ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 3 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

dama tuni na yi tunanin samun wannan tarbar farin
Cikin daga gare ki.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan suka juya hirar ta su zuwa wani zancen
daban. Sun jima suna hira daga nan suka yi
sallama.
Ko ba komai Haana ta dan samu nutsuwar
zuciyarta kadan da haka har ta samu barci ya yi
awan gaba da ita
Alhaji Jafar ne ya yi sallama ya shigo dakin
Haj. ASIya wato Mommy inda ya tarar da ita tana
shirin barci. Bayan ta amsa sallamar cikin
murmushi ta ce, “Daddy ai na yi tunanin a can ma

za ka kwana dubi agogo ka gani, gaskiya yau
hira ta yi dadi wato hirar yaushe gamo aka yi
kenan.
Shi ma murmushin ya yi ya ce, Wane ni na
kwana a can ina tare da Su amma zuciyata tana
gurin ki. Ya fada yana kokarin zama a kan gadon.
Kenan na canja tunanina.
Da hakan kuwa ya fi yi miki sauki.
Gaba dayansu suka saka tariya, tun lokacin da
komai ya daidaitu Alh. Jafar bai da wani buri illa
ya ga ya farantawa mai dakinsa domin idan ba ita
ba babu mai iya zama da shi, tun faruwar
kaddararsu Hameed da Aziza take ta dandanar
bakin cikinsa wanda hakan ya janyo rashin jituwa
tsakaninsa da dansa Muhammad saboda ganin
yadda take cikin damuwa a kodayaushe ya ji bai
son mahaifinsa bai son yi masa biyayya don ganin
baya bawa mahaifiyarsu wani farin ciki.
Haka suke ta yin rayuwa cikin rashin sabo da
jituwa tsakanin uba da da, uba zafi da zafi, ba don
Haj. Asiya na tankwara Muhammad da babu wani
sabo da ko daya da za su yi Www.bankinhausanovels.com.ng
To tunda suka daidaita ya shiga ba ta kulawa da
Soyayya kamar wasu sababbin amare duk don ya
wanke kuskurensa na baya duk abin da yake faruwa
Muhammad ne kadai ya san da hakan sabanin
sauran yan uwansa da yake shi ne babba tsamarsa
da mahaifisa suna jinta ne su kadai bai bari
yaransu shiga ba saboda a rayuwar sa ba shi da
abin da yake so sama da mahaifiyarsa.
Ganin jituwar iyayensa yasa ya sauko daga
fushin da yake da mahaifinsa har yake sakar masa
da kuma tsayawa da mahaifiyar tasa ta yi a kan
duk abn


dole ya zama da nagari a kan duk abin da
da
mahaifinsa zai saka shi.
Kulawa da ya gani da irin soyayyar da yake ba
ta yasa ya zama mai sauki ga mahaifinsa har suka
zo suna shiri, dama ya zo Nigeria ne a wannan
lokacin don ya daidaita zuri’ a dinsa ya hada ta guri
guda domin a wancan lokacin ya kudiri niyar dukda
abin da mahaifinsa baya so shi zai yi don ya,,,,, yaddah
mahaifiyarsa cikin damuwa. Wannan kenan.
Gyara zama ya yi ya ce, ‘Mommy har kullum
ina kara gode Allah da nake samun damar da nake
gyara dukkan kuskuren da na yi a baya babu abu
mafi farin ciki a rayuwata da na ba ki hakurin duk
irin bacin ran da na saka ki tun rasuwar Hameed da
irin zafin da nake ta nuna miki har ku ka hakura ki
ka zauna da ni ba ki taba nuna gajiyawa ko kasa
zama da ni ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kin yi kokarin ganin sai da ki ka dawo da
kaunarta a zuciyar babban dana da bai ganina a
matsayin mahaifi mai adalci. Asiya tarin alherinki
gare ni yana da yawa ina fatan Allah ya hada mu
gidan Aljanna ni da ke ba ni da burin wata mata a
aljanna ni ke nake fata ki zamo min Hurun’ in di
ta.Zuri
Murmushi ta yi ta ce, Daddy ka daina tuna
baya komai  ya wuce mu kara godewa Allah,
Allah yasa kuma mu tashi a Aljannar tare.
Ameen.
Nan ya kwashe duk irin hirar da suka yi su da
su Manma Bara ya fada mata da irin yadda suka
tsara komai sun tsara cewa a gurin taro za su sanar
da cewa an dawo da auran dangi duk wanda yake
da wadda yake so ya fito ya aura zai kuma dauki
nauyin kowanne aure mutukar yana da rai da
lafiya.Ta yi farin ciki da jin komai har ranta ta ji dadi
sai dai guri daya zuwa biyu ne ya fi daga mata
hankali jin cewa an hada auran Muhammad da
Fadeela, wanda ta san cewa ko kadan Muhammad
ba zai taba yarda ya auri Fadeela ba domin bai
boye mata komai na rayuwarsa. Raihanatu yasa ka a
ransa cewa idan bai aure ta ba, to ba zai taba aure
ba, ga shi kuma ita an ce ga wanda za ta aura.
Wannan abu ya daga mata hankali, amma da yake
mace ce jaruma ba ta bari ya gano damuwa a
fuskarta ba, haka ta ci gaba da nuna masa jin dadin
labarin da ya zo mata da shi.
Ta taya shi murna ganin yadda yake nasara da
Zuciyarsa a yanzu ba kamar da da take kamar ta
karfe ba.
Haka suka gama shirin barcinsu suka faranta
damuWa a
ran junansu soyayya dai sosai kamar ba tsofaffi ba.
Ko da yake ita fa soyayya ba inda aka takaita ta ko
iyakance ta ba ga yaro ba ga tsoho. Asuba ta gari
Daddy da Mommy (Dariya). Www.bankinhausanovels.com.ng
*Sallama ta yi ta shigo dakin Granny wadda take
zaune kan sallaya ta idar da sallar Walaha, tana jan
carbi. Sai da ta amsa sallamarta sannan ta daga
hannu tana yin addu a sai da ta shafa, sannan ta
juyo ta dube ta samu gefen gado ta zauna.
Ta ce, Raihanatu kalau ki ke kuwa, na ga
yanayin damuwa duk a tare da fuskarki?
Rau-rau ta yi da idanunta da suka cika taf da
hawaye ta ce, Granny ni da Ya Abba ne na rasa
me na yi masa yaki ya daga wayata da na yi masa
magana sai ya hauni da tsawa da masifa bayan
kuma ya san bana so tun jiya na kasa gane kansa.
Yauwa kuma ke da Yayan naki an ganku a
rana ko dai wani abu kika yi masa fada min
gaskiya idan kina son na shiga cikin al amarin.
Ba ta iya boye nata komai ba yadda suka yi da
shi ta fada mata har shi kansa abin da Mr. Sameer
ya yi mata ba ta boye ba duk ta kwashe ta fada
Mata, sai dai ta nuna na Mr Sameer bai wani dame
ta ba, kamar fushin da Ya Abba ke yi da ita.
Take Granny ta gano cewa Ya Abba kishin
Sameer ne ke damunsa wanda har takai bai son
Haana din ta yi masa batun shi, nan ta kara ganewa
har yanzu Ya Abban na son ta farin cikinsa kawai
ya sadaukar don ganin nata farin cikin.
Matsowa ta yi kusa da ita ta kama hannunta ta
Rike ta ce, “Raihanatu gaskiya yayanki bai kyauta
miki ba, amma kiyi masa uzuri ko wani dalili ne
yasa ya yi miki haka, duba da hakan bai taba
faruwa a kanku ba.
To Granny me zai sa ya yi min haka, ya san
zan shiga damuwa kamar yadda baya so na shiga
damuwa, nima haka ko me ke damunsa kamata ya
yi ya fada min kamar yadda nake fada masa nima.
Granny yadda bana son bacin ransa idan har ya ce
min kada na auri Mr. Sameer wallahi zan fasa don
na ga kamar saboda shi muka bata a kan na yi masa
maganar shi.
Da sauri Granny ta ce, ‘Ba za a yi haka ba, duk
abin bai kai a yin haka ba, miko min wayar taki ki
kira min shi na ji dalilin fushin da yake da ke sai na
sasanta ku.”
Nuna mata inda wayar take ta yi saurin dauka
ta ce, Granny bari na saka a speaker na ji ko zai
fada miki laifin da na yi masa.
Granny ta dage ta bari amma ta ki dole a hakan
ta kira, bugu daya biyu ya daga ya ce cikin cikin
tsokana.Yar tsohuwa mai ran karfe yau kewa ta aka yi
ne aka kira ni da safe haka?
Cikin jin dadi ta ce, “To dan nema na yi laifi
idan na yi haka tunda kai ba ka kira ni ba, ai ni na
kira ka to ya Lagos din?
Cikin dariya ya ce, “Ba ki yi laifin komai ba, to
ina kwana da fatan duk kowa ya tashi lafiya,
saboda ban kira kowa ba dama yanzu na ke son
kiran Abba kafin mu shiga meeting.
“Kowa lafiya sai dai ban da mutum daya.
Da sauri ya ce, “Granny waye bai da lafiya’? Www.bankinhausanovels.com.ng
Fada min na ji.”Kanwarka mana da ka batawa rai ta kasa
nutsuwa saboda ta ce min kana fushi da ita.
Oho! No, Granny ban san me yasa na yi mata
haka ba, ban san lokacin da na yi mata tsawa da
masifa ba hakan da na yi yasa na kasa nutsuwa
dalilin da yasa na kasa kiranta ko na daga wayarta,
na san zan ji muryarta cikin damuwa ni kuma bana
son ji.Granny bari na kira ta yanzu na ba ta hakuri,
Ya Abbanta bai kyauta mata ba, tunda da kansa ya
saka ta damuwa bana so ta dauka cewa na canza.
Aa, ga ta nan ma gaba na bari na ba ka ita ku
daidaita, saboda kuka ta so ta yi min.Cikin
kaguwa ya ce, Granny bani ita don
Allah.”
Da sauri Haana ta karbi wayar tun kafin
Granny ta miko mata fuskarta dauke da murmushi
jin abin da ya fada.
Hello Ya Abba na please ka yi hakuri ba zan
kuma yi maka zancen Mr. Sameer ba tunda na ga
saboda haka ka yi fushi.”
Wa ya fada miki saboda haka ne, ki yi hakuri
ban san na yi miki haka ba.
Ya Abba ni ce zan fara ba ka hakuri, wallahi
Idan ba ka so na auri Mr. Sameer zan hakura tunda
har na iya hakura da son wanda nake so.
“Haana kada ki kara cewa haka ni da ba ki na
na ce miki bana son Sameer. Sameer dan uwana ne
Jinina ne na tabbata yana son ki zai kuma ba ki
dukkan farin cikin da ki ke tunani idan ki ka kara
fada min za ki ki auran Sameer zan yi fushi da ke
fiye da wanda na yi a baya.
Ya Abba me yasa ka ke son ka koyi fushi da
ni bayan ba haka muka saba yi da kai ba ka taba
fushi da ni ba haka nima bana s0 a kan wani dan ya
shigo rayuwata ka ce za ka yi fushi da ni a kansa
haba Ya Abba mai yasa za ka yi min haka…. Nan
da nan kuka ya zo mata.
Da sauri ya ce, Haana me ye kuma na kuka
daga wannan maganar ko so ki ke ki daga min
hankali na kasa abin da na je yi wa Abba.
Ba buri na kenan ba damuwata kawai kai za
ka yi fushi da ni fiye da wanda ka yi da ni idan na
ce.Sauri ya yi ya katse ta ya ce, “To na janye mu
bar maganar komai ya wuce.
Da gaske komai ya wuce. Ta fada cikin
zumudi
Eh, kashewa Granny waya kada mu karar
mata da credit anjima zan kira ki.”
Cikin dariya ta ce,Kawai mu cinye babu
wanda take kira kullum wayarta dankare take da
kudi, Abba yana saka mata ko ba za ta kira ba.
Haka dai suka yi sallama ta mikawa Granny
wayar ta ce, ‘Na gode Granny ya Abba ya daina
fushi da ni bari na je na shirya na tafi school. Ta
rungume Granny ta dan ba ta kiss a geten
kumatunta ta fice da sauri tana dariya.
gefen
Murmushi ta yi ta bi ta da kallo tana yaba irin
kaunar da yaran sukewa juna tabbas da Abba
Karami bai musu haka ba babu wanda zai dace da
rayuwar Raihana sai shi, to amma ya za su yi tunda
shi ga abin da ya hango a nasa ganin, su kuma ba
haka suke so ba.
A gajiye ta dawo daga makaranta babu abin da
ya fi damunta irin yunwa ita ke dirabin daf da za ta
shigo estate din nasu daidai lokacin da Mr Sameer
ya sako hancin motarsa daga babban get din
ya
Danfillo Estate.
Yana ganin motarta ya tsaya cak ya ki barin
gurin sai wani tokare gurin ya yi yadda ba zai ba ta
damar wucewa ba.
Tana ganin shi ne ta wani daure fuska ta ji
kamar ta je ta shako shi tsabar haushinsa da take ji,
kawai sai ta danna hon ya cika gurin da kara.
Tana hango fuskarsa dauke da murmushi ya yi
saurin daga glass din motar tasa ya kunna heater da
yake yanayin garin akwai sanyi. Www.bankinhausanovels.com.ng
Wani irin takaici ya kamata saboda abin da ta
yi masa don ya cika masa kunne ne, shi kuma ga
shi ya yi maganinta, cikin ranta ta ce,Lallai man
din nan dan rainin hankali ne ni zai kular ko?
Nan ta dauke hannunta daga kan hon din ta
rasa me za ta y1 na gaba, ganin ya dage ba sh1 da
alamar ba ta hanya ta zuciya, ga shi kuma yunwa
na kara nukurkusarta. Tsaki ta saki ta kashe motar
ta fito cikin zafi ta nufi motarsa tana zuwa ta
bubbuga masa da yake a rufe take da bakin glass,
yana kallonta ita ba ta ganinsa duk sai dariya ta
kama shi jin yadda ta ishe shi da bugu.
Ya dan dau ‘yan sakwanni kafin ya bude mata
yana budewa cikin dakiya ya ce, “Miss Haana can
help you.”
Wani irin takukin takaici ya zo zuciyarta ya
tsaya cikin zafi ta ce, “Ban sani ba malam ka ba ni
hanya na wuce ka wani tare hanya kamar don kai
kadai aka yi.
NI na isa na ce haka, wai wannan cin dacin me
ye na haka shigo ki raka ni sai ki fada min
dalilin yin sa.Cire kai ta yi ta dube shi cikin jin haushin
yadda yake kara raina mata hankali.
Ban da lokacin magana da kai na ce ka ba ni
hanya na wuce abu na ko kuma wallahi na sace
maka duk tayoyin ka na yi maka asarar fitar na bi
ta wancan get din tunda estate din ba get daya ne
da shi ba.
Wani irin kallo ta yi masa ta datse lebenta
tsabar takaicin abin da ya fada mata tsayawa ta yi
tunanin mai za ta fada masa ta yi, domin ya gama
kai ta bango take ta tuno abin da zai kona masa rai
lokaci daya, domin haka Haana take da wuya kayi
nasara a kanta in dai magana ce. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta ce, “Ayya malam maza wuce abin ka nima
ga can Ya Abba ya dawo zan je gurinsa ya gaya
min kalaman soyayyarsa masu dadi, don ka je kai
ma an fada maka ai ba haushi ko ganin laifi zan yi
ba maza tafi kada kuda ya riga ka.
Tana gama fadin haka ta juya abin ta kafin ta
shiga motar, sai da ta juyo ta ga yadda yanayin

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  gurina. Oya, …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *