ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 2 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

dama da girma komai sai a hankali.
Alh. Jafar ya ce, Hajiya kafar dai taki da dai
sauki ko dole ne kina sake ganin wanı kwararren
likitan tunda kin ki yarda a fita da ke. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kayya Jataru wane fita kuma shekara nawa za
mu kara nan gaba, kafa dai Alhamdulillah, ba
kamar da ba yanzu ana samun afuwa sosai domin
babu abin da ‘yan uwanka ba sa yi a kai, kai dai
kawai ka bar maganar da aka ce abu ya fara
haduwa da girma sai dai kawai addu’a da kuma
hakuri, amma dai yanzu akwai afuwa sOsai.
“To Allah ya kara sawwakewa.
“Ameen. Hajiya Babba da Mama Bara suka
fada a tare.
Hira mai dadi suka shiga yi zuwa can kuma
Mama Bara ta canza musu ita da maka su kan
Zaman da ta zo domin shi.

Ta ce, Alhaji ni kuwa da na so mu yi wata
magana da kai to amma gwara na barka ka dan nutsu
zuwa kwana biyu kan sannan ka gama hutawa sai mu
yi ta kafin nima na koma koda yake ni din ma zan
dan yi sati a nan kafin na koma gwara dai na bari
din ba yanzu ba.
Ya ce. “Haba dai ‘yar uwa wace nutsuwa kuma
ki ke nema gurina ai ni tuni na nutsu tunda gani
cikin ku ga Hajiya kusa da ni ai ni ba ni da wata
damuwa wane kuma hutu zan yi bayan wanda na yi
tun dazu awar mu nawa yanzu da zuwa. Ya fada
yana dariya.
Ita ma dariyar ta yi ta ce, “Haka ne kuma fa.
To kin gani, me ye maganar da za mu yi ki
fada na ji ko ina can ta kama ki kira ki fada min ai
za ki iya bare kuma gani ga ki.
Gyara zamanta ta yi ta ce, “Gaskiya ne, Alhaji
maganar babba ce, ban kuma san yadda za ka
dauke ta ba, amma mutukar za ka tsaya ka fuskanta
za ka ga akwai tarin alheri a cikinta, kuma na
tabbata kowa zai yi farin ciki da ita.”
Haka ne ke nake saurare fadi mu ji Www.bankinhausanovels.com.ng
Alhaji a yanzu dai kaf cikin zuri a din nan ba
mu da babba a cikinta sama da kai dalilin da yasa
na cehaka kuwa saboda kai namijine, ni kuma
mace dOmin a duk inda namiji yake shi ne gaba da
mace, domin ko wacce ta haife shi ce ta yi ba
daidai ba zai iya zama ya yi mata nasiha kai kan ka
ka san da wannan.Wannan duk haka yake.


To Alhamdulillah, bayan haka kOwa yana bin
duk maganar da ka kawo cikin zuria din nan a
matsayin ka na babban uba a cikinta kai ne alkalin
cikinta tumda kai ne gaba da kowa.
Shiru ya yi yana saurarenta yana ta gyada kai
bai nuna kaguwa a kan abin da za ta ce ba yana dai
bin ta ne har zuwa ta sauka.
Kwanakin baya ne ina zaune sai ga wayar
Mustapha ya kira ni ya ce. yana da wata matsala
yana son gani domin bai son mu yi maganar a
waya suna son zuwa Abuja shi da Hamza a nan na
ce musSu nima daman ina shirin zuwa jibi lokacin
da ya kira ni. Nan dai ta kwashe duk abin da ya
fada musu ita da hamza da kuma abin da yake son
a fahimtar da kai don bai bayyana kowa ya sani ba.
Duk ta kwashe ta fada masa.
Shiru ya yi yana jinjina kai ya kasa cewa komai
sai a nan Haj. Babba ta ce, Jafaru ni a ganina
wannan abin, abin dubawa ne, idan har aka hana
Mustapha yin abin da yake so kamar an shiga
hakkinsa idan da a ce kafin a daidaidata suka yi
aure ai ka ga ba za a je a ce a raba auran ba, tunda
an hana auren dangi, ina ganin tunda har ya danne
abin da yake ransa bai bayyana muku ba yanzu ma
mafita ya rasa shi yasa ya zo ya fada muku.”
Shawarata a nan ina ganin a janye wannan Www.bankinhausanovels.com.ng
wannan tsaurin da kuka yi wa yaranku ina mai tabbatar
muku da cewa idan har za ku yi kwakkwaran
bincike sai kun samu wasu cikin varanku da suke
SOn Junansu suna jin tsoron bayyanawa ne don ba
barinsu za ku yi ba, amma a nawa hange idan aka
bar su kowa ya kawo wanda yake so ina ganin ba
karamin tarin farin ciki zurî a din nan za a samu ba
duba da irin kaunar da kowa ke yi da dan uwansa
Idan ku kuka duba kowannenku auran dangi
aka yi masa ba mu taba samun matsala ba, sai a
kan abin da ya faru a kan Hameed da Aziza, idan
har yanzu ba za a saki wannan tsaurin ba to fa ina
hango wata amtsala a gaba, amma ba haka nake
mana fata ba. Ni dai fatana a bar Mustapha ya hada
auran nan da yaransa tunda sun riga da suna da
wannan buri 1dan an yi haka zai san an yi masa
adalci an kuma nuna masa KARAMCI zai kuma ji
dadi ya yi farin ciki da ku duka baki daya.”
Alhaji Jafar ya numfasa ya ce,Hajiya na ji
duk abin da ku ka ce na ammce na kuma bada
gudummawar zan dauki nauyin wannan auran da
hannuna domin har kullum ina neman abin da zan
yi don na farantawa Mustapha rai don kawar da
abin da na yi masa a baya na yi nadamar duk abin
da na yi a baya bana kuma fatan na sake janyowa
zuri’a dinmu wani tabo a zo ana kuka da ni.
Hajiya insha Allahu daga wannan ranar ba
wanda zai kawo wata bukata mutukar ta ci gaba ce
a dangi a ce ban karba ba, ina sane da
gudummawar da ‘yan uwana suke ba ni a lokacin
da na nema don haka su ma yanzu lokacinsu ne da
yanzu za su nemima a gurina na yi musu daga yau na
datse wannan dokar hana auran dangi tunda abin da
muka hana ba addini ba ne.
Tsananin farin ciki ne ya kama Hajiya Babba
da Mama Bara, nan ta shiga sanya masa albarka da
shi da bayansa baki daya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ameen, Ameen.” Babu adadi Mama Baraka ta
fada, nan ta ce, “Alhajina Allah ya saka maka da
alheri nima ina da tawa bukatar tunda haka ne.
Dariya ya yi ya ce, Ke nake saurare yar uwa
ki fada min kowacce iri ce insha Allahu zan biya
miki ita matukar ba ta fi karfina ba tunda yanzu ina
cikin farin ciki.”
Murmushi ta yi ta ce, Haka ne ina ganin tunda
mu ne manya kuma komai ana son ya fito daga
gare mu don na kasa su gani su yi koyi da shi, to
hakan ne kowa zai yi farin ciki.
Ina ganin tunda Mustapha da Maryam din suke
Ciki daya sun hada yaransu aure mai zai hana mu
ma da muke manya mu ma mu hada auran
Mahammadu naka da Fadeela tunda na jima da
sanin suna son juna ka ga idan mun yi haka mun
haskakawa zuri’a tunda sun hada kowa zai samu
damar sakin jiki tunda abin ya faro ta gurinmu ko
kai ya ka gani?
Shiru  ya yi zuwa can ya ware ya ce, “lna
gani babu wata matsala da ina da wani uzuri
wannan zuwan da muka yi da har na yi niyyar hada
auran shi Muhammad din da ‘yar wani aminina,
amma a yadda na ga fuskarsa bai amince ba.
Amma tunda shi kadai na fadawa ban fadawa uban
yarinyar ba tunda ga gida bai koshi ba ai ba za a
kai dawa ba, ya san halin Fadeela tunda sun rayu
guri guda ina ganin ba matsala ko dalilinta ne ma
da na yi masa magana a ga sauyi a fuskarsa.ba
Tsananin farin ciki ne ya kama Mama Bara
domin burinta da na yarta zai cika yadda ta dauki
abin sai ga shi ya zo mata cikin sauki ba tare da an
kai ruwa rana ba, cikin jin dadi ta ce, DAn uwa
Ubangiji ya cika mana ladan wannan abin da muka
yi mun gode Allah dama duk wani kuskure idan ya
faru manya ake son fara ganin sun gyara sannan
yara su gani su yi koyi.”
Hirar jin dadi suka yi tare da kara samun wata
addu’a a gurin mahaifiyarsu wanda ta ce musu ta fi
su jin dadin faruwar haka tunda rai ya yi mata rana
an samu matsala daga gurin nata an kuma samu
mafita a gurinsa.
Karfe sha daya saura na dare ya fito daga gurin
mahaifiyarsa ya nufi gidan sa gurin iyalansa har
bakin get Mama Bara ta rako shi suka rabu cikin
farin ciki tare da tsayarwa cewa za su zauna zaman
family domin fayyacewa kowa kudurinsu da suke
da shi ko kuma su ce suka zartar.
A daidai wannan lokacin suma gidan Alh.
Mustapha da Granny suna tattauna tasu matsalar.
Granny ta ce, “Aisha ni a anawa ganin tunda
Raihanatu ta nuna min cewa ta amince da Sameer
din nan ina ganin ai ba wani aibu ba ne duk abu
guda suke a gurinmu duba da abin da ya Yayanta
ya ce damu babu yadda za mu yi haka Allah ya
tsara. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kuskurenmu daya da ba mu bayyana musu
abin ba tun wuri shakuwarsu da kaunarsu hakan ne
yasa suke ganin kamar Ciki daya suka fito, shi yasa
kowa ya kasa cewa ga wanda yake SO, musamman
shi Mustapha karami shi ne namiji shi ya kamata
ya nuna mata hakan ya tsaya Zurfin ciki har Allah
ya kawo Sameer din.
Yanzu idan ba mu yi haka ba shi kansa yaron
zai zarge mu da wata manufa tamu kuma ba haka ba
ne a gurinmu ba, mu dai har kullum burin samun
masalaha a cikin wannan zuria din duk abin da zai
kawo matsala ba ma son ya fito ta gurnmu.
Tunda Mustapha karami ya ce, Haka to mu
daure mu ba shi kwarin gwiwa tunda farin cikn ta
yake sO mu ma kamata ya yi mu ba ta shi.
Umma babu matsala ai ni ba ni da wani abin
cewa face abin da ku ka ce, idan har zabina ne to
ba ni da kamar yayanta, amma da yake komai
mukaddari ne daga Allah ba ni da ta cewa sai abin
da Allah ya tsara tunda alherin abin muke nema.
“Wannan haka yake Aisha ba mu san me Allah
ya shirya ba fatanmu dai mu nemi alherin abin shi
ne kadai abin da za mu yi mu bar masa sauran
Cewar Granny.
Abba ya ce,Tunda kowa ya gamsu babu
matsala bana jin sai na nemi Ammina da wannan maganar tunda ke Umma ta fada miki na san akwai
kunya tsakaninmu tunda duk zuciyoyinmu sun
yarda kan zabinta da kuma abin da yayanta ya ce
ina ganin idan mun yi taro zan zo mu su da yadda
abin ya zo da sauyi sabanin zaman da na yi da su a
baya wato Hamza da Hajiya Bara atu ina ganin mu
tsaya a haka ko ya ku ka gani?
Duk suka amince da hakan sai dai Ammi har
ranta ba ta so haka ba, amma jin ba yarta ce ta ce
ba ta son shi ba da ita ce ko za ta mutu ba ta isa ba
sai ta aure shi don yadda take son Ya Abba a ranta
wata rana ma mantawa take cewa ba ita ce ta haife
shi ba.
Babu yadda za ta yi dole ta yarda da kaddara ta
zo ta same su kuma abu na zuri’a  ka ce wani abu a
kai a ce ka nuna rashin son wani.
Abba ne ya raka Granny dakinta sai da ya ga ta
shiga, sannan ya juya ya koma inda ya bar Ammi
anan ya zo ya same ta yana ganin fuskarta ya
karanci damuwarta. Zama ya yi yana daddanarta
yana nuna mata yadda rayuwa take ba lallai ne abin
da mutum yake so zai samu ba.
Nasiha da kwantar mata da hankali da ya san
ko kada ba ta so haka ba ya kuma nuna mata cewa
Amminsa ba ta da laifi shi ne ya hana a fada mata
yana son ta dole ba yadda ta iya haka ta bi abin da
yake so don ganin ta kori damuwar da take gani a
fuskarsa take ta nuna masa komai ya wuce. Www.bankinhausanovels.com.ng
Juyi take a kan gado barci ya gagari idanunta
saboda damuwar da take ciki, tun ba yanzu ba take
neman wayar Ya Abba a kashe ta kasa samunsa
hakan ba karamin daga mata hankali yake ba.
Ya za ta yi da ranta ko ina za ta ga farin ciki  wai yau Ya Abbanta yana fushi da ita abin da
bai taba faruwa da ita ba, idan har ba fushi yake da
ita ba ya za ai ya kashe mata waya.
A can kuma daya bangaren na zuciyarta
takaicin abin da Mr. Sameer ya yi mata take shi ne
ya bata mata rai, amma shi ne da yin fushi.
Dole ta nemawa kanta mafita me shi Mr
Sameer din ya dauki kansa ne ko don ta nuna tana
son shi shi ne zai ke nuna shi mai power ne a kan ta
waye shi mai yake da shi me kuma yake daukar
kansa ko yana tunantn son da take masa ya yi
zurfin da zai ke nuna mata wannan zafin da
hayakin kai, sam ba za ta dauka ba.
Idan Ya Abba ba zai goyi bayan auran da take
gani za ta yi da shi ba to a yanzu daf take da ta
dakatar da shi tun kafin magana ta yi nisa, domin
ba za ta auri wanda Ya Abba baya so ba, ta
fuskanci Mr. Sameer ba mai sauki ba ne ita kuma
ba ta shirya auran mutum mai irin halınsa ba, yana
tunanin da Ya Abba ya ce yana sonta za ta tsaya
ma ta saurare shi sam haka ba zai yiwu ba, mutum
biyu ne ZUCIYA DA RUHINTA duk wanda ta
samu cikinsu za ta iya rayuwar farin ciki da su, Ya
Abba ko Malam M.J sai dai kuma kash! Tuni ta
fitar da wannan tunanin da mafarkin.
Tuni ta hakura da Malam M.J don yanzu haka
ma tana jin an yi auransa da ‘yar uwarsa, shi kuwa
Ya Abba ba za ta taba tunkararsa da cewa tana son
shi ba tunda ga tubalin da ya dora ta ya tsani macen
da za ta ce tana son shi, matukar Mr. Sameer zai ci
gaba da yi mata haka za ta dakatar da shi daga
cikin rayuwarta saboda babu dole a so.
Kwance take kan gado tana ta wannan zancen
zucin wayarta ta fara ruri kafin ta daga wayar sa
da ta duba agogon bangon da ke manne jikin
dakinta ta ga karfe sha biyu da kusan rabi da sauri
ta da ga a tunaninta Ya Abba ne, ko Mr. Sameer.
ldan Ya Abba ne ta ba shi hakuri, idan ta bata masa
rai, idan kuma Mr Sameer ne a shirya take da duk
wani zafi da danyan kan da zai zo mata, domin sun
yi ma da wanda ya fi shi zafi, ga mamakinta sai ta
ga Fadeela ce.
Da sauri ta dauki wayar ta kara a kunnenta ta
ce, Hello, ‘yar uwa lafiya dai ke ce da waya a
cikin daren nan.
Cikin doki da murna ta ce, Lafiya lau yar
uwata ina cikin farin Ciki ne a wannan daren na ce
babu wadda ya kamata na sanarwa halin danake
ciki irin ki: Www.bankinhausanovels.com.ng
Haana burina ya cika na samu abin da nake so
yanzu Mama take fada min cewa Daddy ya yarda
da aurenmu ni da Ya Muhammad farin cikin da
nake ciki ne yasa na kasa barci ba don dare ba ne
da kin gan ni yanzu a dakinki domin kin wuce haka
a gurina. Haana kina da kirki da yawa kuma
maganganunki akwai hikima a ciki ga shi da ban
daga hankalina ba abin ya zo min da sauki, ina son
ki da kaunarki ‘yar uwata.
Duk irin damuwar da Haana take ciki sai da ta
JI wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyarta take ta ce.
Kai gaskiya Fadeela na yi miki murna ba
karamin farin ciki ba ne ka samu abin da ka ke So a
rayuwarka na taya ki murna sOsai wallahi.
Cikin jin dadi ta ce, Haana ko ba ki rantse ba
na san yadda ki ke Sona za ki so na samu
dukkan abin da nake so ke ma ina miki fatan
samun haka.”
Hmmm, ke dai bari, to ameen dai.
To yawwa ya dai ba kya ganin akwai wata
matsala gurin Ya Muhammad dangane da auran
nan?
Ckin dariya ta ce, Babu wata matsala Haaana
amtsalarmu daya dama Daddy tunda har ya amince
ba mu da wata matsala.
A to 1dan haka ne nima na yi farin ciki sosai
Allah ya nuna mana wannan lokacin mu sha biki
abin mu.Ameen
Ameen yar uwa na yi farin ciki da hakan
dama tuni na yi tunanin samun wannan tarbar farin
Cikin daga gare ki.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan suka juya hirar ta su zuwa wani zancen
daban. Sun jima suna hira daga nan suka yi
sallama.
Ko ba komai Haana ta dan samu nutsuwar
zuciyarta kadan da haka har ta samu barci ya yi
awan gaba da ita
Alhaji Jafar ne ya yi sallama ya shigo dakin
Haj. ASIya wato Mommy inda ya tarar da ita tana
shirin barci. Bayan ta amsa sallamar cikin
murmushi ta ce, “Daddy ai na yi tunanin a can ma

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 4 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  gurina. Oya, …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *