DAN WAYE? CHAPTER 4 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? CHAPTER 4 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsayar 
Ya mike ya fita,.a lokacin suka hadu da
Mubarak ya shigo.
Sun gaisa, ya ce.  Kamar na sanka?” Ya ce, “Ba dai ka manta ni ba, ranar da ka mari kurmar nanTake Mustapha ya kama hannun sa suka fice, ya ce.”In tambaye ka mana”. Ya ce, “Allah Yasa na sani”Ya ce, “Ko ka san sunanta?”
Ya kada kai, “A’a”  “To gidan su fa?”
Ya ce, “Ban sani ba, in da ka ganta nima
haka na ganta”.

Abokina, raina yana kuna, zuciya ta tana
Kunci, rayuwata ta baci duk dalilin marinta, Zan
so in bata hakuri, na damu”.
Mubarak ya ce, “Ai shi dan Adam girma
ne dashi, musamman aka ce mace. Ai in fada
maka mace aba ce mai matukar daraja”.
Haka ne, na kuma gano hakan a rayuwa
ta. Tabbas hakan abu ne mai muhimmanci”
Sun dade suna hira har suka yi musayar
lambar waya. Gaba daya tare suka zauna, ya
nunawa manyan abokansa Mubarak suka gaisa,
lokacin da za su tafi Mustapha ya ce.
Ka zo mu rage maka hanya”.
Ya ce, “A’a, ai tare muke da kanwata”.
Mah ce ta ciro wayar Mubarak dake caji,
ta ce.
Www.bankinhausanovels.com.ng
,”Ka ajiye waya ta dame ni da kara”.
Ya karba yana duba (missed calls) din da
ya gani, ya ce. Ta ce. “Na so in dauka sai kuma na rasa
inda zan danna”
Ya sa dariya ya ce, “Mah, kin kusa in sai
miki taki. Allah Yasa in samu aiki, duk sai na
mayar dake ‘yar gayu”.
“Ka dai ji da shi”
Dai dai lokacin wayar tashi ta soma kara, ya
daga, ya ce. Ya aka yi abokina?”
Ya ce, “Nayi ta kira, da alama ba ka kusa”
Ya ce, Yanzu na shigo Mah dina take
fada min” Ya ce, “To ka gai da ita, kawai na bugo
mu gaisa, in kuma tambaye ka labari. Don Allah
in har ka san inda yarinyar nan take ka taimaka
min”.
Ya ce, Na fada maka ban san inda take
ba, amma zan cigita”
Suka yi sallama.


Alpha da Mustapha suna zaune kofar
gidan su Alpha suna hira, kanwar Alpha ta fito,
ta ce yaje inji Hajiya. Ya tashi ya shiga ciki, bai
dade ba ya fito ya ce. bros
“Zan je karbowa Hajiya dinki, zan je in
dawo, ka jira ni”.
Ya ce, “A’a, muje in raka ka”
Sun isa karbar dinkin Alpha ya fice, yayin
da Mustapha yanaz zaune cikin motar. Kamar
ance ya kalli kofar shagon, ita ce suka fito.
Gaban sa ya fadi, don zahiri ita ce
Tsoro da fargaba suka dirar masa don ba
dai ta soma yi masa gizo ba.Bakin sa dauke da
addu’a yana kuma rokon Alah Ya sauwake masa
wannan lalurar, don shi a gurinsa soyayya lalura
ce. Ya fito ya biyo su, su kuma suna son tsallaka
titi, yana bayan su. Www.bankinhausanovels.com.ng
Surayya ta gane shi, don ta kuma tabbatar
shi ne wanda yan mata suka ringa nuna shi a
bikin Rukayya Ibrahim Umar, mutum mai aji sai
bala’in girman kai.
Ta masa kallo shekeke dai dai lokacin ne
Izzatu ta kula da shi, bakinta ya furta.
“Hasbunallah!”.
Suka tsallaka suka bude motar su
suka shiga, kafin ya farga sun yi mata (key) sun
yi tafiyar su.
Ya dafe kai yana fadin.
“Ya salam!”.
Alpha ya kwalla masa kira, ya tsallako ya
Ce.
“Alpha na ganta”Ya ce, “Wa?”
Yarinyar nan”.A ina? Ya ce, “Ita ce wacce.suka fito”.
Ya ce, “Kai muje wajen telan”.
Sun shigo shagon telan sun gaisa, sannan
suka gabatar da bukatar su, domin suna son su
san inda yan matan suke, musamman Izzatu.
Don haka ya dube su ya ce
saboda me zanyi muku bayani akan
su? Kurma ce, sunanta Izzatu, amma ban san
gidansu ba. Ni ne telan su”.
“Ka taimake mu ka bamu lambar wayar
ta”.
“Kai! Gaskiya in ta san ni na baka baza su
ji dadi ba”Suka ce, “Haba, ka taimaka”.
Kawu  ya ce, “Kaga in na baku ban
kyauta ba”Wani abokin telan mai abin dariya Abba
Alasan, mutum ne mai barkwanci, ga surutu, yaCe.
“Alhaji na san gidan su, ni kawata ce, har
cikin gidan su nake zuwa, zan iya yi maka
kamfen, amma fa biya na zaka yi, don ka san ba
a aikin banza a Kano”.
Kawu Zizu ya harare shi, yayin da Sani
Kike ya ce.
“Ka gani abinda za a yi kawai ku kaishi
Maleysia yayi karatu”.
Gaba daya suka fashe da dariya har
Mustapha ya kule, saboda shi ba ya son rainin
hankali. Su kuma gaba dayan su in za kayi
zaman minti biyar da su to sai kayi tanadin
maganin ciwon ciki.
Shi Alpha ya san halin su, ya ce.
“Abba Alasan, in zaka yi mana kamfen
zaka je Maleysia karatu”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi kam Kawu Zizu ya hana lambar waya
don ya ce bashi da ita, haka suka hakura suka
fita.
Abba Alasan ya ce, “Kaji min mutum,
nima da za ta soni sa kai zanyi”.
Ya basu dariya, ya ce, “Yar kurma fa ta
hadu, sai dai gayen akwai girman kai, amma sun
dace, don har kama naga suna yi”.
Kawu Zizu yana jinsu bai tanka ba, in da
sabo ya saba da caftar su.
Suna tafe a mota ya ce, “Alpha, yarinyar
nan ba zata so ni ba, na rasa ya zan fitar da ita a
raina”.
Ya shafi sumar sa tare da cije labban sa,
ya girgiza kansa ya ce.
“Mata yan rainin hankali ne, Allah Ya
sani na so kawai iyaye na suyi min aure, ba wai
inga mace ince ina sonta ba, domin mata yan
rainin hankali ne, in sun gano kana son su ka
shiga uku. Ka ga wani mugun kallo da dayar tayi
min? Daga ganinta yar tsurku ce”.
Alpha ya ce, “Babu komai, ni zan san
yadda za a yi mu samu (address) dinta”.
Yanda Mustapha ya gyada kai abin
tausayi.
Yana sauke Alpha gida yayi, cikin falon
Mami ya shiga ya kwanta. Ta fito ta ganshi, ta
ringa kallon sa, ta ce.Lafiya?”
Yayi kasake, “Mami na ganta yau”.
Ta ce, “Wa?”
yace, “Ita din da na fada miki”.
Ta ce, “Kayi mata magana
Ya girgiza kai, sai taji tausayin sa saboda
gaba daya ya zama kalar tausayi, ya ce.
Mami, ba zata so ni ba”.
Momin ta zauna gefen sa, ta ce.
“Kayi hakuri ka nutsu, saboda bana son ka
damu kanka. Ka san Hausa sunce matar mutum
kabarin sa, ka daure ka ringa cin abinci”.
“Mami damuwa ta biyu ce, na rasa me
yasa kike min wasu abubuwa a rayuwa. Nakan
tsinci kaina da shiga kunci, Mami ki fada min
duk abinda baki so. Yanzu fa ba da bane Mami,
ma’ana na gima, bana son in sanya ki a
damuwa”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya kura mata ido, ta dube shi ta ce.
“Boy, bana son zafin rai, yanzu ba gashi
ka shiga damuwa ba. Da ba ka nuna zafin ranka
ba hakan ba zata faru ba. Ina son ka bi duniya a
sannuYa ce, “Mami na fahimce ki, zan kiyaye.
Amma ina bukatar addu’ar ki, domin bata da
hijabi”.
Fibe star, wani gidan abinci ne dake titin
Gwarzo, nan ne majalisar su Mustapha inda anan
suke zaman hira. Bayan sallar isha suke zama
suyi hirar su, daga nan kowa ya kama gaban sa.
Mustapha ya taho zuwa majalisa sai ya ga
Mubarak ya yi (parking), ya ce. iro
“Abokina, ina zuwa
Ya ce, “Gida za ni”
“A’a, ya na ganka anan ka ce kuma gida za
ka?”
Ya ce, “Um”.
ya ce,”To zo mu tafi, amma bari inje inga
wani abokina, saboda na san yana jira na”.
“Ka je abinka, bana son in bata maka
lokaci”.
Mustapha ya dan hade fuska ya ce.
“Mubarak, wai me yasa kake irin haka? Ka
san Allah Shi Yake hada mutane, in ba ka amince
min ba shi kenan, ka gaida Mah”.
Mubarak ya bude murfin motar ya shiga,
suna ta hira har suka shiga wajen, a cike yake da
matasa irin gayun nan, motoci kuwa a gurin
wannan na wane waccan. Ya nemi guri ya yi
parkin).Sun fito ya samu kujera ya zauna, shi kuma
suna magana da wanda zai gani.
“Mubarak Bala”. Ya juyo ya ce, “A’a Saminu Sabi’u, rai kane
ga rai?”
Suka tafa, sun jima suna hira sannan
Mustapha ya dawo. Nan fa suka zauna suna hira,
sai sha daya na dare ya kai shi gida.
Washe gari da Mustapha ya je majalisa suka
tambaye shi ina abokin sa’?
Ya ce “Yana gidan su”.
Suka ce, “Ka je ka taho mana da shi, ya iya
cafta”.
Ai kuwa suka dauko shi, tun daga rannan ya
Zama suna hira a majalisar tasu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Rayuwa kenan, Mubarak da Mustapha sun
zama abokai, ta inda Mustapha ya gano Mubarka
ba shi da aiki. Shi ya karbi takardun sa ya nema
masa aiki kamfanin mahaifin sa, ya kuma samu
babban matsayi. Mubarak ya samu aiki, ya kuma shiga
kamfanin da farin jini, domin yana da kirki da son
al ‘umma, ya kuma iya zama da kowa lafiya.
Sannan shi bai dauki kansa matsayin kowa ba face
dan talaka, me neman rufin asiri.
Mah tafi kowa farin cikin samun aikin
Mubarak, domin sun samu rufin asiri. Ya gyara
musu dakunan su da suke zubahaka ya gyara musu
Soron gidan su wanda suke fargaba kar ya fadi, an
sumunce gidan su, an gyara. Www.bankinhausanovels.com.ng
Shi ma kansa Mubarak ya gyara dakin sa,
ya shimfida kafet, ya kuma sa katuwar katifa, ya
sanya t.b da DBD duk na kamfanin L.G. Har dan
karamin (Generator) ya siya. An yiwa gidan su
fenti, Mah ta dawo kamar yar amarya.
Malam Bala ya yi farin ciki kwarai, domin
burin sa ya cika, ya kuma san ko yau Allah Ya
amshe shi to Mubarak zai rike Mah.
Tunanin Mubarak shi ne, tunda ya samu
aikin sa wanda zai tsaya da kafafun sa, ai Zai nemi
auren Suhaila.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 11 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 11 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI           …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *