ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 13 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sarai Ya Abba ya fuskanci ba ta ji dadin abin
da ya yi mata ba, amma shi cikin ransa ya ji dadin
haka, don ya yi hakan ne don daya daga cikinsu ya
Ji haushi, sai ya ga kamar damuwar tata ta fi ta
Sameer. Nan da nan ji ya yi damuwa tana ziyartar
zuciyarsa don kO kadan bai san ganın Haana dinsa
cikin damuwa ko da kuwa wacce iri ce. Tabbas da
ya san za ta shiga wannan damuwar da bai yarda
sun tsaya ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya Abba ya yi saurin taka motarsa don su yi
sauri barin gurin. Shiru motar ta yi babu wanda ya
ce kanzal can dai Rauda ta ce,Sister wai mai ya
faru da ku ke da Ya Sameer.
Me ki ka gani kin san halinsa ba sai na fada
miki ba.
“Gaskiya ne.
Yana jin su bai ce musu komai ba don bai son
su sak0 masa maganar Sameer don ya ji ya bata
masa rai domin shi ne ya janyo damuwar da ya
gani a kan fuskar Haana dinsa nan ya ji yana son
korar damuwar da take son zama a cikin ranta.
Da sauri ya ce, Haana wai ina batun malamin
ki ne kwana biyu na ji kin daina min maganarsa kin
yarda da magana ta ko? Ya fadi hakan ne don ya
San maganarsa ce kawai zai ga farn ciki a kan
fuskarta ya kori kuncin da KUNAR ZUCIN da
yake hangowa a kan fuskarta ba wai don baya

Hankalinsa kwance don ya gano cewa Haana
ba son Sameer take ba shi ne kawai yake sonta, ita
kuma ba ta ba shi damar da zai ce yana son ta ba
tunda ya gama fahimtar haka sai ya fara dauke
damuwarsa a kan sa ya shiga tunanin yadda zai yi
ya furta mata kalmar so tun kafin Malam M.J ya
dawo rayuwarta don matukar bai bayyyana mata
tsananin son da yake mata ba muddin M.J ya dawo
Cikin rayuwarta to zai rasa walwala da dukkan
wani farin cikinsa baki daya saboda yana gani za ta
zabi M.J ta bar shi.
Girgiza kai ya yi ya ce, “Allah kada ka kaddara
min haka albarkar Fiyayyen Halitta ba ni da mata
abokiyar rayuwata uwar ya yana Sai Raihanatu
Mustapha Nasser Danfillo jina wadda ni da ita
muke ZURI A DAYA, kuma DANGIN JUNA
DANGANTAKARMU ba zata tsaya iya nan ba,
har sai ta kai mu ga DANGANTAKAR AURE
yadda za mu ja IGIYAR RAYUWARMU ni da ita.
Saboda ba ni da wani buri illa na bude idanuna
na ga MISs Haana a matsayin mata ta zamo min
SANYIN IDANIYATA, Ya Allah Ka cika min
burina. Wannan shi ne tunanin da addu’ a yake yi
lokacin da yake kwance a dakin barcinsa cikin
dare. Www.bankinhausanovels.com.ng
A can bangaren Haana kuwa tana kan
Whatsapp tana ta yi can, can ta ga Mr. Sameer
Online da kamar ba zata kula shi ba kawai sai ta
Hau don yin typing kawai sai ta gan shi yana rubutu


Sako sai ta yis auri ta fita tana jiran me zaice mata.
Can sai ta ga ya turo mata hoton fuska ja
alamar fushi, tana gani sai ita kuma ta yi dariya sai
ta tura masa na murmushi.
Ya sake turo mata jar fuska rututu, ita kuma ta
turo masa na zare ido, tare da alamar tambaya. Sai
Yanzu ya yi magana ya rubuta, Au! Baki ma san
me ki ka yi ba ko?
Ta tura masa “Eh, sai ka fada.
Babu abin da na sani ni dai na ga ka dau fushi
da ni. Ta rubuta ta tura masa.
Kin sani kin dai take ne kawai.
Na ce maka fa ni babu abin da na sani bare na
take ka fada min mana.”
Hoton heart (Zuciya) ya turo mata wanda ta
tsage tana zubar jini. Dif ta yi ta kasa cewa komai
yana ganinta online amma ta yi shiru ita ba ta ce
komai ba ta fi minti biyar ba ta ce da shi komai ba.
Miss Haana kin ki cewa komai, kuma na ga
kin duba abin da na turo miki gaki online kina sane
da abin da nake nufi, amma sai ki nuna kamar ba ki
gane ba. To na fito fili na fada miki ina son ki na
muradin auranki ki cire hayakin kanki ki ba ni
dama na fito mu yi aure, don rannan a gabanki
Granny take yi mana tsiya da ciwon baki kin ga
Azumi yana kawo kai ki ba ni dama mu yi Azumin
nan a cikin gidanmu kin ga na huta da zuwa gurin
Ammi neman tuwo bare Granny ta yi min gori
Tana gama karantawa kai tsaye ta ce, Mr.
Sameer kasan kai dan uwana ne tsakaninmu babu
yaudara bari na fito na fada maka don Allah ka yi
hakuri ina da wanda nake so kuma shi nake son
aure ina nan ina jiransa dawowa cikin rayuwata
Don Allah ka fhaimce ni bana Son mu wahalar da
junanmu ko ya janyo na yaudare ka gwara na fito
na fada maka gaskiya ka yi hakuri Allah ya ba ka
wacce ta fi ni.
Ba ameen ba.”
Ya ka ke so to na yi da kai?
Kawai ki so ni kamar yadda nake son ki shi ne
abin da nake so. Ya hada da red tace ya turo
alamun cikin fushi yake maganarsa.
Mr. Sameer ba zan iya ba.
Dole kuwa ki yi tunda ina son ki.
Ba a dole Mr. Sameer tunda kai ba ubana bane wai me yasa ka fiye fitina ne.
Dole na yi fitina mana saboda wanda ki ke so
baya son ki ke ce ki ke son shi, hasalima ya manta
da ke cikin rayuwarsa da yana son ki da ya dawo
Cikin rayuwarki tuntuni. Haana ina son ki yi
facing reality ki daina yaudarar kanki da zuciyarki
ko kin ki ko kin so ba ki da miji sai ni wanda ki ke
So ba son ki yake ba, tun da har yanzu ban taba
ganin ya tako ya zo inda ki ke ba.”Wannan ba matsalarka ba ne k0 ya dawo cikin
rayuwa ta ko baya dawo ba wannan ni ta shafa zan
kuma ta jiransa ko da zan tsufa ba miji please Mr.
Sameer ka fita cikin rayuwata ban so ka ba ni
CIwon kai da yawa ka yi rayuwarka na yi tawa,
idan za ka shigo cikin rayuwata ka saka min
damuwa da ciwon kai a shirye nake da na datse
Igiyar zumunci na da kai please leave me alone ban
shirya daukar damuwa a rayuwata ba. Tana gama
tura masa ta raka shi da tsaki. Ta yi sauri ta sauka
daga online din ta bace. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana gama karantawa ya yi murmushi ya ce,
“Haana masu gari just wait and watch. Shi ma ya
sauka daga online din ransa a bace.
Bayan sun gama chat din ta ajiye wayarta cikin
bacin rai ta nufi bandaki ta yo brush ta zo da niyar
kwanciya don yau Mr. Sameer ya gama bata mata
rai ta kuduri niyar ko kallon arziki ba zai kuma
samu a gurinta ba ya je ya yi rayuwarsa ita ma ta yi
tata shi ne ya fi.
Tana gama saka kayan barcinta ta ji alamar
sako ya shigo wayarta. Tsaki ta saka don ba ta raba
dayan biyu shi ne ya yi mata sakon ganin ta sauka
online da ta yi niyar ba za ta dauka ba ma sai kawai
wata zuciyar ta ce mata bari na duba na gani na ga
kuma da wane rainin hankalin ya zo min, saboda
ba wani abu da zai sake ce min na saurare shi kuma
ya kare ni da shi sai dai gaisuwar Musulunci.
Cikin fushi ta dauki wayar don dubawa ga
mamakin ta sai ta ga sabanin abin da ta zata wani
irin farin ciki da annashuwa sune suka bayyana a
kan fuskarta sakamakon sunan Malam M.J radau
da ta gani a kan screen din ta da sauri ta hau kan
gadonta cike da doki da zumudin duba abin da ya
turo mata, Da sallama ya fara yi mata.
Assalamu alaikunm.Raihanatu ya gida ya karatu da fatan kina mai
da hankalinki a kai na san kina da buri a kan
wannan karatun naki plcase ki dage
Murmushi ta yi ta kankame wayar ta sumbace
ta, ta dawo ta ci gaba da karantawa.
Raihanatu dama na turo miki wannan sakon ne
don ba ni da wani lokaci nawa cikakke amma idan
na samu lokaci zan kira ki, amna kafin nan ina son
ki taya ni da addu ‘a don yau Allah ya Cika min
burina zan auri yar uwata Fadeelah da nake
Mutukar kaunarta kamar raina zai fita, tunda nake
ban taba son wata ‘ya mace a duniyar nan ba sama da
Ita, an sa mana rana zan dawo Nigeria a yI shagalin
bikinmu daga nan sai mu koma gaba daya da ita.
Na san za ki taya ni murna saboda babu wanda
na tuna a cikin dalibaina sama da ke don ta mu ta
zO daya shi ya sa na turo miki wannan sakon don
ki taya ni murna da tatan za ki halarci shagalin
bikinmu idan na zo kasar har gdanku zan zo.
Ki huta lafiya daga Malamin ki MUHAMMAD
JAFAR (M.J).
Wani irin rudani da tsananin rikici da BUGUN
ZUCIYA lokaci guda hade da tashin hankali su ne
suka hadu suka kawo Ziyara cikin zuciyar Haana.
Wurgi ta yi da wayar kan gadon ta take ta ji
zuciyarta ta tsananta da bugu ta ji wani irin duhu
yana kokarin rufe mata idanu, ta ji wani irin haki
yana zuwar mata kamar wata mai Asma. Ta rasa
me za ta yi ta JI nutsuwa. Nan da nan ta ji bakin ta
na fadin.
“Innalillahi wa ‘inna ilaihir raji un! Jin bakin ta
na fadin haka nan ta shiga nanatawa nan ta ji
Tana fadin
dukkan addu’o’i Www.bankinhausanovels.com.ng
Tana ji kirjinta na dada rikewa can dai ta ji
nutsuwa ta fara zuwa mata. Jin hakan sai ta fara
tunanin ko mafarki take yi. Tabbatarwar da ta yi a
farke take sai kawai ta runtse idanunta take ta ji
wani irin zazzafan hawaye ya zO mata sai a lokacin
ta ji wani irin salama a zuciyarsa.
Sai a lokacin ta samu damar yin kuka tana
cewa, ‘Na shiga uku! Malam M.J me na yi maka da
za ka yi min haka, ashe dama ba sona ka ke ba? Ba
ka ma san me nake yi ba ina nan ina son maso wani
ashe kai kana can cikin duniyar ka tunanin ka da
mafarkin ka dama rayuwarka gaba daya su na
gurin wata, ni ina nan ina ta dakOn soyayyarka da
ba ka san ina yi ba?
Ya Abba da Mr. Sameer you are right da ku ke
fada min gaskiya na yi facing reality.
Malam M.J me yasa ka yi min haka, me yasa
ba ka fahimci cewa nima ina son ka ba, kamar
yadda ka ke son yar uwarka, koma fiye da yadda
ka ke son ta? Malam M.J na kai ne rayuwata,
murmushi na, farin cikina, kukana, dariyata, kai
komai na rayuwata dukkan shaukki na gaba daya
na dora shi a kanka ashe ni nan ban sani ba
yaudarar kaina nake.
Yau na kara tababtarwa kai na cewa da gaske
ka yi nisa da rayuwata ba zan taba samun ka ba,
bare har farin ciki na da burina su cika. Malam M.J
da ka san irin son da nake maka da ba ka ba wa
kowacce ‘ya mace zuciyarka ba domin ni ce kadai
wadda na fi dacewa da ka so ni, yau ya zan yi da
rayuwata babu kai a cikin ta da duniya ta gaba
daya?
Ya zan yi na rayu a wannan duniyar kana can
taka duniyar da wacce ka ke so? Zuciya ta saba da
so da kaunarka babu wanda take gani sai kai sai
daga baya ka zo ka bayyana min cewa sam tunanin
ka ba ya kaina ba ka hango ni ba a cikin tunanin ka
wanda da ni A TUNANINA ba ka da wadda za ka
So sama da ni.
Malam M.J me yasa ka shigo rayuwata? Me
yasa ka shigo duniyata da har kaddara ta hada ni?
Da na san za ka shigo rayuwata ka hana ni sukuni
da ban yarda kaddara ta hada ni da kai ba. Wayyo
Ammi, Abba, Granny, Ya Abba zan mutu kuje ku
nemo min Malam M.J na ku fada masa zan mutu
idan bai dawo cikin rayuwata ba, ba zan iya
rayuwa da wani namiji ba idan ba shi ba.
Kan tiles Haana ta samu guri ta yi zaman
dirshan tana kukanta da dan karamin haukan da ta
shiga na wucin-gadi. Ga shi dare ya soma yi sosai
wajen daya da rabi saura gurin wa za ta je a cikin
wannan tsohon daren ta kai wa damuwarta, idan
ma ta je ta ce masu akan namiji ta shiga wannan
tashin hankalin? Idan kowa ya goyi bayanta Ammi
Ce mutum ta farko da za ta fara kushe ta, dole
matsayinta na cikakkiyar Bafullatana ta boye tunda
ta gaji kunya gaba da bayanta.
Kukanta ta shiga yi tun tana yi da hawaye har
Ya dawo na zuci a ranar ba ta runtsa ba, in ban da
radadi da KUNAR ZUCI babu abin da take ji cikin
zuciyarta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Tun da garin Allah ya waye Ammi ba ta ji
motsin Haana cikin gida ba, wanda ta san hakan ba
al’adarta ba ne rashin tashi da wuri ko da kuwa
weekend ne har suka fara shirin break fast ba ta
gan ta ta fito ba. Ammi ta ce, “Uwata dubo min
wannan kasar a dakinta ko lafiya take ban ji motsin
ta ba. Tana nufin Aziza Karama don lokuta da
dama wata rana haka take kiran ta.
Ammi in dai Aunty Haana ce dazu ina dakinta
ta ce min ba ta jin dadi ni ban yi zaton ba ta fada
miki ba.
Ba ta jin dadi me ya same ta kuma’?
Ta ce min dai kanta ne ke ciwo, kuma tana jin
barci shi ne na fito na bar ta a dakin.
To, aiban sani ba bari na je na duba ta na
gani.Daidai lokacin da Abba ya sauko falon shi ma
yana cigiyar ta, nan Ammi ta fada masa tare suka
rankaya zuwa dakin nata.
Kwance take kan gado ta wani takure kamar
mai jin sanyi, suna zuwa suka shiga kiran sunanta
karkarwar sanyi take yi da sauri Abba ya ce,
Subhanallahi! Ammina ba ki da lafiya, amma ko
ki kashe A.C din nan ga shi sai rawar sanyi ki ke?
Da saurí ya je ya kashe A.C din ya zo ya taba
goshinta rau ya ji shi kamar garwashi. Ammi ma
ta taba jikin ta ce, “Ki na rashin lafiya ba za ki fada
amana ba?
Aisha ki bar ta mana ta ji da Ciwon da take ji
mana, Ammina me ke damun ki ne Ciwon naki tun
yaushe ne, me kuma ke damun ki bari na kira
Doctor ya duba ki yanzu., Abba zazzabi ne mai
zafi ya rufe ni tun dare ya ki sauka.
Calm down Ammina ki daina ku ka zai kara
janyo miki wani ciwon daban. Www.bankinhausanovels.com.ng
Suna cikin haka sai ga Granny nan da Ya Abba
suka shigo dakin a rude suna tambayar me ke
damunta. Ganin yadda kowa ya rude a kan jin
rashin lafiyarta duk sai ta ji tausayin su ya kama ta
a ranta ta ce da za ku ji dalilin ciwon nawa da dama
daga cikinku babu wanda ba zai ji haushi na ba,
malam M.J me yasa ka yi min haka? Me yasa ka
kasa gane cewar nima tuni na kamu da son ka
kamar yadda ka kamu da son ‘yar uwarka ba ka yi
wa ZUCIYA DA RUHI na adalci. (Sunan littafin
Sa’adatu Waziri mai fitowa nan gaba idan Mai
duka ya yarda).
Tana jin likitan da ya zo duba ta yana fadawa
Abba cewa damuwa ce ta yi mata yawa ga kuma
wata damuwa da take son jefa kanta a ciki. Haba
jin haka Abba ya shiga jero mata tambayoyin cewa
me yake damunta da za ta boye ta ki gaya musu?
Ba ta samu damar ba shi amsa ba likitan ya ce,
damuwar zai iya yiwuwa a kan karatu ne.

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Suna cikin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *