ZUMA CHAPTER 6 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 6 BY SHATUUU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A lokacin bayan yayi hanging da zaa bude muku zuciyata ji nake kamar gobara takeyi, tamkar wuta ake rura min haka nake jin wani zafi, gaba daya se jikina shima ya dauki zafin, nan na kwanta akan gado inata kuka ko zan samu naji zuciyata tayi sanyi.+

A bangaren Aliyu yana office na sanar mishi da halin da ake ciki, kawai se ya mike ya fita daga office ya cewa messenger dinshi duk wanda yazo yace dashi ya fita. Seda yayi exiting gate din baki daya sannan ya tare me napep yace ya kawo shi Aminu kano, a ganin shi sanin halin da nake ciki shi ne number one priority dinsa amma Fatima kam ita nata case din me sauki ne. Yana zuwa ya kirani a waya amma seda ya kira for more than seven times ban dauka ba, sunan shi ma bacin rai yake saka min. Ina ganin a gurin shi shine karon farko da yaga rigima ta, ni kaina nasan hankalin shi a tashe yake amma a lokacin ko a jikina,kullum ranar duniya faranta masa nake, kullum rana am making sacrifices for him to amma wannan karon ina jin na gaji dole ko sau daya na tauna tsakuwa dan aya taji tsoro.

Ganin bazan daga kiran ba da gaske yasa shi turo min text yana fada min na yi hakuri nazo waje yana kirana, kada na hukunta shi da laifin Fatima. Amma ban ma kula ba balle na bari words dinsa suyi sinking cikin zuciyata har ya samu galaba a kaina. Bansan iya lokacin da ya dauka yana jirana ba amma yafi awa biyu sannan ya kuma kirana lokacin zuciyata ta dan yi sanyi yasa na dauka amma ko sallama banyi ba balle gaisuwa

“Sahiba! Ina waje ina jiranki, kizo ina son muyi magana”

Kashe wayar nayi na mike na wanko fuskata sannan na zumbula hijab na fita, can na hango shi kan daya daga cikin concrete chairs din da suka kawata gefen Dental clinic, yana zaune kana kallon shi kaga wanda ke cikin matsanancin tashin hankali da kuka damuwa. Yana hango ni ya mike yana sakin min murmushi, se na juyar da kaina ina kara cika ina batsewa. Zama nayi can nesa dashi idan kazo ba zaka kawo cewa tare muke ba zakai tunanin kowa daban yake, tasowa yayi ya zauna kujerar dake facing dina, gurin yayi shiru se karar kadawar bishiyu da ya haifar da sassanyar iska me dadin gaske. Inda ace hankalin mu a kwance yake tabbas babu romantic moment kamar wannan amma ina zuciyata tana nesa da tashi.

“Sahiba kuka kikayi?”

Ya fada hankalinshi yana kara tashi, ko kallon shi banyi ba ya sake cewa

“Kiyi hakuri nasan kilan kin gaji da hakurin da nake baki amma shi ne kawai abinda zance miki…”

“Kaga dan Allah idan da wannan kazo zaka iya tafiya, na fada maka lallai lallai idan kana son na huce to ka bani numbers dinta na kira na rama zagin da tayi min!”

Kanshi ya dafe nasan ayyanawa yake dama haka nake? Ko kuma ya ayyana haka hada mata biyu yake? To ina son yasan mata biyu bana ragon namiji bane.

“Nasan bazaki iya ba, nasan ba haka tarbiyyar ki take ba. Ita ma Fatima she’s pregnant and i think pregnancy hormones ne ke aikin su”

Tsira mishi idanu nayi for quite a while kafin nace

“Ni kake fadawa pregnancy hormones? Ina ruwana dasu nima mace ina period and i also have hormones amma ni inada tunani. Nasan ko ance ka zaba ni ko matar ka zaka zabe ta amma ba sai kazo kana kareta a gabana ba, ina son kasan nima inada gata kuma idan da Daddy zaiji abinda ya faru tabbas se ya fasa baka ni!”

A fusace na mike na nufi hostel na barshi nan zaune da uban tagumi, God! Allah ya yafe min se bayan na koma daki naji me yasa na huce haushina a kan shi? Nasan yanzun ranshi a bace yake kuma ni ce sanadain hakan. Se naji kuncin ya karu memakon naji ya tafi.

Dama Aliyu ai Zaki ne, tankar lion haka ya nufi gidan shi, na riga na gama kunna shi nasan itama zaije ya kunnata kuma na masa haka saboda tasan muhimmanci na a wajen mijinta, tunda ni bazan iya fada da ita ba, to kuwa zan hana su zaman lafiya a gidan su, ni kishi na me sauki ne da tayi hakuri ni banida nufin cutar da ita amma tunda tayi min hakan to tabbas se ta gane kuren ta. A kofar Gida napep ya aje shi ya sallame shi sannan ya tura kofar dake makale jikin gate din data kawata gidan. Yana saka kafar sa sukai kicibis da Bilkisu. Kallon farko ba zaka ce tasan wata kalma wai ita shahada ba, gaba daya batai kama da ahlin manzo ba, tana cikin wata fitted kimolly English gown pink, jikinta an mata adon stones masu kyalkyalin gaske, kanta wani uban wig ne baki sede an mata kalba dashi yan kananana da suka zubo bayanta, kadan daga ciki kuma colored wig akai amfani dashi, wani pink wani gold wani maroon. Haka dai, fuskarta anyi dolling dinta har baka gane ya ainahin kamarta take, farantanta anyi fixing nails tare da saka musu nail Polish golden. Duk wannan abin she still answer sunan musulma kuma baka isa ka kafirta ta ba saboda musulma ce. Ya tsane ta tsana me tsanani sede koda wasa bai nunawa kuma bai taba hana ta zuwa wajen Fatima ba. Washe baki tayi tace

“Ango ango!”

Kallonta yayi yace

“Bilkisu sannu!”

Daga haka ya shige ciki ita kuma ta tuntsure da dariya ta ficewar ta. Fatima na zaune akan carpet tayi daidai tana shan fruit ga tsohon ciki da haihuwar shi ke kwana kusa, yaranta su munif sunata wasa abinsu. Seda gabanta ya fadi yadda taga fuskar Aliyu a hade se taji taste din abarbar da take sha ma ta daina ganewa balle kankanar da dama tamkar ruwa saboda rashin zaki. Zama yayi lokacin su munif suka rugo suna masa oyoyo! Kansu ya shafa yace suje gidan uncle Nu’uman. Hannunsu ya kama suka fita sannan Aliyu ya maida hankalin shi akan Fatima data tsare shi da idanu sakkowa yayi ya zauna gefen ta yace

“Fatima! Me kike so? Me kike tunanin kike yi? Me yasa kika kira Fatima kika zage ta…”

“Ni? Yaushe ? Wallahi karya take yimin? Ni kuma?”

Daukar wayar ta yayi tayi saurin kai hannu da niyyar karbar wayar ya tankwabe hannunta, number ta yayi dialing da ya riga yayi mastering cikin kwakwalwar kanshi sega suna ya fito “Jaka” dagowa yayi ya kalleta itama ta kura masa idanu sede tsoro ya gama kama ta, tana tuna yadda suka kwaso ta wancan karon, maida kanshi yayi kan wayar inda ya shiga details din yaga ta kirani sau uku ban dauka ba na karshe kafin nashi na dauka munyi maganar 50seconds. Mika mata wayar yayi yace

“Kirata ki bata hakuri yanzunnan!”

Kallonshi tayi tace

“Haba baban munif kai dai ka bata hakuri amma ta yaya zan bata hakuri”

Wata tsawa ya daka mata ya kara maimaita mata yace

“Ki bata hakuri nace”

Ita kuma tace sede yayi duk abinda zaiyi amma nayi kadan ya bani hakuri, bai ce komai ba ya dauki wayar ya fita tayi murmushin nasara kamar yadda Bilkisu ta tsara mata, yafi awa daya taji ya turo gate ya shigo a daidai parlon taji yana fadin

“Baffa bismillah!”

Da sauri ta mike tayi bedroom dinta, zama tayi tana runtse idanun ta tana making mental note cewar ba Baffan da take tunani bane idan kuma shi ne to tabbas ta kadai har ganyenta. Turo kofar yayi yace

“Kizo munyi baki!”

Hannun shi ta kama tace

“Baban munif me kakeyi haka?”

Hannun shi ya kwace yace

“Ki fito suna jira!”

Ficewar shi yayi ya koma parlon ita ma babu yadda ta iya haka dole ta fito tana ta rakube rakube kamar munafuka, gabanta nata faduwa kamar zata haifa abinda ke cikin ta saboda tashin hankali. Tun kafin ta karaso Baffa ke surfa mata masifa yawan bakin shi zai fito, har ta karso tana zama yace

“Aliyu bata wayar ta kira ta bata hakuri!”

Haka ina kwance se ji nayi wayata na ringing, mikewa nayi na zauna ina nazarin number ganin zata katse yasa na dauka, cikin muryar Kuka naji ance min

“Fatima, matar Aliyu ce Fatima dan Allah Kiyi hakuri abinda ya faru!”

Nayi shiru words dinta da muryarta na min sinking cikin kaina aamma bance komai ba sede ina ayyana da nice ko zai sakeni bazan bada hakuri ba. Ta kusan minti biyar tana magana bance mata ta tafasa ba se naji a background din ana cewa

” Kaga yar mutunci ko amsa ki batai ba amma ke kina hauka, inace uban ki seda ya aura mata hudu, shi ne ke zaki ja da ikon Allah to ki sani rabo kisa yake a banza se ki mutu suyi aure kuma ta zauna da yayanki….”

Se nayi hanging naji wani farin ciki ya saukar min naji duk wata damuwar dake cikin raina ta yaye, tamkar nayi tsalle haka nake ji ko babu komai tasan ni din wacece. Ko da ya kirani da daddare se mukai normal maganar mu in fact ko zancenta bamu saka ba kuma tun daga wannan ranar bata kara kirana ba, sede har gwara ta cigaba da kiran akan abinda ya kunno kai!!!”Kanki daya kuwan Fatima? har burga da threat din Aliyu zai saka ki bata hakuri! Nifa tuna kin bawa yarinyar nan hakuri ji nake kamar na mutu”

Bilkisu ta fada tana kara sakin ashar, Fatima dake zaune tace

“Bilkisu Baffa ne fa, Baffa Aliyu ya kira shi yasa ni dole na bata hakuri kuma shegiyar ko uffan ba tace min ba. Nima bazaki gane yadda nake ji cikin zuciyata ba, kenan tayi galaba a kaina?”

Ta fada tana share hawayen dake zubowa daga gefen idanunta. Dariya Bilkisu tayi tace

“Oh! Har kin hakura kenan? Kin yada makamanki kenan? Haba Fatima karki manta kudurinki da kuma burin zuciyar ki, ya kamata ko ta wanne hali ne ki cika shi”

“Kema kin san ni wacece Bilkisu kinsan cewa bazan yadda makamai na da wurwuri haka ba, se na buga naga yadda zaayi tukun, ta yaya seda naje tsakiyar yaki sannan na juya? Kinsan ba Fatima bace!”

Yawanci idan kaji mata suna rike da irin wannan munanan kudirin cikin zuciyar su to ka sani idan ka duba rayuwar su zaka san cewar suna da past experience marar kyau. HBari na baku labarin wacece Fatima. Malam Haladu shi ne mahaifin Fatima, dan asalin garin mashi ne ta jihar katsina, nan ce mahaifar shi anan kuma ya tashi, yayi gadon sanaar gidan su wato kasuwanci sede shi din dama baya da zeal a hakan yayi auren fari wata Hajara can nesa da mashi ya auro ta, ya kuma tafi da ita kano anan ya fara tada nashi iyalan. Se ya zamana ma da yazo ya yadda kasuwancin saboda rashin uban daki haka se ya kama kanikanci wanda dashi yake ciyar da iyalinshi.

Tabbas da aka saukar da ayar aure seda aka fara da biyu har zuwa hudu, ba daya aka fara ba, i can say hakan shi ne abinda maza ki tutuya dashi, zakaji bahaushe yace me mace daya aminin gwauro, haka dai zance kala kala. Aure babba sunna ce wadda dukkan wani dan halak da ya yadda shi din musulmi ne yana alfahari dashi, sede mu a kasar hausa ya zamana auren ya zama tamkar ana misunderstanding gaba daya concept din aure. Zakiga mai gida a gidan shi, bai gama wadata iyalan shi na gidan ba, abincin ci se ya fita ya nemo, wani ma bashi da halin ciyar dasu haka wasu se suyi shekaru basu sayawa yaransu kayan sawa ba amma kullum se kaga karawa kansu lodi suke ta hanyar aure, idan ka taba su se suce sunnar manzon Allah SAW suke jadaddawa, bayan ba haka koyar war shi tace ba, in fact sun jahilci teachings dinsa, duk koyarwar musulinci babu wanda ya danne mu amma muke danne kanmu da kanmu saboda son zuciyar mu.

Haka ta kasance gidan malam haladu mata daya ma da kyar yake iya ciyar da ita amma seda ya aura mata hudu cif ya cike gidan, kowacce seda ta haifa yara sama da biyar idan ka dauke babar fatima. Kamar yadda muka sani hajara ce ta farko , ita ce uwar gida me iko me mulki, ita ke rike da kambun gidan se yadda tace haka sauran matan suke yi, dukkansu biyayya suke mata, saboda zaman lafiyar ka data yaran ka shi ne yi mata biyayya. Yaranta tara biyar daga ciki mata ne sauran hudun ne maza, ta biyu kuma yar soron dinki ce cikin kwaryar kano, sunanta Attine itama yaranta bakwai dukkan su mata, ta uku yar adamawa ce da wata kanwar kakanta take rukonta anan dawanau, only God knows yadda yayi ya aureta, yaranta takwas daya ne kawai namiji. Maman Fatima Talatu ita ce karama, lokacin da ya aureta girma ya kama shi, dan yawancin yaran hajara sun girme ta, ina ruwan namiji shi dai indai mace ce ai ba ruwanshi da age difference, idan kikai magana zasu ce age is just a number! Yeah duk wanda yasan soyayya ya kuma fada tarkon soyayya to tabbas yasan age doesn’t matter, soyayya ba ruwanta da kudi, kyau, ilimi ko kuma background. Shiyasa se kaga couples sunyi aure ka dinga tunanin how on earth waccan zata aura wancan? Soyayya ita ce amsar. Amma dukda haka se Allah ya bamu kwakwalwa for us to think, mu auna abu akan mizani not only zuciya, dan zuciya sede ta kaika ta baro ka.

Hajara abinda tafi tsana take kuma fargaba shi ne wata ta shigo ta haifa namiji shiyasa sukai zaman lafiya da Attine saboda bata taba haifar namiji ba amma da Lawisa ta haifa namiji daya seda taji a jikinta. Maman Fatima sunan ta Hassana tana da Hussainar ta wadda ta rasu tun suna yara, ita yar kankia ce Ta katsina state. Tunda tazo taga halin zaman gidan itama tabi sawu, ita din dealing din da ake mata yafi na kowa, a gurin miji kamar banza haka take ko nace bora ce dama, a gurin kishiyoyi kullum a tsangwame, yaran miji sun raina ta bata isa tayi ko aike ba sede tasa hijab ta samu yaran makwabta ta aika, a haka zaman ya kasance har ta samu ciki me shegen laulayi amma ko sau daya babau daga kafa a girki ko aikin gida, wani lokacin idan tayi aikin sede ta wani jiri na dibar ta, haka zata shiga daki ta kwanta amma da zarar sun lura da hakan zasu fito da ita, tayi kuka ta godewa Allah a haka rayuwar ta tafi cikin kunci da kalubale iri iri, Hassana cikin dare ta fara nakuda me tsananin gaske da taimakon kishiyoyin nata ta haifa yara uku duk maza! To fa zan iya ce muku idan aka tambayi hajara wacce rana ce ranar bakin cikin ta a duniya to wannan rana ce. Wannan haihuwa se ta saka mata kima a idanun malam haladu dan it’s a blessing ace an taba haihuwar yara biyu cikin gidanka balle azo kan yara uku lokaci daya, ya dinga nan nan da yaran, ranar suna yayi bajimtar da ko haihuwar Anty Saki babbar yayar su fatima baiyi ba, hakan ya kara daga hankalin hajara da yan koranta.

A haka yaran sukai watanni uku, wani yammaci Hassana na girki a zaure dake nan ne suka kafa duwatsun murhun su suna girki a gurin, bayan ta ta goya Alhassan dake fama da zazzabi tasan kuma babu me karbar mata shi, dan da safe har fasa ihun mutuwar shi tayi saboda suma da yakeyi amma ko ci kanki matan gidan basu ce mata ba, se shi haladun ne yazo ya karbe shi yace ta shirya suje asibiti amma Attine tace ita yaranta cuta nawa sukai baa je ba dan haka itama sede a tsaga masa goshu, tana ji tana gani haka aka tsaga na mugunta aka barbada magani yaron ya dinga tsanyara kuka kamar ana cire masa rai, ta koma daki ta saka su a gaba tana kuka kamar ranta zai fita. Kukan Alhussein da taji yasa ta wurgi da maficin hannunta ta nufi daki sede abinda ta gani so yayi ya zautar da ita, alhussein kumfa na bin bakin shi yayinda dayan na ukun Abubakar ke amai ta baki ta hanci, rasa wanne zata dauka tayi se ta fito ta daura hannu akai tana ihu tana kururuwar su taimaka mata, amma babu wanda ya kallesu ta koma dakin ta tadda su a yadda ta bara su sema tsananta da jikin yayi ta kara fitowa tana binsu daya bayan daya tana fada musu amma ba wanda ya kulata, a takaice tana kallo yaran suka mutu kuma a kasan ranta tasan abu aka basu amma wa zai yarda da ita? Meye shedar anyi hakan. Seda ta koma kamar mahaukaciya saboda rasuwar yaran bayan nan da kwana uku Alhassan shima ya mutu. Ita zuciya Allah yayi mata dangana da mantuwa, a hankali kamar baza tai ba se ta hakura ta cigaba da zaman gidan malam haladu na bata baki, a haka ta samu ciki Hajara tasa Attine ta jaya daki ta bata abinci me dauke da maganin zubar da ciki aikuwa babu jimawa ciki yabi rariya.

Duk wata wahala da zuka tunano To Hassana ta shiga cikin ta, bayan yan shekaru se ta haifa Fatima bayan several attempts na zubar da cikin Allah baiyi ba, lokacin da Fatima tazo duniya babanta ya manyanta zakai tunanin it din jikar shi ce bata wani san soyayyar uba ba se ta uwa, ta daku hannun matan babanta hakanan yayinta, se ya zamana azabar da Hassana ta sha nafila ce akan wadda yarta tasha. A haka ta girma da kyar tayi primary da secondary, kullum a ranta tana ayyana ko wanne hali zata shiga ba zata zama bora a gidan miji ba, ba zata taba dandanar abinda Hassana ta danadana ba.Baffa yayan mahaifiyar Fatima ne, rikon ta ya koma hannun shi lokacin da malam haladu ya rasu, a lokacin ne suka samu yancin su suka bar gidan, hatta gado da aka raba hajara ta zauna akan shi ta hana su, ita dai Hassana haka ta dauki yar ta tayi gaba shi ne Baffa ya dauke ta ya hada da nashi yaran anan ta samu ta kare secondary school dinta har Allah ya nufa ta hadu da Aliyu sukai aure. Tana da yara uku dukkan su maza ne.

+

Wata ranar lahadi ina kwance a daki ina waya da Aminatu tana fada min zata fita lectures sannan kuma Yassar dake son ta zai je yaga Daddy, dama Mom ta fada min yaya mariya ma ta fada min ta samu tsayayye kuma zaa hada bikin mu dukka mu uku ayi a tare. Naji dadi sosae dukda ban fiya son hadewar biki ba amma ko babu komai nasan cewar hakan zai sauka kawa mutane da kuma shi kanshi Daddy din ayi taro once and for all.

Sallama mukai nace mata karshen week zan dawo saboda mun gama exams din first semester se ta final semester dina da zan fara, kar kuso kuga murnar da nake idan na tuna journey of millions of miles is gradually ending, babban farin cikin da nake zanyi aure zamu kawo karshen dukkan wani tashin hankalin Fatima, a tunanina ta hakura ko kuma idan mukai aure zata sakawa zuciyat ta sallama ta dangana, ashe ba Fatima haladu matar Aliyu nake nufi ba, dan ita din a tsaye take kam akan kudirin ta. Muna gama wayar na lura da missed calls din Sahibi, dama a ciki nake dashi bai tashe ni sallar asuba ba yau. So se kawai na share banyi returning call din ba shima kamar wajen five minutes se ga kiran  shi ya shigo wayata. Harda bata fuska kamar irin yana gabana dinnan ko kuma yana kallona ta wayar

“Sahiba how are you!”

“Nayi sallar asuba! Da baka tashe ni ba”

Dariya yayi sosae wanda ya tabbatar min yana cikin nishadi yace

“Haba my dear! To babyn ki ya karaso”

For the time been seda nayi tunanin wanne baby din seda yace

“Fatima ta haihu”

“Oh mashaaa Allah! Yaushe me kuma aka samu?”

Da murna and excitement cikin muryar shi yace

“It’s a baby girl of course”

Naji dadi ya ratsa ni saboda how desperate yake son ‘ya mace, nasan wannan

“Na mata huduba da Fatima kamar yadda nayi miki alkawari”

Haka yace min tun farkon da na san sunan matar shi Fatima yace min ai sunan yana da matukar muhimmanci a rayuwar shi shi yasa da zarar ya samu yarinya mace to Fatima zai saka mata plus wadda ta rike shi sunanta Fatima dan haka idan ya saka Fatima yana nufin duka mu ukun.

“To Alhamdulillah! Allah ya raya ta yayi mata albarka, kace her mummy loves her. So dukkan su lafiya suke?”

“Amin Amin Sahiba, itama tana sonki. Babyn lafiya take Maman ce de Bpnta yayi high wai se sunyi keeping dinta under observation”

A raina nace tana masifa da balai ta ina bpnta bazai shooting ba. Na ce

“Allah ya bata lafiya, karka damu ai wannan din is very common ga matan da suke da ciki ko kuma suka haihu. So ta kwantar da hankalinta zai sauka a hankali”

Daga haka se muka koma maganar mu yake fada min sunyi magana da Daddy last week yace masa yana jiran su gidan saurayin yaya Mariya su yi magana idan yaso zai masa magana da Yassar din Aminatu se ayi finalizing date.

Bayan satittika Daddy ya cika alkawarin shi yace musu dukka su turo magabatan su zaayi magana. A wannan satin haka nayi squeezing na tafi Dutse, Hibba tasa ni dole se naje a cewarta ai ana bukatar babba a gidan kuma dama ni ke playing role din babba. Seda na fara zuwa gidan yaya Rahama sannan na koma gida yamma likis. Daddy na zaune a tsakar gida hannunshi da wayar shi yana dannawa haka idanun shi sanye da farin medical glasses. Shi kadai ne sauran yaran na cikin parlo ina jiyo muryoyin su na tashi, da alamar wata hajar ake bajewa. Sallamata yasa shi dago kanshi muna hada ido ya sakar min wani tattausan murmushi, kamar charm se naji na samu wani karfin gwiwa, nima murmushin na sakar masa ina jin a duk duniya bayan manzo na babu wani mutum mafi soyuwa a zuciyata kamar dattijon nan, a wajen wasu he might be a monster amma a gurina shi din angel ne. Inda yake zaune na isa tareda dan tsugunna wa na kama hannun shi nace

STORY CONTINUES BELOW

“Daddy!”

“My pharmacist! Ya hanya”

Ina jin pride cikin muryar shi duk lokacin daya ce min hakan,

“Alhamdulillah! Daddy, ya aiki ya sabon office dinka?”

Da yake lokacin anyi commissioning dinshi matsayin commissioner of justice har biki mukai a gida dan har parent din Hibba seda suka zo.

“Not bad! Ya karatun? An kusa karewa ko?”

Nayi murmushi nace

“Wata daya da kwana uku ya rage nayi exams din”

Se yayi min adduoi sannan yace naje gurin Yan uwana suna jirana tun dazun, da gidan Rahama zasu biyo ni shi ne bai bada fuska ba. Dariya nayi sosae yace wai shi ya tsufa baya son ana barin shi shi kadai a gida. Ina shiga parlon Amal da Lubna suka yo kaina suna bude muryar su suna ihun sannnu da zuwa, rungume su nayi sannan na zauna Nawwara ta zauna gefena tana shafa ni tana fadin

“Sannu yaya Nanah wallahi duk kin rame”

Murmushi nayi nace

“Ba dole ba, Aminatu fa ita da yaya Mariya?”

Basu bani amsa ba saboda shigowar dukka su ukun ashe banma lura auta bata nan ba se lokacin, ta Nanike ni tana fadin

“Yaya Nanah sannu!”

“Yawwa Ummu”

Muka gaisa dasu yaya Mariya wai order suka bayar na snacks saboda zan dawo shi ne sukaje karbowa, Daddy aka dibarwa nashi da dinner dinsa wanda mostly ma greens ne saboda ya fara samun HTN kuma last da aka gwada BGL dinsa ya shiga danger line so muna ta kokarin controlling diet dinsa dalilin da yasa Aminatu ta tafi school of nursing kenan, Nawwara kuma zata fara MLS wannan shekarar a Bayero. Lubna tace medicine take son yi saboda mu hadu mu kula da Daddy dinmu. Seda mukai sallar maghrib sannan muka ci abinci se ya zama kamar wata karamar dinner ce mukai. Ranar ko time din Aliyu ban samu ba shima sau daya ya kira yace naje muyi hira da yan uwana.

Wani lokuta idan wani mummunan abin zai same ka kana ji a jikinka, ba lallai ka fahimta ba har se abin ya faru sannan zaka fahimci dalilin canjawar yanayin ka. Ni dai nasan lokacin da na kwanta zuciyata fari tas take, in fact murmushi fal fuskata nayi bacci saboda babu wani farin ciki a duniya irin kasancewa da yan uwanka da kuma masoyin ka, amma da asuba dana tashi se naji I’m down sosae, naji kamar zuciyata nayi min zafi . Se na alkanta hakan da hormonal changes saboda na fahimci ovulation nake. Haka Nayi sallah na koma na kwanta inata tunanin abinda bazan iya fadar menene shi ba, na dai san tunani nake se bacci can ya lallabo ya tafi dani wata duniyar. Se nine na tashi ranar jumaa ce, kafin na sakko daga gado na karanta kahfi sannan na danji damuwar da nake ciki ta ragu. Kitchen na wuce na tarar already Lubna ta fara hadawa Daddy breakfast se na koma na tashi sauran muka gyara gidan tas, suka hada wanki da giga aka kira me yi yazo ya tafi dashi. Komawa nayi na daki nai wanka na shirya cikin lace gown ban daura dankwali ba na zauna ina taje kaina, sallamar Daddy tasa na fito yace mana ya fita office muka mishi Allah ya kiyaye ya fita. Ko mintina biyar basu cika ba naji Amal na fadin

“Daddy ka fasa fita ne?”

Daga daki naji yace

“Aa zan fita bakuwa nayi ne”

Haka kurum naji gabana ya yanke ya fadi, addua nayi murmuring a bakina sannan na saka ribbon na kama kan dashi na maida dan kwali na na rufe sannan nace su tashi mije muyi cefane. Veil na yafa na dauka purse dita na nufi parlon Daddy, da sallama na shiga yana zaune saman kujera ya tattara dukkan hankalin shi ya bawa matar dake zaune kejerar dake facing dinsa, a cinyarta yar karamar baby ce da bazata wuce watanni biyu ba, ta zura hannunta cikin baki tana sha, anyi mata kwalliya da maroon da milk din kaya a jikin ta, gaba daya suka juyo suna kallona, nima kallon ta nake da tunanin ko wacece ita din? Daddy yayi gyaran murya hakan yasa duka muka dauke kanmu ni kuma na karasa shigowa tareda gaishe ta sede data amsa min seda na kara kallonta haka kurum nake jin kamar nasan muryar somewhere, amma a ina? Nima bazan iya tunawa ba

“Nanah ya akai?”

“Daddy zan ce maka zamu je kasuwan.”

“Allah ya kiyaye, kun lissafa kudin dana bayar zai isa?”

Kai na gyada ina murmushi nace

“Ya mayi yawa fa”

“To is ok se kun dawo, ku kula da kanku nima zan fita idan na sallami bakuwa ta”

Daga haka na mata sallama ta amsa tana bina da kallo hakan ya tabbatar wa Daddy ban santa ba itama haka. Driver Daddy ya kaimu sabuwar kasuwa mukai siyayya sannan muka dawo yana ce mana ya kamata ya koya mana mota, dukka muka yarda akan Daddy idan ya yarda. Bamu samu Daddy a gida ba itama bakuwar ta tafi bamu neme shi ba muka cigaba da aikin mu se nima aikin yasa hankalina ya kwanta na cigaba da aikina. Ina yi muna waya da Sahibi.

Da daddare Daddy ya dawo seda ya gama cin abinci wajen 10pm ina zaune ina waya da Sahibi Ummu tazo tace min Daddy yana kirana. Sallama nayi mishi na tafi wajen Daddy bayan na dauka dogon hijab akan kayan baccina, na fita zuwa dakin shi. Yana zaune kan carpet dishes din daya ci abinci baa kwashe ba hakan yasa na dauke su nakai kitchen sannan na dawo na zauna nace

“Daddy akwai abinda kake so?”

Kan shi ya girgiza yace

“Alfarma nake so kiyi min Fadimatu”

Gabana ya fadi, a take a wannan lokacin nasan cewar an bude sabon shafi a rayuwata, a wannan lokacin nasan ZUMA da nake lasa ta kare, ZUMA data rage asalin ZUMA dince me dalli ba mai dadi ba, a wannan lokacin kaddarata ta fara kuma haka time din ya fara ticking, kalmomin da Daddy ya fada min suka canja min rayuwata completely, na rasa former self dina na koma wata sabuwa!

About AIS

Check Also

ZUMA CHAPTER 11 BY SHATUUU

ZUMA CHAPTER 11 BY SHATUUU Www.bankinhausanovels.com.ng  Bayan watanni hudu nayi nisa cikin service dina, duk …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *