HEEDAYA CHAPTER 38 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 38 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Abba ne xaune parlon Kaka, ita kuma tana xaune daga kan darduman da tayi sllh hannunta rike da carbi, tun fara 

bayanin Abba kaka ke kallonsa kamar a lkcn ta fara ganinsa, har sai da ya kai aya kaka ta ki cewa komai sai xare ido 

take, Bude kofar parlon aka yi hade da sallama Baffa ya shigo, ya xauna saman kujera yana kallon Kaka ya gaisheta, 

jin tayi shiru bata amsa ba yace “Lafiya Baaba??” Kaka ta kunce ha6ar xaninta ta fara matsar kwalla tana shessheka 

tace “To dai tunda mu ke kallon banxa bai ta6a hadani da Heedayah ba Allah ya so ni, Umaru kaga shi yasa aka ce 

mutum ya ji tsoron Allah ko, yanxu da na biye ku nace baxa a rike wnn yarinya ba tun farkon kawota gidan nan da 

Amadu yayi da na shiga uku na lalace yau, amma da yake xuciyata fess ban biye xugar kowa ba, inji Amadu ya fada 

maka waye uban Heedayah, to wllh duk abinda mutum xai yi ya ji tsoron Allah ya ji tsoron gamuwarsa da Allah, ni 

dai duk xaman mu da yarinyar nan ko kallon banxa ban ta6a yi mata ba balle in hantare ta wllh, Allah ubangiji ya so 

ni, wa enda suka yi hakan ma Allah ya yafe masu, ni fa lkcn da ubanku ke da rai na sha tsinto yara a titi su girma 

wajena in aurar da su, kalar tawa baiwar kenan, shi sa Heedayah ma nayi mata rikon da ku kanku ban maki ba…..” 

Tana kai wa nan ta mike ta nufi gun akwatinta tana share guntun hawayen idonta, daga akwatin tayi tace “Allah me 

yanda ya so….” Baffa yace “Me kuma xa ki yi da akwati Kaka” Kaka ta juyo da sauri tace “Ai Abujan xa ku kai ni in 

karanto ma uban duk abun arxikin da aka yi mata ba tare da mun dubi cewar a titi aka tsintota tana galantoyi ba, to 

wai ma waye silar riketa a gidan nan?? ba ni din bace dai, nan nan nan Amadu ya watsar da lamarinta ya bar mu 

daga ni sai Rakiya muna ta wahala da ita meye ba mu yi mata ba na gata wanda ko gaban uban nata take ba lallai yyi 

mata ba, har filina sai da na kusa siyarwa lkcn da xata makaranta, daga karshe ma Amadu koramu yyi ni da Rakiya daga gidansa ta dalilinta, shi dai kawai Allah ya basa baiwar tsinto mana ita ne ya kawo mana, amma asi bai mata ba, 

kashinta, fitsarinta, duk bbu wanda ni da Rakiya bamu ci ba, barin ni don Rakiyar ma gantalin aikinta take tafiya ta 

bar ni da ita” tana magana tana hawaye, daga Abba har Baffa kallonta suke baki bude, Ta sharbe majina tace “Kuma 

na daga jaka ace min ina xan je sbda rashin tsoron Allah, to Abuja xan tafi” Baffa yace “Haba kaka, ke ya kamata ki 

bi su, ko su ya kamata su xo su sameki a nan??? Da girman ki xaki ce xaki bi su Abuja, ba su ya kamata su xo nan su 

maki godiya su baki girman ki ba” Cikin daga murya Kaka tace “Aa wllh bbu ruwana da wani girman kai, rawanin 

tsiyar xa ku dinga laka6a min, shi yasa fa aka jefo shaidan daga aljanna aka ce, to meye kuma wani girma kamar 

wata gyambo, Allah ai shine abun girmamawa, bana son girman daga yau ma idan xaku ce min Patuu duk ku ce bbu 

ruwana da iskanci, meye wani da girmana kamar dai ni na halicce shi uban yarinyar, mu tafi kawai ku dora ni a mota 

inyi tafiyata, bance wani gantalalle ya kai ni ba dama” Abba dai bai ce komai ba sai kallonta yake, Baffa yace “Toh 

ki jira Allah ya kai mu gobe lafiya mana” Kaka tace “Ba a xuwa Abujan da daddare ne ko walakanta ni ku ke son ku 

yi?” Baffa yace “Yanxu idan ance ki bi hanyar nan da ba shi da kyau ai baxa ki bi ba kaka” Kaka ta jinginar da 

akwatin ta koma ta xauna tace “Matsiyatan yan kidinafin ma kadai ai sun isa hanani tafiya yau, shegu” Mikewa 

Baffa yyi yace “Na shigo in gaisheki ne dama, sai anjima” Bai jira cewarta ba kamar yanda Kaka bata ko kallesa ba 

har ya fita parlon, kaka ta rike ha6a baki bude tana naxarin Maganganun Abba, can ta daga hannu sama tace “Ni dai 

Allah ya rufa min asiri wllh, dama tun ranan da na fara ganin Deedayah na ji ta kwanta min sosai, ban bari tayi 

rashin uwa ba ko na sakwan daya, ban kyamace ta ba, abinda ma nake mata ban ma jikokina ba wllh” Washegari da 

ya kasance Friday, da safe karfe takwas Mami ta gama shirin komawa Kaduna tare da Farida, ta shiga bangaren 

Ammin Heedayah don yi mata sallama, Heedayah ta fito daki don a nan ta kwana tun bayan da ta dawo gidan nasu 

da Khaleel daren jiya gun Abbanta, ta xauna gefen Mami tana kallonta tace “Mami good morning” Mami tace 

“Morning dear, how was ur night” Heedayah tace “Alhmdllh, Ina xa ki Mami?” Mami tace “Xamu koma kaduna 

yau” cikin sanyi Heedayah tace “Mami tafiya xa ku yi ku bar ni nan?” Ammi dai bata ce komai ba, Mami tayi 

murmushi tace “Abbanki xa su taho anjima sai ki biyosu” girgixa kai tayi ta mike tace “Noo Mami we are going 

together, ki jirani in hada kayana” tana fadin haka ta koma dakinta da sauri, Mami ta mike tace “Sae kun taho 

Amina” Ammi ta mike tace “Aa ki jirata ku tafi din Hajiya….” Mami tace “Aa, kamata yyi ku taho tare din xai fi” 

Ammi tayi shiru ganin Mami ta nufi kofa ta bi bayanta da sauri tace “Abban su Islam yace ya turo maki sako ta 

WhatsApp ki duba yanxu Hajiya” Mami tace “To in sha Allah” har bakin gate ta rakasu snn ta koma ciki, tsaye taga 

Heedayah a Veranda, ta juya da sauri ganin uwartata tana goge hawayen idonta, Ammi ta dinga kallonta snn tace 

“Don’t worry dear, anjima xa mu wuce Kadunan gaba daya ai, flight sai nan da karfe biyar in sha Allah na yamma” 

Heedayah tayi shiru bata ce komai ba, Ammi ta wuce ciki. Mami na komawa ta bude WhatsApp din nata taga flight 

ticket guda biyu da Abban Heedayah ya turo mata, rasa ma abinda xata ce tayi, Dinar dake xaune tare da ita a parlon 

tace “Jirgin dai da baki son bi shi xa ki bi at last, ki kirasa kawai ki ce kin gani Allah ya saka, sai in kai ku airport din 

xuwa nan da karfe goma tunda flight din sha daya ne” Mami dai tayi shiru bata ce komai ba. Mumy ce xaune dakin 

Sadiya idonta yyi bulu bulu don kuka, Hajiya Sadiya tace “Ni fa wllh wllh idan ba ke kika yi ido hudu da shi wanda 

aka ce shine uban Heedayah ba kika xo nan kika fada min hakan da bakin ki to ni ba yarda xan yi ba, sai kace wasan 

kwaikwayo a taya wnn sanannen Mutumin xa ace shine ubanta, ‘yar kamar wnn mutumin ta bace farat daya ace ba 

mu ji a gari ba” Mumy ta fyace majina da tissue din hannunta tace “Nima dai shi na gani Sadiya…” Sadiya tace “Toh 

wai da kika kira Shuraim din me ya ce maki?” Mumy tace “Uban me xai ce min dama, kawai ce min yyi eh haka ne, 

nayi nayi nayi ya fadadada min bayani amma yace bai san komai ba haka kawai Abbansa ya gaya masa shi ma, to ya 

xan masa?” Sadiya tace “Kaii karya ne wllh, wnn sanannen bawan Allah dai karya ne ace shi ya haifi Heedayah, ta 

ina suke kama? Shi baki ita fara, snn me kudi da fame kamarsa xai bar ‘yar sa a makance??” Hajiya Baturiya dake 

dakin duk tana sauraronsa tace “Abinda ku ke mancewa a nan shine, shi wnn bawan Allah Honorable Ahmad Yusuf 

Ishaq da ake batu akai, duka duka yaushe ya fara siyasa da har yyi sunan?? Ina jin bai kai shekara uku ba, don ko da 

yana siyasar ma to gaskiya a shekaru uku xuwa hudu jama’ah suka san sa har ya xama famous haka, xai iya yiwuwa 

sai bayan batar ‘yar tasa ya shiga siyasa gadan gadan har yyi kudi haka, kuma idan baku manta ba ni dai na sha fada 

maku wnn yarinya bata yi kama da yar kananun mutane ba, ku dubi jikinta ko a lkcn da Barrister ya kawota bbu 

wani alamar wahala kawai dai makauniya ce….” Mumy dake ta mata wani shegen kallo tace “Toh in sha Allahu ba 

ubanta bane shi din, idan Allah yayi duniya don manzon Allah, taya ma xa ayi ya xama ubanta, mutumin dake 

neman takarar gwamna a jihar kano, meye hadin biri da gada, yarinyar da mijina ya tsintota a makance a daji bbu 

galihu….” Hajiya Baturiya tace “To yanxu idan da gasken shine ubanta ya xa kiyi Maryam?” Mumy ta fashe da kuka 

tace “Wllh wllh ba shine ubanta ba in sha Allah, matsiyaciyar yarinyar da Mai gidana ya tsinto a bola xa ace attajirin 

nan ne ubanta, dubi fa uban plazozin da yake da shi a jihar nan da ma kano, in sha Allahu ni baxan ji kunya ba muna 

nan da ku xa ku ga karya ne, idan kuwa gaskiya ne toh sai dai fa ayi hakuri da abinda xai faru” Sadiya tace “Toh 

Allah ya sa karyan ne, amma idan haka ya kasance ai baki ci ribar komai ba wllh” Mumy tace “Ai sai dai idan ba ni 

Maryam ba, yanxu ma gidan Dakta xan tafi in ji abinda ake ciki nasan yanxu kaka tana da labari tare da ita” Sadiya 

tace “To mu je mana gaba daya” A tare su ukun suka tafi gidan Baffa a motar Mumy…. karfe shidda saura Abban Heedayah ya fito government house na Kaduna tare da few convoy, tun shigowarsu kaduna ya kira Shuraim da ya 

xo har government house din ya samesa don kai sa gidan Baffansa, sanye yake da khakinsa da yayi fitting dinsa 

sosai, Shuraim suka gaisa da gwamna dake tare da Abban Heedayah don da shi xa a taho gidan Baffa, tun da 

Heedayah ta yi ido hudu da Shuraim bata sake yarda ta kallesa ba, kuma ta ki gaishesa, shi ma din bai sake kallon 

direction dinta ba, mota daya ta shiga da Abbanta da Amminta, motoci biyar ne banda na sojoji da na governor da 

suka yi parking a kofar gidan Baffa, Shuraim ya sauka, Heedayah ta bude motar ta fito don Allah Allah take ta ga 

kaka ta nufi gate da sauri, parent dinta ma duk suka sauko motar, da ido Shuraim ya bi ta don sai da ta d’an bugesa ta 

shiga gate din gidan, Heedayah na shiga main parlor din gidan ta fara kwala ma kaka kira, Mumy ce xaune parlon da 

kawayenta da Mum din Sudais suna magana kasa kasa, bata ko kula da su ba ta ci gaba da kiran kaka…. Sai ga Kaka 

ta fito dakinta, da gudu Heedayah ta tafi ta rungumeta, Kaka tace “Ina gwamnan yake??” Kaka bata rufe baki ba 

Shuraim ya shigo, ganin Mumy a parlon ya ki karasawa, yana kallon Kaka yace “Xa a shigo…” Kaka ta tura 

Heedayah tace “Su shigo mana me suke jira a waje, ai tun daxu nake ta jiransu Umaru yace min suna hanya, mu dai 

ba mun rike yar su da amana ba, wanda ya ki Heedayah yau ne ranan jin kunyarsa, don ma Sudais da muka hada 

baki da shi aka rike Heedayar yana can kasar waje, da ba don shi ba, ba don ni ba da yanxu wani labarin ake ba wnn 

ba…..” Mumy dai sai kikkifta ido take, haka Umman Sudais, Ammi ce ta fara shigowa parlon da wife din governor 

din garin da sallama, Kaka ta amsa da karfi ta karaso cikin parlon tana kallonsu Mumy cikin fada tace “Ku tashi ku 

basu waje su xauna mana, kun ja6e kamar masu neman aiki” Kallon kaka kawai Ammi take da murmushi, Kaka ta 

fashe da kuka sosai tana kallon Ammi tace “Wllh kamar kinyi kakin Heedayah, ni dai dama nasan Heedayah ba 

gantalalliya bace, dama kallon banxa bai ta6a hadani da ita ba, wa enda suka yi mata ma Allah ya yafe masu ita ma 

kuma ta bar su da Allah, amma ke banda lalacewa ta sameki garin yaya kika sake yarinya makauniya kamar akuya ta 

shiga duniya, a titin kano fa Amadu ya tsintota tana galantoyi bbu idanuwa, da karo karo ya hada dubu milyan 5 ya 

biya kudin aikin idonta a kasar Indiya wllh, har ni sai da na bada nawa gudunmawar, bbu yanda basu yi in bi su 

indiyar ba nace su tafi kawai a barni in ta masu addu’a kawai, to ba gashi ba yau komai ya xama labari ba, ai 

makiyan Heedayah sai dai ciwon xuciya ya kai su lahira yau….” Kaka tayi tsit ganin gwamna ya shigo tare da 

Mahaifin Heedayah, Mumy sai xare ido take daga inda take xaune ga xufa da ya bi ya dameta, kamar hadin baki lkci 

daya ita da su Sadiya duk suka mike suka koma bayan kujera kamar munafukai suna gwale ido…. Kaka ta saki kuka 

kamar yar yarinya tace “Dama bbu yanda banyi da d’an bakin cikin nan Shureen ya kai ni gwamnet house ba sai ga 

gwamnan yau a gabana….” Abban Heedayah ya isa har gabanta yana kallonta ya xauna nan kasa.

About AIS

Check Also

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} Www.bankinhausanovels.com.ng  Dana ga Anty Meerah …

One comment

  1. Hello! I just would like to give a huge thumbs up for the great info you have here on this post. I will be coming back to your blog for more soon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *