ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 14 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Suna cikin haka sai ga Granny nan da Ya Abba
suka shigo dakin a rude suna tambayar me ke
damunta. Ganin yadda kowa ya rude a kan jin
rashin lafiyarta duk sai ta ji tausayin su ya kama ta
a ranta ta ce da za ku ji dalilin ciwon nawa da dama
daga cikinku babu wanda ba zai ji haushi na ba,
malam M.J me yasa ka yi min haka? Me yasa ka
kasa gane cewar nima tuni na kamu da son ka
kamar yadda ka kamu da son ‘yar uwarka ba ka yi
wa ZUCIYA DA RUHI na adalci. (Sunan littafin
Sa’adatu Waziri mai fitowa nan gaba idan Mai
duka ya yarda).
Tana jin likitan da ya zo duba ta yana fadawa
Abba cewa damuwa ce ta yi mata yawa ga kuma
wata damuwa da take son jefa kanta a ciki. Haba
jin haka Abba ya shiga jero mata tambayoyin cewa
me yake damunta da za ta boye ta ki gaya musu?
Ba ta samu damar ba shi amsa ba likitan ya ce,
damuwar zai iya yiwuwa a kan karatu ne.

Sai lokacin Abba ya dan ji sanyi don ya san
halin diyarsa da naci a kan karatu mutukar ta
kuduri wani abu sai ta ga ta cimma burinta, sannan
za ta ajiye damuwar ta.
Kwana biyu ta yi tana jinyar zuciyarta ga halin
da Malam M.J ya jefa ta babu wanda ta fadawa
halin da take ciki illa Zahra, don ko Rauda ba ta
fadawa ba. Zahra ta cika da mamakin jin furucin da
ta ji wai Malam M.J ya yi nan ta shiga juya abin a
ranta tare da dorawa maza raddin rashin alkawari
duk da kuwa ta san ba furtawa ya yi cewa yana
sonta ba, amma ai duk wanda ya ga yadda suke ya
san akwai kauna da shakuwar da za ta nuna cewa
su masoyan juna ne tunda ba sa iya boye emoton
dinsu ga kowa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsaye yake bakin kofar dakinta yana sauraren
duk abin da take fadawa Zahra, ransa ya yi mugun
dadi jin cewa M.J ya yaudari kanwarsa, wanda


dama shi ne matsala din shi. Yau kuma ga shi da
kunnensa ya ji Haana na kuka na fadawa kawarta
cewa Malam M.J ya yaudare ta ba za kuma ta taba
yafe masa ba yadda ya sa ta yi ta bata time tana
jinran dawowarsa cikin rayuwarta.
Jin sautin kukanta yasa ya ji ba zai iya jurewa
ba yasa ya juya zuwa dakinsa. Murna zai yi ko taya
Haana dinsa damuwa domin ganinta cikin damuwa
yasa ya rasa dukkan nasa sukunin, tabbas rashin
MJ a rayuwar Haana dinsa shi ne farin cikinsa
ZUCIYA DA RUHI dinsa mutukar ta same shi, shi
kuma lokacin ne zai shiga tashin hankali mara
misaltuwa a rayuwarsa, saboda yadda yake jin so
da kaunarta ba zai iya barin ta auri wani ba shi ba
Kasa nutsuwa yayI dole don saboda tunawa da
ya yi Haana dinsa tana cikin damuwa tana kuma
bukatar rarrashi da wani a kusa da ita, don ya
mantar da ita ko ya kwantar da hankalinta. Da sauri
ya bar dakinsa ya koma nata.
Zaune take jingine kan gado tana ganinsa tayi
sauri ta share hawayen da yake zubo mata ta yi
saurin kirkiro murmushin yaki, ta ce, “Abba yau na
yi fushi ba ka zo ba tun dazu nake sa ran ganin ka
ban gan ka ba wai ina ka je ne?
Dazu na zo kina barci na fita, don bana son
tashin ki daga barci, ina son kuma ki fada min me
ya sa ki kuka da ki ka gan ni ki ke son boyewa?
Murmushi ta kirkiro ta ce, Ba kuka nake ba
fa.”Haana ba kya yin karya ba kuma na son ki yi
min ita yanzu oya tell dime the truth ina kallon
fuskarki akwai damuwa kuma kina son boye min
ita maza yanzu nake son ji. Www.bankinhausanovels.com.ng
Kasa daurewa ta yi sai da hawayen ya zubo ta
ce, “Please Ya Abba ka manta ka bari tunda nima
na riga na bari, zan kuma manta.
Kai tsaye cikin dakewa ya ce, Me zan manta,
me kuma zan bari, please kada ki boye min
damuwar da nake gani a fuskarki ki fito ki fada
min ko zan iya kawo miki mafita tunda yanzu na
fara ganin canji da dama a gare ki.
Da sauri ta ce, “Ya Abba wane canji ka soma
gani a tare da ni please ka fada mini.”
Boye damuwarki mana ba kya so na sani,
sabanin da da ba kya iya boye min komai ko kina
ganin yanzu kin girma za ki iya samawa kanki
dukkan mafita a cikin rayuwarki?
Girgiza kai ta yi ta ce, “Ba haka nake nufi ba
Ya Abba har karshen rayuwata ba ni da wanda zan
nemi shawara gunsa sama da kai. 99 Tana yi tana
kuka.
Girgiza kai ya yi ya ce, “Ban son ganin wannan
kukan ki tsayar da hawayen nan haka mu yi
magana.
Ya Abba am sorry ka jima kana fada min
magana a kan Malam M.J ba na nuna maka ba na
dauka, sai dai naji ka kawai na takaita maka dai
yanzu duba wayar nan ka karanta ka ji abin da ya
ce mini
Ba sai na gani ba Haana na ga duk amsar
komai a fuskarki tun shekaran jiya na kuma ji
komai daga bakin ki ki na fadawa Zahra. Kar ki
damu haka kaddara take dama ba lallai ne abin da
ka ke so shi ka ke samu ba. Haaana na san kina son
M.J shi kuma yana son wata hasali ma shi bai fada
miki yana son ki ba, forget about Malam M.J kina
zaune Allah zai kawo miki wanda ya fi shi komai.
Ki yi min alkawarin za ki cire damuwarsa da
yadda babu wanda zai gane kina cikin damuwa duk
da kuwa ba abu ne mai sauki cire abin da ka ke so
lokaci guda ba, amma idan har ki ka yi kokarin
mantawa da shi ni kuma zan ci gaba da ba ki
kulawa da mantar da ke dukkan damuwarki sai na
ga ba kya cikin damuwa da sannu za ki ga Allah ya
kawo miki wani cikin rayuwarki da zai sa sam ki
daina tuna M.J. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da zan ga M.J da na hukunta shi da saki zubar
hawayen nan da ya yi matukar ina raye na hadu da
shi sai na dauki wannan fansar, don bai san yadda
nake ji da Haana dina ba, Abba da Ammi ne kadai
za su iya sa ta damuwa na bar Su ba wani ba.
Murmushi ta yi har sai da hakoranta suka
bayyana, sannan ta ce Na gode Ya Abbana kuma
zan yi duk yadda ka ce sai dai ina son ka yi min
uzuri a hankali zan yi kokarin mantawa da shi.
Sannan ina son ko da ka hadu da shi kada ka
hukunta shi laifina ne ba nashi ba, da tun farko na
yarda da shawararka da ka ba ni ba, da bai kai ni ga
shiga wannan halin ba.
Zan yi kokarin cusa tsanarsa a zuciyata haka
kadai zan yi yasa na manta da shi. Yanzu kuma a
gaban ka zan goge number dinsa, domin kada ina
ganin ta ina tunawa da shi. Tana gama fadin haka
ta janyO wayar ta goge lambar tasa.
A jiyar zuciya Ya Abba ya yi cikin ransa ya
shiga murna da godewa Allah da haka ta faru, nan
ya shiga tunanin ta wacce hanya zai bi don ya
fallasa asirin da yake zuciyarsa ya kasa gane dalilin
da ya hana shi fitowa fili ya fada mata abin da ke
Zuciyarsa, ga shi kuma an zo kan gabar da zai fada
mata din.
Suna cikin wannan halin Rauda ta zo ta same
su a nan ta samu labarin abin da yake wakana
Haana din ta ba ta hakuri da ta boye mata ba ta
fada mata ba.
Ta cika da mamamki jin abin da ya faru nan ta
dinga tuno haduwarsu a CountryMall yadda ta ga
tsananin shauki da tsantsar kaunar da Malam M.J
yake nunawa ‘yar uwarta shi ne zai turo mata
wannan sakon haka kawai ta dinga juya maganar,
to ama babu abin mamaki tunda namiji ne shi.
Can kuma kasan zuciyarta fargaba ta dinga
shiga ka da yanzu kuma ta ce za ta komawa
Sameer tunda ga abin da ya faru da ita da Malam
M.J dinta. Haka dai ta yi kokarin boye wannan
damuwar a cikin ranta. Suka hadu ita da Ya Abba
suna kwantar mata da hankali da ba ta baki a kan ta
daure kada ta bar damuwa cikin ranta. A wannan
Lokacin Haana ta j1 dadi, don ta soma sakewa da
kuncin da take yi wannan lokacin. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yau kwanaki hudu kenan da faruwar al’amarin
Mr. Sameer ne zaune cikin dakinsa ya gama
shirinsa tsaf, ya dawo jikin mirrow din da ke
manne jikin bangon dakinsa, ya kalli kansa cikin
madubin ya yi murmushi ya ce, “Haana lokaCi ya
yi yanZu da zan je gare ki, tunda na cika aikina
Muhammad ka yi ganganci da ka ke so ka ce za ka
hana ni son Haana, na raba ka da ita zan yi kokarin
Gama sa ta manta ka ta kuma tsane ka.
Haana ki yihakuri jefa ki cikin wannan
damuwar da na yi hakan da na yi ita ce kadai da
zan samu na raba ki da M.J dinki domin na same ki
cikin ruwan sanyi ba ni da matsala a yanzu zan yi
Kokarin duk yadda zan yi ki so ni fiye da yadda ki
ke son M.J. Abba ba na ta tashi tunda ke ba ki gane
yana son ki ba, shi kuma ya ki ya fada miki tun
kafin ya fada miki ni kuma zan sake bayyana
miki.”
Yadda al’amarin yake tun ranar da Sameer ya
karbi wayar Haana suna tare da Rauda da zummar
zai duba wayar a nan ya yi bincike a wayarta
kamar yadda ya yi zargin zai ga sunan Malam M.J
haka ya gani ya yi sauri ya canza sunan ya maida
lambobi yadda babu mai gane wa ya saka tasa
lambar da ya sai sabon layi ya mayar sunan M.J a
kai.
Ya kudiri niyar idan ya gabatar da kansa a
masoyinta ta ki amincewa da shi to ta nan ne zai
turo sako a matsayin M.J ne yadda za ta ji ta tsane
shi ta daina son shi, ta daure su so juna, shi kuma
M.J din ya sanya shi a blak list yadda duk yadda
Zaiyi ba zai same ta ba. Kamar yadda ya zarga hakan
ne kuwa ya faru, shi ne dalilin da ya sa ya turo
mata wannan sakon a matsayin shi ne ya turo mata,
sarai ya samu labarin rashin lafiyarta, amma sai ya
nuna sam shi bai ji ba ma.
Tun ranar da suka rabu bai sake bi ta kanta ba
bare har ya je inda take, Rauda har waya ta yi masa
ta ce ga ta ba ta da lafiya ko bai ji ba? Ya ce mata
yana busy ne idan ya gama zai kira ta.
Zaune ya iske duk ‘yan gidan a falo suna ta hira
can ya hangı Haana kwance kan three sitar yana
ganin ta ya wani sauya fuska kamar ma bai san
wani abu ya faru da ita ba.
Kai tsaye gurin Granny ya nufa ya çe, “Hajiya
Kaka ya girma ya kuma kwarin kashi?
Murmushi ta yi ta ce, Kwarin kashi sai godiya
yana nan yana fin naka, wai ina ka shiga ne kwana
biyu ban gan ka gurin dubiyar mis mis din taka ba,
ko ba ka da labarin ba ta jin dadi ne? Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba Mr. Sameer ba hatta Haana da take gefe
guda sai da abin ya ba ta dariya, shi ma dariyar ya
yi daidai lokacin da Ammi suka shigo falon ita da
Ya Abba da alamun unguwa suka je. Sai da ya
gaida Ammi, sannan ya ba wa Granny amsa da
cewa.
Ni da farko ban sani ba kullum idan na fita tun
safe sai dare nake dawowa dazu ne Rauda take
fada min shi ne yau na ce bari na zo mu gaisa da ku
na kuma duba ta. Granny ai ba ta so na sani ba tana
da lamba ta ba me yasa ba ta kira ta fada min ba?
To dai maganar korafi ta kare tunda yar
uwarta ta fada maka kuma ga shi ka zo.
Haka ne Granny ya jikin nata kuwa?
Su da Ammi suka amsa da sauki. Can ya hangi
Abba ko tsayawa bai yi sun gaisa ba ya nufi
gurinta. Murmushi ya yi a boye shi ma ya je ya
zauna kusa da kujerar da take daidai kafarta da
yake Abba na zaune a kusa da kanta. Bayan sun
gaisa ya ce, “Abba ya mai jiki, kai ma ba ka kira ka
fada min ba duk kai da ita kunyi laifi.”
Wannan ba zai zama laifi ba sai da a kira shi
ajizanci irin na dan adam, ita ke ciwon ni kuma
uzurarrika sun y1 min yawa, ban sani ba ko ba ka
da masaniya tunda kana shigowa gidan, ka ga bai
zama lallai na san cewa ba ka sani ba.
Gaskiya ne Miss Haana ya jikin naki?
“Da sauki.”
Tunda Abba yake jin yana kiranta Miss Haana
bai taba jin haushin hakan ba sai yau don cikin
salon da ya kira sunanta ya yi ne da biyu, don ya
bata masa rai, kuma kwarai ya yi nasarar yin haka.
Ke kin sha maganin ki kuwa na fa san halin
ki?
Cira kai ta yi ta dube shi jin yadda ya yi
maganar kamar cikin fada, ta san yana ba ta
kulawa sosai da nuna damuwa, ta dube shi ta ga
kamar ransa a bace, sai ta ce,Yanzu zan sha ga
shi nan gabana.
Bai ce da ita komai ba ya dauka ya fito da su
daga cikin kwanson su ya ce, “Oya na ga idan ba a
gabana ba ne ba kya shan magani tunda kina
daukar kan ki kamar Nur ko.
Bai yi wata-wata ba ya daukO ruwa ya mika
mata ya ce ta sha, nan ta soma yi masa salon
shagabarta. Wani irin kishi ne ya kama Mr. Sameer
ganin yadda Ya Abba yake son nuna masa ,,,,,,
MIss Haana zan koma ina da uzuri. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da wuri haka Mr. Sameer.
“No, kar ki damu we should meet later.
Bai jira cewarta ba ya juya abin sa. Ta cika da
mamakI wato mutumin nan fushi yake da ni don na
ga tunda ya zo bai wani saki fuska ba. Abin da ta
fada a ranta kenan.
Ran Ya Abba ya yi fari tas domin ya yi abin da
yake masa dama shi ma ya iya yana raga masa ne,
don kawai zaman lafiya. To amma yanzu bai jin zai
dinga raga masa. Haana ta dube shi ta ga yana
murmushi ita ma sai ta yi murmushin duk da ba ta
san na me ye ba.
Ya Abba yana jin dadin yadda yake ganin
rashin jituwar Haana da Sameer ya yi farin
ciki da ya fuskanci ba sa shiri haka ya dinga Jin
sam ba shi da damuwa.
Bayan sati daya da faruwar haka da yamma Mr.
Sameer ya dawo daga motsa jiki can ya hangi
Haana da kaninta Nur sun nufi gidansu Hajiya
Babba da sauri ya karkata kan motarsa ya ja ya sha
gabanta. Tana ganinsa ta dan saki murmushi shi ma
ganin sakin fuskarta shi ma ya saki.
Mr. Sameer sarkin san motsa jiki an dawo
kenan na fuskanta. Ta karasa fada cikin murmushi
hannunta rike da na Nur.
Murmushin ya sake yi ya ce, To ya ba zan yi
tsadar gani ba uwar gidan M.J tunda an ce ba a yi
da ni ai sai na nufi inda ake yi da ni ka san inda ake
Son ka nan ka ke zuwa.
MISS Haana ki cire komai a ranki mu gyara
alakarmu ta ‘yan uwan juna na hakura da ke ba wai
don ba na son ki ba, don kawai kina da wanda ki ke
so. Na yi tunani idan na biyewa zuciyata zan ma
daina rabar inda ki ke, ina miki fatan zaman lafiya
da shi idan na bata miki to ki yafe ni.
Take yanayin ta ya sauya ta ji wani irin
tausayinsa ya kama ta abin ka da mace mai rauni.
Jin furucinsa sai ta ji kamar ya dauki mashi ya caka
mata a kahon zuci, ko kadan ba ta son jin wani ya
ambaci sunan M.J ta tsani jin sunansa bare a tsaya
ana ba ta labarinsa. Www.bankinhausanovels.com.ng
A fakaice yake kallonta don ganin yanayin da
ta shiga ta yi kamar za ta ce wani abu sai ta dake
kawai ta ce, “Mr. Ba wai kin ka nake ba, ka
fuskanci dalilin da na fada maka a baya.
Ai na gamsu tuntuni shi yasa nima na fadi
haka ganin tuni M.J ya gama yin tasiri a zuciyarki
ba kya ganin kowa sai shi.
Wannan karon kasa boye damuwarta ta yi ta ce,
Please Mr. Sameer ba na son ka sake yi min
maganar M.J bana son jin ko kadan.”
“Kan wanne dalili?
Ba sai ka ji dalili ba, kamar yadda na ce ka
manta please ka manta ba na son kowa yana kawo
min batun sa ko saka shi cikin al’amarin na ina son
1n manta da shi saboda na samu nutsuwa.
Babu damuwa zan yi duk abin da ki ka ce
mutukar hakan zai saki farin ciki, a yanzu a shirye
nake da na baki dukkan wata gudunmawa da za ta
saki fari ciki. Ni Sameer a shirye nake ki ba ni
kambun zama babban abokinki amininki domin

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Suna cikin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *