BABBAR YARINYA CHAPTER 5 Oum Aphnan

BABBAR YARINYA CHAPTER 5 Oum Aphnan

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Fuuu ta wuce ɗakinta ,taje kan hamshaƙin gadonta ta zauna tana dafe dakai tana faman girgiza ,kamar ƴar ƙwaya a dole an mata ba daidai ba,hajiya zainab da dunfarowarta kenan taga sanda ta kwalle bawan Allah da mari yasa Zuciyarta tsayawa da harbawa na wucin gadi,hakan ya baiwa Islam zarran wucewa safely .

Cikin Murya kamar za tayi kuka ta ƙarasa gaban Barrister Magan

“My Deepiest Apology onbehave of my daughter don Allah kayi haƙury yarinya ce,kai mata uzuri Afwan ,Mu shiga daga ciki ko?”

Ɗagowa yayi da idanuwarsa da suka rine sukayi jajir ya kalleta,sannan yayi wani irin dariyar yaƙe da yafi kuka ciwo

“Momy Islam bata sona,basai na shigo ba,Sai Anjima”

Da sauri ya juya ba tareda ya kalli kowa ba ,ya nufi motarsa 

“Suwaiba”

Ta ƙwallawa Mai aikinsu kira cikin tsananin fusata 

Yarinyar kamar zata kifa ta zo gabanta cikin uniform ɗinta

“Na’am Hajiya gani!”

“Maza Jeki ,ki kiramun Islam,ko me takeyi tazo ina neman ta”

Dasauri ta juya ,zuwa ɗakin ,saidai tana cuna kanta tun kafin tayi magana ta jefeta da wani irin tsawa da ya sakata firgita

“Outttttttt!”

Da gudu suwaiba ta fita,itakuma Islam ta dafe maƙoshi tanajin yanda ke mata suya saboda Shouting ɗin da tayi.

Hajiya zainab da ta kira  Akram a waya ,jan baya tayi akan kujera ta zauna a falon tana jijjiga ƙafa ɗaya duniyar nan kaf ta rasa meke mata daɗi ,tabbas Abun Islam ya fara wuce limit ɗin da za’ayi shiru ,this is not the first time da tayi wannan Abun,Alhaji buba kam Hankalinsa kwance ya ajiye katuwa pot belly ɗinshi sai gudanar da Sha’anin Business ɗinsa da jama’a yike ,sam kamar ma abunda Islam tayi bai damesa ba

Hajiya zainab zuru tayi masa da ido tana kallonsa ,cikin ɓacin rai,Yina faman waya Abunsa yina ɓaɓɓaka dariya 

Shiru tayi dafe da tagumi har ya gama kafin ta ɗago ta kallesa

“Sweet Bakaji Abunda nace maka Islam tayi bane wai yau a cikin gidan nan?” 

“Naji mana ,To me kikeso Inyi bacin ke kinba yaro haƙuri ,kuma nima nace maki anjima zamuyi waya sa me girma gomna,Don Allah kar mu daƙile rayuwar ƴannan,tana iya yuwuwa rawar kai ya kawo mata irin na ƴaƴan masu ƙasa,itakuma ta nuna masa izzarta a sarari ,tunda ai inda itaɗin ba ɗiyar Alhaji Buba bane,Shima cewa zaiyi yafi ƙarfinta ,to shi Barristern mangan shiya jawa kansa daya ɗakko dala ba gamo”

Sakin hanci da baki tayi tana kallonsa ,har ya kai aya 

“Oh really? Alhaji yarinyar nan a laifin da tayi har kana da bakin tare mata ,bama mu taru muyi punishing ɗinta ba?”

“Ah haba dai horo? Uhmuhmahah sam bashi yuwuwa inda Ace ƴarnan ƴan mitsiyata ne kare bazai tako hanyarta ba,kaf ɗinsu ribibinta suke saboda ita kaɗai Allah yaban ga dukiya na tara na sakar mata tai wadaƙarta dashi”

Caɓe baki kurum tayi ,ta juya kai daidai nan Akram ya shigo. 

Cikin Nutsuwarsa ya ɗuƙa ƙasan kafet ya suka gaisa ,kafin Alhaji buba ya umurcesa da ya miƙe ya zauna a kan Kujeran.

Cikin Narkakiyyar murya wanda daga gani kasan tana cikin tsananin damuwa ta fara koro masa labarin abunda ya faru tsakanin Islam da Manga

Wani gauran numfashi yaja ya aje ,adaidai sanda yaji ta kai ƙarshen maganarta 

“To ynx momy me kike ganin mafita ma wannan Alamarin don ni zahirin magana ,kaina ya kulle?”

Waigawa tayi ta kalli Alhaji buba da yayi kasaƙe ba tareda yace komai ba

“Alhaji kayi shiru meye mafita?”

“Karku damu dani hajiya zainab ,duk yanda kuka yanke ai Islam ikon ku ce” 

Jan dogon Numfashi tayi “Shikenan ,to ni Abunda na yanke a raina shine ,a aurar da Islam shine kaɗai mafita,kuma aure cikin gajeran lokaci in ma so samu ne a yau ɗin nan inyaso tarewa sai bayan ta dawo daga UK”

Tsit ɗakin yayi ba wanda yace ƙala ,har sai da ta gaji tace” ya naji duk kunyi shiru ne ?” 

 “Hajiya zainab maganar ne yayi mun banbaraƙwai ,tunda nasan dai kinsan Islam batada wani manemi tsayayye duk korasu take”

Kai tsaye tai magana ba tareda ta kalli kowa ba “Oh baga Akram ba ,sai ai masu auren zumunta ,inta kama a yau yau ɗin nan !”

Da sauri akram ya miƙe tsaye bakinsa na motsi ya kasa magana,itama kuwa daidai ta sako ƙafa zatashigo taji furcin Hajiya zainab na ƙarshe

A gigice ta ƙarasa shigowa

“Auren zumunci? Nine zaaiwa auren dole sai kace wata Gantalalliya da tayi abun kunya,Abba dan ɗina kanajin matarka ? Hmm wait bari inji me zakace ,zaka biye mata ne ku aurar sani ga wannan abar (Ta yarfe hannunta tana nuna Akram from head to toe cikin mugun harara) ko kuma zaka biyewa raayin matarka ne,wacce na lura sam ta tsaneni baƙin ciki take mun”

Ɗau! Ya yanke ta da mari ,dafe wajen tayi da sauri cikin mamaki tace “Ka mare ni,ehem mugu Azzalumi ? Wallahi sai kasan ka mareni kuwa  ….Amaka!?” ta ɗaga murya tana kiran guard ɗinta 

“In baki iya bakinki ba next time ni da kaina zan ɗauki dorina insa ya zane mun ke,shashasha kawai ,samu waje ZAUNA!! ….Akram ɗauki waya ka kiramun soba kabani in gayyace su ɗaurin Auran Islamiyya gobe da safe Inshaallah”

About AIS

Check Also

BABBAR YARINYA CHAPTER 6 Oum Aphnan

BABBAR YARINYA CHAPTER 6 Oum Aphnan Www.bankinhausanovels.com.ng  Razana yayi da yanke Hukunci Alhaji Buba ,take …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *