ZABI NA CHAPTER 11 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 11 BY FADEELARH

Www.bankinhausanovels.com.ng 

3 days Later..

AHMAD MUHAMMAD FADOUL RESIDENCE

UNGUWAN RIMI GRA+

Kwance take a cikin Duvet a kan gadon dakin tana ta kuka yayinda Zaheera take zaune a gefenta tana lallashinta.

Tun ranar da ta farka aka sanar da ita komai ta birkice musu.. Roqon Abba ta dinga yi akan a warware auren don ita ba Zayd din da take so bane wannan amma sam Abba ya qi sauraron ta. Gaba daya yinin ranar ana ta faman lallashin Ameera amma ta qi sauraron kowa.. Wannan abu ya ba Aunties dinta mamaki sossai.. Zarah da Zaheera tare da ‘yan biyu kuwa har rasa bakin lallashi suka yi..

Ammi ce ma tayi qoqari ta shawo kanta har ta daina kukan da take yi amma fa ta qi yi ma kowa magana musamman Zayd wanda da zarar ya shigo dakin nata sai ta juya mishi baya tayi kamar tana bacci.. haka yake zama yayi ta mata magana yana bata haquri amma sam bata ce mishi komai.

Sossai wannan abu ya dame shi.. Da ka gan shi a ‘yan kwanakin zaka gane yana da damuwa.

Ko da ya ga abu ya qi gaba ya qi baya ne ya matsa ma likitocin akan a sallame ta tunda she is doing very much better, a ganin shi maybe change of environment will help clear her mind kuma ma shi kanshi ya gaji da asibitin..

Dr George ya amince Ameera ta tafi gida.. nan da nan yayi discharging dinta tare da basu medication dinta da kuma yi musu alqawarin zuwa duba ta.

A nan asibitin Abba da Umma suka zaunar da Ameera suka yi mata nasiha sossai sannan suka yi mata addu’a… tana ji tana gani suka tafi suka barta yayinda ta dinga kuka.

Ammi dai ta sani sarai idan ta bar Zayd ya tafi da Ameera wahala zai sha don kuwa ta kula yarinyar akwai kafiya da tsatsaurar ra’ayi..

Nan da nan tayi shawara da Zayd din akan lallai a wuce da ita gidan ta tayi koda kwana daya sannan ta tare.

Da farko bai so hakan ba don kuwa ya sa a ranshi lallai idan yayi ma Ameera bayanin komai zata gane.. all he need is space with her and he believes he can clear the air.. he couldn’t refuse his mom and so he had no choice but to agree to her decision.

A nan asibitin Zarah da Mustapha suka yi musu sallama..

Zarah tayi ma qawarta alqawarin zata ziyarce ta idan ta tare gidan mijinta.

Zayd ma ganin ko ya bi su matar tashi ba fuska zata bashi bane ya wuce Kamfanin shi inda ake needing attention dinshi for the past days…1

Tunda suka shigo gidan Abbu kuwa hankalinta ya qara tashi domin kuwa bata taba ganin danqareren gida kamar shi ba.. ta ya zatayi adjusting da irin wannan rayuwar?? Ga qannen shi Zaheera, Maheera, Meher harda dangin Ammi na Adamawa da suke maqale da ita kamar chewing gum.. Hatta Ridwan, Riyaz da Baby eesh (yaran Zaheera) suna nan maqale kamar sun san ta dama.. Ta ya zata yi adjusting da wadannan mutanen???

Duk inda ta juya all she see is kyawawan yara masu dogon gashi na larabawa da fulanin asali, ko alama bata dace ba a matsayin matar yayan su.. class dinsu bai yi matching ba.. for the first time ta amince da maganar Layla da tace ta fi dacewa da shi, atleast ita kyakyawa ce fara mai dogon gashi don haka ko banza sunyi matching a ta nan bangaren..

STORY CONTINUES BELOW

How she wish it’s just a dream… amma inaaa, it’s the reality for her.

Yanzu haka sai da suka hada mata ruwa tayi wanka sannan Ammi ta janye su gaba daya suka nufi kicin don dafa ma Ameera abinci.. (kun san Ammi da son girki especially wannan karon it’s for her daughter in-law) yayinda suka bar Zaheera a tare da ita.

“Ameera please ki cire damuwa a ran ki.. ki sa a ranki cewar zaki samu kulawar da kike so a wurin twin brother na..”

Ameera tayi saurin kallon Zaheera tana share hawayen ta tace “ban gane twin brother dinki ba… ku ma twins ne??”

“yes.. we are twins qila saboda we are not identical ne shiyasa baki kula ba.. na ga alama dai baki wani san komai akan Zayd ba maybe ma shiyasa kika bi kika damu.. bari in fadi miki briefly who your husband is”

Gani nayi Ameera ta tashi zaune ta natsu tana kallon Zaheera wadda ta ga lallai akwai kamarni na ‘yan uwa amma tabbas they ain’t identical unlike Meher da Maheera..

A yadda Ameera ta natsu zaka tabbatar lallai tana son jin labarin..

“Kamar yadda kika riga kika sani Abbun mu Ahmad Muhammad Fadoul asalin dan Saudi Arabia ne.. shi kadai iyayen shi (my grand parents) suka haifa.. My grand father was a twin amma twin brother dinshi ya rasu tun suna yara, He was into oil business, kafin ya rasu few years ago ya kasance one of the top oil distributors a Saudi Arabia.. burin grand father din mu akan Abbu shine idan ya girma yayi taking over business din shi amma kuma a bangaren Abbu yana da nashi burin, he had his dreams.. burin shi shine ya zama wani a qasar shi, wanda qasar shi zata yi alfahari da shi.. what better way than becoming an ambassador, someone who can help in the development of foreign policy with a host nation.. Dukda Grand father din mu bai so ba he had no choice but to support him.. Abbu ya karanta international relation a Bristol University a qasar Ingila, and that was where he met her- Ammi. Ammin mu Nana Aisha ‘yar nan qasar Nigeria ce, iyayenta fulani ne ‘yan Adamawa state.. A lokacin da suka hadu da Abbu a Bristol University itama karatu take yi, he was already in his final year and ita tana first year dinta studying Accounting.. Well, sun hadu suka fara soyayya.. manya suka shigo zancen har dai suka yi aure. Sun cigaba da zama a qasar Ingila inda Abbu yayi masters dinshi a can din yayinda Ammi ta cigaba da nata karatun.. Bayan sun gama ne suka koma Saudi Arabia and daga nan ne aka haife mu- Ni da Zayd. Bayan mu, Ammi ta qara haihuwa amma kwanan shi daya yaron ya rasu.. daga nan bata qara haihuwa ba sai bayan shekara goma sha hudu ta haifi Maheera da Meher wadanda suma twins ne. A lokacin da Su Maheera suke da shekara biyar ne Abba ya samu appointment a nan Nigeria inda yake wakiltar kasar Saudi Arabia and we settled in Abuja”

“tell me about you and him..” Ameera ta fada yayinda ta zama so much interested.1

Zaheera tana murmushi cikin tsokana tace “kina nufin about him dai ko??”

Ameera ta duqar da kanta cike da kunya tace “no.. both of you”

Zaheera tayi dariya tace “what can I tell you about us?? Ni da Zayd ‘yan biyu ne, tunda muka taso muke qaunar junan mu sossai.. it’s easier for twins of thesame sex to blend with eachother compared to those of the opposite sex but guess what, Ni da Zayd sossai muka shaqu da juna.. kullum muna tare, bacci ne kawai yake raba mu”

Dariya tayi sannan tace “could you believe cewar ranar da na fara ganin period dina Zayd na fara fadi ma?”

Ameera ta zaro idanuwa tace “Nooo”

Zaheera ta girgiza kai tace “Yes… it’s crazy but wallahi I just feel he is the closest person to me than every other person (not even Ammi).. he was actually the one that told Ammi.. A ranar bazan taba mantawa ba duk ya bi ya damu.. har hawaye yayi saboda ganin yadda na sha wahala.. Zayd is such a sweetheart tun muna yara.. dukda tare muka shigo duniya he has always been like an older brother to me, baya bari komai ya same ni.. I have always been the troublesome one amma a kullum shi yake taking blame for my every mischievous act.. we share a very strong bond that uptil today bamu iya yini bamu ji muryar juna ba.. thank God for technology we can see each other even if we are not close. Zayd yana da haquri sossai sannan yana da kirki, he supports me in everything.. kamar yadda na fadi miki he is a sweetheart and I dont intend to make you jealous but I swear I love him very much that I cant live without him” ta fada tana kallon Ameera wadda ta dan yi murmushi, murmushin da ta fi kama da yaqe.

“lokacin da muka gama karatun secondary school din mu a Saudi Arabia ne muka rabu.. he had to go to Cambridge university to study Architecture.. Ban fadi miki ba, Zayd tun yana qarami yake son zane.. I remember how his room looked like lokacin muna yara, drawing papers, crayons, pencils all over.. and guess what, babu abinda yake zanawa sai Gidaje da motoci.. dukda I wasn’t interested in all of those haka nake zama ina kallon shi yana yi tunda I cant be anywhere idan ba kusa da shi ba.. A kullum idan muna hira abinda yake fadi mun shine idan ya girma zai zama architect ya gina qaton company na qera gidaje sannan yayi hiring ma’aikata dayawa.. yana so company dinshi yayi fice not just in the country but all over the world. Again, duk wata latest mota da zata fito sai ya siye ta saboda yana bala’in son Mota a rayuwar shi.. A lokacin kallon shi kawai nake yi yana bani dariya… a tunani na burin is to big amma na manta da cewar Zayd is this person da idan yayi setting mind dinshi akan abu bazai taba hutawa ba sai yayi achieving wannan abun… Look at him today.. at the age of 29, he is the owner of City-shelters with head office in Abuja and branches in Kaduna and Lagos, yana da ma’aikata kusan guda dari biyar suna aiki a qarqashin shi.. ya samu contracts a qasashe da dama especially Dubai.. A yanzu haka ba latest mota ba na tabbatar babu abinda Zayd bazai iya mallaka ba a duniyan nan idan dai kudi yana siyan shi”

Zaheera ta riqo hannun Ameera tace “Gaba daya rayuwar Zayd is perfect sai dai yana da matsala a bangare daya..”

Zuciyar Ameera ce ta buga yayinda tayi saurin fadin “matsala kuma? wacce irin matsala?”

“Bai yi sa’a ba a bangaren mace da soyayya.. tabbas Zayd is an extremely busy person, baya da lokacin kan shi ma balle na soyayya amma it doesn’t give the women that crossed his life the right to hurt him.. first it was Na’eema and second your step-sister Layla..”

Ameera dai tun kafin ta ji ko wacece Na’eema ta ji ta tsane ta…

Muryarta tana rawa tace “wacece Na’eema”1

Zaheera ta dan bata rai sannan tace “wata sakaryar yarinya ce fa.. ‘yar qawar Ammi. Na’eema Abbas Turaki”

Cike da mamaki Ameera tace “daughter of former Governor na Jigawa state??”

“yes ita.. Allah dai ya sa yana da sauran kwana a gaba amma she would have ended his life a daren farkon su na aure…”3

“what??”whaaat??? aure??? Ya Zayd ya taba aure?? I mean uhmmm kina nufin..”+

“Hey relax..” Zaheera ta fada tana murmushi a dalilin wani tsananin kishi da ta hango a idanuwan Ameera..

“Yeah, Zayd ya taba yin aure amma it lasted for few hours.. babu abinda ya faru a tsakanin su don haka ke ce zaki zama…”

“Ya Zaheera please…” Ameera ta fada cike da kunya yayinda Zaheera ta fashe da dariya tace “ah okay, sorry about that..”

Ta gyara zama sannan ta cigaba da fadin “..Well, Hajiya Rabi ta kasance qawar Ammi.. irin matan nan ne masu son abun duniya… kin san yadda siyasar qasar nan take, da zarar mutum ya sauka daga mulki shikenan zaki ga kamar walqiya arzikin shi ya qare.. I wonder why it’s so. Shekaru biyu da suka wuce ne Hajiya Rabi ta nace ma Ammi akan su hada Zayd da ‘yarta Na’eema aure.. A wannan lokacin dama burin Ammi ta ga Zayd yayi aure saboda tana tsoron yadda kudin shi suke multiplying by the day sannan baya da mata balle magaji.. again Ammi ta kula sam mace bata gaban Zayd.. tunda yake bai taba yin wata budurwa ba, toh ya za’ayi yayi budurwa when he doesn’t even have time for himself.. idan tayi mishi maganar aure sai yace yana kan nema bai samu ba, da ta gaji ne tace mishi zata nema mishi mata and he gave her the go ahead.. a cewar shi ta sauqaqe mishi babban aiki.. aikuwa ba tare da bata lokaci ba tayi mishi maganar Na’eema sannan tace ya je gidan su ya ganta…”

Zaheera ta fashe da dariya sannan tace “Aikuwa sai da yayi wata uku bai je ya ga Na’eema ba, it wasn’t intentional though.. he was so busy that he didnt have the time to go see her. Na tuna lokacin sai da Ammi tayi fushi da shi sannan ya je.. Bayan ya dawo da muka yi magana a waya na tambaye shi what she looked like and whether he liked her or not kin san me yace??”

Ameera ta girgiza kai yayinda take kallon Zaheera..

“cewa yayi wai bai kalle ta ba don haka bai san ko ya take ba sannan tunda Ammi ta zabar mishi ita yasan tana da hali mai kyau ne..”

Ameera ta zaro idanuwa tace “what??”

Zaheera tana dariya tace “it’s the level of how unserious he is when it comes to women and relationships.. tun daga ranar da ya je bai qara zuwa ba.. dayake ya ba Ammi greenlight sai kawai aka fara shirin biki, wata biyu kacal aka sanya.. Na’eema tun tana sa ran Zayd zai qara dawowa gidan su ko kuma atleast ya kira ta a waya har ta cire rai.. daga baya da tayi ma Mom dinta complain shine ta fadi ma Ammi.. Ammi ta kira Zayd tayi mishi fada ya bata haquri sannan yace a turo mishi lambar wayarta tunda dai ba zuwa zai yi ba.. aikuwa fa ko da aka tura mishi bai kira ba, I doubt idan ma yayi saving.. Ke in taqaice miki zance dai Na’eema ce ta dinga kiran shi a wayar.. watarana yayi picking wata rana kuma ya jefa ta voicemail”

STORY CONTINUES BELOW

Ameera dai mamaki ta dinga yi. A yadda take jin labarin Zayd a yanzu tana mamakin yadda ya qasqantar da kanshi ya dinga zuwa gidan su don neman soyayyar Layla??.. how did he do it?? does that mean he really loved Layla??? is he still in love with her???

“haka dai muka shirya komai na bikin with zero interest a bangaren ango.. Da lokacin bikin yayi kuwa cewa yayi babu wani events din da zai halarta don haka we should go ahead without him.. Kudi kuwa ya bayar da su har sunyi over.. ita kanta Na’eema she made a fortune outta the poor soul saboda duk wasu hidimar da tayi shi yayi sponsoring.. A haka dai aka daura auren su aka kai ta daya daga cikin gidajen Zayd wanda yake Maitama…”

Zaheera tayi shiru tana kallon Ameera wadda take cike da tension.. Haka kawai Ameera ta tsinci kanta cikin fargaban abinda zata ji next..

“A daren da aka kai ta Zayd ya dade a gida Ammi da Abbu suna ta ja mishi kunne tare da nuna mishi muhimmancin aure.. sun ja mishi kunne akan kar ya wulaqanta ‘yar mutane kuma ya tabbatar ya bata kulawar da yakamata because idan har ya cutar da ita Allah bazai qyale shi ba.. A wannan lokacin Zayd was willing to accept his wife suyi zaman lafiya, he promised himself zaiyi qoqari ya bata dukkan kulawar da yakamata and he will try to love her da zuciya daya.. atleast ya bar gidan Ammi da wannan qudurin only for us to find out that he has sent her packing in less than an hour”

“what happened?? me tayi mishi?” Ameera ta tambaya muryarta tana rawa.

“A lokacin da ya koma gidan shi ya nufi section dinta yana daf da shiga dakinta ne ya jiyo ta tana magana da Mom dinta a waya.. da ya sa kunnen shi da kyau ne ya ji tana fadin bazata bari komai ya shiga tsakanin su ba sai ya sha poisoned drink din da ta hada mishi wanda ko minti biyar bazai yi ba zai mutu and afterwards zata gaji part of his wealth a matsayinta na widow dinshi…”5

“Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un.. akan dukiyar shi tayi niyyan kashe shi???” Ameera ta fada hankali a tashe

“Yes Ameera, kudin da I am sure idan ta tambaye shi ma zai bata even more than what she will supposedly inherit idan da ta kashe shi din…”

Jikin Ameera ne yayi mugun sanyi yayinda Zaheera ta cigaba da fadin “Kin san abinda yayi?? a lokacin da ya bata takardar sakinta ya bata cheque worth millions of naira da takardun gidan da take ciki kyauta and he left.. abinda take so kenan kuma ya bata and he stayed alive”2

Ameera tace “what?? he did that??? maimakon yayi reporting dinta for attempted murder??”

Zaheera ta fashe da dariya tace “Zayd will never do that.. baya taba rama sharri da sharri sai dai da alkhairi. Na tuna lokacin Ammi was very sad and devastated.. ta hada Dan ta (wanda take bala’in so) da matar da ta kusa kashe shi.. She felt guilty and was seriously ashamed of herself. She couldn’t even look Zayd in the eye. Da qyar aka shawo kanta ta rage damuwa amma fa har gobe idan ta tuno sai ta ba Zayd haquri.. shi kam tun baya jin dadin yadda ta sa abun a ranta har ya koma yana ma tsokanarta da abun. Hajiya Rabi da Na’eema har gida suka zo gwiwowin su a qasa suna roqon Ammi amma ta qi sauraron su.. Ammi was beyond angry that she threw them out of the house like dogs.. tayi warning dinsu akan idan basu fita daga rayuwar mu ba zata kai su qara.. Dadyn Na’eema ma ya ba Abbu haquri sannan ya gwada mishi if he had known cewar abinda suke qullawa kenan he wouldn’t have let them.. Abbu yayi accepting apology din shi amma fa he made it clear to him cewar babu maganar aure a tsakanin Zayd da Na’eema har abada. the last time we heard ma sun sayar da gidajen su harda wanda Zayd ya ba Na’eema sun bar Abuja sun koma Jigawa because somehow maganar ta fito mutane sun ji and it became unbearable for them to continue to live here, whether the Dad was involved or not still remains a mystery”

Zaheera ta saki ajiyar zuciya sannan tace “and then after the drama with Na’eema came na Layla, Your step-sister.. Yanzu kuma ga ki a matsayin matar mu”

STORY CONTINUES BELOW

Zaheera ta riqe hannun Ameera tace “I swear to God Zayd yana son ki Ameera, ya fadi mun sannan na gani a idanuwan shi, na gani a actions dinshi.. I really don’t know how you did it amma kin kai matsayin da hatta Layla bana ji ta kai a zuciyar shi.. Please I beg you, take care of him.. Na sani cewar you have alot of questions to ask him.. feel free to ask him and I am sure zai fadi miki gaskiyar shi.. and another important thing, please kiyi qoqari ki sa idanuwa akan shi.. Zayd yana over stressing kanshi, try as much as possible to help minimize it for him.. ban san yadda zaki yi ba but you have to do it.. haka a duk lokacin da kika ga yayi isolating kan shi toh tabbas he is sick, ko kadan baya qaunar asibiti shiyasa idan yana ciwo he doesn’t tell anyone don kar ace ya je asibiti ko ya sha magani…”

Ita dai Ameera tuni hankalinta yayi nisa a tunani.. tabbas bata so kasancewar Zayd mai kudi ba, kudin ma na fitar hankali.. bata son irin rayuwar da ta tsinci kanta a ciki toh amma kuma Allah ya jarabce ta da son Zayd, irin son da zata iya sacrificing mishi komai nata, a ciki kuwa harda farin cikin ta.. ta tausaya mishi da ta ji labarin shi a wurin ‘yar uwar shi and tayi alqawarin she will always stand by him and protect him with her life if necessary.4

Qwanqwaso qofar dakin aka yi sannan aka bude.. Masu aikin Ammi ne suka shigo da trolleys guda biyu na abinci kala-kala.

Ammi ce ta shigo tana fadin “Allah dai ya sa Ameera ta natsu ta daina kuka..”

Zaheera tana murmushi tace “ta daina Ammi..”

“Masha Allah.. yanzu dai abinci zaki ci, fadi musu wanda kike so su zuba miki” Ammi ta fada yayinda ta qaraso ta zauna a kan gadon itama making everything awkward for Ameera.

Ammi ta shiga lissafo mata sunan abinci kala-kala yayinda masu aikin suka dinga bubbude abincin.. wani qamshi mai dadi ya dinga tashi.. the kind that is irresistible!

Ita dai Ameera har ta gama lissafowa babu wani abincin da ta gane sunan shi a ciki don haka ne ta saita murya a hanakali tace “na qoshi” dukda kuwa deep down ranta ya biya a dalilin qamshin da ke ta tashi.

Ammi tace “what?? me kika ci da har zaki qoshi Ameera?? ke da kika kwanta jinya… hala ba kya cin abinci ne??? aikuwa dole Zayd ya sa miki ido…”

Zaheera ce tace “hmmm.. Ammi ina ganin don bata taba tasting abincin ki bane shiyasa..”

Kafin Ameera tayi magana ne Zaheera ta sauka daga kan gadon ta nufi gaban trolley din ta fara nuna ma masu aikin abincin da zasu zuba mata.. Yadda Zayd yake sa abinci kala-kala a plate din shi amma in small quantities itama haka Zaheera ta sa suka zuba mata.

Bayan sun zuba ne ta sallame su ta janyo bed tray table ta dora a kan gadon sannan ta dora plate din tare da fresh Orange juice tace “bisimillah.. idan kuma kina so a dinga baki ne fine..”

Ameera ta dago kanta da sauri tace “zan ci da kaina Ya Zaheera.. nagode”

Ammi dai tana ta kallon yarinyar yayinda take birge ta sossai.. ita dai haka kawai ta ji tana bala’in son Ameera tun ranar da ta ga hoton ta.. there is something about the girl that tells her cewar she will be the perfect companion for her son…

Ameera wadda ta ga fork, knife da spoon neatly kept a gefen plate dinta ta sa hannu ta zaro cokalin.

Kallon plate din take yi yayinda ta rasa wanda zata fara da shi..

“dont mind me ooo, haka mijin ki yake cin abinci shiyasa na zuba miki haka kema.. gwara ki fara practice tun yanzu” Zaheera ta fada

Tabbas Ameera ta san hakan.. ta tuno lokacin da ta je gidan Zarah da suka dafa abinci kala-kala har take fadi mata na Zayd ne.

Da na gabanta ta fara.. aikuwa tana kai cokalin farko bakinta na ga ta lumshe idanuwa.. Ameera dai bata taba cin abinci mai dadin wannan ba.. first time da ta ci abincin da ya fi na Umman ta dadi.

STORY CONTINUES BELOW

“Delicious right???” Zaheera ta tambaye ta

“not as delicious as mine, yeah???” suka jiyo muryar shi a bakin qofar dakin.

Gaba dayan su suka juyo suka kalle shi yayinda ya kashe musu ido daya.

Ameera dai zuciyarta ce ta buga a wannan lokacin a dalilin ganin shi.. wai yanzu wannan kyakyawan ne mijinta?? Zayd din da take bala’in so a rayuwarta ya zama nata??? what a dream come true for her..

A yanzu da take kallon shi sanye yake cikin qananan kaya na wandon Sweat da polo T-shirt.. yayi kyau sossai.. da alama ya je gida yayi wanka sannan ya zo because he looked fresh with zero stress a tattare da shi..

Da sauri ta duqar da kanta yayinda zuciyarta take ta bugawa.

“a wurin wa ka koya?” Ammi ta fada tana hararar shi.

Yana dariya yace “a wurin ki Ammi na” ya qarasa wurinta yayi mata kiss a kumatu sannan yace “but I insist nawa ya fi dadi.. You should be proud”

Ammi tana murmushi tace “I am proud of you son”

“tanx Ammi dearest..”

Ya nufi wurin Zaheera ya ja kumatun ta yace “sweetheart how you?” tana murmushi tace “i am good.. kayi kyau as always”

Kashe mata ido daya yayi yace “shukran..”

Gani nayi yana kallon Ameera wadda take ta jujjuya cokalin hannunta sannan ya kalli Zaheera wadda tayi mishi signal akan he should go ahead..

Murmushi na ga yayi sannan ya hau gadon ya zauna very close to Ameera ya sa hannu yana shafa gefen fuskarta yana kallon stitches din da aka yi mata a saman goshin ta very close to her hairline.

“I am glad you’ve stopped crying Habibty.. how are you feeling?? ciwon yana miki zafi??”2

Gaba daya Ameera a rude take.. qamshin turaren shi mai dadi ne ya cika ta yayinda ta shiga wani yanayi na daban a dalilin shafa gefen fuskarta da yake yi… bata san lokacin da ta lumshe idanuwan ta ba yayinda zuciyarta take ta bugawa.

Da qyar ta girgiza mishi kai alamar a’a.

Hannunta wanda tayi targade ya kamo yana dubawa yace “wannan fa?? yana ciwo?”

Nan ma girgiza mishi kai ta qara yi alamar a’a

“meyasa bakya cin abincin?”

Ba tare da ya jira wani abu ba ya karbi cokalin hannun ta sannan ya debi abinci ya kai saitin bakinta yace “oya open your mouth”1

Ameera dai bata san lokacin da ta bude baki ba ya sanya mata.. her weakness- she can never refuse Zayd saboda bala’in son shi da take yi.

Ya dago next spoon zai kai bakinta wanda tuni ta bude ne na ga ya dawo da spoon din ya kai bakin shi..

Hakan ya sanya Ameera ta dago kai ta kalle shi cike da mamaki yayinda Zaheera da Ammi suka fashe da dariya.

“there, abinda nake son gani kenan.. your eyes” ya fada yana murmushi yayinda Ameera tayi saurin duqar da kai itama tana murmushi.2

Why is the guy doing this in front of his mom??3

Wayar shi ce tayi ringing yayinda na ga ya duba sannan ya sanya ta silent ya mayar ya ajiye.

Zaheera wadda ta leqa wayar ta ga sunan Manager din shi na Abuja ce tace “Bazaka yi answering ba???”

“Nope”

“aaah lallai a gaishe ki Ameera.. you have just done something extraordinary.. the first time da mijin ki yake sa wani abu a gaban City-shelters and that’s YOU.. wannan kadai proof ne da zai tabbatar miki da lallai zaki samu irin kulawar da kike nema…”

Wani mugun sanyi Ameera ta ji a ranta jin maganar Zaheera.

Babu abinda take so sama da soyayyar Zayd da kuma kulawar shi… toh amma still akwai abubuwan da take so yayi mata clarifying- things about Layla..

oh yeah????4 days later!!

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Kwance take a cikin bargo tana ta kuka kamar kullum..

Layla dai tun ranar da suka ji zancen auren Ameera ta shiga tsananin tashin hankali.

Dukda Hajiya Suwaiba ta basu assurance cewar da zarar ta dawo ta kai buqatun su zuwa wurin malaminta komai zai daidaita hakan bai sa ta ji sanyi ba a ranta.

A ranar kuwa har suma tayi saboda tashin hankali.. Mama ce ta yafa mata ruwa ta farfado.. babu yadda Mama bata yi ba akan su je asibiti amma sam ta qi.. A wannan lokacin dama ba’a sallami Ameera ba don haka ko alama bata son zuwa asibitin balle ta gan ta.

A cikin ‘yan kwanakin nan Habib ya matsa mata da messages da kiran waya amma tayi watsi da shi.. qawayen ta kuwa har gida suka zo suka jajanta mata abinda ya faru.. kamar kullum Haleema ta dinga roqon ta on behalf of Habib especially now that she has lost Zayd amma ta qi.

Su Maryam dai kallonta suka dinga yi suna mamakin dalilin da ya sanya ta guje ma Habib one time.. sun tabbatar ba qaramin laifi yayi mata ba.. babu yadda basuyi ba da Haleema ta sanar da su abinda ya faru tsakanin su amma ta qi.. tabbas dukda su din qawaye ne akwai abubuwa irin wannan da basu sani ba a game da Haleema da Layla..

Yusrah da Maryam basu taba sanin cewar Layla da Haleema were having sex da guys din nasu ba and they decided to leave it that way because sun sani sarai duk ranar da suka gano it might be the end of their friendship.

Umma kuwa duka ne kawai bata sha ba a wurin Mama amma idan har baqaqe da munanan kalamai na kissa da sun kashe ta.. safe, rana da dare zagi da ashar babu kalan da bata sha daga wurin Mama.. Hatta su Ibrahim an hada da su.. su kam har duka Mama tayi musu amma bata huce ba.. Haka qannen Abba su Anty Khadeeja suma bata qyale su ba.. a cewarta suma munafukai ne.. Shi kan shi Abba duk tsaurin ido irin nashi sai da ya kwashi rabon shi dukda yawanci a bayan kunnuwan shi take yi..1

Daga Abba har Umma basu kula ta ba saboda dama sunyi anticipating bori irin wannan daga wurin Mama.. idan ta gaji zatayi accepting reality and move on, Allah yasani whatever is happening to her and her daughter is no one’s fault except for theirs and theirs alone…

Qannen Abba dai sai daga baya suka san abinda ya faru da har Mama take behaving that way.. su kam har ga Allah sun ji dadin abin don kuwa sun fi son Umma, tana kyautata musu sossai.

Mama ce ta shigo dakin riqe da wayarta tana murmushi tace “ke tashi ki saki ranki.. Hajiya Suwaiba ta kira ni yanzun nan ta dawo.. tace gobe da sassafe tana nan zuwa ta karbi saqon mallam.. nan da ‘yan kwanaki kadan zaki shiga daula”7

For the first time in days Layla tayi murmushi yayinda ta tashi zaune da sauri tace “dagaske Mama.. yauwa wallahi sai yanzu na ji dan sanyi. Finally zan kori tsinaniyar yarinyar nan daga rayuwar shi dukda ta riga ni more.. “

“Maganar rigan ki morewa ma bata taso ba Layla.. ke zaki mora har qarshen rayuwar ki don haka kawai Allah ya kaimu gobe Hajiya Suwaiba ta zo mu ji zance”

“toh Mama, ni kam ko nawa ne ake buqata ki bayar idan dai har zan samu Zayd an gama”

A haka dai suka cigaba da qulle-qullen mugun abun su.

STORY CONTINUES BELOW

♤♤♤♤♤♤♤♤

Washegari!!

Wuraren qarfe Goma na safe Hajiya Suwaiba tana zaune a dakin Mama suna maganar zuwa wurin malam.

“Wai dama Malamin yana can Hadeja ne?? ai nayi tunanin nan garin ne har ina fadin sai mu je tare..” mama ta fada tana kallon Hajiya Suwaiba wadda take zaune a qasa ta miqar da qafafuwanta, Fuskarta duk ta ji bleaching ga wasu zinarai a wuyan ta da kunnuwanta.. babbar mace kenan! irin matan da Mama take son yin mu’amala da su.9

“toh yanzu me zai hana ki zuwa Hajiya Hindatu?? ai nayi tunanin tare zamu je” cewar Hajiya Suwaiba

“Anya kuwa.. ai Abban su bazai bari inyi tafiya ba.. ina zan ce mishi zani toh??”

tsaki Hajiya Suwaiba ta ja sannan tace “ai kin ji tsiyar.. gaskiya ke din wata iri ce.. ai bai kamata ace sai abinda ya fada za’a yi a cikin gidan nan ba.. Ai yakamata ace tuntuni ke kike mulki a cikin gidan nan.. Gaskiya Hajiya Hindatu kinyi sake dayawa.. wai ma ban tambaye ki ba, ya aka yi kika zauna tsawon shekaru kina fama da kishiya bakiyi maganinta ba?? ai gaba dayan su daga shi har ita basu isa su qetare duk wani sharadin da zaki gindaya a cikin gidan nan ba..’

Shiru Mama ta dan yi tana tunani sannan tace “kuma fa haka ne Hajiya Suwaiba.. wallahi wannan din bai taba zuwa mun a rai ba..” tayi murmushi tace “toh ai kin ga dadin amintaka da irin ku kenan.. ba gashi yanzu kin wayar mun da kai ba? yanzu dai yadda za’ayi mu fara da aikin yarinyar nan tukun don kuwa wallahi kwana biyu duk ta bi ta lalace..”

“ai wannan din an gama.. yanzu dai tunda bazaki iya zuwa ba sai ki fadi mun dalla-dalla abinda kuke so sai ki bani wani kaso a cikin ladan aikin Malam in kai mishi.. in ya so daga baya idan aiki yayi kyau sai a kai mishi cikon. ko ya kika gani???”

“hakan za’ayi qawar arziki.. ai duk bayanin da nayi miki a baya shine..”

ta miqe ta nufi wadrobe dinta ta bude tare da sauko da qatuwar Ghana-must-go ta kudi tace “yanzu nawa zan baki??”

Hajiya Suwaiba dai sakin baki tayi cike da mamaki tana qare ma Ghana-must-go din ido.. A ranta ne tace “duk kudi ne a ciki ko me??”6

“ki kawo kamar dubu dari biyar mu gani..” ta fada yayinda take kallon Mama ta gani ko zata girgiza jin hakan amma ga mamakinta sai ta ji Mama tace “toh”

wato hakan yana nufin kudade ne masu yawan gaske a cikin Ghana-must-go din. Babban magana!

Gani tayi Mama ta qirge kudade sannan ta mayar da Ghana must go din cikin wadrobe.

Ko da ta miqa ma Hajiya Suwaiba dubu dari biyar da hamsin ta gani..

“sai ki shiga mota ki sha ruwa a hanya.. Allah yasa mu dace” Mama ta fada

“Ameen Hajiya Hindatu.. Gobe da safe zan kama hanya.. idan komai yayi kyau zuwa jibi zan juyo”

♤♤♤♤♤♤♤♤♤

ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE

UNGUWAN RIMI -GRA

A yau kwanan Ameera daya a gidan mijinta.

Tun ranar da Zaheera ta bata labarin rayuwar Zayd ta Samu natsuwa.. Su Ammi dai sun kula ma kamar bata sakin fuska sai ta ga Zayd din.. dukda ba wani magana take yi mishi ba amma da ta gan shi sai mood dinta ya canza to a happy one.. da alama dai tayi accepting auren wholeheartedly.

Ganin haka ne Ammi tayi ma Zayd magana akan tarewar Ameera tunda all is good and he was beyond happy to hear that.. Allah ma ya sani ya gaji da zuwa gidan Ammin don ganin matar tashi with all eyes on them.2

Nan da nan aka shirya Ameera aka kai ta gidan mijinta.. Gida danqarere, qaton gaske ga kyau na bala’i kamar zane. Ameera dai ta qarasa zama baqauya domin kuwa duk yadda ta ga haduwar gidan Abbu da na Zarah basu kai na Zayd ba.. Mai karatu kar mu bata lokaci wurin kwatancen gidan Zayd, just keep fantasizing…!!

STORY CONTINUES BELOW

Su Anties dinta Aminatu, khadeeja da Zainab tare dasu Ibrahim sun je sun ga gida.. Sun ji labari cewar Zayd yana da kudi amma ganin wannan danqareren gida da dukiyar da aka narka a ciki sun fahimci kudin nashi na fitar hankali ne.. aikuwa dole ne hankalin Layla ya tashi, dole kuma suyi hauka ita da uwarta toh amma kuma aikin gama ya gama.

Sossai suka ji dadin yadda Qannen Zayd da ‘yan uwan Ammi suka karrama su.. ko alama basu da girman kai.

Nan da nan kuwa gida ya cika da abokanen arziki.. qawayen Umma da makwabtan su suka dinga tururuwa zuwa ganin gida tunda dama ba biki aka yi ba, haka qawayen Ammi na nan Kaduna ma suka dinga zuwa..

A nan dai aka dinga kallon kayan lefen Ameera da ba’a samu gani ba… akwatuna saiti shidda, guda talatin da shida danqare da kaya masu bala’in tsada.. Ga kuma makullan manyan motoci sabbi gal har guda uku… mutane dai sun girgiza ganin wadannan kaya, an sa albarka yayinda aka dinga yi ma Ameera fatan alkhairi.

Haka dai mutane suka tafi suna labarin kayan lefe da kuma gidan Ameera.. tuni an baza labari a social media yayinda aka dinga reposting ana ta commenting with so many girls wishing they were in Ameera’s shoes.

*************

Da daddare wuraren qarfe tara suna zaune a main sitting room na gidan suna hira..

Zaheera, Maheera, Meher, Mustapha, Zarah, Ameera, Zayd…

Su Ridwan da Riyaz (yaran Zaheera) suna ta wasan su a tsakar falon.

Maheera da Meher as usual suna nan maqale da Ameera wadda take riqe da Baby Eeesh (‘yar Zaheera) yayinda Zaheera take zaune tare da Zayd.. ita kuwa Zarah tana maqale da mijinta.

Zayd dai hira suke ta yi amma gaba daya hankalin shi yana kan matar shi wadda take so calm and collected.. duk wani motsin Ameera a idanuwan shi.

Mustapha yana kallon shi yace “abokina na San ka qagara gobe kowa ya watse ya baka wuri kai da amarya ko?”

dayake an kira Ammi daga Cilantro an sanar da ita ana buqatar attention dinta shine tace su Zaheera su shirya gobe zasu koma Abuja tunda dai komai normal.. gwara su bar newly wed din su sha iska haka nan…

“Wallahi kuwa abokina, we have alot to…”

“hey shut up akwai yara a nan??” Zaheera ta fada yayinda Ameera ta ji kamar ta nitse don kunya. Su Zarah kuwa sai dariya suke yi.1

“I wasnt about saying anything wrong Sweetheart”

“still” ta fada in a reprimanding tone yayinda su Mustapha suka cigaba da yi mishi dariya.

Meher ce tace “Yanzu shikenan Akhiyy anan zaku zauna ba Abuja ba??”

“Yes princess, for now yes.. Habibty tana zuwa school so she needs to be here and I also need to be where she is..”

“toh ayi mata transfer ta dawo Abuja mana” Maheera ta fada.

Shi kanshi Zayd yayi wannan tunanin amma ya sani cewar Ameera will go against it especially because iyayenta suna nan and even her friend Zarah is here… Zata fi sakewa a nan din for now!

“No princess, Habibty will not like the idea… kar ku damu idan anyi hutu zan dinga kawo muku ita and kuma zaku dinga zuwa.. hey, even on weekends if I am not busy I will bring her”

Meher ce ta kalli Zaheera tace “ni kam dama ku bar mu a nan mu zauna tare da su Akhiyy tunda ana hutun school ne”

Zayd ya zaro idanuwa yace “whaaat?? wa ya fadi muku ana zama gidan amarya daga tarewar ta?? don Allah ku tafi ku bar ni da matata.. yanzu haka don bani da yadda zanyi da ku ne..”1

STORY CONTINUES BELOW

Zaheera tayi mishi wani irin kallo tace “wato da ka kore mu ko? toh babu inda zamu je.. muna nan, sai gobe zamu tafi”

Ameera dai tashi tayi da sauri riqe da Baby Eeesh ta bar falon a dalilin kunyata ta da Zayd yake yi.. A da tana yi mishi kallon shiru-shiru babu ruwan shi ashe ba haka bane.

Maheera da Meher ma nan da nan suka miqe suka bi bayan ta.. Su kam Allah ya sani suna son Ameera.

Zarah ce tace “yayana duk ka sa qawata ta cika da kunya ta bar mana falon.. you no try for her at all”3

“toh wai me nace..”

“Nothing Mr. Romeo.. Ubangiji dai Allah ya baku zaman lafiya, ya kawo ‘yan biyu dayawa” cewar Mustapha.

“Ameen” gaba dayan su suka fada.

Haka dai suka cigaba da hirar su har su Mustapha suka yi shirin tafiya gida.. Zarah har daki ta je tayi ma qawarta sallama..

Wani ikon Allah kuwa har yau basu samu sun zauna sunyi magana akan abubuwan da suka faru ba a ‘yan kwanakin nan..

Ni kuwa nace yakamata su zauna!!

♤♤♤♤♤♤♤♤

Washegari Zayd da Ameera ne suka mayar da su Zaheera gida.. Instantly suka fara shiri don tafiya airport..

Dayake private jet din Abbu na jiran su a Airport din nan da nan suka kammala shirin su suka tafi.. Har airport din su Zayd suka raka su yayinda Ammi take qara yi musu nasiha akan su kula da junan su sossai..

Su Maheera kuwa sun yi ma Ameera alqawari akan kullum zasu kira ta a waya su gaishe ta..

A haka dai suka yi sallama suna ta kewar juna.

Sai da jirgin su ya tashi ne su Zayd suka juyo..

Gidan su Ameera suka wuce straight don kuwa ya sani sarai Ameera tana missing gidan nasu just dai bazata fadi bane.

Ka kyauta Romeo!!

♤♤♤♤♤♤♤♤

GIDAN MALAM FAROUQ ABDALLAH

MALALI

Yaran Gidan ne zaune a falo.

Layla tana kwance a kan kujera tana latsa waya yayinda su Ibrahim suke kallo..

“Allah sarki Ya Ameera, wallahi I am missing her very much” Ibrahim ya fada

Suleiman ne yace “wallahi nima haka, ka ga fa da yanzu ta siyo mana sabon Indian film muna kallo”

“Umma tace nan da kamar kwana biyu haka zamu iya zuwa gidan ta kuma ai” cewar Aliyu

Munnir ne yace “Dagaske?? kai amma na ji dadi.. ina son gidan wallahi, very big and beautiful.. ashe Ya Zayd mai kudi ne sossai shine….”

Layla ce ta katse shi tare da fadin “Dan ubanku meye kuke cika mun kunne da surutun banza? wallahi zanyi muku dukan banza idan kuna..”

“Assalamu alaikum” ta jiyo muryar Ameera wadda ta haddasa mata da faduwar gaba.

Ibrahim ne yace “wa’alaikis Salam” yayinda duk suka miqe suka rugo wurin Ameera a guje..

Zayd wanda yake biye da ita kuwa ganin yadda yaran suka rugo a guje sai yayi saurin janyo ta jikin shi tare da dakatar da su yace “Whoa.. qanne na ku bi ahankali kar ku karya mun mata mana..”1

Gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda Layla wadda ta cika da baqin ciki ta ji kamar ta mutu ganin Ameera maqale a jikin Zayd.

“Ya Zayd bazamu karya ta ba dagaske” Aliyu ya fada yayinda suke dariya.

STORY CONTINUES BELOW

Ita dai Ameera tunda Zayd ya rungume ta duniyar ta canza gaba daya.. wani irin sanyi ne yake ratsa ta yayinda ta ji kamar su kasance a hakan har abada..1

Layla wadda tuni ta tashi zaune sai kallon su take yi cike da tsananin bacin rai.. wani mugun kishi ne hade da baqin ciki suka rufe ta yayinda jikinta yake ta rawa..

Umma ce ta fito daga dakinta tare da su Anty Khadeeja

“ashe baqi muka yi a gidan” cewar Umma

Anty Zainab ce tace “Su Ameera amare.. lallai kam ana ji da wannan angon”

Zayd wanda ya kula Ameera tayi nisa ya tabbatar bata ji su ba don kuwa da ta ji tuni zata zare jikinta daga nashi..

Bakin shi ya kai saitin kunnen ta yace “Habibty ga su Umma fa sun fito..”

Zaro idanuwa tayi da sauri ta janye daga jikin shi cikin kunya yayinda duk ta bi ta rude..1

Su Ibrahim ne suke ta yi mata dariya yayinda Layla ta ja mugun tsaki ta miqe da sauri ta wuce daki tana kuka.. her reaction went unnoticed by all of them present amma kuma sam babu wanda ya bi ta kanta.

“Umma ina wuni”

“sai yanzu kika gan ni Ameera??”

Ameera ta duqar da kan ta cikin kunya tace “kiyi haquri Umma.. dama fa”

“ba sai kin bani haquri ba.. ai na ga komai” Umma ta fada cike da tsokana yayinda su Zayd suke ta yi ma Ameera dariya.

Zayd dai har qasa ya duqa ya gaida Umma da su Anty khadeeja.. ita ma Ameera ta gaishe su yayinda suka dinga tsokanarta tana noqewa.

Su Ibrahim dai excusing kansu suka yi yayinda suka koma dakin su.

Umma ce ta kalli Ameera tace “ki tashi ki hado ma mijin ki kayan motsa baki mana..”

Cike da kunya Ameera ta tashi ta nufi kicin yayinda Zayd ya bi ta da idanuwa.. su Anty Zainab kuwa suka cigaba da tsokanarta.

“Su Ammi sun tafi ne??” Umma ta tambaye shi

“eh Umma.. sun tafi. Yanzu ma daga airport muke, mun je mun raka su”

“Allah sarki.. ta kira ni a waya dazu da safe ai.. Allah ya sauke su lafiya”

Gaba daya suka amsa da ‘ameen’

“Anty Goben zaku wuce Kano kenan??” Zayd ya tambayi su Anty Khadeeja.

Anty Khadeeja ce tace “insha Allahu..” Ya kalli Anty Aminatu yace “Anty ke kuma Sokoto ko??”

Anty Aminatu tana murmushi tace “ashe baka manta ba Zayd..”

Sau daya suka zauna tare da Zayd a asibiti har suka yi hira da shi… sunyi hirar families dinsu da labarin iyayen su wadanda suka rasu shekaru da suka wuce and alot more… da alama he grabbed alot more than they thought a hirar tasu… He is a good listener for sure!

ta cigaba da fadin “…nima zan je Kanon inyi kwana biyu.. daga can ne zan wuce Sokoto”

Zayd yayi murmushi yace “Gobe zan turo driver sai ya kai ku airport.. ina ganin zai fi dacewa ku bi jirgi saboda tsaro. Again, zanyi arranging yadda za’a yi connecting ma Anty Amina flight zuwa Sokoto nan da kwana biyun Insha Allah”

Anty Zainab ce tace “ah haba dai.. wannan dawainiya haka??”

Like seriously?? dawainiya??? if only sun san yadda yake planning ya kyautata ma every last dangin Ameera…!!

“Babu komai Anty.. it’s the least I’d do for you”

Anan suka dinga godiya tare da sanya mishi albarka.

STORY CONTINUES BELOW

“Insha Allah zamu samu lokaci mu zo har gida mu gaishe ku..” Ya fada.

Anty Khadeeja tace “aikuwa zamu ji dadi sossai.. Allah ya bar zumunci yayi albarka”

Gaba daya suka ce ‘ameen’

A daidai lokacin ne Ameera ta fito riqe da tray ta qaraso wurin Zayd wanda yayi saurin sa hannu ya karba har yana fadin “Habibty ya kika ciko abubuwa haka?? hannun ki fa…”

Murmushi tayi tace “hannu na ya warke Yaya.. targade ne fa ba karaya ba”

Umma da su Anty Aminatu ne suka kalli juna suna murmushi.

Ko da ta tsugunna zata zuba mishi dakatar da ita yayi yace “I got this.. just sit”

Gani suka yi ya dauki Goran kunun aya yana analyzing dinshi yayinda yace “wannan meye??”

“kunun aya ne, hala baka san shi ba??” cewar Umma

“gaskiya ban san shi ba”1

“toh ga lemu nan ka sha..” Anty Zainab ta fada tare da nuna mishi kwalin Exotic din da yake kan tray din.

Zayd wanda tuni ya bude Goran kunun ayan ne yace “No Anty.. bari in sha wannan din”

Aikuwa suna kallon shi ya zuba a cup ya shanye.. ba tare da yayi magana ba ya qara zubawa a cup ya shanye..

Dago kai yayi ya kalli Umma yace “ina son wannan abun Umma.. ya ake yin shi??”

Gaba dayan su suka fashe da dariya yayinda suke mamakin sauqin kai irin na Zayd.. A yanzu haka da yake zaune cikin su zaka rantse ba wani hamshaqin mai kudi bane.

Umma ce tace “kar ka damu idan dai kana so zan dinga aiko maka da shi Zayd.. aikin kunun aya akwai wahala”

Murmushi yayi yace “aikuwa nagode sossai Umma..”

Wayar shi ce tayi ringing ya duba sannan yayi answering.

Bilal ne..

“Okay ina zuwa” Bayan ya kashe wayar ne ya kalli Ameera yace “Habibty ana nema na a ofis.. bari in je, idan na dawo sai mu tafi gida.. is it okay???”

Muryarta qasa-qasa tace “it’s okay Yaya..”

Miqewa yayi ya kalli Su Umma yace “sai na dawo”

“toh sai ka dawo Zayd… Allah ya tsare”

Anty Zainab ce ta kalli Ameera wadda take zaune tace “bazaki raka shi bane Ameera??”

Ameera ta miqe kanta a duqe ta bi bayan shi suka fita.. Da alama dai dama tayi niyyan raka shi din amma kunya ta hana ta.

☆☆☆☆☆☆

Layla wadda take zaune a kan gadon tayi tagumi tana ta sauraron hirar su yayinda hawaye ke ta bin fuskarta..

da yanzu ita ce a matsayin Ameera.

Zuciyarta ce take ta zafi yayinda kanta yake tsananin ciwo.. gashi babu kowa to comfort her.. Mama ta fita, ta je gidan wata qawarta.

Jin Zayd da Ameera sun fita ne tayi saurin miqewa ta nufi window tana leqen su.

Hango shi tayi jingine da mota yayinda Ameera take fuskantar shi..

Gani tayi ya sa hannu ya shafa fuskarta yana yi mata magana ita kuma tana murmushi.. daga nan kuma sai ya juya ya shiga dalleliyar motar shi.. motar da bata taba ganin irinta ba.1

Ameera wadda take tsaye ce ta daga mishi hannu alamar bye-bye yayinda ya sauke glass din motar yayi mata wata magana.. fashewa tayi da dariya sannan ta juya da sauri ta shige gida..

Gani nayi Layla tayi saurin sakin labulai ta ruga a guje ta haye kan gadonta ta fashe da sabon kuka..2

Tabbas tayi asara a rayuwarta, A yanzu kam the only thing keeping her strong shine malamin Hajiya Suwaiba.. dole ne malamin nan ya raba Ameera da Zayd, idan kuwa ba haka ba lallai zata shiga babban matsala..!

About AIS

Check Also

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH

ZABI NA CHAPTER 13 BY FADEELARH Www.bankinhausanovels.com.ng  Washegari!!+ ZAYD AHMAD FADOUL’S RESIDENCE UNGUWAN RIMI GRA …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *