ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 18 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 18 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Eh mana. Rauda ta mayar mata cikin fadada
murmushin fuskarta. Gaba daya suka sanya dariya.
Ya Abba ne ya ce
To ni bari na wuce tunda na ga mai Ciwon ta
fara jin sauki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nan Haana ta ce. “Kai Ya Abba, ya za ka tafi,
ai da ka tsaya mun yi hirar da kai don sai ta fi dadi
ma
Kar ki damu, ina da aiki ne, ba don haka ba sai
na zauna mu yi ta hira har sai kun ce da ni ya 1sa
haka na tashi na kara gaba
Sai ta yi dariya ta ce. “Shikenan Ya Abba sai ka
dawo Ta mai daga masa hannu alamar
bye bye. Sauri ya yi ya bar dakin. Don shi kadai ya
san abin da yake ji a zuciyarsa. Haka ya dinga jin
wata irin damuwa tare da wani irin shauki na so da
kaunarta da ya Ji suna ratsa masa zuciya. Ya dinga

jin duniyar na yi masa yawo, Haka ya dinga jin
kamar ya rasa komai da kowa ne a duniyar tasa.
Tabbas rashin Haana a cikin rayuwarsa ba
Karamin gibi aka yiwa rayuwarsa ba, dole haka zai
hakura ya barta ta auri Sameer ba wai don ya so ba,
sai dai kawai don ta sami abin da ta ke so cikin
rayuwarta, ta kuma karasa rayuwar cikin farin ciki.
Ta cigaba da murmushinta don shi ne abin da ya ke
Son gani a fuskarta, bai son ya ga ta sh1ga damuwa
ko wani tashin hankali cikin rayuwarta, don haka
Ya sadaukar da nasa farin cikin ita ta samu.
Ya na fita Haana ta bi shi da kallo har sai da ya
fice gaba daya sannan ta juyo ta dubi Rauda.
Rauda ina son life style din Ya Abba, naso na
samu mijin aure irinsa, da ana iya canza halayya da
na canza na Mr. Sameer ta koma irin ta Ya Abba,
saboda komai nasa cikin tsari yake yinsa ba shi da
hayaniya ko kadan, sabanin Mr. Sameer da kullum
sai ya isheka da surutu ko ba ka yi niyyar magana
ba sai ya sanya ka. Www.bankinhausanovels.com.ng
Amma shi Ya Abba kuwa maganar ma wata
Rana sai ka nema za ka samu a wajensa, gaskiya
matarsa ta yi sa ar miji. Rauda ni ban san me ya sa
Ya Abba ya ki nuna min cewa ya na Sona a lokacin
da nake cikin damuwar rashin Malam M.J. na yi
tunanin zai ce ya na sona.


Amma sai naga kulawar da ya ke bani sam ba
Irin ta so ba ce, kawai dai yana so ya ga ina farin
Ciki ne. rauda ba don Ya Abba ya sha min fada
akan cewa kada na sake na furtawa namiji ina son
shi indai ba shi ya furta da bakinsa ya na s0 na ba,
da tuni na fito fili na fadawa Ya Abba ina son shi.
Rauda yau ina fallasa miki abin da ya ke raina
ba tun yau ba, babu wanda na fadawa sai yau. Ba
tun yau nake kasa kunne na ji Ya Abba ya ce ya na
Sona ba, amma shiru har Malam M. ya shigo
rayuwata ya kuma tafi amma banji ya ce komai ba,
har kuma ga shi yanzu na tsayar da Mr. Sameer
amma banji ya ce komai ba.
Rauda ban yi masa bane, ko ni ce ba na cikin
kalar matan da ya ke so?. Rauda da tun tuni Ya
Abba ya fada min ya na sona, da ban shiga halın da
na shiga ba, da ko Malam M’J bai zo ya shiga
rayuwata ba balle har ya yi min abin da ya yi min a
baya,, da kawai sai na rungumi soyayyar Ya
Abbana ba ruwana da kowa
Kan bala’i! rauda ta fada cikin ranta. Haana da
ma kema kina son Ya Abba amma ba ki taba nuna
masa ba har ya ke dauka a zuciyarsa kin kasa gane
abin da ya ke nufi. Sai dai kuma ba ki da laifi,
kamar yadda ya koyar da ke ba ke ce mai laifi ba,
shi ne mai laifin da bai furta miki ya na sonki ba ke
kuma ya hanaki ki nuna kina son shi
Tabbas ba don zan batawa Ya Abba rai ba da
na fito na fada miki mawuyacin halin da ya ke ciki
a kanki, illar daya ce, na riga da na yi masa wannan
alkawarin ba don haka ba da na fada miki”.
Amma kuma a zahiri sai ta yi murmushi ta ce.
Sister kin san Ya Abba shi haka ya ke babu mai
gane irin kalar matar da ya ke so, sai dai mu taya
shi da addu’a. ke kuma Allah ya sa Ya Sameer ya
sauya halayyarsa ta koma irin ta Ya Abba.
Amma shi din ma sai naga kamar life style
dinsa ta yi, zai iya baki duk farin cikin da mai irin
halayyar Ya Abba zai baki, don naga shi din ma ba
daga nan ba”. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kayya Rauda, Ya Abba irinsa ba su da yawa.
Ba don na dauki abin da ya koyar da ni ba, da tuni
na furta masa so. Matsalar tun da ki ka ga ya fada
min haka to ya tsani halayyar, kuma duk yadda
mukee da shi idan na yi hakan zai iya tsanata,
kuwa da na yi abin da Ya Abba zai tsane ni gara na
bar abin har na mutu.
Mutum biyu naso a rayuwata, na sO kuma na
rayu da daya daga cikinsu, Ya Abba da Malam
M.J, tunda kuwa ban samu ba duk wanda ki ka ga
na aura zan zauna da shi ne kawai don na rasa
wadannan
Nan Rauda ta katse ta da cewa. “Sister ki daina
fadar irin wadannan maganganun, yanzu idan Ya
Sameer ya ji ba zai ji dadi ba”.
Sai dai idan ke za ki fada masa”.
“Ni kuma?”. Rauda ta fada cikin zaro idanuwa.
Eh mana, da wa mu ka yi zancen da za ki ce
haka, don haka ki bar wannan zancen amana, ko
Ya Abba ba na so ya sani. Yarda da ke ta sa na
bayyana miki dadadden sirrin da ke raina tsawon
shekaru kuma ban taba fadawa kowa ba sai ke a
yanzu bare wani ya fahimci ZUCIYA ta da RUHI
na kan abin da suke ciki’
Murmushi Rauda ta yi ta ce.Babu mai jin
wannan maganar, ZUCIYA ta nima kadai da RUHI
na na ajiyewa amanarsu HAR ABADA babu mai
ji Yawwa Aminiyata, na fuskanci gaskiyarki ta
na aiki, ga shi gani na ya sa ciwon ki ya tafi, kinga
yanzu dole na tuhumeki. Me ya sa tun ranar da na
fada miki ina son Mr. Sameer ba ki sake dawowa
mun sake maganar ba, k0 zabina bai miki ba?.
Turo baki gaba tayi ta ce. yanzu ciwon kai zai
dawo, ba Ya Abba ya ce banda tuhuma ba
Au ho, da wannan logic din ku ka biyo?, to ba
ki isa ba sai kin fada min tunda ina nan ba zan bari
CIWon ya tashi ba. Dariya suka shiga yi duka su
biyun, nan kuma Rauda ta baje a kan gado ta na
fadin CIWOnta ya tasht. Haana kuwa cewa ta ke
Wallahi ba ki isa ba sai kin tashi Www.bankinhausanovels.com.ng
Yau kwana uku kenan, Haana ta shiga damuwa
da yawa ganin yadda Ya Abba ya daina walwala,
kuma ko da yaushe fuskarsa dauke da damuwa, ga
shi ya rage shiga cikin jama’a, ko ita bai fiye zuwa
inda ta ke ba. Haka ta dinga jin damuwarsa ta na
hana ta sukuni da walwala ita ma.
Yau ta yanke shawarar za ta je har dakinsa da
wannan maganar don sam ya dauke kafarsa da
zaman falo.
Knocking ta y1 kusan sau uku, sai daga baya ya
ba ta umarnin shiga, ko kadan bai kawo wa ransa
cewa ita ce za ta shig0 ba. Ya na ganinta ya yi
saurin korar damuwar da take shimfide a fuskarsa.
Sallama ta yi, ya amsa mata, sannan ya yi mata
Girgiza
nuni da resting chair da ke dakin nasa. Girgiza
masa kai ta yi Sannan ta ce Mu je baranda muyi
maganar Bai musa mata ba, ganin ma ta juya
shima sai ya bita.
Zaune suke kan wasu kujeru ma su laushi da
aka tanade su don hutawa can back yard na gidan.
Cira kai ta yi ta ce.
Ya Abba don allah ina son ka fada min me ya
ke damunka kwana biyu? Ko cikin gidan nan ka
sauya ko kadan na daina ganin walwala a tare da
kai, ka kaurace mana, ko hira da muke da kai ka
daina. Wai me ya ke damunka?, bai kamata kana
boye damuwarka kai kadai ba. Haba Ya Abba, da
ni ce sai ka sani a gaba dole sai ka sanyani a gaba
na fada maka damuwata sannan hankalin ka zai
kwanta, to kuwa nima yau sai ka fada min ko numa
na yi fishi da kai”.
Gaskiya ne, ina cikin damuwa babba ma
kuwa, saboda Abba ne da Granny suke fishi da ni
kan UMARNI da suka ba ni ni kuma na kawo muSu uzirina, akwai wacce suka ce za Su aura min na
ki yarda
Ya Abba auren dole za su yi maka, da wa za
Su yi maka auren dolen, kai kuma mai yasa ba ka
Son zabin na su? tunda kai ka ki fitowa da wacce
ka ke so ai dole su yi maka haka.
Girgiza kai ya yi sannan ya ce. Haana ba
auren dole za su yi min ba. wacce za su bani din ce
ba ta sani ba, ni kuma bana son su takura ta wajen
yi mata dole tunda ba ta shirya aurena ba.
Wace ce ita, a ina ta ke, karya ta ke ta ce ba
ta son Ya Abbana. Ka fada min a ina ta ke, ni zanje
da kaina na bata order, don sai ta so ka, sannan zan
dawo na fada maka cewa ta amince. Ya Abba
saboda ita ne na rasa ganin murmushi da walwala a
fuskar ka?. Ko ma wacece ba ta 1sa ta sanya Ya
Abbana damuwa ba, wace ita’?.
Nan da nan sai ga tsanar yarinyar ta fito kan
fuskarta. Sai kuwa ta dora da “Please Ya Abba, ka
yi shiru, ka fada min ko wacece kar ka bari na fara jin
tsanar wacce ka ke so Cikin raina
“Haana ki yi hakuri ki kwantar da hankalin ki,
kar ki bari wani ya ji. Ban da Abba da Granny ba
wanda ya santa, ko ke idan na fada miki ba saninta
za ki yi ba. Ke dai ki tayani da addu’a su daina
fishi da ni, fishinsu ya fi daga min hankali a yanzu
da nake cikin wannan halin .
To shikenan bari na je na ba su hakuri, nasan
za su sauraren1 tunda nasan ba sa s0 nima na shiga damuwa. Ta na gama fadin hakan ta mike da sauri ta baar wajen. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da sauri ya yi saurin janyota gaba daya ta yo0
jikinsa, haka suka hada jiki sun yi kusa da kusa
SOsai don kowannen su ya na jin fitar num fashin
dan uwansa. Lokacın da hakan ya faru kuwa karat
a idon sameer daga nesa ya hango su, nan ya jl
wani bakin kishi ya kama shi kamar zuciyarsa zata
fito, Wajen da bai zo ba kenan ya juya ya koma
cikin KUNAR ZUCI.
Kowannensu cikin ido ya ke kallon dan
uwansa, nan ta ke Haana ta ji wani irin shaukin so
ya darsu cikin zuCIyarta. Sauri ya yi ya raba ta da
Jikinsa ya na mai fadin Sorry
Kasa ta yi da kanta, haka kawai ta ji wata irin
kunyarsa da wata irin kaunarsa ta kama ta, nan ta
dinga shakar kamshin turarensa a hancinta. Haka ta dabarce. Ganin ta shiga Gilty ya yi saurin cewa.
Hanna kar ki jewa da Abba ko Granny da
wannan maganar bare har ki ba su hakuri su daina
fishi da ni. plecase promise me, za ki bar wannan
maganar ta tsaya a tsakani na dake kawai kamar
yadda ba sa so kowa ya sani. Ina so ki rike min
Sirrina, ba don kin nemi na fada miki damuwata ba
da ba zan taba barin wani ya ji abin da yake
damuna ba.
Amma ni ganin kin damu ya sanya na fada
miki don kar ki ce ban fada miki abin da ya ke
damuna ba, amma ki barni da su da kan su za su
fahimci me nake nufi. Ke dai kawai ki tayani da
addu’a su fahimci abin da nake nufi su daina fishi
da ni.Shikenan Ya Abba, zanje na yi duk abin da ka
Ce na yi matukar hakan zai sanya ka farin ciki,
addu’a kuwa dama kullum cikinta nake Allah ya sa
ka samu nasara cikin komai naka
Murmushi ya yi sannan ya ce. Yawwa my
Sweet sIster haka nake son na ji kin ce. Na gode
Murmushi ita ma ta yi ganin yau ta ga nasa
murmushin. Ko kadan ba ta son ta ga fuskarsa ta
canza daga yanayin farin ciki 1tama sai nan take ta
koma hakan. Wannan duk koyarwarsa tun ta na
yar karama ya sabar mata da hakan.
Sun jima suna hira, can ya hangi Abba zai fita
ya yi saurin buya don kar ya ganshi. Haka Haana ta
shiga tsokanarsa wai Babba da shi ya na buya
kamar wani Nur idan ya yi wa Amm1 laifi za ta
bigeshi. Ganin yadda ta ke dariyar sai kawai ya
buge da kallonta yana murmushi ya kara jin wani
sonta ya na kara shigarsa.
AbbA Ransa a bace ya shiga gida, duk yadda ya yi ya
boye damuwarsa amma abin ya faskara, babu abin
da idanunsa suke nuna masa sai Haana da Ya Abba
da yadda suke tare da juna suna shakar numfashin
juna. Shin me hakan ya ke nufi, karya dama Haana
take masa ba son shi ta ke ba yaudararsa ta ke
shirin y1?, idan ba soyayya suke da Abba ba yaushe zai yi mata irin wannan rikon ba tare da ta hana shi
ba. Baya mantawa fa by mistake fa ya rike mata
hannu amma ta hau shi da fada, amma da yake
Abba ne ya ga abin da ya faru da idonsa kuma ba ta
hana shi ba.
Nan ya kudiri aniyar zai nuna mata bacin ransa
SOsai, amma tunawa da ya yI cewa maganr da ya
Jewa iyayensa ba ta karbu ba. Idan kuwa hakane
daga shi har Abban ba mai nasarar samunta a
matsayin matar aure bare kuma M.J da ya ke
tunanin tasa ce shi kadai.
Zaune ya ke a daki shi kadai ya rasa yadda zai
Bullowa wannan lamarin, ya kulla wannan ya
kwance, ga uwa uba kuma wata damuwa da ta cika
masa ransa wato maganar Rauda, amma tunaninsa
gaba daya yadda zai mallaki Raihanatu yanzu ya
ke. ya tabbatar idan Haana ta fara samuwa Rauda
ba za ta yi masa wuya ba. Amma kuma idan ya
tuna sharadin yayensa duk sai ya rushe masa
tunaninsa ya kuma rasa mafita, ta ko ina ba shi da
wani abu da zai ce shi ne madogararsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yadda ya ke ji a zuciyarsa ta kokarin hana shi
wannan auren abin ya yi masa yawa. Nan wata
dabara ta fado masa, ya yanke tunkarar Kakarsa da
matsalar da ya ke ciki wacce yasan ita kadai ce za
ta sanya mahaifinsa dole.
Abba ne da Granny a dakinta, wannan karon
ma sun sake kiran Abba a karo na biyu. Nan Abba
ya ce.
Abba yau ne ranar da muka baka don ka je ka
yi tunani mu ji ko har yanzu kana kan bakan ka
tunda muka rabu. Idan haka ne kuwa yanzu ne zan
yi fishi da kai na sosai
Ya Abba ya muskuta ya ce. Abba don Allah
hakurin dai nake kara baka, wallahi ba kin abin da
ku ka ce nake yi ba, Amminka ba ni ta ke so ba, ta
na da wanda ta ke so, nasan halin da ta ke ciki don
ba ta boye min komai na damuwarta, yanzu idan ta
Ji ni za a aura mata ranta ba zai so ba don za
ta dauke ni mai son kansa da kuma rashin tausaya
mata kan halin da ta ke ciki. Nasan ba za ta ki abin
da ku ka sanyata ba, sai dai za’a tauye mata
hakkinta na aura mata wanda bashi ta ke soba. Ni kuma Www.bankinhausanovels.com.ng
burina naga ta samu farin ciki dauwamamme a
cikin rayuwarta, don Allah Abba ku fahimci
manufata, ba wai kawai son raina ne na ki
amincewa da abin da ku ke so ba sai dai don ni din
ni kadai ne abokin shawarar Amminka, ba don
sanin abin da ta ke so ba da tuni na amince kun
yanke hukuncin komai. Don haka Abba ina
rokonka da ka bar Amminka ta auri wanda ta ke sO,
ni kuma ka nemo min duk wacce ka ga ta dace da
ni don kasan cewar ba ni da wani zabi da ya wuce

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 16 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  murmushi ta …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *