ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 8 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

ka fice min daga gida. Yaudarar da ka yi min ta nuna cewa koya maka aka yi, don haka ban yarda ka Kara min ko minti guda ba cikin minti biyar din nan. Kada na fito naga Keyarka a nan. Mustpha wuce mu je” Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsananin mamaki ne ya bayyana a fuskar Sameer, ko kadan bai taba tunanin haka ba daga wajen kawun nasa. Tunda ya ke bai taba ganin tsana a fuskar wani mutum ba irin wacce ya gani yau da aka nuna masa. Sai dai ko kadan ransa bai baci ba, domin duk abin’ da ya yi masa bai ga laifinsa ba, don hakan ya nuna har yanzu ya na cikin fishin. Kuma duk wanda Zur’arsa za su yi masa haka dole ne ya yi fiye ma da hakan.
A ta ke shima ya ji ba zai iya zama a cikin Estate din ba. Kai tsaye kawai ya juya zuwa Kaduna domin ya fadawa iyayensa su san abin da za su yi su kori wannan bakar gabar domin ya na ganin abin ya fi Karfinsa.
******
Kwancce ta ke akan gadonta ta yi ruf da ciki sai kuka ta ke yi kamar hawayenta za su Kare. Tun

dazu Rauda ta ke bata baki amma ta ki ta daina
kukan. Haka ta rabu da ita ta koma gidansu.
Ya jima akanta amma ba ta san ya shigo ba.
Haka ya dinga jin wani abu ya na yawo a cikin
zuciyarsa. Tabbas ba don Abbansu ne ya yi mata
wannan tsawar ba ba ya jin zai iya barinsa haka,
don babu abin da ya tsana irn a yiwa sister dinsa
tsawa ko fada.
Haka ya janyo stool ya zauna daidai saitin
kafarta. Kai tsaye ya fara bubbuga mata kafarta.
Tana jinsa amma ba ta motsa ba. Jin ya ambaci
sunanta ta yi saurin dago kanta ta dubeshi fuskarta
cike da hawayen Www.bankinhausanovels.com.ng
Cikin kuka ta ce.Ya Abba ka ga yau abin da
Abba ya yi min ko?. tsawa da fada duk lokaci
guda, ya sakani damuwa. Mai na yi masa da zai yi
fishi da ni haka, ko Mr.Sameer ne ya jawo nima ya
yi fishi da ni haka?.


Da sauri ya dawo gabanta ya fara share mata
hawayen da suka cika mata fuska ya ce “Come on
my little sister kada ki damu, Abba ba zai taba fishi
da Haana dinsa ba. Nasan fishin da ya yi ne ya
saka idonsa ya rufe har ya yi miki tsawa. Amma
nasan ba don haka ba Abba ba zai taba yi miki
tsawa ba, kuma nasan da ya huce zai zo ya
rarrasheki. Ni kaina banji dadin yadda ya yi mikn
ba, banda shi kuma ba wanda zan iya kyalewa ya
yi miki wannan tsawar na kyale shi ba, don dole sai
ya fanshi kansa da hukunci daga wajena.
Yanzu dai ki daure ki daina damuwa ki saki
ranki ki tuna yanzu a gaban Abbanki ki ke babu
wanda zai sake bata miki. Ina son ma ki saki ranki
kamar ma Abba bai miki wannan tsawar ba,
yarinya ta gari ba ta fishi da Abbanta idan ya yi
mata fada. Ina son idan anjima ya huce ki je ki ba
shi hakuri
Dariya ta fara yi jin yadda yake rarrashinta
kamar wata karamar yarinya. Tana jin ya ce ta je tabaiwa Abban hakuri ta kuwa turo baki gaba ta ce.
Ya Abba kada ka ce na je na baiwa Abba hakuri
na fuskanci yanzu dai kawai ya daina sona tunda ka
ga na yi masa magana amma ya ki Saurarena nasan
ko na je ma ba zai saurareni ba Www.bankinhausanovels.com.ng
Girgiza mata kai ya yi sannan ya ce mata.
Haana ba mu taba hin musu da ke ba, don haka
kada mu fara yanzu, ki yi abin da nace miki kawai
idan ba so ki ke nima na yi fishi da ke ba. Cikin
sauri ta zaro idanuwa tace
Ya Abbana zan yi abin da ka ce Allah, saboda
ba ka taba fishi da ni ba. Ina ji a raina idan ka yi
fishi dani zan iya rasa dukkan farin cikina gaba
daya, zan iya jure fishin da Abba ya yi da ni, amma
ba zan iya jure fishin da Ya Abba zai yi da ni ba.
Please Ya Abba kar ka yi fishi da ni ko da a cikin
Dream dinka ne
Dariya ya yi mata sannan ya kai hannu ya
lakuce mata hanci yace. Kwantar da hankalinki.
ba zan taba iya fishi da Haana dina ba ko da a
mafarki ne kuma zan ta baki farin ciki har sai kin
ce ya isheki”,
Sai ta sake sakin wani murmushin ta ce.
Yawwa Ya Abbana, shi yasa nake matukar sonka
fiye da kowa da komai, tun da ka tafi na yi missing
dinka, amma yanzu nasan tunda ka dawo ba zan
sake samun damuwa a dukkan matsalolina ba”.
Sun jima suna hira, sai can kuma ta tuna da
Mr.Sameer, ko yanzu a wane hali ya ke. da sauri ta
ce.Ya Abba bari na bugawa Mr.Sameer waya na
ji ya na ina ko ya na gidansa na cikin Bstate
dinmu
Nan ya bata UMARNI ta buga ta ji a ina ya ke.
idan ya na waje ne ya fita ya same shi. Bugu daya a
na biyun ne ya daga wayarta cikin fara’a ya ce.
Yes Miss Haana kina lafiya dai ko, da fatan
dai ba ki yi fishi da abin da Abbanku ya yi miki ba
dai ko?
Na yi mana, shi yasa ma na kira ka na baka
hakuri, don ban ji dadi ba ba haka naso ba, sannan
na ji kuma yanzu ka na ina Ya Abba zai fito yanzu
sai ku hadu
Look Miss Haana, bana son jin haka daga
bakin ki, nima mahaifina ne, ya na kuma da damar
da zai min ko wane irin hukunci. Idan ki ka tuna
yadda ya saka min doka ni kuma na ZO na karya.
Kin ga kuwa duk wani punishment din da ya bani
daidai ne shi a wajensa, ni ban yi fishi da abin da
ya yi min ba.Tunda dai mun yi nasara da abin da na zo yi kuma insha Allah sai mun yi nasara a kansa.
Wannan fishin nasa kar ki damu ni I am felling
better Www.bankinhausanovels.com.ng
Shikenan na ji yanzu ka na ina?
Ni yanzu fa kin ganni na kama hanyar
komawa Kaduna
Kaduna ta fada cikin mamaki mai cike da
razana.
Eh mana, kina mamaki ne?
Ka yi fishin kenan?, tunda ga shi ka koma
Kaduna
Wa ya fada miki? UMARNI Abba ya bani, ni
kuma bana son yace ga abin da yake so, ni kuma
na ce ba zan yi ba a gaba kuma a samu matsala. Ki
gane duk abin da zai yi shi yanzu cikin fishi zai yi
shi, idan ya zo ya tarar ba na nan ransa zai yi fari,
amma 1dan ya zo ya tarar da ni zan 1ya kara masa
damuwa, ni kuma ba na fatan haka
Shikeman yanzu ga Ya Abba din sai ku yi
magana. Sai kawai tamika masa wayar suka
C1gaba da magana, sannan suka yi sallama da juna
bayan shi ma ya nuna rashin jin dadin tafiyar tasa.
Amma da ya yi masa bayani sai ya gamsu ya kuma
Jinjina masa da tunanin da ya yi. Daga nan kowa ya
ajiye waya.
A tare suka jero tare da Ya Abba akan zai raka
ta ta baiwa Abba hakur1. Nan suka iske ba ya nan.
Kai tsaye suka nufi wajen Ammi. Nan ta fada
musu fishin da ya yi da kuma fadan da yayi don
me yasa ba ta kira shi ba ta fada masa cewa ga
abin da ya ke faruwa ba. Da ba zai bari ya yi
wannan kwanakin ba. Ga shi kuma Granny tayi
fishi da shi don ta maki daga wayarsa, duk abin yayi masa yawa.
Nan ta ke Haana ta ji tausayin Mahaifinta ya
kama ta. Ta san ya na yi wannan abin ne kawai don
ya kare mu su mutuncinsu da tuno 1rin wulakancin
da kuma wariyar launin fatar da ‘yan uwansa suka
yi mu su.
To amma dai tunda yanzu komai ya zo da sauki
da hakura ya y1 aka zo aka gyara zumunci da hakan
zai fi. Tuno irin damuwa da tashin hankalin da
Abbanta ya shiga a baya, sai ta ji yanzu ba ta ganin
laifinsa. Sai dai duk da haka za ta so ya hakura ya
manta da abin da ya faru a baya. Abu ne daga
Allah an rubuta shi cewa dole zai faru, ba kuma
wanda ya ke da ikon hanawa. Haka ta wanzu cikin
wannan tunanin.
Washegari misalin karfe sha daya na safe sai
ga motocine a kalla sun kai guda shida. Haka suka
yi jerin gwano suka shigo cikin Estate din Dan fillo
da ke garin Kano. Manyan motoci ne na gani na
fada tamkar daga fadar shugaban kasa suka fito.
Abba ne ya fito cikin shigarsa mai kyau. Sanye
ya ke cikin farar shadda hade da babbar rigarta, ya
sha hularsa tangaran ya kara yin wani kwarjni na
musamman, kai da ganinsa ka san ya na cikin
kwanciyar hankali da kuma tarin dukiya. Ya Abba
shi ma ya fito cikin shigarsa mai kyau. Kaftani ce a
Jikinsa. Ya na dauke da case, ya Z0 ya saka a bayan
motar. Shi ne ya budewa Abba mota ya shiga,
sannan ya bude na shi Side din ya zauna.
Ya na tura hancin motarsa da zummar su fara
tafiya nan suka hangi motoci suna shigowa cikin
Estate din na su. daga shi har Abban suka shiga
duba ga tarin motocin suna mamakin ganin hakan.
Musamman ma Abba da ya cika da mamaki saboda
babu wata mota da ya sani Cikinsu. Haka ya bi
lambobin motocin ko zai gane, amma bai gane ko
daga ina suke ba.
Ga shi dai kuma bai yi meeting point da kowa
ba bare ya ce ya na zaton zuwan su. Mustapha
tsayar da motar nan mu gani saboda ban gane
wadannan motocin ba. Fito mu ga ko Su waye, don
ba na jin zan yi baki
To Abba Ya fada cikin ladabi. A tare suka
bude motar ta su suka fito suna kallon motocin da
suka nufo su. har yanzu dai fuskarsa dauke ta ke da
mamakin wadannan motocin. A haka dai motocin
suka karaso wajensu.
Hange ya ke ko Allah zai sa ya hango wanda ya
sani a cikinsu. Jeep ce har guda uku sai murano guda
daya sai kuma final discoussion guda biyu.
Direban Jeep din kawai ya gani. Lokaci guda ya ga
duk sun faka, haka kuma kamar hadin baki lokaci
daya aka soma bude motocin. Tsananin mamaki da
rudewa suka bayyana a fuskar Alh Mustapha don
babu ‘wanda idanunsa suka fara yi masa tozali da
shi sai Alh Ja’afar nasa. Daga shi sai Alh Lukman
sai kuma Alh Aminu. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bude baki ya y1, ya ma rasa mai zai y1, farin
ciki ko kuma bakin ciki. Nan ya hangi dattijan
iyayensu guda biyu, Haj Safiya da Haj Babba. A
tsaye ya ke ya ma kasa daga ko da kafarsa daga
inda ya ke. tun kafin ya yi wani abu sai ya hangi
Alh Ja’afar ya na tahowa gareshi idanuwansa cike
da kwalla ya zo ya rungume shi.
Shi ma kawai sai ya ji ya rungume dan uwan
nasa. Hakika kauna ta jini ba karya ba ce. Lokaci
guda Abba ya J1 wani 1rin farin ciki ya mamaye
masa kO ina na Jikinsa. Shin wai mafarki ya ke ko
dai gaske ne?, a ce wai yau shi ne a jikin dan
uwansa. Haka ya dinga jin wata kaunarsa ta na
shigarsa, sai kawai ya ji duk wani kunci ya na barin
jikinsa.
Cikin raunanniyar murya Alh Ja afar ya fara
magana. “Mustapha don Allah ka yafe min, ina so
ka yi min aikin gafara, duk sharrin shaidan ne da
zuciya suka kaini ga aikata haka. Ya na gama
fadin haka sai hawaye mai hade da kuka.
Jin muryar dan uwansa cikin kuka, sai shi ma
kawai ya ji kukan ya zO masa nan ya yi saurin raba
shi da jikinsa tare da girza masa kai ya ce. “Yaya
Ja’afar ba kuka za ka yi ba, godiya ya kamata mu
yi wa Allah da ya kawo mu wannan rana, na kuma
yafe maka
Ai ya na kawowa nan sai Alh Ja afar ya sake
rungume shi. Sai suka koma kamar wasu yara suna
kuka.Mustapha ina Son na fada maka cewa. yau
nayi nadamar abin dayi maka a baya. Idan har
ka na da wani hukunci da za ka yi min, to a shirye
nake na karbe shi komai tsaurinsa indai hakan zai
sa ka yi farin ciki.
Ga shi ni ne Babba, amma tsabar son raina da
kuma son zuciya sai da suka sa na yi abin da bai
dace ba. Don Allah ni dai na roke ka da ka yafe
min Mustapha. Sai kawai kuka ya ci karfinsa, Da
sauri shima ya dora da.
Yaya Ja’afar na fada maka ka daina kukan
nan, komai ya wuce a wajena tunda har ku ka tuna
da ni bayan tsawon wadannan shekaru da ba mu
sake haduwa ba
“Ni kaina Mustapha ina rokon afuwarka da
yafiyarka domn ni kaina a shirye nake da karbar
hukuncCin ka ko wane ir1 ne. nasan dai son Zuciya
ne ya janyo mana haka, ni Aminu kwarai na bada
gudummawa sosai wajen farraka ZURI’ A DAYA,
don haka ga mu nan gaba dayanmu mun zo neman
afuwarka da kuma neman sulhu. Insha Allah za mu
yi kokarin ganin mun gyara duk wani kuskure da
muka yi a baya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sauri Abba ya yi ya saki Alh Ja’ afar ya zo ya
rungume Alh Amnu sannan ya ce. Yaya Aminu
plcase, don Allah ku daina wannan maganar kuna
kara karya min zuciya. Ku zo mu shiga daga ciki
Daya bayan daya ya bi duk ‘yan uwan nasa ya na
Kiran sunan sU Suna gaisawa tare da rungume juna.
Duk cikin su babu wanda ya iya daurewa bai
zubar da hawaye ba, musamman iyayensu mata.
Gaba daya murnar ganin ‘yan uwansa bai sa ya ga
Granny ba. Can sai ya hange ta tana zubar da
kwalla. Da sauri ya karaso gareta ya rungume ya
na fadin. “Don Allah Umma ki yi min afuwa na
sanyaki damuwa da na yi
Girgiza masa kai ta yi. Babu komai na yafe
maka, komai aiya wuce
Rike da hannun yayyensa biyu suka shigo
gidan tare da Aminu wanda ya ke kusa da su. shi
kuwa Ya Abba tunda ya yi tozali da Granny dinsa
ya je ya rungume abarsa.
Suna shigowa falon kuwa ya shiga kiran
Ammi, wai ta zo ta gani. Ai kuwa gaba daya ita da
Yaranta suka fito a rude don jin mai ya faru. Ta na
zuwa kuwa sai ta yi mutuwar tsaye, ganin abin
mamakin da ko a mafarki ba ta taba kawo shi ba.
Sauran yaran da basu gane 1yayensu bane, kawai
sai suka fada kan Granny da murnar ganinta ta
dawo.
Haana kuwa ji ta yi kamar ta zuba ruwa a kasa
ta sha don murna. Ai ko gaisawa ba ta bari an yi ba
TayI saurin tafiya wajen Mamah Mee don ta fada
mata. Jim kadan kuwa itama sai ga ta nan da
yaranta. Ai kuwa ta na ganin yayyenta da iyayenta
sai ta fashe da kuka ta je ta fada jikin Haj Babba.
Kukan da ta ke yi ne ya kara karya zukatansu,
Tabbas duk inda dan uwanka ya ke na ka ne. duk
Ir’in jarumta ta maza amma sai da kowa ya sake
zubar da hawaye. Tabbas jini da ‘yan uwantaka ba
Karya bane, domin duk wanda ya yanke zumunci
tsakaninsa da dan uwansa na jini ko kuma ya ke
musulmi mutukar ya mutu bai tuba ba, to
musulmi makomarsa jahannama ce, Allah ka tsare mu da shiga wuta, Ubangiji ka tsare mu da aikin shaidan
da na Zuciya, Allah ka tafiyar da mu akan
zumuncinmu mu da Zuri’ ar mu gaba daya.
Bayan yan koke-koke da aka yi. Ammi da
Mamah Mee ne suka hadu da yaransu wajen
hidima da baki da abin motsa baki. Hatta Ya Abba
shima taimakawa ya ke wajen kai komon. Bayan
sun gama ne yaran suka watse don hira da junansu,
sai aka bar iyayen don su tattauna da juna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan an bude taro da addu’a, Alh Ja’a far ne
ya fara magana da cewa. “Yau ina matukar farin
Ciki da wannan rana da Allah ya nun min wacce
ban bar duniya ba sai da Allah ya nuna min har na
zo da kafata na baiwa dan uwana hakuri kan tarin
laifukan da na yi nasa, wanda kuma na samu
goyon bayan yan uwana, don haka ne ma nake
kara neman afuwa a wajensa, Ina neman kuma ku
kara tayani ba shi hakuri kan abin da na yi masa a
baya
Alh Aminu ne ya cafe da “Muka dai yi masa
Yaya Ja’a far, ba don na goyi bayan haka ba, ai da
abin bana tunanin zai kai mu ga haka. Laifi dai
dukkanmu mun yi masa, muna kuma neman afuwarsa. Insha Allah za mu hada kanmu ba za mu
sake barin irin wannan ta sake faruwa cikin

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Suna cikin …

One comment

 1. ALBISHIR GAMASU LIZIMTAR KARATUN ALQUR ANI

  1. Kyakkyawan Hadisi Daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: 'Idan mutum ya mutu danginsa suka shagaltu da jana'izar sa,wani kyakkyawan mutum zai tsaya a kansa a Lokacin da ake rufe jikin mamaci, wannan mutumin yakan shiga tsakanin mayafin da kirjin mamacin.

   Lokacin da aka gama binne sa, mutane suka dawo gida, mala'iku 2, Munkar da Nakeer (Mala'iku biyu na musamman masu tambayar kabari), zasu zo cikin kabarin sa suna kokarin raba wannan kyakkyawan mutumin da mutumin da ya mutu, don su sami damar yi wa mamacin tambayoyi a game da imaninsa. 

  Ammaa kyakkyawan mutumin nan zai ce, 'Abokina ne shi. Ba zan barshi shi kaɗai ba. Idan an nada ku don yin tambayoyi, kuyi aikinku. Ba zan iya barin shi ba sai na shigar da shi Aljannah '.

   Bayan haka sai ya juya ga abokinsa (mamacin nan) ya ce, 'Ni ne Alkur'ani, wanda ka saba karantawa, wani lokacin da babbar murya wani lokaci kuma da karamar murya. Karka damu. Bayan Munkar da Naker sun game maka tambayoyi, ba za ka sami baƙin ciki ba. ' 

   Lokacin da Munkar da Nakir suka ƙare tambayoyin su ga wannan mamacin, sai kyakkyawan mutumin nan ya shirya masa daga Al-Mala'ul A'laa, shimfiɗar siliki cike da miski.

   2. Annabi (SAW) ya ce: 'A ranar sakamako, a gaban Allah babu wani Mai Ceto da zai sami matsayi sama da Alkur'ani, ba Annabi ko Mala'ika.'

   3. Don Allah a tura wannan 'Hadisin' zuwa ga Yan uwa muslmai …. saboda Annabi (SAW) ya ce: 'Ka bada ilimi daga wurina ko da aya ɗaya ce'. Allah Ya bamu iko.Ameen

   4. Muna addu'ar wannan sakon da muka kawo zai isa zuwa ga musulmai akalla miliyan biyar a duk faɗin duniya cikin kwanaki bakwai (7) masu zuwa, Insha-Allah. Da fatan za a tura wannan sakon a YAU ga abokai da dangi dan samun lada mai yawa daga Allah (SWT).

   * Idan ka dauki Al-Qur'ani, Shaidan yakan kamu da ciwon kai.
   * Idan Ka buɗe shi, sai ya fadi.
   * Idan Ka karanta shi, sai ya suma.
   * In kukayi kokarin tura wannan sako na Alkairi, zaiyi kokarin sanyaya muku gwiwa.

  Allah Ka amfanar damu da abinda muka karanta ko muka saurara Ka Kuma datar damu

  Yaa Ilaheeyhttps://mynovels.com.ng/aymana-hausa-romantic-novels/

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *