DAN WAYE? CHAPTER 5 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? CHAPTER 5 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Soron gidan su wanda suke fargaba kar ya fadi, an
sumunce gidan su, an gyara. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi ma kansa Mubarak ya gyara dakin sa,
ya shimfida kafet, ya kuma sa katuwar katifa, ya
sanya t.b da DBD duk na kamfanin L.G. Har dan
karamin (Generator) ya siya. An yiwa gidan su
fenti, Mah ta dawo kamar yar amarya.
Malam Bala ya yi farin ciki kwarai, domin
burin sa ya cika, ya kuma san ko yau Allah Ya
amshe shi to Mubarak zai rike Mah.
Tunanin Mubarak shi ne, tunda ya samu
aikin sa wanda zai tsaya da kafafun sa, ai Zai nemi
auren Suhaila.

Itama Suhaila tayi farin ciki kwarai, domin
Mubarak yayi mata alheri mai yawa sanmun
aikinsa.
Mah ta ce da Mubarak, in Mustapha ya zo
yayi mata magana su gaisa, domin taji kaunar sa
tun kafin ta ganshi, saboda ya nuna wa gudan.
Jininta so kwarai.
Mustapha ne zaune a madaidaicin dakin
Mubarak suna hira ya ji shigowar Mah, da yake ta
shiga makotan su dubiyar ‘yan kaciya.
Mubarak ya ce da Mustapha.
“Ka zo mu shiga ku gaisa da Mah”.
Ya yi murmushi ya ce, “Kai, ai nayi girma
da shiga gidan mutane, kace dai ina gaida ta”.
Mubarak.ya bata fuska, ya ce.
“Ba za ka iya shiga cikin kejin mu ba?”
Ya zaro ido ya ce, “Yanzu a ina nake zaune
za ka yi min mummunan zato?”.
“To tashi muje”.
Ya ce, “Um-um, ka barshi kawai”.
Ya ce, Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “Haba abokina, haka zamu yi da
kai?”
Sun shiga gidan sun gaisa a mutunce, hira
sosai suka ringa yi da Mah, kaunar sa taji tana yi.
Shi kam Mustapha gani yake bai taba ganin
mace mai kirkin Mah ba, don komai ta dauko ta
bashi. Wannan ya sanya Mustapha ko Mubarak
yana nan ko baya nan zai shiga gidan. Haka kuma
yana yi mata alheri sosai, haka shi ma Malam Bala
yana jin dadin abotar tasu.
Mustapha ya dubi Mubarak ya ce.
Ina tunanin yarinyar nan ba mutum bace,
domin ta shiga rayuwa ta, don ba na iya bacci
yadda ya kamata”.
Mubarak ya yi jim yana tunani, bai son ya
raka shi tayi musu wulakanci. Domin shi har ga
Allah yana kaunar Mustapha, ba kuma ya son ayi
masa wulakanci. Sannan yadda ya fuskanta
yarinyar tana da fushi, don ranta ya baci da marinn
da akai mata. Yana tausayin Mustapha game da
tarkon so da ya fada.
Yayi gyaran murya ya ce, “Mutumina ba
kun hadu a gurin tela ba?”
Ya ce, “Um abun ne amma ai na mika
gurin


Da yake suna kofar gidan su Mustapha ne Alpha
ya karaso suka zauna.
Abokan Mustapha duk sun tsani Mubarak,
ba don komai ba saboda Mustapha ya fifita shi
akan su. Kuma abokan sa ne tun na kuruciya, shi
kuwa haduwar hanya kurum. Shi yasa sam in sun
ganshi ba su fiya magana ba, kuma su ba sa hira da
shi mai tsayi, sai in ba ya gurin su ringa kushe shi
a gurin Mustapha. Shi ma Mubarak da ya fuskanta
sai ya rage zuwa gurin su, sai dai in shi Mustaphan
ya je.
Misalin biyar na yamma suna cikin
(goslow kamar ance ya waiga, ya ganta zaune
tana duba wata jarida. Kamar yanda ya gansu a
gurin telan nan, gabansa ne ya fadi da ya ga tana
murmushi, bai san sanda ya saki nasa ba.
Shi kam bai san an basu damar su wuce ba
sai da yaji na bayan sa yana yi masa (horn) ya
duba, ita tuni sun wuce. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana jan motar sa kai tsaye shagon telan
nan ya yi, yayi nasara babu kowa a gurin telan sai
Abba Alasan.
Sun gaisa ya ce, Na zo gurin ka, ka
taimaka ka kaini gurin yarinyar nan”
Abba Alasan ya yi dairya ya ce.
“Wai yar kurma? Cabdijan! Gaskiya zan
fada maka, na san gidan su, sai dai sam ba ta kula
maza. Ka ganni da raha ta nake yi mata wasa, tayi
maza tamin (warning) din babu ni babu ita. Amma
Zan
nuna maka gidan su, kuma zan nema maka lambarta.
ta. Ka bani taka, in na s8mu zan yi maka (text) din
(number). Bari na rufe shago muje in raka ka
gidan su”.
Ya rufe shagom ya raka shi ya nuna masa
gidan, yayi masa godiya, ya ajiye shi, ya bashi
dubu biyar ya ce.
Ga wannan”
Da kyar AbbaAlasan ya amsa.
Yana kwance cikin dakin sa kan doguwar
kujera ya ji shigowar (text), ya dauka yana
dubawa, sai ya ga Abba Alasan ne ya bashi
lambar. Ya buga ya yi masa godiya, ya ce.
“Abba, Allah Ya kaika Maleysia”.
Ya ce, “Amin, kaima Alah Ya baka yar
kurma”.
Um-unm Abba, za muyi fada da kai”.
Ya ce, “Haba Alhaji, akan me?”
Ya ce, “Baka san sunanta ba?”
Ya ce, “Sunanta Izzatu”.
Ya ce, “Don Allah a daina kiranta da ‘Yar
kurma”.
Ya ce, “To na fada maka daya sunan da
muke kiranta da shi?”
Ya ce, “Fadi naji”
Ya ce, “Sarkin kyau”
To da Allah Abba ku daina kallon ta”,Abba ya fashe da dariya, “Naji, zan kira ta
da Izzatun ta”
Ya ce, “Abba in yi maka alkhairi’mana”
Ya ce, “Ina ji”
Ya ce, “In nayi nasara za kaje Maleysia”.
Ya yi wani ihu ya ce, “Kace yan uba za a
mutu”.
Ya ce, Su waye’yan uba
“Kawu Zizu da Sani Kike. Allah na je
Maleysia karatu sake su zanyi, don na daina abota
da su”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mustapa yayi ta dariya yana mamakin
barkwanci irin na Abba alasan.
Ya ce, “Na gode Abba”.
“Ai ni ne da godiya”.
Mah ita da maigidanta suna zaune’suna hira,
ya ce.
“Halima, hankali na ya kwanta yanzu,
domin Mubarak ya samu aiki. Abinda nake soya
samu iyali ko naga jikokina”,
Ta ji dadi, ta ce, “Kamar ka shiga zuciyata,
amma mu bari muga iya gudun ruwan sa. Ka san
yaran yanzu komai nasu bisa tsari suke, don
rannan muna hira yake fada min cewar shi tsarin
sa yafi son ya mallaki gidan kansa ko da bai
mallaki abin hawa ba, ya ce ba ya sha’awar haya?”
Malam Bala ya ce “Banda abinsa ko
wadannan dakunan ai sai ya gyara”
Mah ta zaro ido, ta ce.
“Ni kam Malam bana sha’awar zama da
sirika, bare shi dan zamani”.
Ya ce, “To Allah Ya taimaka”.
Ya dube ta ya ce, “Ai naga hankalin sa ya
karkata gurin Suhaila”
Gaban Mah ya fadi, shin fitowa za tai ta
sanar da mijinta’yar uwarta ba ta bukatar wannan
aureno kuwa?
Ta ce, “Malam, mu dai ci gaba da addu’a
Allah Ya bashi mace ta gari”.
Mubarak na daukan karatu wajen wani
malami, sai da yaga Mustapha sai ya fahimci
Mustapha malami ne, domin a zuwan su sai da
malamin ya ragi daliban sa ya sa Mustapha na
basu karatu. Domin Mustapha yayi karatun sa a
Sudan, yayi (digree) na biyu a Madina, yana da
karatu Arabi da boko. Haka nan shi ne shugaban
kamfanin babansa, don komai na hannun sa.
da Tun abokan sa na jin haushin Mubarak har
Sun hakura sun zama daya.
Mahaifin sa ya riki Mubarak, ya amince
masa kwarai da gaske, domin ya auna shi sai ya
same shi mutum ne mai ma’ana.
Suhaila na matukar kaunar Mubarak, domin
mahaifiyarta ta nuna mata ba su dace da Mubarak
ba, don ita matar manya ce, Mubarak kuwa me
yake da shi? Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Mami, ina mamaki, wai samu da
rashi ba na Allah bane? Kuma wannan aikin nasa
zai rike mu”.
Ta doke bakinta, ta ce, “Zan yi maganin ki,
duk kyawun ki, duk ilimin ki ki zauna gidan
karamin mutum? Ba zai yiwu ba  a yanzu ya soma tunanin ya rabu da Suhaila, ba
don komai ba saboda yana tsoron samun matsala
Mubarak ya zo sai Momi ta hana ta
Dan Zumuntar su, kuma gaba za a samu matsala ko
ya aure ta. Saboda in uwa ba ta sOn aure toh
akwai matsala, shi kuwa Mubarka mutum ne me
tunani da hangen nesa, gashi da hankali, shi yasa
abin yake matukar damun sa.
Yana zaune falon Mutapha yayi tagumi
Mustapha ya fito yana tashin kamshi. Kayan jikin
su iri daya ne, wanda Mustapha ya siyo musu da
yaje Cairo, a yanzu suturun su iri daya ne.
Har ya fito bai sani ba, ya dungure shi ya
Ce.
“Mubarak, lafiya?”
Ya dago ya ce, “Me ka gani?”
Ya ce, “Kana da damuwa”,
Ya ce, “Ina da ita”
Ya ce, “Ina son Suhaila, to amma ba zan
same ta ba”.
Ya ce, “Saboda me? Nayi tsammanin ‘yar
uwar ka ce?”Ya ce, “Mahaifiyar ta bata so na'”.
“Haba! A tunani na yar Mah ce”.
Ya ce, “Saboda ban da canji”
Mustapha yayi tsaki ya dubi Mubarak ya ce.
“Allah Ya kyauta”.
Anan Mubarak ya sanar da shi komai yace
“Zan je gidansu yau, don bai kamata ace ka
hakura ba tunda kuna son juna, ai arziki na Allah
ne. Kada kaji haushi na, har naji bana son
mahaifiyar ta, domin bana son iyaye irin su. Ban
Son uwa mai idon cin Naira, gata mata mai kudi”.
Kai mata mu rage mugun son kudi, don
hakan ke sanya ya yanmu cikin mugun hali. Ya dafa kafadar sa, ya ce.
Kanutsu, zan je gurin Suhaila”
Izzat tayi shirin kwanciya kan (bed) dinta
taji wayarta na motsi, hakan ya nuna mata cewar
(text message) ya shigo. Ta ci gaba da gyaran
jikinta, sai a lokacin Surayya ta shigo, ta dube ta.
Kai Aunty Izzat, sai kace wata matar aure,
ke kullum sai kin dauki Ramshi ta ko ina sannan
za ki kwanta”.
Ta ce, “Ke, ni a rayuwa ta ina son kamshi
fiye da komai, don a ina so ko juyi nayi inji
Kamshi na fita a jikina”.
Surayya tayi dariya, ita kuma Izzat ta
kwanta, ta dauki wayarta. Sakon da ta gani yasa ta
zuwa tsakiyar gado ta sake karantawa.
Izzat!Ita zuciya tana son wanda yake kyautata
mata, haka zuciya na kin wanda yake munana
mata. Sai dai zan so ace kin kasance mai yafiya
mai afuwa akan mutumin da kike ganin ya zalunce
ki Kin san Allah Yana son bayin sa masu yafiya
Izzat tayi jigum tana mamakin wannan
sako, tayi kamar ta goge sai ta barshi.
Da safe da ta idar da sallah tana cikin shafa
addu’a wayarta ta motsa, sai da ta shafa addu’a ta
dauko.
Salam Www.bankinhausanovels.com.ng
Hasken idaniyata, rayuwa ta. Kin hana
zuciya ta sakat, bana iya bacci, ba na iya cin
abinci, komai na wa ya tsaya, amincewar ki nake
nema. Da fatan kin tashi lafiya, kin sanya ni cikin
addu’a..
Izzat ta jima tana karanta sakon, waye
wannan?A ina ya santa? Wa ya bashi lambarta?
Ta goge sabon sakon har da na jiyan ma
tana fadin.
“Ba zan yi soyayya ba, nayi banji dadinta
ba”

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 11 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 11 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI           …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *