ZUMA CHAPTER 7 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 7 BY SHATUUU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Daddy ya cigaba da kwada ma yaya Mariya kira, hankalin shi a mummunan tashe ya mike tareda riko hannuna ya fito yana sake kiran yaya Mariya, da ace bamu tada generator ba babu abinda zai hana makwabta jiyo muryar Daddy.+

“Nawwara! Amina!! Amal!!!”

Kusan dukka a tare suka fito kowacce sanye da kayan bacci, alamu sun nuna basu masan a yadda suka fito ba, dan kayan baccin mu yadda kuka san dakin miji zamuje, kanshi ya dauke daidai fitowar baba Asabe tana fadin

“Baban Nanah lafiya? Me…”

Se tayi shiru ganina a halin da nake ciki, sauran sunyi shiru kowa tunani yake me ya sameni haka? Sun san lafiya nake zaune Ummu ta kirani akan naje Daddy yana kirana, to me ya canja ni lokaci daya haka.

“Asabe zanje zan kai Nanah asibiti, zamuje da Nawwara da Aminatu. Ki zauna da sauran”

Bai ma jira me zasu ce ba yaja hannuna muka tafi, Nawwara da Aminatu suka zumbulo hijab suka biyo bayan mu, driver na ganin Daddy ya taso amma Daddy ya daga masa hannu, da kanshi ya tuka motar yana jera min sannu da bazan iya irgawa ba. Bamu tsaya a ko ina ba se a cikin ER din Rasheed shekoni dake cikin garin Dutse. Tambayar da suka fara yiwa Daddy ita ce ko ina da asthma, Daddy yace ko daya ban taba ma yin hakan ba, yasan dai ya fada min abu ne se yaga idanuna sun kara girma, lokaci daya na tamke zuciyata haka na fara kokawa da numfashi na. Likitan ya kalleni yace min

“Fadima! Look up and look at me!”

Dagowa nayi kamar yadda yayi min umarni na kalleshi yace

“Brace yourself, take a deep breathe!”

A hankali naja numfashi amma dukda haka numfashin bai daidaita ba se nurse din ya kawo min leather gloves yace na hura mata iska, hurawa nayi da karfi a hankali naji jikina yana saki na lumshe idanuna, sannan na bude jin bugun da zuciyata yake yana raguwa tareda normalizing. Fitowa sukai yace da Daddy abinda nayi Panic attack ne, da dukkan alamu abinda ya fada min ya tsorata ni sosae shiyasa, zai iya zamana zan kara yi indai na tsorata ko kuma nake jin tsoron faruwar wani abu, to repeated episode na panic attack din zai zama panic disorder.

Gaba dayajikin Daddy yayi sanyi yazo inda nake ya kama hannuna fuskar shi kamar zaiyi kuka yace

“Nanah sannu kinji?”

Kaina na gyada kawao saboda bakina yayi min nauyi na kasa budewa dukda so nake nayi hakan. Daga karshe suka sallame mu muka tafi gida. A mota ma ina gaba na lumshe idanuna inata blocking kwakwalwata akan kada ta tuna komai daya faru a parlon Daddy ta bari se na nutsu idan yaso se muyi tunanin amma ina taki bani hadin kai se echo

“kimin alfarma ki hakura da auren Aliyu!”

Inaga tunda nake ban taba jin munanan kalamai irin wannan ba. Yana packing na fito da hanzari na nufi daki baice komai ba yace su kula dani ya tafi. A gidan dukkan su idanun su biyu suna jiran dawowar mu, kowa sannu yake jera min with so much care and affection, sede na gyada kai kawai amma bakina yaki yin magana, ji nake harshe na kamar ya kumbura, kamar ya cika min baki. Daki na wuce nayi alwala sannan na cire hijab din jikina, wanda na riga na jika shi da ruwa saboda dashi nayi alwalar, banyi tunanin cire shi ba. Wayata na janyo na kashe ta duka dukda naga alamar missed calls da message amma ni bai dameni ba. Kwanciya nayi tareda jan bargo su kuma ganin hakan yasa dukkan su yi min sallama suka bar Amal wadda tare muke sharing dakin da ita. Kwanciya tayi babu dadewa bacci ya dauketa se na mike na sakko na nufi toilet na rufe kofar tare da zama kan toilet seat na kifa kaina akan cinyoyina na saki kuka, se da hawayen suka fara sakkowa naji wani abu me daci yana taso min tun daga cikina har kan harshena, wani katon abu ya tsaya a makogarona. Nayi tunanin da zarar na fara kuka zanji dadi amma se naji akasin haka, hankalina ma kara tashi yayi, can kasan zuciyata fal yake da tsoro yadda zan iya rayuwa ba tareda Aliyu ba, yanzun shi kenan? Fatima taci bulus, da nasan ita ce wadda tazo gurin Daddy da safe babu wani dalili dazaisa na gaishe ta, shiyasa naji muryar ta very familiar. Nayi kuka kamar zan fita da zuciyata waje, na mike naje na kalla mirror dake cikin bayin dukda da dare ne baasan kallon mudubi amma ni ina ruwana? Me ya dameni inaga a wannan lokacin ko aljanu na gani rungumar su zanyi. Fuskata tayi kacakaca da hawaye, idanuna da suke fari sunyi jawur kamar garwashin dake ruruwa, kallon kaina da nayi se naji zuciyata ta kara karyewa na kifa kaina akan sink na cigaba da kukan wanda bansan har yaushe na dauka ina yi ba.

Ban taba ganin dare me tsawon wannan ba a rayuwata, gari yaki wayewa bacci yaki zuwa, tun ina kukan da nishadi har na hakura se hawaye dake gangarowa kawai, ban taba gaskata ana kwana kuka ba se da abin yazo kaina. Karshe nayi alwala nazo dan nayi sallah amma ina mikewa se naji I’m weak se na kara fashewa da kuka a haka nayi sallar da babu abinda nake karantawa se kuka nasan Allah ya san me nake nufi, ita kanta sallar bansan rakaa nawa nayi ba nidai kawai sallah nake babu kakkautawa kuma shima kukan babu kakkautawa. A haka aka kira sallar asuba se naji bacci me karfi yana neman daukata haka ina gyngyadi na jira akai sallah nayi sannan na haura gadon na kwanta tareda tashin Amal dake gefena, ban jira ta mike ba na kwanta bacci me nauyi marar dadi ya daukeni.

Bani na farka ba se wajen sha daya na safe, babu kowa a dakin se ni daya amma a gama gyara shi tas, mikewa nayi na shiga toilet na yi brushing nai wanka sannan na fito, Aminatu na zaune da wayar ta a kunnen ta tana waya, shiryawa nayi inajin nauyin dake kirjina ya ragu amma still idanuna basu washe ba sema dan dagawa da sukai saboda kukan da nayi, fuskata ko digon murmushi babu akan ta maganar ma ji nake kamar bazan iya yi ba.

“Yaya Nanah ya jikin?”

“Alhamdulillah!”

Na bata amsa da wata hargitsatsiyar muryar dani kaina I’m not sure idan murya ta ce, Aminatu kallona tayi nasan so take ta tabbatar ko ni din nayi maganar, kaina na dauke na zura abayar dana fito da ita sannan na daura dankwali. Tare muka fita da ita zuwa parlon kowa ya rungume ni Suna tambayata yadda na kwana da jiki, na amsa da sauki sannnan na kwanta akan kujerar ina tunanin ko ya Aliyu yake ko Daddy yace masa ya dakata da turo war? Jiya yake fada min how important ranar nan take dashi, jiya muka kulla alkawarin komai ruwa, komai iska komai zafi we got our back, amma kalla yadda ranar ta kare. Se naji kuka ya taho min hakan yasa na mike da sauri nayi daki tare da fadawa toilet na dinga kuka kamar raina zai fita, can naji ana knocking se na kunna ruwa saboda zai hana aji sheshekar da nakeyi. A haka na gama na wanke fuskata na fito ban samu kowa ba se na koma parlon. Daddy na zaune ina zama nace

“Daddy good afternoon”

“Afternoon ya jikin naki”

“Alhamdulillah!”

Na bashi amsa sannan na dan kwanta tareda lumshe idona se Naji yana cewa

“Dama zan ce muku na bada aurenku kuma na saka ranar nan da watanni uku kawai, Allah yayi muku albarka”

Se naji inama dani a ciki, inama hakan bata faru ba, inaji Aminatu na squealing har Daddy yana fadin

“Aminatu murna kikeyi?”

Se sauran suka fara dariya ya mike tare da cemin

“Nanah zo mana”

Yana fita na mike inajin gabana yana fadiwa, bansan me zai fada min ba kuma, kilan yace ya bada auran nawa sede wannan wish din nawa ne, wannan zuciyata ce take da wannan burin. Amal tace

“Yaya Nanah bakya murna ne?”

Ban ma jiyo ba balle na bata amsa na wuce parlon Daddy, yana zaune na zauna nima ina tunanin me zai ce min kuma

“Nanah, nasan ba abu ne mai sauki ba rabuwar da nace kiyi dashi ba, amma ke yata ce bazan iya trading kwanciyar hankalinki ba. Ina son kiyi hakuri ki fawallawa Allah wani zai zo , tunda har matar shi zata iya tako kafarta gidannan tayi min warning bana tunanin empty threats ne kamar yadda Aliyu ya fada, she meant duk abinda ta fada. Kiyi hakuri kiyi min wannan alfarmar Kiyi addua nima inayi miki Allah zai duba lamarinki kinji?”

Kaina na gyada ina goge hawayen dake sakkowa daga idanuna, ko Yaya Aliyu yake da yaji labarinnan? Ko me yakeyi ko wanne hali yake ciki? Yanzun shi kenan a kiftawar idanu komai ya lalace, wanne wacce irin kaddara ce me muni? Me yasa rayuwa zatai min haka? Me yasa kaddarar bata zo ba tuntuni se yanzun? Wannan shi ne abinda ya dinga min yawo a kaina , kafin washegari na rame saboda kuka da tashin hankali, nidai bazan yi jayayya da Daddy ba amma kuma bazan daina tsinewa Aliyu ba, tunda muke bamu taba awa goma idon mu biyu bamui waya ba se wannan karan da na kashe wayata dukda ciwon da zuciyata takeyi na rashin jin muryar shi amma ya zanyi? I’m helpless!

_Time will never change the things you told me, love will bring us back to me and you, if only you could see!_FATIMA+

Tana zaune a parlo ta gama yiwa little baby dinta wanka, tana shiryata tareda tuna irin artabun da aka sha kafin ta yadda ya saka Fatima a cewar ta dan me zai saka sunan Nanah, kunji fa bayan itama sunan ta Fatima kuma tasan marikiyar Aliyu Fatima ce. Kamar daga sama taji muryar Aliyu daga cikin bedroom yana fadin

“Eh ranar asabar mahaifinta yace na tura iyayena zasuyi magana ta karshe….A’a kowacce gida daban….Ban fada mata ba nafi son se magana ta kankama tukun…..To babu damuwa zan sameka acan!”

Idanunta ta runtse dan duk tunanin ta Aliyu ya hakura tunda taji tunda akai case din bata kara ganin wani suspicious abu ba, hakan yasa itama tayi kokarin maida abin bayan zuciyarta amma ashe ita haukar ta take shi kuma yana nan yana munafurta ta. To tabbas da ita yake magana kuma idan yaga ya auri yarinyar nan sede idan ita din bata numfashi. Ranta a mugun bace ta jefa Fatima a bayanta ta daure da zani sannan ta cigaba da kawar da kayan da suke a parlon sede hakan kara dagula mata lissafi yake, ji take kamar ta wuce cikin dakin ta bubbuga bakin shi Aliyu da take ganin tozarta ta zaiyi. Amma idan tai haka tabbas ta barar da plan da tayi tun tuni saboda counterattack.

Fitowa Aliyu yayi hankalin shi yana kan karanta message din da Nanah tayi masa, se smiling yake kamar bakin shi zai yage, ita kanta Fatima ba zata tuna last time da ta ganshi so cheerful haka, tun kafin case ya hadata da Nanah.

“Zan fita, se zuwa anjima zan dawo, Akwai abinda zan taho dashi?”

Tana kakkabe shawl din Nanah data kwaso daga kan dryer ta kalleshi wani mugun kishi na cinta saboda yadda taga yasha bugaggiyar getzna brown wadda ta mishi kyau a farar fatar shi, kanshi sanye da hula Bamanga,

“Ina zaka je ne?”

Ta fada tana tsare shi da idanu, kanshi ya girgiza yace

“To fa! Zanje office mana”

“Ko kuma gurin waccan karuwar ba, Aliyu kaji tsoron Allah”

Ranshi a bace yace

“Ke dallah rufe min baki, kada ki kuskura ki kara cewa wata karuwa! Da tsoron ki zanji rubbish!”

Yana fada ya fice daga gidan saboda baya son ta bata masa rai. Tunda ya fita itama ta dauki mayafinta ta fita zuwa gidan Bilkisu dake babu wata tazara tsakanin su. Tunda taga mota kofar gidan ranta ya kuma baci dan tana da tabbacin bilkisu na tareda wani katon amma a halin da take ciki ba wannan ne damuwar ta ba, damuwar ta ya zatayi da Nanah. Tana shiga su kuma sun fito daga wanka, dake gidan gafiya fito na bugeki ne yasa toilet din tsakar gida yake. Bilkisu na kwance jikin wani gabjejen mutum shi kuma se smooching dinta yake, Fatima taji kamar tayi ihu dan idan akwai abinda take adawa dashi to zina ce, tayi fadan ma Bilkisu tayi waazin amma kwata kwata Bilkisu taki bari ya shiga zuciyarta. Sallama tayi wanda yasa Bilkisu kallon sashen da take tace

“Mom Munib kece haka? Sorry bari na saka kaya shiga dayan dakin.”

Ta fada tana dariya kasakasa tare da sake makalkale alhajin, kai ta girgiza ta wuce ciki tana maida abinda ta gani bayan kwakwalwar kanta saboda bashi ne lokacin magana ba, rayuwar Bilkisu ce idan taga zata iya ta cigaba. Bata jima ba kuwa ta shigo tana fadin

“Mom munib ai da kin kirani da kanki haka?”

“Zauna Bilkisu ina cikin balai da masifa!”

Yadda ta fada zakai tunanin wani abinne me girma gaske though ita a gurin ta wannan din babbar masifa ce me firgitar wa ace mijin da ta yiwa lakani da mijin mace daya shi ne zaije ya toxarata ta a idon duniya ya auro wata, wannan wasa ne, Aliyu bai san wacece ita ba, bai san a kanshi babu abinda ba zata iya ba dan taga ta zaina ita daya a gidan.

STORY CONTINUES BELOW

“Me ya faru? Kin ganki kuwa duk a birkice”

Bilkisu ta fada tana bata dukkan hankalin ta, tsaki Fatima tayi tace

“Ai girman Allah yasa ki ganni a nutse haka, ni ina can nasan na gama tufka akan waccan shegiyar Fatima ashe bai tufku ba, ashe wai asabar zaayi gaisuwa”

“Gaisuwa? Wai kina nufin ta iyaye ko me?”

“Ita fa! Ya zanyi Bilkisu”

“Har option kike dashi, ai gobe safiya nayi zakara ya baki saa kije kiyi wa uban yarinya kashedi, dama tuntuni seda nace kiyi haka tsoron mijinki ya hanaki yin komai, amma idan uban nada hankali bazai bari ayi auren ba”

Tayi shiru for a while tana tunanin anya taje har wannan extent din, amma shi kadai ne hope dinta na baza ayi auren ba amma kuma ya zatayi da Aliyu

“To ya zanyi da Aliyu?”

Bilkisu tayi dariya sosae tace

“Se ki fututtuke kice bake bace, se kiyi amfani da weakest point dinsa ki hana shi yin komai, nifa da nice ke da tuni nasa teacher na zaure ya hargitsa su to ke se kice Allah zai kama ki, naga akwai lokacin da zaki tuba”

Hararar ta Fatima tayi tace

“Kede bakida kai wallahi, ance miki we’re guaranteed of tomorrow, ko yanzun ran mu zai iya fita. Zan dai je amma gaskiya bazan yi shirka ba”

Haka ta koma gida tana sakawa da kuncewa, amma lallai dole ne se taje Dutse taga wacce yar matsiyatan ce take neman hanata zaman lafiya. Washegari da sassafe Aliyu ya fita what a coincidence ya tafi wani daurin aure shida mahaifin shi a gombe state. Yana fita itama ta shirya ta dauka yaran ta kaisu makwabta sannan ta kira Bilkisu akan tazo su tafi amma Bilkisu tace sun tafi Abuja itada mutumin data gansu tare jiya da yamma bayan ta tafi. Tasha taje har lokacin zuciyatta tana gargadar ta akan kada fa tayi abinda zatayi dana sani amma ina hankalinta ya gushe ita dai kawai burin ta ta cimma bukatar ta kawai. Tana sauka a tasha ta samu acaba da zai kaita gida dubu kamar yadda address din ya nuna, tana shiga cikin unguwar taga gidaje kalakala wasu masu kyau wasu kuma tun asalin ginin gidan wanda ya tsufa yaci duniya. Ta tsaya tana kallon wani kwarababben gida tana ayyana wannan shi ne gidan su Nanah, amma se ta kara duba sunan maigidan taga Ibrahim Ginsau hadejia. Wani saurayi ta tambaya ya nuna mata wani gida dake facing dinta, da shakku tace

“Ibrahim hadejia ginsau fa”

Yace mata

“Eh badai commissioner of justice ba?”

Kanta ta girgiza dan baa ce mata haka ba tace

“Yarinyar shi tana BUK”

“Shi ne dai”

Ya fada sannan ya wuce abin shi, ita ba haka Bilkisu tace mata ba, tace mata yar matsiyata ce, kamar yadda Fatima take to amma wannan kankararren gidan da ke gabanta fa? Wucewa tayi ta nufi gate din gidan, tayi knocking na kusan five minutes sannan aka bude karamar kofar, police din yace

“Ya akai?”

“Nazo ganin mai gidan ne”

Se ya ruf kofar ya koma can ya dawo yace ta shigo, ajiyar zuciya ta sauke ta shiga, lokacin Daddy ya fito da niyyar zuwa office, Ta kalleshi sau daya taga ya mata kwarjini se taji inama bata zo ba amma tunda ta fito har tazo din to gwara ayita ta kare kawai.

“Daga ina haka? Banganeki ba”

Tace

“Ai baka sanni ba shiyasa, daga kano nake”

A tunanin shi daya daga cikin yan uwan yaran shi ne se ya mata iso ciki bayan ya dakatar da driver. A parlon shi ya sauketa har lokacin kallon gidan take, kenan Aliyu zai auro mata yar masu arziki tazo ta raina ta, idan ba haka ba a talauce ya aureta ya zai auro yar wannan gidan.

“Ina jinki”

Ya fada bayan ya zauna, ta gyara zama tana fadawa kanta ta kashe gobarar nan for life, idan idanunsshi suka hanata to tabbas ta samu matsala kuwa.

“Sunana Fatima matar Aliyu da yake neman auren yarinyar ka Fatima”

Da mamaki Daddy ya kalleta, hakan yasa ya gyara zaman shi yace

“Lafiya?”

“Ita ta kawo ni , nazo na fada maka ni da kake ganina zan iya komai dan na hana wata auren mijina, mijina nawa ne ni kadai duk wadda ta kuskura tayi mistake din shiga gidannan wallahi sena haukatata kaji na rantse har da Allah, shi yasa nazo na fada maka tun yanzun kasan me zakai”

Daddy yayi shiru cikeda tsoro lokaci daya maman Aminatu ta fado ransa sannan ya tuna Maman Ummu yadda suka dinga banka masa asiri, shifa duniya yana tsoron asiri, lokacin ne na laiko nayi ma Daddy sallama, ita kanta data ganni seda tasha jinin jikinta. Bayan na fita Daddy yace

“Shi ne dalilin zuwan ki? Shi je kawai matsalarki?”

“Ka daina cewa kawai, a gurina wannan yakin na rai ne, dan a yadda nakeji zan iya yin komai indai babu wadda zata aurar min mijina”

Kai Daddy ya gyada yace

“Ina miki albishir yata bazata aura mijinki ba, ki koma gida ki jira hunkucin makaranta duniya.”

Magana ya fada mata amma ko a jikinta a ganinta burin ta ya gama cika, ta tafi zuciyatta fes ko me Aliyu zaiyi yayi as far as ubana ya hanani auren mijin ta ita fa taci riba, dan ita ba haka taso masa ba so tayi ta musu hauka a cikin gidan amma wannan katon gida, police officer da ta gani, matsayin Daddynah da nata matsayin yasa tayi haka kuma gashi taci nasara!”Daddy yana kirana idan na dawo zan kiraka”+

“Ok bye for now”

Ya fada kamar yadda yake fada min kullum, aje wayar yayi ya mike daga ya dubi Alhaji Anas dake zaune a gefen shi, hannu ya mika masa yace

“Ni zan wuce gida, a gaida madam”

Kai Alhaji Anas ya gyada yace

“Zasuji, amma ka fada masa sun maida zuwa dutsen se Sunday”

“Tun tuni ma , Yaya na gama fada min na kira shi na fada masa”

“To ubangiji Allah ya kaimu”

Daga haka sukai sallama ya tafi ya barshi anan zaune, yana isa gida ya tarar Fatima har ta kwanta, ita a yunkurunta kar ya mata wani abun dan tasan zuwa yanzun Daddy ya sanar da Aliyu komai ta kuma san idan zai shigo zai shigo ne tamkar mayunwacin zakin da ya jima bai ci ba, tasan karshen abinda zai mata ya mare ta kilan har yace taje gida, to ita ta shiryawa wannan tasan na lokaci ne da zarar ya wuce shikenan shima zai dangana ya koyawa kanshi hakuri, balle tasan ma wacce mace Aliyu zai so kamar yadda ya sota? A ganin ta ai babu wata mace da take da tata saar. Shikam ganin ko ina a kashe yasan ta kwanta kuma hakan nada nasaba da yadda suka rabu da safe, lemu yasha sannan yayi wanka ya zo ya kwanta tareda fara kiran Nanah amma har yayi mata wajen four missed calls bata amsa ba se kawai yace may be itama tayi baccin.

Washegari bayan yayi sallar asuba kiran Daddy ya shigo masa, gabansa ba karamin faduwa yayi ba ganin kiran da sassafe which is unusual gashi tun kafin ayi assalatu yake kiran Nanah wayatta a kashe, kada wani abu ya same ta kenan. Dauka yayi yana jin yadda bugun zuciyar shi ke kara gudu haka kurum yaji kirannan babu dadi

“Daddy barka da asuba”

“Barka dai Aliyu ya iyali”

“Lafiya lau Daddy”

“Magana nake so muyi dakai, ina son kaji ni da kwakwalwar ka bada zuciyar ka ba, ina son ka nutsu ka saurare ni”

Bai san lokacin da ya zauna ba akan dutsen dake gefen shi, sede bai ce komai ba Daddy ya cigaba da fadin

“Matar ka Fatima tazo jiya…”

“Fatima kuma?!”

“Eh ita fa, tazo wajen sha daya na safe, ba warning tayi min ba, a nutse tazo sede tayi threatening dina akan idan na aura maka yata to zatayi ko menene na ganin ta hana auren ko ta fitar da ita…”

Se yayi shiru yana kara jujjuya hukuncin daya yanke, yana tuna lokacin da yace da Nanah ya fasa aura mata Aliyu irin abinda tayi, abu ne da bazai taba mantawa dashi ba saboda ya kadu iya tsorata yayi, babu abinda danshi daya fi so da kuma tausayi kamar Nanah, yana sonta tsananin so amma babu yadda zaiyi bazai iya trading zaman lafiyarta da kwanciyar hankalinta saboda abinda take so ba, yasan rabuwar masoya babu dadi amma zatai coping a sannu a hankali

“Daddy dan Allah kayi hakuri dan Allah Daddy”

“Aliyu me yasa kake bani hakuri bayan ba laifin ka bane, itama ba laifin ta bane tunanin tane hakan, ita tana ganin it’s the only way of keeping you to her. Ita nata salon kishin kenan. Kayi hakuri amma fadima tayi kankanta ta fuskanci duk wannan abun,”

“Daddy me kake so kace?”

Ya fada kunnuwansa suna tsoron abinda Daddy zai furta,

“Aliyu kayi hakuri amma na fasa aura maka ‘yata Fadima”

” Daddy wallahi ina sonta itama Fatima iya baki kawai ta fadi hakan amma ba zata iya aika tawa ba”

HDan murmushi Daddy yayi dama yasan zaayi hakan ya kuma shiryawa hakan.

“Aliyu matar ka meant dukkan abinda ta fada, zata iya saboda da tana tsoro ba zata baro kano ta taho har nan dutse ba tareda sanin ka ba sannan tazo tayi only empty threat? Aa kayi tunani. Ina maka fatan alkhairi kai da ita”

Bai jira Aliyu ya kara magana ba ya datse call din, Aliyu ya sauke wayar yana jin wani jiri yana neman yadda shi daga kan dutsen da yake zaune, kanshi ya kwantar a hannun shi ya cigaba da jujjuya maganganun Daddy, ya dauki lokaci da bai san iyakar lokacin ba a zaune yana sakawa da kuncewa. Mikewa yayi ya juya se lokacin ya tuna ashe walk ya fito yi kamar yadda ya saba duk bayan sallar asuba ashe zai riska mummunan labarin. Wayar shi ya ciro yanzun ya gama gaskata abinda Anas da sauran abokan shi ke fada masa Fatima ta raina shi bai isa da gidan shi ba, to shi yana ina har taje Dutse? Yana ina? Nanah ya fara kira amma har lokacin wayar a kashe network ke fada masa, kanshi ya dafe dan yasan akan zancen ta kashe wayarta, se kuma hankalin shi ya koma tunanin ita a wanne hali take ciki, idab shi namiji zaiji abinda yake ji yanzun ita fa mace mai rauni kamar ta?

Iya yadda ya bude kofar zai fada maka tsananin bacin ran da yake ciki, takun shi kadai zai iya saka gaban ka ya fadi balle fuskar shi da tayi jawur kamar tomato, hannun shi yasa ya tura kofar parlon sede cak ya tsaya na wasu mintuna yana kallon wani mummunan sight a idanun shi. Se kuma ya karasa da sauri yana karbar munib daga hannun Fatima dake sanye da hijab bayanta goye da little Fatima dake tsa uban kuka,

“Me ya same shi? Ya naga bakin shi yana kumfa?”

Sakin shi tayi tana kuka tana fadin

“Nima haka na shigo na same shi shi da Munsif”

Marinta yayi a zuciye yace

“Da gidan uban wa kika je da safiyar nan?”

Hannunta ta dafe kuncinta dashi idanunta na kara zubar da hawaye se lokacin ta tuna abinda ta fada

“Kin kurmance ne?”

“Aliyu is not right abinda kake, kaje mu kai shi asibiti tukunna”

Mikewa yayi ya saba yaron a baya ya dauka wallet dinsa ya fice itama ta mara masa baya tana jin duniya ta mata zafi. A asibitin  nassarawa suka kaishi, cikin gggawa aka karbeshi amma ko minti daya baayi ba suka sanar musu ai poison din da yaci ta gama shiga jikin shi so suna tunanin tun a hanya ya rasu. Wani ihu Fatima ta saki tana kankame Aliyu not minding a ina suke, shima tiketa yayi dan support yake bukata, munib dinsa ya rasu? Ya mutu saboda poison, what poison ya ayyana a ranshi. Haka ya dauki gawar suka juya suka koma gida, Fatima nata kuka tana jin inama zata dawo da awanni biyu da suka gabata, inama bata fita ta bar su ba may be da baiji yunwa har yaci naman da ta sawa maganin bera jiya kafin ta kwanta ba, Aliyu bai kuma ba magana ba se rungume yaron da yayi a kirjin shi yana jin yadda zuciyar shi Ke bugawa kamar me gudun marathon, kirjin shi zugi yake masa kamar ana soya abu a gurin. Suna zuwa gida ya fara kiran mutane yana fada musu wasu yana musu message, haka akai janaizar yaron aka kaishi makwancin sa su kuma kallo daya zaka musu kaji kamar kai musu kuka.

About AIS

Check Also

ZUMA CHAPTER 11 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 11 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng  Bayan watanni hudu nayi nisa cikin service dina, duk …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *