ZUMA CHAPTER 8 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 8 BY SHATUUU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Duk bansan abinda ke faruwa ba saboda na riga na kashe wayata baki daya tun friday da muka dawo daga asibiti da daddare, tsoro na daya shi ne kiran Aliyu ya shigo min wayata bansan me zance masa ba, bansan a wanne hali yake ciki ba bansan ba ko Daddy ya bashi wannan mummunan labarin. Haka na cigaba da zama da waya a kashe babu abinda nake se dai idan maganar ta dawo min na shiga toilet na saki ruwa nayi kuka na wanko fuskata na fito. Wajen yamma Aminatu ta gama shiri zata koma hadejia inda anan take nursing training dinta cikin sabuwar school of nursing da aka bude, dakina ta shigo hannunta rike da plate din abinci ta zauna gefe na tareda aje min tace+

“Yaya Nanah an samu matsala ne da Aliyu? Naga yau kika ce zasu zo amma shiru”

Furta sunan Aliyu da tayi se naji idanuna sun ciko da kwalla, nayi saurin kawar da kaina ina bude baki na dan iska tasa hawayen ya koma, saboda bana son wani yaga ina kuka akan maganar har suga laifin Daddy ko suce zasu mishi magana shi kuma yaga kamar bai isa dani bane ba. Amma hawayen nan seda ya zubo tana gani ta tashi ta tura dakin ta dawo lokacin kuka sosae nake ta rungume ni tana bubbuga bayana amma ta kasa fadar komai, seda nayi shiru dan kaina sannan tace

“Yace ya fasa? Ko”

Kaina na girgiza na fada mata yadda abin ya faru, se kawai ta saki salati tana fadin

“Amma matar nan tsinanniya ce, Allah ya wadaran matan da suke ganin namiji nasu ne su kadai, shi kuma Daddy ya yadda da wasu empty threat dinta, haba baiyi tunanin halin da zaki shiga ba?”

Nayi dan murmushi me ciwo Aminatu kenan, suna sauran abinda zasu fada kenan so na dauki hakan a matsayin rehearsals kafin suma su buga tasu dramar.

“I’m going to meet Daddy, so yake zuciyar ki ta buga, kinga idonki kuwan yayi ja, ga kin rame yau ko abinci baki ci ba, akan wata zai hanaki farin ciki”

Ta mike a fusace nayi saurin riko hannunta ina girgiza mata kai, nace

“Aa Aminatu dan Allah karki haka, Daddy bai nufin cutar dani, in fact yayi hakan to protect me. Irin Fatima suna nufin duk abinda suka ce. Ni bana son a ja maganar shiyasa tuntuni ban fada muku ba”

Da mamaki take kallona sosae sannan tace

“Kin hakura kenan? Kina nufin ke zaki iya hakura dashi”

Se nayi murmushi nace

“Da ai bansan shi ba Aminatu, yanzun ma zan koya rayuwa babu shi, it’s hard bana fatan ko makiyi na yaji abinda naji daga Friday zuwa yau, zuciyata kamar ana soya ta haka nake ji, ban taba sanin haka rabuwa da abunda kake so yake ba, freling ne na se wanda ya faru akan shi shi daya zaiyi testifying!”

Na fada ina goge hawaye na, tayi shiru tana ta kallona se can ta miko min abincin tace

“To kicinko yaya ne”

Spoon din na dauka na deba abincin na kai bakina se naji wata yunwa tayi rushing cikina a hankali na saki jiki naci sosae sannan nasha lemu da ta kawo min. Muna zaune naji sallamar Amal tana fadin

“Yaya Rayyanatu ki shigo yaya Aminatu na dakin mu”

Mikewa Aminatu tayi tana fadin

“Kinga Rayyanatu har tazo, bari mu tafi”

Mikewa nayi na dauki hijab muka fito, Rayyanatu ta gaishe dani na amsa sannan na dauko musu frozen meat pie daga freezer muka raka su har gate inda driver ke jiran su. Se na dauki wayata da niyyar kunnawa se na fasa karshe dai na aje wayar kawai ina kallonta ina ayyana abubuwa da dama da suka faru dani cikin yan kwanakinnnan, abubuwa marasa dadi wanda nake jin kamar duk wata kaddara me muni a bayan tawa take, abu ne da ban taba kawowa ba shi ne rabuwa da Sahibi, it was last thing da ya taba zuwa kaina amma kalla kaddara yadda tazo ta ruguza komai, wai ni ce ni Nanah nake cewa bana son tashin hankali, ni uwar fada rayuwa kenan.

STORY CONTINUES BELOW

Dake sauran sisters dina basuda kula kamar Aminatu yasa babu wanda ya kuma kawo komai se Amal ita da muke sharing daki tare tace duk na canja, na rage magana ko akwai damuwa nace mata babu. Se ta kyaleni. Washegari wajen six Daddy ya gama shirin shi hakan yasa muka tafi tare, dan zaije kano. Tunda muka bar gida nake bacci se yasa driver ya sake min ac yadda zanji dadin baccin. Ban farka ba seda muka shigo kano sannan na tashi, ya dubeni yana fadin

“Sleepy head!”

Nayi murmushi sannan aka tsaya na kuskure bakina muka cigaba da tafiya, a Abdullahi Bayero road nan muka shiga, can karshen layin wani gida an saka tampon da mutane kamar ana zaman makoki. Mukai parking dan nesa daga gurin, Daddy ya dubeni yace

“You wait inside bari mu dawo”

Kaina na gyada na juya ina kunna wayata dan na tambayi hibba suna ina ne, messages sosae suka shigo min kusan duka na Aliyu ne se na Hibba. Ban duba ko daya ba nayi dialing numbers din Hibba amma bata dauka ba, se nabi message thread dinta naga tace min zaayi lecture a compound pharmacy zaa hada constituent susp Amoxicillin da syr pcm. Kashe wayar nayi dan time din 9am ne akwai sauran lokaci. Idanuna na lumshe ina yanke hukuncin se dare zan zauna na kira Aliyu mu gama magana dashi, ya kamata tunda yanzun na fara jin saukin abinda nake ji.

Daddy naga ya taho, bayan shi da wasu mutane se security din shi da kuma driver dinsa, yana isowa ya leko ta window yace

“Daughter fito kiyiwa Aliyu gaisuwa”

Gabana ya fadi naji wanne Aliyu kuma ana zaune lafiya, i hope ba dai Aliyu nawa ba , ba Sahibi ba ko? Fitowa nayi ina gyara zaman mayafin jikina, nan idanuna ya sauka cikin nashi,a take naji muguwar faduwar gaba ta saukar min, ya rame yayi baki, idanun shi looking sleepy, damuwa da kuma tashin hankali. Kallona yake da dukkan being dinsa, tamkar zai zuke ni da idanun shi, se naji wani feeling yayi rushing daga kafafuna zuwa tsakar kaina, kafafuna suna rawa amma idanuna na cikin nashi, na manta da mutanen dake gurin, shi kawai nake gani. Daddy ya taba ni hakan yayi snapping dina daga cikin kallon da nake masa, wani numfashi naja me karfi na gaida na gurin nace

“Ya hakuri?”

Duka suka amsa da Alhamdulillah but amma i need explanation waye ya rasu, na juya zan koma naji muryar shi yace min

“Munib ne ya rasu”

Juyowa nayi da sauri idanuna kamar zasu fadi kasa saboda yadda suka bude nace

“Yaushe ? Me ya same shi? Innalillahi wa Inna ilaihil rajiun! Ayya Allah ya jikan shi ya masa rahama kayi hakuri!”

I know how much that kid meant to his dad, zance daya biyu zai ce Munib, wani lokacin har tausayin yayan da zan haifa masa nake, dan gani nake Munib ya cike dukkan wani gurbi. Amma kalla Allah ya dauke abin shi, ganin zanyi kuka yasa na koma motar na kifa kaina ina kuka a hankali, abu goma da ashirin, kukan ganin shi nake, ina ganin shi ina hango tsantsar soyayya ta cikin idanun shi, idanun shi nuna min how much he missed me, idanun shi na nuna min tashin hankalin rabuwa dashi ga kuma tashin hankali riskar mutuwar abunda yafi soyuwa wajen abinda nake so, ya ilahi! Ina zan tsoma raina naji sanyi!

Kamar Daddy yasan tunanin da nake ya miko min ruwa me sanyi nasha and i felt some easiness rushing through my veins, tabbas ruwan sanyi shi kadai yasan inda rai yake, dan kuwan ya sanyaya min nawa. Tunda muka bar gurin Daddy ke yimin nasiha yana fada min na dauki komai yazo rayuwata matsayin kaddara, kuma shi yana ganin kaddara babu marar kyau kowacce me kyau ce dan ko duk munin ta end result din me kyau yake komawa, na kuma yadda da hakan sosae amma fa ba yanzun ba se daga baya na fahimci me kalaman Daddy ke nufi. Har kofar compound pharmacy ya aje ni, dan corridor nabi ina gyara zaman lab coat dita, Hibba da Intii na tsaye ko jirana suke oho, Hibba na hango ni ta taho da sauri tana fadin

“Me ya samu wayar ki?….”

Ganin yanayina se tayi shiru kawai ta ja hannuna muka shiga na bawa intii da sauran friends dina hannun muka gaisa, mutumin na shigowa ya fara bayanin da muka riga muka sani, constituents din amoxicillin da group din shi da class din shi, mode of action, chemical formula da komai da ya dangance shi sannan ya kaimu ciki ya fara nuna mana yadda ake hada shi in a powdered form, it was very interesting dan dama na dade ina jiran ranar da zaayi, so se na maida komai a bayan zuciyata na zauna naji na kuma fahimta. Se daya da rabi muka fito kuma mun gama lectures dinmu na ranar se kawai muka tafi zancen project dinmu da muka bayar ayi binding dinsu. A gurin naga wata tana ta kallona da muka hada ido se ta taso tazo ta min sallama tana murmushi tace min

“Kinga inata kallon ki ko?”

Na danyi murmushi bance komai ba tace

“Wallahi da wata Anty na kike kama, kanar taku ta baci wallahi dama da ace tana kasar nan zance tabbas itace”

Se nayi murmushi nace

“Ayya! Nagode”

Hibba tace

“A ina take?”

Se tace mana ai tana South korea acan take zama. Se kuma ta dakko wayarta ta fara nemo mana picture dinta amma se aka rasa, tace dan Allah bari tasa a turo mata dan tana son na gani se supervisor na ya kirani kan na sameshi a buk old site yanzun nan, se kawai mukai sallama banma karba number dinta ba.

Straight ko daki ban koma ba na tari napep se BUK, yana zaune office din shi shi kadai sanyin acn da naji ta nemi saka ni na fara gyangyadi, ina nan tsaye har ya kammalla abinda yake sannan ya dube ni yace+

“Meye topic dinki?”

Nace dashi

“exploring the exciting world of the wonder agents called drugs”

Ya dago ya kalleni yace

“Are you done?”

Wani lokacin project supervisors are annoying, shi fa yace na gama naje nayi binding zuwa friday na masa submitting shi ne yake tambayata ko na gama,

“Sir kace nayi binding ai”

Se ya miko min paper yace

“Add it to your background of study!”

Chapter one ma! Na ayyana a raina karba nayi inajin wani irin bacin rai yana taho min amma se na mishi godiya na fita kawai, napep na kara hawa na koma akth, lokacin da na isa tuntuni yamma ta fara yi dan anyi laasar ma, kawai dai saar da nayi ina period shi yasa. Daki na wuce straight na cire kayan jikina nayi wanka sannan na dawo na kwanta tareda janyo paper na fara dubawa se naji it makes sense idan na kara akan abinda na riga na rubuta. Wayata na dakko daga cikin handbag dita na jona chaji sannan na kunna dan kiran Hibba da kuma Daddy. Daddy na kira na masa ban gajiya, bai kashe ba seda yasa nayi dariya wadda na manta rabon da nayi. Ina kashewa na kira Hibba se naji ringing din wayar karkashin pillow dina. Tsaki nayi na aje wayar dan na tabbatar bata tafi gida ba kenan. Sake dakko wsyar nayi ina duba messages din Aliyu da yayi min lokacin da wayata take a kashe, dukka kusan abu daya ne akan hukuncin da Daddy ya yanke, kalaman da yyi amfani dasu were really heartbreaking, kaina na kifa kan pillow ina sakin kuka, ko se yaushe zan daina kukan nan da nake? Ni kaina na gaji da yinshi gashi har na fara jin idanuna na min kaikayi, dazun dana shiga rana se naji kamar wuta aka saka musu to amma ya zanyi? Banida wani option daya rage kukan shi kadai nakeyi naji dan sauki a raina. Ina wannan halin naji an zauna gefena, da sauri na dago tareda fara goge idanuna amma ina ta riga ta kama ni.

“Kema tunanin da nakeyi kike? Wannan da muka hadu da ita tasan Mom dinki ko?”

Se naji hawayen ya dauke a idona, why am I stupid ne, me yasa ni ban ayyana hakan ba se Hibba ce ta kawo hakan a ranta, ni tunanin mummy take nufi shi ne abu na karshe da yazo cikin zuciyata. Kallon Hibba nayi nace

“Could it be mummy take nufi ?”

“To da wa take nufi? To kukan me kikeyi idan ba na wannan ba?”

Se nayi shiru ina wasa da yatsuna kafin nace

“Ni fa banyi tunanin hakan ba ko kadan, ta baki number ta?”

Kai ta girgiza cikeda mamakin wauta irin tawa tace

“Kukan me kikeyi?”

Se naji zuciyata ta karye se na kara sakin wani kukan ina fadin

“Hibba! Daddy yace bazan aura Aliyu ba!”

“Kamar yaya? Innalillahi wa Inna ilaihil rajiun! Wani abun ne ya faru kuma?”

Gaba daya se naga hankalinta ya tashi, idanunta sun ciko da kwalla , kaina na girgiza na fara fada mata abinda ya faru daki daki har kawo dazun dana hadu dasu

“Dama haka ake ji Hibba, haka pain din yake? Ji nake kamar na ciro zuciyata na yar da ita gaba daya na huta. Anya zan iya rayuwa kuwa?”

Se wani kukan ya kara kwace min, it pains sosae idan har ace nasan power of love da ban cika baki ba, bansan ba ko cika bakin dana dinga yi ne yasa komai ya kwacube min lokaci daya. Hibba ta dinga lallashi na tana ta sympathizing dani bata san wannan sympathy da take nunawa ba shi ke kara breaking dina.

STORY CONTINUES BELOW

Da daddare na gama karatu ina ayyana ko na kira Aliyu? Amma idan na kira shi kamar ina kara bashi hope ne dukda har lokacin bamuyi magana ba, wani irin son naji muryar shi kawai nake, se naji inama lokacin da muke waya nayi recording da yanzun kawai sede nayi playing naji, nasan jin muryar shi kadai zai saka min nutsuwa. Wayata ta katse ni i was hoping naga kiran daga Oga Aliyu ne amma se naga kiran daga gurin Anty Sumayya ne, se na dauka muryata can kasa muka gaisa, tace min Daddy ya kira su ya fada musu abinda yake faruwa

“Kiyi hakuri kinji Nanah better days are coming inshaaa Allah, kada ki ce hakan zata kara faruwa aa wannan kaddara ce daga Allah so yake ya jarraba ki yaga imaninki”

“Anty to ya zanyi da zafin da nake ji cikin zuciyata? Ji nake kamar zata fito saboda bugun da take”

“A hankali zata daina Nanah, kede kiyi addua sosae sannan ki maida hanakali ki kare karatun ki cikin nasara kamar yadda kika saba.”

“Wacce adduar zanyi?”

Dan a lokacin ji nake duka kwakwalwata ta, nasan kilan kuce ina exaggerating feeling din ko? Ba zaku gane ba indai baku taba experiencing me ake ji a jilted love ba. Dariya tayi tana mamakina tace

“Nanah ina hisnul muslim dinki yake? Nan zaki tsinto addu’oin da zakiyi, i assure you zakiji hankalin ki ya kwanta.”

“Inshaaa Allah zanyi Anty, to amma ya zanyi da Aliyun kuma”

“Daddy ya fada masa ai so ke ba se kinyi masa bayani ba, kawai dai kibi a hankali ku rabu, ki rage numbers of phone calls da kukeyi a rana, a haka zaki wayi gari babu shi. Kinsan Allah yake da plan so far duk wannan abin idan Allah ya nufa ke matar shi ce to duk balai se anyi, nasan kin tuna yadda biki na ya kasance, kin tuna case din da akai har akayi auren Nasiba daga baya akai nawa. Nasan ba zaki manta ba, ina yawan bawa yan mata da suka samu kansu cikin yanayin ki, komai lokaci ne gashi yanzun lokaci yayi, I still remembered the days da nake kuka ina rokon Allah ya kawo min dauki, Allah bai kunyata ni ba nayi aure kuma wanda nake son shi na aura, so abinda nake so ki gane duk balain matar shi, duk yadda Daddy yake kin abin idan Allah yayi zakuyi aure to tabbas se kunyi saboda haka Allah ya kaddara, idan kuma dama yasa ku hadu ne to share memories shikenan babu yadda zamuyi se kuma mu jira right person yazo yayi sweeping dinki ku tafi.”

Tabbasa maganganun Anty Sumayya kept me going sede to some extent ina ganin kamar misguiding dina tayi, da ace dai ta barni yadda na saka raina cewar rabuwa zanyi dashi ina ganin da komai yazo min da sauki. Bayan mun gama waya na janyo hisnul muslim ina duba adduoi kuma na samu wadda nake so haka nayi ta maimaita su har bacci me nauyin gaske yayi nasarar dauke ni.

Bayan kwana biyu na dan rage damuwar da nake ciki amma kuma saboda kukan da nake idanuna se na dama ya tabu, ban taba sanin da gaske kuka yana saka ciwon idanu ba se akaina, idona na dama yayi jawur tareda kankacewa, idan zan fita se na nemo glasses na saka saboda da zarar rana ta taba idanuna se naji kamar an saka min barkono ciki.

“Kizo muje gurin shi ya duba idanun ki mana”

Hibba ta fada a kusan karo na bazan iya irgawa ba, nace

“Waye shi din?”

Nasan saurayin ta take nufi amma dole se na mata haka

“Dr. Noafal fa nake nufi”

“Kinyi min booking appointment ne?”

Harara ta tayi tace

“Kai shi ne fa!”

Na danyi dariya nace

“Nasan shi ne mana, muje to”

Har office din shi mukaje a ophthalmic department, yana zaune shi daya sanye da farin medical glasses gaban shi system din shi ce yana only god knows what, sallamar mu da yaji ya sashi mikewa yana sakin murmushi ma abar kaunar shi, itama idanun ta na cikin nashi tana ta murmushi se naji tamkar na koma dan kwata kwata sun manta dani, Hibba ta fara motsawa da fadin

“Patient na kawo”

Zama yayi yana shafa kan shi yace

“Badai Nanah ba ko?”

“Ita mana”

Kallona yayi lokacin dana karaso ciki ina gaishe shi ya amsa yana fadin

“Me ya sameki?”

Shades din dake kan fuskata na cire hakan yasa ya fara min examination yana recording aftet 30minutes ya fara bayani akan i need a pair of eye glasses saboda tun kafin yanzun dama shi ranar da ya fara ganina yasan idanuna basu da lafiya balle kuma yanzun. A office ya barmu ya fita akan zai dawo se ta zauna tana fadin

“Nanah dan Allah karki makantar da idanun ki akan abinnan kiyi hakuri ki daina kuka haka”

Kaina na gyada nace

“Nifa I’m ok na gaya miki”

“Kice min you will be ok dai”

Hakanan muka cigaba da hira dan kusan ita takeyi, bai jima sosae ba ya dawo da abu hannun shi, ya aie a gabana yace

“I hope frame din zaiyi fitting taste dinki”

Dauka nayi na bude sega glasses masu kyau, na kalla Hibba dake kallon shi sannan na kalleshi nace

“Har kayi? To bari na maka wiring kudin ta account dinka”

“Dear kina jinta?”

Ya fada yana kallon Hibba da take murmushin jin dadin abinda yayi min, hannunta na kama na fara masa godiya yace babu komai ai a gurin shi we deserve the world.

Bayan sallar isha ina duba bind copy na project dina ina ayyana irin wahalar da na sha akan topic din da bama ni nayi choosing ba, fin karfi akai aka bani shi, amma at the course of research nayi exploring abubuwa da dama wanda da zaayi amfani da project dina am sure wasu abin akan magani zasu gyaru. Wayata ta fara ringing, janyo ta nayi ina jin wakar dake tashi wadda na sakawa mutum kwaya daya tak wato Aliyu Sahibi na❤️

Nothing is gonna change my love for you, you ought to know by now how much I love you, one thing you can be sure of I never ask for more than your…..

Kiran dana kusa sati ina anticipating shigowar shi, a hankali nayi sliding tareda karawa a kunnena, muryar shi ta doki kunnena wanda shigar sound waves din seda ya saka dukkan jikina ya amsa, se lokacin zan iya measuring how much ive missed him.

“Kina jina?”

Kaina na girgiza ina dawowa daga tunanin dana luluka nace

“Mhmmm”

Yace

“Ina jiran ki, can we talk?”

Ban bashi amsa ba na kashe tareda mikewa na dakko bubun material din dana saka da safe na mayar bayan na goga oil perfume dina sannan na zura slippers dina na yafa veil na fita, gabana yanata faduwa amma zuciyata dauki take, idanuna murna suke zasu yi arba da abinda suka kwana biyu basu gani ba.

About AIS

Check Also

ZUMA CHAPTER 11 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 11 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng  Bayan watanni hudu nayi nisa cikin service dina, duk …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *