingam tace “Tabb, da kyar 

kuwa wnn mutumi ace baxai samu gwamna ba, ku kun ga jama’arsa kuwa, mu dai shkkn kin mana bakin ciki, da kin 

rike yarinyar nan da yanxu government house sai dai mu shiga duk lkcn da muke so mu fito lkcn da muke so, amma 

yanxu ai sai dai kishiyarki ta shiga ta fito duk sanda ta ga dama, ni dama uban Heedayan xai ganni yace yana so duk 

da ba wai na hakura da Junaid bane amma wllh yarda xanyi ya aureni, kuma kar kiyi tunanin sbda ya aureni xa ki 

dinga xuwa government house, nima ba nuna xanyi na san ki ba gaskiya” Banda hararta bbu abinda Mumy ke yi da 

idanuwanta da suka yi jajir, Salima ta tabe baki tace “Duk da haka bai baci ba, da yanxu xa ki amince Shuraim ya 

aureta ai rass kema sai yanda kika yi da gidan gwamnati wllh” wani kallo Mumy ta dinga yi ma Salima tana huci, 

kafin tace komai Sadiya tace “To ai gaskiya ta fada wllh Maryam, kyansa kawai Shuraim ya aureta mu ga ta tsiya, 

kinga kuwa ikon Rahina daga ranan ya kare, Heedayah ta xama surkarki sai yanda kika yi da ita, idan ma rabata xa 

ki yi da Rahinar duk sai kiyi amma gaskiya wnn garabasar idan ta wuce mu kuma mun shiga uku, wllh shawara me 

kyau Salima ta kawo, d’an ki fa ke aurenta, waye kuma Rahinah ai sai yanda kika ce xa ayi”

About AIS

Check Also

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} Www.bankinhausanovels.com.ng  Dana ga Anty Meerah …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *