ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 7 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 7 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

auren zumunci. Banda haka ba na jin ta na yiwa wani namiji cikinmu wani abu banda matan. Ashe kuma ta nuna muku halin nata?”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haana ta tabe baki ta ce. “Lallai ta na da aiki, wato ita burinta aure ne, ba wai a shirya don zumunci ba. Da ace babu wannan tunanin na son tayi auren zumuncin da ba za ta so a shirya ba”
Murmushi ya yi. “Ina ganin ba ita kadai ba ma, ni kaina ina son a shirya, don a dawo da batun

auratayya a junanmu, saboda ni ma na gano wadda
nake so”.Rike haba Haana ta yi ta ce “Oh! Mr.Sameer kenan, kenan na daina ganin laifin Fadeelah, kaima kenan kanka ka zo yiwa aiki, ka na da wata da ka ke so cikin family, shi yasa ka yi haka?. Ko da ya  ke kai ai ka yi KoKari tunda ka hada mu da ‘yan uwanmu, ga shi kuma kowa ya yi farin ciki hakan kuwa Allah ne kawai ya san ladan da ka samu”.
Rauda ta ce “Gaskiya kam ya samu lada. Mu ai mun fi su jin dadin, saboda su suna da yawa, mu ne dai muke a gefe guda” Www.bankinhausanovels.com.ng
“No Rauda, mu ma mun ji dadi sosai Shekara ‘ nawa ba ma tare da ku. Ba wai mantawa muka yi da ku ba, kawai dai rudin zuciya da sharrin

shaidan da suka yi riba akan iyayenmu, tunda ga shi mun taso sai mu rike zumuncinmu a dawo zama waje daya. Ta hakan ne za’a manta da abin da ya faru shekarun da suka shude”’.Gaskiya ne wannan. Zan cigaba da yi muku addu’a kai da Fadeelah Allah ya baku abin da ku ke so. To ita mun ji wanda ta ke so, kai kuma fa, Ko ba haka bane Rauda?”. Haana ta furta hakan cikin murmushin zolaya.
Murmushin yake Rauda ta yi sannan ta furta “Gaskiya kam”. Sai kuwa shima ya café maganar da “Ai ban fada mata ba, sai nan gaba idan komai ya daidaita”’
Zaro ido Haana ta yi, sannan ta shiga jinjina kai sannan ta ce. “Gaskiya Mr.Sameer zan_ baka
shawara, gwara tun wuri ka fada mata, don ban yarda da jira ba. Yanzu sai mutum ya cutu, don ni na gwada na gani. Idan kawai ba za ka iya ba, ni ka fada min da kaina zanje na fada mata ta sani da wuri. Ta fada cikin rawar kai da alamun jimamin nata ciwon. Idan kuma ba ta yarda ba fa?”’. Sameer ya fada da sauri. Haba dai, ai kuwa ba ta isa ba. Mr.Sameer indai ka na tare da ni zan yi duk yadda zan yi ta so ka’’“To idan kuma na ce Miss Haana ce fa’?’Da sauri ta zaro idanuwa waje ta ce. ““Nasan ba ni bace ai, saboda ni abokiyar Mr.Sameer ce, babu wannan maganar a tsakaninmu. Da har ni ina yi  maka zabe a cikin zuciyata na abokiyarka, na jima ina son ka bani wannan damar’
Har cikin ransa ya ji furucin da ta yi masa, bai kuma so hakan ba. Ganin Rauda tana wajen sai ya share kamar maganar ba ta bugi zuciyarsa ba. Sai kawai ya ce Godiya na ke Abokiyata, yanzu ki bani lokaci zan fada miki ita idan komai ya koma normal’’. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sauke wata ajiyar zuciya ta yi, saboda furucinsa ya taba mata zuciya, don ta jima da hango abin da ya ke son furta mata a idanuwansa. Ta na sane ta ke kauce masa gudun kada ya farin cikinta, domin duk wanda ya ce zai shiga rayuwarta da sigar so ba Malam M.J dinta ba, kamar ya yi KoKarin korar duk wani farin cikin ta ne ya, kuma yi niyyar gayyato mata damuwa ne cikin ranta.
Da sauri ta ce “Rauda na ji kin yi shiru ba kya iya cewa komai, ke ba za ki sako baki ba kan Mr.Sameer ya fada mana wa ya ke son mu taya shi yaKin samunta ba?”
Murmushi ta yi sannan tace. “Haana kenan, bai kamata mu takura masa ba, kin dai ji abin da ya ce. Mu bari komai ya daidaita, da kansa zai fada mana. Kuma bana jin dai ko ma wace za ta Kishi”.
“Yawwa Rauda kin fuskance ni kenan sosai, nasan kema za ki yarda da abin da na fada, idan komai ya gyaru komai zai zo cikin sauki”’Karfi da yaji sai da Haana ta sauya salon hirar  suka koma wata hirar. Haka suka wanzu kowa na saka abin da ya ke ransa. Motar su na parking cikin gidan su Haana Ya Abba ya na fitowa da niyyar zai fita. Wani thu da doki Haana da Rauda suka yi. A tare suka fito daga cikin motar suka nufo inda ya ke suka rungume shi cikin tsananin murna.
Cikin sauri ya yi KoKarin raba su da jikinsa, musamman Haana da take ba muharramarsa ba. Cikin murna shima ya ce. “Haka ku ka Kara girma Haana da Rauda?”. Rauda ce ta amsa masa da cewa.
Ya Abba kai ma fa ka Kara girma, sannan ga shi ka yi wani fresh da kai, ga kuma wata Kasumba da ka bari ta yi maka kyau sosai kamar ba Ya Abbanmu ba”. Murmushi ya yi, sannan ya kalli Haana ya ce.
“Wai haka my Princess?”. Haana itama cikin doki ta ce “Eh mana Ya Abba, ka canza mana sannan kuma ka Kara girma da kyau ga kuma wani kwarjini da naga ka yi min kamar ba Ya Abbana ba. Totally you are change my sweet Ya Abba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta na gama fadin haka sai ta sake rungume shi. Har cikin ransa sai da‘ya ji wani iri. Da sauri ya sake raba ta da jikinsa ya ce. “Oh come on Haana_ – ke bakya ganin kin girma ne?, kina abu kamar Haana din da da na sani tun da can. Yanzu ai sai ki bar ma su Nur”.
Turo baki ta yi gaba ta ce. “Ya Abba na yi fishi tunda yanzu ka daina sona da tarairayata kamar da. Wato ka na jin tunda yanzu na girma na daina sonka na bar wa su Nur kenan?”Ba haka nake nufi ba sister, wa ya isa ya rabani da ke ai sai dai mutum. Yanzu dai ki yi hakuri kar haduwarmu ta farko a yau ta sa ki yi fishi da Ya Abba don sai na yi nadamar dawowata”
Kyalkyalewa ta yi da dariya ta ce. “Wasa nake maka. Wane ni da zan yi fishi da kai Ya Abbana, ai har abada”. Duk su ukun suka kwashe da dariya. Shi kuma Sameer ya na gefe ya na kallonsu da yadda suke dokin ganin juna hade da soyayyar juna.
Haka ya dinga ganin Haana ta na Kara birge shi cikin ransa. Sai dai kuma ta yi wani abu da ya taba masa zuciyarsa wato rungume Abba da ta yi. Da Sauri Haana ta juryo tace “Oh Mr.Sameer mun barka tsaye meet my best Brothcr Ya Abba wanda nake fada maka. Ya Abba ga Abokina kuma Yayana Mr.Sameer. lokacin da ba ka nan ya na a matsayin Yayana, amma yanzu da ka dawo zai tashi daga matsayin Yaya, zai koma Abokinsa. Abokin ma fa na biyu tunda kai ne na farko”
Nan ma gaba daya suka sa dariya. Kawai sai suka ga Sameer da Abba sun rungume juna. Haana da Rauda suka Kara cika da mamaki ganin yadda suka gane junansu. Ashe ganinsu ne ya sa Ya Abba ya manta da komai bai ga Sameer ba. Tabbas sun gane juna tun daga sunan da suka ji suna kiran juna kuma daga ji kasan sunan yarinta ne.
Tabbas dole su gane junansu, tun da lokacin suna shekara tara zuwa goma abin ya faru, don haka babu wanda ya manta da sunan kowa. Sai dai kawai kama da ta sauya tunda an girma amma suna ba zai tafi ba. Nan Ya Abba ya cigaba da tambayar ‘yan uwansu domin dama shi kadai ya ware ba shi da wani dan uwa a lokacin, daga shi sai Sameer yayan Rauda sai Aziza sai Farouk wan Rauda da shima ya rasu bayan rasuwar su Aziza. Don haka shi kadai ya yi rayuwarsa sai Kannenshi, shi yasa ba zai iya manta sunan kowa ba suna kansa.
“Ina Fu’ad, Muhammad lawyer, Isma’il, Abdul da Yusif wai duk suna nan don Allah?’’. Haka ya shiga tambayarsa shi kuma ya na amsa masa, Duk sai dadi ya cika su Haana yadda suka ji ya na ta fadar sunan ‘yan uwansu wadanda ba su taba jin sunan nasu ba ma sai a lokacin da suka je suka ga wasu.
Ganin hirar ba za ta Kare ba Haana ta zo ta yi saurin kama hannun Ya Abba ta ce “Ya Abba mu shiga ciki, idan ka biye ta Mr.Sameer ba zai barka ka huta ba” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Au to sorry sister dina, ba za ki gane ba ne shekarun da yawa, yadda na yi missing dinku haka shima nake yin nasu. Na godewa Allah da ya kawo haduwar ZURI’A DAYA waje guda, Allah ya Kara hada kawunan mu. Yau kwana za mu yi muna tunawa da hade da hira mai dadi
Gaba dayansu suka amsa da “Ameen ya Allah”. Nan suka nufi cikin gida bayan su Rauda sun dauki kayansu. Cikin daga murya suka ji an ce mu su.
“Kai ku tsaya nan’. Da sauri suka juya. Haana na ganin Abbanta ta tafi da sauri za ta rungume’‘shi don murnar ganinsa. Ta na nufo shi kuwa ya daga mata hannu ransa a Bace. Ai sai hankalinta ya tashi don tunda ta ke a rayuwarta Abbanta bai taba yi mata haka ba.
A take ta ji wata irin damuwa da tashin hankali sun shigeta, nan take ta fara hawaye Cikin bacin rai ya ce. ‘Kai mara AlkKawari mai fuska biyu, haka mu ka yi da kai, ina dokar da na saka maka, ko ka manta da iyakar da na yi maka da Zuri’ata?. To shikenan tunda ka manta ka yi fatali da abin da na shardanta maka, to yau wa’adin da na baka ya cika.
Minti biyar na baka ka zo ka fitar min daga Estate din nan tun kafin na saka a yi maka korar kare”
Gaba dayansu sai suka razana musamman ma Haana. Da sauri ta zo gaban Abbanta tace “Abba ka yi haKuri na yi maka bayani, Sameer ba wanda za ka kora bane, danka ne kuma kamar mu, shi ma jininka ne don dan gidan dan uwanka ne kawu Aminu’.
Cikin daga murya ya ce “Ke rufe min baki, ni ba ni da wani dan uwa mai wannan sunan, idan ma akwai shi to tuni na manta da shi. Aliyu da Mukhtar su kadai ne ‘yan uwana, bayan kuma su ban yarda a hadani da kowa ba”Za ta yi magana ya yi saurin yi mata wata tsawa ya ce. “Ki bace min da gani ki bani waje”. Ai kuwa ta yi cikin gida da gudu ta na kuka Rauda ma ta biyo bayanta. A take ya mayar da kallonsa ga sameer ya ce. “Ka zo ka bace min daga nan tunda ka yi abin da ranka yake so ba ka da wani abu da za ka ce min tunda ka shigo rigar mutunci ka ha’ince ni.
Duk abin da ka ga na yi maka ina sane, tun farkon ganina da kai na gane ka, na barka ne kawai don ta bangarenka.ne kawai zan samu damar da zan aika saKon da nake so ga maha’intan iyayenka. Babu ni kuma babu su, nasan kaima sun turo ka ne kaima ka zo ka yaudare mu, to ba ka isa ba. Sameer a gabana aka haifeka, banga wani girma ko wayo da za ka yi min har na kasa ganeka ba. Iyayenka mayaudara ne, maha’inta. Sun yi Www.bankinhausanovels.com.ng
mana abin da ba za mu taba mantawa da su ba har abada. Wannan ta sa bana Kaunar duk wani abu da zai fito daga yare su.
Duk mutumin da ya gujeka a matsayinsa na jininka, sannan kuma daga baya ya dawo ya ce wai yana sonka to Karya yake akwai wani abu a ransa. Sameer kai ba wanda zan zauna na bata lokacina akansa bane saboda haka na baka UMARNI ka zo ka fice min daga gida. Yaudarar da ka yi min ta nuna cewa koya maka aka yi, don haka ban yarda ka Kara min ko minti guda ba cikin minti biyar din nan. Kada na fito naga Keyarka a nan. Mustpha wuce mu je” Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsananin mamaki ne ya bayyana a fuskar Sameer, ko kadan bai taba tunanin haka ba daga wajen kawun nasa. Tunda ya ke bai taba ganin tsana a fuskar wani mutum ba irin wacce ya gani yau da aka nuna masa. Sai dai ko kadan ransa bai baci ba, domin duk abin’ da ya yi masa bai ga laifinsa ba, don hakan ya nuna har yanzu ya na cikin fishin. Kuma duk wanda Zur’arsa za su yi masa haka dole ne ya yi fiye ma da hakan.
A ta ke shima ya ji ba zai iya zama a cikin Estate din ba. Kai tsaye kawai ya juya zuwa Kaduna domin ya fadawa iyayensa su san abin da za su yi su kori wannan bakar gabar domin ya na ganin abin ya fi Karfinsa.
******
Kwancce ta ke akan gadonta ta yi ruf da ciki sai kuka ta ke yi kamar hawayenta za su Kare. Tun

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Suna cikin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *