DAN WAYE? CHAPTER 3 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? CHAPTER 3 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Hadiza ta fi mu’amala da
kawaye fiye da kanwar tata, sai dai duk da haka
ba ta bawa yayan ta fuskar da za su raina
kanwarta ta ba, amma sai ta shekara ba ta je
gidan yar uwar ta ta ba. Ita kuwa Halima tana yawan zuwa, da taga Www.bankinhausanovels.com.ng
kamar yar uwar tata na nuna gajiyawar ta, sai
itama ta janye. Don a yanzu danta Abbas bai
dade da aure ba, sam ba ta san komai akai ba, sai
satin bikin ta aiko mata, ita kuma ranar bikin duk
da bata ji dadi ba haka ta daure ta je, kuma danta
da mijinta sun halarci daurin auren.
Sam ba ta yi mata shisshigi ba wajen
bikin, saboda komai na ‘yan gayu ne, kawayenta

ne akai, itama ba ta ce cikanta ba. Bayan la’asar
ta bata abinda Allah Ya hore mata ta tafi gida.
Mah tana jin tsoron lamarin Suhaila da
Mubarak, don ta san zai yi wuya yar uwarta ta
yarda da lamarin. Shi yasa sam bata kaunar taji
Mubarak ya ce za su gidan.
Indan har suhailah tqje (school) in bata da
lacca sai ta taho gidan Mah, shi yasa Mah ta
zuba ido don taga ya lamarin zai faru.
Suhaila na zaune ita da mahaifiyar ta a
falo, ta ce.Umma, nayi miki maganar samawa
Mubarak aiki naji kinyi shiru, don Allah ki sa
Baba ya sama masa aiki”
Ta ce, “Wai ke me ya dame ki da Mubarak
ne? Naga rawar kan ki akansa tayi yawa, bana
SOn shisshigi”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta dubi Umman nata ta ce.
“Rawar kafa? Kai Umma, Mubarak fa nace?
Ta ce, “Ko Bala kika ce ko Halima”
Tayi (shock) ta dubi Umman nata kamar
zata yi magana, sai kuma ta fasa. Wayar ta dake
vashe tana kara ta dauka, tana gama amsawa sai
ta kwanta tana yin 2go ita da Mubarak dinta.


*****
Kamar yadda ya saba ganinta cikin
mafarkin sa a yau ma ita ce, ya farka ya tsaya
yana tunani, gabansa ya ringa faduwa, abinda
yake ji a zuciyar sa yana ci gaba da jinsa.
Ya ce, “Na shiga uku, maganar Mama
gaskiya ce ina sonta”.
Ya ce, “Waiyo! Na fada tarkon so”.
Mustapha ya dade yana fadar shi bai ga
amfanin soyayya ba tunda aka yaudari Faisal
wani abokin sa.
Karamin hauka Faisal yayi akan Asma’u
shi ya sanya yaji ya tsani mata, don ya ce sam
basu da tausayi matukar sun gano kana son su
shi ya sanya sam bai rabar mace bare ace
maganar soyayya ta shiga tsakanin su.
Wannan yanayi da ya tsinci kansa yanayi
ne da bai dace da rayuwar sa ba, bai son rainin
hankali, su ko mata lamarin su akwai raini.
Ya dafe kansa yana fadin.
“Allah na tuba, kada ka jarrabe ni da son
mace, macen ma musaka”
Kail Anya za ta so shi? Haduwar su ta
farko ya wanke mata fuska da mari, anya kuwa
za ta amshi soyayyar sa? Ina ma zaiz ganta? Ko
dai ba mutum bace? Www.bankinhausanovels.com.ng
Alpha ya shigo da sallama yana fadin.
“Musty, baccin me kake ne? Ka manta za
muje bikin kanwar Anwar?”
Yaja tsaki ya ce, “Ku je abinku, ni fa bana
son sabga da mata”
In da sabo sun saba, su gasu yan son
warwasawa, shi ne gidan su bashi da waigi, duk
motar da ya ga dama yake hawa, amma sam shi
babu casu cikin ransa. Don a bayan idanun sa
cewa suke bai waye ba. Amma su Alpha sun san
in daukan wanka ne duk (group) dinsu ya fisu
Iya sa kaya, illar sa daya mace ba ta gabansa.
Anya kuwa yana da lafiya?”
Ita ce maganar su a bayan idonsa, don ko
irin dan biye-biyen nan da samari suke ma mata
shi Allah Bai dora masa ba. Kyale shi da zafin
rai, wannan kuwa halitta ce.
Ya dubi Alpha, “Da kai muke tare na mari
wata yarinya?”
Ya girgiza kai, “Da wanwar ne. Ya dai
Musty?
Zo ka zauna”. Ya ce da Alpha.
Bayan ya zauna ya ce. l
“Anya ba mugun bakin ku ya fada min
ba?
Ya ce, “Kamar ya?
‘A hankali ya furta mai rada, ya ce.
“Sonta ya shiga rayuwa ta, ina zan ganta?
Alpha ya ware ido yana duban abokin
nasa yana mamaki, ya ce.
Ikon Allah, dama a rayuwar ka za ka So
mace?Ya ce, “Waye ni da ba zan zauna da mace
ba? Waye ni da ba zan so mace ba? Ni rainin
hankali ne kawai bana so, domin ba zan dauka
ba. Ina zan ganta Alpha? Ka gaya min”  Www.bankinhausanovels.com.ng
Alpha yayi sauri ya ce, “A ina ku ka
ganta?Ya dafe kai kamar mai nazari, ya furta.
Titin Yakasai, wajen get din makarantar
Shekara, Kai! Ba a nan ba, ina ga kamar titin nan
da ya shiga sabuwar unguwar Yakasai. Kai
Inaga a nan muka hadu”,
Ya ce,”Za mu ringa yawan shiga unguwar
ko Allah zai sanya mu ahdu. Kaga, kayi wanka
mu fita”.To”
Alpha ya fice, shi kuma ya shiga wanka,
ya fito ya soma shirya jikinsa.
Kai Mustapha in yana gayu tamkar yar
budurwa, yanayin gyaran gashin sa da inda ya
kwanta lif-lif abin sha’awan ne. Haka nan
kyakkyawar fuskar sa gewayaiya, idan yana
magana abin sha’awa, domin wushiryar sa kawai
abar kallo ce, ga shiryayyun hakora.
Mustapha ya kammala ya fito sanye cikin
lallausar shadda wacce ta ci aikin sama, anyi
mata dinkin boda, hannun sa rike da hula. Ya
shigam ciki mahaifiyar sa na zaune daya daga
cikin luntsumarmmun kujeru, ya ce.
Mamy sannu da gida”.
Ta dauke kai tamkar bata ji ba, gaban sa
ya ba da ras! Kada a koma ‘yar gidan jiya.
Mamie ta daga masa hannu, ya juya dai
dai lokacin da ya ji muryar mahaifin sa yana
magana, yace
“Malam Mustapha ina Zawa jikin ka a
sanyaye?”
Ya cc, “Za mu fita ni da abokaina ne
Mahaifn nasa ya ce.
Ya ya dai?”
Ya ce, “Ba komai Ya juya ya fice zuciyar sa kunshe da
takaicin abinda mahaifiyar sa ke yi masa.
Alh. Majid ya dubi matar sa ya ce.
Ni kam kina bani takaici, kina sa min
damuwa a lokuta da dama. Saboda Allah me Boy
yayi miki? Za mu bata, za ki dawo da halin ko?
Ka haifi da a cilkinka ka tsane shi? Ke wacce irin
mutum ne? Yaron mu yaro ne na gari, da bai
gyagije ba ai da bai zama haka ba”.
“Ka, manta wuyar da na sha kafin Boy ya
ringa mu’amala da ad’umma ya ajiye girman kai?
Duk wannan nayi nasarar raba shi da su, to
amma wannan Zafin ran nasa yana matukar
damu na..”
Ya datse ta cikin tsananin fushi, ya ce.
Wai ana sakewa mutum hali ne bare ki
sake masa’? Ni dai ina fada miki ita rayuwa ba a
mata haka. Tun yana yaro ba ki damu da shi
ba har girma ma, kada ki fa dasa kiyayyar ki
cikin zuciyar sa, ance miki haka ake kunyar dan
farin? Ke naki yayi yawa, shi daya fa muka
mallaka”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, To amma yan uwa sun haifamin.
Ko sun haifa miki ba kamar wanda kika
haifa da kanki ba”
Nan dai yai tayi mata ansiha akan rashin
kulawar ta akan dan nata.
Ki kan bani mamaki, domin duniya a
aynz kowa nasa yake s0, amma ke banda ke.
Allah kina kona min rai, za mu gauraya dake
Ta zumbura baki, “Naji”. Ta mike tayi
ciki.Mubarak shi da Suhaila sun isa gidan Dan
Hausa, inda ake kamun kawar Suhaila, ko ince
aminiyar ta tun suna yara, kuma ga gida ga gida
Suke. Amarya Surayya Ibrahim Umar ta hango
shigowar su, ta sha kunu ta tabo kawarta
Nusaiba Tijjani, ta ce.
Nusy, kinga sai yanzu Suhaila ta iso”.
Nusaiba ta sa baki ta ce.
“Allah ni wannan kawar taki haushi take
bani, duk inda za ka ganta ita da wannan direban
nata, ko ince dan rike mata jaka”.
Rukayya ta harari Nusy, ta ce.
“Za ki soma ko?
Ta ce, Ban son inga mace da namiji suma
manne da juna matukar ba ma’aurata ba”.
Ta ce, “Kina da gaskiya, sai dai na yarda
da su, ba yanda kike zaton su ba.
Nusy ta ce, “Allah Ya kyauta”.
Dai dai lokacin Suhaila ta iso wajen.
Ran amarya ya dade, da fatan ba a yi
fushi dani ba”.
Ta juyo gurin Nusaiba ta ce, “Ayi min
afuwa, naga kin sha kunu”.
Ta dan kada kafada ta ce, “Ai in kina tare
da wancan baza ki zo akan lokaci ba”
Ta juya ta ce, “Zo muje in sama maka
waje”Ta kama hannun sa suka wuce inda ta je ta
nuna masa kujera, da yake su ne manyan
kawaye, ta tafi.
Ya zauna yana kallon mata iri-iri, ya
hango yar kurma. Yarinyar iya haduwa ta hadu,
ga ta da fara’a,
Yana kallo tana ta gaisawa da jama’a, ya
mike don ya je su gaisa. Kaifn ya karasa ya ji
tana fadin.
“Surayya, kamu muka zo ba wai kula
samari ba. Wai shin me yasa yanzu duk aka bata
mana addinin mu, aka gurbata mana shi? Zuwa
kamu ace sai da maza? Ni kam ban da Rukayya
na da girma a gurina da babu dalilin da zai sa na
ZO wajen nan”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Jin haka yasa shi ya juya, don shi ma ya
hangi gaskiya a al’amarin ta.
Anyi kamu an tashi  kuma anyi
(dinner) wacce anan kuma Mubarak da
Mustapha suka hadu. Ko da yake su Mustapha
abokan ango ne, yayin da Mubarak ya rako
Suhaila, wacce tana daga cikin manyan kawaye.
Mustapha yana zaune Cikin abokan sa,
amma su gaba daya hankalin su na kan mata
kowacce sharhi suke akanta.
A hankali ya ji gun ya gundure shi, ya
mike. Amma a gaskiya kyau da iya (dressing),
da yadda ya dauki wanka ya dauki magana a
gurin, don yan mata sai fareti suke a (table) din
da yake.
Ya mike ya fita,.a lokacin suka hadu da
Mubarak ya shigo.
Sun gaisa, ya ce.  Kamar na sanka?” Ya ce, “Ba dai ka manta ni ba, ranar da ka mari kurmar nanTake Mustapha ya kama hannun sa suka fice, ya ce.”In tambaye ka mana”. Ya ce, “Allah Yasa na sani”Ya ce, “Ko ka san sunanta?”
Ya kada kai, “A’a”  “To gidan su fa?”
Ya ce, “Ban sani ba, in da ka ganta nima
haka na ganta”.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 11 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

DAN WAYE? BOOK 2 CHAPTER 11 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI           …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *