DEEMAH CHAPTER 4 BY ZAHRATEEY

DEEMAH CHAPTER 4 BY ZAHRATEEY

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Nayi mamaki sosai da masu gidan basu dawo nan kusa ba, kwanaki sun ja watanni sun shud’e ni dai har yanzu ban saki jiki da zaman gidan ba, domin nasan bada jimawa ba komai zai zama mafarki, yan gidan ku sunfi bani tausayi sosai, yanda suka bararraje suka shantake kamar babu mutuwa, ina jiye musu ranar da zasuyi kwanan titi ko kwanan gidan _Inna Abu_ ko kuma wani gida wanda ko rabin kyaun gidan mu na da bai kai ba.

A yau muka cika wata shida a cikin gidan, ina fitowa daga kitchen naji _Baba K_ yana ta faman “to, to Allah ya kawo ku lafiya alaji” yana ajiye wayan ya tashi ya fara taka rawa yana wakar miliyan goma suna tafe, sai a lokacin ba fahimci cewa ta faru ta kare dan da alama dan k’arya ne ya kira kuma hakan na nuna cewa me gidan na hanyar dawowa, d’akin _Mama Qudi_ na shiga na sameta tana kwance a kan royal kujerun dake cikin d’akinta sai faman danna remote takeyi tana canja tasha ” su _Mama Qudi_ an samu duniya” na fad’a a cikin raina, dama duk kayan gado da kujeru gidan _Inna Abu_ aka kai aka zuba a d’akunan da babu komai, ita kuwa sai murna take ta faso gari, dan kujeru biyu ne yanzu a falonta saboda girman falon, ko wani d’aki kuma an zuba gadon matan gidan mu, dama d’akuna biyar da hud’u gadajen matan gidan mu, d’aya kuma dama kayan _inna Abu_ ke ciki, sai boys quarter kuma d’aya kayan d’akin _Baba K_ d’aya kayan d’akina, sauran kuma sayarwa akayi _Baba K_ ya zuba kud’i a aljuhu.

Ina zuwa nace mata ta had’a kayanta duka ta ajiye a guri d’aya, domin _Baba K_ ya sayi sabon gida can za’a koma, dan naji yana waya d’azu, da sauri _Mama Qudi_ ta sauka daga kan kujera ta h’au tattare tattare, haka suma sauran matan gidan mu na bisu d’aya bayan d’aya, hatta sauran k’annena hud’u da suka rage a gidan duk sai da nasa kowa ya had’a kaya cike da zumud’in zuwa sabon gida.

Karfe hud’u dai-dai aka fara shigowa da motoci cikin gidan, ta window na l’eka na ga motoci uku ne na alfarma, kuma _Khalil_ ne ya bud’e gate din, a hankali duk suka fito daga motar fuskarsu d’auke da mamaki, sai bin ko ina sukeyi da kallo, _Khalil_ dama yana bud’e musu gate ya koma can 6angarensu ya barsu da rufewa, tsaye sukayi a waje na kusan second talatin sannan suka fara takowa zuwa cikin gidan, Babban mutum ne a gaba sai wata mata a bayansa sai yara shida yan mata uku maza uku, ina jin suna knocking na koma d’akina, sai naji _Baba K_ yana saukowa tare da cewa ” maraba da bak’in karamci gani nan zuwa ashe dai har kun gane gidan” ya fad’a yana murd’a k’ofar cikin falon.

“Bismillah shigo shigo” ya fad’a yana wage hakora, _Ya Kolo_ da suke saukowa saboda jin hayaniya tace “Hajiya kece yauba gidan namu?” Kallo ne ya koma kansu, bayan an gaigaisa shine _Ya Kolo_ ke bayanin cewa ai itace ta bugeni da mota kwanaki, kuma sau biyu tana zuwa dubani amma ina barci, godiya sosai _Baba K_ ya shiga mata na d’aukan nauyin kud’in asibitin da tayi, shine take cewa ai asibitin mahaifinta ne wato me _A&S Company_ sosai yan gidan mu sukayi mamakin rashin girman kanta, ashe y’ar masu kud’i ne har hakan amma bata nuna alamar komai ba, bayan shurun da sukayi na d’an lokaci _Baba K_ ya aika aka kira mu duka wai muzo mu kwashi gaisuwa, bayan mun fito sun gaigaisa dan ni a al’adata babu gaisuwa sai sannu, sai matar take cewa “Bake bace kwanaki kuka kai mana aike a gurin biki, daga shagon _Iya Loja_?” Sai a lokacin na kalle ta, kuma na ganeta kenan ma gurin da mukaje d’in dama na mahaifinta ne, sai yanzu naji matar ta burgeni, gaskiya tayi ne a rayuwa haka nake son in ga mutum me kudi ko talaka yana abu cikin tsari da sanin yakamata. “Eh nice Hajiya, dama ke kika bugeni da mota ashe? Kiyi hakuri laifi nane saboda ina cikin damuwa ne a ranar” murmushi tayi tace min ” babu komai ni zan baki hakuri ai tunda nice nake tuk’i cikin gaggawa dan akwai inda zanje, kuma muna shirin komawa UK ne amma saboda abin da ya faru yasa muka d’an jinkirta da naga yanayin jikin naji sai muka tafi” murmushi na mayar mata ina jinjina karamci da mutunci irin nata.

Alajin ne ya katse shurun da cewa “ya akayi kuka saya gida me kyau irin haka?” Nan fa _Baba K_ ya fara bada labarin yadda akayi ya saya da kuma kud’in da yanzu yake jira a gurin alajin sai gida kuma da zasuje su gani. Kowa a gurin mamakin rashin wayon _Baba K_ yakeyi da kuma takaicin halayyarsa na son kud’in daya kai shi ya boro shi, “dama wanda yaki sharar massalaci zai yi na kasuwa ai” na fad’a a cikin raina, bayan ya gama bayyana komai sai Alaji yayi gyaran murya ya fara bayanin cewa shi bai saida gidansa ba, hasali ma gidan ya saya ne ya bari a gyara mishi kuma bayan an gama ya sa aka zuba furnitures saboda zasu dawo Nigeria baki d’aya, kuma kamfaninsa d’aya bud’e a Nigeria yana buk’atan kulawar yaransa, shiyasa suka dawo baki d’aya, duk yaran business admin suka karanta, shiyasa abin yazo mishi da sauki ya d’aura su a matsayin shugabannin 6angarori daban daban a cikin kamfanin, sannan wata d’aya ya rage bikin yaransa duka both mata da mazan. Kuma ba dan baya son gini bane yasa ya sayi gidan, kawai yana son ya zauna cikin anguwan marasa k’arfi ne domin ya rinka taimaka musu. A yanzu _Baba K_ ya dai fahimci cewa damfaransa akayi aka kwace mishi gidanshi sannan aka bashi wannan gidan da takardun bogi, kuka ya saka yana tsinewa _Atika_

Bayan ya gama kukan ya juyo ya kalleni, ganin ko kad’an babu damuwa a tare dani yasa yace “kin san dama abin da suka zo suyi kenan amma kikayi shuru kika barni na afkawa tarkonsu ko?” ko d’agowa banyi ba, yadda nake zaune ina kad’a kai babu alamun zan tanka mishi ma, sake maimaita tambayar yayi, ganin haka yasa Hajiya tace mishi meyasa yayi tunanin hakan, shine yake bata labarina da abin da yasa yayi tunanin ina sane, mamaki ne duk ya kamasu, taya za’ayi ace mutum na irin hakan, anya babu aljanu a cikin lamarina, haka kuma na koma topic of discussion, harda cewa za’a samo malami ya dubani, daganan alaji yace “Khadeemah da gaske kinsan hakan zai faru?” Kwarjinin mutumin yasa na kasa sharesa, “eh hakane” na fad’a ina basu labarin duk abin da nasani game da _Atika_ sosai sukayi mamakin halayyarta kuma suka bawa _Baba K_ laifi tare dayi mishi nasiha, wanda ni nasan ya shiga ya fita ne kawai.

Bayan an gama jajanta lamarin aka tambaye shi ina yake ganin zamu koma, shine yace gidan _Inna Abu_ Alaji yace ba damuwa zuwa gobe sai mu koma su zasu wuce gidan iyayensa dake GRA, a chan zasu kwana, dama a chan suke sauka duk sanda suka zo cikin kasar, dawowar da zasuyi ne yasa suka sayi gida suma dan su zauna a ciki, duk da cewa ya sayi wani fili ana mishi gini tare da yaransa maza dan yafi son su zauna kusa dashi idan sunyi aure, amma kila sune zasu zauna a chan shi da matarsa zasu zauna a nan d’in.

Haka kuwa akayi suka tafi suka bar yan gidan mu da jimami, duk da cewa sunji haushin abin da nayi amma kuma basu ga laifi na na son ganin _Baba K_ ya shiryu ba, haka kowa ya kwana da damuwa a ransa, washe gari Alaji ya bada mota mubi tare da direba muka kwashe komai ba mu muka koma gidan _Inna Abu_, ko ya rayuwa zata kasance a gidan, Allah masani.

Tarbar arziki ai a mutanen arziki akeyi wa, tabbas hakan take, mu ina mahaifinmu ya gaji arziki balle har ya samu tarbar arziki? Yanda dai nayi tsammani hakan ne ya faru, duk yadda takeji da _Baba K_ sai ga shi tace ba zai zauna mata a gida ba, salon wai itama ya sayar da gidanta.
+
Mun sha wahala kafin ta yarda a kan sati guda kawai zamuyi, kuma zuwa lokacin ya tabbatar ya nemi gurin zuwa dan ita kam ba zata iya da wannan halayyar ta sa ba, abin haushi wai matar data sanya ka a halin banza bata ta6a kwa6arka ba komai kayi dai-dai ne itace zata juya maka baya wai kuma sunan ta mahaifiya!
Kwanan mu uku yayyin mu maza suka samo wani gida me d’auke da d’akuna shida, d’akuna biyar a ciki da babban falo sai zaure dake da d’aki d’aya, kewaye kuwa guda biyu ne irin na wasu gidajen haya, se tsakar gida me d’an fad’i kad’an. Ranar da muka cika kwanaki shida a gidan _Inna Abu_ aka gama gyara gidan kuma suka zuba sabbin kayan a ciki,  namun kuma suka sayar suka bud’e d’an karamin shago a gaban gidan suka zuba kayan provision a _Baba K_ da sunan ya rinka saidawa.
Fatan mu dai shine Allah yasa kar ya sake jawo mana wani abin domin halin _Baba K_ abin tsoro ne kuma idan ba wani ikon Allah ba me hali fa baya fasawa, ranar asabar muka koma sabon gida d’akuna hud’u na matan gidan mu, d’aki d’aya ni da _Kisma_ sai d’akin zaure na samarin gidan, _Baba K_ kuma sai dai ayi ta juya shi kamar waina a d’akunan matan gidan.
_Inna Abu_ dai anji kunya mun barta ita da halinta da kuma d’akunan gidan da ba kowa, mata kamar mayya, me zatayi da d’aki har bakwai a cikin gidan tsaban bakin hali da son zuciya ta za6i ta barmu a layi idan da bamu samu gida ba, Allah kuma ya so muma muna da yan uwa masu rufin asiri kuma masu dakakkiyar zuciya ba masu mutuwar zuciya ba. Duk da cewa jikinta yayi sanyi da ta ga bamu wulakanta ba, amma sai ta basar tana wani jin ita wata ce tunda gidanta a yanzu yafi namu girma da kyau.
Yan uwan baban mu basuji abin da ya faru ba har sai da muka koma gidan da muke a yanzu shine _Inna Suwaiba_ ta basu labarin komai, duk da cewa sunji haushin _Baba K_ amma kuma sunji tausayinsa akan abin da mahaifiyarsu tayi mishi. Kamar abin kirki _Baba K_ ya fara rike shago, sai dai me? Mun koma gidan jiya ya cigaba da sayar mana da abinci, iya dai kud’in ka iya shagalinka. So yake sai ya ga bayan kud’in hannun su _Mama Qudi_ wanda yayyin mu suka basu na kayan gado da aka sayar, sauran abin da aka sayar kuma shine aka bud’e mishi shago da shi.
Ni dai abin be wani dame ni ba, dan kuwa an riga an saba, to wani dare ne jamage bai gani ba a gidan _Baba K_? Ai idan dai a gidan kake kuma a gidan ka tashi yaci ace ka cire komai a cikin ranka da idan dai _Baba K_ ne yanzu na lura son kud’insa zai iya halaka shi. Wata uku da tarewar mu akayi engagement din _Kisma_ sosai taji dadi dan wai ta gaji da irin rayuwar gidan, sai dai akace kana yin naka Allah yana na shi kuma na shi din shine dai-dai.
STORY CONTINUES BELOW
Tun jiya da dare _Kisma_ take zazza6i tana kuka wai zuciyarta na zafi kuma gabanta sai wani irin fad’uwa yakeyi, kuka ta dinga yi har ta godewa Allah, mu kuwa tun muna d’auka da wasa har abin ya fara bamu tsoro, duk yan gidan mu munyi zuru zuru a falo, ita kuma tana kwance a tsakiya sai rike kirji takeyi tana numfashi daker, addua _Goggo Fulera_ tayi mata a ruwa ta bata ta sha, ba laifi dai abin ya d’an lafa ta koma ajiyar zuciya a kai a kai, a haka dai muka kwana a zaune, ni duk tunani na mutanen _Baba K_ ne suke mata wani abin, sai dai ashe abin ba haka bane, abu ne wanda ya shafi rayuwarta.
Karfe bakwai na safe muka ji ana buga k’ofar gida, da sauri _Khalil_ ya fita dan ya duba, sai ga shi ya dawo fuskarsa d’auke da tashin hankali “Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun” na fad’a ina kallon _Kisma_ cike da tausaya wa, ashe dai abin da zai faru kenan shiyasa duk ta rikice mana, duk wani me rai mamaci ne, kuma kowa lokacinsa yake jira, babu wanda zai mutu dan wani yaji dadi kuma babu wanda zai rayu dan wani yaji ba dadi, _Harun_ ya rasu ya tafi ya bar ta a cikin rayuwar da takeyi mara dadi wanda take ta fatan samun sauyi idan suna tare, ashe ba zaiyi tsawon rai har burinsu ya cika ba, _Kisma_ ta rasa masoyi na hakika domin yana sonta so na Allah ba dan wani abu nata ba.
Tunda _Kisma_ taji labari ta dinga suma har sai da tayi wani dogon suma da ya tashi hankalin mu, da addua da rokon Allah aka shawo kanta, a ranar ne kuma tayi kuka a cikin hayyacinta wanda ya karyamin zuciya, rashin masoyi babu dadi, cikin ikon Allah ta fara d’an walwala tana kuma cin abinci, sau biyu ina raka ta gidan domin ta gaida mahaifiyarsa, kannen shi biyu suma sun zo kusan sau hud’u suna dubata, ko yaushe ina cikin bata baki dayi mata nasiha a ranar da  _Inna Abu_ tazo ta sameni ina mata nasiha shine take ce min ni da ban san dadin masoyi ba bazan iya fahimtar ta ba ai gwara in barta tayi abin ta ko zata samu sukuni, sosai maganar tayi min zafi amma kawai na share dan bana son in 6ata ran _Mama Qudi_.
Duk yadda rayuwa yake zuwa mana haka muke bi tare da rungumar kaddaran mu hannu bibbiyu. Ina zaune a k’ofar shagon _Baba K_ ina jiran ya bani sugar zan sha garin kwaki, ina yi ina duba agogo dan akwai wani aikin da _Iya Loja_ ta samu, saura mintina talatin lokaci ya cika, wayarsa ce ta fara ringing, kasancewarsa tecno yasa duk abin da za’a fad’a zakaji, “idan baka fito a yau ka taho Abuja ba zamu karasa tsohuwarka tare da y’ar ka _Kisma_ tunda mun kasa kashe _Khadeemah_ amma muna aiki a kanta dole ne mu sha jininta domin shine abin da zai k’ara d’aukaka kungiyarmu” ana gama magana aka kashe wayar, kallonsa nayi naga yadda yake zufa kafin inyi magana naji wani irin wari ya daki hanci na, ikon Allah ashe zawo yayi a jikinsa, sake kallonsa nayi na kuma kalli k’asa tabbas zawo yayi ba wai gizo ido na yayi min ba “kaje ka gyara jikinka bari in tsare maka shagon sai ka shirya mu tafi abujan” na fad’a ina d’auke kaina daga kansa, shi kuma mamaki ne ya rufe shi akan abin da na fada, a hankali ya janye jikinsa ya shiga gida, ni kuma na zuba k’asa a gurin na kwashe na zubar a chan wani juji dake kusa da gidan namu, sannan na dawo na fesa air freshener a shagon.
Bayan ya gyara jikinsa ya fito ya sameni a shago “me kike nufi da in shirya muje _Khadeemah_ kefa macece me zakije kiyi? Dama nemanki sukeyi balle sun samu shikenan tsuntsu daga sama gasasshe! A’a ba zai yiyu ba kiyi zamanki ni zan tafi inje in same su, dan ba zan iya bari su d’auki ran mahaifiyata ba a wannan karan, dan haka ki zauna ni kad’ai zan je!” Ajiyar zuciya nayi da naga _Baba K_ har yanzu da d’an guntun imaninsa, amma duk da haka dole ne muje tare, tunda har suka nuna nafi karfinsu sun kasayi min illa to tabbas ko da naje baza su iya komai ba “hakuri zakayi amma ya zama dole muje tare, kuma duk abin da nace kayi dole ne kayi a wannan ga6ar, kai ka sanya mu a bala’i, dan haka kai zaka fito damu daga cikin ta, amma ba da taka kwakwakwar za’a yi amfani ba a wannan ga6ar, za dai ayi amfani da gangan jikin ka da kuma muryarka, sai dai kwakwalwata ita zatayi aiki, dan haka ka saurara da kyau kaji abin da zan fad’a maka” na dad’e ina ranta6o masa bayani yana kad’a kai kamar kadangare kafin a karshe nace “idan kayi duk abin da nace zamu iya tsira da yardan Allah, idan kuma tsoro yasa ka kasa shikenan, sai ka shirya zama kai kad’ai a cikin rayuwar ka domin nasan idan sun gama da yaran ka zasu koma kan matan ka daga matan ka zuwa kannenka zuwa duk zuri’ar ka, dabara ya rage ga mai shiga rijiya.
Tafiya mukeyi a cikin mota babu me cewa d’an uwansa wani abu kowa yayi zurfi a cikin tunani, chan _Baba K_ ya ta6oni yana cewa “kina ganin haka shine dai-dai?” 6ata rai nayi nace “idan kana da wani shawara wanda yafi wannan ko wani mafita wanda ya d’ara wannan sai ka kawo, idan kuma babu dan Allah kayi shuru muyi abin da ya dace shine kawai maslaha” Me da kwallar dake kokarin zubowa daga idanuna nayi, ina karawa kaina karfin gwiwa, rai na fansa ga ahalina, ruhina zai samu salama idan na d’auki fansar mutuwar yan uwana yayata da kannena, wannan shine kawai maslaha ga duk wani masifar da suke kokarin sake tunkaro mu ta wannan fannin. Abin da nake kokarin yi shine dai-dai, zan iya kuma komai zai zama tarihi da yardan Allah.Mun isa _Abuja_ lafiya lau, duk da cewa munyi dare amma tunda dai mun isa lafiya ai sai godiya, dama munyi akan shi kad’ai zai tafi ni zan jirashi a wani gurin, idan sun amince da abin da muka shirya sai ya taho ya kaini, idan kuma aka samu ak’asi sai muyi wani dabaran daban. Saboda tsaro na saka nikab tunda sun riga da sun sanni.
+
Inda muka yanke zanje in jirashi na nufa, shi kuma suka tasa kyeyarsa a mota suka tafi, dan sun riga sun san zai zo din shiyasa suka ajiye masu jiransa. Suna isa suka had’u da mutumin daya gayyato _Baba K_ zuwa kungiyar, hararansa ya yi ba tare daya bari mutumin ya lura ba, shi kuma mutumin murmushi ya yi wa _Baba K_ sannan suka shiga d’akin chanja kaya, bayan sun saka suka 6ace zuwa d’akin taro.
Sanye kowa yake da kayan tsafi Ja da Baki dogon riga sai Bakin kyalle da suka d’aura a goshinsu sannan Farin fenti a gefe da gefen fuskar su, bayan an kai gaisuwa ga sarauniya da kuma gunkin su, suka koma gefe suka tsaya kamar body guard, yau ma sun sake samun sabbin members dan haka duk abin da ya faru rannan haka ya faru a yau, bayan an kammala aka koma kan _Baba K_ aro jarumta da natsuwa yayi ya yafa wa kansa sannan ya fara musu bayani kamar yanda na tsara mishi, bayani ya yi me tsawo dalla-dalla ta yadda zasu yarda da shi ba tare da kokwanto ba, kuma cikin ikon Allah suka amince. Suka nuna mishi jin dadin su, tare da alkawarin barin ahalin mu na har abada idan har komai ya tabbata yadda suke so. Godiya _Baba K_ ya musu tare da alkawarin kawoni a washe gari.
Bayan taro ya watse _Baba K_ ya sameni a inda mukayi da shi kuma ya min bayanin duk abin da ya faru tare da nasarar da muka kusa samu, sosai naji dadin hakan kuma nayi godiya wa Allah, sannan muka nufi wani karamin hotel na kama mana d’aki biyu d’aya nawa d’aya na shi.
Washe gari kamar yadda ya yi alkawarin zuwa tare dani, hakan ne ya faru, nima yau har dani a saka wannan shegen kayan ga shi over size, idan ba irin mu masu kuzari ba sai kiga mutum kamar wani taliya a cikin ruwa, irin su _Baba K_ kenan ni duk da irin tashin hankalin daya riske ni bayan na ganni a gaban mugayen mutane marasa imani hakan bai hanani d’arawa ba, shi _Baba K_ din ma sai ya zama kamar fefan da iska ya kwasa daga cikin takarda.
Bayan sunyi abin da suka saba suka bayarda na bayarwa suka shanye jinin cike da walwala a fuskokin su, sannan aka dawo kaina, ni abin ma abin amai duk sun koma min horror, abu kamar a film yau gashi ganin ido na ni yar _Baba K_ wani irin tsoro ne ya kama zuciyata amma na dake na fuskance su, kamar yadda _Baba K_ ya musu bayani haka nima suka sake maimaitamin abin da nina tsara abina, yi nayi kamar ban san komai ba na fara kuka ina basu hakuri tare da bawa _Baba K_ hakuri akan ya mayar dani gida ni bazan iya zama a cikin su har na wata biyu ba, kuka nayi sosai amma su duk dariyar suke ta shekawa, na _Baba K_ yafi komai bani dariya ma saboda shi ba’a son ransa yakeyi ba kuma kallon yanda sukeyi shima yakeyi kafin ya yi shiyasa abin ya mayar da shi kamar wani solo6iyo.
STORY CONTINUES BELOW
Bayan an tashi aka sallami _Baba K_ akan sai bayan watanni biyu zai dawo, ni kuma zan zauna gidan Felicia har sai komai ya daidaita sun samu yadda suke so, kafin a mayar dani gurin tsafi gabadaya, amma kuma kullun zamuje a gwada yin tsafi dani har ranar da zasu dace su samu nasara. Cike da damuwa _Baba K_ ya koma gida washe gari, ga shi sam bai yiwa yan gidan mu bayanin cewa ya san inda nake ba, shima basu san inda yake zuwa ba kwana biyu da baya kwana a gida, sai dai babban damuwar shine ina na shiga. Yana son fad’a musu abin da yake faruwa amma ya kasa saboda na nemi alfarman hakan, dan har gwara ace 6ata nayi basu san inda nake ba akan ace ina hannun azzaluman nan.
Duk hankalin yan uwa da abokan arziki a tashe yake saboda 6atar da nayi, duk da cewa da yawa mutane ba sona sukeyi ba amma sunji ba dadi da aka ce an nemeni an rasa, wasu da suka san abin da _Baba K_ ya aikata sukace kila nima sun d’aukeni sun kasheni kamar sauran yan uwana, wasu kuma sukace kila aljanu ne suka daukeni, wasu ma sukace yawon banza na tafi, ai dama in ba yawon banza ba me nakeyi har yanzu banyi aure ba tunda ni ba karatu ba balle in fake dashi kuma kanne na duk suna gidan miji, bana kula saurayi balle ace kila kawai lokaci ne beyi ba, wato sai na kula saurayi za’a gane cewa Allah bai riga ya kawo lokacin auren nawa bane. (nikam mutane suna bani mamaki matuka wallahi, sun kasa gane cewa aure da mutuwa da haihuwa lokaci ne, idan har yayi babu tsimi babu dabara sai anyi ko anaso ko baa so dole ne ya faru, kai komai na duniya na tafiya tare da kaddarar bawa ne, idan har Allah bai nufa ba ko ana ha maza ha mata sai dai ayi a gama yanda Allah ya tsara dai hakan za’a bi, akwai wani abu da muka kasa ganewa, shi kaddara a rubuce yake tare da silarsa, abu me kyau da mara kyau idan kaddaransu tazo babu me iya chanjawa sai Allah daya jarrabeka da wannan abun, me kudi dan yana cikin daula Allah ne ya jarrabe shi domin ya gwada imaninsa, idan yaci sai kaga ya dace arziki masu albarka sunata shigowa, haka zalika talaka shima Allah ne ya jarabceshi yaga yanayin imaninsa, shima idan yaci sai kaga alkairai da dama suna riskatsa, haka kuma me kudi ya zama talala ko talaka ya zama me kudi duk jarabawa ce daga gurin Allah domin ya gani shin zaka rumgumi kaddara ka gode masa ko zakayi izgili ga hakan, dan haka mu gane cewa a duk lokacin da Allah ya jarrabi bawansa to karfin imaninsa yake kokarin aunawa amma dayawa sai mu kasa tsayawa muyi tunani dai-dai sai dai mu fara wasu abubuwa karshe harda sa6on Allah da shirka).
Ni ina chan a gidan Felicia hankali na a rabe kashe biyu, d’aya ina tunanin mutanen gidan mu, d’aya kuma ina tunanin abin da zai iya faruwa nasara ko ak’asinsa, a kullun sai munje gurin taro kuma sai an d’aureni da wasu jajayen igiya, ayita wani tsubbuce tsubbuce ni dai nawa inyi ta raba idanu kamar shege a rabon gado. A haka har na cinye wata guda a garin Abuja a gurin yan tsafi kuma a gidan Felicia, wai duk da zunuban shan jini da suke kwasa harda karin wasu abubuwa, dan ita Felicia har da mata karuwai take dasu a gidanta, kullun da irin mazan dake zuwa kwasan su, nima tayi iya kokarinta gurin ganin na amince da harkar da sukeyi amma naki, abin takaici har da mata musulmai kuma matan arewa ma sun fi yawa a ciki.
Sannu sannu bata hana zuwa sai dai a dad’e ba’a je ba, a yau na cika wata biyu cif a garin _Abuja_, kuma a yau _Baba K_ zai dawo domin sun kasa nasara a kaina, duk da cewa ina cikin farin ciki mara misaltuwa, domin kuwa a yau muke sa ran kawo karshen azzalumai sai dai kuma a wani 6angaren ina cikin tashin hankali da damuwa da bakin ciki wanda ni kadai na barwa kaina sanin abin da ya faru, wanda tabbas yana cikin kaddara ta, kuma mafi munin kaddara daya afku a kaina, nayi iya bakin kokarina wajen kare kaina da kuma toshe duk wani kofa da zai cutar da rayuwata amma abin ya faskara, kuma na kar6i kaddarata hannu bibbiyu, Allah ya bani ikon cin dukkannin jarabawan da zan fuskanta a gaba.
Kamar kullun muna isa gurin taro aka fara duk wani al’adar da aka saba, _Baba K_ ma yazo, sai wani ciccin magani yake shi ala dole ya zama daya daga cikin su, domin tsarin shine idan suka samu yadda suke so dani zasu rabu da yan gidan mu, idan kuma basu samu ba, _Baba K_ zai dawo cikinsu. Kasancewar yau ba’a inda aka saba taron akayi ba, sai ya zamana akwai gurin zama, Kowa ya bada hankalinsa gurin duk abin daya sa a gaba hankali kwance, masu shan jini sunayi masu rawa da kida su ma duk sunayi, masu hira sunayi haka masu hutawa sunayi, Kamar da wasa muka fara ganin mutane suna durowa, cikin k’ank’anin lokaci suka zagaye mu, tashin hankali da ba’a sa masa rana, yanda duk aka seta bindiga daga ko wani 6angare yasa mukayi saranda. Babban abin tashin hankalin shine babu damar 6acewa dan yau ba’a yi amfani da jajayen kaya ba, kowa da kayansa yazo shiyasa ba’a tafi inda aka saba ba dan hasali daga gurin murnan zagayowar shekara na d’iyar sarauniya muke baki d’aya. Cikin kankanin lokaci akayi gaba damu baki d’aya, daga chan kuma ni da _Baba K_ aka sama mana gurin kwana, washe gari bayan na tattara duk bayanan dake hannu na, na damka musu muka musu sallama muka tafi bayan sun had’a mu da goma ta arziki muka kama hanyar _Bauchi_.
Tuna baya…
Zamu je tare, amma ni zaka barni in shiga cikin gari domin samun bayanai akan yan sanda na kwarai, a chan zan kai rahoton komai tare da rakon alfarma akan suje garin _Bauchi_ suyi bincike a kan mu, idan sun samu bayanan duk abin da na fada sai mu fara aiki dasu, idan kaje kungiyar kuma sai kace mu su, zaka kawoni amma da sharadin zasu bar rayuwarka idan suka samu biyan bukata, idan kuma basu samu ba zaka dawo cikin su.
Hakan kuwa akayi bayan yaje ya musu bayani suka yarda, ni kuma cikin sa’a na had’u da wani me napep na roke shi alfarman gayamin inda zan samu d’an sanda me gaskiya, anan ya min kwatancen wani police station a cikin suleja tare da sunan police din da zan samu, bayan naje cikin sa’a na same shi, na kuma yi mishi bayanin komai tare da abin da nake shiryawa, bayan ya saurareni yace min zai je garin namu amma sai ya fara ganawa da _Baba K_. Bayan fitowarsu _Baba K_ daga gurin taro ya kirani na mishi kwatancen inda nake, bayan yazo police din ya mishi tambayoyi inda ya bashi gamsasshiyar amsa sannan suka yanke hukuncin tafiya tare washe gari.
Bayan sunje yayi bincike kuma ya samu duk wani bayanai wanda ya tabbatar mishi da gaskiyar lamarin sai ya dawo tare da kiran wayana inda nake amsa wayarsa a sirrince kuma nake gaya mishi cewa zamu fita a duk sanda muka shirya fitan, a haka har ya gano gurin sosai ya kuma gama tsara yanda zasu kama mutanen, sannan ya aiko min da sakon camera da  recorder ta hannun driver din Felicia wanda nake amfani dashi cikin dabara a duk sanda muka fita, shine kuma abubuwan dana had’a na basu a ranar da zamu koma _Bauchi_ nida _Baba K_.

About AIS

Check Also

DEEMAH CHAPTER 15 BY ZAHRATEEY

DEEMAH CHAPTER 15 BY ZAHRATEEY Www.bankinhausanovels.com.ng  Tana zaune a kan kujera tana kallonsu cike da …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *