FARAR WUTA CHAPTER 6 BY AISHA MAHMOOD

FARAR WUTA CHAPTER 6 BY AISHA MAHMOOD

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Dukkan wata ma’ana ta mamaki da kuma tashin hankali shine yadda fuskar Amina tayi a lokacin da take kallon Hajiya Kilishi.+

“Taɓa Aminu dana sa akayi tsaraba ce ga ƙwaƙwalwar ki Amina don ki saurare dukkan abunda zan gaya miki da kyau, ki yarda da dukkan kalamaina sannan kuma zuciyarki ta tabbatar da cewar Kilishin da zaki sani a yanzu da gaske take al’amuranta.”

Tayi shiru bayan ta faɗi hakan hannunta na jawo wayarta da ta ajiye a gefe, babu ƙarar kiran dake shigowa alamun a silent ta saka ta.

“Ya akayi Awwalu?”

Muryar tata da ta canja tar ta tambaya cikin wayar bayan ta kara ta a kunnenta… Har a lokacin Amina bata motsa daga yadda take zaune ba, idanunta basu canja daga yadda suke kallonta ba, sannan ƙwaƙwalwar ta bata wartsake daga mamakin dake zagaye da ita ba, Ƙirjinta dake ɗagawa cikin numfashi mai nauyi shine kaɗai abinda zai sa ka san cewa idan ka taɓa ta ba zata tafi ta faɗi ba.

Wataƙila magana guda ɗaya aka fada a cikin wsyar wadda ta gamsar da Hajiya Kilishin, don bata ƙara cewa komai ba ta kashe ta kawai ta sake mayar da ita gefenta, sannan ta sake kallom Aminan, hasken fuskarta na yayewa alokaci guda

“Duk abinda zaki ji a yanzu ya zama tsakani dake ne Amina, idan ba haka ba a ƙarshen zancena zaki gane abinda zai faru idan har kika sako mutum na ukun mu a wannan zancen koda kuwa mahaifiyarki ce.

Da farko mu bar duk wani kewaye-kewaye mu tafi ga abinda yasa kika shigo gidan nan, tunda ni dake dama duk wani mai hankali mun san akwai dalilin aurenki da Ma’aruf…”

Ta gyara zamanta kaɗan sannan ta cigaba…

“… Cire mahaifinki ki ajiye shi a gefe, amma ko mahaifiyarki ta san ruwa baya tsami banza, a muryarta kawai na fahimci cewa irin zurfin tunaninta kika ɗauko Amina, ku duka kun san ba kowacce mace ce zata taka irin matsayin da kika taka a banza ba, zan ƙara tabbatar miki cewa shigowar ki cikin gidan nan dama cikin rayuwar Ma’aruf wani abu ne da ba don taimakona ba, ba zaki taɓa samunsa ba ko zaki mutu sau ɗari ki dawo, saboda a rana guda zamu iya samun mata dubu da zasu yarda da auren Ma’aruf ko da kuwa ciwon da yake dashi yafi haka tasiri, don ba’a  wayewar kowacce rana mata ke samun namiji irinsa ba.

Kuma shi kansa Amina, da an bashi zaɓi na sani tsaf zai kawo macen da zata fi ki a komai don irinsu kawai ya sani kuma yake mu’amala dasu, amma sai nayi amfani da ƙarfina da kuma ikona nace ke kaɗai za’a bawa wannan matsayin wanda dole kowa ya yarda da hakan, don haka duk wata soyayya da kika ga kina samu daga mutanen gidan nan dama shi Ma’aruf ɗin da ya fara saurarar ki duka saboda ni suke miki ba don komai ba, ni na ɗora su akan turbar zuciyarsu ta so ki kuma hakan ya zame musu kar dole.”2

A yanzu Amina tayi ƙoƙarin sunkuyar da kanta tana kallon hannayenta dake faman rawa suna kakkarwa akan cinyarta, zuciyarta na bugawa ne kamar zata faso kirjinta ta fito yayin da kowanne kalaman Hajiya Kilishin ke shiga kunnenta da tsantsar rudani da kuma tashin hankalin da akace ba’a saka masa rana.

Kuma shirun da Hajiya kilishin tayi baiyi tsawon da zata iya fitar da komai ba lokacin da muryarta ta cigaba da cewa.

“Bari in ɗauko miki komai tun daga farko Amina, ta haka ne zaki fahimci zance na.

Lokacin da ina yarinya a wajen kakata na girma, ita ta raine ni tun daga lokacin yaye har girma na, a wajenta na samu tarbiyya da kuma tarin wayo da dabaru irin na zaman duniya, har yasa tun a ƙananun shekaru ina iya kallon rayuwar mutum na bashi shawara mai kyau da zata ɓulle ga matsalolin sa, hakan yasa ƙawayena dama mutanen unguwar a lokacin suka laƙaba min sunan ƴar baiwa.

STORY CONTINUES BELOW

Bayan wani lokaci sai wannan kakar tawa ta rasu don haka dole na koma gidanmu inda naje na tarar da tarin ƴanuwana, don mahaifinmu matansa uku ne kuma ƙaramar cikinsu wato mahaifiyata ce kawai mai ƴaƴa tara, sauran biyun akwai mai goma sha ɗaya da kuma sha uku.

Rayuwar gidanmu ba dadi sam, saboda a wajen kakata na saba komai namu mu uku ne kawai dani da ita da kuma wani almajirinta Awwalu da take riƙewa, don haka sai rayuwar gidan yawan tazo min a wuya, gashi babu ruwan kowa dani hatta mahaifiyata kuwa da hankalinta yafi karkata kan yayyena da suka fi girma a lokacin, don haka da lokacin shigata babbar sakandire yayi sai na samu mahaifina nace ya maidani makarantar kwana don zata fi mun daɗi, al’amarin kamar ba zai yiwu ba da ƙyar da rabo dai na samu na tafi.

A can na hadu da ƙawayena biyu kuma ƴanuwan da zan iya kira da na jini wato Salamatu da Saratu, wadannan mutane biyun Amina sunyi min duk wani gata a lokacin zama na a makaranta da ya kamata ace iyayena ne suka yi min, hatta kuɗin jarabawar karatuna tsaf su suka biya min har muka kammala, don ban daɗe da shiga makarantar ba mahaifina ya rasu abubuwa suka sake harigitsewa a gidanmu.

Kowacce mace taƙi fita tare da ƴaƴanta kuma aka ƙi a raba gado kowa ya koma yana zaman kansa ne da kuma zaman gasa a tsakani don kowacce mace tana so ne ace ƴaƴanta sune suka fi samun arziƙi, musamman Innata da take ganin itace ƙarama an riga an rainata ita da ƴaƴanta don haka bata damu da duk wata hanyar da yayyena ke bi su samo kuɗi ba indai za’a samun, burin kowacce kawai ace ita da ƴaƴan ta su ke ƙyallin maiƙo a gidan.

Abinda nazo na tarar kenan bayan na kammala makaranta na dawo, wani abu da tun bana saka shi a raina har ya zamo kwanci tashi nima tunanina ya karkata ga hakan, sai dai ni tawa ƙwaƙwalwar ta raina irin hanyoyin da suke bi, na kasa yarda cewa mutum ba zai iya magance matsalolin kansa a rayuwa ba sai ya tsugunna neman taimakon wani daban, don haka na shiga amfani da ƙwaƙwalwata wajen cimma manufata.

Almajirin da kakata ta riƙe Awwalu yana aikin masinja a wani kamfani, da taimakon sa da kuma dabara ta na samu aiki a kamfanin a matsayin mai gyara da kuma harhaɗa takardu… In taƙaice miki zance Amina, wata na biyu a wajen nan na fara karbar kuɗi sama da albashi na ba tare da kowa ya sani ba, kafin a shekara kuwa, ni da Awwalu muna samun daidai da abinda ma’aikatan wajen nan ke samu, ban taɓa bawa wani jikina ba sannan ban taɓa bin wani malami ko boka ba, da wayo da dabarata nake komai ta yadda babu mai zargina kuma dukkan wani bincike ba zai taɓa biyowa ta kaina ba.

Kuɗin da nake samu a kowanne wata sai da ya zama hatta a cikin gidanmu babu wanda ake kallo sai ni, mahaifiyata da ƴanuwana duk suka dawo suka raja’a a kaina, aka shiga bani wani irin girma da ban san yana wanzuwa a duniyar nan ba, ya zama zan iya taka kowa a gidanmu in zauna lafiya, nasa aka rushe ɓangaren ɗakunan mu aka gina mana danƙarere da ya tsone idon sauran ƴanuwana kafin daga baya suma su dawo su kwantar da kansu.”

Muryarta tayi shiru a daidai wannan lokacin alamun ta tuna wani abu da ya saka ta murmushi, wani murmushi da har sautin sa sai da ya fito kafin tace.

“A wannan lokacin ne kuma na nemowa kaina mijin aure Amina, munyi ƙoƙarin canja kamfanin aiki ne ni da Awwalu don na yarda da karin maganar da hausawa ke cewa zama wuri ɗaya tsautsayi, don haka muka je kamfanin Bakori a wata ranar laraba, inda kafin mu shiga na hango Alhaji Mansoor ya fito daga ciki ya shiga motarsa, tun da na ganshi a wannan lokacin na sawa zuciyata cewa shine mijin aure na, don haka bamu nemi aikin ba nace da Awwalu mu juya, kuma kafin sati ya zagayo na bi hanyar da sani na ya manne a zuciyar Alhaji Mansoor.

Na kashe kuɗi sosai a wannan lokacin duk da ba sai na gaya miki yadda na aiwatar da komai ba zan gaya miki cewa sati guda na shafe ina siyan shafi guda a jaridar da Alhaji Masoor ke karantawa, ana wallafa hotona cikin irin ayyukan da na san dole suka ja hankalinsa.

STORY CONTINUES BELOW

Har da masinjan ofis ɗinsa da ma direbansa na haɗa baki dasu suna bashi labaraina, kuma bayan ya yarda da auren nawa, sai da na toshe bakin mutane da yawa wajen fallasa wani abu mummuna akaina.

Lokacin da na shigo gidan nan kuwa Amina da naga Maimuna, a lokaci guda na raina kaina na kuma ƙara yarda cewa sa’ata ce kawai ta shigo dani cikin rayuwar Baffa, don wanda yake da mata irin Maimuna babu abinda zai kaishi auren irina.

Amma ban damu sosai ba, tunda na san na shigo daular arziƙi ne kuma na ciri tuta a cikin ƴanuwana da a lokacin suka maida ni kamar mahaifinmu saboda biyayya.

Ban daɗe ba lokacin da Maimuna ta sami cikin Shukra ƴarta ta uku, don haka sai nayi amfani da hali irin nawa na ja ɗanta na biyu wato Ma’aruf a jikina, na so haɗawa har da Jamal ma amma shi da yake yafi wayo a lokacin sai ya mannewa uwarsa.

Ni na yaye Ma’aruf da hannuna Amina, ni na raine shi tun daga wannan shekarun har zuwa girmansa, don ko bayan haihuwar Maimuna bai bar wajena ba itama kuma bata yi magana ba saboda nauyi na da take ji a sannan, don a lokaci guda na zage na karɓi gidan, ni nake yin komai musamman da bata da lafiya, bayan tayi haihu kuma ni nayi ɗawainiyar da ƴanuwanta ma basu yi ba, hakan yasa a lokaci guda na samu soyayyar kowannensu, hatta Baffa kuwa, don sanda ya aure ni ba zan tantance irin son da yake min ba, amma a cikin shekara guda sai da na tabbata ni da Maimuna munyi kunnen doki a zuciyarsa.

Soyayyar kowa na siya tsakani da Allah don bana yarda da gaibu Amina, kamar yadda baba yarda da aikin wani boka ko malam da baya zuwa ko’ina, ni ina yin shiri na shekara da shekaru ne ba na wani ɗan lokaci kaɗan ba.

A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar mana har ta kai na fara haihuwa nima, a wanann lokacin tsananin kirki da kyautatawata yasa na kere Maimuna a zuciyar Baffa ta yadda ita kanta bata damu ba, don tana ganin cewar na cancanci hakan.”

Tayi shiru wucewar wasu sakanni tana kallon Aminan kafin ta cigaba.

“Bari na gaya miki wani daga cikin babban sirrina don ki ƙara tabbatarwa cewa da gaske nake al’amarina… Nice na gurguntar da Maimuna…”4

Babu shiri Amina ta ɗago ta kalle ta, idanunta na haskawa da tsananin mamakin da yake ƙaruwa akan wanda take ciki. Sai kawai tayi murmushi mai zurfi tana kallonta itama.

“Ƙwarai Amina, ni na saka Maimuna ta rasa ƙafafunta, kin san dalili?”

Ba ta bata damar amsawa ba ta cigaba.

“Na gaya miki Maimuna tana kyau, to labulen ɗaki na kawai nake ɗagawa in hango ta ranar girkinta ta nufi ɓangaren Baffa, idan tayi kwalliyar nan bana iya daurewa kishina dake tasowa Amina, rana daya na yanke cewar ba zan iya jurar cigaba da ganin zuwanta ba don haka takanas na tafi asibiti na samu wani ma’aikaci a ɓangaren ƙashi, na bashi maƙuden kuɗaɗen da a lokaci guda ya bani wani magani mai kama da poison wanda ke lalata har ƙashin mutum.

Kuma sai da na jira har bayan watanni huɗu da rashin lafiyar zazzaɓi ya kamata sannan na haɗa baki da wani yaro daga Nijar yazo har gida yayi mata allurar maganin nan a matsayin likita, kuma babu wanda ya san ni na dauko shi don nambarsa na sanya a wayar Baffa da sunan likitan gidan Dr. Ashiru, nace idan yazo yace Dr. Ashirun ne ya turo shi.

Kuma bayan yayi mata allurar ƙafafun nata sun lalace gabaɗaya na bashi kuɗi ya koma ƙasar sa Nijar, shi kuma Dr. Ashiru yazo yace bai san yaron ba, da aka duba lambar aka ga ma ba tasa bace dole aka haƙura don ko ƴan sanda basu iya samo komai ba.

Kuma bayan haka ni na zauna nayi jinyarta Amina, tun kafin a yanke ƙafafun har muka je India aka cire su gabaɗaya, shekara guda da rabi na ɗauka ina jinyarta, na hana kowa wannan ɗawainiyar hatta ƴaƴanta da ƴanuwanta tunda na san na samu abinda nake so, na san tsawo na da nata ba zai taɓa daidai a idanun Baffa ba, kuma hakan ya ƙara min ƙima a idanun kowa a gidan nan ta yadda nake cin kare na babu babbaka, kowa yana girmama ni da bani darajar dana siya a wajensu, hatta ƴaƴan Maimuna a idon kowa kamar nawa suke don babu adadi su  Munaya zasu zo su faɗa min abinda mahaifiyar tasu ma baza su iya faɗa mata ba ko kuma su nemi shawarata akan abinda ita bata ma sani ba.

STORY CONTINUES BELOW

Don haka yanzu na san kin fahimci cewa saboda ni kika samu soyayyar kowa gidan nan, da kuma abinda nake nufi cewa duknwanda kika furtawa wannan zancen kamar kin bude masa kofar lahirarsa ne.”

Muryarta tayi shiru a wannan lokacin,  wucewar wasu sakanni sai kuma ta taso a hankali ta dawo kujerar kusa da inda Aminan ke zaune, kuma bata damu da rashin kallonta da har yanzu bata yi ba ta cigaba.

“Mu dawo kan abinda ya kawo ni, dalilin da yasa na aura miki Ma’aruf Amina, kamar yadda na faɗa ba don ki zo kiyi rayuwar zaman aure bane kamar yadda naga kin fara kokarin yi a yanzu, na kawo ki gidan nan ne saboda ki taya ni mu ƙarasa babban burin da nake dashi a duniya.

A farkonsa ban tsara dake ba, amma daga ranar da Baffa ya yanke shawarar cewa dole Ma’aruf ya ƙara aure, daga ranar kika shigo cikin lissafina Amina, don Ma’aruf ginshiƙi ne guda a cikin burin da nake son cimmawa a yanzu, ina ɗora shi ne akan matakan da zasu kaini ga yin nasara ɗaya bayan ɗaya, don haka idan har aka samu matar da zata raɓe shi wadda ba zan iya juyawa ba Amina abubuwa zasu lalace min ba kaɗan ba, shi yasa tun kafin kowa yayi wani yunƙuri musamman mahaifiyarsa dana san a tarin ƴanmatan dake danginsu zata iya haɗa shi da wata, na duba bayana na zaɓo ki.”

Sai da ta sake gyara zamanta tana fuskantar Aminan dake zaune a gabanta ta sunkuyar da kanta sannan tace.

“Ɗago nan ki kalle ni Amina…”

Ta kuwa ɗago da kan nata amma bata kalle ta ba, gashin idanunta sun hade suna shaida jiƙewar hawaye alamun kuka take yi, wani murmushin yaso giftawa a leɓɓen Hajiya Kilishin amma ta tare shi, don da kukan Aminan da kuma shi ɗin, duka bata ga muhallinsu a yanzu ba.

“Sati guda zan baki kiyi tunani, idan har kika yarda dani, zan ƙawata rayuwarki da dukkan ƙawar da baki taba tunani ba Amina, zan miki liƙin alheri har sai hannayenki sun kasa tarewa, zan ɗaga ki ki zama tauraruwa a idon kowa musamman cikin danginki, zan kyautata rayuwarki da ta dukkan makusantanki idan har kika miƙo min hannunki na kama kamar yadda na tsara komai…”

Ta sake yin shiru tana kallon haɗewar gashin idon nata, sai kawai ta haɗiye yawun dake bakinta sannan ta ƙarasa furta abinda ke tahowa tun daga ƙasan zuciyarta, abinda take jin ko da duniya zata taru akanta ba zai canja ra’ayinta ba.

“… Idan kuma har kika zabi yin katoɓarar fallasa ni don ki tsira, na rantse miki da ubangijin da ya halicce mu rayuwarki zata dulmiya ne a baƙin ruwan da zaki yi ta yin ihun da babu wanda zai taɓa jiyo muryarki!”1

***

Tun da ya shigo gidan jikinsa ya bashi akwai wani abu da ya faru, don fitilar falo ma a kashe take, iya hasken ta korido ne  kawai yake a kunne, a falon ya ajiye wayoyinsa da su kaɗai ne a hannunsa sannan kai tsaye ya nufi hanyar koridon, ɗakinsa yayi niyyar wucewa ya watsa ruwa don Allah ya sani a gajiye yake, amma a lokaci guda idanunsa suka kai kasan ƙofar dakinta da nan ma fitilar a kashe take.

Har ya wuce ya dawo ya tsaya ya kwankwasa, kusan sau uku amma shiru bata amsa ba, sai yayi tunanin sallah take don a lokacin masaltai ke kiran isha’i, don haka sai kawai ya juyo ya dawo ɗakinsa.

Ya kunna fitulun ciki da suka gauraye da haske a ɗakin komai yana fitowa tar cikin kammalen da yake. Ma’aruf yana da tsaftar da duk wanda ya zauna dashi zai gane, don indai abu nasa ne to ba zaka taɓa zuwa kaga komai ba’a muhallinsa ba, sannan kuma yana da haƙurin da zai zauna da wanda bai damu da hakan ba, shi yasa ya iya zama da Ishaq dake wular da komai inda yaga dama.

Minti goma kawai ya ɗauke shi gama shiryawa cikin wasu kayan bayan yayi wanka, ya dawo falon daidai lokacin da wayarsa ke ƙara a inda ya ajiye ta, lambar mutumin da yasa ya nemo masa bayani akan Mr. Okafor ne, ya tsaya kawai yana kallon kiran ba tare da ya dauka ba har ya katse sannan ya tura masa dan guntun saƙo cewar suyi magana zuwa gobe.

STORY CONTINUES BELOW

A yanzu ya sani cewar  tarawa kansa abubuwa yana ɗaya daga cikin abinda ke saka shi damuwa har ciwonsa ya tashi don Allah ya sani a yanzu yana tsoron ciwonsa fiye da kowa, ya sani cewa idan abubuwa suka lalace masa a yanzu bai san me ya cimma a rayuwarsa ba. Shi yasa bai ɗauki kiran mutumin ba, don a yau kaɗai abubuwan da ya fuskanta suna da yawa.

Takardar sammacin da ya samu ɗazu a Office ta girgiza shi ba kaɗan ba, ya kasa hango inda Rukayya da iyayenta suka samu karfin gwiwar kaishi kotu akan zancen Hamida, kalaman Baffa su suka bashi damar ƙin saurararsu amma bai taba tunanin hakan daga garesu ba. Ya kira Ishaq sunyi maganar amma duk tsawon tattaunawar su ya gaya masa cewa chance din da suke dashi kaɗan ne don a matsayin Hamida na mace dole ne a wajen mahaifiyarta ya kamata ta zauna har girmanta kuma ƴan bayanan da suke dashi game da dalilin su na dawowarta wajensa basu da karfi sosai.

Sannan bayan yayi haka ya san yayi aiki a Office din amma ya tabbata idan ya koma gobe zai samu kura-kurai da yawa, don a cikin aikin ya gama yanke dukkan abinda ya riga ya tsara game da zancen kotun da kuma Hamida.

Kuma baya buƙatar yin zancen da kowa shi yasa ko cikin gida bai shiga ba tunda Baffa baya nan yayi tafiya Abuja, yaga kiran Mami amma shima bai bi bayansa ba kuma itama bata sake kiran ba har yanzu.

Ƙafafunsa suka sake komawa kitchen ɗin bayan ya kunna fitila yana nazarin komai, akan table ɗin kitchen ɗin, jerin kayan abincinsa ne kamar yadda take tsara su kullum, yaji wani abu ya zarce cikin makogwaronsa, a cikin ƴan kwanakin nan ya sani cewar yarinyar nan ta taimakawa ƙwaƙwalwar sa wajen samun hutu ta wani ɓangaren, don akwai nutsuwa sosai ace idan aiki ya zuƙe shi da rana akwai inda zai iya zuwa ya huta ba wannan hargitsatsen gidan nasu shi da Ishaq ba. Kamar ya zauna yaci abincin sai kuma kawai yaji ba zai iya hakan ba alhallin bai ganta ba.

Sai kawai ya zaro wayarsa ya kira lambar Samirah, bugu ɗaya biyu kuwa ta dauko, muryarta a ciki ta fara cewa ‘To Mami.’ kafin tayi sallama.

“Yaya barka da dare.”

“Kun yini lafiya?”

“Lafiya ƙalau.”

Ta amsa sannan tayi shiru tana jiran abinda zai faɗa a gaba, kuma hakan kaɗai ya bashi amsar da yake nema cewa Aminan bata ciki don haka kai tsaye yace.

“Sai da safe.”

Ya kashe wayar ya zura ta a aljihunsa sannan ya koma cikin gidan, ɗakinta da bai shiga ba a yanzu shi ya nufa kuma bai jira komai ba ya buɗe shi, fitilar a kashe take kamar yadda ya gani sai dai babu duhu a ciki don hasken fitilar waje na shigowa ta windon ciki, kuma a lokaci guda idonsa ya hango masa ita, tana zaune daga gefen gadon ɗakin ta ɗora kanta akan gadon yayin da jikinta yake a dunƙule, kamar dai ranar daya fara ganinta, ranar da ya fara ganinta a matsayin matarsa.

Wannan shine karonsa na biyu shigowa ɗakin kuma ya sake tarad da ita a irin wannan yanayin da ya san cewa tabbas akwai abinda ya faru. Hannyensa duka biyun suna cikin aljihu, sai ya fito da ɗaya daga aljihunsa ya sosa kan hancinsa yana kallon idanunta da suke a rufe.

“Assalamu alaikum.” Muryarsa ta ratsa ɗakin cikin amonta.

Kamar wancan karon ta dago kanta da sauri ta kalle shi amma bata mike ba, kallonsa take yi cikin hasken ɗakin wucewar sakanni biyu kafin bakinta ya amsa sallamar tana ƙoƙarin dagowa daga kishingiden da take.

Sai kawai ya juya ya koma ya kunna fitilar dakin, haske ya gauraye koina, yana nuna masa kumburarrun idanunta da tabbas kuka tasha dasu.

“Me ya faru? Me ya same ki?”

Tambayar ta fito sak kamar ranar da ya ganta cikin daren nan, amma wannan karon sai yaji abinda yake son tambayar yafi hakan, zai iya jero kusan guda goma don ya samu gamsashshiyar amsa.

STORY CONTINUES BELOW

“Babu komai.”

Ta fada tana ƙoƙarin juya kanta gefe don naɗe sallayar da take kai, yana iya ganin dogon hancinta wanda da alama ta murza shi fiye da kima.

“Kayi hakuri, ban ji lokacin da ka shigo ba, barka da dawowa…”

Muryarta ta faɗa sanda ta gama ninke sallayar ta miƙe tsaye tazo zata wuce shi, amma sai kawai ya riko hannunta na hagu ta baya ya tsayar da ƙafafunta.

Ba shiri Amina ta cije lebbenta tana kallon tiles ɗin dake ƙasan dakin, gayawa zuciyarta take yi cewa ta daurewa wani kukan dake shirin tasowa a ƙirjinta amma sakon baya tafiya sam, don lokacin da ya jawo ta baya ta dawo gabansa ƙwalla ta sake cika idanunta taf.

A yau ɗaya rayuwarta ta canja, ta shiga tashin hankalin da bata san da me zata kwatanta shi ba, a cire mamakin halayen Hajiya Kilishi daya nade zuciyarta a gefe, tsoro da taraddadin hatsarin da ta kawo kanta cikinsa ya hargitsa kowanne abu mai kyau na tunaninta, tana tuna kalamanta, tana tuna ranar da ta yanke hukuncin karɓar auren nan, da wani zai gaya mata da wani abu ko da makamancin haka ne… da tabbas labarin zai canja daga yadda yake yanzu.

Ita bata san ma me take ji ba, bata san yadda zata fassara halin da take ciki ba, kawai dai ta sa zuciyarta ta karye da kowanne abinda kalaman Hajiya Kilishin ke nufi, kuma shi kansa Ma’aruf ɗin ma a yanzu bata yarda dashi ba, don bata san me Hajiya Kilishi ke nufi da ‘matakan da take ɗora shi akai don tsarinta ya tafi daidai ba.’

Zuciyarta tayi rauni da yawa ta yadda fuskar Aminu ce kawai ke yawo a kanta da tunanin halin da yake ciki, shi yasa a  karo na farko tun bayan ranar da aka kawota gidan, hawaye ya kasa tsayawa a idanunta, don a wannan lokacin tana jin cewa kukan shine kawai sauƙin abinda take ji a kirjinta.

“Ki gaya min abinda ya faru da kuma dalili da yasa kike kuka.”

Ma’aruf dake riƙe da hannunta ya fada da muryarsa cike da ikon dake nuna mata cewa da gaske yake yi, sai tayi ƙokarin maida kukanta ta hanyar share idanunta da ɗaya bayan hannunta sannan ta shiga gyara tsayuwarta don ji take kamar zata fadi.

“Me ya same ki Amina?”

Bai gaji ba ya sake tambaya a lokacin da take jin kamar ƙamshin turarenta na kassara kasusuwanta ne, bata da wani zaɓi da ya wuce ta lalubo wani sauti daga can ƙasa maƙoshinta idanunta har yanzu suna ƙasa tace.

“Aminu ne ya gamu da hatsari, yana asibiti tun jiya.”

“Ya salam, Ya salam, wane asibiti ne?” Bai san waye Aminun ba, amma ya fahimci ɗanuwanta ne.

Ta girgiza kanta wani kukan na shirin ƙwace mata.

“Ban sani ba, muna waya da Amma sai… Sai wayar ta ɗauke.”

Zancen ya fito daga can ƙasan maƙoshinta ba tare da ta tsara shi ba.

Sai kawai yasa ɗaya hannunsa da baya rike da ita ya zaro wayarsa daga aljihu, santsinta ya biyo hannyensa yayin da ya kunna password ɗin da yatsansa sannan ya shiga wajen dial log kafin ya miƙo mata.

“Ki kira ta sai muji wane asibiti ne?”

Sai a yanzu ta ɗago ta kalle shi kuma kafin tayi saurin sake maida idanunta ƙasa, ya gani cewa har yanzu kwalla ce taf a cikinsu, a hankali nata hannun suka karbi wayar don babban abinda take bukata a lokacin kenan, kuma ga mamakinsa bata matsa ba ta shiga danna nambar wayar Amman.

“Assalamu alaikum.”

Sautin muryar mahaifiyarta da ya fito ta ciki yasa a yanzu ƙwallar idanunta ta gangaro… Karo na farko a duniya taji so take ta ganta a gabanta wannan lokacin ta rungume ta, so take ta cusa kanta a jikinta ta rera kukan da har yanzu take jin nauyi ta a ƙirjinsa, ta gaya mata cewa tayi nadamar ƙin gasgata maganganunta, don abinda ya shigo cikin rayuwar tasu yanzu wani abu ne da duk ƙarfin hangensu basu gano ko rabinsa ba, wani tashin hankali ne da ya tsallake dukkan tunaninsu.

STORY CONTINUES BELOW

A yau ta ƙara yarda da zancen Amma na cewar babu wani auren gaske tsakanin mai kuɗi da talaka a wannan zamanin, indai ya faru to tabbas akwai wani boyayyen abu dake ƙasa, Amma tace rayuwarki zaki sadaukar musu Amina, ashe su duka basu sani ba cewar bayan tata rayuwar suma tasu ta shigo ciki wataƙila har da sunan duk wani da ya rabe su ma.

“Amma, Amina ce.”

Muryarta ta fito tana kakkarwa kamar yadda hannunta keyi acikin nasa.

“Amina… Amina.” yadda muryar Amman ta kira ta a jere da wani irin sautin ajiyar zuciya yasa lebbenta talewa cikin kokarin wani kukan.

“Me ya faru ɗazu wayar ta dauke? Mun gwada yafi sau hamsin kuma bata shiga ba. Har Hajiya Kilishi na kira ita kuma ba’a dauka ba?”

Sai da ta hadiye wani abu a ƙirjinta jin sunan Hajiya Kilishin  sannan ta iya cewa.

“Amma wayar mutuwa tayi kawai, kuna ina yanzu? Ya jikin Aminun?”

“Gamu nan mun dawo gida don Baba yace bai yarda yayi zaman asibitin ba, yanzu dai sunyi masa abinda zasu yi masa mun dawo gida, gobe kuma zamu tafi jigawa gidan wannan  ɗanuwansu Fatiman mai gyaran karaya, saboda duka ƙafafun nasa biyu sun karye Amina.”

Sautin kukan da ya fito daga bakinta shi yasa Amman cewa.

“Ba kuka zaki yi masa ba Amina, addu’a zamu yi Insha Allahu zai samu sauƙi don ance shi mutumin ya iya aikinsa, ba za’a haɗa dana asibiti ba.”

Muryar Amman dake lallashinta itama a karye take kawai, ta sani suna da kuma matsayinta na Uwa shine abinda ke rike ta daga nata kukan.

“Ku duka zaku tafi Amma?” Tayi ƙokarin tambaya ta cikin kukan muryarta a rarrabe.

“A’a, dani da Baba da kuma Fatiman da zata kaimu gidan zamu tafi, su Maryam suna nan saboda makaranta, ita kuma Hajiyan Fatiman saboda jinyar Inna (kakar Fatiman) ne ba zata samu zuwa ba.”

Sai da tayi wata ajiyar zuciya mai nauyi sannan tace.

“Ina Aminun?”

“Bacci yake Amina, tun jiya sai yanzu bayan magaribar nan sannan ya samu baccin, idan ya tashi na kira ki, wannan nambar waye?”

Bata amsa ba don bata san me zata ce ba, kuma shirunta ya bawa Amma amsarta don haka sai tace.

“Addu’a zaki yi tayi masa Amina, kowanne ɗan adam baya wuce ƙaddararsa, komai zai zo da sauki insha Allah.”

Kalaman kaɗai sun isa su kara tsoratar da Amina, don ta san idan har Amma zata faɗi haka to al’amarin ba ƙaramin abu bane, don komai tsananin rashin lafiyar mutum Amma bata zuzuta shi haka, balle ma akan Aminu da yake namiji, don haka bata san lokacin da bakinta ya ƙara talewa da ƙoƙarin yin kukan da har yanzu take dannewa ba.

“Zan saka Maryam ta kira ki da safen kafin mu tafi, su can gidan Kawu Malam zasu koma kafin mu dawo.”

Ɗaga kai kawai take kamar Amman na kallonta yayin da sautin kukan ke shaƙewa a ƙirjinta yana fitowa a kakkatse, Allah ya sani rabonta da irin wannan kukan tun Maryam bata da lafiya, lokacin da aka nemi kuɗin maganinta aka rasa, tana kallonta a kullum tana tunanin mutuwa zata yi.

Ma’aruf yasa hannu ya karɓi wayar daga wajenta  bayan sunyi sallama, ya maida ita aljihunsa, bata kalle shi ba har yanzu tasa bayan ɗaya hannunta tana ƙoƙarin share hawayenta, da hannun da ya mayar da wayar ya sake riko ɗaya hannun nata ya tsayar da ita daga goge hawayen, sannan a lokaci guda ba tare da ta ankara ya jawo ta jikinsa, karo na farko ya rungume ta, hannunsa ɗaya ya zagayo wajen ƙugunta yayin da kanta ya samu mazauninsa a kusa da wuyanta.

“Kar ki maida shi zai cutar dake… Just let it out.”

Muryarsa ta faɗa a cikin kunnenta da wani sauti daya shiga dagargaza dukkan wata jijiya ta dauriya a jikinta.

STORY CONTINUES BELOW

Kuma a karo na farko Amina ta manta komai akan Ma’aruf ta sunkuyar da kanta a jikinsa don babban abinda take buƙata kenan, kukan da sautinsa kaɗan ne ya suɓuce daga bakinta yayin da jikinta ke girgizawa a cikin hannunsa.

***

Bayan kwana biyu.

“Kin shirya?”

Ma’aruf ya tambaya yana kallon Amina data fito riƙe da wata ƴar ƙaramar jaka a hannunta da kuma wani madaidaicin basket, doguwar riga ce a jikinta ta baƙar abaya, ta yafa baƙin mayafin kawai akanta ba tare da ta saka ɗankwali ba, tana tsaye daga hanyar koridon dakunan tana cakuɗa yatsunta cikin junansu, har yanzu ta kasa yarda da abinda yazo dadaddare ya gaya mata jiya cewa ta shirya zasu je jigawa a yau.

Jiya da safe a wayar tasa suka yi waya da Amma ta shaida mata lokacin tafiyarsu wanda bayan hakan tayi ta binsa da kallo tana so taji yace wani abu amma bai faɗa ɗin ba har ya fita, ya barta a zagayen halin da take ciki, kuma Allah kaɗai ya san yawan abubuwan data saka ta kwance a cikin kanta a jiyan wanda duk iya tunanin nata yana ƙarewa ne a gaɓar da bata san yadda zata yi ba.

Haka ta yini har a jiyan tana share hawaye duk lokacin da ta tuno cewa duk irin halin ciwon da Aminu ke ciki saboda ita ne, saboda itan da bata san yadda zata budi baki ta gayawa wani ba, ko da Ma’aruf ɗin ne kuwa tunda shi kansa babu alamun yana da wata masaniya irin wadda ita ta sani yanzu akan Mamin, duk da cewa bata gama sanin ainihin abinda take nufi game dashi ba ko kuma shi nasa ra’ayin akanta.

Sai da daddare bayan ya dawo ne kawai yace ta sako mayafinta zasu shiga cikin gida, wajen Mami suka fara zuwa kamar yadda suka zata, kuma gaishe ta kawai suka yi kafin ya furta abinda yasa kowannensu mamski daga ita har Hajiya Kilishin.

“Gobe zamu wuce Jigawa Mami, na san kin samu labari, brothern ta ne ya gamu da hatsari zan kaita ta dubo shi.”

Har yanzu tana jin nauyin yadda idanun Hajiya kilishi suka dinga kallon fuskarta, tana jin tafiyarsu a ko’ina na fuskar tata, yadda ta dinga kallonta da wani irin yanayi da yake nuna mata cewa itama a lokacin taji zancen, da kuma yadda tata zuciyar ta dinga bugawa har sai da taji kamar ta tsugunna ƙasa ta ɗauko ta lokacin da suka miƙe tsaye, don tsabar tsoro ƙirjinta fayau ta dinga jinsa kamar yadda jikinta ya zama kamar fallen takarda har lokacin da suka tafi ɓangaren Hajiya Maimuna, idan acan ma suka sha addu’ar Allah ya kiyaye hanya kamar yadda Mamin tayi tata.

Jiya haka ta kwana tana juyi akan gado, da asuba kuma tunda tayi sallah bata koma ba, don yace mata ƙarfe takwas zasu tafi a yau ɗin zasu je su dawo kamar yadda ya tsara.

Abincin breakfast ɗin da tayi ma bai ci ba don yace mata azumi yake yi kasancewar ranar Alhamis ce. A yanzu ya shigo daga wajen maigadi ne da ya gama wanke masa motarsa, yana tsaye daga bakin ƙofar falon yayin da karar yadda maigadin ke share ruwan wankin motar daga waje ya cika falon.

“Kin shirya a haka?”

Ya ƙara tambaya yana kallonta, sai ta sunkuya ta kalli kayan jikinta sannan ta dago ta kalle shi tace.

“Eh na shirya.”

Shi nasa kayan dogwaye ne kalar sararin samaniya, ya saka hula wadda ta dace dasu, da ace zuciyarta a nutse take ta sani tsaf zata tsaya yabawa yadda kayan suka karɓe shi amma a yanzu ba abinda ke gabanta kenan ba, tashin hankalin dake kwance a ƙasan zuciyarta ya isa ya binne ta da ranta. Sai kawai ya taho gabanta riƙe da mukullin motarsa a hannu, kuma bata matsa ba, don watakila a yanzu ta saba dashi a kusa da ita, kar a lissafa da shekaranjiya lokacin da ya rungume ta, wannan don ba’a cikin hayyacinta take ba kowannensu ya sani.

Hannunsa taji ya sauka akan gashinta da ya fito ta gaba kafin yace.

“Shi wannan ba’a rufe shi?”

Zuciyarta ta buga yayin da wani abu ya tsarga tun daga saman kan nata har zuwa tafin ƙafafunta amma ta haɗiye shi, sai ya matsa baya kadan sannan yaba cigaba da kallonta yace.

“Bana son wani yaga gashinki.”

Bata ɗago ta kalle shi ba amma kalaman sun daki zuciyarta ta yadda duk tarin hargitsin dake ciki sai da suka girgiza. girgizawar da bata yi tunanin zuciyar tata zata yi ba a yanzu tare da abinda ya faru game da ita.

A hankali ta juya ta koma ɗaki, wani pink dankwali ta ɗauko ta daura, ai kuwa ya hau sosai da kayan ya ƙara haska fuskarta, wanda bata ko gani ba ta sake ɗaukan ƴar ƙaramar jakarta da kuma wannan basket din ta fito, sai da ta tabbata ta kashe fitulu da switches ɗin ko’ina, na fridge kawai ta bari sannan ta fito.

Yana tsaye daga bakin barandar falon yana jiranta, wani guntun murmushi da yayi mata yasa gumi fitowa a tsakanin yatsunta kafin ta bashi waje ya kulle ƙofar gidan, kuma juyowar da yayi yasa shi tsayawa dab da ita, wanda kafin tayi tunanin yin gaba idonta ya hango mata wasu manyan ledoji akan booth ɗin motarsa.

“Mami ce ta aiko a kawo miki, yanzu muka yi waya tace ki kai musu.” Muryarsa ta faɗa dab da bayanta.2

Zuciyarta ta buga a ƙirjinta, hannayenta suka fara rawa riƙe da kayan nan, ta sani bana tasirin muryarsa ne kaɗai bane har da na sunan Hajiyan Kilishin daya furta. Numfashinta ya shiga kakkatsewa a kirjinta ta yadda tayi tunanin zai iya jinta amma sai taji lokacin da yayi baya ya ɗauki waya yana cewa.

“Zuwa 10 zasu iso Faruk, idan kana ƙaunar Allah ka tabbata kana nan…”

Sai kawai tayi ƙarfin halin motsa kafafunta ta tafi wajen motar, ta isa wajen daidai lokacin da idonta ya nuna mata sauran kayan daga gefen motar, buhun shinkafa guda biyu da jarkokin mai suma guda biyu.

Ta haɗiye wani abu a maƙogwaronta kafin ta ajiye kayan hannunta, ta buɗe ledar farko inda kayan tea manya-manya gwangwanayen su Madara ya shiga idonta, a ɗaya ledar kuna wani ƙaton food flask ne shi kadai mai faɗi, taji har a lokacin hannunta na girgizawa a hankali sanda ta buɗe shi, kuma tun kafin ta gani ƙamshin wani farfesun naman kaza ya cika hancinta, shine fal ya kusan cika flask din har baki.

Ba shiri ta rufe idanunta tana jin koina a jikinta na girgizawa. Fata take da dukkan imaninta cewa Allah ya kawo mata mafita akan matar nan.

“Ya ubangiji kaine tanadin kowanne bawa idan ya fada masifa, Ya Allah na miƙo maka hannaye na ka taimake ni akan wannan al’amarin da yafi ƙarfina, ba zan iya ba ya rabbi! Bani da wata mafita da wata dabara wadda ta wuce taka ya Allah.”

Wani lokacin bawa yana yin addu’a ne akan gaɓa, wani lokacin ubangiji yana amsa addu’a ne a take! Kuma komai yana da tushe yana da asali, kamar yadda tafiyarsu Jigawa ke shirin zama tushen faruwar abubuwa masu yawa.

Kuma rashin sani yana ɗaya daga cikin raunin ɗan Adam!1

***

Waye yake cikin wannan rashin sanin ne?Ruƙayya na tsaye daga jikin windon, hannunta rike da kofin wani shayi dake tiriri, idanunta na manne akan shukokin harabar gidan nasu dake waje, kamar nazarinsu take tana son gano wani abu a jikinsu, amma a zahiri kalaman aminiyar mahaifiyarta da ake kira da Hajiyar Sudan wadda ke magana a baya ne suka shiga kunnenta.+

” … Da mun tura wanda za’a samu ya kwance abin nan ke kin sani Nafi, yadda na ake da tabbacin na kabari baya dawowa haka aiki na yake ci…”

Sai kawai ta juyo a hankali tana kallon Hajiyar Sudan ɗin kafin kai tsaye ta katse ta.

“Ban gane ba, ta yaya zamu iya kai abin har cikin gidan?”

“Yanzu duk bayanin da muke yi baki ji komai ba? Tunanin me kike yi bayan wannan?”

Cewar Mahaifiyarta Hajiya Nafisa, amma ga Hajiyar Sudan ɗin wani shu’umin murmushi tayi tana kallonta sannan tace.

“Ƙyale ta Nafi, yanzu zata fahimce ni tsaf.”

Ta fada ba tare da ta ɗauke idonta daga kan Rukayyan da itama ke kallonta ba, kuma da hannunta na hagu ta yi mata inkiya da alamun ta ƙaraso ta zauna a gefenta.

Rukayya ta kalli wajen, ta sake kallon fuskarta… Allah ya sani bata son matar sam, don ta daɗe tana zargin itace ta bawa mahaifiyarta shawarar data fito da ita daga gidan Ma’aruf, sai a yanzu da suka ga da gaske babu yadda zasu yi da ita akansa sannan suka hakura, ko kuma tace mahaifiyarta ta hakura don har yanzu bata gama yarda da ita Hajiyar Sudan ɗin ba sam, amma sanin cewar bata da wata hanyar da ta wuce tata yasa ta cije lebbenta kawai sannan ta ƙarasa ta zauna ba tare da kallonta ba.

Kuma kai tsaye sai ta fara bayani daga inda ta san zata fahimta.

“Yanzu mun aika masa da takardar sammaci, ba nufinmu a shiga shari’a ba kamar yadda nayi miki bayani, a iya gaban alkali za’a sulhunta komai a tsakaninku kin san duk abinda zaki faɗa da kuma shaidun da muka samu wanda zasu saka komai ya tagi daidai, don haka daga nan za’a baki ƴarki ki taho gida da ita.

Kwana ɗaya kawai a tsakani, zaki haɗa kayanta wanda a ciki zamu san yadda za’a dinke ƙullin nan a cikin jakar yadda babu wanda zai tiya gani, sai ki kirashi wani waje inda zaku haɗu ki kalallame shi da zancen wannan yarjejeniyar taku, ki karbi kuskurenki da komai ki kuma bashi yarinyar da cewar kin yarda ta koma hannunsa kamar yadda kuka shar’anta, ki gaya masa cewa bayan wani lokaci ya dinga kawo miki ita kina ganinta.

Da wannan zamu barta a wajenta tsawon sati guda inda a sannan ne za’a sami wadda zata je gidan da sunan ta kawo sauran kayanta, a wannan lokacin za’a sami dabarar da zata kwance ƙullin nan, wanda da anyi hakan Ruƙayya, shikenan sai ki cigaba da kurbar shayinki kina kallon abinda zai biyo baya.”

Ta ƙarashe zancen da wani faffaɗan murmushin da ya sassauta zuciyar Rukayyan a lokacin, don sosai yasa ta jin cewar kamar da gaske sunyi nasarar sun gama, tayi niyyar magana amma sai mahaifiyarta ta riga ta.

“Idan komai ya tafi daidai, sai ke kuma ki bar hakarƙarin mu ya huta haka kije can ki ƙarata.”

“Ai babu abinda zai kuskure ma, na gaya miki idan kinga an samu saɓani a wannan abin Nafi, to gawar da aka binne zata fito ta dawo duniya, don haka ku kwantar da hankalinku kawai.”

Wannan zancen yasa su yin dariya dukkaninsu kafin hankalin Ruƙayya ta juya ga wayarta da ta shiga ƙara daga can inda ta baro ta a jikin windon data tsaya.

STORY CONTINUES BELOW

Ta mike a hankali riƙe da kofinta ta koma wajen, sunan Jawad daya nuna akan screen din wayar yasa ta kurɓar shayin kafin ta ɗauki wayar ta kara ta a kunnenta.

“Barbie yau kika ce, 5pm.”

Me yasa zai tuna mata? Ta sani, ta sani cewa shekaranjiya ta gaji da nacinsa da ba zai kare ba tace masa zasu hadu a yau, kuma da zata iya a yanzun ma zata kara masa lokaci ne, amma ta san ko ta kara ba zai barta ba don haka dole ne ta daurewa kanta a yau ta fuskance shi.

A hankali ta ajiye kofin hannunta akan windon, sannan tace.

“Ban manta ba J.”

Taji ajiyar zuciyarsa daga ciki kafin yace.

“Then where did you decide?” (Ina kika zaba?)

Ta sake cije lebbenta na ƙasa

“Where we first met.” (Wajen da muka fara haɗuwa.)

Kalaman suka daki zuciyar Jawad da tasirin da ita bata san shi ba, don a nata ɓangaren ta zabi fadar haka ne don zuciyarta ta tsara mata cewar a wajen da suka fara haɗuwar anan ya kamata ta kawo ƙarshen alaƙarsu gabaɗaya, ko yaƙi, ko ya so.

Kuma ƙarfe biyar da ƴan mintunan tayi mata a kofar Joint ɗin ‘Harish’, ta fito daga motar ta bayan ta jera ta a layin sauran dake wajen sannan ta gyara zaman dan mitsitsin mayafin data dora akan doguwar rigar jikinta ta atamfa, wadda akayi mata wani ɗinkin mai kyau daga kasa kuma tayi buɗewar umbrella, takalmin kafarta ba mai tsini bane wannan karon don ta sani rashin nutsuwar zuciyarta ba zai barta ta iya tafiya a cikin mai tsinin ba, ta shiga ciki babu mutane sosai, ƴan kaɗan ne kawai ke zaune akan kujerun wajen yayin da iskar yamma da kuma ƙamshin shuke-shuken wajen ke shiga hancinta.

Daga can karshe ta hango Jawad, zaune akan table din da a wajensa suka fara haɗuwa, ba zata tantance idan tebur din ne ko an canja shi ba amma dai wajen ne, yana sanye da wasu dogwayen kaya Kaftan, yasa hula dark brown wadda ta fito da hasken fatarsa tar a cikin yammar, Jawad mai kyau ne ba sai kowa ya tuna mata hakan ba. Kuma da alamu ya jima a wajen don tuni an sauke shi da shishar da yake bula hayakinta a iska.

Kafafunta suka ƙarasa wajen a hankali sanda shima ya hango ta, kuma a lokaci daya murmushi ya sauka akan lebbensa yana ƙara tuna mata da kammaninsa.

“Kina da cika alƙawari Babe, yana daya daga cikin abubuwan da suke kara haukatani akanki.”

Bata yi murmushin da ta saba kamar kodayaushe ba sai kawai ta jawo kujerar dake fuskantarsa ta zauna.

“Wane flavour za’a kawo miki?” Ya tambaya yana tasowa daga kishingiɗen da yake.

Ta ajiye wayarta akan table din tare da earpiece ɗin hannunta sannan ta kalle shi sosai.

“Ka san ba abinda ya kawo kenan ba Jawad, idan zaka kyauta ma just put yours aside muyi magana.”

Ya gyada kansa yana kallonta.

“Zanyi duk abinda kika ce Barbie.”

Da haka ya ajiye tasan gefe yana cigaba da kallonta, idanunsa na lumshewa akan fuskarta. Bata damu da yadda yake kallon nata ba kai tsaye ta fara magana.

“Jawad abubuwa sun cakuɗe a rayuwata yanzu, I’ve got alot going on table da ba sai nayi maka bayaninsu ba amma hakan ne yasa na yanke alaƙa ta da kai, don bani da wannan lokacin Jawad, abinda nasa a gabana ya karato don haka dole ne na ajiye ka a gefe.

Kuma nayi ƙoƙarin nuna maka hakan ta duk hanyar da zan iya amma ka kasa ganewa, shi yasa na yarda muyi wannan haduwar don in shaida maka komai baki da baki.”

Tunda ta fara maganar bai ko kifta idanunsa ba, kallonta kawai yake da dukkan irin emotion din da zata iya tsinta a cikin idanunsa, wanda basu dame ta ba ta cigaba.

STORY CONTINUES BELOW

“Idan baka manta ba Jawad, tun farkon alakarmu na gaya maka cewa babu aure a tsakaninmu na san baka dauki maganar da muhimmanci ba a lokacin amma ni da gaske nake tun a sannan. Bari na fito fili na gaya maka gaskiya Jawad, a lokacin da na haɗu da kai ina cikin damuwar da ni kaina ban san mecece ita ba that is bayan mutuwar aurena na biyu, so na kula ka ne kawai don ka taimaka min in manta damuwa ta, and you really did help ‘cox we wasted away ta hanyar ta hanyar da har sai da kasa na kusa manta cewa ina da abinda nake so bayan kai.

Yadda kayi treating ɗina Jawad da tsananin kulawa da komai shi yasa zuciyata ta yi laushi akanka har kayi tunanin duk abinda nake yi maka zai iya sawa na canja ra’ayina akanka, but honestly ban ɗauke ka komai ba more than a toy (abin wasa), baka taɓa zama wani abu mai daraja har da zan kalla da sunan aure ba Jawad.

Zuciyata ta mutum ɗaya ce a duniyar nan kuma ina jin cewa ko za’a tsaida tashin duniya akaina ba zan taba iya canja hakan ba. So ka taimaka min mu karkare komai a yanzu, Let’s just end everything here don ni tuni na fara gudanar da da sabuwar rayuwar da a cikinta zan cimma burina, ka taimaki kanka ka manta dani kaima Jawad.

Erase all those memories kayi pretending babu abinda ya taba faruwa tsakaninmu wanda na san a cikin kankanin lokaci zaka ji ka manta dani gabaɗaya. Ka kalli kanka, kana da komai the looks, status, kuɗi, age, time… You have it all J. (Kana da komai) zaka samu ƴanmata guda dubu da kallo ɗaya zaka yi musu and in no time they will be throwing themselves over you. Ka fahimta dan Allah Jawad cewa ni ba komai bace a rayuwarka.”

Ta ƙarashe da dukkan fatan ya fahimce ta a cikin idanunta, kuma har a lokacin kallonta yake shima, sai da ta kai ƙarshe ɗin sannan ya ƙifta idanunsa a hankali, yana komawa da baya, ya jingina sosai da kujerar da yake kamar kwanciya zai yi sannan muryarsa ta fito.

“Anything more Barbie?” (Akwai wani abu kuma Barbie?)

Ta haɗiye yawu a makogwaronta sannan ta girgiza kanta.

“Nothing more Jawad, shikenan idan har ka fahimce ni.”

Sai ya gyada kansa haɗe da rufe idanunsa ya buɗe kafin yace.

“Thank you.” ( Nagode.)

Ta kalle shi tsawon wasu sakanni zuciyarta na son nazarin yanayin dake kan fuskarsa wanda bata gane ba kuma ta kasa gano komai ɗin, hakan yasa kawai ta dauki wayarta data ajiye sannan ta mike tsaye.

“Nagode nima, sai wani lokacin.”

Ya sake gyada mata kansa ba tare da yace komai ba, kuma da haka ta juya ta tafi, idanunsa suka bi bayanta da kallo, zuciyarsa na tsagewa da yadda jikinta ke kaɗawa da tafiyar da take yi yayin da ƙwaƙwalwar sa ke dawo masa da kalaman abokinsa Haro.

“Ka sake gwada ta for the last time Man, idan har tana nan akan bakan ta cewar ba zata saurare ka ba, nayi maka alƙawari ni zan taya ka yarinyar nan tayi biyu babu a rayuwar ta, dama na tsane ta J, kaima ka san na tsane ta!”

Ya cije bakinsa da ya bushe yayin da wani guntun murmushi ya sauka akan leɓɓen nasa lokacin da Ruƙayya tayi kwana ta fita daga wajen tana ɓacewa ganinsa. Wayarsa ya zaro a cikin aljihunsa ya shiga neman nambar Haron, bugu kaɗan kuwa ya ɗaga lokacin da ya jawo kan shisharsa, kuma sai da ya zuƙo hayaƙinta ya busa a iska sannan yace.

“Tayi biyu babu Haro, let the plan start!”2

***

Jigawa,

11:05 Am.

“Gwara ki fito fili kawai ku fadi gaskiya, yanzu ke baza ki so in fara tafiya in gano me akeyi va? Idan yaso ko ta email sai na rubuto muku abubuwan da zaku tanada?”

Aminu ya fada yana kallon Amina da ta gama gaya masa irin tashin hakalin da ta shiga jiya, tana zaune a gabansa tana ƙoƙarin zuba sukari a kofin tea ɗin data take hada masa.

STORY CONTINUES BELOW

Abinda ya faɗa yasa ta yin murmushin da bata shirya masa ba tana kallonsa, kafin tace.

“Allah ya shirye ka Aminu, ai wallahi ina jin mutuwar ce kaɗai ma zata iya kashe bakin ka.”

“Daga fadar gaskiya, yanzu ke tsakani da Allah baza ku so ku sami wata ƴar expo ba? Wannan harkar fa harka ce ta dindin idan an tafi an tafi kenan.”

Tissue din dake gefenta Amina ta dauko ta jefe shi dashi a fuska.

“Aminu wannan fa ba zancen wasa bane.”

Ya ɗaga duka hannayensa sama.

“To shikenan, ai ke yanzu naga alama dama baki shirya mata ba, gashi nan har kin canja sai washewa kike yi wai ke amarya, dan Allah Amma bata yi haske ba?”

Ya tambaya yana kallon Amman da ta idar da sallar walha a lokacin, bata amsa ba sai jawai ta juyar da kanta gefe kawai ta cigaba da laziminta.

Kuma sai akayi sa’a kafin shima ya kara cew komai wayarsa a gefe tayi kara, ya ɗauka ya shiga sake amsa gaisuwar tarin mutanen da duk bayan ƴan mintuna ake kiransa. Amina ta sake kallon Amma data juyar da kanta tana lazimi, kafin itama ta sunkuyar da nata ƙasa a hankali ta shiga wasa da wani zobe a yatsanta, wani abu take ji yana tokarewa a cikin zuciyarta duk sanda ta kalli Amman.

Kusan awar su guda kenan da sauka, awa guda da zuciyarta ta narke lokacin da Ma’aruf ya tsugunna a gaban su Baba harma dasu Baban Kurna da suka yi sa’ar ganinsu don a safiyar ranar suma suka zo, yadda ya tsugunna a gabansu kansa a ƙasa suna amsa gaisuwarsa wani abu ne da girmansa yasa har yanzu ta rasa inda zata ajiye shi a cikin ranta, don har ciki ya shigo ya gaishe da Amma da kuma Aminun, sannan har yanzu idanunta suna hango mata damin kudin daya ajiye a gefen shimfiɗar Aminun lokacin da zai fita.

“Guess what?” (Kin san me?)

Ta tuna yadda muryarsa ta furta hakan daga bayanta lokacin da ta sake binsa wajen mota tare da wasu yara don su ɗauko kayan nan ita kuma ta dauko jakarta da lokacin da suka tsabar zumuɗi tsaya bata ko tuna da ita ba ta buɗe kofar motar ta fita.

Yadda ya tsaya a kusa da ita bayan ta juyo yasa ta kallon gefe ta hango yaran suna tafiya cikin gidan kafin girgiza kanta a hankali idanunta a kasa tana kallon jakar data dauko.

“Naga yadda zaki koma idan kin ƙara girma.”

Hakan yasa tayi saurin ɗagowa ta kalle shi, ya harde hannayensa duka biyi a kirji riƙe da wayoyinsa, kuma a take sai ya bata amsar tambayar da idanun nata ne suka yi masa.

“Kamar ki ɗaya da Mamanki, na daɗe ban ga masu kama haka irinku ba.”

Ruɗani idon nata ne ya tafi lokacin da ta sake sunkuyar da kanta kafin ta iya lalubo muryarta.

“Haka kowa yake cewa.” Ta faɗa a hankali.

“Haka kowa yake gani that’s why.”

Bata ce komai ya sake cewa.

“Naji dadin ganinsu sosai Amina, yanzu naga inda kika samo wannan kirkin naki.”

Bata san lokacin da wani guntun murmushi ya suɓuce a lebbenta ba duk da halin da take ciki. Ta sake ɗagowa ta kalle shi, har a lokacin kallonta yake da yanayin da bata iya fassara shi, yanayin da yake ƙara tuna mata cewa har yanzu bata san inda zata ajiye shi a zuciyarta ba.

“Nagode sosai.”

Sai a lokacin tayi masa godiyar da tunda suka taho a hanya take fama da ita a bakinta tana tunanin yadda zata fade ta, kuma murmushin da yayi a wannan lokacin sai da ya kusan tsinka zuciyarta ba don kalaman Hajiya kilishi dake daure da zuciyar tata tamau ba.

A wannan lokacin Ma’aruf na kallonta ne tunanin mai yawa a zuciyarsa, Allah ya sani wani abu ya motsa a zuciyarsa game da ita tun daga ranar da ya fara ganinta.

STORY CONTINUES BELOW

Ya cewa zuciyarsa tausayinta ne da kuma mamakin ganin ƙankantar ta, don a lokacin da Mami tayi masa zancenta da kuma lokacin da ya tsinci sunanta a kayan Jamal, zuciyarsa bata kawo masa ko kadan cewar zai ganta karama irin haka ba. Kuma duk sanda ya sanda yake tare da ita a yanzu yana mantawa da dalilin da yasa ya yarda da aurenta ko kuma yadda na auren nasu ya kasance, yana ji ne kawai kamar zamansu wani abu ne da ya daɗe daga cikin tsarinsa, don abubuwa da yawa ya banbanta da irin zaman da yayi da Rukayya.

Tare da Ruƙayya gani yake kamar duk abinda yake yi dole ne, don ita tana da tarin expectation ɗinta akansa, ta daɗe tsara wata irin rayuwa tare dashi a cikin kanta da a wancan lokacin shi ba abinda ke gabansa kenan ba, shi yasa abubuwa da yawa kai tsaye zata gaya masa tace yayi kaza ko ya kamata yayi kaza wanda duk da ba saurarata yake yi ba, hakan baya masa daɗi, amma ko fuskar Amina ya kalla, innocent kammaninta kaɗai yana sashi jin wani cikakken iko irin wanda kowanne namiji ke ji akan iyalinsa.

Don haka yadda take kallonsa a wannan lokacin, yasa shi ture abubuwa da yawa a cikin kansa ya tako ya karaso gabanta, ya tsaya dab da ita sosai lokacin da kallon cikin idanun nata ya koma kalar mamaki da kuma ruɗani, irin ruɗanin da ya kula dashi tun ranar da ya dawo ya same ta tana kuka, zuciyarsa ta gaya masa cewa so yake ya rungume ta har sai kayanta sun koma ƙamshin turarensa gabaɗaya, amma yayi kokarin ture zuciyar dake gaya masa hakan yace.

“Kin manta baki ɗauko basket ɗinki ba.”

Ta kuwa juya ta kalli basket din dake ajiye akan kujera kamar bata san dashi ba sannan ta dawo da fuskarta wanda hakan yasa ta ƙara matsowa dab da jikinsa amma sai tayi saurin yin taku baya kaɗan kafin tace.

“Abinci ne a ciki, ban sani ba ko zamu yi magariba a hanya, kace kana azumi.”

Bayan ta faɗi hakan, bata san me yake tunani ba don sai da wasu sakanni suka wuce kafin yayi magana.

“Ban san ta yaya zance miki nagode ba, amma I’m really grateful, Allah ya saka miki da alkhairi dear.”

Dear, dear, dear….

Sunan da ya kasa barin zuciyarta kenan har yanzu, yake rikita zuciyarta duk sanda ta tuno duk kuwa da irin zagayen tashin hankalin da take ciki ba cewar shi kansa a yanzu bai kamata ta yarda dashi ba duk kuwa da yadda komai nasa ke nuna mata akasin haka.

“Amina…”

Muryar Amma ta dawo da ita zahiri, ta ɗago da sauri ta kalle ta, har Aminu ya gama wayar yana shan tea din data hada masa.

“Ko zaki karɓo mana maganin da za’a saka masa yau a cikin gidan, kina shiga ɗaki na farko ne wajen Malam Ibrahim ɗin.”

Malam Ibrahim Mijinyawa shine ɗanuwansu Fatima mai dorin, kuma gidan nasa ba’a cikin garin Jigawan yake ba, a wani ƙauye ne dake gaba kadan mai suna Kuɗai, gida ne kato da iyalansa, amma kusan rabin dakunan gidan yana saukar marasa lafiya ne wanda ciwonsu yayi tsamari ya zama sai anyi kwanaki ukun da yake bayarwa kafin a bar wajensa, don haka inda suke ɗin dakuna ne a jere kamar asibiti, sai dai bayan su ɗin wani ɗaki ne kawai daga can gefe inda aka sauki wani yaro da nasa iyayen suma da suka zo daga Kaduna.

A jiya su biyar Amma tace mata sun zo, bayan ita da Aminun da kuma Baba, sai kuma Fatiman da ta kawo su gidan da kuma wani ɗanuwanta Yusuf da a jiyan su suka koma, dama an taho dashi ne don yayi mata rakiya tunda ita ba kwana zata yi ba.

Sai ta mike a hankali ta shiga neman inda ta ajiye mayafinta a dakin lokacin da Aminu yace.

“Anjima su Baban Kurnan zasu tafi Amma?”

“Eh, Babanku yace da sun dawo daga masallaci zasu kama hanya, su zasu tafi da waɗannan kayan da Amina ta kawo ma don mu sami sauƙi jibin.”

Kalmar ‘waɗannan kayan’ ita ta tsaida kafafun Amina cak a inda taje, don ta san waɗanne kaya take nufi, kayan abincin da suka fito daga hannun Hajiya Kilishi.

STORY CONTINUES BELOW

“Wallahi matar nan tana ƙoƙari Amma, Allah dai ya saka mata da alkhairi.”

Taji Aminun ya sake faɗa kuma ga mamakinta sai taji Amman tayi shiru bata ce komai ba, zuciyarta ta buga a kirjinta, ta juya da sauri a lokaci guda ta kalle ta, kanta na kasa a yanzu tana ninke wasu kayan Aminun, fata take ta fadi wani abanin tunanin sauran mutanen ko ta sami kofar da zata iya tunkararta da zancen da bata san ita ina fara ba, amma ga mamakinta sai tayi ajiyar zuciya sannan tace.

“Amin ta kyauta kam, haka Babanku ma yayi ta fada.”

Sai kawai tayi saurin sunkuyawa ta damƙo mayafinta dake ƙasa sannan ta haɗiye abinda ke bakinta da karfin da zata iya kafin ta muryarta ta fito wani iri.

“Bari naje Amma.”

Da haka ta tura ƙofar net ɗin ɗakin ta fita, tana jin kamar tana ɗauke da nauyin duniya ne bakiɗaya a kafaɗunta, Amma ce kadai fatanta amma ko ita bata san ta yadda zata fara gaya mata komai ɗin ba.

Abinda bata sani ba shine, idan ubangiji ya amsa addu’ar bawa, sai komai yazo masa a bazata, don wajen karfe ɗaya Aminu ya samu bacci, Baba kuma tun bayan tafiyarsu Baban kurna ya fita zuwa cikin gari. A lokacin ne Amma ta kira ta zuwa waje, kasan wata katuwar bishiya daga cikin gidan suka zauna inda aka shimfiɗa wata tsohuwar tabarma, kuma kalamanta na farko suka gutsirtsira duk wani saurin ƙarfin gwiwa da take jin cewa tana dashi na iya fuskantar wannan tashin hankalin.

“Amina a wannan zamanin mafarki baya tabbata, kin sani ba zan taɓa yarda cewa lafiya kike zaune a gidan nan ba ko?”

Lokacin da ta faɗi hakan kallonta take da ƙwallar data cika idanunta taf, amma sai ta girgiza mata kai ta cigaba da cewa.

“Ni uwa ce ina kallon abinda ya shige wannan zahirin, dukkan kalamanki da kuma abinda ke faruwa basu isa su sa in kasa hango damuwarki ba… Watakila a kwanakin baya muryarki a waya taso ta ɓoye min wani abu tunda ba ganinki nake yi ba, amma a yau kallonki kawai na yi Amina, na zaƙulo tarin abubuwan da ban sanki dasu ba fal.”

Sautin muryar Amman ya fito da ɗimbin abubuwa masu yawa, masu yawan da a cikinsu babu wanda bai sake karya zuciyar Amina ba, yana tuna mata da rayuwarta ta baya data shuɗe cikin wani kankanin lokaci, lokacin da Hajiya Kilishi bata yiwa Baba wannan kiran ba balle har a fara ƙulla zaren ƙaddarar ta, lokacin da bata kirga damuwa a cikin lissafinta tana kwana tana tashi ne kawai da mafarkin abinda gobe zata haifar.

“Me suke yi miki Amina? Ki faɗa min abinda yake ƙasan wannan kyautatawar…”

Ba shiri leɓɓenta ya tale cikin kokarin yin kuka yayin da take cakuɗa yatsunta cikin juna, kuma kaf a cikin bayanin da bakinta ya fara, layi biyu ne kawai ya sa fuskar Amma haskawa da tsananin mamakin da ko na nesa zai ganshi karara, amma bayan wannan layi biyun, saurarar bayanin ƴarta tata take yi da dukkan wata nutsuwar da take da ita a duniya… Nutsuwar da take da ita ta Halimatus- Sadiyar ta, sannan nutsuwar da a cikinta ta shafe shekaru ashirin da ɗoriya a gidan aurenta ba tare da wani mahaluki a duniyar nan ya taɓa jin kanta game da mijinta ba.

Nutsuwar da a cikinta ne idan za’a taro duk mutanen da suka santa a rayuwa, ƙaryane a samu mutum guda da zai tabbatar da wani aibinta baiyananne… Nutsuwar da a cikinta wasu tarin abubuwa suka faru da idan da za’a buɗewa Hajiya Kilishi su, zata yi dana sani sau dubu na inda ta kawo kanta, zata raina duk wani tunaninta dama wayonta, zata san cewa tayi kuskure wajen amfani da ƙwaƙwalwarta wajen cimma munafunci, mugunta, yaudara har ma da zalunci.

Zata gane cewa ba an halicci ƙwaƙwalwar mace ne don ta fitar da da kaidi kamar yadda take taƙama ba, zata san cewa Allah ya halicci ƙwaƙwalwar mace ne don ta samarwa kanta duniya da kuma lahirarta a tafin hannunta kamar yadda ita tayi.

Kuma a karo na farko tun bayan tsawo lokaci wani murmushi ya suɓuce a fuskar Amman, ita ta sani ba’a banza jikinta ya bata cewar bata son kai ƴarta cikin wannan gidan ba, ashe wata halittar ce mai ɗauke da irin ƙwaƙwalwar ta a wajen, banbancin kawai shine ita waccan ƙwaƙwalwar cike take da duhu tata kuma fara ce kal!

STORY CONTINUES BELOW

Idan kissa da dabara Kilishi ke taƙama dashi, tazo wajen da yake daidai ita, hausawa sunce karen bana maganin zomon bana! wasan nasu ne yanzu, kowa zai yi nasa cizon da sunan ceto! Kuma Amina da Ma’aruf ɗin data zaɓa dasu za’ayi wasan! Wasan da a karshensa Sarki ɗaya zai tsaya a wani matsayi da ita ta riga ta saba dashi.1

Don mutane ukun da ta ga ƙarshen makircinsu a rayuwarta, bata jin Kilishi ta ko kamo yatsan ƙafarsu, kuma kamar yadda ta nuna musu, haka zata tabbatarwa da Kilishi itama yadda cikakkiyar macen data amsa suna da matsayinta ke amfani da ƙwaƙwalwarta a bigiren da ubangiji ya halitta mata ba bigiren shaidan ba, zata nuna mata irin yadda tayi asarar nata tunanin a duniyar nan!

A hankali ta gyara zamanta sannan ta furta.

“Daga yau kar na ƙara ganin hawaye a fuskarki kamar yadda baki taɓa ganinsa a tawa ba…!”

Waɗannan kalaman su suka zama na farko da ta shiga sauke ƴarta daga raunin da ta hau kai zuwa dakakkiyar Aminarta da ta san ta baro hannunta da ƙwarin gwiwar cewa zata iya tunkarar yaƙin dake gabanta saboda mahaifinta.

Banbancin shine wannan karon zata sa ta fuskanci yaƙin ne saboda kyautatawar rayuwarta… a tafin hannunta zata ɗora mata rayuwar gidanta sannan a ɗaya tafin, zata ɗora mata Kilishi bayan sun sa ta biyo ta kan matattakalar…1

‘Ɗan hakin da ka raina…!

***

Haseenah Guest Inn, Jigawa.

04:30pm

“Gidan da ka dauko Hamidan zaka koma Ma’aruf, a cikin mutanen gidan na san baza a rasa wanda zai tsaya maka a matsayin shaida ba, na gaya maka kuɗi kawai zaka basu har sai kayi limiting iya wadanda kake so, don wannan ita kadai ce hanyar da nake ganin zamu bi.”

Muryar Ishaq ta faɗa a cikin wayar dake kare a kunnen Ma’aruf wanda ke tsaya a barandar wani ƙayataccen Guest inn dake cikin garin na Jigawa. Hannunsa ɗaya ya zura a cikin gashin kansa kasancewar ya cire hular kansa ya baro ta a cikin mota.

“Na gaya maka babu shaidar da zan gabatar Ishaq, ka barsu suyi dukkan abinda zasu yi, I have my ways akanta ita Ruƙayyan ita ta sani.”

“Ka shirya faɗuwa kenan tunda ka san kotu ita da shaidu take dogaro ko?”

Ya cije leɓɓensa kaɗan.

“Ko hakan ne zai faru let them Ishaq, na san abinda zanyi. Kar ka tanadi komai kawai ka cigaba da harkokin ka, Allah ya kaimu ranar.”

Da haka suka yi sallama a wayar da wataƙila itace ta huɗu tsakaninsu a yau kaɗai, ya kashe wayar daidai lokacin da wani ma’aikacin Guest inn ɗin ya ƙaraso inda yake.

“Yawwa yallaɓai, gashi an kammala komai.”

Cewar matashin yana miƙo masa wani muƙulli.

“Nagode sosai.”

Ya faɗa da murmushi yana karbar muƙullin ya zura a aljihunsa, kuma a cikin wayar tasa ya sake nemo nambar Hajiya Kilishi.

A wanna lokacin Hajiya Kilishi na ɗakin Baffa wanda dawowarsa kenan daga tafiyar da yayi zuwa Kaduna, shayinsa take ƙoƙarin hada masa yayin dashi kuma yake daga can kan kujera yana shafa man robb akan kafarsa don fitowarsa daga wanka kenan a lokacin.

Fuskarta ɗauke da faffaɗan murmushi ta ɗaga wayar tana fadin.

“Mai gaskiya na, kun taho ne?”

Ma’aruf ya girgiza kansa lokacin da yake tafiya wajen motarsa.

“A’ah Mami, yamma tayi sosai, so zamu kwana ne sai gobe, yanzu ma zanje in dauko ta daga can.”1

A lokaci guda irin wannan shirun dake biyo bayan walƙiya bayan haskawarta kuma kafin zuwan tsawa ya ratsa ƙwaƙwalwar Hajiya Kilishi da ta tsaya daga kokarin ɗebo madarar da take yi tana jinsa.

Biyu kenan! Sau biyu kenan a jere Ma’aruf ya yanke irin wannan hukuncin ba tare da tuntubarta ba, na farko tafiyar tasu zuwa Jigawan da kai tsaye yazo yake gaya mata tare da kowa, a yanzu kuma kwanansu a garin? Me yake shirin faruwa ne?

Ta girgiza kanta a fili lokacin da shi yake cigaba da gaya mata wani sabon labari na cewar baya son tuƙin dare ne, ba sai wani satin ba kamar yadda ta tsarawa Awwalu, a gobe ko jibin nan Ma’aruf zai sake komawa cikin ciwonsa. Ba ta yin saken da abubuwa ke cakuɗe mata, dole ne ta kwantar dashi don ta fahimci duk abubuwan data gano cewa suna ɗagewa daga cikin tsarinta.2

Wani abu da bata sani ba shine, abubuwa ma basu fara ɗagewa ba ko kaɗan!

***2

Kun fahimci cewa kowa ya shirya a wannan Babin????6

To su waye zasu yi nasara? su waye zasu fara su kasa? Su waye kuma zasu faɗi kasa wanwar??Ina zamu je?”+

Aminah ta tambaya lokacin da Ma’aruf yayi wata kwana data dauke su daga titin da ta kula cewa tun da suka shigo cikin garin Jifaywan a dazu shi suka yi ta miƙewa, muryarta a hankali ta fito yayin da take kallon hanyar.

“Wani waje.” Amsar tasa ta fito a gajarce ba tare da ya kalle ta ba.

Sai ta juyo a hankali ga barin kallon titin da suke kai ta kalle shi ita, idanunta na shaida rashin fahimtar zancen, a can ciki kuma ruɗanin da take ciki, kamar ba zata ce komai ba amma sai muryarta ta sake fitowa.

“Nayi zaton gida zamu tafi.”

Kalaman suka fito tare da nauyin yadda a yau bakinta ya furta wani waje daban da sunan Gida, saɓanin wajen da ta taso da rayuwarta a ciki. Ya girgiza kansa sannan ya juyo ya kalle ta, nauyin idanunsa suka sa taji kamar ta sunkuyar da kanta amma ta daure.

“Dare yayi kuna bana son tuƙin dare a babbar hanya, so anan garin zamu kwana sai gobe tukunna.”

Yadda sautin muryarsa ya fito a cikin motar da kuma yadda yake kallonta yasa ta haɗiye wani abu a makogwaronta da bata san meye ba kafin ta gyada kanta alamun ta fahimta sannan kuma ta sunkuyar dashi ƙasa ta shiga wasa da karshen mayafinta, tattaunawarsu da Amma bata kare ba sam zuwansa ne ya katse su, wanda ta san haka ne, da tun a can ta roƙe shi fa ya barta ta kwana tare dasu idan yazo da safen sai ya koma ya ɗauke ta, wani abun ya sake zarcewa makogwaronta tuna cewa a yanzu bata san ina zai kaita su kwana ba ma.

Amma duk da haka sai taji wani ɓangare a cikin zuciyarta na washewa, zuciyarta na rage nauyin da take ɗauke dashi a ɗazu mai cike da taraddadin rashin sanin abinda zata yarda dashi a al’amarin Hajiya Kilishi, ko ba komai yanzu ta san tana da babbar hanyar da take da yakinin zata samawa kanta mafita kamar yadda Amma ta fara gaya mata, Har a yanzu tana jin tasirin kalamanta da ya cika kanta taf! Yana ƙara buɗe wasu sababbin shafuka da a iya zagayen tunaninta gabaɗaya ita bata hango su ba.

Tana jin yadda amon kalaman nata ke zagaye cikin kanta, ma’anarsu na bi ta cikin jijiyoyinta suna taso da ƙarfin gwiwar da ta nemi ta rasa, kuma duk da taraddadin da take ji, koina a cikin kanta dama jikinta yana gaya mata cewar yanzu ne komai zai fara, don kamar yadda Amma ta fada ne babban kuskuren da Hajiya Kilishi tayi, ya riga ya bude musu ƙofar nasarar su.

“Mafitar ta riga tazo hannunki Amina, buɗe idonki kawai zaki yi ki kalle ta, kina da rabin maganin wannan matsalar yanzu a hannunki, wanda babban abun shine sanin halinta da kikayi, ita kanta bata sani bane amma tayi babban kuskure wajen bayyana miki sirrinta duk kuwa da na san cewa iya abinda take so ki sani kawai ta faɗa akwai sauran ƙurar da dole na san ta lulluɓe. Amma tun ana na fara raina lissafinta Amina, don da ace tayi bunƙasar da zan sara mata, da zata sami tarin hanyoyin da kema zata juya ki ba tare da kin san sirrinta ba…”

Wasu daga cikin kalaman Amman kenan da suka ƙara saka ta yarda cewa mahaifiyarta na cikin irin daidaikun matan da ake misali dasu a duniya, masu halayen da dimbin jama’a zasu gani tamkar a mafarki, da kowacce kalma da ta gaya mata a yau, zuciyarta ta ƙara yarda cewa mahaifiyarta itace babban makamin da zata iya tunkarar komai dashi a duniyar nan bayan addu’a.

Sai dai akwai wani abu guda daya a cikin kalaman nata dake fassara abinda zuciyarta bata taɓa lissafawa ba, abinda har yanzu da ta tuno yake rikita lissafinta yana sa hannayenta rawa, har yanzu bata gama sanin tunanin Ma’aruf game da ita ba, don haka ba zata taɓa iya ɗorar da komai ba a wannan fannin.

Ta rufe idanunta tsawon wasu sakanni kafin ta sake buɗe su tana ƙoƙarin saita kanta. Amma ta gaya mata cewa lokacin wani rauninta ya kare, kar ta yarda wani abu ya gaya mata cewa an fi ƙarfinta ba zata iya ba, tace mata itama macece, duk wani abu da take taƙama dashi itama tana dashi, kawai ita tana amfani da nata wayon ne ta mummunar hanya, don haka idan ita zata ɓullarwa gaskiya, a lokaci kadan ne zata kawo karshenta don gaskiya itace sama da komai a duniyar nan.

STORY CONTINUES BELOW

“Kilishi bata fi kowacce mace ba a duniyar nan Amina, yadda take takama da wayo da kuma dabararta, haka Allah ya halittawa ƙwaƙwalwar dukkan mata don ita mace uwa ce, an halicci mutane da yawa da zasu rayu a ƙarƙashinta wanda kowanne da irin ƙalubalen rayuwarsa, shi yasa Allah ya buɗe ƙwaƙwalwarta ta yadda zata iya samar da mafita kala-kala a fannin rayuwa.1

Wasu matan basa gane hakan ne har suyi yunƙurin sanin abinda zasu iya, matan kuwa da kika ga suna zaune lafiya tare da mazajensu ƴaƴansu harma da duk wanda zai raɓe su, sune wanda suka iya buɗe wannan baiwar tasu, Mata irin Kilishi kuma sune wanda suke amfani da wannan baiwar ta hanya mai munin da har suke ganin cewa sun fi kowa.

Yanzu girma yazo kanki da gaske Amina, kin fara ganin hakan tun daga ranar da kika bar karƙashinmu, kuma hausawa sun ce aure yakin mata, yaki ne da kowacce mace akwai kalar nata, don haka kema dole ne ki bude ƙwaƙwalwar ki, ki karɓi wannan girman sannan ki fuskanci naki yaƙin Amina…”

A daidai wannan lokacin suka shigo harabar wani haddadden gini mai tarin fitulun dake ta haske suna maraba da daren da bai kai ga ƙarasowa ba. Ma’aruf ya tsayar da motar a jerin motocin dake tsaye a wajen daidai lokacin da idonta ya zare akan sunan wajen.

Haseenah Guest Inn.

***

“Mene ne total charges for Adjustment and Uncollectables?”

Ma’aruf ya tambaya a cikin wayar da yake yi daga cikin dakin, yana zaune ne akan wani dan karamin dining table dake can karshen dakin yayin da hannunsa ke rubutu a cikin notepad din dake kan teburin. Kayan jikinsa wata loose T-shirt ce da ya siyo da kuma wani gajeran wando kalar grey.

“Next…”

Ya sake faɗa bayan mai maganar na ciki ya gaya masa wani adadi da ya rubuta a cikin wayar.

“Ka gaya min Net Patient Revenue din?”

“Na gaya maka yallabai, shine na biyu bayan total charges na Patient Care gabaɗaya.”

Mai maganar daga cikin wayar ya fada, sai ya gyada kansa yana bude shafin baya, ya karanta abinda ya rubuta sannan ya sake dawowa inda yake yace.

“Operating Expenses din fa?”

Mutumin na ciki ya sake faɗo masa wani adadi da ya shifa rubutawa.

“Sannan sir akwai Bad debts ɗin wancan…”

“Sai kuma Natural Expense ɗin?”

Ya katse shi ba tare da ya saurari abinda yake cewa ba, mutumin ya ɗanyi shiru kafin ya faɗo wani adadi na makudan kudin da saida Ma’aruf ya jinkirta kadan yana saurarar sa kafin ya rubuta.

“Yallaɓai ka saurare ni akan zancen bashin nan, bamu da wata hanya ne dole…”

“Just tell me the total Sadiq.” (Kawai ka gaya min jimlar komai gabadaya Sadiq.)

Muryarsa ta fito a hankalin da take tun bayan sallar magariba da yayi buda baki.

“Wallahi yallabai zai fi kyau ka duba Report ɗin gaba ɗaya tukunna gabadaya 42 pages ne, idan ka karanta komai you will realize that…”

“Ka gaya min total din kawai Sadiq.”

Yadda sautin muryar tasa ta fito wannan karon ita tasa Sadiq din sarewa daga dukkan ƙokarin da yake fanin zai iya shawo kansa, yayi ajiyar zuciya a hankali sannan ya fadi wasu makudan kudade da shi kansa Ma’aruf ɗin ya sani idan za’a bincike account dinsa na bankuna tsaf a tattaro komai baza ‘a taba samun wannan adadin ba, don haka bai ma rubuta ba, wani guntun murmushi ne ya suɓuce a lebbensa yayin da yayi baya ya jingina da kujerar da yake kai yana kallon gabansa tamkar Sadiq ɗin ne a wajen.

STORY CONTINUES BELOW

“Wallahi yallabai…”

“Sadiq”

Ya katse shi, sautin muryarsa can ƙasa amma kuma a kausashe.

“A rufe asibitin, a tsayar da komai, kwana kaɗan na baku, I’m coming in few days, ku san yadda zaku gyara wannan abin in a reasonable way kafin zuwa na. Idan ba haka ba, na rantse da Allah wasu ne zasu ci muku abinda kuka ɗiba ba ku ba, and just dare me and see.!”

Yana faɗin haka ya kashe wayar, ya cilla ta kan teburin da karfi har sai da screenguard ɗin dake kanta yayi wata katuwar tsaga guda daya, sannan ya cusa hannayensa duka biyu a cikin gashinsa yana ƙoƙarin saita numfashinsa, ransa ne yake shirin baci ya sani, amma yana kokati da dukkan iyawarsa ya danne hakan kamar yadda ya saba yanzu a kwanakin nan. Bakinsa ya shiga karanto hasbunallahu wa ni’imal walkil  daidai lokacin da kofar toilet din dakin daga can gefe ta buɗe bayan abinda zai iya kira aƙalla minti talatin.

Ya sauke hannayensa daga fuskarsa kafin ya juyo ya kalle ta, tana tsaye daga kofar kamar zata koma ciki ne ta sake rufewa, babu shiri yaji dukkan abinda ke cikin kansa na sulalewa yana bin iska, rigar da ya siyo ita ta saka, kusan iri daya ce da wadda ya taɓa gani ta saka a gida ranar da tashi cikin daren nan, me tsawo daga baya amma ta gaba kuma iya gwiwa take kawai, kuma yadda idanunsa suka riƙe hoton siraran kafafunta a wancan lokacin shi yasa kai tsaye yace a mayar da wanda ya ɗauko a ciro masa ita.

Daga yanayinta kawai ya san ta saka ne don bata da wani zaɓi, tunda wani mai wanki da guga na Hotel ɗin yasa yazo ya karɓi kayansu don ya wanke zuwa gobe, idanunsa kallonta kawai suke tun daga nan, ta yafa bakin mayafinta da bata bayar dashi ba akanta amma duk da haka gashinta na fitowa kamar ɗazu da safe.

Daga inda Amina take tsaye, cakuɗa yatsunta kawai take yi cikin junansu saboda rawar da hannayenta ke yi musamman a yanzu da take ƙara ganin wautarta na fitowa a haka, amma ya zata yi, har tawul a cikin toilet din ta ɗauko ta ɗaura taga abin bai dace ba ta cire shi.

A ajiye ma zancen ƙafafunta dake waje a gefe, tunda take bata taɓa lissafawa cewa zata yi kwanan hotel a rayuwarta ba idan har ba wai Makkah ko wata kasar taje ba, wanda shima ba’a irin wannan yanayin take hango shi ba, shi yasa tun da suka shigo zuciyarta ke rabewa gida biyu tana sake haɗewar da har a yanzu ta kasa samun sauƙi duk kuwa da ƙarfin halin da ta tattaro a ranta.

Ganin yadda yake kallonta yasa ta juya da sauri ta ƙarasa jawo ƙofar toilet ɗin ta rufe sannan ta shiga tahowa cikin ɗakin. Wani abu ya zarce maƙogwaron Ma’aruf da yake kallonta tana tahowa sai mutstsika yatsunta take yi cikin junansu yayin da siraran ƙafafun nata ke tafiya.

Tare da Ruƙayya yasha tambayar kansa meye babban interest dinsa game da mace, sai dai a lokacin ya kasa tsaida zuciyarsa akan komai banda kyawunta don ita ɗin kyakkyawa ce, amma a yanzu ya samu wannan amsar da ya daɗe yana nema, don yadda zuciyarsa ke sake ɗaukan hoton ƙafafun Amina tana masa kyakkyawar ajiya, a wani yanayi ne da wataƙila ko bayan ransa ba zai manta ba.

Ta ƙaraso kamar mara gaskiya ta wuce shi ta nufi wajen wani ɗan ƙaramin table da ma’aikatan wajen suka kawo musu abinci kamar yadda ya basu umarni.

Kuma sai a sannan tayi magana, tun bayan da suka idar da sallar isha da ya bata wayarsa ta sake kiran mahaifiyarta ta shaida mata cewa basu bar garin ba sai gobe tukunna.

“Wanne abincin zan zubo maka?”

Yaji ta tambaya daga bayansa inda taje ta tsaya, sai kawai ya ture komai a ransa ya taso ya taho inda take, ta juya bayan nata kamar yadda ya zata tana ƙoƙarin buɗe plates ɗin masu wasu irin manyan-manyan murafe kamar na abincin sarakai, a hankali ƙafafunsa suka tako ta kan carpet ɗin dake shimfide a wajen ya ƙaraso ya tsaya dab da bayan nata idanunsa na nazarin ɗan karamin jikinta dama siraran hannunta, bayan haka tsawonta ma gabadaya iya kafaɗarsa ne, ya san yana da tsawo don shi da Jamal ana cewa duk tsawon Hajiya Maimuna suka yi, amma bai taɓa tsayawa yayi nazarin yadda yafi wani tsawo irin haka ba sai akanta, don ko Ruƙayya ya sani ne cewa da kaɗan yafi ta.

STORY CONTINUES BELOW

Kuma wataƙila shirun da yayi ne yasa ta juyowa a hankali hannunta rike da murfin da ta ɗauko guda ɗaya, idonsa ya sake kaiwa kan kafafunta a yanzu data juyo, sai yanzu ya lura cewa akan farcen kafafun nata akwai kalar baki alamun lallen da bai gama fita ba, kuma yadda farcen ya rabu kala biyu fari da baki yasa shi kasa daina kallonsu.1

Amina ta sunkuya kalli ƙafafunta da yake kallo tana son ta nemo abinda ke wajen amma bata ga komai ba, yadda yake tsaye dab da ita kaɗai ya isa yasa zuciyarta rabewa gida biyu, amma tunda bata rabe tun a lokacin data fahimci cewa yau zata kwana daya daki daya dashi ba, bata jin a yanzun ma zata yi. Ta sake haɗiye wani abu karo na ba adadi a maƙogwaronta tana son kore ɗimbin tunanin dake kanta kafin ta sake yin magana.

“Zaka ci abincin?”

Muryarta ta fito ne kamar tana son tuna masa cewa ba’a kafarta fuskarta take ba, kuma hakan yayi aiki don a lokaci guda ya ɗago da idonsa ya kalle ta.

“Naci abincinki, kin manta?”

Ta yaya zata manta, da wannan busashshiyar doya da ƙwan data soya tun safe yayi buɗa baki, tea ɗin wajen kawai yasha ya cinye doyar gabaɗaya, a lokacin tana waya dasu Amma, tana daga karshen ɗakin kallon yadda yake buɗe-bude a cikin labtop ɗinsa yana cin doyar, wani abu da ya kara nutsar da zuciyarta a cikin kirjinta tana jin dama abinda tayi yafi doyar kaɗai, sannan kuma wani abu da ya fara buɗewa kalaman Amma dake sa hannunta rawa kofa a zuciyarta.

Sai ta girgiza kanta a yanzu tana ƙoƙarin cigaba da kallonsa.

“Ai wannan ba zai isa ba, idan mutum yayi azumi gwara yaci abinci da yawa.”

Ya gyaɗa kansa shima yana kallonta.

“Na sani, amma raina ne ya fara ɓaci yanzu, bana jin zan iya cin abincin.”

Kawai sai ta samu kanta da tambayar.

“Me ya faru?”

Kuma fitowar tambayar yasa taji kamar ta fara yin nisa da taraddadin dake zuciyarta.

Hannunsa ɗaya taga ya zura cikin gashin kansa kamar abinda zai faɗa zai yi masa wahala kafin wucewar sakan biyu yace.

“Ina da abubuwa da yawa a gabana, so mutane na using wannan opportunity ɗin suna cuta ta, Annual report din MMB- 6 aka aiko min yanzu, kuɗin da suka ce sun kashe a shekarar nan Amina ko ni bani dasu yanzu.”

Ba maganganun ne suka daki zuciyar Amina ba, sautin muryarsa ne yadda ya fito cike da wani rauni da idan za’ayi musu da ɗimbin mutane zasu kwana suna rantsewa cewa ba daga muryar Ma’aruf wannan raunin yake ba, ba shiri taji ta hadiye wani abu a makogwaronta kafin tace.

“Meye MMB-6?”

Wataƙila idan ta fara sani meye shi din zata fahimci abinda maganar tasa take nufi.

“Asibiti na ne da yake Abuja.”

Sai ta sake gyaɗa kanta tana jin kamar maganar tafi karfinta, amma kuma kai tsaye sai tace.

“Ance idan hankali ya ɓata hankali ake sawa ya nemo shi, yanzu ko ranka ya ɓaci babu abinda zai canja, kamata yayi ka samu nutsuwa mai kyau, sai kayi amfani da hakan ka gano koma wane irin akasi ne aka samu.”

Maganganun suka tafi har ƙarshen zuciyar Ma’aruf, suna fito da irin kwanciyar hankalin da yake ji a duk lokacin da ya gayawa Mami damuwarsa kuma ta bashi ɗaya daga cikin shawarwarin ta, Amina bata sani bane amma itace mutum ta farko daya dangance shi bayan Ishaq da suka san da zancen asibitin nan.

Abu ne da ko Mamin bata sani ba, kuma shi yasa dama yake damuwa duk sanda aka samu matsala akansa don ya san babu wanda zai iya bashi shawara mai kyau akan hakan tunda ko Ishaq baya yiwa zancensa. Kuma haka kurum ya zaɓi boyewa kowa sanin da zaman asibitin don so yake yi da gaske ya binne duk wata halayyarsa ta baya tare dasu kamar yadda yayi wa kansa alƙawari.

STORY CONTINUES BELOW

Zama likita yana daya daga cikin burinsa na farko a duniya, don haka nacin da zuciyarsa ke masa shi yasa shi tsallakewa zuwa garin Abuja ya gina ƙaton asibitin guda inda ya danka amanarsa a hannun wani likita mai suna Sadiq, shi yake jagorantar komai na asinitin don hatta tarin likitocin dake musu aiki shi yake biyansu, shekaru biyar kenan da kafa asibitin, kuma tun bayan shekaru biyun farko aka fara samun matsala a annual report din da suke bashi duk ƙarshen shekara, ya zama kudin da suke cewa duna amfani dashi duk shekara ya fara fin karfin tunaninsa.

Sai gashi yanzu minti ɗaya kawai gaban Amina duk dauriyarsa ya kasa riƙe wannan sirrin ya fallasa mata komai, amma kuma da ta bashi sai tasa bai ji yayi nadamar sanar da itan ba, hasalima zuciyarsa gode masa ta dinga yi don aƙalla abinda ta faɗa ɗin ya sama mata wani sauƙin.

Sai kawai ya gyaɗa kansa yace.

“Thank you.”

Sannan ya zagayo ta gefen table ɗin yace.

“Me zaki zuba mana?”

Tambayar tasa ta juyowa itama tana jin nauyin abinda ya faɗa, plates din ya shiga budewa gabadaya yana tara murafansu a hannusa ɗaya.

“Wanne kafi so a ciki?” Ta samu kanta da tambaya babu wani dalili.

Ya girgiza kansa shima.

“Ni zan ci ko meye kika zuba, favourite abinda nake so baya cikin wadannan.”

Ya fada yana kokarin ajiye murafan a gefe, sannan kai tsaye ya shiga gaya mata irin abincin da yake so wanda kusan duka na gargajiya ne, sanda yace mata har da ɗanwake sai da ta tsaya tana kallonsa, don ita a tunaninta mutane kamarsa basa ɗaukar abincin gargajiya da muhimmanci.

Ya tambaye ta abinda take so itama kuma sai ta samu kanta da ture komai a ranta ta shiga gaya masa, kuma da kowacce kalma data faɗa tana ji kamar tana karkaɗe ragowar taraddadin dake ranta ne.

“Ina son chocolate, sannan zan sha lemon zoɓo a koina kuma a kodayaushe.”

Ta fada lokacin da yake tambayarta abinda take so na kayan kwaɗayi.

Ya gyada kansa.

“Naga alama, cox naga zoɓo da yawa a fridge dinki.”

Ta gyada kanta a hankali itama.

“Ina ga ba zan taɓa iya dadewa babu shi ba a koina.”

“Wow, I like the enthusiasm.”(ina son kwarin gwiwar nan.)

Muryarsa ta gito da slamun cewa shima ya fara jin dadin sakewarta.

Sai tayi wani guntun murmushi da bata san daga ina ya fito ba tana kallon abinda take zubawa.

“Wane kalar chocolate kika fi so?” Da alama so yake hirar ta cigaba da yin nisa.

“Kowanne.”

Wannan karon muryarta ta sake fitowa kamar silin gashin dake faɗowa ƙasa a hankali ba tare da ta dago ba.

“Chocolate bai dame ni ba amma I always enjoy Ferraro Rocher.” (Ina jin dadin Ferraro Rocher.)

Bata taɓa jin ko sunan ba, kuma sai Allah ya taimake ta kafin tayi tunanin abinda zata faɗa, wayarsa dake can kan table ɗin daya baro ta ta shiga ƙara, don haka ya karbi plate din da gama zubawa ya tafi wajen, ya ajiye plate shi akan table din sannan ya kara wayar a kunnensa ya shiga magana da wani cikin Pidgin english, irin tsantsar Pidgin din da ita bata taba ji ba ma, amma kuma sai yayi mata dadi, yadda sautin muryarsa yake haɗewa cikin accent ɗin da kana ji ka san ya fito ne daga Jinsin Hausa/Fulani.

‘Matar ƴan gayu.’

Haka Aminu yayi ta tsokanarta ɗazu, kuma ita kanta duk da hargitsin yanayin da take ciki ta sani cewa kamar yadda Hajiya Kilishi ta faɗa ne, idan banda kaddara ko zata mutu sau ɗari ta dawo Ma’aruf yafi karfinta, don a yanzu da kowacce wucewar rana tana ƙara gane cewa yafi ƙarfin hangen da take masa a lokacin da ta yarda da auren nan. Shi yasa ko a yanzu kawai ƙwaƙwalwarta ta kasa auna mata adadin kuɗin da ya kashe wajen kama ɗakin nan don kwana ɗaya kawai.

STORY CONTINUES BELOW

Ta ɗebo farfesun kifi na ƙarshe a cikin wani ɗan bowl sannan ta juyo tana hango shi daga can inda ya zauna a jikin table din yana magana, kuma kayan jikinsa na T-shirt da gajeran wandon nan suka sake tuna mata da wanda ke jikinta itama, ba shiri ta hadiye wani yawu a maƙogwaronta tana jinjinawa kaddara, don in ba ƙaddarar ba ba zata taba hango kanta a irin wannan yanayin tare da wani namiji kuma dadin daɗawa a Hotel ba.

Ƙafafunta duka karasa a hankali har gabansa, ta tsaya daga gefensa sanda ya dago daga rubuta wani abu da yayi a jikin wata ƴar jotter yana kallonta, ya taimaka ya ture mata kayansa dake kan table din kafin ta ajiye plate din a hankali kusa da dayan sannan ta juya niyyar dauko ruwa wanda tun dazu ta ganshi a fridge din dake can gefe, amma sai kawai taji ya riƙo hannunta na hagu, dogwayen yatsunsa suka ratsa cikin nata yana riko ta, a lokaci guda numfashinta ya katse a ƙirjinta yayin da yatsunta suka yi sanyi kalau!

Ya sake riƙo hannun nata sosai sannan ya jawo ta baya ta dawo gabansa, shi yana zaune ita kuma tana tsaye a gabansa da kafafunta duk a waje, ba shiri ta dunƙule tafin kafarta akan sassanyan marbles din ɗakin, sannan ta rufe idanunta a hankali tana jin yadda yake motsa yatsunsa a cikin nata.

Ta buɗe su daidai sanda ya gama wayar, idonsa yana kan kafafunta ne da har yanzu ta rasa me yake gani a jikinsu, kuma kafin ta gama tunanin hakan taji ya jawo ta zuwa kasa a hankali, ya durƙusar da ita a gabansa, dab dashi sosai wanda hakan yasa ta sunkuyar da idanunta ƙasa tana cije gefen lebbenta.

“Wata magana nake son muyi Please…”

Yadda muuryarsa a fito a hankali da kuma zurfi ya haddasa faduwa da saukar numfashinta.

“Zamu iya yi yanzu?”

Ya ƙara tambaya a lokacin da take kokarin tsayar da iska a kirjinta, da kyar ta daure ta daga kanta sau biyu babu kari. Shina ya gyada nasa kan a hankali yana cigaba da kallon fuskarta.

“Na sani a yadda komai ya fara a tsakaninmu  akwai tarin irin tunanin da kike yi akaina, na san an gaya miki tarin abubuwan da ba lallai ne na iya ƙaryata miki su ba, kinji wanene ni ta bangare da yawa na sani Amina, kuma har nima na bada gudunmawa wajen saka miki wani tunanin akaina tun a wancan lokacin, wani abu da nayi shi ne ba don komai ba sai don in hana faruwar auren a tsakanin mu.”

Yayi shiru ya cigaba da kallon fuskarta, kuma ganin yanayinta bai canja ba yasa shi cigaba.

“I’m a mess Amina, akwai tarin abubuwan dake gabana kuma a tsakiyarsu ne na tsinci zancen aurenmu wanda ni tun bayan lokacin dana rabu da Ruƙayya ban kara tunanin cewa zan sake aure ba, abubuwa sunyi min yawan da bana son nauyin komai ya sake ƙaruwa akaina, saboda haka wannan wasiƙar da na baki nayi ne don in tsorata ki ta hanyar da zai sa ki ƙi yarda sabida su Baffa baza su saurare ni ba a lokacin, abinda na manta a wannan lokacin shine ban isa in canja ƙaddarar da Allah ya hukunta ba tunda hakan babu abinda ya canja.”

A wannan lokacin numfashin dake ƙirjin Amina ya kasa tsayawa waje guda, sai kokari take dashi kamar kifin da ya fito daga rywa yana wutsil-wutsil, hasken fitukub dakin ya karu a idanunta yayin da wata iska ta shiga busuwa daga maka-makan windunan dskin kasancewar a sama suke.

“Daga ranar da na fara ganinki Amina, nayi nadamar abinda nayi, na san cewa ban kyauta ba da har na saka wannan tsoron da na gani a cikin idanunki, wanda duk da hakan kuma bai hana ki kyautata min ba, bai hana ki nuna min kirkin ki da kuma halayenki na gari ba, kuma yanzu wannan kirkin naki nake kwaɗayin cigaba da samu Amina, ina son nutsuwar da nake samu a wajenki don itace babban abinda nake bukata wajen tafiyar da rayuwata a yanzu, shi yasa nake rokonki da ki manta duk wani hasashe da kike yi kaina Please, ki bani damar da zamu yi normal life kamar yadda kowa yake yi, wallahi nayi alkawarin ba zan taɓa cutar dake ba insha Allah.”

STORY CONTINUES BELOW

“….Kamar yadda na faɗa miki mafitar ta riga tazo hannunki Amina, Kilishi ta bude miki kofar samun nasarar da ita kanta bata sani ba, so nake ki dauki dukkan maganganunta kiyi wa taki zuciyar ado dasu Amina, don takunta zaki bi, dukkan abinda ta fada kema shi zaki yi, banbancin da za’a samu tsakanin ke da ita shine, ke ita zaki yiwa Amina, ita zaki lulluɓe da rigar amincinki ba kowa ba, ita zaki zamewa farar wutar da ba zata taɓa sanin cewa ƙonata kike yi ba.

Kuma hanyar farko da hakan zata kasance shine idan kika sami soyayyar mijinki…”

Kalaman da Amma na ɗazu su suka biyo bayan dukkanin bayanin Ma’aruf a cikin kan Amina, ta tuna yadda take kallon Amman cike da ƙarin bayanin da bata furta ba Amman ta cigaba.

“Kilishi ta gaya miki cewa soyayyar mijinta ta fara samu a saman ta kowa, shi ya fara yarda da ita kafin ta buɗe zuciyar kowa ta fara aiwatar da manufarta, idan baki sani ba yau ki sani Amina cewar taƙamar kowacce mace a duniyar zuciyar mijinta ce, idan taci riba anan to wallahi duk girman wata matsala koda kuwa ta mahaifiyarsa ce ta tsallake ta.2

Yaron nan ya riga ya zama mijinki a yanzu ko munso ko bamu so ba, don haka kije ki ƙara dagewa, ki dage wajen kyautata masa har zuciyarsa ta ƙara yarda dake akan yanzu, sannan da zarar kun koma kije wajen Kilishi ki tsugunna ki gaya mata cewar kin yarda da sharaɗinta bama sai lokacin da ta gindaya miki yayi ba, ki ƙasƙantar da kanki a gabanta ta sigar da ba zata taba iya haska cikin zuciyarki har tayi wani hasashe ba, waɗannan sune matakan farko Amina, kuma ina tabbatar miki idan kika tsallake su, dukkan sauran zasu zo ne bi da bi kuma a sauƙake…”2

Waɗannan sune kalaman dake saka sa hannyenta rawa a ɗazu, sune kalaman Amman dake rikita lissafinta suna gaya mata cewar ba zata iya dorar da wani abu akan Ma’aruf ba tunda bata gama sanin tunaninsa akanta ba… Sai gashi tun ba’aje koina ba hanyar farko tazo mata da sauki.

Allah ya amsa addu’ar ta, Ma’aruf ya cire dukkan wani kokwanton dake zuciyarta da waɗannan iya kalaman nasa, a yanzu ta yarda cewa shi da gaske zuciyarsa wankakkiya ce akansa, abinda take ta taraddadi daga bangaren Hajiya Kilishi yake dama.

Taji yadda mamaki ke cinye zuciyarta tun daga ƙasa, ashe komai ba mai wuya bane kamar yadda Amman tace, kowacce mace tana da irin nata ikon a hannu, kawai burga da barazana ce ke saka wasu yin ƙasa su yarda cewa an fisu su baza su iya ba, gashi tun basu ko bar garin nan ba ta fara samun yardar Ma’aruf a hannunta, idan haka ne kuwa ta yarda da maganar Amma na cewar da gaske Kilishi ta kiyaye su, don ko ita a yanzu tana jin ƙarfin gwiwar cewa zata iya.

Kuma cikin wata irin sa’a, sai ya ƙyale ta bai nemi amsarta ba har suka kammala cin abincin da komai.

Wajen ƙarfe goma sha ɗaya saura Amina ta dunkunkune a karshe gadon ɗakin har a lokacin tana ta faman sake-sake a ranar, don ko ka kaɗan ba bacci take ji ba, abubuwan da ta fuskanta a yau suna da yawan da har yanzu basu gama narkewa a cikin ranta ba. Ta juya bayanta ne tana kallon ɗaya gefen ɗakin yayin da hannunta ke wasa da ƙarshen bakin mayafin nan data yafa a akanta.

A yanzu fitulun ɗakin duka a kashe suke, Ma’aruf ya kashe su kafin ya shiga toilet don ta riga shi kwanciya, sai da ya gama aikinsa tana kwance tana sake-sakenta sannan ya tashi ya kashe fitulun duka ya shiga toilet din.

A yanzu babu wani haske sai na waje da yake shigowa cikin ɗakin, kuma wucewar minti biyar kawai sai kofar toilet din ta buɗe, hasken fitilar ciki ya ratsa duhun ɗakin kuma duk da ta juya bayanta sai da hasken ya shiga idonta kafin taji ya rufe ƙofar duhun na sake dawowa.

Taji gadon ya motsa yana shaida mata hawowarsa zuwa daya gefen da sanda yaje jan sauran bargon da ta rufe ƙafafunta dashi zuwa nasa jikin.

Sakan ɗaya, biyu, suka wuce tana cigaba da wasa da mayafinta kafin taji muryarsa, can ƙasa a hankali kamar duhun daren.

STORY CONTINUES BELOW

“Amina…”

Ya kira sunanta kamar wannan ne karo na farko daya fara faɗa, yadda tunaninta ya tsaya cak haka ma daren ya tsaya, kamar shima yana jiran amsar da zata bayar ne.

Tayi kokarin haɗiye wata busashshiyar iska a makogwaronta sannan tayi dauriyar amsawa a hankali.

“Can I hold you.. ?” (Zan iya riƙe ki?)2

Bata san me take tunanin a wannan lokacin ba, bata san ma me taje yi va ko kuma abinda yake faruwa a cikin kanta, ta san dai kawai zuciyarta ta ƙirga wucewar wasu sakanni ne data san cewa jiranta yake yi kafin duk wata dauriyarta ta rinjaye ta wajen ɗaga kanta a hankali.

Kuma bata san ya akayi yaji ta ba, don a lokaci guda yasa hannunsa daya ya janyo ta zuwa jikinsa, ya juyo ta tana fuskantar sa yayin da hannunsa ɗaya ya zagaye waist ɗinta, sannan ɗan kaɗan ya ratsa ƙafafunsa a tsakanin nata.

Ya hade ta da jikinsa har tana jin kara bugawar zuciyarsa kamar kaɗawar igiyar ruwa a bakin teku wanda sautinsa ya haɗe da amon tata zuciyar, ya zama idanunta basa ganin duhun daren sai wanda ke tsakaninsu kawai, numfashinsu ya hade waje guda yayin da ƙamshin turare da kuma sabuntar kayansu ya cika hancinta.

Kuma bai isa Ma’aruf ya gama rikita zuciyarta ba sai da ya sunkuyo da fuskarsa daidai cikin wuyanta ba shiri kuwa jikinta ya shiga girgizawa gabaɗaya a cikin nasa, kuma ga mamakinta sai taji yayi wani abu kamar murmushi sannan a cikin kunnenta ya furta maganar data rikito da duniyarta bakiɗaya ta rugurguje.

“Kar ki damu, not now, not here.” (Ba yanzu ba, ba anan ba.)5

Shikenan! Ma’aruf ya gama da rayuwarta!

***

Kano.

09:30Am

No. 58 Mafara Street, NNDC Sharaɗa Quaters.

“Wai har kun dawo?”

Surayya ta faɗa a lokacin da ta fito dafa daki tana kallon Amina daje zaune a tsakiyar falon nasu tare da Sameerah wadda ta cika gabanta da kayan breakfast.

“Tun wajen ƙarfe takwas fa suka dawo. Yayan har ya tafi aiki ma.” Sameerah ta bata amsa lokacin da take hada nata tea din.

“Auren ma’aikacin kamfani na da wuya ko?”

Surayyan ta fada tana kallon Amina lokacin da tazo ta zauna a kusa da ita tana ɗaukan pillow ɗin kujerar zuwa cinyarta.

Da murmushi a fuskar Amina tace.

“Gashi nan dai, ni ban saba ba har yanzu.”

“Gaya min zaki yi idan da wuya tun wuri in kori Tahir.”

Kafin ta amsa Sameerah tace.

“Ki kore shi ma, don Wallahi Baffa yace ba wanda zai sake yiwa aure a gidan nan sai man da shekara biyar. Su Salma sun karya tattalin arzikinsa.”

Dariya kawai Amina tayi tana kallonsu lokacin da musun da suka saba a kullum ya kaure tsakaninsu, don ma wai Munaya na can ɓangarensu ne.

Sai dai duk yadda dariyar tata ta kai akan lebbenta kawai take, don daga can kasan zuciyarta taraddadi ne fal da kuma tunanin abinda ke shirin faruwa.

Don kamar yadda Samirah ta fadawa Surayya ne, tun wajen karfe takwas da ƴan mintuna na safe suka iso garin Kano, don Ma’aruf ya gaya mata cewar yana da tarin aikin dake jiransa a office, kuma ya sauke ta a gida ne ya tafi bayan ya rungume ta yayi kissing saman kanta lokacin da suka shigo ciki ya buɗe mata gidan da muƙullin dake jikin na motarsa, sannan ya juya ya barta tana kokarin hada zuciyarta waje guda ya koma wajen motar tasa da ya bari a waje.

Kuma shigarta gidan ya sake tsayar da zuciyarta waje guda, yana tuna mata da kalaman Amma.

“…da zarar kun koma kije wajen Kilishi ki tsugunna ki gaya mata cewar kin yarda da sharaɗinta bama sai lokacin da ta gindaya miki yayi ba, ki ƙasƙantar da kanki a gabanta ta sigar da ba zata taba iya haska cikin zuciyarki har tayi wani hasashe ba, waɗannan sune matakan farko Amina, kuma ina tabbatar miki idan kika tsallake su, dukkan sauran zasu zo ne bi da bi kuma a sauƙake…”

STORY CONTINUES BELOW

Zuciyarta ta gaya mata cewa wannan lokacin shine zaiyi daidai da zuwanta wajen Hajiya Kilishin, don a yanzu ne zata yarda cewa da gaske zuciyarta ta wanku wajen yarda da ita. Shi yasa ta tattaro dukkan dauriyarta ta taho cikin gidan inda Sameerah ta shaida mata cewa Mamin tana wanka.

“Kin gama? Mamin tace tana jiranki a ciki.”

Muryar Sameerah ta dawo da ita zahiri, ta ɗago tana kallonta daga can jikin hanyar koridon dakin Mamin, ta san lokacin da Surayya ta tashi ta shiga ciki amma ita bata san lokacin da ita ta tashi ba, taji zuciyarta ta buga a cikin ƙirjinta amma kuma sai fuskar Amma ta gifta a idanunta ta kore hakan, ta gyara yafen mayafinta sannan ta mike a hankali tana zagaye table din da Sameerah ta cika da kayan breakfast din, kafafunta suka taja cikin korido din lokacin da Sameerah ke gaya mata cewa ta tafi ta shiga wanka, kanta kawai ta gyada mata kafin ta rike handle din kofar dakin.

Da dukkan addu’o’in da zata iya karantowa a zuciyarta ta tura kofar dakin, kuma kamshin turaren wutar da taji tunda ta shigo dakin shi ya fara shiga hancinta, ta hango shi kuwa yana ci daga can kan bedside drawer dakin daga cikin wata haɗaddiyar burner irin wadda Sameerah ta taba kai mata.

Sai taji ta shaki wata busashshiyar iska a makogwaronta lokacin da ta hango Mamin, tayi wankan kamar yadda aka fada ta shirya cikin wata doguwar rigar atamfa da aka baza mata stones tana ta kyalli, kamar ƙyallin dake son nunawa duniya cewa ita kadai ce Kilishi irinta.

Ƙafafunta suka karaso ciki da sallama, sallamar da Mamin ta amsa da murmushi a fuskarta, murmushin nan nata mai nauyin da sai a yanzu Amina ke jinsa a saman kafadunta.

“Ashe ƴan jigawan har sun dawo, yaya kuka tarar dashi Amina?”

Takaicin da ya taho ya taru a kirjinta wani abu ne da ba zata iya misalta shi ba, amma haka ta daurewa masa ta amsa.

“Jikinsa da sauki Mami.”

Kuma sai da ta jira ta nemi bakin gadonta ta zauna sannan kai tsaye muryarta ta sake fitowa.

“Mami na yarda da dukkan zancenki, na yarda zanyi dukkan abinda zaki sani ba tare da wani ya san komai ba, dan Allah kar ki sa a sake taɓa kowa a cikin ƴanuwana, raunin dake jikin Aminu yayi yawa, dukkan kafafunsa biyu sun karye… Zanyi dukkan abinda kika ce da yanzu Mami don ni kaina ina son rayuwata ta inganta, na miƙo miki hannayena kamar yadda kika umarta don ba zan taɓa yin katoɓarar yin ganganci da rayuwar iyayena da ƴanuwana ba, darajarsu tafi komai a wajena.”

Muryarta tayi shiru na wani lokaci sannan ta sake ratsa shirun ɗakin amonta na rawa.

“Na rantse da ubangijin daya halicce ni Mami, zan yi miki biyayya kamar yadda kika umarta, baza ki taɓa dana sanin bayyana miki sirrina ba insha Allah.”

A cikin ɗakin wani irin shiru ya sake giftawa, irin shirun nan mai tsantsar zurfi, zurfin da a cikinsa zukata ke saƙa abubuwa da yawa, kamar yadda zuciyar Kilishi ke saka mata dubunnan abubuwa a wannan lokacin yayin kallon Amina take da dukkan irin nazarin da ƙwaƙwalwarta ke iyawa, tana jin yadda a bayan kanta wasu kofofi ke buɗewa kuma tunaninta na nutsewa cikinsu na son gano wani abu daban saɓanin abinda bakinta ke furtawa.

Sai dai duk iya kokarinta, ta kasa gano abinda yake saman fuskar Aminan, a wannan lokacin, don tsoro da kuma rudanin da take gani karara suna fitowa tare da kalamanta, kuma takaicin yadda ubangiji ya biye sirrin kowacce zuciya ya kamata, don baza ta taɓa yarda kai tsaye cewa yarinyar nan ta karbi tayin ta kai tsaye haka ba, amma da yake ita Kilishi ce, sai tayi gyaran murya a hankali sannan ta faɗaɗa murmushin dake kan fuskarta, a kusa zata gane komai ba sai anje da nisa ba ta yiwa kanta wannan alƙawarin.

“Shi yasa na barku kuyi tafiyar nan dama Amina, don so nake kije ki ga ɗanuwanki ki san cewa babu wasa a al’amarina kamar yadda na jaddada miki komai, kuma Alhamdlilah naji dadi sosai da idonki ya buɗe kika fahimci gaskiya tun a yanzu, tun kafin mu shigo da wasu cikin lissafin.”

STORY CONTINUES BELOW

Muryarta ta fito ne da wani irin sanyi kamar ƙanƙarar dake narkewa a cikin ruwa, Kuma da faɗin hakan bata jira komai ba sai ta taso, ta wuce ta ta nufi wardrobe ɗin dake dakin. Wajen da ta bude na farko ya nuna mata ajiyar da tayi na wata bakar jaka, ta dauko ta sannan ta sake buɗe wani wajen inda jakunkunan ta suke a jere, kuma a cikin aljihun guda ɗaya ta ɗauko Sachet mai yawa na wani magani sannan ta rufe komai ta juyo, da takunta a hankali ta sake dawowa wajen da Aminan ke zaune akan carpet, inda daga gabanta akwai wani stool da aka bari a wajen, ta ajiye wannan jakar da kuma magungunan a gaban Amina sannan ta nemi kan stool din ta zauna kafin muryarta ta sake ratsa dakin.

“Komai mai sauƙi ne Amina, umarni na kawai zaki dinga bi shikenan sai duniyarki ta koma kamar aljanna, don zan cika miki dukkan wadannan alkawuran dana dsukar miki har ma da karin wasu da bamu lissafa ba, Kin fahimce ni ko?”

Kuma kamar yadda ta zata, sai ta ɗago ta kalle ta idanunta na shaida sauran tsoron da a lokacin dama ya kamata ace yana barin fuskar tata, ta gyaɗa kanta sau biyu sannan ta sake maida shi kasa, kuma abinda Hajiya Kilishi ta gani a idanun nata ya shiga barazanar goge kokwanton da take yi akanta, amna tayi wulli dashi a lokaci guda.

“Yayi kyau, yanzu ki saurareni sosai kiji abinda nake so dake.”

Amina ta sake gyaɗa kanta tana ƙara gyara zamanta lokacin da Muryar Hajiya Kilishin ta cigaba da shiga kunnenta.

“Akwai abinda zanyi a kamfanin su Ma’aruf cikin satin nan, kuma zan yi shi ne ba tare da yana nan ba, don haka yanzu za ki taya ni abinda ya kamata ace ni zanyi don dama lokaci yayi da hakan zai koma hannunki.

Abinda ke cikin jakar nan magunguna ne, na san an gaya miki cewa Ma’aruf yana da wata rashin lafiya ta ƙwaƙwalwa, sunanta ‘Bipolar Disorder’ ya same ta ne a shekarun baya lokacin da rayuwarsa ta canja bayan rasuwar ɗanuwansa, cuta ce dake canja tunaninsa a duk lokacin da ta tashi, abubuwa suna cakuɗewa a cikin kansa har baya sanin abinda yake yi.

A London ake yi masa magani tun daga wancan lokacin kuma suna ɗora shi akan ingantattun magunguna tun daga sannan, amma da farko Ma’aruf bai karbi ciwonsa hannu biyu ba balle har ya dinga kula da kansa, baya taba shan magungunan sa akan kari wanda hakan ke ƙara bawa ciwonsa bigiren yaɗuwa, tun kafin yayi aure nake yi miki wannan zancen Amina kuma tun a sannan na karɓi magungunansa na ajiye a wajena.

Ma’aruf kamar ɗan dana haifa na dauke shi, kin sani tun a wancan labarin dana baki, don haka a baya na tsaya da ƙafata sosai wajen takura masa a duk lokacin da ya kamata yasha maganin, kafin daga bisani na fahimci cewa hanyar nasarata tana tattare da ikon da nake dashi ne akan magungunan sa. Ina son Ma’aruf Amina, amma son da nake yiwa cikar burina yafi karfin nasa, shi yasa nake rufe idona a duk lokacin da buƙatar in kwantar dashi ta taso min ina yin hakan.”

Tayi shiru na tsawon wasu sakanni tana kallon yadda tasirin maganganun ke aiki a fuskar Amina kamar yadda ta zata kafin ta cigaba.

“Magungunan dake cikin jakar nan har America naje na nemo su Amina, magunguna ne dake birkita ƙwaƙwalwar mutum a lokaci guda ya fita daga hayyacinsa, kuma dama ciwon Ma’aruf abinda yake bukata kenan ya tashi, don haka duk sanda nake shirin yin wani abu da na san zai iya zame min ƙalubale, sai in kwantar dashi in gama duk abinda zan yi kafin ya dawo hayyacinsa.”1

Ta kai karshen maganar kamar bata karasa ba, don dukkansu shiru suka yi yayin da nauyin kalaman ke zagaye iskar dakin, ba irin ga Amina da taji hannayenta har rawa suke yi ɗauke da sabuwar rikicewar da maganganun suka sata, don yau ne karo na farko da ta ji ciwon Ma’aruf daga makusantansa, ko shi bai gaya mata ba, cewa kawai yayi ‘I’m a mess Amina…’

Zuciyarta ta ajiye komai a gefe ta shiga gaya mata cewa har ta gama rayuwarta a duniya ba zata taba iya haɗuwa da wata muguwar halittar irin Hajiya Kilishi ba.3

“Na san idan Ma’aruf yayi aure dole ne zargi zai shiga zuciyar wasu idan har na cigaba da rike magungunan sa, don haka wannan yana daya daga cikin dalilan da suka sa na kawo ki gidan nan, daga yau magungunan nan sun koma hannunki.

Ki ɗauka ki tafi dasu, guda uku ne a ciki, ki ɓalli kowanne guda ɗaya ki bashi a gobe, don jibi zan fara aiwatar da abinda ke gabana kuma a sannan bana buƙatar ganinsa a kamfanin.

Wannan shine aikin ki na farko Amina, kuma idan komai ya tafi daidai, zaki fara ganin daidai  bari nayi miki alkawarin farko tun a yanzu, idan na samu abinda nake so Amina zan sa a fitar da ɗanuwanki Aminu ƙasar waje a gyara masa kafafunsa su kamar yadda duke a da.”

Shirun da ya sake ratsa ɗakin mai tsawo ne da babu abinda zaka tsinta a ciki kafin Hajiya Kilishi ta kai ƙarshen zancenta da magana ta karshe kuma mafi girman da daki zuciyar Amina babu zato, maganar da daga ita har Amma basu taba hango ta ba balle tasa ta a jerin tunanin Hajiya Kilishin, kuma duk da dauriyar da take da ita a lokacin sai da kalaman suka tasa allon kirjinta girgizawa da karfin da ta san har Mamin ta lura.

“Maganin dake gefe kuma naki ne Amina, ki dauka ki dinga shansa kullum, na san ba zan iya hana Ma’aruf kula ki ba idan har yayi niyya, amma kuma ba zan lazimci wani abu ciki ba don babu shi ko kadan a cikin lissafina!”2

***

Yaya kuka ga sharaɗan farko na Kilishi??

Ta yaya kuke ganin Amina zata bullo musu????4

Ta yaya zata sa komai ya faru ba tare da Hajiya Kilishi ta ɗorar da zargin da take mata ba??1

Mu dai jira hukuncin Amma ko??

And the Uban gaiyar is over there going crazy akan ƙafafun Amina ba tare da ya san me ke shirin tunkaro shi ba!?1

Wani ya gaya masa cewa su Rukayya ma na can nayi masa nasu shirin suma…

Jawad ma kuma yana nasa!

A tsakiyar komai kuma dai, zamu samawa Ma’aruf wannan nutsuwar da yake nema insha Allah.??

About AIS

Check Also

FARAR WUTA CHAPTER 2 BY AISHA MAHMOOD

FARAR WUTA CHAPTER 2 BY AISHA MAHMOOD Www.bankinhausanovels.com.ng  A wannan daren…+ NO. 38 Ramie Street, …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *