ZABI NA CHAPTER 9 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 9 BY FADEELARH

Www.bankinhausanovels.com.ng 

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI+

Zaune suke a falon gidan yayinda suka yi tsit suna sauraron Abba wanda ran shi yake a bace.. kukan yaran kawai kake ji.. na Layla kuwa harda shesheka.

“Dukkanin ku kun sani cewar a nan falon na tara ku akan maganar yaron nan Zayd.. idan ban manta ke Layla da bakin ki kika ce baki son shi sannan a gaban ki aka yi maganar yace yana son qanwar ki Ameera.. Me zai sa yanzu ana maganar saura ‘yan kwanaki ayi bikin su zaki kawo maganar banza irin wannan??”

Cikin kuka Layla tace “Abba na sani cewar nace bana son shi a baya amma wallahi yanzu ina son shi kuma ni shi zan aura..” ta nuna Ameera tace “duk laifin munafukar nan ne, ta sani cewar Zayd mai kudi ne shine bata fadi mun ba.. tana kallo na rabu da shi shine ita ta zagaya ta..”3

“kiyi mun shiru anan wurin.. Sakaryar yarinya. Ashe kina cikin masu kwadayi da son abun duniya kenan?? Mu qaddara dagaske Zayd din mai arziki ne, kenan saboda hakan zaki aure shi ba don Allah ba?? wannan wane irin halin banza ne kika dauko Layla?”

Ya nuna ta da yatsa yace “Daga yau sai yau kar in qara jin rigima akan Zayd a cikin gidan nan..

Zayd dai shi zaiyi zaman aure da macen da yake so kuma yace Ameera yake so, iyayen shi sun zo sun nema mishi auren ta har an sa ranar bikin su don haka an gama magana kuma ko da wasa kar in qara gani kin sa hannu ki daki ‘yar uwarki balle har ki ambaci kalamai munana a gareta. Sai kiyi ta addu’a akan Allah ya kawo miki naki mijin nagari..”

Layla dai qara fashewa tayi da kuka..

Mama wadda jikinta yayi sanyi ce tace “Haba Abba, a dan duba labarin nan don Allah.. tunda dai Layla ce babba ai…”1

“Dakata Maman Layla.. shin ba na gama magana ba?? toh duk ku tashi ku bani wuri, Haka kawai bazan zauna ku mayar da ni wani qaramin mutum ba..”

Kafin su tashi kuwa ya miqe ya wuce dakin shi.

Umma ta janyo hannun Ameera suka nufi dakin ta yayinda suka jiyo Mama tana fadin “dangin munafukai, wallahi idan har dagaske yaron nan mai arziki ne sai ya auri ‘ya ta don kuwa ita ya fara nema..”4

Layla suka jiyo tace “Wallahi Mama mai arziki ne.. kuma idan har ban aure shi ba itama bazata aure shi ba.. bazan taba bari ba”1

☆☆☆☆☆☆☆☆

Zaune take a kan gadon Ummanta yayinda Umman take goge mata ciwon da Layla ta ji mata a gefen baki.. Har a wannan lokacin Ameera kuka take yi.

“Amma Umma ba kya tunanin maganar Ya

Layla dagaske ne?? ba kya tunanin Ya Zayd dina wani mutum ne daban?? Ni fa Umma dagaske idan har abinda Ya Layla ta fada gaskiya ne na fasa auren shi, ni fa bana son irin rayuwar da ban saba da ita ba..”

“Ssssh yi shiru ki daina kuka.. tabbas wannan zancen na Layla abin dubawa ne. Bari anjima zan samu Abba in ji abinda ya sani a game da Zayd.. idan dai yayi bincike akan yaron yakamata ace ya san komai akan shi. Aure dai bai dace a gina shi akan qarya ba.. don haka dukda yayi bincike akan shi yakamata ya sake yin wani. Yanzu dai ki tashi ki je daki kiyi wanka ki dauro alwala tunda kin ga lokacin sallan Magrib ta gabato..”

“a’a Umma, ni bazan koma daki ba. Wallahi ina tsoron Ya Layla.. baki ji tace zata kashe ni ba?? don Allah ki bar ni a nan tunda dakin Abba zaki kwana kin ji..” ta fada yayinda take share hawayen fuskarta.

STORY CONTINUES BELOW

Cike da tausayin ‘yarta tace “Ki daina tsoron Layla, Babu abinda zata yi miki. Ba a gaban ki Abba ya ja Mata kunne ba? toh kwantar da hankalin ki.. dukda haka idan a nan din zaki kwana shikenan.. Sai ki tashi ki shiga kiyi wankan.. ni bari in kwaso miki ‘yan kayan ki da zaki buqata”

Ameera ta rungume Umman ta tace “nagode sossai Umma”

Umma dai tare da ‘yarta suka yi sallan magrib sannan ta wuce kicin don tuqa tuwo.. Allah ya taimake ta tun da yamma kafin Layla ta shigo da rikici ta riga ta kammala miyarta.. ko da Ameera tayi offering ta taimaka mata tace tayi zamanta ta huta.

☆☆☆☆☆☆☆

Ko da lokacin dinner yayi Abba dai tare da yaran shi maza suka ci abinci.. Ita dai Layla da Mama tun da suka shiga dakin Maman basu qara fitowa ba.. Abincin ma Suleiman ne ya kai musu har dakin.. Ko sun ci ko basu ci ba oho!!

Ita kanta Ameera a daki ta ci abincin shima akan tilastawar Umma domin kuwa ko alama batada appetite.. maganar Layla ce ta tsaya mata a rai.. addu’a takeyi akan Allah ya sa ba gaskiya bane..

the only way to find out is to confront Zayd himself amma wayar shi bata shiga..

Wuraren qarfe Goma ne Umma tayi shirin bacci sannan tayi ma Ameera sallama ta wuce dakin mijin ta.

☆☆☆☆☆☆☆

Umma ta tarar da Abba zaune a kan kujera yana sanye cikin glasses dinshi masu qara ma idanuwan shi qarfi yayinda yake karanta wasu takardu wadanda suka shafi aikin ofis.

ko da ta samu wuri a bakin gado ta zauna jiran shi tayi har ya gama abinda yake yi sannan ya dago kanshi ya kalle ta yace “Ya akayi Umman Ameera?? lallai da magana a bakin ki… fadi in ji”

Umma ta saki ajiyar zuciya tace “Zancen yaron nan ne Zayd.. Anya bazaka sake yin bincike ba akan shi?? ni fa bana so a zo ayi aure a dawo ana da na sani..”

“Babu shakka dole ne in sanar da ke abinda yake faruwa dukda nayi ma yaron nan alqawarin bazan sanar da Ameera ba wanda ina kyautata zaton bazaki fadi mata din ba..”

Cike da mamaki Umma tace “ban gane ba.. kenan abinda Layla ta fada akwai qamshin gaskiya a ciki…”

Girgiza kai yayi alamar ‘eh’ sannan ya fara bata labarin Zayd da asalin shi..

☆☆☆☆☆☆☆

ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE

VICTORIA ISLAND-LAGOS

Wuraren qarfe goma da rabi yana zaune a lafiyayyen study din shi yayinda yake qoqarin qarasa duba wasu reports na wani project da kamfanin shi yake yi a Banana Island.

As usual kofin tea dinshi na nan a gefen Macbook din shi.. Gaba daya Study din ya dauki qamshin designer turaren shi mai dadin gaske wanda ya gauraye da sanyin AC ya bada wani yanayi mai dadi.

Sanye yake cikin qananan kaya na black three quarter sweat da white T-shirt.. fatar jikin shi fara sol sannan so smooth.. Gashin kanshi baqi qirin ya kwanta sai qyalli yake yi.. sajen shi wanda ya sha gyara ya hadu da gashin baki da gemun shi 100% on point… Zayd dai is the definition of perfection.

Gani nayi ya dafe kai sannan yace “Ya salaam.. I forgot to call her, Allah yasa bata yi bacci ba..”

Wayar shi ya janyo da sauri yayi dialing lambar ta.

Zayd dai dazu da yamma ne abokin shi Mustapha ya kira shi akan maganar Ameera.. Ya fadi mishi ya kira ta a waya because she is getting worried kamar yadda Zarah ta fada.

“Hello..” ya jiyo muryarta so low

“Hello Habibty how are you?? ya na ji muryar ki down?? baki da lafiya ne ko kin fara bacci ne?”

STORY CONTINUES BELOW

“Yaya ka gaya mun gaskiya, who are you???”

Zuciyar shi ce ta buga yayinda na ga ya miqe tsaye da sauri yana shafa kan shi..

Cikin rashin fahimta yace “Habibty ban gane abinda kike nufi ba… Zayd Muhammad sunana kuma kin sani..”

“Yaya just tell me… Ya Layla tace kai mai kudi ne…” daga nan ta bashi labarin dukkanin abinda ya faru amma banda dukan da Layla tayi mata because she didn’t want to get him worried.

Zayd dai tunda ta fara bashi labari na ga ya runtse idanuwan shi sannan ya bude.. Dunqule hannun shi yayi yayinda yake ta kai da komowa..

“Yaya na ji kayi shiru.. kenan dagaske ne ko??”

“Hey stop.. ofcourse ba dagaske bane.. idan har ina da irin wannan arzikin me zai sanya in boye identity dina?? look, kin dai san halin Layla.. it’s possible she is trying everything possible to stop our wedding”

“toh Amma Yaya hoton da aka sa a social media fa???”

“Habibty ba ni bane.. kin sani cewar ance akan samu mutane biyu zuwa uku ma a duniya masu kama da juna.. it’s possible an samu error ne ta wani bangare…please ki manta da abinda tace, she is just talking nonsense”3

Shiru ya ji ta dan yi sannan tace “toh Yaya.. meyasa baka kira na a waya? kuma ni idan na kira ka baya shiga”

“Yi haquri Habibty, inda nake ne babu network mai kyau.. amma kar ki damu nan da 3 days zan dawo, ina nan zuwa in gan ki”

“toh Allah ya dawo da kai lafiya”

“Ameen Habibtyn Zayd”

“Yaya in tambaye ka?”

Runtse idanuwa yayi ya bude yayinda ya koma kan kujerar shi ya zauna yace “Go ahead”

“Meyasa kace ka yafe kayan daki bayan ka sani cewar zaka qara ma kanka nauyi ne??”

“Uhmm.. kin gane, akwai wani mai gidan mu ne anan da na fadi mishi zanyi aure shine ya bani kyautan wani dan qaramin gidan shi a nan Kaduna.. the thing is gidan akwai kaya a ciki, dama yakan sauka a gidan ne idan ya je Kaduna toh daga baya ya gina wani shine yace ya bani wannan din in zauna tare da Mata ta.. Yanzu haka idan na dawo zan sa a goge mana gidan kafin a kawo mun ke” ya qarasa fadi yayinda yake fatan Allah yasa ta amince.

Murmushi ya ji tayi sannan tace “Allah sarki.. Allah ya saka mishi da alkhairi”

“Ameen Habibty.. so tell me, how you?? hope you good??”

“I am better now Yaya..”

A haka suka cigaba da hira na tsawon lokaci sannan ya qyale ta don tayi bacci.. da alama she is exhausted from the confrontation she had with her sister.

Bayan ya kashe wayar ne na ga ya jefar da ita kan table dinshi yayinda yayi resting bayan shi sossai a kujerar da yake zaune..

“Yaran nan basu jin magana.. they had to post our pictures on social media.. dole ne in dakatar da su Ammi akan kai kayan lefen nan.. it will just blow things up.. at this point I just can’t lose Ameera”

☆☆☆☆☆☆☆☆

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Mama tana zaune gefen Layla wadda take kwance a kan gadon dakinta tana ta rusa kuka..

Tunda Abba ya yanke hukunci take kuka.. Abincin ma qin ci tayi..

“Ki kwantar da hankalin ki Layla.. ni fa ban amince da zancen nan naki ba, Har yaushe mai arziki irin wanda kika kwatanta zai bata lokacin shi akan irin wannan??? ki duba fa ki gani tsawon watanni nawa kenan da Zayd ya fara zuwa wurin ki?? me zai amfana da shi idan yayi hakan?? gaskiya ki sake bincike akai…” Mama ta fada cike da confusion. Da alama itama bata amince da maganar da tayi ba.

“Wallahi Mama kin ji na rantse miki Zayd ne.. Ni ban san meyasa yayi hakan ba amma wallahi shine.. Kuma gobe zan shirya in je kamfanin nashi, dole ne ya canza ra’ayin shi.. dole ne ya qyale waccan baqar bazan don kuwa ni na dace da shi” Layla ta fada tana kuka.1

Mama ta janyota ta rungume ta sannan tace “eh toh babu laifi idan kin je kin tabbatar din.. Idan har dagaske yana da arziki dole kam ki aure shi, duk bala’i kuwa sai kin aure shi.. Yanzu kam ki rage kukan nan ki sassauta ma kanki kar zazzabi ya kama ki.. Yakamata ki natsu ki fara tsara yadda zaki koma cikin rayuwar Zayd da qarfi da yaji”2

“aikuwa na riga na gama tsara komai Mama.. if it means for me to kill Ameera I will do it don Allah ya sani bazan bari ta auri Zayd ba ina kallo…”Washegari dai kamar yadda Layla ta tsara haka ta shirya tun da safe ta nufi kamfanin City-shelters don neman Zayd amma bata same shi ba.. ta samu information akan yayi tafiya.. ko da ta tambaya lokacin dawowar shi ba’a fadi mata ba domin kuwa fadin whereabouts din mamallakin kamfanin is highly confidential.

Hakanan ta dawo jiki a sanyaye da niyyar komawa washegari..

Abin haushi shine yadda batada lambar wayar shi.. tun lokacin da ta kore shi daga rayuwarta tayi deleting lambar shi..

Umma dai a jiyan da Abba ya fayyace mata komai akan Zayd sossai ta cika da mamaki.. A lokacin ita kanta bata amince a bashi auren Ameera ba saboda rayuwar su ba daya bane kuma ta san halin Ameera.. bata son spotlight a al’amuran ta.. being the wife of a rich business man like Zayd will mean dole ta shiga mutane.. ta sani sarai she wont be comfortable a irin wannan rayuwar..

Da qyar Abba ya shawo kanta tare da yi mata bayanin halayen Zayd masu kyau.. Ya jaddada mata lallai zai riqe musu ‘yar su cikin amana..

Umma dai akan dole ta haqura ta sanya albarka yayinda tayi alqawarin bazata fadi ma Ameera gaskiyar al’amarin ba kamar yadda suka buqata.

Ni kuwa nace Allah yasa kar tayi musu bori idan ta gano gaskiya..3

Ameera kuwa wasa-wasa ta qi komawa dakin su.. A lokacin da Layla ta fita daga gidan ne ta samu ta shiga dakin ta kwashi kayan ta daidai yadda zata buqata har tsawon sati daya.. Babu yadda Ummanta bata yi da ita akan ta koma dakin su ba amma sam ta qi.. ita kam har ga Allah tsoron Layla take yi domin kuwa bata manta threats dinta ba.. a ciki kuwa harda kissa.. Don haka prevention is better than cure.

Hatta falo ta daina zama saboda Layla.. Su Ibrahim duk basu ji dadi ba.. Yawanci a dakin Umman suke samunta su zauna suyi hirar su.. babu yadda basu yi akan ta fito suyi kallo ba amma sam ta qi..

Ita kuwa Layla ta jera kwanaki uku tana zarya zuwa City-Shelters amma bata ga Zayd ba.. A rana na uku ma har maqalewa tayi ta qi tafiya.. a tunanin ta sun hana ta ganin shi ne kawai.. Haka ta yini tana jira amma shiru.

Su kuwa ma’aikatan kamfanin dama sun saba da ganin ‘yan mata kala-kala sun zo neman CEO din nasu but this time around sunyi mamakin nacin Layla.. by now ai yakamata ace kowa ya ga hotunan da aka baza a social media na shi da Ameera.. yakamata ace ‘yan matan da suke bibiyar shi su haqura haka nan..

☆☆☆☆☆☆☆☆

CITY-SHELTERS

ALI AKILU ROAD-KADUNA CENTRAL

Zaune yake a executive chair din danqareren ofis dinshi wanda ya hadu iya haduwa… ofis din babba ne sossai wanda ya qawatu da kayan jin dadi na zamani.. Wani daddadan qamshi ne ya gauraye da sanyin na’urar sanyaya daki ya bada wani yanayi mai dadin gaske..

Macbook dinshi ce a gaban shi with a tea cup beside it as usual.. Hankalin shi sossai yayi nisa a reports din da yake dubawa..

Zayd dai jiya daddare ya shigo Kaduna.. A yau din yana da meeting da wasu clients wadanda suka zo daga Kano.. A yanzu haka yana qoqarin duba proposal din su ne saboda ya ji dadin tattaunawa da su a meeting din.

Qwanqwaso qofar shi aka yi aka shigo.. mutane biyu ne suke da damar yin hakan ba tare da ya basu izini ba- Secretary dinshi Adriana sai PA dinshi Bilal.

“Sorry to interrupt sir, it’s time for the meeting” Adriana ta fada cike da girmamawa.

Miqewa yayi yace “thanks Adriana, is Bilal in his office??”

STORY CONTINUES BELOW

“Yes Sir, I already informed him..”

“okay great”

Gani nayi ya nufi wurin hanger ya janyo suit dinshi yana qoqarin sanyawa yayinda Adriana ta kwashi Macbook dinshi da wasu files zata kai mishi conference room din kamar dai yadda take yi kullum.

Bayan Zayd ya sanya suit dinshi na ga ya kwashi wayoyin shi sannan ya wuce ya fita..

Yana fita ya tarar da Bilal tare da Adriana suna jiran shi don haka ne suka nufi wurin Lift tare, Bilal a gefen shi yayinda suke tattaunawa akan meeting din da zasu shiga yayinda Adriana take biye da su a baya.

Lift din da suka shiga lift ne that is meant for the CEO (Zayd) alone.. ba tare da sauran lifts suke ba..

Asali dai ofis din Zayd yana 5th floor ne yayinda conference room yake ground floor.

☆☆☆☆☆☆☆

Tsaye take a gaban Receptionist wadda ta sanar da ita lallai CEO ya dawo and he is very much present in the building.. matsalar dai daya ce sai tayi booking appointment da shi don kuwa ba haka nan yake ganin mutane ba tunda dai bai san da zuwan ta ba… Layla dai roqon matar tayi akan ta kira shi a waya ta fadi mishi ita ce ta tabbatar zai bada go ahead akan ta gan shi amma matar ta qi sauraronta..

Bata ankara ba ta hango wani lift wanda yake daban da sauran ya bude..

Hango su tayi sun fito suna ta magana da wata a biye da su..

ZAYD!!

Da sauri na ga ta nufi wurin su..

Zayd wanda hankalin shi yayi nisa wurin sauraron bayanin da Bilal yake yi mishi har ga Allah bai kula da Layla ba wadda take daf da su..

“Zayd” ya ji an kira shi cikin familiar voice

Ko da ya juya ganinta yayi tsaye tana murmushi yayinda ta qaraso kusa da shi..

Gani nayi tana qare mishi kallo sama da qasa.. Lallai hoton shi da ta gani ma bai yi mishi justice ba kamar a reality.. ya masifar yin kyau, fari sol kamar tsada, Gashin kanshi da na fuskar shi sai qyalli suke yi.. Ga wani lafiyayyen qamshin turaren shi da yake tashi, daga jin qamshin ba sai an fadi maka ba ka san designer ne na bala’i.. Sanye yake cikin black suit wanda yayi fitting dinshi.. hatta shirt da neck tie dinshi black ne.. a taqaice dai he was dressed in all black… dayake fari ne sai kayan suka bala’in yi mishi kyau.. in all he is looking stylishly handsome like a model!!

Tabbas Zayd dinta ne..

“Who are you?? Have we met before???” ya tambaya yayinda yake kallonta cikin ido.

Zuciyarta ce ta buga da jin tambayar shi..

Bai gane ta bane???

Tabbas muryar shi kadai ta isa ta sanar mata cewar shine.. amma kuma me zai sa yayi mata wannan tambayar???

Da qyar ta saita murya tace “Laylar ka ce fa Zayd.. baka gane ni bane??”3

Bata rai yayi yace “Pardon?? yakamata in gane ki ne??”3

Kasa ma magana Layla tayi don kuwa ta zama confused.

Gani nayi ya kalli designer wrist watch din da ke hannun shi sannan ya kalli Bilal yace “please deal with this Bilal.. I am running late for my meeting and dont stay long coz I need you with me”

“Okay Sir” Bilal ya fada harda sakin murmushi.

Layla wadda ta cika da tsananin mamaki kasa magana tayi tana kallon shi yayinda ta ga ya wuce da Adriana wadda ta take mishi baya.. Staff din kamfanin suna ta gaishe shi yana amsawa cike da fara’a as usual.

STORY CONTINUES BELOW

Jikinta ne ya fara rawa yayinda hawaye suka fara wanke mata fuska..

Bai gane ta bane ko kuwa wulaqanta ta yayi don ya rama abinda tayi mishi?? Lallai ta fara amincewa ba shi bane dagaske, da shine bazai taba yi mata haka ba don kuwa Zayd din da ta sani yana bala’in sonta.. he will be happy idan har ta zo inda yake tana nema su shirya!

Bilal wanda yake tsaye yana kallonta sossai ya ji dadin abinda Zayd din yayi mata… Allah ya sani ya tsani Layla a rayuwar shi.. Ba Zayd kawai ba hatta shi ya sha wahala don kuwa ko batar da kamarni, dressing da dialogues din da ya dinga shirya ma Zayd kadai aiki ne balle kuma yadda suka dinga baro Lagos da Abuja wani lokaci cikin dare (dukda a private Jet dinshi ne) just to reach Kaduna saboda ita and at the end ta wulaqanta shi.. She deserves the worst treatment.

“da alama kinyi research kin gano ko shi waye kenan..”3

Da sauri ta kalli Bilal tana share fuskarta tace “excuse me??”

Yayi murmushi yace “you heard me right Layla.. Kina tunanin bai gane ki ba ko? or maybe kina tunanin ba shi bane?? toh let me tell you this, thesame Zayd talaka mai zuwa gidan ku zance, mai sanya kodaddun kaya wanda yake da tabo a goshin shi wanda kike wulaqantawa shine wannan Zayd din da kika gani yanzu.. The CEO of City-shelters, the only son of the Saudi Arabian Ambassador, His excellency Ahmad Muhammad Fadoul”

Ya dan yi shiru sannan yace “wait why am I even telling you something you already know??”

Girgiza kai yayi yana murmushi ya cigaba da fadin “…well, ina gani kamar akwai buqatar yin hakan for confirmation right??”

Layla wadda tayi freezing a tsaye ma kasa magana tayi.. tayi regretting rayuwarta in totality a yanzu.. Yanzu ya zata yi??

“By now na san kin sani cewar qanwar ki Ameera zai aura, thesame one you despise so much.. I am guessing kin zo kiyi congratulating din shi ne. toh kar ki damu zan isar miki da saqon ki” Ya fada cike da tsokana yayinda ya juya zai tafi.

Bai yi steps biyu ba ya juyo fuskar shi a daure yace “Allah ya sani I never really liked you right from day one and I am glad you revealed your true color on time.. Allah ya tsare shi daga sharrin masu kwadayi da son abin duniya irin ku. and yes, see you NEVER” sannan ya juya ya bi hanyar da su Zayd suka bi earlier.1

Wani wawan jiri ne ya kwasheta.. ta tafi zata zube ne ta ji an riqo ta.. Ko da ta dago don ganin ko waye kuwa wata ta gani, da alama ma’aikaciya ce a kamfanin.

“Lafiyan ki dai ko???” ta tambayeta

Girgiza kai tayi alamar ‘eh’ yayinda tayi saurin share hawayen fuskarta ta gyara tsayuwarta sannan tace “i am fine.. nagode”

Matar dai qara kallonta tayi sannan ta wuce abinta..

Layla kuwa jiki a sanyaye ta fice daga kamfanin.. Allah ya taimake ta babu mutane a wurin da Zayd da Bilal suka yi mata wulaqanci.

Ko da ta fita kuwa qafafuwan ta sunyi bala’in sanyi.. ji tayi kamar an kwashe mata kayan cikinta gaba daya… she felt so empty and useless! Kalaman Bilal ne suke ta yawo a qwalwarta yayinda suke tormenting dinta..

Gani nayi ta daga kai ta qara kallon building din wanda gaba dayan shi is made of glass sannan ta sauke idanuwanta qasa…

Yanzu Zayd ne yake da wannan kamfanin?? yanzu shikenan a haka zata koma gida bata samu sun yi magana ba?? yanzu haka zata zuba idanuwa tana kallo zai auri Ameera?? yanzu shikenan ita da wannan daular sai dai kallo??2

Gani nayi ta fara tafiya cikin zafin rai tana kuka tana fadin “wallahi bazan bari ta aure shi ba.. da ta aure shi ina kallo gwara na sheqa ta lahira. in ya so dukkaninmu mu rasa..”

Tana tsaye tana jiran Napep yayinda hawaye ke wanke mata fuska ne wayarta tayi qara alamar text message ya shigo..

Ko da ta duba wata lamba ce amma ta ga saqo kamar haka:

“Pretty please kiyi haquri ki dawo mu cigaba da rayuwar mu.. I miss you so much! kar ki manta cewar ni kadai zan iya auren ki tunda na san ki a matsayin ‘ya mace.. duk wanda zaki aura idan ya gane you are not a virgin he will send you away.. please think this through and get back to me.. I love you very much and I will be waiting for you anytime”

Yours truly Habib!

Gani nayi ta runtse idanuwan ta yayinda wasu hawaye masu zafi suka cigaba da gangarowa.. Yanzu shikenan bazata taba iya goge abinda suka dinga aikatawa da Habib ba a rayuwarta?? dagaske duk wanda ya aure ta zai gane ita din second hand ce???5

Jikinta ne yake ta rawa yayinda kanta yayi mata nauyi.. wani mugun zazzabi ne ya saukar mata lokaci guda..

Wani Napep ya zo wucewa ta tare ta shiga..

Tunda tayi mishi kwatancen inda zai kai ta kuwa ta dora kai bisa gwiwa ta dinga rusa kuka kamar ranta zai fita..

Mai Napep dai dukda bai san abinda ke faruwa ba sai lallashinta yake yi har ya kawo ta gida!GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Jiki a sanyaye Layla ta iso gida.. Da qyar take tafiya yayinda take bin bango.. Jiri ne yake ta diban ta.. Ko da ta shiga gidan babu kowa a falon don haka straight dakin Mama ta wuce.

Mama tana Zaune akan gadon dakinta tana waya da Hajiya Suwaiba wadda suke hiran wata sarqar gwal da ita Mama take so ta siya.

Ganin Layla ta fado mata a gigice ne tayi saurin yin sallama da Hajiya Suwaiba tare da fadi mata zata kira ta anjima.

“Ke lafiya kike kuwa???”

Da sauri ta miqe ta nufi wurinta ta kamo ta.. Hankalinta ne yayi mugun tashi a dalilin jin jikin Layla da tayi ya dauki zafi sossai har tana kyarma.. Ga hawaye da ke ta bulbulowa daga idanuwanta..

Janyo ta tayi ta zaunar da ita kan gado sannan ta zauna a gefenta itama a rude tace “kenan dai dagaske shine??”

Layla dai rushewa tayi da kuka yayinda tace “na shiga uku Mama, Wallahi shine.. Zayd ne..” Daga nan ta bata labarin wulaqancin da yayi mata harda ma wanda Bilal ya dora a kai..

Mama dai salati ta shiga yi tare da dafe kai.

“aikuwa dai wannan yaro bai kyauta mana ba da ya boye mana asalin shi.. lallai wadancan munafukan sun sani sarai shiyasa suka maqale mishi..”

“Wallahi Mama bazan bari ta aure shi ba.. idan dai har ba ni zai aura ba toh wallahi itama bazai aure ta ba”

“sha kurumin ki Layla.. ai dole ne in tashi tsaye akan wannan lamarin.. tunda abin ya zama haka dole ne in hada da neman taimako. Bari yanzu zan kira Hajiya Suwaiba dama kwanaki ta bani labarin malaminta wanda yake taimaka mata a al’amuranta na yau da kullum.. sai mu ji ko zai iya taimakon mu akan wannan. Dama dai harka ce ta kudi kuma muna da shi..”

“Yauwa Mama, kawai ina so a karkato hankalin shi zuwa gare ni ya aure ni.. Ni dai buri na shine a raba su.. idan ma haukatar da ita za’ayi ko sheqa ta lahira zai yi wallahi I dont care.. I only want Zayd for myself” ta fada yayinda take share hawayen fuskarta.3

“Kar ki damu Layla ta.. idan har na nemi taimako a wurin malamin Hajiya Suwaiba na tabbatar zamuyi nasara.. Yanzu dai kwanta ki natsu ki huta sannan ki cire damuwa a ran ki..  Zayd dai baya da Matar da ta wuce ke”2

Layla ta qarasa hayewa kan gadon ta kwanta yayinda Mama ta tashi tana fadin “banda sakarci irin nashi ma ai bai kamata ya gwada mace ta haka ba.. waye zai je wurin budurwa a talauce? ta ya zata saurare shi?? da ya fito a asalin shi ma ai da yanzu an sha bikin naku.. ki more arziki ya more kyakyawar Mata. ita kanta baqar banzan can na tabbatar ta san ko shi waye ne shiyasa ta maqale mishi din, na rasa yadda aka yi shi kuma ya amince da ita duk munin ta.. Qila ma asiri suka yi mishi shegu dangin mayu, Zan karya shi kuwa”

Layla dai ta dan ji sanyi a ranta a dalilin wannan shawarar ta Mama.. A yanzu ta fara jin qamshin zata zama matar Zayd.6

Gani nayi Mama ta dauki wayarta ta kira Hajiya Suwaiba.

toh fa…

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

ZAYD AHMAD FADOUL’S MANSION

UNGUWAN RIMI GRA

Wuraren qarfe biyar saura yana tsaye a makeken kicin din gidan wanda ya hadu iya haduwa yana qoqarin kammala Chicken and cheese salad din shi.

Zayd dai rabon shi da abinci a yau tun breakfast din safe.. Yinin yau din suna cikin meeting tare da clients dinshi da suka zo daga Kano.. he was so busy that he didn’t even had the chance to eat lunch don haka da yunwa ya dawo gida.

STORY CONTINUES BELOW

A dalilin yunwar da yake ji ne yayi deciding ya dafa simple meal wanda zai gama da sauri.

Bayan ya kammala yayi serving kanshi neatly ne ya koma kan daya daga cikin kujerun lafiyayyen Island din da yake kafe a kicin din ya zauna..

Abin mamaki dukda bala’in yunwa da yake ji abincin da ya zubo dan kadan ne.. Dama haka yake, zai damu mutane yana jin yunwa amma idan ya samu abincin kuma dan kadan yake ci.

Idan ka kalli yadda yayi serving abincin zaka rantse wani professional Chef ne yayi serving customers a 5-star restaurant ko kuma yayi presenting ma Judge a wani cooking competition..

Zayd dai haka yake.. Ya koyi girki wurin Ammin shi wadda kuka sani cewar professional cook ce.. Tabbas babu wata macen da zata gwada mishi iya girki.. He is a very good Cook!

Tunda ya fara cin abincin kuwa bai tsaya ba sai da yayi clearing plate din.. one cup of Fresh Orange juice dinshi ya shanye tas sannan ya miqe..

Wata na’ura na ga ya danna wanda nan da nan wasu samari guda biyu suka shigo sanye cikin uniform na aiki.. har qasa suka duqa suka gaishe shi ya amsa sannan suka duqufa aikin gyaran kicin din.

Zayd dai wayoyin shi ya janyo yana dubawa ya fita..

On his way to his room ne yayi dialing lambar wayarta..

AMEERA!

“Hello Yaya..” ya jiyo ‘yar qaramar muryarta mai dadi.

A lokacin ya bude qofar dakin shi ya shiga..

Tirkashi!! wani daki ne na gani mai bala’in kyau.. Mai karatu tsayawa baka labarin gidan Zayd gaba daya ma bata lokaci ne domin kuwa gida ne mai dan karen kyau.. komai designer komai mai kyau, A taqaice dai gida ne kamar Aljannar duniya..

“Hello Habibty.. ya kike??”

“Lafiya lau Yaya, ka dawo??”

“Na dawo Habibty..”

“masha Allah, ya hanya?? na san ka gaji ko?”

“Alhamdulillah, na gaji sossai amma hakan bazai hana ni zuwa ganin ki ba anjima..”

Murmushi kawai tayi ba tare da tace komai ba.

Zayd wanda ya haye kan lallausar king sized bed dinshi ya zauna ne yace “na ji kinyi shiru, ko baki so in zo ne?”

“ina so ka zo Yaya.. kar ka manta fa sau daya ka taba zuwa”

“kuma fa haka ne, gashi yau saura kwana tara bikin mu.. Allah ya nuna mun wannan ranar”3

Wannan karon ma shiru ya ji tayi bata ce komai ba..

“Habibty ban ji kin ce Ameen ba.. ko dai baki son aurena ne??”

“Ina so Yaya, kawai dai ina ta gani lokaci na gudu ne..”

“Ni kuma gani nayi kamar baya gudu Habibty.. ban qi a daura mana aure ba bayan sallan juma’a jibi”3

“Yaya??” ta fada cike da mamaki

“what?? ai na riga na gama shiri Habibty, kudin sadaki yana nan intact.. na hada miki kayan lefen ki… gidan mu kuma gobe zan je in goge shi.. so tell me, what else??”

“Allah sarki Yaya, Yanzu kai daya zaka yi aikin??ko zaka zo ka dauki su Aliyu su je su taimaka maka??” ta fada cike da tausayin shi.

Da sauri yace “No kar ki damu, ai gidan baya da girma besides akwai wani abokina da zai taimaka mun. Yanzu dai tell me, me kike so in zo miki da shi anjima?”

Tun kafin ya gama magana tace “babu komai Yaya, please kar ka wahalar da kanka”

“ai baki isa ba.. ko Apple ne zan riqo miki tunda dai na san mutumin ki ne”

STORY CONTINUES BELOW

Zayd dai duk wani abinda Ameera take so da wanda bata so ya haddace su tun ranar da ya sa ta bashi labarin ta a telephone conversation dinsu lokacin da yayi mata qaryar an bashi bonus.

“toh Yaya nagode..”

“Habibty godiya tun kafin in kawo?”

Dariya tayi bata ce komai ba.

“Ya su Umma da Abba?? kin ga fa bamu taba haduwa da Umma ba.. da akwai hali da na shigo mun gaisa da ita.. ko ya kika gani??”

Ameera wadda ta cika da murna ce tace “aikuwa na san zata ji dadi.. nima zan ji dadi sossai. Zan fadi mata”

A haka dai suka cigaba da random hira wanda yawanci shine mai yin tambayar tana amsa shi..

Da qyar ya qyale ta suka yi sallama.. Allah ya sani Zayd yana enjoying hira da Ameera.. A rayuwar shi ya kasance a very good listener! ya tabbatar idan suka yi aure he will have her talk to him all the time..

Lambar Bilal na ga yayi dialing yayinda yake fadin “Allah ma ya sani na qagara ayi auren nan in huta da wannan batar da kamarnin da nake yi”

Ko da Bilal din yayi answering ji nayi yace “get everything ready for later please….”

Bayan ya kashe ne ya sauka daga kan gadon ya wuce dressing room dinshi don shirin yin wanka.

☆☆☆☆☆☆

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Ameera wadda take zaune a kan gadon dakin Umma bayan ta gama hira da Zayd a waya ne na ga ta sauka tare da daukar hularta ta sanya a kai.

Ji nayi tace “bari in je in fadi ma Umma cewar Ya Zayd zai shigo su gaisa anjima”

Ko da ta fita straight kicin ta nufa tunda ta san cewar Umma tana can din.

A daidai lokacin da ta fito din kuwa Layla ma ta fito daga dakin Mama zata wuce dakinsu don yin wanka.

Wani gululun abu ne ya tokare mata maqoshi a dalilin hango Ameera da tayi.. Gaba daya abinda ya faru earlier a City-shelters ne yake dawo mata, daga wulaqancin da Zayd yayi mata har zuwa baqaqen maganganun da Bilal ya gaya mata..

Ranta yayi mugun baci yayinda ta ji kawai tana buqatar rama wulaqancin da aka yi mata..

Gani nayi ta bi bayan Ameera da sauri.

Ameera wadda ta shiga kicin bata ga Umma ba ta jiyo motsi a bayan kicin din ta waje don haka ne ta nufi hanyar qofar bayan kicin din..

Aikuwa tana daf da fita ne Layla ta tura ta da qarfin gaske… Ihu Ameera ta sa yayinda kanta ya bugu da cupboard sannan ta fadi akan hannunta sumamma..3

Umma wadda take bayan gidan jin ihun Ameera ne ya sanya ta rugo a guje.. ko kafin ta shigo Layla ta gudu domin kuwa itama ta firgita da abinda ya faru..

“Inalillahi wa’inna ilaihir raji’un… Ameera! Ameera!! na shiga uku.. Ameera…” Umma ce ta qaraso wurin ‘yarta jikinta yana rawa yayinda take kuka.. Jini ne yake ta zuba daga gaban kanta..

Da sauri ta zauna a gefen Ameera ta dago kanta tana kuka yayinda take girgiza ta..

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. ku taimaka mun.. Ameera don Allah ki bude idanuwan ki..”

Su Ibrahim ne suka shigo kicin din ta baya… Asali dakin su yana ta baya ne daga gefe shiyasa suka jiyo kukan Umma..

Gaba dayan su kuwa rudewa suka yi ganin Ameera a kwance bata numfashi.. Ibrahim da Munnir ne suka zagaye su yayinda Aliyu da Suleiman suka tsaya a tsaye suna ta rusa kuka..

“Umma me ya samu Ya Ameera?? ta mutu ne?” Aliyu ya tambaya yayinda jikin shi yake ta rawa..

Cikin kuka Umma tace “ban sani ba Aliyu” ta kalli Ibrahim tace “yi sauri ka je daki na ka dauki waya ka kira Abban ku..”

A guje Ibrahim ya fita daga kicin din yana ta kuka..

Ko da ya kira Abba cikin kuka ya bashi labarin abinda ya faru..

Aikuwa hankali a tashe ya dauko driver na staff bus din ma’aikatar su suka nufi gidan.. Cikin qanqanin lokaci suka iso.

Abba yana salati ya shigo gidan da sauri ya nufi kicin din.. Ko da ya qarasa wurin su da sauri ya janye ta daga jikin Umma ya dauko ta a guje ya fito da ita.. Gaba dayan su suka bi bayan su..

Umma tana kuka ta qarasa dakinta ta dauko hijabi sannan ta biyo bayan su.. tuni Abba ya sa Ameera a bayan mota yayinda Umma ta shiga bayan itama..

Ibrahim ne yace “Abba zan bi ku” Su Aliyu suna kuka suka ce su ma zasu je..

Abba wanda yake a rude ya kalli Ibrahim yace “ka shiga mu je.. ku kuma kuyi haquri ku zauna ku yi mata addu’a”

A guje Ibrahim ya shiga..

Munnir ne ya ruga ya bude musu gate yayinda direban ya ja suka bar gidan da sauri.

Layla wadda take tsaye jikin window tana kallo aka sa Ameera a mota.. Gaba daya jikinta yayi sanyi..

“Yanzu idan ta mutu fa? shikenan ni na kashe ta??” ta fada a sanyaye.

“Me ke faruwa ne na ji hayaniya a gidan?” ta jiyo muryar Mama.1

A firgice Layla ta juyo tana sosa kai tace “nima ban sani ba Mama, kawai dai na ga Abba da Umma sun fita da Ameera.. kamar batada lafiya ne, kuma na ga Ibrahim ya bi su..”

Tsaki Mama ta ja tace “shi kuma sakarai meye na bin su?? haka kawai wannan mayyar matar duk ta janye mun hankalin yara na”  ta wuce ta fita daga dakin.

Ko da ta fito Falon ta tarar da su Munnir zaune a qasa suna ta kuka.. A nan ne ta tambaye su abinda ya faru yayinda suka bata labarin abinda suka gani.. kicin din ta shiga ta ga jinin Ameera a qasa..

Aikuwa sai da jikinta ya dan yi sanyi ita ma..

Ji nayi tace “wannan irin jini haka.. ashe kuwa babu biki tunda amarya ta ji rauni”

About AIS

Check Also

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng  Washegari!!+ ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE UNGUWAN RIMI GRA …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *