DEEMAH CHAPTER 7 BY ZAHRATEEY

 DEEMAH CHAPTER 7 BY ZAHRATEEY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

No.1 hausa novels, site all over the world with more than 5000 books uploaded, the site was found on 2014 by ////////////

All our books are free, we do not charge for uploading , we upload novels, daily and over 400+ chapters montly.

Tunda na tashi yau nake jin faduwar gaba, ga wani irin bugawar zuciya dake damuna, ga zazza6i duk ni kad’ai, toh meke ishirin faruwa ne haka? Nayiwa kaina tambaya, tabbas akwai wani abu dake faruwa wanda ya danganci rayuwata. “lafiya kuwa, meke damunki?” _Kisma_ ta fad’a tana k’arasowa kam gadon, hannunta ta kai ta ta6a wuyana da goshina duk taji zafi rad’au “baki da lafiya fa, kinji jikinki kuwa, bari in had’a miki ruwa kiyi wanka sai muje asibiti” ta fad’a tare da shiga toilet din. Mintina kad’an tayi sannan ta fito ta taimakamin na daura towel sannan na shiga nayi wanka, ban wani dade ba saboda rashin karfin jiki, dan ma ruwan dumin ya min dadi.

+

Bayan na fito na samu harta fito min da kaya doguwar riga me dogon hannu, daker na iya fesa body spray ko mai na kasa shafawa kawai nasa inner wears sannan na saka doguwar rigar, turare ma _Kisma_ ce ta tayani fesawa. A falo muka samu su _Alaja_ “lafiya meke damunta” duk suka fad’a a tare, bayan ta musu bayanin cewa zazzabi ne kuma asibiti zamuje sai sukamin fatan samun lafiya, sannan mijin _Alaja_ ya bamu kud’i masu dan yawa wai muyi amfani da shi. A waje muka samu direban yana jiran mu, babu wani 6ata lokaci muka kama hanyar asibiti.

Kamar dai ko yaushe asibiti ba’a raba shi da tarin jama’a, kasancewar saurayin _Kisma_ yana da duty din safe sai komai ya mana sauki bamu bi layi ba, dan ya fito da kansa gurin nurses station yasa suka mana abubuwan daya dace sannan ya kar6i folder dina muka wuce tare, dayawan mutane sunji haushi domin tun safe suke gurin amma ko gamawa da nurses station basuyi ba balle ace an kai folder dinsu har su saka ran ganin likita, domin wanda suka samu dama ire iren mu duk sun shige sun bar su, da wanda suka san nurses da wanda suka san doctors da wanda suka san metrons duk dai wanda suke da connection da manya da kananun ma’aikata. (Jama’a muji tsoron Allah mu rinks adalci a duk inda muka tsinci kan mu, ku rinka bin komai yadda yazo ba wai mu rinke juye shi ba, wallahi idan wani ya yafe wani ba zai yafe ba haka kuma bakin wani guba ne sai kaga ka kasa samun cigaba ko nasaran dakake bukata idan da zaka bincika sai kaga is all due to irin wadannan kananun laifukan da ba’a d’auke shi a bakin komai ba, akwai emergency cases wanda ba sai an sanka ba da anga yanayin ka za’a fara ta kanka amma wanda zai iya jira ya daure ya rinka yin abu tsakani da Allah dan kowa nada nashi uzurin a rayuwa a kuma ko ina Allah ya ajiye mu muyi kokarin kwatanta adalci).

Bamu wani jima ba muka fito muyi running wasu test, wanda zamu kar6a a ranar muka jira sauran kuma sai washe gari, abin ma yazo da sauki ba sai mun dawo ba yace zai kar6o ya kawo mana sai yamin bayanin duk abin daya dace, wasu magunguna kawai muka saya muka wuce, a mota nake cewa _Kisma_ bamu kyauta bafa munje mun samu mutane amma saboda mu muna da yanda zamuyi ga shi har mun gama mun fito su kuma ko oho, daure fuska tayi alamun haushi taji kenan, ni kuma ban fasa magana ba sai da na fad’a mata rashin jin dadin abin da muka aikata duk da cewa ina jin jiki amma dayawa kila sun fini amma basu da mafita, karshe ma earpiece ta saka ta kyaleni, murmushi kawai nayi na kwanta a jikin kujeran motar har muka isa gida.

Sai a lokacin ta kulani ta taimakamin muka shiga cikin gida, lokacin sallar azahar yayi da alamu shiyasa muka taras ba kowa a falon sai su _Ummita_ suna wasa amma anata cin zalinta, idan tayi ihun tayi ihun sai tayi shuru idan ta samu dama sai ta gantsara musu cizon da sai hakoranta ya fito daganan sai ta sulale ta gudu idan kuma suka kamata gashinta shi zai yi bayani ranar. As usual hakan ne ya faru, ta samu dama ta aikata abin da take so ta gudo d’aki, ina shan tea ta fado kan gadon tana zare ido alamun rashin gaskiya “ke meye hakan wai” na tambaya ina kallon yanayinta, dama fuska tayi tana shirin kuka, ita dai kuka baya mata wuya asaran hawaye kamar a kanta aka sauke kuma tanayi tana lashe hawayen, ni dai ba haka nake ba sai dai idan wani a cikin dangin babansu ta biyo, “idan kika min kuka sai na zane ki sai kiyi me dalili” da sauri ta hadiye kukan ta kara matsowa kusa dani tana kallon kofa, bance mata komai ba har na gama na sha magani, alwala ma da zan shiga ban d’aki bina tayi sai da _Hindatu_ ta dauketa suka fita.

Ina idar da sall na kwanta dan hutawa, duk da cewa har yanzu jikina da zafi babban damuwata faduwar gaban dake damuna, na san dai hakan na yawan faruwa dani ne idan har wani abu zai samu wani na kusa dani ko kuma ma abin ya riga ya faru, ganin na kasa samun sukuni yasa na samu _Alaja_ ta kira gida taji komai lafiya lau sai dai 6atan mu shine kawai damuwar, daki na koma na kwanta ina yan adduo’i a zuciyata, idan ba gidan mu ba kenan mijina ne wani abu yake faruwa da shi, tunanin hakan ne ya karamin tashin hankali nan danan zazza6i ya sake karuwa jikina ya koma kamar garwashi.

Har dare jikina yaki dadi sai da aka dauramin drip sannan na samu barci, yaran kuwa ashe kuka sukayi tayi dan ganina a kwance babu lafiya, daker _Hindatu_ da _Kisma_ suka rarrashe su  suka samu sukayi barci amma sai ajiyar zuciya sukeyi. Ni kam barci ne ya daukeni sosai amma mafarke mafarken da nayi sune basumin dadi ba _Sufyan_ dina tare da wata mace bayan _Jidda_.

_______________________

Jama’a ne da yawa a ciki da wajen masallacin dake cikin karamin kauyen dake a cikin Forest wanda yake hanyar _Jos_ mutane sai fitowa sukeyi suna musabaha da ango tare da taya shi murnan aure, sosai yake cikin farin cikin auren _Bibalo_ domin yarinya ce me hankali da tarbiyya wanda mazan gari kowa yake fatan ta kasance matarsa amma sai Allah yasa shi din shine mijinta, fara’a sosai ke bayyane a saman kyakyawar fuskarsa. A haka har aka soma watsewa ango da abokansa suka nufi gidansu amarya domin su kwashi gaisuwa.

Amarya tayi kyau matuka a cikin atamfa riga da zani ta sha d’auri me kyau haka kwalliya dai-dai misali sosai kowa ke yaba kyaun da tayi ita kuwa babu abin da yake ranta kamar taga d’an binni, so take yazo ya yaba kwalliyar da kansa hakan zai fi sanyaya zuciyarta, tana cikin tunani akayi sanarwan ga ango da abokansa, wani irin dadi taji a ranta kamar tayi tsalle taje ta shige jikinsa ita kam Allah ya gani tana son d’an binne sosai da sosai, kawayenta ne suka gyara mata lullu6i sannan suka riko hannunta suka fito tare, direct gurin ango da abokansa sukaje inda akayi ta daukan hoto, su kuma ango da amarya sai satan kallon juna sukeyi har aka gama aka waste.

Kasancewar gidanta na bayan gidan _Baffa_ shi yasa ba’a kaita da wuri ba sai bayan da akayi sallar magriba, sosai tayi kuka duk da cewa ga gida ga gida, babban abin da yasa ta kukan nasihar da iyayenta da kuma goggoninta suka mata shine ya tsinka mata zuciya ta fahimci cewa auren ma yaki ne na mata wanda sai kayi hakuri ka kauda kai kuma ka kai zuciyarka nesa sannan zaka samu salama tare da natsuwar zuciya domin ba wai dadin cikin auren zaka fuskanta kawai ba har da rashin dadi da kuma wasu jarrabawa da zai iya riskar ka, sosai suka mata nasiha me sanyaya zukata mesa zuciya ta rusuna, kuma ta tuna da cewa zaman duniyar kanta ma ibada shine a kan gaba balle kuma zaman aure wanda yake dauke da taken “aure ibada” a haka har aka kaita gidanta tana kuka tare da sanyawa a ranta cewa ibada shine abin da ya kaita kuma zatayi kokari gurin kare martaban da mutuncin gidansu ta hanyar yin biyayya tare da kiyaye ayyukan dana sani. Bayan sallar ishai ango da abokansa suka iso akayi duk wata alada da aka saba sannan suka tafi suka bar amarya da angonta, suna masu musu fatan alkairi acikin rayuwarsu.

Sati biyu nayi a kwance kafin na samu karfin jikina, su _Ummita_ ma duk sai da sukayi zazza6in sati guda dan tunda suka ganni a kwance su ma suka fara zazza6i. Duk da cewa naji saukin jikina amma duk da haka wani lokaci sai inji ba dai-dai ba idan na tuna mafarkin da nake yawan yi na mijina da wata mace daban bayan _Jidda_ ban sani ba ko duk kishi ne yake damuna shiyasa nake wasu tunanin na daban, da karfin addua na samu wasu abubuwan suka ragu.
+
Lokaci wucewa yakeyi ba tare da jiran wani ko wata ba, shiyasa yake da kyau mutum ya yawaita aikata alkairi a duk inda yaje ko kuma duk inda yake, lokaci baya jiran kowa sai dai a jirashi, haka mutuwa sai dai ya tunkare mu kai tsaye a lokacin da wa’adin mu ya cika ba tare daya kwankwasa mana kofa ba, rayuwa yana tafiya da dadi da rashinsa wanda hakan ne yake sa mutum ya kara samun darasi na zamantakewar yau da kullun, lokuta da dama sai dai mu dogara da wasu mutane kamar mu, mu kan manta da cewa Allah shine kawai wanda ya isa ya yaye mana duk wani damuwar mu, wani lokaci sai mutum ya ga rayuwarsa baya tafiya dai-dai, shirka ma’ana had’a Allah da wani halittarsa yana d’aya daga cikin manyan laifukan dake durkushe rayuwar dan Adam, idan da ace mutane zasuyi dogaro ga ubangiji wanda ya halicci komai da komai kuma yake sanin duk abin da yake wakana a cikin rayuwar halittarsa koma muce ya riga ya sani tun kafin ya halicci komai da komai ya zo mana da sauki, da rayuwarmu tayi haske, da rayuwarmu ya kyautatu kuma mun samu dacewa duniya da lahira.
Kamar yadda lokaci yake tafiya kuma muke kara nazarin rayuwa tare da d’aukan dabi’u da darrusa masu kyau kuma muke ajiye dukkan ayyukan da basu da kyau hakan komi yake tafiya dai-dai a gurin mu cikin lami da lumana. Mun cigaba da zuwa makaranta tare da neman ilimi dai-dai gwargwado da tsare kan mu da mutuncin mu kamar yadda yake a cikin addininmu, a matsayin mu na mata munyi kokarin kare martaban gidan mu dana kanmu da kan mu, ba tare da mun bari harsashen mutane akan yan matan jami’a na lalacewa da tarwatsa tarbiyyan da suka samu ya tabbata akan mu ba.
A yanzu haka muna ajin karshe a cikin _UDUS_  dani da _Kisma_ inda ni nake aji na biyar ita kuma take aji na hudu, cikin shekarunnan abubuwa da yawa sun faru ciki har da rashi da mukayi na mijin _Alaja_ da kuma _Inna Tani_ kanwar _Inna Abu_, kuma a lokacin ne su _Mama Qudi_ suka san cewa muna _Sokoto_ kasancewar duk yan gidan mu sun zo hakan ya faranta ran mu domin munyi kewarsu, sosai sukaji dadin ganin mu har da kukansu, _Mama Qudi_ ta nemi gafarata kuma na yafe mata, kafin su koma dai muka sasanta komai ya wuce a gurin mu baki d’aya, yara kuwa sun sha gata a gurin yayyina da kanne na, kowa so yake ya dauke su, ga kaya da abubuwan ciye ciye da suka jibgo musu ga yawo da suke fita dasu cikin jin dadi da annashuwa, sai da sukayi sati biyu sannan suka koma suka barmu da kewa.
Bayan haka kuma _Baba K_ ya karye sanadin dukan da matarsa tayi masa kuma ta sai da gidan ta sai da shagonsa sannan ta had’a da gidan _Inna Abu_ duk ta sayar a garin son kudin su, ko da muka tambayi yanda akayi _Goggo Fulera_ take cewa ai matar ta sayi wani gida me kyau ne shine suka koma ciki da ita da _Inna Abu_ da  _Baba K_ bayan komawarsu tazo ta kore su a gidan(su _Mama Qudu_), shine suka sayi wani gida da kud’in business din da suka fara, domin suma sun samu alkairi da yawa a cikin kasuwancin nasu, bayan sun bar gidan sai ta sayar ta had’a da shagon _Baba k_ da gidan _Inna Abu_ bayan ta sayar sai ta koresu daga gidan bayan tayi wa _Baba K_ dukan tsiya daya so ya yi mata rashin d’a’a, sosai muka kwashi dariya a lokacin da ake bamu labari, wai yanzu haka suna gidan dasu _Ya Kolo_ suka saya duk sun zama wani iri, kuma sai a yanzu suka fara tunani na da neman Inda muke nida _Inna Suwaiba_ da _Kisma_ wai su nemi yafiyarmu dan kila harda alhakin mu yake bibiyarsu.
STORY CONTINUES BELOW
Yanzu haka muna ta shirin rubuta jarabawan karshe kafin mu koma _Bauchi_ saboda _Alaja_ itama zata koma _Lagos_ gurin yan uwanta. Komai da zamu tafi dashi mun shirya mun had’a komai a guri d’aya, yaran suma sun k’ara girma yanzu suna shekaru na hudu da yan watanni, har sun fara zuwa wata makaranta suna nursery 2, rigimar su kuma dai abin da tayi gaba gasu da shiga rai ga kyau ga tsawon kafa, dan idan ka gansu zakace sun kai biyar suna neman na shida, ga shegen wayo da kuma kwakwalwar rike abu. Fannin islamiya ma ban barsu kara zube ba, sai da na tabbatar suna fahimtar komai idan akace abu babu kyau akace za’a shiga wuta idan anyi nan danan suke tsorata su bari, hakan ya d’an rage musu wani abu fannin rashin ji, haka idan akace idan sunyi abu zasu shiga aljanna shikenan kuma har sai kun gaji da jin sunayi din.
6angaren _Kisma_ da likita kuma har an sanya musu rana, da zaran mun gama za’ayi biki a _Bauchi_ duk da haka _Baba K_ bai san da hakan ba sai dai yan uwansa ne suka sani, dan sunce mu bari sai mun koma sai yaji zancen tunda dama ya sallama mu. A nawa 6angaren han yanzu ina adduar Allah ya bayyana min mijina kuma yasa ya soni a cikin zuciyarsa kamar yadda nake son shi. Maganar aure har an gaji dayi min dan da zaran anyi zan fara kuka, hakan yasa suka hakura da zancen akan da zarar na gama karatu za’a had’ani da malaman rukiyya domin su duba ni, ni dai kawai jinsu nake yana shiga yana fita kamar iska.
_________________________
Zaune yake a gaban _Baffa_ suna hira kamar ko yaushe, dama gurin zuwansa kenan ya d’auki karatun addini sannan suyi hiran duniya kafin ya koma gidansa. Suna gama hira ya yi wa _Baffa_ sallama sannan ta wuce gidansa.
A saman sallaya ya same ta tana karatun alkur’ani, sai da ya jira ta gama sannan suka shafa adduar tare, “sannu da dawowa” yace yauwa “sannu da zaman gida na barku ku kad’ai” murmushi tayi sannan tace “babu komai ba ga shi ka dawo ba, wata rana ma kila ni zan tafi in barku ko kai ka tafi ka barmu” 6ata rai yayi hakan yasa ta shiga ba shi hakuri, sannan ta kara da cewa “abu me kyau ne mu rinka tuna mutuwa a ko da yaushe saboda bamu san Inda zata riske mu ba, sannan tunawa da mutuwa yana sa mu samu saukin son zuciya, domin idan muka tuna cewa zamu mutu baza mu rinka damuwa da k’ele-k’elen duniya ba zamu rinka tunawa da lahira kuma baza mu damu da talaucin da muke ciki ba domin mun san cewa idan muka mutu ba za’a binne mu da wani abu daga cikin abin duniyar da muka tara ko ak’asinsa ba sai dai da likafani wanda shi ne zai zame mana rigar karshe, idan mukace ba zamuyi tunanin mutuwar ba babu tsimi babu dabara dole zai zo, idan kuma mukayi tunanin sai kaga mun kara samun imani mun cire son zuciya a zuqatan mu mun koma ga Allah, shi mutuwar yana kan kowa dan haka dole ne mu rinka tunawa da ita domin ya kara mana tsoron Allah da kuma fuskantar tanadin da mukayiwa lahirar mu” ta fad’a d’auke da murmushi a fuskarta, kallon ta kawai yakeyi yana me alfaharin samun mace kamarta, zai so ace ya tuna koshi waye domin ya sadata da ahalinsa itama ta samu farin cikin ganin danginsa, ya san cewa duk wani masoyinsa zai mishi farin cikin samun mace irin _Habiba_, _BibanSufyan_ ya furta, d’ago kanta tayi ta kalle shi, “ina alfahari dake kuma ina kaunarki har cikin zuciya ta, ina sonki matata uwar y’ay’ana” wani irin dadi ne ya ziyarci zuciyarta, a duk sanda ya furta mata kalmar so ko kuma kalaman soyayya sai taji kamar tafi ko wace mace sa’ar mijin kwarai me son farin cikin iyalinsa…
Shekaru uku kenan da aurensu, kuma yaransu uku, biyu yan biyu ne mata sai yaronta wanda take shayarwa a yanzu, zama sukeyi cike da so da kaunar junansu, zama me tsafta da natsuwa hade da kwanciyar hankali, abu d’aya ne yake damunta da shi, yawan ambaton _Jidda_ idan yana barci, hakan ya nuna mata cewa akwai wata mace a rayuwarsa ta baya, fatan ta Allah ya dawo mishi da tunaninsa domin taje ta ga danginsa, sai dai duk sanda ta tuna da Kalmar _Jidda_ sai taji faduwar gaba…
_________________________
Gida ne me kyaun gaske me d’auke da 6angarori mabanbanta, kyau da girman gidan ya zarce dukkan tunani, sai ma ka shiga gidan zaka fahimci cewa naira na aiki bama kad’an ba, ga masu tsaro dake da tarin yawa, kuma a ko wani 6amgare akwai gidaje uku a jere, sannan ko wani 6amgare da na shi gate din. 6angaren farko shine na me gidan baki d’aya wato _Alhaji Sudais Muhammad_ da suke kira _Daddy_ da matansa biyu _Lami_ da suke kira da _Mama_ sai kuma _Halima_ wacce suke kira da _Hajja_. Sai 6angare na biyu _Kawu Sadis_ da suke kira _Abba_ da matansa biyu _Maryam_ da suke kira da _Amma_ sai kuma  _Rukayya_ da suke kira da _Momma_. 6angare na uku kuma _Kawu Samir_ da suke kira _Baba_  da matansa _Wasila_ da suke kira _Momy_ sai _Rashida_ da suke kira da _Mamy_ sai 6angare na hud’u _Kawu Salman_ wanda suke kira _Abbu_ da matansa _Bilkisu_ wacce suke kira _Ummi_ da _Hauwa’u_ wacce suke kira _Anty_ sai 6angaren karshe shine na _Sufyan_ da matarsa d’aya _Jidda_ wacce suke kira da _Ammi_.
Ga6a-d’aya gidan Allah ya albarka ce su da tarin y’ay’a mata, ko wani 6angare suna da takwas takwas, ko wace mace hudu, sa6anin 6angaren su _Lami_ wacce bata da ko d’aya _Halima_ kuma take da kwaya d’aya  _Anty Aisha_ sai bayan da suka cire rai da zata sake haihuwa shine ta haifi _Sufyan_ wanda da yawan mutanen gidan suka tsani su bud’e ido su gan shi a gidan kasancewarsa magajin ga _Alhaji Sudais_ wanda bayan dukiyar da Allah ya azurta zuri’arsu da samu shima yana da na shi na kan shi wanda ya zarce wanda mahaifinsu ya tafi ya bar musu, dukiyane me tarin yawa kuma shine mamallakin _A&S_ Companies da Parks ma’anar _A&S_ kuwa shine _Aisha&Sufyan_ y’ay’ansa biyu da Allah ya azurta shi da samu.
________________________Wata babbar macece ta fito daga cikin d’aki tana cewa “dama ashe zaki dawo, ai nayi tunanin kin tafi kenan saboda abin da bai kai ya kawo ba, na fad’a miki ki hakura da auren _Sufyan_ domin ba zanyi fatan had’a zuria dasu ba, sanin kanki ne cewa dan kishiya tace kuma bana tunanin ita ma zata so had’a zuria damu, dan haka ki cire shi a ranki _Hanifa_”.
+
Kallonta wacce aka kira da _Hanifa_ tayi sannan tace ” yanzu duk irin son da nakeyi wa _Ya Sufyan_ sai ya tashi a banza dan saboda son kai da son zuciya irin naku keda _Ummata_ wannan wace irin rayuwa ce _Mama_ a gaskiya bana tunanin zan iya hakuri da rashin shi a cikin rayuwata, na Riga na fad’awa _Ummata_ cewa matukar baku dawo da shi ba tabbas ni zanje har gurin _Daddy_ in sanar da shi abubuwan dake faruwa, dan kunga cewa _Hajja_ macece me hakuri da kawar da kai? Haka zalika dan kunga cewa _Anty Jidda_ macece me saukin kai da d’aukan duniya ba a bakin komai ba? Karfa ki manta _Anty Jidda_ da _Hajja_ suna da masaniyar cewa kune silar 6atan _Ya Sufyan_ shurun da suka muku ba wai tsoro bane kawai sun bar wa Allah komai ne, toh wallahi _Mama_ ku tuba tun wuri tun kafin abubuwa su dagule kuzo kuna dana sani, matukar kuma bakuji bari ba to zakuji hoho” ta fad’a tana barin gurin zuwa side d’in _Anty Jidda_.
A birkice ta shiga 6angaren _Jidda_, ganin yadda ta fad’o kamar an biyota yasa _Jidda_ ta tashi tana cewa ” _Hanifa_ lafiyarki kuwa, kina matsayin mace kina irin wannan gudun?” Ganin hawaye a idonta yasa tace “subhanallah! Lafiya kuwa, meke faruwa meke damunki ne haka?” Sauke kanta tayi kasa ” _Anty Jidda_ na san kinsan gadkiyar abin da ya yi silar 6atar baban su _Afifa_ haka itama _Hajja_ ta sani, shin menene yasa ba zaku d’auki mataki ba, bafa yanzu suka fara illata ku ba, sunyi akan yaranki da basuji ba basu gani ba saboda wani banzan kudurinsu, tabbas yanzu na kara sanin dalilin bakin zuciyarsu ne yasa aka haifeni a titi ita kuma dayan Allah ya hanata haihuwa” ta fad’a tana cigaba da kukanta.
Tausayinta ne ya kama _Jidda_ tana sane da cewa _Hanifa_ na son mijinta kuma tayi wa kanta alkawarin had’a auren su, tabbas zata cika domin _Hanifa_ bata da bakin zuciya irin na iyayenta, tana tausaya wa yarinyar domin har zuwa yanzu an rasa me aurenta saboda bata fito ta hanya me kyau ba, “kiyi hakuri kinji, kuma ki rinka tausasa harshenki akan iyayenki, domin hakan bai dace ba, ko me zasu miki ki daure kiyi hakuri ki kai zuciyarki nesa saboda gujewa fushin ubangiji” d’aga kai kawai tayi saboda kukan nata yaki tsayawa “karki damu idan har ina raye tabbas aurenki da baban su _Afifa_ babu fashi, duk abin da Allah ya kaddaro wa bawa babu makawa sai ya faru, dan haka ki cigaba da addua idan har alkairi ne yana dawowa zamu sha biki” duk da cewa murmushi ne a fuskarta amma ita kad’ai ta san yanayin da take ciki, tana son mijinta tana kuma kishinsa, amma kuma tana tausayawa _Hanifa_ a yanda ta taso da iyayen da ba na gari ba matukar bata samu _Sufyan_ ba zata iya chanjawa tabi sahun iyayenta, gwara ma ayi abin tun tana cikin hankali da karfin imani.
Sallaman _Anty Aisha_ ne yasa _Hanifa_ ta share hawayenta tare da yiwa _Jidda_ sallama, bayan fitanta _Anty Aisha_ ta k’arasa falon, zama tayi a kusa da _Jidda_ ta rike hannunta “ko ni bani da zuciyar da kike da shi, kina da zuciya me kyau wanda hakan ne yasa na kara fahimtar abin da yaja k’anina gareki, da ace mata zasu samu kyakyawar zuciya irin taki da sun zauna lafiya acikin gidajen su, da sun zauna lafiya da abokan zamansu, amma duk da haka ki chanja tunani akan auren _Hanifa_ da mijinki ba dan komai ba sai dan kar amaimaita abin da yake faruwa a cikin ahalin mu”.
Kallon _Anty Aisha_ tayi sannan tace “ina son mijina _Anty_ kuma ina matukar kaunarsa, ba wai haduwar hanya mukayi da _Sufyan_ ba, kina sane da cewa tun muna secondary school muka had’u ya tafi ya barni daganan muka sake had’uwa a jami’a, shekaru bakwai mukayi tare kafin mukayi aure inda mukayi shekaru goma sha uku idan an had’a ya zama shekaru shirin, soyayyar shekaru ishirin ba wasa bane, na yarda da kaina na kuma yarda da mijina, mutum ne shi wanda ko da zai auri mata hud’u tabbas zai rike su da amana ba tare da an samu wariya ko nuna fiffiko ba, ina kishinsa _Anty_ amma kuma nafi kowa sanin cewa mijina me ra’ayin auren mace sama da d’aya ne, tun fil azal na san da hakan shiyasa ban ta6a d’aurawa kaina mugun kishin da zai hana wa mijina dani kaina kwanciyar hankali ba, idan har _Hanifa_ ko wasu matan kaddararsa ne dole ne ya auresu, shin kina ganin cewa ban yi dai-dai ba da nake kokarin k’ara d’aura zuciyar _Hanifa_ bisa dai-dai sa6anin yadda da ace halayyar iyayenta ta d’auko da kila na dad’e da barin gidan _Sufyan_? Shin baki tausaya mata ne _Anty_ shin zaki so ace irin haka ya samu wani namu na kusa kuma wani nada damar taimakonsa amma yaki? _Anty_ ko me nakeyi ina duba gaba ne, y’ay’ana da kannena su nake dubawa, (kama tu dinu tu dani) duk abin da kayi a wani me kyau ko mara kyau tabbas zai dawo maka, _Anty_ ba gwara mu cigaba da aikata me kyau muna kwa6ar zuqatanmu ba, muna hana zuqatannmu abin da zai iya kai mu ga halaka muna d’aura shi a kan turba ta gaskiya wanda muke fatan samun dace ranar gobe kiyama? _Anty_ komai na duniya me karewa ne kuma me gushewa kowa nasan rayuwa me kyau kuma kowa nasan rayuwar morewa amma gaba ake dubawa ana duba lahira shin me zata haifar idan anki bin umarnin ubangiji da koyarwan manzo, fatana shine inyi koyi daga cikin halayyar matan sahabbai da matan manzon tsira nasan ba zan iya irin nasu kokarin ba amma in  kokarin kwatantawa”.
Kallonta _Anty Aisha_ takeyi cike da sha’awa, tabbas banyi bakin cikin kasancewarki a cikin dangin mu ba, tabbas ke d’in yar halak ce kuma wacce take abin koyi ga ko wata mace a doron duniya musanman ma wanda suka zauna dake, banyi dana sanin sanya wa d’iyata _Jidda_ ba domin inason tayi koyi da kyawawan halayyarki, tabbas na yarda fin mutum shekaru ba shi bane zai sa kafi mutum sani ko ka fishi hangen nesa ko kuma ka fishi iya zama da mutane, tabbas kina da halayya me kyau da kuma kyakyawar zuciya, ba zan gaji da maimaita hakan ba ina me alfaharin samun sirika irin ki, duk da cewa ana mana kallon masu kyaun zuciya da bamu d’auki duniya a bakin komi ba duk da tarin dukiyar mu amma idan aka had’a da naki halayyar ba komai bane, y’ay’anki sun samu uwa ta gari, kuma nima kanina ya samu mace ta gari kuma dangin mu sun samu sirika ta kwarai, Allah ya cigaba da kara daura zuciyarki akan turba ta gaskiya, muma Allah ya bamu kyakyawar zuciya irin naki” _Hajja_ dake kokarin shigowa ta duba jikin _Jidda_ ta amsa da amin, sannan ta shigo “tun d’azu nakejin tattaunawar ku, Allah ya muku albarka kuma ya bayyana mana _Sufyan_ a duk inda yake” amin duk suka amsa sannan suka shiga tambayarta ya jikin ta, sun dad’e suna d’an ta6a hira kafin _Hajja_ ta koma 6angarenta _Anty Aisha_ kuma sai da sukayi sallar magriba sukaci abinci sannan ta tafi.
A 6angaren _Hanifa_ kuma bayan ta koma d’aki ta kira wata kawarta take fad’a mata yanda sukayi dasu _Mama_ da _Jidda_ shine kawar take cewa tayi dai-dai ta cigaba da dulmiyar da zuqatansu har sai tayi nasaran samun biyan bukatunta. Tana zaune akan gado ta kwashe da wani irin dariya ” _Jidda_ kenan, me kike tunani, ni zan soki ne a matsayinki na matar masoyina, da alama kin kusa kai kanki inda zakiyi dana sani, ai ni banga macen da zata zauna da _Sufyan_ kuma in sota ba, tabbas dole ne zai sa inyi koma meye dan samun _Sufyan_ dina a kusa, nasan tabbas su _Mama_ zasu dawo da shi idan na tada musu hankali ko nayi yunkurin kashe kaina, ke kuma _Jidda_ cikin sauki zaki amince da had’in auren mu, duk da cewa nasan ba zai so aure na ba, amma martabarki da kimarki a gurinsa zai sa ya amince da auren ba tare da jayayya ba, ni kuma shikenan na samu abin da nakeso cikin ruwan sanyi, _Sufyan_ nawa ne ni kad’ai babu wata mace da zata sake ra6arsa matukar ina raye domin danni akayi shi kuma dan shi akayi ne, duk me son _Sufyan_ sai nayi ajalinta, basu _Mama_ kad’ai bane suka yi nasaran kashe miki yara har dani kaina domin babu me haifar magajin _Sufyan Sudais_ sai ni _Hanifa_…
________________________
No.1 hausa novels, site all over the world with more than 5000 books uploaded, the site was found on 2014 by ////////////
All our books are free, we do not charge for uploading , we upload novels, daily and over 400+ chapters montly.

About AIS

Check Also

DEEMAH CHAPTER 15 BY ZAHRATEEY

DEEMAH CHAPTER 15 BY ZAHRATEEY Www.bankinhausanovels.com.ng  Tana zaune a kan kujera tana kallonsu cike da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *