ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 11 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Granny ai ni ba ni da matsala tunda ina da ke, ke ce
uwar gida sai kuma amarya da zan sake sai ki yi
hakuri, ki ajiye kishi; domin duk rana daya za a
kawo min ku. Www.bankinhausanovels.com.ng
Aa ni kam ka yi min tsufa ina ni ina kai ai ni
din nan da ka gan ni sai yaro dan sha bakwai ba
tsoho ba wanda ya kusan hararar arba in.
Dariya aka saka yi wannan karon sai da Ya
Abba ya dan dara, nan suka sake Granny a gaba
saida Abba ya tsawatar musu. Haka ya ja Ya Abba
suka fice don rakiyar da zai yi masa har cikin ransa
bai so zai tafi ya bar Sameer da Haana tare ba da da
yadda zai ya fasa wannan rakiya da ya yi ta amma
babu dama yana ji Sameer na fada mata abin da ya
kawo shi gidan ba ta yi musu ba ta nufi kicin. Take

ya kara jin kishinsa yana ta taba masa zuciya, da
saurai ya fice daga falon.
Washe gari misalin hudu da wani abu zaune
yake cikin dakinsa ya gama shiri zai je wajen
Haana su dan taba hira. Farida ce kanwarsa ta yi
knocking din dakinsa ya ba ta damar shigowa.
“Farida ya aka yi ne? Ya fada yana mai tazar
gashin kansa yana duba madubi.
Wata damuwa ce da ni Yaya da fatan dai za
ka fuskanci abin da na zo maka da shi.”
Nan da nan ya mayar da hakalinsa gaba daya
gurinta ya ce ina jin ki Farida me ye damuwar ta ki
insha Allahu zan fahimce ki koma da me ki ka zo
min. Www.bankinhausanovels.com.ng
Guri ta samu ta zauna gefen gadonsa sai da ta
zauna ya ce me ye fada mun na ga duk kamar
Jikinki a sanyaye me ke faruwa?
Sai da ta nutsu sannan tace,Ya Sameer don
Allah tambaya nake son na yi maka da fatan za ka
bani amsarta, amma ka yi hakuri.idan na sani me zai hana na fada miki babu damuwa ki yi min ita duk tsaurinta.


Shin tsakanin Yaya Haana da Yaya Rauda
wace ce wadda ka ke so take kuma son ka?
Wace irin tambaya ce wannan kuma?
Shi yasa na ce don Allah ka yi hakuri, ina da
wata hujja ne da yasa na yi maka wannan maganar,
Haana nake So to tsakanina da Rauda kuwa
kawance ne da so da kauna na DANGIN JUNA,
me ki ka ganı ki ka yi min wannan tambayar?
Lokuta da dama na sha ganin damuwa a
fuskar Ya Rauda a duk lokacin da ku ke tare da Ya
Haana a hankali na dinga fuskantar akwai wani abu
da take boye muku ba ku sani ba na sha yi mata
tambaya sai tana kaucewa akwai wata rana da na
zo na hange ta tana labe tana kallon ku har ku ka
bar gurin ba ku san tana gurin ba, kawai sai gani na tayi a gabanta tana gani na sai ta yi saurin saka hannu Www.bankinhausanovels.com.ng
ta goge hawayen da yake zuba a idanunnta.
Babu irin tambayar da ban yi mata ba ta ki ta
fada min abin da ya sa ta kuka karshe sai ce min tayi abu ne ya fada mata cikin ido. Dole na bar ta a
haka, amma sai na ci gaba da bincike a kanta.
Ka san kaf cikin zuri a din mu ni babu wadda
jinina ya hadu da ita sama da Yaya Rauda tana da
kirki tana kaunata ina kaunar ta, kodayaushe muna
tare da ita hakan yasa na ji ina matukar kaunarta,
dazu ne da na je nemanta dakinta ba ta nan shi ne
na ga wannan karamin dairy a kan gadonta da na
dauka zan ajiye mata sai kawai na hangi sunan ka
da manyan baki hakan ya ja hankalina har sai da na
karanta abin da ya ruda ni da kuma ba ni mamaki.
Ya Sameer ka duba kai ma ka gani da idanun
ka Ya Rauda son ka take son da babu algus ganin
abin da ke tsakanin ku kai da ‘yar uwarta Haana
yasa ta kasa nuna maka har ka gane ga shi ka
duba.” Ta mika dairy din.
Wani irin shakku da mamaki ne suka bayyana a
kan fuskarsa tun da kanwarsa Farida take
maganar yake cike da mamaki ya kuma kasa katse
ta har sai da ta tsaya da kanta don abin ya yi
matukar girgiza shi.
Daga mata hannu ya yi Cikin wani irin takaici
da haushin kanwar tasa ya ce, Ke Farida ba na son
shirmen kin nan wa ye ya fada miki wannan
zancen shirmen da ki ka zo min da shi tunda ba ji
ki kayi ta fada miki cewa ni din take so ba. Daga
ganin sunana a cikin dairy din ta sai kawai ki ce ni
take nufi an fada miki cewa ni ne kadai Sameer a
duniyar.Cikin damuwa ta ce,Yaya kai kadai ne
Sameer Aminu Danfill0 ban da kai ban san wani
ba, plcase Yaya ka fahimce ni mana ka duba nan
gurin ka karanta za ka yarda cewa kai take nufi ba
wani ba.
Karba ya yi ya soma dubawa tsananin mamaki
ne ya yi awon gaba da shi jin irin kalaman ban
tausayi da nuna tsananin so da kauna da Rauda
take masa wanda shi sam ba don haka ta faru ba ba
zai taba sanin cewa Rauda na son shi tunda shi ko
kadan bai taba kawo haka a cikin ransa ba. Babu
inda ya ji abin da ya taba masa rai inda ta ce.
“Yau ce ranar da na gane Sameer yana Son Sis
Haana dole na hakura da shi ko da zan mutu da son
shi ba zan taba barin sh ko Haana su san ina son
shi ba. Ya Sameer ba zan taba barin ka san ina son
ka ba tunda yar uwata ka ke so zan ta boye son ka
da kaunar ka har karshen rayuwata.
Wayyo ni Rauda ashe mafarkina da burina ba
za su taba cika ba. Allah ka yaye min Wannan
azabar son da nake ji a raina. Ina son farin cikin
yar uwata ba zan taba barin na ba ta matsala a kan
wanda yake son ta. Www.bankinhausanovels.com.ng
Haka ta yi zanen wata fuska mai dauke da
hawaye alamar kukan take yi.
Runtse idanunsa ya yi, ya yi sauri ya wurgar da
dairy din yana wani sauke numfashi tabbas
kalamanta sun taba masa zuciya, ya kuma tausaya
mata cikin irin halin da take ciki.
Haka ya bude idanunsa da suka kada suka yi
jajir da su ya furzar da wani numfashi mai zafi, ya
maida kallonsa ga kanwarsa Farida ya ce
Farida me yasa ki ka yi haka? Me yasa ki ka
dauki sirrinta da ta boye ki ka kawo min na gani,
bayan kin san irin tarin hakkin duba sirrin wani?
Me yasa ki ka yi haka? Sam ba ki kyauta min ba,
ba kuma ki kyautawa ita Rauda din ba tunda kin
tona mata asirin abin da ta boye ba ta Son wani ya
gani, ba ita ki ka batawa ba yanzu ni ki ka batawa
tunda har ki ka sanar da ni halin da take ciki a
kaina na bayan ni kuma gaba daya tunanina ba
haka ba ne.Farida ya ki ke so na yi yanzu, bayan tarin so
da nake yi wa Haana? Rauda ba ta da matsala tana
da kikri da matunta mutane ko kadan ba ta
cancanta da haka a gurina ba ta so ni na ce bana
sonta. To amma babu yadda zan yi dole ne ta
hakura, tunda tuni zuciyata ta riga da ta ginu da son Haana, bana jin zan iya hakura da ita.
Da da hali zan iya auran su su biyu dana hada,
amma na san duk cikinsu babu wanda zai yarda zan
aure ta ne don na ba wa zuciyarta da burin da
mafarkin abin da take so, amma ba wai don zan iya
hada sonta da wanda nake yi wa Haana ba.
To amma ina hakan ba zai yiwu ba, tunda abin
nan babu wanda ya sani daga ni sai ke zan so ki ja
bakin ki ki yishiru, mu boye abin cikin sirri ki je ki
mayar mata da wannan dairy din kada ki kuskura ta
gane cewa kin gani bare tasa a ranta kin karanta.
sai na san yadda zan yi na yI nisa da ita
yadda gani na ba zai sa ta damuwa ba, plcase my
SIster ki daure ki yi min wannan taimakon.
Murmushin yake ta yi ta ce, Yaya Sameer da
ka bi ta tawa da ka hakura ka karbi tayin
soyayyar da Ya Rauda take maka don na fuskanta
zata fi nuna maka so a kan wanda Haana take maka.
A gabana na sha jin Ya Haaana na cewa mu taya ta
da addu’a Allah ya dawo mata da Malam M.J dinta
cikin rayuwarta, don shi take mafarkin aura. Shin
anya kuwa Yaya Sameer, Ya Haana tana son ka
kamar yadda ka ke son ta?
Tsawa ya daka mata wadda har sai da ta razana
cikin zafi ya ce, Farida dauki abn ki ki fice min
daga dakin nan ba na son kara ganin kafar ki a
dakin nan ko don kin ga na jaki jikina fiye da
sauran kannena shi ne har za ki 1iya tara na da
wannan maganar oya leave me alone fice kar na
kara ganin ki a nan. Www.bankinhausanovels.com.ng
Da sauri ta dauki dairy din ta fice cikin fushi
Tare da jin haushinsa tana sane dama ta y1 masa
haka ta san dama Haana din ba ta taba ba shi dama
ba duk da kuwa ta san yana sonta tana ja masa rai,
hakan yasa tunda ta gano Rauda na son shi ta saka
a ranta sai ta bi ta karkashin kasa ta yi mata
kamfen wannan ma dairy din bincike ta yi ta je ta
dauko ba tare da ita kanta Rauda din ta sani ba don
kawai ya san halin da take ciki ya hakura ya so ta
kamar yadda take son shi.
Safa da Marwa ya shiga yi a cikin dakinsa,
domin ya rasa abin da yake masa dadi cikin
zuciyarsa duk kuma babu wanda ya janyo masa sai
Farida mai dan banzan karan ba ni da har ta je ta
binciko masa wannan labarin mara dadin ji da ya
san da wannan batun za ta zO masa da bai tsaya ya
saurare ta ba ga shi tana son jefa shi cikin tashin
hankali.
Cire kansa ya yi sama yana kallon silin a
bayyana ya ce, Please Rauda ki yi hakuri ba zan
Iya hada son kowa da Haana ba da babu ita a
rayuwata zan 1ya karbar tayin soyayyar ki. Duk
wani shiri da kuduri a nan gurin ya gama saka duk
abin da ya zo masa zuciyarsa ya kuma sawa
ZuCiyarsa cewa hakan ne kadai zai zamo masa
mafita.
Granny ce zaune a dakinta ita da Abba ta kira
shi ne don su zanta abin da ke ranta. Tana zaune
kan resting char da ke dakinta shi kuma Abba na
gefen gadonta yana zaune. Ta dube shi ta ce
Mustapha na kira ka ne domin 1na son mu yi
wata muhimmiyar magana da kai kan yara nan
guda biyu sai dai ban san kai me ye hangen ka a kai
ba.
Ya gyara zama SOsai ya ce, “Su wa fa ba dai
Mustapha Karami da Sameer ba?
Ba haka nake nufi ba ina nufin Mustapha din
da kanwarsa Raihanatu ya batun namu na baya da
kudurinmu na son hada auransu yana nan ko kuma
ka canza?”
Daidai lokacin da ya Abba ya kawo kansa
dakin Granny kan tasa matsalar don ko kadan bai
san Abba yana gidan ba ma.
Gabannsa ne ya fadi jin furucin da ya fito daga
bakin Granny da sauri ya ja ya tsaya don sauraron
abin da Abban nasa zai ce cikin ransa ya shiga
rattaba addu a da Allalh yasa tun kafin ya furta
musu ashe su tuni suna da wannan hange lallai
manya hangenSu sai su ya gode Allah da ya sa
hakan ta faru.
Ajiyar zuciya Abba ya sauke ya ce, “Gaskiya
ne Umma ina da wannan burin da kuma tunanin sai
dai kuma a yanzu ya canza don ban san yadda zan
bullowa sauran ‘yan uwana da wannan maganar ba
tunda mun riga da mun kara kafa doka a kan hana
yaranmu auren zumunci gudun abin da ya faru a
baya kada a zo a sake bata zumunci.
Tunda ina ganin daga ni sai ke kadai muke
da wannan kuduri mai zai hana mu rufe maganar
tunda ba mu riga da mun bayyanawa kowa ba don
kada a ce an samu matsala a bangarenmu. Ko kuma
ya kika gani? Www.bankinhausanovels.com.ng
Mustapha kana ganin hakan shi ne mafita, ba
ka ganin yadda yaran nan suka shaku da juna da
kuma kaunar junmansu, idan har kai ba ka lura ba ni
na lura akwai wata boyayyiyar dangantaka a
zuciyar da basa nunawa kowa amma ni na gama
karantarsu musamman shi Abba yadda shi baya iya
boye son da yake mata, amma 1dan jama a sun gani
sai suna tunaniln so ne kawai na jini ba na aure ba.
Umma ina da burin ganin Mustapha ya, auri
yar uwarsa na Jima da ajiye haka a zuciyata ba na
kinsa sai dai ba na son a ce ni ne na karya doka a
cikin Zuri’a kuskure na daya da a lokacin da muke
zaman ban fito da wannan maganar bare a sam0
mana mafita a cikinta. amma duk da haka zan san
yadda zan je musu da wannaii maganar.
A Jiyar zuciya ta yi ta ce Duk na karbi
UZURIN ku kai da sauran yan uwanku na
fuskanci tunanin ku da hangen ku a kan zuri’ a din kuma na son a ce an kara samun matsala a
zuri a din nan duk abn da zai kawo rabuwar kai
barin sa shi ne alheri ba zan so a ce matsala daga
gun mu ta fito ba, addu’a kawai za mu shiga yi
idan auransu da muke shirin hadawa alheri ne duk
rashin son zuri’a sai an yi shi saboda haka Allah ya
kaddara.
Don haka na yarda da abin da ka ce mu bar
maganar, amma insha
Allahu Mustapha ba shi da mata sai kanwarsa cikin yardar
Allah.
Allah yasa Umma nima haka nake so.
Farincikii ne ya kama Abba da sauri ya juya ya
koma sIde dinsa don kada a zo a gan shi ya yi labe
tunda duk ya ji abin da yake son ji daga Umma har
Abban nasu, duk suna goyan bayansa a kan hadin
auransu. Tambayar da ta tsaya masa da ya yi wa
kansa ita ce Haana din fa ita ma tana son auran
nasa ko dai son da take masa bana aure ba ne na
shakuwa ne na tsakanin Yaya da kanwa ne? Idan
kuwa haka ne zai fi kowa bakin ciki da faruwar
hakan.
Yana Cikin wannan halin sai ga Haana ta shigo
dakinsa dauke da laptop dinsa kirar Apple, kallo
daya za ka yi mata ka gane tana cikin damuwa.
Nan da nan shi ma damuwar ta bayyana a
fuskarsa bayan ya amsa sallamar da ta yi masa,
Cikin kaguwa ya ce, Sister lafiya na gan ki haka
fuskarki dauke da alhini?
Ajiyar zuciya ta yi sannan ta kirkiro murmushi
ta ce, Ya Abba wai haaya me ye ke tsakanin ku
kai da ita ne yasa ka boye min labarinta ba ka taba
fada min ba bayan tun kana can nake fada maka
dukkan matsala ta da damuwa ta a kan Malam
M.J?
Ka yi hakuri dazu na zo dakin ka ba ka nan zan
yi amfani da system dina babu modern ga kuma
wareless din gidan babu network mai kyau shi ne
na dauki naka system din da na ga akwai m1ordern
akai kawai sai na yi amfani da taka.
Ban san me yasa na ji ina son na yi maka
bincike ba kawai maimakon na yi login out na duba
nawa din sai kawai na shiga duba inbox dinka
messages din Haaya da na gani rutuitu a ciki wanda
ko dubawa ba ka yi ina cikin nazarin wacece ita
Haaya din sai kawai na ga sabon sakon ta ya shigo
da sauri na duba har sai da na soma gajiya.
A takaice dai na fuskanta koma wace ce Haaya
din nan tana son ka so kuma mai tsanani, sai yadda
nake jin kalamanta kai ne ba ka son ta. To why? Ya
Abba me ta yi maka da ba ka son ta? Abin da ya sa
naji ina tausayınta duk da ban san ta ba, ban kuma
san dalilin da yasa ba ka son ta ba, saboda irin
rayuwa daya muke fuskanta da ita son maso-wani
kamar yadda nake, ko da yake ita ka san kana son
ta, ni kuwa ba duk wahalar da nake a kan Malam
M.J babu wadda ya sani. Www.bankinhausanovels.com.ng
Please Ya Abba ka daure ka so Haaya mutukar
tana da hali na gari da kuma fitowa cikin zuri a mai
kyau, ni kadai na san irin halin da take ciki son da
ka ke ba a son kana yi ba, ka tausaya mata ko nima
zuciyar Malam M.J da tunaninsa za su yo kaina ya
dawo cikin rayuwata.
Runtse 1danuwansa ya yi ya bude nan da nan
suka kada suka yi jajir ya ce Ya isa haka Haana
bana son jin kina cewa a tausaya a so ki, kin fi
karfin M.J har da rayuwarsa ma gaba daya da da
yadda zan yi na cire miki KUNAR ZUCIN da ki ke
JI a game da shi da tuni na yi Haana kina da taurin
kai na ce ki manta da M.J a rayuwarki ki yi facing
reality, kin ki ba na so kina sa damuwarsa a
rayuwarki shi kadai ne namiji da zai iya kawo farin
Ciki cikin rayuwarki ki saki ranki idan Allah yasa
har ba yaudararki yake ba za ki ga wata rana ya
dawo cikin rayuwarki Tswww! Ya yi tsaki yace, Look! Haana na
roke ki da ki manta da rayuwar M.J gaba daya da
dukkan alama ba zai iya baki dukkan farin ciki ba
da zai 1ya da zai ke neman ki a waya ga shi kuma
kina cewa kina kiran wayarsa ba ta shiga, Why
Why!! Why!!! Haana me yasa za ki kirkiri matsala
ki dorawa kan ki bayan kuma ba ki da mafita a kan
ta bayan hakuri? Www.bankinhausanovels.com.ng
Haana da na san dawowa ta Niger1a ba za ta
saki faran ciki ba ya mantar da ke dukkan wata
damuwarki wallahi da ban dawo ba, ko kadan bana
Son ganin damuwarkI bare tashin hankali, amma
rana daidai ne da ba zan dinga ganin damuwar nan
a fuskarki ba.Kin san na fara tsanar M.J domin duk
shi ne ya janyO wannan damuwar 1dan har ba za ki
dinga yi min magana ba zan yi fushi da ke zan
kuma daina nuna damuwa ta a kan dukkan wani
al,amarin ki.
Da sauri ta goge hawayen da ke zuba a fuskarta
ta ce.Ya Abba don Allah ka yi hakuri na yi maka
alkawarin daina shiga damuwa zan yi dukkan abin
da ka ke so, amma ina son ka taya ni da addu’a

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE

ZURI’A DAYA BOOK 3 CHAPTER 17 BY SA’ADATU WAZIRI GOMBE Www.bankinhausanovels.com.ng  Mun tsaya  Suna cikin …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *