YAR MAHAUKACIYA CHAPTER B KARSHE BY SAJIDA

 YAR MAHAUKACIYA CHAPTER B KARSHE BY SAJIDA 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Sun jima zaune sunyi shiru kowa da abinda yake sakawa a zuciyarsa jiran vilowar Elhaj Muhammad suke ,

Bayan kamar minti arba’in sai gashi ya shigo da damin goro a hanunsa yayi salama

Suka amsa masa a tare suna kalonsa

Waje ya samu ya zauna ya fuskance su ya ce ” cikin ikon Allah an daura aure a gaban shedu sanan kuma ga goro na samu Kiran sarki na shaida masa ya ce eh aure taya shi ake Allah ya sanya alkhairi,

Hajiya Hawau ta ce” kana nufin *Rahma* ta zama matar *Dan Aljannah*?

Elhaj Muhammad ya ce ” Kwarai kuwa ni na wakilce ta liman ishak ya wakilci Mubasshir Allah ya sa alkhairi aka hada

Hajiya Hawau ta ce ” Alhamdulilah Allah abin godiya tabas alkhairi aka hada Allah ubangiji ya fi karfin su Allah ya kare duk wani mugun abin da za’a jefa dan a bata wanan taraya sanan Allah ya hada Hankalinsu

Hajiya Fadimatu ta amsa da Amin ya Allah

Haka suka gama suka tatara suka nufi gidan Hajiya fadimatu

Suna shiga suka tarar da Yar Mahaukaciya konce saman doguwar kujera tana bacinta  , cikin nitsuwa Hajiya Hawau ta karasa ta tataro gashin kanta ta daidaita mata shi sanan ta dora mata dan kwalinta da ya fadi a hankali ta ce ” ina ji a jikina ke Yar Halak ce, sanan ke ba mutuniyar banza bace , hakan yasa na gommaci ki auri bawan Allahn nan tun kafin su saka rayuwarsa a garari, jinina ne Idriss sai dai kash bashida mahaifiyar kirki , sam bai yi dace da uwa ba , haka yar uwarsa tayo halayar mahaifiyarta Wace ta raba soyayar da da uwa,

Ni na san Ilyasu baya cikin hankalinsa shi yasa nake yi masa uzuri Allah ya yaye masa abinda ke damun sa ya haskaka rayuwarsa, kema Allah ya baki hakuri da juriya kan rayuwar da zaki tsinci kanki nan gaba

Hajiya Fadimatu dake zaune tana kalon Hajiya Hawau tayi Murmushi ta ce ” Baba tabas ance zamani ya canza kana iya haihuwar yaro ka kasa tankwasa shi , na sani ne bi’izinillah gata muka yiwa Mubasshir l’a zai gode mana kan hakan , aman fa ina neman wata alfarma

Hajiya Hawau ta kaleta ta ce” Alfarmarki KO maicece fada min ita insha Allah zanyi kokarin ganin na cika miki

Hajiya Fadimatu ta ce ” bana son su san an aura musu juna nafi son na kara wanke yata ta goge da ilimi ta yanda zata kwaci kanta koda za’a cutar da ita, ina son yaronki da kansa ya nuna yana so dan kar yaga an bashi kyauta yayi kokarin banbanta darajarta da ta Sahla du da ita bazawara ce aman itama mutun ce so plz hajiya ki taya ni mu boye musu

Hajiya Hawau tayi shiru ta ce ” to aman hajiya kar mu taka dokar musulunci fa , kar aje ta kula wasu samarin bayan ita ga mijinta

Hajiya Fadimatu ta ce  ” tabas wanan shi na fara tinawa aman kuma zan saka ido sosai a al’amuran ta , l’a komai zai tafi daidai

Habiya Hawau ta ce ” Toh Allah ya kama mana

Sun kusan minti talatin sanan Yar Mahaukaciya dake sheka bacinta ta farka da adu’a a bakinta tana rike dan kwalinta dake kokarin koncewa ,

Ido ta zaro ganin Hajiya Hawau zaune , ta mitsika idanuwanta ai bata san lokacin da ta tashi da Sauri ta fada jikin Hajiya Hawau ta saki kuka ta rukunkumeta

Itama kukan take na yaushe gamo sai da Hajiya Fadimatu ta ce ” ya isa hakanan sanan suka sasauta

Hajiya Hawau ta talafo fuskar Yar Mahaukaciya ta ce ” kiyi hakuri yata , kiyi hakuri

Yar Mahaukaciya ta girgiza kai ta ce ” Haba hajiyata ki dena bani hakuri kan laifin da ba naki ba sanan wly ni na yafe har cikin zuciyata ,

Hajiya Hawau tayi murmushi ta ce ” Allah yayi miki albarka ,

Ta amsa da amin sanan ta juya wajen Hajiya Fadimatu ta ce ” Mamana tun yaushe kika dawo? KO tare kuka zo?

Hajiya Fadimatu cikin murmushi ta ce ” Mun dan jima da shigowa kina dan hutawa shi yasa naki na tashe ki dan na san halinki sarkin aiki ta karasa tana murmushi

Haka sukayi ta labarin su har yama tayi direban Hajiya Fadimatu ya mayar Da Hajiya Hawau gida cike da kewarsu Yar Mahaukaciya

Gidan Mubasshir ,

Zaune suke saman diner suna cin abinci Sahla ta sha ado sai zuba kamshi take tana iyayi shi kuwa gangar jikinsa kawai ke tare da ita aman zuciyarsa ta tafi aikinta tinani wata can daban

Sahla ta ce ” konci tashi yau har munyi kwana biyar da aure , husby yaushe zaka kaini na ga momyna?

Mubasshir ya kaleta ya ce ” au har kinyi kewar gidan ne?

Sahla tayi fari da idanuwanta ta ce ” eh to ba sosai ba aman momyna nafi kewa

Mubasshir ya ce ” Sahla ba fa mu kadai bane a cikin gidan nan

Sahla ta tsayar da cin abincinta ta ce” eh man husby akoy masu aiki KO?

Mubasshir ya ce ” no banda masu aikin akoy iyayena a cikin gidan nan

Sahla ta ce wasu iyayen naka bayan Hajiya

Mubasshir ya kaleta a ransa ya ce *Hajiya* au bazata ce mata mama ba? A fili ya ce ” eh banda maman Mubasshir inada iyaye da nake kyautatawa suna saka min albarka dan gamawa da duniya lafiya kuma ina son matata ta koyi halayana na kirki

Sahla ta dan yatsina fuska a ranta ta ce lale ma har wasu bare Kenan ka yayubo min a gida tabas zanyi août da koma su waye su , aman a fili ta ce ” oh ohk toh kuma a wajen ina suke?

Yayi murmushi ganin yanda bata iya boye damuwarta ya ce ” ai ki gama cin abincin sai mu tafi ki Gansu KO?

Sahla ta ce ” ba damuwa

To fa Sahla shin kin sans abinda mijinki ke tanadar miki?  ……….’

[

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                    42

Bayan ta gama cin abincinta yana zaune saman baban kujerar tsakar falon yana kalon TV ta fito da wandon nata da rigar ta ce ” mu tafi husby

Mubasshir ya dago kansa yana kalonta shi bai san ana konbo da rama ba sai a kan Sahla ya girgiza kansa ya mike ya dauko mata abaya baka da mayafinta ta karba ta saka tana yatsina suka kama hanya , ita dai burinta ta ga su waye a cikin gidanta

Tafiya ta kai ta minti goma da suka yi a tsakar gidan sanan suka ISO wani wajen mai shegen kyau , abinda ya bata mamaki yanayin ginin wajen ya fi nata kyau , haka dai ta zuba ido tana biye da shi har ya tura ya shiga da salama , ta biyo bayansa itama tana wara idanuwanta

Wata irin zabura tayi abinda idanuwanta suka gane mata , wasu tsafi ne yangom a zaune a saman cafet suna cin abinci wata tsanwar miya mai warin dadawa ta doki hancinta idanuwanta suka sauka a saman miyar gogo wace sam ba hakora a bakinta abincin ma sai ta dame shi sanan take iya hadiyewa ga bakin nata gaba daya ta jamula shi da miyar wata irin tashin zuciyar ba gyaira ba dalili ta tasowa Sahla da sauri ta saka hanunta ta toshe bakinta da hancinta ta zaro ido ganin Mubasshir ya saka hanu yana sakawa wata tsohuwar abinci a bakinta sanan ya juyo ya nuno mata sahla , Abinka da tsafi aikuwa ta Mike da kyar tana fadin Yau ga matar Yaron mu har cikin gidan mu

Sahla ta shiga baya baya dan ta lura dukan su fama suke su taba mata jiki , bata Ankara ba taji wata ta taba ta tana juyowa ta ga Gogo ce ai bata san lokacin da ta saki ihu ba ta juya da gudu ta nufi bangarenta tana rusa kuka wiwi

Mubasshir ya zaro ido ya san a rina aman bai taba tinanin abin zai kai haka ba , wai a nan ta tardo su an kimtsa su ne , da irin kafin ya tafi aiki da yake biyowan nan ne da ta suma ma dan a lokacin suka farka wasu har kashi a nan suke yin kayansu dan kuwa tsafi ne sosai ya tara yake ciyarwa da shayarwa bisa yardar hukuma da saka hanunta harma masu gatan dan kuwa irin kulawar da yake basu tafi wace zasu samu a gidan nasu

Sai da ya zazaunar da su yayi Kiran masu kula da su sanan ya juya ya nufi bangarensa

Yana shiga kakarin amai ya fara ji ya girgiza kansa ya nufi dakinsa yayi konciyarsa ya dauki waya yayi Kiran mahaifiyarsa

Daidai lokacin suna zaune Hajiya Fadimatu na gyarawa Yar Mahaukaciya gashinta dan gobe zata fara zuwa makaranta wayar dakin tayi ringin

Yar Magaukaciya ta mike ta dauko dan wayar jikinta da doguwar waya Wace za’a iya janta

Hajiya Fadimatu ta ce” daga maga mu ji kowaye?

Yar Lahaukaciya ta daga ta yi salama

Daga dayan bangaren Mubasshir ya ja wani dogon nunfashi ya kasa amsa salamar muryar nan duk da sanin mahinmancin salama haka kawai ya tsinci kansa da wani irin yaunin baki

Yar Mahaukaciya ta ce ” hello , heloooooooo?

Ta mikawa Hajiya Fadimatu tana fadin Mama ai ba’a magana KO an datse Kiran ne ban sani ba ?

Hajiya Fadimatu ta karbi wayar daga hanun Yar Mahaukaciya ta kara a kunanta tayi salama

Daga dayan bangaren Mubasshir ya amsa salamar a kasalance sanan ya ce ” Maman Mubsshir ina yini

Hajiya Fadimatu ta saki murmushi dan ta gane ya kasa amsa salamar ne jin muryar Rahma , ta amsa gaisuwar sa sanan ta ce ” lafiya nake jin muryar taka kamar maran lafiya?

Mubasshir ya shiga kame kame ya ce” am daman aa baci ne nake ji shine nayi kira nayi miki sai da safe

Hajiya Fadimatu ta ce ” To Allah ya tashe mu lafiya , am daman insha Allah tomorrow yarinyata zata fara zuwa makarantar islamiyar fa

Mubasshir ya danyi Jim sanan ya ce ” Maman mubasshir plz a kula da tsaronta direba ya ringa kaita yana jira har ta fito ya daukota ya dawo da ita saboda kinga ba’a so a san inda take , sanan malaman nasu mata ne kadai?

Hajiya Fadimatu ta ce ” da mata da maza ne

Yayi Jim sanan ya ce ” To maman Mubasshir plz ta kula

Hajiya Fadimatu ta ce ” kai ni fa na haifeka zakana kokarin koyar da ni yanda zan kula da yata? Aman ai batayi baci ba KO na baka ita kayi mata hudubar?

Da Sauri ya ce ” no maman Mubasshir kiyi hakuri ba haka nake nufi ba , love u , good night

Hajiya Fadimatu tayi Murmushi a ranta ta ce zama kayi nufin hakanan din aman a fili ta ce ” ohk by a gaishe min da Sahlan ta datse Kiran

Mikewa yayi zaune daga koncen da yayi ya shiga kikifta idanuwa ya ce ” Maman Mubasshir plz da hakuri kika yi KO wani irin malami take da bukata sai na dauko ya ringa koyar da ita saboda kar aje rana ta baci ldriss ya hadu da ita alura ta tono garma ( to fa ka tabatar dan haka kake gudun fitarta? )

Haka yayi ta tinane tinane hardai ya yanke shawarar da shi kadai ya san kayansa ya gyara konciyarsa yana adu’ar baci ya lumshe ido yana fatan zakara ya bashi sa’a ?

Karfe bakwai ta gama abinda ta saba sanan ta shiga wanka tana fitowa ta zauna ta shafa mai ta daga kayan makarantar tata ta islamiya doguwar riga ce har kasa sanan hijabi shima har kasa da nikaf na matan aure da budurwar dake bukatar saka shi

Ta saka rigar Kenan tana kokarin konce hijabin dan an daure shi ne da wata yar igiya wayar dakinta tayi kara ta matsa a hankali ta daga tare da salama

Hajiya fadimatu ta ce ” yar Fadimatu sauko ina jiranki yanzu

Yar Mahaukaciya ta ce” to mama

Ta ajiye wayar ta sauko da hijabin dan Hajiya Fadimatu ta konce mata daurin tana zuwa ta tarar da Hajiya Fadimatun zaune tana zuba abinci cikin faranti , ta duka tana gaisheta

Hajiya Fadimatu ta amsa tana murmushi daidai nan aka turo kofar falon aka shigo

AA ne cikin wata dakakiyar shada fara kar sai zuba kamshi yake ya shigo da salamarsa

Hajiya Fadimatu ta zaro ido ta ce ” lafiya da safiyarnan? Mai ya fito da kai yau? Ka manta al’adar mu ne?

Mubasshir ya karaso yana murmushi ya kama hanayen mahaifiyarsa ya ce” Maman mubasshir i really miss u , kinga abokina ya gayaceni yau shine na biyo na ganki kafin na fice

Hajiya Fadimatu ta ce ” Kenan ka karya dokar?

Mubsshir ya ce ” Maman Mubasshir Al’ada ba adini ba , kinfi kowa sani , so please ki bar maganar nan kiyi murnar ganina

Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta ce” to sanunka da zuwa

Yar Mahaukaciya dake tsugune ta ce” barka da safiya yaya

Mubasshir ya juyo ya zuba mata ido ba wata kwaliya tayi ba aman har wani fizga yanayinta yake, ya ce ” Barkan ki

Yar Mahaukaciya ta Mike ta mikawa Hajiya Fadimatu hijabin na hanunta ta ce ” Mama na kasa kunce wanan daurin gashi lokaci ya kusan yi

Mubasshir bai san ta ina maganar ta fito ba saï ji yayi bakinsa na fadin” halan wanan rigar da ita zaki tafi makarantar ?

Hajiya Fadimatu da Yar Mahaukaciya suka kale shi a tare , da tambaya a fuskar su

Sai a lokacin ya gane cewar yana fa son ya kwafsa kansa hakan yasa cikin basarwa ya dana wayarsa yana kalon kofa ya ce” am naga kamar tayi kadan ne , am manta ,

Ya mike yana fadin Maman Mubasshir tayi sauri dan hanyata ne na sauke ta sai na fice yayi waje yana karasa zancen

To fa Malan yayadai???????

[

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                    43

Ya kai minti ashirin a zaune cikin mota yana jira , abinda bai taba yi ba a rayuwarsa wato zaman jiran mutun ya fito koma waye dan koda mahaifiyarsa zai fita ta san halinsa bata barin sa zaman jira dan kuwa yanzu zai fara shiga yana fita yana takurata da Maman Mubasshir ki fito plz, aman wai yau shine zaune yana jiran fitowar wanan yarinyar da ba komansa bace , haka kawai ya ja tsaki a fili ya ce ” dan na kula da amanar da na daukowa kaina ne da ba dan hakan ba da ba Wanda zai fito da ni a yau daga gidana ,

Yana tsaka da mita ya hango fitowarta ya tsura mata ido nan da nan ya ji wani sanyin dadi na ratsa shi ganin hijabinta har kasa sai dai fuskarta a bude kuma da alama da nikaf a hanunta ,

Horn ya dana hakan ya sa ta nufi motar dan kuwa ita a tinaninta ai yayi tafiyarsa tana isa ta Buda baya ta shiga tana furta barka da warhaka Musa direba

Maganar ta tsaya mata a makogwaro sanadiyar hada idanuwa da suka yi ita da Dan Aljannah

Ido ta zaro tayi Saurin dora hanunta a saman bakinta tana kikifta ido ta ce ” yaya yaya kayi hakuri nayi tinanin Musa ne yake yi min horn i’m sorry  ta karasa tana kokarin bude motar ta fita sai karkarwa hanunta yake sanan motar taki buduwa

Sai da ya gama kalonta a yanayin tsoro son ransa sanan cikin dakakiyar mirya ya ce ” ba’a tsayar da ni jira , wanan ya zama na farko kuma na karshe cos hakan na bata min rai ba kadan ba , ki dawo gaba dan ni ba Musa direba bane

Wani iri yake saukan mata a jiki yanayin maganarsa gaba daya tamkar tayi tsere haka take jin zuciyarta nayi mata lugude da kyar ta samu ta bude motar ta fito tana ta adu’a ta bude gidan gaba ta shiga kanta a kasa sanan ta kama yar karamar yatsarta tana ta murzawa da karfi tamkar ita tayi mata wani laifin

Tafiyar kurame ne suke domin ba Wanda ke cewa dan uwansa ufan sanan KO saukar numfashin su ba mai ji sai yatsarta da ta koma jajawur dan azabar murzata da take tunda suka fito tsawon tafiyar minti arba’in Kenan dalilin gosulo , suna isowa makarantar ya shiga direct har cikin kofar baban office din malamin mai suna ustaz Mu’azu ya faka

Cikin nutsuwa ta dago kanta sai taji ya ce ” ina zuwa

Fita yayi ya shiga office din bai wani jima ba sai gashi ya fito da wata malama a bayansa ta karaso wajen Yar Mahaukaciya ta bude motar ta fito

Tana fitowa ta tsuguna ta gaisar da ita , ita kuwa sai washe hakora take ta kamata ta mike sanan ta ce ” muje madame

Sai da ta sada Yar Mahaukaciya da ajinta sanan ta dawo wajen Mubasshir AA

Tana zuwa ta ce ” an gwada mata kuma insha Allah za’a kiyaye , aman fa dalilin bazata zaman jiran malaman mu maza ba zatana sauka a lokaci daban daban dan haka dole mu dauki nimber wayar ka idan ta tashi da wuri muyi kira kazo ko ka turo a mayar da ita gida

Mubasshir ya ce” wanan duka ba damuwa idan dai har za’a kiyaye wanan , sanan komai akeda bukata ni za’a kira ba ita ba so ya mika mata takarda ya ce ganumberna personnel koda yaushe kika kira zan daga

Malamar mai suna Husnah ta karba tana godiya ya juya ya shige motarsa yana hamdallah a cikin zuciyarsa

Tafiya yake wayarsa ta fara ringin sai da tayi har sau uku sanan ya mika hanu ya dauko dan ganin KO waye ke kiransa da safe haka

Number Hajiya Marhaba ya gani hakan ya sa ya nemi waje yayi parking ya daga tare da salama

Hajiya Marhaba dake haki ko tsayawa amsa salamarsa bata yi ba ta ce ” Mubasshir ina gidanka ina jiranka yanzu

Mubasshir ya ce ” am Hajiya Gidana kuma? Ni ai ina gidan Maman Mubasshir fa

Hajiya Marhaba ta ce ” ohk mu hadu a can din

Kafin ya bata amsa har ta datse kiran a hankali ya furta ya Salam sanan ya tada motarsa ya juya kanta ya nufi gidan mahaifiyarsa

?????????

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      45

Kamar yanda suka zo haka suka koma tafiyar kurame suna isowa ta kama kofar zata bude ta fita

Mubasshir da ya kasa hana kansa magana ya ce ji mana

Yar Mahaukaciya ta jiyo tana kalon kasa dan koda wasa bata iya kalonsa cikin ido

Mubasshir ya mika hanunsa ya karbi nikaf din dake hanunta ya daga yaga eh lale nikaf din ne

Ya ce ” mai yasa ke bakya saka shi ne?

Yar Mahaukaciya ta dago ta kale shi , idan bata manta ba wataran ta taba riskar hirar su da Hajiya Hawau yana fada mata cewar ya tsani yan matan nan masu saka nikaf din munafurci dan abinda suke aikatawa gonda gagarumar karuwa da su yawancinsu aman yau kuma ya tambayeta mai yasa ita bata saka ba?

Tambayarki nake , Muryar Mubasshir ta dawo da ita daga duniyar da ta fada ta ce ” Am daman ance na matan aure ne , yan mata sai idan mutun yana da ra’ayi ne zai saka idan kuwa baka ra’ayi to karka saka

Mubasshir yana sauraronta sam bai so maganar ta tsaya daga nan ba ya lumshe ido ya ce ” aman ai zawarawa ma na iya sakawa KO?

Yar Mahaukaciya ta dago idonta suka yi ido hudu ta kawar da kanta ta ce ” eh

Ya Mika mata ya ce ” toh ki ringa rakawa duk inda zaki je tunda zawarawa ma na iya sakawa kinga kina layi KO?

Yar Mahaukaciya ta karba ta daura a fuskarta idanuwanta kadai ake gani ba’a ganin sauran fuskarta , ta dago ta sauke idanuwanta cikin nasa ,

Wani irin yar yaji a jikinsa harma yayi nadamar Sakata daura nikaf din , dan da ta daura kawai sai kyan idanuwanta suka fito ba kadan ba har wani walkiya suke balatana na tsakiyar nan mai kama da na mage , Saurin kawar da kansa yayi yana fadin kina iya tafiya

Yar Mahaukaciya ta kama ta bude kafin ta fita a hankali ta ce ” Allah ya saka da mafificin alkhairi sanan ta fice tana tafiyarta da ta saba

Ba shi ya bar wajen ba sai da yaga eh lale ta shiga falon sanan ya ja yayi gaba yana mai jin haushin kansa irin yanda yake mantawa da ayukansa masu mahinmanci wajen tinanin gyara rayiwar yarinyar nan , dan ba dan ya daukarwa kansa alkawarin kulawa da ita da bazai tsaya batawa kansa lokaci a kanta ba , aman insha Allah zai nema mata miji Wanda ya san zai kula da ita domin Allah a daura musu aure KO yayi abinda zai fishe shi ( toh fa )

Tana shiga Hajiya Fadimatu na amsa waya ta zauna sai da ta gama ta gaishe ta

Cikin murmushi take amsawa ta ce” ah Yar Fadimatu ya akayi kika saka nikaf din?

Yar Mahaukaciya tana cirewa ta ce” Mama ai yaya ne yace na saka kar na kuma fita babu shi

Hajiya Fadimatu a ranta ta ce toh kaji shi da ya tsani saka nikaf yau kuma shine da kansa yake cewa a saka ? Lale yau kam ta gama yarda da abinda take zargi aman zata gwada shi tayi murmushi ta ce ” toh ki ke kiyi wanka sai ki sauko mu ci abinci

Yar Mahaukaciya ta amsa tana mikewa ta nufi dakinta

Konci tashi har Hutun su Yar Mahaukaciya ya kare sun koma makaranta inda wanan karin da wani irin gata take tafiya wanda wataran direba ya kaita wataran Maman Mubasshir kanta kawai sai ta shirya wai rakiya zata yi mata har cikin makarantar ba wanda bai Santa ba sanan yanzu idan bata son zuwa ta ci abinci har inda take ake kawo mata cikin mutuntawa

Yau ta tashi a lati dan kuwa mura ta hanata baci sai daidai asuba ta samu ta rintsa jikinta zafi rau da zazabi

Hajiya Fadimatu ta fito karfe bakwai da rabi ta zauna tana jiran saukowar Yar Mahaukaciya abin mamaki har karfe takwas tayi bata sauko ba , a fili ta ce” lafiyar Yata kuwa? KO ta tafi ne? No bazata tafi bata sanar da ni ba dan ba dabi’arta bace

Hakan yasa ta mike ta nufi dakin Yar Mahaukaciya tana fatan Allah yasa lafiyarta lau

Tana shiga ta hangota konce lulube cikin bargo tana karkarwa , Da sauri ta karasa ta dan yaye mata bargon tana fadin Yar Fadimatu lafiya?

Yar Mahaukaciya dake barin sanyi har hakoranta haduwa suke da kyar ta iya furta mama can cikin kasan makoshinta sanan ta maida idanuwanta ta rufe

Ai da gudu Hajiya Fadimatu ta juya tana rarumar wayarta ta danawa doctern su kira ta fada masa yarinyarta ba lafiya kuma sosai ne jikinta yayi zafi sosai

Doctern ya ce ” To Hajiya Zan karaso nan da Awa biyu dan makocina ya rasu muna wajen jana’iza

Hajiya Fadimatu ta ce ” Eyah Allah ya jikansa ta datse Kiran ta shiga neman lambar Mubasshir dan kuwa bazata iya zubawa yarta ido a haka ba har tsawon wani lokacin

Lambarsa ta wajen aiki take kira dan tasan a wanan lokacin yana office aman secreteria dinsa ta dauka tace bai karaso ba

Tana kokarin Kiran numbersa ta gida duk ta rude taji takun hayowa matatakalar dakin nasu

Da Sauri ta leka ta ga Mubasshir ne ya shigo ai bata san lokacin da tace ” Yarona maza karaso Yarinyata ba lafiya plz

Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa da ita ya kara Sauri ya haye saman ya nufi dakinsa na da Wanda Yar Mahaukaciya ta zaune shi ya tura ya shiga ya karasa saman gadon da Hajiya Fadimatu ta yaye mata rufar tana kokarin daure mata gashin kanta ta kamata ta mikar da ita daga koncen da take

Saurin kawar da kansa yayi dan kuwa irin doguwar rigar barcin nan ce mai sulbin gaske duk da tsayinta aman lafewa take a jikin mutun , idanuwansa ana mike ta suka sauka saman mamarta dake tsaye tsai tamkar su tsole ido hakan ya mugun kayar masa da gaba da dana sanin kalonta

Hajiya Fafimatu ta ce” wai zaka kama min ita ne na saka mata hijab mu kaita asibiti KO kalon kasa zaka tsaya yi yarinya na galabaita?

Mubasshir cikin inda indar da bai san yana da ita ba ya ce” mmmmamar Mubasshir bara na dauko docteur Halima a haka bazata iya jiran harkar asibiti bâ

Kafin ta bashi amsa ya fita ya figi mota ya nufi office din Docter Halima tana tsaka da aikinta ya daukota ya kawota

Tana zuwa ta shiga gwaje gwaje nan ta gano mura ce ke damun Yar Mahaukaciya ta rubuta magunguna suka Fito da AA dan ya Mayar da Ita wajen aikinta

Bayan ya ajiyeta ya nugi pharmacie dan siyan magungunan da aka rubuta

Bayan ya siya ya kaiwa Hajiya Fadimatu ya dawo falo ya zauna ya kuna TV aman ina hoton dazu ya fado masa a idanuwansa a fili ya furta ” A cikin nan yaro ya konta kuwa? Dan cikin gonda nashi na namiji dake shafe da nata , a shafe yake tamkar bata cin abinci KO haka halitarta take???

I dn kw

[

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      46

Shi kadai yana zaune tamkar sabon kamu yana magana da kansa daidai Hajiya Fadimatu ta sauko daidai ya ce” To kai Mubasshir mai ya shafeka idan ma ba nata bane?

Hajiya Fadimatu ta ce” Lafiya kake magana kai kadai?

Mubasshir ya mike yana dan murmushi ya ce” No maman Mubasshir ba komai ina dai tinanin wani abin ne,

Hajiya Fadimatu ta ce” toh Allah shi kyauta

Mubasshir ya ce” Maman Mubasshir ya jikin Yar taki?

Hajiya Fadimatu ta ce” ah yanzu da sauki har baci ya dauke ta 

Ajiyar zuciya ya sauke  sanan ya ce Allah ya kara lafiya

Hajiya Fadimatu ta amsa da amin

Ba ita ta farka ba sai gabanin la’asar domin maganin nata na mura mai saka barci ne , tana farkawa cikin ikon Allah da karfin jikinta ta farka ta shiga bayi ta wanke jikinta ta wanke bakinta ta dauro alwalah ta fito ta dauko Zani da Riga na atampa ta saka ta kabarta sallah

Tana gama salolinta ta mike ta cire hijabin ta koma dan kuwa har a lokacin barcin bai saketa ba ta ja zif dinta tayi konciyarta dan bata son saka rigar da ta dan kama ta kuma ta konta da ita  , baci yayi awon gaba da ita

Cikin nutsuwa ya turo kofar ya shigo da yar salamarsa shirun da yaji ne ya saka shi idasa shiga dan ya san kawai tana barci

Hangota yayi ta hade kafafuwanta tana bacinta rigingine aman gashin kanta gaba daya ya rufe mata fuska ,

Gaba daya ya tataro courag dinsa ya nufi gadon yana adu’ar Allah ya sa bacin take dan ya ga ta canza kayanta ne ma ya saka shi nufar inda take ,   

Yana zuwa ya dan dakata daga nesa da ita yana kalonta , jikinta daidai da ita , fuskarta ta yara ce , yanayin jikinta bata sha fama ba , to aman wacece ita? Yaron da ya rasu wanene shi? Mai dinta ne ? A ina ta samo shi? KO dai sato shi tayi? Idan ba sato shi tayi ba to dan waye ? Da ita ta haife shi da jikinta ya nuna duk da akoy matan da idan sun haihu cikinsu na komawa ya lafe aman wanan ai a shafe ne yake daga ganinsa

A fili Ya furta no bazan iya ba , bazan ci gaba da zuba miki ido a haka ba aje ki cutar da ni, a yanzu haka na gaji da irin cutar da ni din da kike dan haka hakurina yazo karshe yau bazan kuma hakura da hakan ba

Gadan gadan ya nufeta yana tatare kafar wandonsa

Hanayensa biyu ya saka ya tayar da ita daga konce

Cikin tsoro ta buda idanuwanta ta sauke su cikin nasa wanda yayi iya yinsa dan ya hada idanuwan da ita

Bakinta ta buda cikin karkarwar baki ta ce ” Yaya mai akayi? Lafiya?

Mubasshir ya ce ” who are u?

Yar Mahaukaciya ta zuba masa ido jikinta ya fara karkarwa gabanta na dukan uku uku tsoro ya darsu a zuciyarta

Cikin karaji Mubasshir ya ce ” da ke fa nake bazaki bani amsa ba ?

Yar Mahaukaciya tayi Saurin fadin wayo Mahaukaciyata  ta fashe da kuka ta hade kanta da gwuiwarta , sosai take kuka har jijiyoyin wuyanta sunyi rako rako

Wani irin tausayinta ya darsu a zuciyar Mubasshir a hankali ya sauke hanunsa daga kafadunta cikin dakakiyar muryarsa ya ce ” wacece Mahaukaciya?

Yar Mahaukaciya ta dago kanta ta sako daga Saman bed din cikin sarkakiyar murya ta ce” Mahaukaciya itace Mahaifiyata , bansan kowa ba ban san komai ba , Mahaukaciya da ita na fara bude idanuwana , ita na fara gani , mu ci abincin mu mai tsami , mu sha ruwa a bola , Mahaukaciya tana cikin Hauka aman tana nemo abinda zamu ci da cikin mu , Mahaukaciya koda an taba ta tayi min duka tana dawowa ta rungume ni muyi baci,

Ta silale kasa cikin kukan mai tsuma zuciya ta dago ta hade idanuwanta da Na Mubasshir Wanda ya zamto tamkar mutun mtuni ta kwashe gaba daya labarin rayuwarta ta fadawa Mubasshir dake zaune yana kalonta

Bayan ta gama bashi labarin Hajiya Fadimatu dake rabe tana sauraron su ta kara kasa kunenta

Mubasshir ya kare mata kalo ya ce ” Karya kike Rahma, Karya ne , shin taya zan yarda da ke? rahma kina nufin neman mahaifiyarki ne ya saka kika baro bolarku? Taya ma zan yarda da ke duk irin yanda Hajiya ta kula da ke ta daukeki tamkar yar cikinta aman kika watsa mata kasa a ido kika yi mata karya? Ni wanene da bazaki yi mini ba ? Ki fada min gaskiya Rahma wacece ke ?

Yar Mahaukaciya ta lumshe idanuwanta , tabas ta san akoy ranar kin dilaci aman ta so sai ta hadu da mahaifiyarta sanan hakan ta faru , mikewa tayi a hankali ta nufi saman drewernta ta dauko alkur’aninta ta zo ta zauna gaban Mubasshir ta lumshe idanuwanta ta dora hanunta a saman kur’anin ta ce ” Na Rantse da ,,,,,……  Kafin ta karasa fadin abinda yake bakinta Mubasshir ya Mike ya karbe kur’anin cikin zaro ido ya ce ” *Baki da hankali ne?*

Yar Mahaukaciya ta Mike itama cikin karajin ta ce ” *Ka  barni na rantse Mubasshir , ka barni na rantse maka da alkur’ani mai girma duk da irin yanda mutun da gaskiyarsa yayi rantsuwa da shi yake samunsa ka san duk jahilcina na san idan bakada gaskiya ka rantse da shi ka halaka*

Ta kuma fuskantar sa ido cikin ido ta ce ” *Tabas ni Mahaukaciya ce dan kuwa Mahaukaciya ta haife ni* sanan na boyewa Hajiya ne dan ina mace , macen ma mai rauni marar gata , ina gudun idan hajiya ta koreni ina zan dosa, ina gudun wani abin ya kuma tunkarata, ina gudun fadawa wata halakar , aman a kulun cikin bakin cikin biyewa Mama ta gidan nan nake , domin a kulun na kali darajarta da kimarta sai nayi kuka na karyar da nake yi mata , aman a yanzu alhamdulilah tunda Allah yayi kafin na bar gidan nan kun san KO wacece ni , na gode da kulawarku gareni Allah ubangiji ya biya ku ranar gobe kiyama

To fah , shin Yar Mahaukaciya zata kara GABA ne ? Ya aurenta da Mubasshir zai kasance? Zata ga mahaifanta ne KO yaya?

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      47

*Happy Juma’at, Allah ya karbi ibadun mu, Ya kyautata karshen mu, ya sa Aljana ta zama makomar mu dan nabiyin Rahamati*

  Tana gama fadar haka ta juya cikin mutuwar jiki ta nufi akwatinta dake ajiye sai a lokacin ta tina zip din rigarta a kunce ta kama ta ja sama , ta buda akwatin ta zaro hijab dinta fari kar tana dagowa ta ga Hajiya Fadimatu ta harde hanayenta tana kalonta shima Mubasshir din ita yake kalo inda ta kasa fasara kalon kyama ne KO na ki ne yake jifanta da shi?

Hankalinta ya kai kololuwar tashi da ta ga harda Fadimatu a wajen Kenan ta ji abinda ya faru ? A fili ta furta ya salam

Hajiya Fadimatu ta matso tana kalonta fuskarta cike da tausayi idanuwanta jajir jikinta ba kwari a hankali ta furta” *Tafiyar ce?*

Yar Mahaukaciya ta kara sada kanta kasa tana ta zubar da hawaye

Hajiya Fadimatu ta kara matsowa ta dago Fuskar Yar Mahaukaciya ta ce ” Rahma, ki dubi girman Allah ki fada min a mai kika daukeni? Matsayina a wajen ki

Yar Mahaukaciya ta sada idanuwanta ta ce ” Ke uwa ce a wajena , Wace ta karbe ni ta kula da ni ina alfahari da ke sanan zanci gaba da yi miki adu’a duniya da kiyama

Hajiya Fadimatu ta jayota ta rungume ta tsam a jikinta , haka yar Mahaukaciya ma ta rungume ta tana kuka mai tsuma zuciya tana ji tamkar ta rungume Mahaukaciyarta ne a haka

Sun kusan minti uku a haka sanan ta saketa ta juyo wajen Mubasshir dake tsaye da kur’anin a hanun sa yayi Sakai yana kalon su , ta ce ” Yarona , na yarda da abinda Rahma ta fada, tabas bata taba haihuwa ba , sanan kwarai ta taba yin rayuwar bola, kuma eh lale yawan tinanin da take yi harda kuka wani likacin na tinanin mahaifiyarta ne , haka zalika yarinyar nan bata sato dan kowa ba kaninta ne dan kuwa dan mi ake satar yayan mutane? Ai dan tsafi ne da kudi a gidan nan da gangan na sha zubar da kudi dan na gwadata ta wanan fanin aman KO gyara take sai dai ta dage ta share ta mayar koma ta gewaye, sanan kafi kowa sanin a yanzu tanada ilimin yin aiki da card dinka dake wajenta ta kwashi abinda taga dama tayi tafiyarta aman bata taba kawowa a tinaninta ba , a vidion nan nasha jin ta furta Mahaukaciya aman ban san inda ta nufa ba , na yarda da ita dan baka san rayuwar titi bace , duk tsafi , duk sanyi, duk ruwa a wajen nan a nan suke, ba KO tabarma bale ayi tinanin katifa, Allah kadai ya san irin warin da suke ciki sai su kansu, dan haka ni Mahaifiyarka na karbi Rahma da hanu bibiyu zan Rayu da ita a matsayin yata koda an samu mahaifiyarta sanan ni Fadimatu ni zan aurar da ita da yardar Allah a inda zata huta dan kuwa hutu shi yafi dacewa da yata..

Mubasshir dake tsaye shi ya rasa ma mai yake ji a cikin zuciyarsa, ya rasa ta inda zai fara fuskantar wanan damuwar taya zaiyi da rayuwarsa ne ?(?),    cikin sanyin jiki ya juya ba tare da ya tofa ufan ba ya shige motarsa ya kama hanya ya nufi gidansa

Yana zuwa yau bai KO leka mutanen nasa ba , ya fice direct sai dakinsa

Yana shiga ya ajiye kur’anin a gefen gadonsa ya tsuguna a nan ya saka hanunsa ya  barbaza gashin kansa ya rufe idanuwansa cikin firgici ya bude ya mike da wata irin kara ya shiga watsi da kayan dakin yana fadin no , no ,no , Mubasshir kaifa ba mahaukaci bane , kaifa ba Mahaukaci bane , mai ya hadaka kuma da wanan? Tabas duk abinda ta fada gaskiya ne, to aman idan har gaskiyar Kenan ta boye wani abin , dan kuwa bazai yiwu ta ce wai ta zauna a gidan kato har tsawon sati daya wai ya bar mata gidan a nan kasar Nigeria? Wasu mazan da kamar su warto matan a gari shi ya samu wanan santaleliyar a gidan sa shi ba ustaz ba ,ba komai ba kuma ya zuba mata ido? No wanan ai bazan yarda ba kawai ya ciyar da ita ne ita kuwa ta biya shi, ya kaiwa table din daki duka da hanunsa

Gabansa ya kara faduwa da ta tuna harda mace ta nemi ta nemeta wai ta gudu , a yanda ya san gidan nan da matakan tsaro ita ta isa ta gudu ba tare da an Ankara da ita ba ? No bazan shanye wanan ba , kawai ta yi abinda ake so da ita ne ta samu hanyar FITA, ya rufe idanuwansa wasu zafafan hawaye suka zubo masa daga idanuwansa Wanda rabon *Honorable AA Mubasshir* da ya zubda su har ya manta wai yau gashi yana zubar da su ya furta *Ludu* Kenan ???? Inalilahi wa’ina ilaihi raj’une ya silale nan kasa yana hawaye tun karfinsa yana fadin oh my god , Ya Allah ka kawo min dauki domin wanan ciwon yafi karfina , wanan ciwon bazan iya magancewa kaina shi ba , wanan ciwon ya zarce da tinanina ya fi karfin karfina

To fah shin wani ciWo ne wanan? Sanan maiye damuwar honorable da idan ma Yar Mahaukaciya ta gamu da abinda yake zato? Zato zunubi ne koda ya kasance gaskiya ne , shin honorable ya manta da wanan ne???????????????

Happy juma’at daga Yar Buzuwa yar Mutan Niger Sajida❤❤❤❤❤

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      48

A nan kasa ya yasu cikin wani irin hali marar musaltuwa ance idan mutun na mawuyacin hali baya jin sha’awar komai aman yana rufe idanuwansa hotonta da rigar barcin nan ta fado masa a idanuwansa firgigit ya kuma bude idanuwansa yana maimaita A’uzubilahi mina shaidanin rajim yana rufe ido

Daidai nan *Sahla* ta shigo dakin da salamarta ganin AA a zaune a kasa ya sakata karasawa da Sauri tana fadin *Hubby* lafiya ?

*Mubasshir* ya dago kansa ya zuba mata idanuwa yana kalonta a ransa yayi hamdallah dan kuwa da bata zo din bama tabas da shi ya je ya fitar da abinda ke damunsa

Hanu ya Mika ya jawota nan kasan inda yake zaune ya shiga yamutsata da haushi haushi abin kamar hauka tun tana ganin zata iya jurewa har ta fara kuka tun karfinta daman abin da har a lokacin ta kasa sabawa da shi kulun sai ta jure ta kai zuciyarta nesa duk irin jarabarta gashi yau tamkar ba a hayacinsa yake ba

Shi kuwa gaba daya rikide masa tayi ta koma masa macen da yafi kyankyami a rayuwarsa sanan yafi bukatar kasancewa da ita hakan yasa ya zage yayi mata horo na abinda tayi masa ( tofa sowie Sahla) bashi ya barta ba sai da yayi mata jinajina ya kai sai ta ja nunfashinta da karfi take iya fitar da shi , ya Mike a hankali ya nufi bayi ya sakarwa kansa ruwa sai da ya jima kana ya fito ya taimakawa Sahla Wace take takawa tamkar sabuwar amarya

Yana gama shiryawa ya zauna saman gadonsa ya bude kur’anin Rahma inda ya karanta sunanta *Rahma Idriss* ya dauko biro ya goge sunan Idriss din ya fara rubuta *M* kuma sai ya rufe ya ajiye ya mike ya fice daga gidan GABA daya

Wasa wasa sai da Yar Mahaukaciya tayi jinyar sati guda a gida jinya mai kama da hutu domin har dan kiba ta kara jikinta yayi wani irin freich domin wani hadin sabulai da Hajiya Fadimatu ta hada mata da kanta ga manta da take shafawa mai kara sulbin fata da kuma sheki , Hajiya Fadimatu kanta da tayi yawon kasa kasa tana sarawa kyan Yar Mahaukaciya kuma tana ji a jikinta cewar Mahaukaciya Mahaifiyarta ba Mahaukaciya bace tun haihuwa dan kuwa alamu da yawa suna nuna hakan , kulun cikin adu’a suke Allah ya bayana ta a duk inda take .

Zaune take da wata doguwar riga baka mai duwatsu jajaye da fari a jikinta kanta ba dan kwali ta saka ribom ja ta daure shi ta buda litafinta tana bitar karatun da akayi bata nan

Salama aka yi daga kofar shigowa ta daga kanta ta amsa  tare da mikewa tana dafa kirjinta

Wanda ya shigo shima hakan ya zaro ido ya shigo da Sauri yana fadin beautyna kece KO idanuwana ne?

Yar Mahaukaciya ta ce ” Yaya Abdallah kaine?

Abdallah yayi wata dariyar Farin ciki daidai nan Hajiya Fadimatu ta fito tana fadin tamkar salama nake ji

Abdallah yayi Saurin tsugunawa yana gaisheta

Hajiya Fadimatu ta amsa cike da sakin fuska sanan ta ce ” Kun san juna ne Yar Fadimatu?

Yar Mahaukaciya ta kaleta ta ce ” Lah Mama ai shine Wanda ya kaini gidansa nayi sati a can din nan

Hajiya Fadimatu ta ce ” kai masha Allah na gode sosai da irin rikon da kayiwa yata Allah ya saka da alkhairi

Abdallah ya kara sine kai yana Sosa kansa ya ce ” aa mama ai yiwa kai ne

Bayan sun zauna Abdallah ya dubi Maman Mubasshir ya ce ” Mama daman Karin albashi muka samu gaba daya mutanen kanfanin sanan ni an kara min matsayi shine nazo nayiwa elhaj din godiya dan ban san gidansa ba kuma a office din ma sunce yayi hani da aje gidansa ya ce idan ana neman sa a zo nan kuma sai Allah yayi na taki sa’a na tardo sister a nan

Hajiya Fadimatu ta ce” eh hakane kaga yarinyata ce kwanakin baya ta samu wata jarabawar ubangiji aman Allah ya tsawatarwa abin sai dai yarona kaninta bai rayu ba

Abdallah ya zaro ido yana fadin Allahu akhbar Allah ya jikansa da rahama

Hajiya Fadimatu ta ce” amin , ya Allah , aman matar taka tayi aure?

Abdallah yayi jim yace ” ai mama itama ta rasu , hatsarin mota tayi sai tokarta aka bine

Yar Mahaukaciya ta zaro ido a tare suka furta inalilahi wa’ina ilaihi raj’une

Hajiya Fadimatu ta ce” haka ne rayuwa kowa da abunda zai zamto ajalinsa sai dai muyi fatan kyakyawan karshe da kuma samun rabo mai kyau a kiyama

Gaba daya suka amsa da amin ,

Suna tsaka da labari Mubasshir yayi salama dan kuwa rabonsa da gidan tun ranar da ya koma gida yayi tafiya Australi da niyar yayi wata aman hakan ya gagara Dole ya juyo ya dawo gida

Hajiya Fadimatu ta dago kanta tana fadin ga bakin Australi sun sauko

Abdallah ya Mike da Sauri yana fadin barka da zuwa Elhaj har yana dan risinawa ya Mika masa hanu dan girmamawa

Mubasshir ma ya Mika masa suka gaisa yana fadin kaine a gidan na Maman Mubasshir?

Abdallah ya ce ” Eh wly Elhaj daman zuwa nayi na kara godiya ashe baka garin ma

Mubasshir ya ce” Haka , yau na dawo , no yiwa kaine ba komai

Abdallah ya kara risinawa yana fadin ” to mama zan fice sai na dawo

Hajiya Fadimatu ta ce”” sanu da kokari a sauka lafiya Abdallah , ta dubi Yar Mahaukaciya dake kalon kasa ta ce ” Yar Fadimatu tashi ki yiwa dan uwan naki rakiya KO?

Yar Mahaukaciya ta mike ta dauki dan kwalin rigarta ta yafa a kanta ta nufi kofa dan rakiyar Abdallah

Hajiya Fadimatu ta juyo bayan fitar Yar Mahaukaciya daga falon ta kali AA da yayi mutuwar zaune yana kalon kofar da ta bi ta fita yana tinanin sabon al’amarin nan , ita kuwa ina ta san shi? Meye hadinta da shi? KO shima yana cikin mutanenta ne ??????????????

Hajiya Fadimatu ta ce ” baka jina ne ina magana?

Mubasdhir ya juyo yana kalonta ya ce ” ina zuwa Maman Mubasshir nayi mantuwa a mota ya Mike ya fice har yana kokarin bige kyauran madubin dake falon

Yana FITA gabansa ya fadi hangota da yayi jingine jikin motar Abdallah ta rufe fuskarta tana murmushi

Wani irin dumdumdum yaji a ransa idanuwansa suka rufe ya fara ganin duhu duhu ya sauko daga matatakalar kofar dakin gadan gadan ya nufo su ya…………….

Muje zuwa taku ce Yar gidanku ce Sajida???

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      49

????????????hhh i’m sorry fans, i’m sorry na dawo

Yana isowa da alamar basarwa ya ce” au rakiyar bata kare ba?

Abdallah ya dan risina yana fadin

Ai ni na dan tsayar da ita Elhaj, yana fadi yana dan Sosa keya irin yaji kunyar sirikin nan

Mubasshir ya hadiye wani daci a ransa sukayi salama Abdallah ya shiga motarsa ya juya cike da murnar ganin Yar Mahaukaciya duk da bata bashi amanar zata iya soyaya da shi ba yana ji a jikinsa zata amince masa

Mai dinki ne?

Yar Mahaukaciya ta dago ta kali Mubasshir sai taga tamkar ba shine yayi maganar ba hakan yasa ta juya a hankali ta nufi ciki shi kuwa ya kasa tsayar da ita gudun raini

Yana dawowa ya zauna kusa da mahaifiyarsa ya ce ” Maman Munasshir yarinyar nan ta fara zuwa makaranta ne?

Hajiya Fadatu ta ce” Wace yarinya kuma?

Mubasshir ya yatsina fuska ya ce ” ta gidan nan

Hajiya Fadimatu ta girgiza kai ta ce” aa sai tomorrow l’a , please kirawota ma ka kaimin ita saloon dan saboda a gyara mata gashinta saboda school

Mubasshir ya dago kansa ya kali mahaifiyarsa bai san lokacin da bakinsa ya furta Yaya kyan kura bare tayi hauka?

Hajiya Fadimatu ta ce” mai kake nufi da hakanan?

Mubasshir ya ce ” Maman Mubasshir manan ki dena cewa taje saloon kar aje a gamu da ita aje a fadawa su Abdul kinga wata matsalar ce

Hajuya Fadimatu ta girgiza kai ta ce ” naji ba damuwa

Haka suka wuni tare har yama tayi ya nufi gidansa ba tare da ya kuma Sakata a idanuwansa ba

Yau ta kama litinin tun karfe bakwai da rabi ta gama shiryawa ta fito fes da ita ,  har bakin mota Hajiya Fadimatu tayi mata rakiya tana kara jadada mata cin abinci a kan lokaci sanan banda cin abu mai sanyi

Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta rungume Hajiya Fadimatu ta ce” Mama karki damu zan kiyaye

Hajiya Fadimatu tayi murmushin itama tana kara gyara mata hijab dinta ta shige suka tafi

Tunda ta iso Fati ke murna haka sauran yan ajinsu banda princesses Wace gaba daya wani irin haushi ya turnuke ta na ganin kanwar AA ta dawo

Zaune yake cikin office dinsa , wayar sa ta dau kukan neman agaji , wanan Kiran na biyar ne hakan ya sa ya mika hanu ya daga

Daga dayan bangaren akayi salama

Mubasshir ya amsa yana fadin ya akayi ne kabir?

Kabir ya ce ” Elhaj daman yau naga Hajiya ta dawo makaranta aman dalilin kokarinta aka canza mata aji aka mayar da ita ajin wanan saurayin dan gidan minister dake sonta , nayi nayi a maido ta sun kiya sun ce wajen yafi dacewa da ita , ni kuma sunki maida ni can din shine yasa nace bara na fada maka a san yanda za’ayi

Mubasshir ya ce ” What? Shi din wanene shi? Dan ubansa na minister shine zai sota ?

Kabir ya ce ” ayi Hakuri Elhaj yanzu haka ina zaune ina hangenta a ajin  , shi kuwa ya dawo da kujerar sa kusanta sanan yau bata saka likaf ba

Ai Mubasshir bai san sanda ya kashe Kiran ba ya mike ya kwashi makulan motarsa ya nufi kofa KO sanar da su baiyi ba inda zai nufa

Tafe yake yana nanata Mubasshir Yar Amana ce a wajenka dan haka Dole kayi takatsantsan  da al’amuran ta , bazai yiwu kana ji kana gani wani dan iska ya kara lalata mata tarbiya bayan ta titi daman da ta samu, Dole ka kawo canji a rayuwarta ka fada mata karta yarda ta kula KO wani saurayi kai zaka sama mata miji idan har bata iya zama sai da namijin a kusanta ( to kaji fa Mubasshir haka ta fada maka)

Haka yayi tayiwa kansa zance tamkar sabon kamu har ya iso makarantar su Yar Mahaukaciya

Masu tsaron kofar Makarantar kansu sunyi mamakin ganin AA da kansa a makarantar gashi ba wani abu ake ba balatana suyi tinanin an gayato shi ne , KO kanwar tasa dake makarantar ce ba lafiya KO wani Abin? Haka dai suka bude masa ya nufi ciki

Yana isa ya tsayar da motarsa ya fito cikin shigarsa ta alfarma ya nufi office din director din fuskarsa da glass na rana baki ,

Yana isa sau daya ya konkwasa

Director din ya amsa da com in

Mubasshir AA ya tura ya shiga yana kokarin zare gilas din idonsa

Director ya Mike da Sauri yana fadin “kai kai kai yau baki ne damu haka?

Mubasshir ya kale shi ya ce ” Asalamu alaikum, i’m sorry director kafin mu gaisa ka fito ka fito min da sisterna daga ajin da aka kaita

Director ya kale shi ya ce” AA ni kasan na san mahaifinka kafin ya rasu , Nasan kai daya ya malaka, kuma mahaifiyarka bata kara aure ba , to taya ta zama kanwarka? Ni fa abin nan na daure min kai kuma kaga dokar makarantar nan fa AA ku da kanku kuka dorata bai dace daga kanku a samu wata matsalar ba fa

Jikin Mubasshir yayi sanyi tabas ya taka doka har biyu a wanan makarantar , ta farko ya saka an karbi Rahma ba tare da takardar haihuwarta ba , a zuwan dan kawai kwakwaluwarta ta bude sai na biyu ya kawo Wanda zai kula da dukan abinda take aikatawa a cikin makarantar a matsayin dalibi shima an yarje masa, to idan yaci gaba da haka za’a samu tangardar dokar

Director ya katse masa tinaninsa ya ce ” Aman fa kayi hakuri AA daman dan a dan daidaita al’amarin ne dan ganin komai ya tafi daidai

She is my wife

Director ya zaro ido yana kalon AA dake tsaye yana dan kakauda kai yana nadamar abinda bakinsa ya fada wata karyar Kenan , director ya ce ” what?

Mubasshir ya dan duko ya dora hanayensa biyu saman table din ya ce ” *yes , She Is My WIFE* director shi yasa kaga inai maka kwana kwana, dan ajin da zatayi ba matan aure ni kuwa da nan na yarda na san baza’a samu malaman banza a nan ba

Director ya ce ” Kai masha Allah , ai da tunda wuri ka fada min haka ai da ba’a soma hadata bama da mazan dan haka muje a maiyar da ita wancen ajin

Mubasshir ya fito daidai an fidosu cin abincin rana nan fa kalo ya koma sama shaho ya dau giwa duk sai masu kalon AA a jarida da kuma TV sukayi arba da shi a fili

Yar Mahaukaciya da Kawarta Fati sun fito suna tafiya da niyar dosar wajen cin abinci suka ji ana yi musu magana

Fati ta fara juyawa tayi arba da AA da director sun nufo su ,ai bata san lokacin da ta furta masha Allah irin kyan da yayi mata a fuskarta ta juyo da Yar Mahaukaciya tana Fadin wayo AA ne

Kalon kalo suka yiwa juna inda yana isowa ya ciro nikaf daga aljihunsa ya Mika mata

Cikin rawar hanu ta mika hanunta zata karba inda garin karkarwar ya kufce ya fadin ,nima na ajiye wayar dan caji????????

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      48

A nan kasa ya yasu cikin wani irin hali marar musaltuwa ance idan mutun na mawuyacin hali baya jin sha’awar komai aman yana rufe idanuwansa hotonta da rigar barcin nan ta fado masa a idanuwansa firgigit ya kuma bude idanuwansa yana maimaita A’uzubilahi mina shaidanin rajim yana rufe ido

Daidai nan *Sahla* ta shigo dakin da salamarta ganin AA a zaune a kasa ya sakata karasawa da Sauri tana fadin *Hubby* lafiya ?

*Mubasshir* ya dago kansa ya zuba mata idanuwa yana kalonta a ransa yayi hamdallah dan kuwa da bata zo din bama tabas da shi ya je ya fitar da abinda ke damunsa

Hanu ya Mika ya jawota nan kasan inda yake zaune ya shiga yamutsata da haushi haushi abin kamar hauka tun tana ganin zata iya jurewa har ta fara kuka tun karfinta daman abin da har a lokacin ta kasa sabawa da shi kulun sai ta jure ta kai zuciyarta nesa duk irin jarabarta gashi yau tamkar ba a hayacinsa yake ba

Shi kuwa gaba daya rikide masa tayi ta koma masa macen da yafi kyankyami a rayuwarsa sanan yafi bukatar kasancewa da ita hakan yasa ya zage yayi mata horo na abinda tayi masa ( tofa sowie Sahla) bashi ya barta ba sai da yayi mata jinajina ya kai sai ta ja nunfashinta da karfi take iya fitar da shi , ya Mike a hankali ya nufi bayi ya sakarwa kansa ruwa sai da ya jima kana ya fito ya taimakawa Sahla Wace take takawa tamkar sabuwar amarya

Yana gama shiryawa ya zauna saman gadonsa ya bude kur’anin Rahma inda ya karanta sunanta *Rahma Idriss* ya dauko biro ya goge sunan Idriss din ya fara rubuta *M* kuma sai ya rufe ya ajiye ya mike ya fice daga gidan GABA daya

Wasa wasa sai da Yar Mahaukaciya tayi jinyar sati guda a gida jinya mai kama da hutu domin har dan kiba ta kara jikinta yayi wani irin freich domin wani hadin sabulai da Hajiya Fadimatu ta hada mata da kanta ga manta da take shafawa mai kara sulbin fata da kuma sheki , Hajiya Fadimatu kanta da tayi yawon kasa kasa tana sarawa kyan Yar Mahaukaciya kuma tana ji a jikinta cewar Mahaukaciya Mahaifiyarta ba Mahaukaciya bace tun haihuwa dan kuwa alamu da yawa suna nuna hakan , kulun cikin adu’a suke Allah ya bayana ta a duk inda take .

Zaune take da wata doguwar riga baka mai duwatsu jajaye da fari a jikinta kanta ba dan kwali ta saka ribom ja ta daure shi ta buda litafinta tana bitar karatun da akayi bata nan

Salama aka yi daga kofar shigowa ta daga kanta ta amsa  tare da mikewa tana dafa kirjinta

Wanda ya shigo shima hakan ya zaro ido ya shigo da Sauri yana fadin beautyna kece KO idanuwana ne?

Yar Mahaukaciya ta ce ” Yaya Abdallah kaine?

Abdallah yayi wata dariyar Farin ciki daidai nan Hajiya Fadimatu ta fito tana fadin tamkar salama nake ji

Abdallah yayi Saurin tsugunawa yana gaisheta

Hajiya Fadimatu ta amsa cike da sakin fuska sanan ta ce ” Kun san juna ne Yar Fadimatu?

Yar Mahaukaciya ta kaleta ta ce ” Lah Mama ai shine Wanda ya kaini gidansa nayi sati a can din nan

Hajiya Fadimatu ta ce ” kai masha Allah na gode sosai da irin rikon da kayiwa yata Allah ya saka da alkhairi

Abdallah ya kara sine kai yana Sosa kansa ya ce ” aa mama ai yiwa kai ne

Bayan sun zauna Abdallah ya dubi Maman Mubasshir ya ce ” Mama daman Karin albashi muka samu gaba daya mutanen kanfanin sanan ni an kara min matsayi shine nazo nayiwa elhaj din godiya dan ban san gidansa ba kuma a office din ma sunce yayi hani da aje gidansa ya ce idan ana neman sa a zo nan kuma sai Allah yayi na taki sa’a na tardo sister a nan

Hajiya Fadimatu ta ce” eh hakane kaga yarinyata ce kwanakin baya ta samu wata jarabawar ubangiji aman Allah ya tsawatarwa abin sai dai yarona kaninta bai rayu ba

Abdallah ya zaro ido yana fadin Allahu akhbar Allah ya jikansa da rahama

Hajiya Fadimatu ta ce” amin , ya Allah , aman matar taka tayi aure?

Abdallah yayi jim yace ” ai mama itama ta rasu , hatsarin mota tayi sai tokarta aka bine

Yar Mahaukaciya ta zaro ido a tare suka furta inalilahi wa’ina ilaihi raj’une

Hajiya Fadimatu ta ce” haka ne rayuwa kowa da abunda zai zamto ajalinsa sai dai muyi fatan kyakyawan karshe da kuma samun rabo mai kyau a kiyama

Gaba daya suka amsa da amin ,

Suna tsaka da labari Mubasshir yayi salama dan kuwa rabonsa da gidan tun ranar da ya koma gida yayi tafiya Australi da niyar yayi wata aman hakan ya gagara Dole ya juyo ya dawo gida

Hajiya Fadimatu ta dago kanta tana fadin ga bakin Australi sun sauko

Abdallah ya Mike da Sauri yana fadin barka da zuwa Elhaj har yana dan risinawa ya Mika masa hanu dan girmamawa

Mubasshir ma ya Mika masa suka gaisa yana fadin kaine a gidan na Maman Mubasshir?

Abdallah ya ce ” Eh wly Elhaj daman zuwa nayi na kara godiya ashe baka garin ma

Mubasshir ya ce” Haka , yau na dawo , no yiwa kaine ba komai

Abdallah ya kara risinawa yana fadin ” to mama zan fice sai na dawo

Hajiya Fadimatu ta ce”” sanu da kokari a sauka lafiya Abdallah , ta dubi Yar Mahaukaciya dake kalon kasa ta ce ” Yar Fadimatu tashi ki yiwa dan uwan naki rakiya KO?

Yar Mahaukaciya ta mike ta dauki dan kwalin rigarta ta yafa a kanta ta nufi kofa dan rakiyar Abdallah

Hajiya Fadimatu ta juyo bayan fitar Yar Mahaukaciya daga falon ta kali AA da yayi mutuwar zaune yana kalon kofar da ta bi ta fita yana tinanin sabon al’amarin nan , ita kuwa ina ta san shi? Meye hadinta da shi? KO shima yana cikin mutanenta ne ??????????????

Hajiya Fadimatu ta ce ” baka jina ne ina magana?

Mubasdhir ya juyo yana kalonta ya ce ” ina zuwa Maman Mubasshir nayi mantuwa a mota ya Mike ya fice har yana kokarin bige kyauran madubin dake falon

Yana FITA gabansa ya fadi hangota da yayi jingine jikin motar Abdallah ta rufe fuskarta tana murmushi

Wani irin dumdumdum yaji a ransa idanuwansa suka rufe ya fara ganin duhu duhu ya sauko daga matatakalar kofar dakin gadan gadan ya nufo su ya…………….

Muje zuwa taku ce Yar gidanku ce Sajida???

??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      49

????????????hhh i’m sorry fans, i’m sorry na dawo

Yana isowa da alamar basarwa ya ce” au rakiyar bata kare ba?

Abdallah ya dan risina yana fadin

Ai ni na dan tsayar da ita Elhaj, yana fadi yana dan Sosa keya irin yaji kunyar sirikin nan

Mubasshir ya hadiye wani daci a ransa sukayi salama Abdallah ya shiga motarsa ya juya cike da murnar ganin Yar Mahaukaciya duk da bata bashi amanar zata iya soyaya da shi ba yana ji a jikinsa zata amince masa

Mai dinki ne?

Yar Mahaukaciya ta dago ta kali Mubasshir sai taga tamkar ba shine yayi maganar ba hakan yasa ta juya a hankali ta nufi ciki shi kuwa ya kasa tsayar da ita gudun raini

Yana dawowa ya zauna kusa da mahaifiyarsa ya ce ” Maman Munasshir yarinyar nan ta fara zuwa makaranta ne?

Hajiya Fadatu ta ce” Wace yarinya kuma?

Mubasshir ya yatsina fuska ya ce ” ta gidan nan

Hajiya Fadimatu ta girgiza kai ta ce” aa sai tomorrow l’a , please kirawota ma ka kaimin ita saloon dan saboda a gyara mata gashinta saboda school

Mubasshir ya dago kansa ya kali mahaifiyarsa bai san lokacin da bakinsa ya furta Yaya kyan kura bare tayi hauka?

Hajiya Fadimatu ta ce” mai kake nufi da hakanan?

Mubasshir ya ce ” Maman Mubasshir manan ki dena cewa taje saloon kar aje a gamu da ita aje a fadawa su Abdul kinga wata matsalar ce

Hajuya Fadimatu ta girgiza kai ta ce ” naji ba damuwa

Haka suka wuni tare har yama tayi ya nufi gidansa ba tare da ya kuma Sakata a idanuwansa ba

Yau ta kama litinin tun karfe bakwai da rabi ta gama shiryawa ta fito fes da ita ,  har bakin mota Hajiya Fadimatu tayi mata rakiya tana kara jadada mata cin abinci a kan lokaci sanan banda cin abu mai sanyi

Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta rungume Hajiya Fadimatu ta ce” Mama karki damu zan kiyaye

Hajiya Fadimatu tayi murmushin itama tana kara gyara mata hijab dinta ta shige suka tafi

Tunda ta iso Fati ke murna haka sauran yan ajinsu banda princesses Wace gaba daya wani irin haushi ya turnuke ta na ganin kanwar AA ta dawo

Zaune yake cikin office dinsa , wayar sa ta dau kukan neman agaji , wanan Kiran na biyar ne hakan ya sa ya mika hanu ya daga

Daga dayan bangaren akayi salama

Mubasshir ya amsa yana fadin ya akayi ne kabir?

Kabir ya ce ” Elhaj daman yau naga Hajiya ta dawo makaranta aman dalilin kokarinta aka canza mata aji aka mayar da ita ajin wanan saurayin dan gidan minister dake sonta , nayi nayi a maido ta sun kiya sun ce wajen yafi dacewa da ita , ni kuma sunki maida ni can din shine yasa nace bara na fada maka a san yanda za’ayi

Mubasshir ya ce ” What? Shi din wanene shi? Dan ubansa na minister shine zai sota ?

Kabir ya ce ” ayi Hakuri Elhaj yanzu haka ina zaune ina hangenta a ajin  , shi kuwa ya dawo da kujerar sa kusanta sanan yau bata saka likaf ba

Ai Mubasshir bai san sanda ya kashe Kiran ba ya mike ya kwashi makulan motarsa ya nufi kofa KO sanar da su baiyi ba inda zai nufa

Tafe yake yana nanata Mubasshir Yar Amana ce a wajenka dan haka Dole kayi takatsantsan  da al’amuran ta , bazai yiwu kana ji kana gani wani dan iska ya kara lalata mata tarbiya bayan ta titi daman da ta samu, Dole ka kawo canji a rayuwarta ka fada mata karta yarda ta kula KO wani saurayi kai zaka sama mata miji idan har bata iya zama sai da namijin a kusanta ( to kaji fa Mubasshir haka ta fada maka)

Haka yayi tayiwa kansa zance tamkar sabon kamu har ya iso makarantar su Yar Mahaukaciya

Masu tsaron kofar Makarantar kansu sunyi mamakin ganin AA da kansa a makarantar gashi ba wani abu ake ba balatana suyi tinanin an gayato shi ne , KO kanwar tasa dake makarantar ce ba lafiya KO wani Abin? Haka dai suka bude masa ya nufi ciki

Yana isa ya tsayar da motarsa ya fito cikin shigarsa ta alfarma ya nufi office din director din fuskarsa da glass na rana baki ,

Yana isa sau daya ya konkwasa

Director din ya amsa da com in

Mubasshir AA ya tura ya shiga yana kokarin zare gilas din idonsa

Director ya Mike da Sauri yana fadin “kai kai kai yau baki ne damu haka?

Mubasshir ya kale shi ya ce ” Asalamu alaikum, i’m sorry director kafin mu gaisa ka fito ka fito min da sisterna daga ajin da aka kaita

Director ya kale shi ya ce” AA ni kasan na san mahaifinka kafin ya rasu , Nasan kai daya ya malaka, kuma mahaifiyarka bata kara aure ba , to taya ta zama kanwarka? Ni fa abin nan na daure min kai kuma kaga dokar makarantar nan fa AA ku da kanku kuka dorata bai dace daga kanku a samu wata matsalar ba fa

Jikin Mubasshir yayi sanyi tabas ya taka doka har biyu a wanan makarantar , ta farko ya saka an karbi Rahma ba tare da takardar haihuwarta ba , a zuwan dan kawai kwakwaluwarta ta bude sai na biyu ya kawo Wanda zai kula da dukan abinda take aikatawa a cikin makarantar a matsayin dalibi shima an yarje masa, to idan yaci gaba da haka za’a samu tangardar dokar

Director ya katse masa tinaninsa ya ce ” Aman fa kayi hakuri AA daman dan a dan daidaita al’amarin ne dan ganin komai ya tafi daidai

She is my wife

Director ya zaro ido yana kalon AA dake tsaye yana dan kakauda kai yana nadamar abinda bakinsa ya fada wata karyar Kenan , director ya ce ” what?

Mubasshir ya dan duko ya dora hanayensa biyu saman table din ya ce ” *yes , She Is My WIFE* director shi yasa kaga inai maka kwana kwana, dan ajin da zatayi ba matan aure ni kuwa da nan na yarda na san baza’a samu malaman banza a nan ba

Director ya ce ” Kai masha Allah , ai da tunda wuri ka fada min haka ai da ba’a soma hadata bama da mazan dan haka muje a maiyar da ita wancen ajin

Mubasshir ya fito daidai an fidosu cin abincin rana nan fa kalo ya koma sama shaho ya dau giwa duk sai masu kalon AA a jarida da kuma TV sukayi arba da shi a fili

Yar Mahaukaciya da Kawarta Fati sun fito suna tafiya da niyar dosar wajen cin abinci suka ji ana yi musu magana

Fati ta fara juyawa tayi arba da AA da director sun nufo su ,ai bata san lokacin da ta furta masha Allah irin kyan da yayi mata a fuskarta ta juyo da Yar Mahaukaciya tana Fadin wayo AA ne

Kalon kalo suka yiwa juna inda yana isowa ya ciro nikaf daga aljihunsa ya Mika mata

Cikin rawar hanu ta mika hanunta zata karba inda garin karkarwar ya kufce ya fadin ,nima na ajiye wayar dan caji????????

??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      50

Mamyna my blood sister *Mariam maman Imran love u*

Mamyna *Khadija ni ma ina sonki irin da yawa din nan*

Jinjina gareki sis *Muneera* ina yinki sosai

A tare suka duka da niyar dauko nikaf din da ya fadi , sai dai ya rigayeta dora hanunsa a sama hakan yasa ta kasa karasa nata hanun sanan ta kasa dagowa

A nitse ya dago fuskarsa cikin sa’a kuwa suka hada ido hudu da shi da sauri ta sada kanta suka kuma mikewa a tare ,

Kara matsawa yayi kusanta ya gyara nikaf din sai gani tayi yana nufo fuskarta da niyar ya daura mata

Abin mamaki KO motsi kasawa tayi ya kama ya daura mata nikaf din a fuskarta , abinda tunda yake bai taba ba domin yana dage mata nikaf din suka kuma yin ido hudu da yayi saurin lumshe idanuwansa wa’inda tini suka fara karbar sakonnin idanuwan *Yar Mahaukaciya*

Cikin mutuwar jiki ya ce ” mu tafi Maman Mubasshir na kiranki

Yar Mahaukaciya ta zaro ido ta ce ” Lafiyarta? Mai ya samu Maman Rahma? Bata jin dadi ne?

Mubasshir ya zuba mata ido irin yanda ta rikice take maimaita masa tambayar dake nufin abu daya a karo uku, wai kuma shi ya ce mata *Maman Mubasshir* ita kuwa tace masa wani *Maman Rahma*

Tabo hanunsa da tayi ne ya tunatar da shi fa ya shiga tinani , firgigit yayi yana fadin ” No lafiyarta lau tana dai kiranki

Yar Mahaukaciya ta juya tayi salama da Fati kawarta suka juya suka shiga mota ya kama hanya ya harbata titi

Tafe yake yana tinani kala daban daban a zuciyarsa , haka bangaren Yar Mahaukaciya domin taga ba hanyar zuwa gida ya kama ba , aman bazata iya yi masa tambayar inda zai kaita ba , ta yarda da shi

Sun kusan minti arba’in a hanyar sanan suka iso wata babar unguwa Wace da gani ka san wanan unguwa ta manya ce,   zama ta gyara ta kara buda idanuwanta tana karewa wanan unguwa kalo a ranta ta ce ” Kai Lagos da abin mamaki take

Tsayuwar motar ne ya fargar da ita ta zubawa kofar gidan da suka tsaya ido , har wani kara murza idanuwanta take

Cikin dakakiyar Murya ya ce” fito

Yar Mahaukaciya gabanta ya fadi ta kali Gabas da yama , kudu da arewa ba kowa irin unguwar nan ce ta yan gayu KO ihu kayi iya kai zai tsaya , ta kuma kalon kasa taga ba kasa bace ta ajiye wata nanauyar ajiyar zuciya a ranta tace” Maman Rahma baga irinta ba , yanzu KO wani abin ya sameni a wajen nan ai bazan iya guduwa dan kuwa wanan takalman da kika sakani sakawa yayi min nauyi

” *Wai bazaki fito ba?* ” Mubasshir ya  fuskarsa a daure

Gaba daya jikinta bari yake , haka ta kokarta ta fito tana Jan kafa ta bi bayansa domin bai shiga gidan da mota ba ,

Kofa kanta sai da suka shiga uku a ta hudun ce ya dora hanunsa kana ta bude , itadai binsa take kawai bata ce komai ba har suka ISO wani banban waje mai kyan gaske , sai a nan ta fara ganin mutane kuma abin mamaki harda tsofafi

Wata tsohuwa ta hango tana kokarin tashi sai dai kusanta ta zubar da ruwa ga yanayin wajen shi kansa santsin ne da shi , ga santsin ruwan , Ai bata san lokacin da ta shige gaban AA Mubasshir dake tafiyar kasaita ta nufi wanan tsohuwa da gudu ta tarota gaba daya ta rungumota a jikinta tana fadin ” Mama dan tsaya na taimaka miki karki fadi

Cikin ikon Allah tsohuwar bata kai kasa ba Yar Mahaukaciya ta kamata ta canza mata wajen zaman ta ciro dan kwalin kayan makarantarta ta gogewa tsohuwar nan hanu da baki sanan ta kakabe mata jikinta ta kara gyara mata zamanta

Tunda ta shige gabansa da gudu ya tsaya yana kalon KO itama irin na Shalan ne wato taji tsoron tsofafin mutane koma yace kyankyami

Abinda ya gani ne ya saka shi maida hankalinsa a kanta , mamakinta bai gama gushewa ba sai da yaga tana gogewa gogo fuskarta harda majina ,  ya kara maida hankalinsa ganin sai labari take bata ita kuwa ta dage sai dariya take baki ba hakori ,   ji yayi gaba daya zuciyarsa tayi sanyi , wata nutsuwa ta sauko masa a cikin ransa Wace ya rasa ta maicece , wani farin cikin ganin gogo na dariya ya sakashi shima yin dariyar sanan ya matsa kusan su ya dan tsuguna yana kalonsu cike da sha’awar yanayinsu

Yar Mahaukaciya gaba daya ta ma manta da shi tana kokarin ganin gogo ta daina yi mata labarin akoy aljana a cikin gidan ,, 

Juyowa tayi a hankali tana nuni da hanunta tana fadin kinga Gogo gidan nan ba wata aljana sanan koda akoy aljanar akoy adu’ar da mamana ta koya min idan kinyita to fa aljanar nan zata kone ,    ido hudu suka kuma yi da Mubasshir dake kalonsu a tsugune domin sam bata san yazo gurin ba

Hadiye maganarta tayi tana kokarin daura nikaf dinta dan gudun baiwa gogo tsoro har cire shi tayi

Mubasshir ya Mike a hankali yana fadin mu tafi ya nufi hanyar fita itama ta kama nikaf din ta daura sanan ta biyo bayansa

Tafe suke a mota yana yi mata gargadi KO nace kashedi kan ta kiyaye harkar maza , ta fita a harkar maza ta cire maza daga ranta

Yar Mahaukaciya ta dago kanta ta kale shi

Ya ce ” Yes ki cire maza a ranki , idan har mazan ne kin damu da su har haka kawai ki fitar da miji guda aman fa na hane ki da zance na hane ki da sauraron maza a titi ba ruwanki da mazan makarantar ku

Ta kuma kalonsa a ranta ta ce” to mai yake nufi da na saka maza a raina? Kuma na fitar da miji aman ya hanani kula su to ta yaya zasu  soni ma a haka?

Mubasshir ya ce” Malama ki kali gabanki gindaya miki sharuda ne nake dan gudun gobe kiyama Allah ya tambayeni kan amanar da aka bani domin ni din nan ni ne tamkar *Mahaifi* a wajen ki a yanzu dan ni nake da ikon aurar da ke  dan haka ki kiyaye bana son na kuma yi miki magana kan harkar Maza ( Toh fa kaji ikon Allah , sai Baba Mubasshir )

Har suka iso yana haikar baki Wanda ta gaji ta kontar da kanta jikin madubin motar cikin ikon Allah baci yayi awon gaba da ita

Suna isowa Wace Maman Mubasshir ta saka ta zo takanas tun daga maroco dan siyan kayan dakin Yar Mahaukaciya da kuma gama shiryata ta fito daga cikin falon ita da wata mata a kusanta Wace ta dan darata da tsayi ga wani irin fari da gareta idanuwanta da farin glas

Har bakin motar ta rakosu sanan tayi nuni da motar Mubasshir Wanda ya fito ya nufesu dan su gaisa

Yana isa ya dan risina dan duk da bata wani tsufa ba ya san zata haife shi hakan yasa ya risina ya gaishe su

Hajiya Fadimatu ta ce ” yawa dan Fadimatu kaga Hafsat matar da ta hadawa yar gidan Mr President dakinta , tazo Nigeria ne na nemeta nima

Mubasshir ya  ce” Masha Allah Maman Mubasshir , sanan ya ci gaba da fadin” yarinyarki tayi min  baci a mota bara na dauko sakona na koma office ,  

Yana gama fada ya juya ya nufi cikin falon inda Hajiya Fadimatu tayiwa su Hajiya *Rafi’at* salama kan sai tayi mata dabara ta zaba sai ta sanarwa *Hafsat*  ta nufi motar *AA* dan ta tashe da yarinyarta su kuwa suka shiga wuleliyar motarsu suka kama hanyar tafiya.

Cikin nutsuwa ta mika hannunta tana tashin Yar Mahaukaciya Wace tayi nisa cikin baccinta na gajiyar fadan AA Wanda bata san abinda tayi masa ba

Firgigit ta farka da adu’ar tashi daga baci a bakinta tana fadin ” kayi hakuri

Hajiya Fadimatu ta zaro ido ta ce ” Yayi hakuri? Mai yayi miki yarinyata?

Yar Mahaukaciya ta saki ajiyar zuciya Sanan tayi murmushi ta ce ” Mamana Ashe mun karaso , bacine ya dauke ni nayi zaton Yaya ne ke tashina, 

Hajiya Fadimatu ta ce ” eyah, lafiya yau aka sauko da wuri haka?”

Yar Mahaukaciya ta ce ” no bamu sauka ba , yaya ne yace kina son ganina”

Hajiya Fadimatu tayi jim , itadai tasan bata tura shi ba aman kuma bazata karyata shi ba gudun kar ta raina shi KO zuwa gaba hakan yasa ta share tana fadin ” fito mu tafi ki huta kafin yama tayi yata”

Daidai sun fito shima ya fito ya karasa yayiwa mahaifiyarsa salama ya juya akalar motarsa dan komawa office

Yana isa secretariar sa ta tarbe shi da dumbin takardu ta fara zano masa jama’ar da suka zo baya nan da sakon’nin da aka badar , tana tsaka da zanawa ya ce ” Mariam kije gida ki huta

Mariam ta zaro ido cike da mamaki tana kalon bayansa da ya juya ya shige office dinsa domin tunda suke ba’a taba tashi kasa da karfe biyar ba , don kuwa AA akoy son aiki sai gashi yau tun kafin shi ya tafi ita ya salameta kuma da alama lafiyarsa lau , tayi ajiyar zuciya a fili ta ce” alhamdulilah ni ma sai naje na kula da gidana da wuri yau

Bayan shigarsa da kamar minti ashirin sai ga Abdul abokinsa yayan Sahla ya shigo office din da salama

Mubasshir ya dago kansa yana amsa salamarsa sanan ya sauke kafafuwansa ya Mika masa hanu sukayi musabaha

Abdul ya nemi waje ya zauna yana mai ajiyar zuciya

AA ya kare karantarsa ya lura duk ransa a jagule yake ya ce” freind yaya dai?

Abdul ya kale shi cikin yanayin tausayi ya ce” Hajiya ta koreni na koma ta kuma korata da kyar na samu ta yafe min aman tace kawai na manta da yarinyar nan domin tayi min nisa, ni na kasa gane wani irin nisa tayi min indai ba auren wani tayi ba KO mutuwa tayi bata duniyar? Nayi nayi ta fada min inda yarinyar nan take aman fafur Hajiya ta kiya taki ta saurareni please freind ka saka baki wly ni ban san mai nayi mata ba

Mubasshir ya yatsina fuska yana matukar mamakin Abdul kan mace ne yake kokarin yin kuka? Ya ce” wai wace kake nufi?

Abdul ya nisa ya ce” *Rahma* nake nufi freind , kuma da ta wani takarkare take hanani sanin inda hasken idaniyata take ta manta ta sanadiyata ta santa ne????

Mubasshir ya gyara zama ya ce” oh yarinyar nan , Au bata gidan? Toh ban gane ta sanadiyarka ta Santa ba , shin ba ka fada min cewar jikar Hajiyar bace?????

[11/16, 21:18] Umar Dalha: ??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      52

Abdul ya dago kansa ya dubi Mubasshir ya tuna eh fa ga abinda suka fadawa Mubasshir aman gaskiya shi zai fada masa gaskiyar zancen KO ya kama masa Hajiya ta fada masa inda Ta boye masa Rahmarsa , cikin alamar dan jin kunya ya ce ” No ba jikarta bace, hasalima bata hada komai da ita ba , ranar da na fara yin tiyata a rasun nan ranar da bazan taba mantawa da ita ba a ranan na hadu da ita , sanan a ranar hajiya ta ganta , yaron da ya rasun danta ne ,,,…………..””””””’,,,,,,,,,,,,,nan ya kwashe duka yanda akayi har daukanta da sukayi shi da Hajiya Hawau ya fadawa Mubasshir Wanda yake sauraronsa kamar ana kara yi masa bita ne kan abinda aka karanta masa

Mubasshir ya ce ” kuma haka kuka dauki yarinyar da baku san KO wacece ba , wada ta shigo maka asibiti da yaro jiki a farfashe? Shin idan fa wata muguwa ce KO sato dan tayi?

Abdul ya kawar da kansa ya ce” she is innocent, tabas Rahma ba muguwa bace, sanan kamila ce, kuma nitsatsiya ce, domin da muguwa ce a zaman mu da ita da KO ta yaya sai halinta ya fito

Mubasshir ya kuma jefo masa tambayar ” kana sonta ne?

Abdul ya gyara zama yace” ina sonta tamkar yar uwata ta jini, ina jinta a jinin jikina,

Mubasshir ya ce” ya akayi ka gane cewar kana sonta? Mai kake ji har ka gane cewar sonta ne kake?

Abdul ya dago ya kuma kalon Mubasshir Wanda daman shi yake kalo, da alamar mamakin tambayoyinsa ya ce” kafi kowa sani domin kai har kayi aure KO?

Mubasshir ya koma ya jongina da kujerar da yake zaune ya lumshe idanuwansa ya ce” kafi kowa sanin KO auren mai nayi,kafi kowa sanin amintaka ta ci karfina har na kasa yin musu da abinda ya zamto tamkar a cikin duhu nake,  ya kuma dago kansa ya ce ” freind tell me dan Allah mai ake ji? May be na dade da fara son matata rashin sanin inda so din soyaya ya nufa ya hana ni ganewa

Abdul ya ja ajiyar zuciya ya ce” tabas kai namiji ne mai kokari, jarumta, na yarda da jarumtar ka , sanan na gode da abinda kayi domin ni, nima Allah ya bani ikon yi maka abin alkhairi ,  ya nisa ya dora da cewa” idan kaga abin sonka kafin ka furta masa kalmar so zakana ji gabanka na faduwa,   koya ka nisanta da shi burinka ka dawo ka gansa,  koda mumuna ne tofa zaka Ganshi ba Wanda ya kaishi kyau, da zarar kun hada idanuwa sai gabanka ya fadi, baka gajiya da kalonsa, ka tsani wani ya rabe sa balatana namiji, ka tsani wani ya kale shi, ka tsani….

Cikin Sauri Mubasshir ya furta wait wait wait yana daga hanunsa sanan dayan hanun yana laluba gashin kansa ya mike da sauri ya debi ruwa ya rufe ido ya shanye tas sanan ya ajiye kofin ya juyo yana kalon Abdul Wanda yayi tsamanin KO kwaruwa yayi ya ce” aman ai idan amanarka ne ma kana iya jin irin haka KO?

Abdul ya ce” koda kanwarka ce bazaka ji irin hakan ba , ina tsaka da zana maka ka katse ni , naci gaba ne?

Mubasshir ya shiga girgiza kai uwa karamin yaro ya ce” No barshi haka is OK

Abdul ya ce” gaba daya abinda na zana maka ba Wanda bana ji a tatare da yarinyarnan , dan haka ya hade hanayensa ya ce” ka taimakeni ka taya ni ta fada min inda take

Mubasshir ya rintse idanuwansa ya bude ya ce” zanyi kiranka zanje na ganta karka damu

Abdul ya taso cikin jin dadi ya rungume Mubasshir yana yi masa godiya sanan yayi masa salama ya fita

Yana tafiya Mubasshir ya shiga zaro ido tamkar sabon kamu ya fada saman kujera jagob ya tatara gashin kansa ya cakula ya rufe ido yana furta inalilahi wa’ina ilaihi raj’une , inalilahi wa’ina ilaihi raj’une , ya buga hanunsa saman table ji kake taratsatsa domin kolba ce ta fashe

Zumbur ya kuma mikewa ya dauki ky din motarsa hanunsa na digar jini aman bai damu ba ya fito ya shiga motarsa ma’aikatan sai kalonsa suke kowa na mamakinsa aman ba Wanda ya nufe shi dan ba fuskar hakan ,

Tuki yake na ganganci kansa ba hula sanan ba Babar rigarsa a jikinsa farar Riga ce kawa ta ciki,  sai dogon wandonsa na shada , idanuwansa sunyi jajajir haka fuskarsa a murtuke , bai san inda zai nufa ba hasalima burin sa ya ganta a gabansa ya kali fuskarta sanan ya furta mata cewar shi fa sam baya sonta yana kokarin kare mutuncinta ne ,

Wani irin burki ya taka aman ina sai da ya bigi Babar motar da ta kwaso kaya take gabansa ji kake piiiiiiiiit karar  oda inda kansa ya fada , jama’a duk suka fifito hanu a saman kai suna furta inalilahi wa’ina ilaihi raj’une

Da Sauri direban babar motar ya taka birki duk suka firfito suka nufe shi

Zaune suke suna cin abinci wayar dakin ta dauki kara , haka kawai ta ji gabanta ya fadi ta mike da Sauri ta nufi wayar ta daga , sakin wayar tayi sanan ta tafi luuu zata fadi tana fadin inalilahi wa’ina ilaihi raj’une

Da Gudu Yar Mahaukaciya ta tareta tana fadin mama lafiya??????????????????????????????????????????????????????????????????

      ??????

??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      53

Da gudu Yar Mahaukaciya ta tareta tana faman fadin ” Mama lafiya? Aman ina sai da suka kai kasa dan kuwa karfin ba daya ba, cikin Sauri ta rarumo wayar ta kanga a kunanta tayi salama

Daga dayan bangaran likitar take shaida mata anga numberta da kuma ta gida a cikin wani litafi a motarsa yana asibitin Jarumai aman bai ji ciwo sosai ba

Yar Mahaukaciya cikin sarkewar harshe ta ce” wa …..wane yayi hatsarin?”

Matar ta ce” *AA MUBASHIR* “

Yar Mahaukaciya ta furta inalilahi wa’ina ilaihi raj’une sanan ta FITA da sauri tayi Kiran direban gidan kafin ya fitar da motar ta haye sama ta dauko hijabin Hajiya Fadimatu da nata sanan ta sauko cikin gudu gudu ta tsuguna kusan Hajiya Fadimatu ta ce” Mamana yaya bai ji ciwo sosai ba , please ki tashi mu tafi wajensa plz mamana”

Hajiya Fadimatu da sai a lokacin ta dawo daga sumar tsoratar da tayi na jin gidan jininta a asibiti ta mike da kyar ta zura hijabin suka fito suka kama hanyar asibitin

Suna isa aka kaisu dakin da aka kontar da shi cikin girmamawa

Tsayuwa tayi tana kalonsa tana tofa masa adu’a tana yiwa Allah godiya da hatsarin nasa bai zo da tsanani ba , waigowa tayi ta kali doctern ta ce” docter bacin nan na lafiya ne?”

Docter ya ce” eh ma’am alurar baci muka yi masa dan ya huta domin da alama tinani yayi masa yawa dan kuwa shi kadai ya zo ya bigi motar sanan an duba motar lafiyarta lau, kuma shi ba shan wani abin maye yayi ba, ba earpice a kunan sa, kuma kwakwaluwarsa lafiyarta lau kawai dai cikin biyu ne KO wani abin ya taba masa ransa KO yana Sauri ya je wani wajen ne hakan yasa ya kasa control din kansa”

Hajiya Fadimatu ta shafa fuskarsa ta ce” Ya jima yana barcin ne?”

Docter ya ce” eh toh sai da muka daidaita komai ya samu kamar awa uku muna ta neman yanda zamu sanar muku, zuwa yanzu yaci ace ya farka ma sai dai da alama yana jin dadin bacin, Muje ma’am na baku takardun da ake bukatar a cike da kuma na maganin sa”

Hajiya Fadimatu ta kali Yar Mahaukaciya dake tsaye itama tana sauraron bayanan likitan ta ce” Yata bara na dawo” ta juya ta bi bayan doctern

Da tafiyarsu Yar Mahaukaciya tayi tsai tana kalonsa sai bacinsa yake gashin idon nan nasa yayi zagar zagar a konce baki yayi lufluf da shi , bakin nan nasa tamkar ya shafa man lebe sai sheki yake namiji da shekin lebe, a hankali ta jawo kujera ta zauna daf da shi ta dago hanayenta ta dora saman cinyoyinta ta tokare habarta ta zuba masa ido tana kare masa kalo a ranta tana matukar mamakin mumurdewar hanunsa shi kuwa ba karfe yake ci ba a saninta bata taba ganinsa yana irin daga karfen nan aman hanunsa yana yan dambe da ake nunowa a tashar TL9 ,

Tana haka har wani irin baci ya kama idanuwanta ta karewa dakin kalo ba wajen konciya hakan yasa ta dan dora kanta daga bakibakin gadon baci yayi awon gaba da ita ( toh fa ke da aka barwa marar lafiya?)

Cikin nutsuwa ta turo kofar ta shiga da salamar ta , murmushi ne ya subuce mata ganin Mubasshir ya farka yana kalon Yar Mahaukaciya dake baci duk da bai ga fuskarta ba yana son sanin KO wacece ke konce kusan sa ,

Shima Murmushin ya sakar mata ya dago hanunsa irin ta karaso

Hajiya Fadimatu ta karasa suka gaisa da gudan jininta ta ce” Dan Fadimatu yaya saukin jikin?

Mubasshir yayi murmushi cikin muryar maran lafiya ya ce” maman Mubasshir i’m sorry”

Ta girgiza kai ta dora yatsarta a saman lebensa ta ce” no dan gidan Fadimatu dena bani hakuri yarona, Allah ya baka lafiya “

Yayi murmushi yana kalon hanunta magunguna ne ya dan yatsina fuska a ransa ya ce ” tap gaskiya ni bazan sha maganin nan ba”

Bayan ta ajiye ledar maganin ta zo a nitse ta tana murmushi ta ce” oh Yar Fadimatu nasan bacin nan na jiya daman bai wani isheta ba , baiwar Allah gashi yanzu mun kado KO abinci bata ci ba

Gaban mubasshir ya fadi ya lumshe idanuwansa yana kalon mahaifiyarsa na kokarin cirewa Yar Mahaukaciya hijabinta dan ya shake mata wuya , yayi gagawar kawar da kansa yana kara rintse idanuwansa a ransa yana ta adu’o’i kan Allah ya kare masa idanuwansa da kalon banban muradin sa

Idanuwanta ta bude suka yi ido hudu da Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta ce” Mama kin dawo? Baci ne ke damuna

Hajiya Fadimatu ta ce” ai Dole yar Fadimatu, Konta ki hutawarki , ai likitan yace zai mabu salama aman sai dai mu tafi gida da yayanki dan nayi Kiran number matarsa ta yiwa mahaifiyarta rakiya bata nan shi kuwa baya son shan magani sai dai mu tafiyarmu gida da shi

Yar Mahaukaciya ta gyada kanta tana leken fuskarsa ta ce” Allah ya kara afuwa

Hajiya Fadimatu ta ce” Amin , sanan taci gaba da hada masa yan magungunan da likita ya ce ya sha idan ya farka sai a basu salama su je gida ya ci gaba da sha

Cikin ikon Allah likita ya salame su suka nufi gida da magungunan su, aman tunda ya farka bai yarda sun hada ido da Yar Mahaulaciya ba , koda tayi masa sanu da jiki hanunsa kawai ya daga mata a hakan har suka isa gida , inda Hajiya Fadimatu ta rasa décision din da zata dauka domin shi dai ba lafiya ne da shi ba, bazata yarda ya kwana a dakunan kasa ba , kuma dakin nasa shine Yar Mahaukaciya ta zauna, sanan tana ganin lokacin ta fada musu gaskiya yayi KO dan su dan saba da juna

??????????????????????

.

??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      54

Tana zaunen nan falon tana waya da Hajiya Hawau Yar Mahaukaciya ta fito da kwaryar fura a hanunta ta sha damu sai kanshin kayan daka da cikwui take, cikin nutsuwa ta dan zauna har Hajiya fadimatu ta gama wayar

Ganinta ta karaso ya saka Hajiya Fadimatu fadin “toh Hajiya sai kin zo zuwa yamar, sanan kar fa ki daga hankalinki da sauki jikin”

Tana gamawa ta juyo da murmushin nan nata mai tsada ta kali Yar Mahaukaciya

Yar Mahaukaciya ta taso ta nufota ta ce” Mamana ga furar yayan nan na dama nasan zai sha”

Hajiya Fadimatu ta ce” Sanu da kokari Yar Fadimatu, aman tafi ki kai masa furar yana dakina”

Yar Mahaukaciya ta juya ba dan taso hakan ba dan kuwa tunda yayi hatsarin nan tamkar ya wani tsaneta ne KO baya ji idan tayi magana dan kuwa sai dai kawai ta ga yana hararanta

Cikin nutsuwa da faduwar gaban da bata san KO ta maicece ba ta tura dakin bakinta dauke da sallama ,

Idanuwa ta zaro ganin AA Mubasshir jingine da bed ya dafe zuciyarsa ya mike kafafuwansa yana kallon kasa sanan ga wani hawaye na bin fuskarsa , bata san lokacin da ta yar da kwaryar furar ta nufe shi har tana harde kafa

Tana isa ta dire gwuiwoyinta a kasa ta saka yatsarta ta lakato hawayen kuncinsa dan tabatarwa kanta kuka yake, cikin sarkakiyar murya ta ce” Yaya Mubasshir jikin ne? Ina ke yi maka ciwo? Ka sha maganinka? Dan Allah ka dena kuka, bara na kirawo Mamana”

Ta mike da niyar FITA ta kirawo Hajiya Fadimatu sai taji an riko mata hannunta riko ba na wasa ba , riko na keta da zafi sannan aka fisgota

Dabash ta zauna domin sauran kadan ta kifo a kansa Allah ya sota, ta shiga zazare ido tana tsoron abinda ya saka ya rike mata hanu haka sanan irin yanda ya hada fuska ka rantse cewar ba AA bane , gaba daya ya zama wani abin tsoro

Nunfashi ya ja ya sauke ya zuba mata ido yana ayana abubuwa da dama a ransa sannan ya bude bakinsa yayi iya kokarinsa wajen furtawa mai raya tinaninsa mugayen kalamai inda ya ce” *I hate you* “

Da Sauri Yar Mahaukaciya ta dago idanuwanta wa’inda suka fara canza launi sai hasken mai kama da na magen da ya fara fitowa ta zuba masa su

Hakan ba karamin karayar da shi yayi ba amman sam baya jin zai iya lamuncewa zuciyarsa abinda take so ya ci gaba da fadin” *Yes i hate you, na tsani na hadu da ke, na tsani na zauna tinaninki sanan rashin lafiyata ta dalilinki ne, ke ke din nan dai ke ba zawara ba aman kinfi zawara sanin hanunki dan har kin iya yanda zakiyi ki rikitar da maza, Abdul na sonki, Abdallah na sonki, jama’a da yawa na harin cewar suna sonki , Ni….ya ja nunfashi yaci gaba karyarki ta sha karya a kaina, Ni nafi karfin nace wai ina sonki abin ba dadin ji dan haka ina mai umartar ki da kiyi gagawar tsayar da daya a cikinsu wa’inda suka zubar da girman nasu na aura miki ki kara gaba dan kuwa bana son na ringa cin karo da ke a cikin gidan nan* “

Yar Mahaukaciya dake kalonsa cikin matsanancin faduwar gaba da tarin hawayen dake zuba daga idanuwanta ta ce” *Mai yasa ka tsaneni? Shin wani laifi na aikata?* “

Mubasshir ya kawar da kansa dan kuwa hawayen nan nata ji yake tamkar ya jawota jikinsa ya saka harshen sa ya lashe su sanan ya rukunkumeta dan kar Wanda ya kalan masa ita, yayi gagawar watsar da tinanin ya ce” *kwarai kuwa kina da laifi, kin fi kowa laifi ke laifinki yafi karfin na kawar da kaina kansa dan haka ki kiyayi abinda na fada miki* “

Yar Mahaukaciya ta Mike da kyar ta juya tana tafiya , har ta kusa fita ta juyo ta dawo inda duk takun tafiyarta bugawar zuciyar Mubasshir ne,

Tana dawowa ta tsuguna kanta a kasa ta ce” *shin tsanar da kayi min ta yan’uwantakar ce KO mai?*

Kwarai tambayar ta zo masa a bazata kuma sai a sanan y’a gane ilimi ne da ita , ya kawar da kansa cikin kame kame ya ce” *ai musulmi baya tsanar musulmi banza haka, ina yi miki son yan’uwantaka wanda koda Maman Mubasshir bata yarda da ke ba dalilinki na musulma zan taimaka miki aman banda wanan son ba wani* “

Yar Mahaukaciya ta kuma cewa ” *Son soyaya ne na aure baka yi min?* “

Mubasshir ya gyada kansa da alamar gajiyawa da tambayoyinta

Da mamakinsa sai gani yayi ta saki murmushi ta ce” *Har ka bani tsoro yaya, daman ni? Wacece ni? Ilimin me gare ni? Mahaifiyata Mahaukaciya ni yar bola har nayi tsamanin soyaya daga namiji kamarka? Ta yi dariya irin da mamaki ta ci gaba” ai dan gata sai Yar Gata, i’a zan fadawa Abdallah idan da gaske yake ya fito inji yayana* “

Tana gama fadar haka ta mike tayi waje da gudu da alamar jin kunyar nan ,

Mubashir yayi gagawar rike daidai zuciyarsa yana sakin wata irin ajiyar zuciya tamkar yayi tsere, ya silale nan ya konta yana kalmar shahada domin a yanda zuciyarsa ke bugawa shi yasan kawai lokacinsa ne yayi, yasan kawai shi tashi ta kare domin bai san ciwon *So* ba, ta kafa masa wuka ta barshi da tsiyayar jini a kahon zuciya,

Toh fa AA ai gwara karka bige plz ku tayani da adu’ar kar ya tafi??????????????????????????????????

??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      55

Tana fita d’akinta ta fad’a, ta ja ta rufe ta silale jikin kofar tana mai da numfashi, a hankali ta furta” *Ya Allah , kai kayi talaka kayi mai kud’i, kai kayi mai gata da marar gata, ALLAH da kai na dogara domin kaine gatana, Allah kayi min zab’i ba zabina ba, ALLAH ka zaba mini abinda yafi zama alkhairi a rayuwata, Ya Allah* ” ta rintse idanuwanta hoton Bakin AA na furta mata kalmar *I HATE YOU* tayi Saurin bude idanuwanta ta mik’e tana fadin A’uzubilahi mina shaidanin’rajim ta fada bayi ta sakarwa kanta ruwa

Bayan sallar Magarib Yar Mahaukaciya ta sauko amsa Kiran Hajiya Fadimatu a falo, ta sha Riga da Zani na atamfa ta zaya mayafi ja tayi kyau tamkar Yar Tsana duk da ba wata kwaliya ta zana ba , tana isowa ta tsuguna ta gaishe da Hajiya Fadimatu

Hajiya Fadimatu ta amsa cikin sakin fuska sanan ta ce” Yar Fadimatu ana salama da ke ina jin Abdallah ne

Yar Mahaukaciya ta sine kai ta mike ba tare da ta amsawa Hajiya Fadimatu ba dan wani irin nauyinta da take ji, ta nufi kofa

Tana FITA Hajiya Fadimatu ta sauke ajiyar zuciya a fili ta ce” astaghfrullah ya Allah ka yafe min wanan abin da nayi , Allah ka san abinda ke zuciyata Allah ka shige min gaba, sanan ta kama hanyar dakinta

Tana shiga dakinta ta tarar da Mubasshir yana zaune saman darduma yana Jan carbi , a nitse ta nufi windown dakin ta bude madubin tana lekawa

Mubasshir dake zaune yana hailala yana neman sauki wajen Ubangijin sa yayi fatiya ya juyo yana kalon Mahaifiyarsa ya ce “Maman Mubasshir ina yini? “

Hajiya Fadimatu ta juyo da murmushinta ta ce ” Lafiya lau Dan Fadimatu, kaga Mamarka da tsegumi KO? Ina kalon yata ne “

Mubasshir ya ce “Yarki?”

Hajiya Fadimatu ta ce” yes zance ake kaga yanda ta ja gefe tamkar Wanda take tsoron saurayin”

Mubasshir ya zaro ido bai san sanda ya ce” What? Zance ? Kuma ita da wa?

Hajiya Fadimatu tayi masa kalon lafiyarka? Domin tambayoyin nasa a jere sanan ya mike lokaci guda har mazari jikinsa yake ,

Da Sauri ya juya ya fada bayi yana tari ya kuna pampo ya sha ruwa da kyar tarin ya sake shi ya juyo ya fito, yana fitowa ya tarar da Hajiya Fadimatu tsaye hankalinta tashe ta ce” Son jikin ne?”

AA ya girgiza kansa da yake Sara masa ya nufi bed ya konta yana rinrintse ido

Hajiya Fadimatu ta bi bayansa ta dafa shi ta ce” KO mu tafi asibitin ne? “

Mubasshir ya girgiza kai sanan da kyar ya ce” maman Mubasshir ba komai karki damu”

Zata yi magana taji ana konkwasa dakin ta taso ta bude a tinaninta Yar Mahaukaciya ce sai ta ga Hajiya Hawau

Murmushi ta saki tana fadin” Hajiya barka da warhaka , sanan ta bata guri ta shige cikin dakin

Hajiya Hawau ta kali Hajiya Fadimatu ta ce” Hajiya da wa yar tawa ke zance ? KO dai shine sirikin namu?

Hajiya Fadimatu ta ce” shine kina gani sai wani kawar da kai take,” ta karashe tana kokarin kawar da fuskarta gefe dan kar ya dagota

Hajiya Hawau ta ce” ai kuwa idan ya shirya ai sai ya fito kawai ayi da shi”

Mubasshir dake sauraron zancen su a ransa ya ce” tazo ganina ne KO tazo ta karasa ni, ? A fili kuwa da kyar ya samu ya tashi ya juyo yana kalon su ya ce” Barka da zuwa Hajaju”

Hajiya Hawau ta karasa tayi tamkar yanzu ta Ganshi ta ce” Dan Aljannah ya jikin?

Mubasshir ya ce” Jiki yayi sauki Alhamdulilah, daman ina son zuwa wajen ki sai gaki kin zo”

Hajiya Hawau ta gyara zama ta ce” toh bani na sha”

Ya dan furzar da iskar bakinsa cikin kawar da kai ya ce” *Abdul ya sameni kan zancen nazo na sameki ki fadan inda Rahma take yana son aurenta , plz ki taimaka ki fada masa na yarda da son da yake mata* “

Hajiya Hawau ta kali Hajiya Fadimatu itama ta kale ta irin kalon aikin banza din nan sanan ta ce” *Ai yata anyi mata miji sai dai kuyi hakuri* “

Irin kwaruwar ta dazu ya kuma yi wanan Karin yama kasa tashi balatana ya shiga bayin ya samu sasaucin kwaruwar da yayi ta hanyar shan ruwa,

Wasa wasa tari ya tirnike shi tun yana rike daidai zuciyarsa har ya saka yana kokarin faduwa,

Da gudu Hajiya Hawau tayi bayi ta dibo ruwa inda Hajiya Fadimatu ta zauna tana rike da shi suka bashi ruwan ya sha, suka kuma bashi ya sha yana ta ajiyar zuciya

Hajiya Fadimatu ta dora kansa saman cinyarta tana shafa bayansa a hankali ta kali Hajiya Hawau da ido tayi mata maganar da su kadai suka gane abinda suke nufi sanan cikin muryar nutsuwa da kontarwa mai sauraro hankali ta ce” *Ya zakayi kokarin boyewa Wanda ta dauki cikinka ta raine ka ta shayar da kai ta juri rigimarka ta ga girman ka damuwarka? Ya zakayi kokarin yin gardama da abinda na hango a kwayar idanuwanka? Shin ka manta alkawarin mu na bazaka boye min sirinka ba?* “

Mubasshir cikin Mutuwar jiki ya dago da kansa daga cinyar Hajiya Fadimatu gabansa na ci gaba da faduwa a ransa ya ce” Kardai Maman Mubasshir ta rigayi Mubasshir sanin abinda ke zuciyarsa? Kar dai Maman Mubasshir ta gane cewar Mubasshir ya kamu da son Yar Gidan Fadimatu? Son da yake kokarin zautar da shi? Kaunar da tayi masa shigar bazata?

Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta kawar da kanta ta ce” *Idanuwanka sun nuna tsantsar tsoro da fargabar abinda na karanta a tare da kai* “

Ta Juyo ta kama kafadunsa ta ce ” *YA KAKE KOKARIN KASHE KANKA KAN HALALIN KA , IYALINKA, MATARKA? SHE IS UR WIFE MUBASSHIR* “

wani irin dum dum dum maganar ke yiwa Mubasshir a kunansa , wasu tambayoyi ya juyo yayi min Wanda nima nace AO??‍♀

Tambaya yake shin Maman Mubasshir ta kuwa san sunan wa ta kama tace matarsa? Shin ta gane KO wanene a gabanta? Idan ta gane yaushe aka aura masa ita? Yaya zai yi da Abdul amininsa? Yaya zaiyi da ita kanta Rahmar?????????????????????????????????muje zuwa ?

??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      56

adu’ar samun sasaucin kunci da tashin hankali

*ALLAHUMA, LA SAHLA ILLAMA JA’ALTAHU SAHLAN, WA’ANTA TAJ’ANUL HAZNA, IZA SHI’ITA SAHLA*

Hajiya Hawau ya tsurawa ido yaga itama shi take kalo, ya juyo ya kali mahaifiyarsa a fuskarta ya karanci sam ba wasa a cikin bayanin ta, 

Wani lalatacen murmushi ya saka yana dan juya kai cikin muryar tausayi ya ce” Eyah maman Mubasshir ba fa ni nake nufi ba, ina nufin *ABDUL* yayan Sahla ne ke son Rahma fa, “

Hajiya Fadimatu ta ce” look son, Rahma matarka ce, taya zakana hada ta da wani kuma? “

Cikin wani yanayi ya juyo ya kale su ya ce” *ku yiwa Allah ku dena hada maganar nan cos ni kunuwana suna jiyo mini wani abin daban, Wanda kuma yake impossible, Rahma dake kofa tsaye tana zance da wani saurayin, gardi, Rahamar da aminina abokina yake matukar so, sai kuma kunuwana su rinka jiyo mini cewar matata ce? Ni ?* “

Hajiya Fadimatu ta mike cikin kakausar murya ta ce” *akoy wasa tsakanin uwa d’a da , sannan akoy zancen gaskiya, Ni Mahaifiyarka ni na samu alwalinka a matsayina na mahaifiyarka da kuma Hajiya Wace ta zamto sheda kuma ta bada amanarta muka yanke wanan hukuncin, ranar juma’a ya daura aurenka da shaidu a gidansa na nan, idan kana musu kayi Kiran sa, idan kuma baka yarda da hukuncina ba to ka watsa min kasa a ido* ” ta karasa cikin yanayin bacin rai, dan a ganinta Mubasshir yama raina ta ne yana so yana basarwa

Mubasshir jikinsa yayi sanyi jin furucin mahaifiyarsa da yanayin bacin rai a tatare da ita duk dan shi, da Sauri ya karasa ya tsugunna kasa gabansa na faduwa ya kama kafafuwanta ya ce” Maman Mubasshir kiyi hakuri please, ba ina nufin ban yarda da maganarki bane, KO ban yarda da zabinki ba, no abin ne ya zo min a bazata, Dan Allah kiyi hakuri”

Hajiya Fadimatu ta sauke ajiyar zuciya ta kali Hajiya Hawau dake murmushin jin dadi, a nitse ta kamo shi ta dago shi suka koma bakin gadon , cikin nutsuwa ta ce” Dan Fadimatu, zaka yi min biyaya ka rike min yata tsakaninka da Allah?? “

A ransa ya ce  tamkar yanda zan rike raina da mahinmanci , a fili kuwa yayi murmushi ya ce” Maman Mubasshir koda aljana ce kika aura min dole nayi biyaya ba zancen musu ” ( ehem ) ya ce GABA da fadin ” damuwata biyu ce Maman Mubasshir, Abokina da kuma ita yar taki”

Hajiya Hawau ta dafa kafadarsa ta ce” abokinka ba yanda ya iya domin matar mutun kabarinsa, sanan inada kwakwaran dalili na yin hakan, dan haka kayi fatan alkhairi kawai, “

Hajiya Fadimatu ta dora da ” to aman mai yasa kace da y’a ta?”

Mubasshir ya dan kawar da kai yayi kokarin kauda kishinsa sanan ya ce” kinga hanzu ma fa da igiyar aurena tana zance Maman Mubasshir , kuma kina kalo kika barta “

Hajiya Fadimatu da murmushi ta ce ” Gidan ku , ta je tayi zancen”

Hajiya Hawau ta ce” aa Hajiya baza’ayi haka ba , an soke zancen”

Mubasshir ya sauke ajiyar zuciya a nitse ya Mike ya nufi bayi ya kuna ruwa ya wanke fuskarsa ya dago kansa yana kalon miror, wani murmushi ya subuce masa a saman lebensa a hankali ya furta ” *Matata ce* , ya lumshe ido yana kalon kasa , sanan ya kashe pampo ya fito a ransa yana fadin “wly idan bata shigo ba zan je na dawo da ita dan kuwa ba zai yiwu ba “

Yana fitowa ya tarar basa dakin, ya sauke ajiyar zuciya sai a lokacin ya samu ya nufi window ya bude yana ta hangawa,  ajiyar zuciya ya sauke ganin basa nan, ya juyo a nitse ya tada Salah saman salaya dan ya kara godewa ubangijin sa da wanan kyautar da yayi masa ba tare da wayon sa KO tashin hankalin sa ba,

Tana shigowa ta tarar da su Hajiya Hawau zaune , direct jikin Hajiya Hawaun ta je ta lafe tana dora kanta a saman cinyarta

Hajiya Fadimatu ta ce” Yar Fadimatu bakon ya tafi?”

Yar Mahaukaciya ta dan sine kanta irin jin kunyar nan bata ce komai ba ,

Hajiya Hawau ta shafa kanta cikin nutsuwa ta ce” Yar Gidana muna son yin magana da ke” ,

Yar Mahaukaciya ta dago gabanta na faduwa , badan komai ba sai dan tsoron kar ace ta koma gidan su Abdul, don kuwa KO da anyiwa Sahla aure mahaifiyarta na nan shi ma Abdul din yanzu tsoronsa take ………….

Hajiya Fadimatu ta gyara zama ta ce”””””””””,,,,,,,,,,,,,”””””””””””

[truncated by WhatsApp]

??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                      57

Hajiya Fadimatu ta gyara zama tayi gyaran murya ta ce” Yar Fadimatu shin na isa na sakaki abu kiyi , KO na hana ki ki guji yinsa?”

Yar Magaukaciya ta yi gaggawar daga kanta jikinta na rawa dan haka kawai ta tsinci faduwar gaba a tatare da ita ,

Hajiya Fadimatu ta kawar da kanta domin sai yanzu wani nauyin tunkarar Rahma da zancen nan ya darsu a zuciyarta , ta kuma juyowa daidai Lokacin da Mubasshir ke saukowa ya canza kayan jikinsa sai zuba kanshi yake ya fesa tiraren Hajiya Fadimatu , ja yayi ya dakata yana kalon su , shi kansa a yanzu gabansa faduwa yake bai san dalili ba ( zaka sani )

Hajiya Hawau ta ci  gaba da fadin ” shin kin dauke mu a matsayin iyaye? Wa’inda suka isa da ke , wa’inda zasu iya yanke hukunci dan inganta rayuwar ki? Wa’inda zasu guji ganin kin halaka sai inda karfin su ya kare? Shin a yau idan muka zo miki da wani hukunci da muka yanke a kanki zaki yarda da shi? “

Zuwa wanan lokacin Yar Mahaukaciya ta gama jika da gumi, domin KO ba komai ta san wanan zancen mai matukar mahinmanci ne, tabas wanan zancen mai mahinmanci ne tana rokon Allah ya sa alkhairi ne, idanuwanta ta dago wa’inda suka kara girma na tashin hankalin da ta shiga ta sauke su a fuskokin su hajiya , wani irin kwarjinin su ya daki kwayar idanuwanta da Sauri ta sada kanta kasa cikin gargadar murya ta ce” Mamana,  hajiyata, iyayena, kun yanke hukunci a kaina shine kuma kuke yi min shawara? Wacece ni? No a duniya banda mahaifiyata sai ku gareni , kun isa da ni , Ko mai kuka yanke a kaina ni na san alkhairi na ne dan haka bani da musu KO ja da maganar ku”

Wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyoyin su, kaunarta da Karin ganin darajarta da kunyarta suka darsu a zuciyoyin nan uku,

Hajiya Fadimatu ta sauke ajiyar zuciya da ido ta yiwa Hajiya Hawau nuni da ta fadawa Yar Mahaukaciya abinda suka yi ,

Hajiya Hawau ta kara gyara zama ta ce” *Daman ranar juma’ar can da ta shige aka daura miki aure ke da Dan Aljannah* “

Bugawar zuciyar Yar Mahaukaciya daidai da kiftawar idanuwanta, domin kwatakwata idanuwan ta kasa tsayar da su sai kikifta su take, jikinta gaba daya rawa yake, kafafuwanta dake tankwashe ta samu ta hau saman su ta yi tamkar zaman rakumi a hankali cikin rawar jiki ta dauko hanunta guda ta tokare habarta , hawaye wani na bin wani

Jikin Hajiya Fadimatu yayi sanyi, ta taso a nitse ta kamo Yar Mahaukaciya ta dora kanta a saman cinyar ta tana shafawa tana gyara mata gashin kanta da shi kansa ya jike wajen hudodin, har a lokacin jikinta rawa yake sanan bata furta komai ba,

Ta kai minti goma a haka , zuwa wanan lokacin shi kansa ji yake kafarsa ta kasa daukar sa, a hankali ya cire hular kansa ya jinginu da jikin abin hawa benen, ya dora hanunsa na dama daidai zuciyarsa yana irga bugawarta ,

Can kamar an tsikare ta ta zabura ta sauko kasa ta hada hanayenta biyu kamar ta zo neman gafara ta ce” *Mamana ki yi min rai, kar ki saka ya kore ni daga inuwarki, shi ya fada min da bakinsa cewar na fitar da miji cikin satin nan ya aurar da ni ya huta da gani na, yanzu idan ya ji cewar an aura masa ni ai har ya hadiyi zuciya ya mutu daman ba lafiya gare shi ba , dan Allah dan Annabi a kashe auren nan tun kafin ya ji ya kore ni mama Dan Allah, kinga sai Abdallahn yayi ya fito daman yanzu ya gama fadar hakan* ” ta karashe zancen tana rushewa da kuka , ta mike da gudu ta nufi hanyar dakinta

Daidai zata hau ta ganshi nan tsaye gabanta ya yanke ya fadi ganin irin yanda yake da kyau haka gashi da alama fuskar sa tamkar ransa a bace, gabanta ya kuma yankewa ya fadi , a ranta ta furta *wutsiyar rakumi tayi kadan ta taba kasa*

Shi ma gabansa ya yanke ya fadi domin idanuwansa sai suka hango masa tsanarsa a kwayar idon Yar Mahaukaciya, nan take kalmar *I HATE YOU* da ya furta mata nan da yan awanni suka dawo masa , ya bi bayanta da kalo har ta shige dakin ta rufo

Hajiya Fadimatu ta mike da niyar bin bayan yarinyarta , Hajiya Hawau ta dakatar da ita ta ce” kar ki bita a yanzu, ki barta ta gama shawara da zuciyarta , “

Hajiya Fadimatu ta koma ta zauna jiki bâ kwari ta ce” tabas idan Yar Fadimatu ta ce bata son Dan Fadimatu zan raba auren nan , dan kuwa bazai yiwu ni da kaina na aurawa yar Amana abinda bata so,

Muryar Mubasshir suka tsinta yana fadin” *NO MAMAN MUBASSHIR BAZA’A RABA AUREN DA BA’A TARE SHI BA MA , BA KYAU* “

Hajiya Hawau da Hajiya Fadimatu suka zuba masa ido irin yanda jijiyoyin hannun sa suka mimike,

Hajiya Hawau ta kawar da kanta tana kokarin danne dariyarta dan kuwa da ka kali fuskar Mubasshir zaka karanto tsantsar tsoron kada a raba shi da abinda yake matukar so, ta kali Hajiya Fadimatu ta ce” *wanan aure mun hada shi ne da niya mai kyau, sanan shi aure raine da shi, kuma wanan karamin dalili ba zai saka mu raba auren nan ba saï da kwakwaran dalili, Rahma na cikin tsoro ne da fargabar yanda Dan Aljannah zai karbi maganar, bayan shi ban karanci tsanarsa a kalamanta ba, ki barsu su sasanta kansu ya nemi soyayar matarsa da kansa ki zira ido hakan shi zai kawo alkhairi ba wai a raba auren ba* “

Mubasshir ya gyada kai uwa shi ake fadawa ya ce ” yawa Hajiya , ai shi kansa sakin ba kyau ana yinsa”

Hajiya Fadimatu ta zabga masa harara ta ce” ai Dole ka fadi haka bayan ka gama fada mata tayi ta fitar da miji kai ka gaji da ganinta KO?  Kai ga dadynta, to sai kayi kokarin fahimtar da ita kaine mijin idan ba haka ba kuwa ,i’m sorry sai dai ka sakar min y’a “

Tana gama fadar haka ta Mike ta nufi kicin dan samawa Hajiya Hawau wani abin Marar nauyi ta ci…

Da ido suka bita sanan a tatare suka sauke ajiyar zuciya , Mubasshir ya kali Hajiya Hawau ya ce””””””””__,,,,,,,””””””””””””””””,,,,_______”””””””””””””

??BELLES écrivaines Nigériennes

‘YAR ??

MAHAUKACIYA? na

   

                    58

*Tabas soyaya ita ke sakawa a damu da mutun idan an ga shiru, idan na ce zan tsaya zano ku wly sai mu cika page din bamu gama bâ, Alhamdulilah Allah na gode da ka bani ikon rubutu tabas alkhairin rubutu shi na samu ba sharin sa ba, sisters godiya marar addadi , tsakanina da ku sai fatan alkhairi, daga taku yar Mutan Niger*

Mubasshir ya zubawa Hajiya Hawau ido , yana matukar son ya kara fada mata kar ta yarda Maman sa ta raba auren sa , aman ina ai da kunya KO ba komai kakar Sahla ce, Dole ya ji kunyar wani abin, Hakan ya sa ya Mike yana kokkarin FITA daga dakin dan bai ga ana marhabun da shi a cikin gidan ba

Cikin murmushi irin nasu na Manya ta ce” dawo ka zauna Dan aljannah,”

Mubasdhir ya juyo yana tafiya kansa a kassa ya dosanu ya zauna stil yana kalon kassa

Cikin nutsuwa ta ce” ni na jajirce da taimakon ubangiji aka daura maka aure da Marainiyar Allah,

Cikin firgicci ya dago yana kalon ta,

Hajiya Hawau ta ci gaba” kwarai kuwa , abinda ya saka ni aikata hakan dan ina tsoron aurawa wani yarinyar amanna ya cutar min da ita, tabas na san bazawarra ce aman idan kayi hakuri ta fi budurwar dadin zama ,”

Mubasshir ya kuma dagowa ya kara kalon ta a ransa ya ce ” Ai fa ni ba dadin zamanta nake so ba, dan kuwa na sani Sahla ta FITA dan ta FITA kama kai,duk da haka ga yanda na same ta ballatana Wace ta waye a harkar? Ni kawai hutu na aura sai kuma ina dan tausaya mata, 

Hajiya Hawau ta ce” ka bani amsa, shin zaka iya kular min da yarinyata? “

Mubasshir ya danyi murmushi ya ce ” ai KO da ban sanki ba girman ki ya isa na girmama abinda kika hango ballatana na yarda da zabin ki, insha Allah zan yi kokarin adalci a tsakaninsu

Hajiya Hawau ta amsa sa cikin farin cikin girmamata da darajata da Dan Aljannah yayi

Bayan ta salamce salar walahar ta ta juyo a nitse ta karasa inda Gajiya Fadimatu ke zaune da abinci a cikin assiete tana jiran ta gama sallar, tsugunnawa tayi har kassa fuskarta da dan murmushi ta ce” Mamana ina kwana, an tashi lafiya? “

Wani sanyin dadi ne ya ratsa zuciyar Hajiya Fadimatu ta ajiye plat din abincin ta kamo Yar Mahaukaciya ta zaunar da ita saman bed din tana kalon ta, can ta ce” jiya kinyi baci baki ci abinci ba Yar Fadimatu,”

Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta ce” kawai sai da na farka na ganni ina baci kuma sai tsoro ya Hanna ni FITA na debo abinci, “

Hajiya Fadimatu ta ce” Tsoron mai?”

Yar Mahaukaciya tayi gagawar dukar da kanta ta ce ” ba komai mama”

Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta dago habar Yar Mahaukaciya ta ce” idan na ga auren nan cutuwa ne a gare ki believe me ba inda zai  da izinin Allah, sanan a yanzu haka idan kika kafe kan bakya so zai sawake miki duk da shi din yana so”

Yar Mahaukaciya ta zaro idannuwanta bata san sanda ta ce ” Yana so?

Hajiya Fadimatu ta ce ” Yes,  yana so”

Yar Mahaukaciya ta dan sadda kanta da matsanaiciyar kunya tana tir da wanan baki nata, a zuciyarta kuwa tasan wacece ita harda AA Mubasshir zai so auren ta? (Haka)

Mikewa Hajiya Fadimatu tayi ta bude werdrob din Yar Mahaukaciya ta ciro wata doguwar riga ta atamfa, rigar taji dinki daga sama ta matse sai ta bude daga kasa, da dan tsaga tsaga a sama daidai kirjin rigar sannan zub din bai hau har sama ba, hanun rigar daya dogo ne daya gajere , jar atamfa ce mai ratsin baki baki kalar fararen fata ???‍♀,

Ta mikowa Yar Mahaukaciya dake zaune sannan ta ciro mata dan kwalin rigar ta miko mata ta ce” tashi Yar Fadimatu ki shirya mu tafi amsar kaya na nadiya nan makota,”

Yar Mahaukaciya ta dago atamfar, dinki ya hadu iya haduwa sai dai kunyar dinki ta saka ta kasa sakawa, sai dai a yanzu bazata taba iya musantawa Hajiya Fadimatu ba , Hakan ya sa ta dauka ta nufi gaban mirror dan ta dan gyara fuskar ta dan Hajiya bata son ta FITA bata saka kwali ba ,

Zama tayi ta yi dan adonta iya lips dinta da idanuwanta ta Mike ta dauki bras dinta ta saka ta saka pant dinta sannan ta dauko rigar har wani kara karan zub din take dan KO tafiya kake zub din na motsi suna Jan hankalin mutun, , cikin nutsuwa ta saka ta ja zub din sannan ta dauko dan abin hannunta baki siriri ta saka , ta dauko dan kwalinta zata daura Hajiya Fadimatu ta shigo tana fadin ” Yar Fadimatu ki fito sai su dauko miki wa’inan bol din , hajiya Karima ce ta ce a zo mata da su saboda wajen mijin Nadiya gidan sarauta ne ita kuwa bata tanadi wanan ba , dan haka bara nayi gaba sai ki biyo ni da sauran

Yar Mahaukaciya ta ce ” To mamana , ki bata kar ta manta”

Hajiya Fadimatu  ta ajiye ta karbi bakin ribom din ta tatara gashin kan Yar Mahaukaciya ta hade waje guda ta saka mata ribom din sai gaba daya ya zubo ya rufe mata wajen da rigar bata rufe ba daga baya sanan ta dauko bololin ta nufi hanyar gidan Hajiya Karima makociyar su,

Bayan ta gama shiryawa ta dauko tirarukan dake saman table din dakin ta yiwa jikinta barin sa ta bude wajen takalman ta ta dauko wani plat mai igiya baki ta daura a kafafuwanta sannan ta fito cikin nutsuwa da mayafinta baki mai shara shara irin mai dan duwatsun nan tamkar sange ,

Cikin nutsuwa ta sauko direct ta nufi kicin tana kwalawa ma’aikatan gidan kira dan ta ga an fitar da kayan ita kawai suke jira

Da ido ya bita sauran kadan ya kware , yana waya da Sahla tana ta magiyar ya amsata yayi mata shiru , cikin sarkewar murya ya ce” Sahla ina zuwa ,”

Kafin ta bashi amsa ya katse Kiran ta kali mahaifiyarta dake zaune tana sauraron labarin nasu ta ce ” Mama kinji fa ya kashe, ni gaskiya sai na kara kwana biyu na kara hutawa dan wly so yake ya kashe ni sam bai san gajiya ba a rayuwarsa “

Hajiya Marhaba ta ce ” ai shiyasa na amso miki magungunan nan sai kiyi ta anfani da su yanzu haka Wanda kika matsan nan kinga dubu hamsin na siyo shi dan karfi ne da shi, sai dai yayi ya gama har ya gaji ba dai ke ki gaji da shi ba “

Sahla ta dan yatsina fuska dan tunda ta matsa maganin nan cikinta ke yi mata wani irin ciwo kokari ne dai kawai take dan Mahaifiyarta ta fada mata anfannin maganin yawa ne da shi , ita fa a gaskiya a yanzu tsoron mazan ma take tun karfinta cause Mubasshir tamkar machine yake shi dai burinsa ya ji sa a birnin nan Wanda jirgin sa mai wuyar sauka ne (?). ” tayi kwafa kasa kasa ta ce” Ashe dai ana gajiya da ita”

Fitowa ta kuma yi da wata Babar leda a hanunta tana kokarin gyara rikonta kwalabe ne a ciki na shan ruwa masu nauyin tsiya ga tsada ga kyau , sam bata lura da mutun a falon ba tana juyowa ta gamshi zaune yana kalonta , gabanta yayi wani mugun faduwa bata san lokacin da ta saki ledar ta fada mata a kafa ba ,

Ido suka rintse a tare dan kuwa yanda ta ji azabar faduwar wanan kofofin haka ya ji a jikin sa , , wani ihu ta saki na azaba da firgici domin ta firgita kwarai da ganin ba zatan da tayi masa a falo ga kuma faduwar wanan abubuwa masu masifar nauyi murafen su masu dan kaifi har daya ya yanke ta, wani wahalalan kuka ta saki gaba daya jikinta na rawa ..

Mikewa yayi cikin zafin nama ya isa wajen ta , yayi gagawar janye ledar ya cire Wanda ya dan yankun mata , yanda jikinta ke rawa haka NASA ke yi, cikin dauriya ya Mika hanu ya daukota cimak ya nufi Babar kujerar dake tsakar falon ya shinfida ta , sai wani kakauda kai yake

Wayarsa ya janyo yayi Kiran Umairah docter matar général kadre makociyarsu dan yanda take karkarwa sai yake jin tamkar wani abin ne ya shige mata kafar,

Minti sha biyar tsakani sai gata ta shigo ta karaso tana fadin “Oh yar gidan momynta ce ba lafiya? Oya cuta baki yi mana adalci ba “

Mubasshir ya dan Mike yana fada mata ga abinda ya faru,

Umairah tayi murmushi ta kama kafar ta Yar Mahaukaciya tana dubawa ba karaya ba gocewa , jin ciwon nan dai ne , hakan ya sa ta dauko compress ta goge mata da alcool ta rubuta mata amoxi ta mikawa AA sanan ta juya ta tafi ,

Mikewa tayi a hankali tana dan rintse idanuwanta ta mika hannu zata kuma daukar ledar ta je ta kaiwa Hajiya Fadimatu ,

Mubasshir ya zubawa kirjinta ido ta tsagogin dinkin nan, gabansa ya fadi yayi gagawar hadiyar wani yawu mai wuya , ya kuma zubawa dogon wuyanta da bayanta ido ba shiri ya kawar da kansa tun kafin ya bada kansa, cikin muryar tasa ta yana hanu ya ce” ina zaki je?”

Gaban Yar mahaukaciya ya Fadi ta dago tana kalonsa cikin gargadar murya ta ce” am daman mamana ce ta ce na kai mata wa’inan wajen amsan kayan Nadiya”

Ya juyo yayi mata kalon kinyi kadan ki fita sanan ya mike a nutse ya nufo ta,

Takunsa take ji sai ji tayi ya kure mata waje, a hankali ya Mika hanunsa daya ya dan rankwafa daidai wuyanta har lumfashin sa na sauka a saman wuyan ta ya kama zub dinta ya …….  ……………………. ……………. ……..(?? oh my Hawee kinyi shiru ki ji yayi mai da zub din KO? Har kin diro, to alhana bazan fada ba ?????????)

??BELLES écrivaines Nigériennes

? YAR MAHAUKACIYA? na SAJIDA

   

                    59

Lumfashinsa na sauka a saman wuyan ta, da gangan ya kara jawota kadan hakan ya Sakata jin bugawar zuciyarsa da Sauri da Sauri, Zip din ya kama da niyar ya ja shi ya rufe sauran wajen da bai rufe bayanta ba , hakan ya baiwa hancinsa damar sauke numfashinsa a kunnanta ,

Jin wanan bakon al’amarin ya saka jikin Yar Mahaukaciya mutuwa, gaba daya jikinta ya saka ta furta ” *Wayo Allahna* ” tayi luuuu zata fadi

Cikin mutuwar jikin shima ya tarota suka fada saman Babar kujerar, da Sauri ya mike yana kakabe jikinsa ya dan gyara tsayuwarsa ya saita muryarsa ya ce ” Kai Bariki, idan mutun ya saba da abu hakane, na tabo miki wajen dake miki kaikayi KO? Yayi kwafa ya dan duko cikin rada rada ya ce ” i’m sorry da na katse miki jin dadin ki dan ba kyau bin maza a waje may be ni kadai zan iya gamsar da ke , aman da alama sai nayi da gaske dan kin fiya zalama” yana gama fadar haka ya juya yana taka mattatakalar dakin ya nufi dakin mahaifiyarsa

Da kalo ta bi bayan sa har ya shige, nanauyar ajiyar zuciya ta sauke , tabas da da ne bazata damu da maganganunsa ba , a lokacin da idan ya yi su ma bata san inda suka dosa ba , sanan da a shekaran jiya ne ma ba zasu wani mugun damun ta ba cos ba’a fada mata cewar miji yake a gareta ba , aman a yau sai ta ji ba dadi, gaba daya sai ta ji ta muzanta, shin ina laifinta dan ta wayi gari ta tsinci kanta a bola? Menene laifinta dan ta rayu a cikin bola? Ta rintse ido a fili ta furta ” *Shin mijina yana yi min kalon fasika ne?* ,

Lami dake tsugune tana maganna ta ce” na’am hajiya?

Yar Mahaukaciya tayi gagawar kallon ta , sannan ta ce” Au Lami kin fito?, kinga bara na saka hijab dina mu tafi mu kaiwa mamana nassan tana ta jira”

Lami ta ce” Ai hajiya Elhaj ya ce a fada miki karki fita, mu mu tafi mu kai kayan”

Yar Mahaukaciya ta ji zancen wani iri ta dago ta ce” Elhajin ne ya fadi haka?”

Lami ta amsata cikin biyaya

Yar Mahaukaciya ta ce ” ohk tohm ki dauka ku kai mata , aman kar ku ce shi ya hana ni zuwa kunji? “

Lami ta ce” to Hajiyata a huta lafiya” suka dauki kayan suka tafi abinsu

Birgima take tana ihun cikinta , fitowa tayi daga bayi ta nufota da Sauri tana fadin Sahla ke kam akoy ragwonci , matsin maganin matan ne kike yiwa wanan ihun? To da a gabansa ne sai ya san abinda kika matsa KO? “

Sahla dake rusar kuka ta cusa hannunta kasanta ta shafo lemar da take ji na binta ta dagowa Hajiya Marhaba dan kuwa bakinta ya kasa magana bale har ta furta kalmar jinnin dake binta

Idannuwa Hajiya Marhaba ta zaro sannan ta juya da gudu tana ihun a zo a taimake ta dan ta kai Sahla Asibiti. ,

Bayan kamar awa uku likitici biyu maza suka fito da nurses sun hada gumi sosai , Hajiya Marhaba ta mike tana karkarwa ta nufe su ta ce” Ya jikin y’a ta docter?

Docter Aliyu yayi gagawar fadin ki biyo ni office dina , yayi gaba inda docter Usman ya bishi da kalo yana jin haushin wanan halaya na docter Aliyu Wanda a da bai san shi da  su ba ,

Suna shiga ya ja kujera ya zauna inda Hajiya Marhaba ma ta nemi waje ta zauna tana sauraron sa cikin bugawar zuciya ,

Docter Aliyu ya ce” wa ya zubar mata? “

Hajiya Marhaba ta dago tana kalonsa da alamar tambaya ta ce” ban gane inda ka dosa bâ?”

Docter Aliyu yayi murmushin rainin hankali ya ce” cikin jikinta wa ya zubar mata?”

Hajiya Marhaba ta zabura tana dafe kirjinta ta ce ” ci…..ciki????? Inalilahi wa’ina ilaihi raj’une, ciki ne da Sahla ? Kuma ya zube?”

Gaba daya cikin firgici take da tashin hankali dan KO an fada mata ba zata yarda cewar Sahla har ta dauko ciki ba , abinda suke nema tamkar ransu gashi sun samu kuma sun barar da shi garin a kara mata kokarin juriyar yawan sha’awar sa , wannan ai shine kaga samu ka ga rashi, ta kuma rushewa da kuka

Docter Aliyu yayi zuru yana son sanin kukan na mainene , can ya nisa ya ce ” tana da aure ne?”

Hajiya Marhaba cikin share Hawaye ta ce” da aurenta mana”

Docter Aliyu cikin jin haushin Kenan ba zai samu kudin da ya hango ba zai samu ba ya ce” Toh dole sai mijinta ya zo wajen nan dan kuwa cikin mun gano cewar matsa wani abin ne akayi dan a zubar da shi, dan haka sai ya zo KO an kawo mana takardun da likita ya saka ayi hakan saboda lafiyarta”

Hajiya Marhaba ta zaro ido ta ce” uban mai mijinta zai yi a nan? Tap KO daya ai KO mai za’ayi ayi shi iya nan docter”

Docter Aliyu ya zuba mata ido shi daman da ganinta ya san ba gaskiya a al’amuran ta shi ya sa ya gano ci a tare da ita hakan ya sa ya gabatar mata da uzurin sa inda Hajiya Marhaba cikin karkarwar jiki ta biya masa muradinsa ta baro offishin sa cike da jin haushin kanta na asarorin da suka sameta a dan kankanin lokutan nan ( wannan Kenan)

Cikin bacinta take jiyo waya na ringin ta Mika hanu ta kashe kafin ta maida hannunta ta kuma kwasan kuka hakan ya sa ta Mike tana murza idannuwanta ta nufi kofa dan bude kofar shigowar,

Tana budewa idannuwanta suka sauka kan fuskar mutanen dake Dana cl din shigowa falon nasu , kirjinta ta dafe ta kurma ihu daidai da daukewar nunfashinta tayi baya yim ta fadi kass inda suka nufota cikin kidima da tashin hankali……………..”’

Shin su wa Yar Mahaukaciya ta gani????????????????????????????????

??BELLES écrivaines Nigériennes

? YAR MAHAUKACIYA? na SAJIDA

   

                    60

Ture turen juna suke wajen kokarin karasawa inda Yar Mahaukaciya ke yashe kasa, da sauri ya rigayeta ya kai hannayensa dake karkarwa tamkar mazari , dagota yayi ya rungume a jikinsa inda ita kuwa ta shiga kwala Kiran a taimaka musu

Da bibiyu uku’uku yake tako matatakalar yana saukowa shi da Mahaifiyarsa dan daga jin wannan hayaniyar ba ta lafiya ba ce,

Hajiya Fadimatu ta ja turus tana kalon abin mamaki namiji ne zaune yana rusar kuka kashirban tamkar an aiko masa mutuwar mahaifiyarsa rungume da Yar Mahaukaciya, gefe ta waiga inda ta ga *Hajiya Hafsat* mai harkokin gyaran dakin amare Wace zata gyara na Yar Fadimatu, da alama ba a cikin hayacinta take ba ,

Cikin kidima ta ce” lafiya? Mai ya samu yarinyata? Waye wannan kuma?”

Sai a lokacin AA ya kali mutumin da kyau, wanan kafar ai kafar Rahmarsa ce, matarsa, amaryarsa, mai Jan ragamar bugun zuciyarsa, konce a jikin wani namijin ya daga bakinta yana kokarin fara busa mata iskar bakinsa dan ta farfado daga sumar da tayi, cikin karaji ya ce ” Karka yarda ka hadda bakinka da gonata”

Mutumin nan ya dago kansa, a tare gabansu ya fadi AA ya nuna shi da yatsa ya ce” *Da,….daddddddy? Mai mai ya hada ka da matata har kake kokarin hade bakin ka da nata? Who are u a wajen ta har da ka samu damar da ban samu ba?*”

Hajiya Fadimatu zuwa lokacin ta gama kidimewa dan hango kwayar idannuwan wannan bawan Allah da yaronta yayi kira da sunan Dady, kwayar idanuwansa da kalar farin sa tamkar na Rahma ne , duk yanda aka yi wannan sun hada jini da ita, cikin wata murya mai nuna gajiyawarta da wannan al’amarin ta ce” ku saurara min haka plz”

AA ya juyo cikin jin Haushi idanuwansa tamkar gauta , wai mutumin da yake matukar girmamawa shine yau yake kokarin hade bakin sa da na Matarsa, shi a tunaninsa nasarun nan masu gaskiya basu iya cutar da nasu iyalan ta hanyar bin wasu matan a waje, lale barikin Rahma yayi nisa har ta kai ta bi wanan baban biloniyan? Mutumin da ya girme mata nesa ba kusa ba , a yau yayi tir da ranar da ya san shi , har ya yarda suka hada kudi wajen gina Babar makarantar da duk Lagos babu irinta, da karfi ya kaiwa table din tsakar dakin naushi, cikin gursheken kuka ya juyo yana kalon Yar Mahaukaciya da aka yayafawa ruwa ta ja ajiyar zuciya ta bude idannuwanta da salati a bakinta ta mirgina zata tashi aman ta kasa hakan ya sa ta saki wani malalacin kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro

AA ya rintse idannuwansa yana jin karar kukanta tamkar ana kyasta masa reza a zuciya cikin wata murya mai nuna faduwar jarumin namiji ya tsare Yar Mahaukaciya da ido gabansa na faduwa dan gudun amsar da zata bashi ya ce” *Mai yasa kike kukan nan bayan ni ya dace nayi?, shin baki fahimci cewar ni aka cuta ba ke ba?, shin kina kukan katangar karfen da aka saka tsakaninki da wannan bawan Allah?, tsoron rayuwarki kike ba shi?,*   Yar Mahaukaciya ta rintse idannuwanta dan kuwa ta san inda ya dosa , ya ce gaba da fadin ” *a cikin su ya fi su kokarin siyan zuciyarki ne har kika shiga wanan yanayin dalilin sa?*

Kafin ta bashi amsa ya juyo wajen wanan mutumi dake tsaye jikinsa na rawa , so yake ya je gareta aman yanayin hararar da take binsa da ita ya saka shi ja ya tsaya yana sauraron wani kalar yare da AA ke furtawa dan har ga Allah shi magaganun a dunkule suke zuwan masa,

Mubasshir ya matso kusan shi cikin yanayi na tsana ya ce” kana son tafiya da matata ne? Mai ya kawo ka gidan mu Elhaj? Why zaka yi kokarin rusa min farin cikina? ” Kasan wani abu kuwa? *I LOVE TS GIRL* ban shirya rabuwa da ita ba sai dai a rabani da lumfashina,

A tare suka zuba masa ido inda cikin wata murya mai ban tausayi wanan mutumin ya dora hanunsa a kafadar AA ya ce ” *SHE’S MY DAUGHTER*

ba Mubasshir da su Hajiya Fadimatu ba , ni kaina sai da na wuntsula jin wanan batu……., muje zuwa ba shi Kenan baYar Mahaukaciya ta zaro ido jikinta ya kwashi rawa, kafafuwanta suna kokarin kasa daukar ta, cikin gargadar murya ta ce” no, ni ? Ni? Bani da Uba, ni *Yar Mahaukaciya ce* ban sanka ba , bazan taba lamunta da kai ba ,

Da Sauri ya matsa kusanta ya kama kafadunta ya ce” tabas ke ce y’a ta daya da na malaka, ke ce ake gwada min a mafarki, ke ce, sai yanzu na tino ki ke da mahaifiyarki, idanuwanki da kalar fatar ki da karan hancin ki da yatsun kafafuwan ki da hannayan ki da tsayin ki , duka nawa ne kika yo, ina tine da ranar haihuwar ki na sauko daga jirgi na kuna waya ta maman ki tayi kirana ta kara min kukan ki a waya, u’r my life my everything, pleasz kar ki juya min baya a yanzu da Allah ya nuna min ke tun kafin raina ya rabu da gangar jikina ,

Yar Mahaukaciya ta yatsina fuska ta saka hannayenta ta cire hanun sa, ita fa wannan tatsuniyar ba da ita ba, ita yanzu haka abinda ya firgita ta ganin wanan matar mai matukar kama da Mahaukaciyar ta, sai dai ita wanan a wanke take, cikin sitirar ta take ,, mai kudi ce, mai kanshi ce,, kawai kama ce , ta dago rinanun idanuwanta daga kalon  Hajiya Hafsat ta sauke su saman hannun wanan nassaran mai Jan fata a Karo na biyu ta saka hannun ta ta cire cikin kunan rai ta ce” Malan ni fa matar aure ce, taya zaka taba min kafada, na fada maka ni ban san wani uba a gareni ba koda duniya zata taru a kaina, kana mahaifina ka barmu ni da mahaifiyata a bola? Muke kwana a cikin bola ? KO dan umana tana hauka ne? KO dan muna hauka ne? Ka kore mû ne? Albishirinka a cikin bola har haihuwa mamana tayi namiji, ta tafi ta barni da shi inda duniya take jifana da nayi cikin shege na haihu, ni din nan dalilin ka da ka watsar da mu har ruwan kwata mun sha, a yanzu haka akoy wa’inda basu yarda cewar Dan Mahaukaciya na ba d’à na bane, na kasance mai bakin jini sai da Allah ya hadani da iyaye na kirki dan haka wani bazai fito min rana tsaka ya ce min wai shi abanna ne na yarda ba, *I HATE YOU* *I HATE YOU*

Cikin wani irin yanayi mai bayar da tausayi yayi Saurin rungume ta a jikin sa dan ta dena jifan sa da wanan kalma da gwara a ce bashi da rai da ya ji ta daga bakin gudan jinin sa,

Cikin yannayin bacin rai ta kwaci jikinta ta juya da gudu tana rusa kuka ta fada dakinta ta rufo

Su duka da kalo suka bi ta , shi kuwa ya fadi nan sumame , cikin firgici suka kwashe shi suka nufi asibiti da shi inda kafin su fita Hajiya Fadimatu ta fada dakinta ta dauko macajin Yar Mahaukaciya ta ciro gashin dake makale a jiki ta bi bayan su , inda Hajiya Hafsat ta zamto tamkar kurma dan kuwa ta rasa tudun dafawa , ga koshi ga kwanan yunwa

Suna isa akayi emergency da shi inda Hajiya Fadimatu ta shiga ta office din docter ,

Basu fi minti goma ba ya farfado aman docter ya yi masa alurar baci

Suna nan zaune sunyi jigum jigum kowa da abinda yake sakawa a ransa inda AA Mubasshir ya zubawa hannayen Elhaj Muhammad Muktar ido yana auna su da  na Matar sa,

Docter ne ya shigo da takarda a hannun sa ya mikawa Hajiya Fadimatu

Ta karba tayi masa godiya

Yana fita ta zauna ta Buda ta karanta , idanuwanta ta lumshe ta sauke ajiyar zuciya domin gwajin gashin Yar Mahaukaciya da Elhaj Muhammad Muktar ya nuna eh lale Y’ar sa ce, jinnin sa ce, ta mikawa Mubasshir result din

Yana karantawa shima ajiyar zuciyar ya sauke ya mike ya nufi motar sa ya shiga ya tayar sai gidan Hajiya Fadimatu ,

Tunda ta shiga dakinta kuka ne take tana rike da dan kwamin Mahaukaciya tana tina rayuwarta da ita , ta mike da niyar ta dauko zoben hannunta Wanda ta tsinta a bola ta kade kofin ruwan da ta dibo dan shan  maganin ciwon kai , ai kuwa ya kwashe ta sai gata yim a kasa koshinta ya fashe ga jiri tana nan konce tana ganin dishi dishi ta kasa tashi kuma ita bata suma ba sai kuka take tana fadin” mamana

Yana shigowa ya haura dakinta ya dan konkwasa , ya kai minti biyu shiru hakan ya sa ya tura ya shiga

Hangota ya yi nan konce tana maida numfashi tamkar an caka mata yikuwa , ai wuli yayi da takardar ya nufe ta , yana isa ya talabota ya dauke ta ya dora ta saman bed dinta , ya mika hannu ya dauko dan kwalin dake yashe dan ya daura mata , warin dan Kwalin ya bugi hancinsa dan kwata kwata kin wanke shi tayi gudun kar warin jikin Mahaukaciyarta ya fita, da auri ya wular da ita yana goge hannun sa,

Hawa yayi ya dan tsaya yana nazarin yanda zai yi mata da rigar jikinta dan ya samu ya goge mata jinin da ya bata mata goshinta,

Rintse idanuwansa ya yi ya leka fuskarta ya ga tamkar baci take dan kuwa idanuwanta a rufe , ajiyar zuciya  ya sauke ya saka hannunsa ya ja ZIP din doguwar rigar , hannunsa na karkarwa ya sabule rigar yana  kokarin sabule rigar ta zabura ta farka tana zaro ido daidai nan aka turo kofar aka shigo

Gabanta ya yanke ya fadi haka gaban Wace ta shigo da kwarin gwuiwar ta yanke ya fadi …….

Shin wacece ta shigo? Yar Mahaukaciya zata yarda da mahaifinta? Ina Mahaukaciya ne? Shin mai sunan Yar Mahaukaciya na kirki?

Duk mai son ci gaban Yar Mahaukaciya ya turon sunan Yar Mahaukaciya ta wanan number *+22792245338*   thx

[12/15, 4:36 PM] ‪+234 902 472 4465‬: ??BELLES écrivaines Nigériennes

? YAR MAHAUKACIYA? na SAJIDA

 

                62

*Ina matukar murna, ina farin ciki karanta message din masoya, tabas bazan taba gajiyawa da ku ba dan sai ana yi da kai ake kula ka, ni Sajida ina kara godiya ga masoya na na nesa da na kusa, harda hawayen farin cikin Ashe ina da masoya, love u ,*

Cikin tsananin firgici suke yiwa juna kalon kalo, Mubasshir kansa sai da ya dan ji dar tamkar an kama shi da wani laifin,

Cikin wata irin tafiya take takowa tana son gaskatawa idannuwanta shin da gaske ne abinda suke gani ku?   

Wani irin ihu ta saki ta kama kanta ta cuje daurin dan kwalin tayi wurgi da mayafin ta nuno su da yatsar ta ta ce” Mubasshir, me nake shirin gani? Wace wanan? Ashe daman kai macuci ne? Ashe daman haka kake? Ni zaka ci amana ka kawo karuwa shinfidarka?

Mubasshir ya rintse idannuwansa ya ce ” SAHLA

Sahla ta kara daga mai hannu tana karkarwa da gursheken kuka , basu ankara ba sai ji kake kwatsam ta kwadawa Yar Mahaukaciya katuwar kwalbar tiraren dake ajiye saman table  , ta juya tana kokarin wawuro wani abin dukan aman har a lokacin bata ga fuskar Wace take kira da karuwa ba

Yar Mahaukaciya da taji saukar kwalba a goshinta ganin idan fa ta tsaya zata Iya halakata a kan abinda ita bata sakawa ranta cewar malakinta bane , hakan ya sa ta Mike tsaye tana haki , daidai nan Sahla ta juyo da wata kwalbar a hannunta sai dai me , idannuwanta suka yi arba da fuskar matar da tafi tsana a duniya, Wace mijinta tun kafin ya zama mijinta ta lura da irin kulawar da yake bata Wace ita da yake kokarin aure bai ba ba,

Kwalbar hannun nata ta fadi kasa inda ta bi bayan kwalbar luuuu kasa sumamiya

Gaba daya abubuwan sun yiwa Mubasshir yawa , yana tsaye ya rasa mai zai yi, tabas ya san ba’a yiwa Sahla adalci ba dan kuwa an yi mata kishiya bata sani ba, aman abin bai kai na tana zuwa ta shiga munanan kalamai ba harda fasa kai , ganin ta fadi sumamiya ce ya saka shi nufarta ya bar Yar Mahaukaciya dafe da goshi kanta na mugun Sara mata, wani katutun bakin ciki ne ya tokare wuyan Yar Mahaukaciya a ranta ta ce” Kenan ni na mutu ma KO dan baka So na? , bata san lokacin da ta ja wani uban tsaki ba ta fice ta bar masa dakin , inda ya raka ta da kalon mamaki yana tambayar kansa tsakin na raini ne KO na kishi ne?

Yana farkawa ya shiga furta sunan ” *ISLAM, ISLAM*

HAJIYA FATIMATU da Hajiya Hafsat suka taso da sauri suna yi masa sanu

Elhaj Muhammad muktar ya damki hannun Hajiya Hafsat ya ce” Ai ba mafarki nake ba KO? Na ga y’a ta, na ga *FADIMATUL ISLAM* KO?  Aman tamkar tana fushi da ni, dan Allah ku kaini wajen ta na gan ta , na nemi yafiyar ta,

Hajiya Hafsat ta ce” please yaya ka kontar da hankalin ka saurare ni

Elhaj Muhammad ya saka hanunsa ya cire Karin ruwan da aka saka masa, daidai nan wayar sa ta kwashi kara tana neman agaji

Hajiya Hafsat ta dauko ta dana ta Mika masa ,

Ganin number shine ce ya daga ya kara a kunnan sa yana salama , dan matar sa ta tafi harkokin kasuwancin ta , yayi ta kiran  number bata shiga sai ya danganta hakan da  bata samu lokaci ba

Yana karawa sai ya ji muryar namiji da harshen turanci yana tambayar idan har shi dan uwan mai wayar nan ne

Elhaj Muhammad mucktar ya amsa da ” Eh matar sa ce

Daya dayan bangaren mutumin ya ce” ouf yawa Daman tun shekaran jiya muke Kiran numbobin wayar tunda aka kawo mana ita

Elhaj Muhammad ya ce” ban gane ba aka kawo muku ita? Ku din su waye? A Wace kasa ce? Sanan mai ya hada ku da ita?

Mutumin ya ce” a hongkong ne , ni likitan mahaukata ne, an tsinto ta ne  ta cicira kayan jikinta tana hauka a titi dan haka muke ta neman family din ta dan kuwa a jiya zuwa yau sai da ta kashe min kare na Wanda na gada tun wajen kakana ,(abinka da arne?). Ya ci GABA” dan haka kayi gagawar zuwa ka dauki wanan Mahaukaciyar matar taka tun kafin na dau mataki a kanta kuma a biya ni kare na,  , yayi masa kwatancen asibitin ya datse

Yana datse Kiran daidai nan Hajiya *Rafi’at* ta shigo da tsananin firgici tashin hankalin jin yana asibiti , ita da suka rabu kan zasu je su nemi afuwar Hajiya Fadimatu tayi hakurin tarewar Hajiya Rafi’at din kafin ta shirya mata dakin Yar ta, sai ga message din kanwar ta Hajiya Hafsat tana fada mata wai suna asibiti

Tana shigowa ya juyo yana kalon ta, ai bai san lokacin da ya janyota ya rukunkumeta tamkar wani zai kwace masa ita,

Su Hajiya fadimatu suka yi gagawar FITA daga  dakin tun kafin tsohuwar soyaya ta bayana kanta a gaban su

Kaji fa, in an tsufa a san an tsufa kawai ehe?

*Cigiya CIGIYA*

*INA BADA CIGIYAR NOVEL DINA MAI SUNA DUK KARYAR KADA TA RUWA CE DAGA BAKIN 70, 70 , 70, DAN ALLAJ WANDA YAKE DA YA TAIMAKA YA TURON TA NUMBER WAYANA KAMAR HAKA +22792245338 NA GODE*

[12/15, 4:36 PM] ‪+234 902 472 4465‬: ??BELLES écrivaines Nigériennes

? YAR MAHAUKACIYA? na SAJIDA

 

                    63

*Haza yaumul akbar; yaumul shukur, yaumul salama! Alhamdulillahi ala ni’matil Islam*

Hajiya Fadimatu ta gyara zaman ta ta ce” Bani labarin yarinyata da mahaifanta,

Hajiya Hafsat ta zauna da kyau ta ce” George Roger ainahin sunan mahaifin Islam kafin ya musulunta, ya kasance Christa ne shi a da, lokacin da ya shigo kasar Misra, aiki ya kawo shi ,  irin ya shiga Wankan nan yayi sake ya bar kayansa a kofar bayin inda aka share aka tafi da su, yana fitowa ya tarar babu nan fa ya rikice ya rasa ya zaiyi domin harda pasport dinsa a ciki ,

Cikin mutanen dake jajanta masa harda aban mu, nan ya taimaka masa ya sauke shi a gidan mu domin aba akoy tausayi ,

Tafiya tayi tafiya a kulun yana Lure da yanayin rayuwar mu, tarbiyar mu, addinin mu, yanda muke cudanyar rayuwar mu cikin girmama juna , irin yanda idan zamu gaishe da na GABA da mu muke tsugunnawa har kasa domin mahaifiyar mu Yar nan Lagos ce aban mu ne na Misra, hakan ya mugun shiga ransa , gashi da tambayoyi , KO mai ya ga muna yi zai tambaya ne , mu kuwa mu bashi amsa yanda zai fahimta,

Ana cikin haka ya wayi gari da matsanancin ciwon kai harda habo , hankalin sa yayi mugun tashi domin ciwon sa Kenan habo da ciwon kai  , sanan idan ya tasar masa ya kan kusan wata yana jinya ,

Aban mu yayi dabara ya kai shi asibitin aminnin sa aka bashi magunguna , yana ci gaba da sha aman sauki sai dai hamdallah kawai, hakan ya sa kulun yana konce ba damar zuwa koda palo ne balatanna bangaran su

Rashin lafiyarsa sai ta shafi kowa tun ba ma sisterna Rafi’at, kulun muna yi masa adu’a

Wata safiya muka shirya muka shiga dan mu gaishe shi sai muka tarar yana ta kakafewa , hakan ya mugun tsoratar da mu , da gudu na juya dan neman agaji ita kuwa ta matsa ta zauna ta dafa kan NASA daidai inda ya fi rikewa tayi bismillah ta karanta masa salatil allahnabiyi kafa daya sannan tayi masa wala haula wala kuwata ilabilah har kafa tara,

Cikin ikon Allah tana sauke hannun ta tamkar ta sauke da ciwon , nanauyan baci ya yi gaba da shi

Ya kusan awa uku yana bacin nan inda muke zaune mun kewaye shi muna ta yi masa adu’a ya farka

Daya bayan daya yake bin mu da kalo inda ya kafe Rafi’at da kalo  , abinki da nasara sai ji muka yi ya ce” I LOVE YOU,

Ido muka tsaro inda ya Mike da kyau ya tsuguna gaban aban mu ya ce” Tabas na yarda da adinninku dad, ban taba tinanin cewar musulunci ya kai haka ba, tabas musulunci rahama ne, musulunci haske ne , ya hade hannayensa ya ce ” *Ina son zama musulmi*

A Ranar munyi murna marar adadi, bayan Aban mu ya tabatar da eh lale da gaske yake ba kokonto a cikin ransa ya dauke shi Ranar juma’a ya tafi masalacin juma’a da shi inda Duban musulmai suka shaida shigar sa musulunci aka daura masa aure da Rafi’at ,

Cikin ikon Allah bayan shekara guda da yan watani aka biyo bayan sa daga America inda ya shirya ya bisu ya gama hada koman sa ya juyo

Bayan shekara hudu har a lokacin bai samu haihuwa ba, a nan suka shirya har ni muka je garin kakansa na wajen uwa Wanda yake a raye a lokacin,

Da zuwan mu an karbe mu hanu bibiyu , a nan aka nuna masa dukiyar mahaifiyarsa sai dai fa da sharadin idan bai dauki Rosemond a matsayin mata bazai dauki dukiyar ba harta da hotunan ta,

Cikin fushi ya ce baya So su rike , aman Rafi’at ta tsaya tsayin daka kan sai ya amince KO da rabon su ga kwon su ne a duniya

Hakan kuwa aka yi bayan ta musulunta da kyar aka aura masa ita muka koma da ita Misra

Aban mu yayi murna haka mama , shi kuwa Muhammad yana matukar mamaki inda Farida bata taba nuna bakin halinta ba

Cikin haka aban mu yayi rashin lafiya Ashe na ajali ne , Allah ya karbi abinsa,

Bayan yan watanni muka tataro muka komo Lagos da zama dan kuwa kwata kwata mun dena jin dadin zama a Misra

Konci tashi arzikin Muhammad ya kara habaka inda ya tsaya tsayin daka dan ganin ya inganta mana rayuwar mu ta fanin ilimi ba’a magana sosai muna jin dadin rayuwa da shi

Ana tsaka da haka ciki ya bayana a jikin Rafi’at, zo ki ga murna  , hankalin kowa saï ya koma kanta inda a nan bakin halin farida ya fito dan kuwa kiri kiri ta nuna ta tsani Rafi’at

Cikin ikon allah ta haihu lafiya inda aka saka mata sunan *Fadimatul islam*

Yarinya tana cikin gata Wanda fada miki shi To fa bata lokaci ne , hakan ya kara tunzura zuciyar farida ta taba kama kuncinta ta ja daidai mahaifinta ya shigo, a Ranar mun ga tashin hankali dan kuwa da kyar aka amshe farida a hanun sa inda yayi mata kashe da Babar murya cewar ba ita ba taba lafiyar yar sa idan ba haka ba shi da ita sai dai  su raba hanya

Tun daga Ranar ta fita harkar mu gabaki daya banda mijinta, Ana haka muka wayi gari ba ita ba labarin ta sanan ba yarinya

Banban  hankalin sai da Farida ta bayana a gaban mu  tayi mana korar kare kan bata san mu ba , abin mamaki shi ma a lokacin take yanke ya nuna bai taba ganin mu ba , muna ji muna gani muka fito ba tare da sanin inda Rafi’at ta nufa ba

Haka muka ci GABA da rayuwa da gadon abana , cikin haka itama mama ta rasu ta barni ni kadai , Allah shine gatana a haka har na zama wani Abu a duniya aman a kulun ina neman Yar uwata ruwa a jalo

Cikin ikon Allah , Allah ya hada mu a ka’aba ,bayan mun zauna ta bani labarin mutumin da ya ceceta Wani Baban malami mai fada a ji a kasar Kano , shi ya kade ta da mota bayan ya dawo daga karatu tsakar dare, cikin ikon Allah tana farkawa cikin hankalin ta ta farka, sai dai tsananin mamakin ganinta a cikin daudar nan da kuma alamar haihuwa da tarin tambayoyin inda muke harda y’arta suka sake saka ta a rudani

Da kyar da adu’a da ban baki da rokon Allah ta samu nutsuwa inda ta fadawa Malan labarin rayuwarta abinda ta sani harda tana konce rungume da Islam Farida ta shigo ta watsa mata wani jini a jikinta sanan ta turo mata wani kasko tirare ya Bade dakin daga nan sai ganin ta da tayi a asibiti

Jin hakan Malan ya gane cewar aikin asiri ne, daman ya shiryawa iyalan sa tafiya haji sai ya saka ta itama da niyar idan ta dawo zasu tafi Lagos ta neme mu ,

Hajiya fadimatu ta sauke ajiyar zuciya ta ce” lale rayuwar ku na cike da abin al’ajabi, aman Alhamdulilah yanzu komai ya zo karshe tunda har sakayar Ubangiji ta fara aikinta

Muryar Hajiya Rafi’at ce ta katse musu hirar tasu inda tana ta zubar da hawaye ta kama hannayen Hajiya fadimatu ta ce ” aunty kiyi min rai ki kaini na ga yarinyata dan Allah

Hajiya fadimatu ta dafa hannunta cikin tausayawa ta mikar da ita ta ce ” mu tafi, domin nima ina son ganin wani irin farin ciki Yar fadimatu zata yi na yin arba da magaufiyar ta sanan ta san cewar ba laifin mahaifinta bane dan ta tsinci kanta a bola ba

Haka suka dugunzuma suka nufi gidan su AA Mubasshir dan hada Yar Mahaukaciya da Mahaifitarta,,,,,,,muje zuwa??????????????????????????????????????Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                     64

Readers na kuma yin mantuwa Sunan kishiyar mahaifiyar Yar mahaukaciya *Hajiya Falmata* na gode.

Suna isowa gidan tayi kokarin bude kofar ta fita Hajiya Fadimatu ta riko hannunta ta ce ” maman y’a ta Dan Allah ku Dan dakata na Fara shiga nayi mata bayani a tsanake Dan bana son ta kuma suma domin a dalilin ta ga Hajiya hafsat  sai da ta suma,

Hajiya Rafi’at tayi murmushi ta koma ta jinginar da kanta, ko ba komai mutumin da ya  rungumi gudan jininka ya kaunace shi ai ya isa a girmama shi,

Cikin nutsuwa ta tura falon ta shiga,  hango Yar Mahaukaciya tayi tana zaune still kukan take bata daina ba, ga goshinta da jini,  Cikin faduwar gaba  ta karasa ta dago kanta

Yar Mahaukaciya na yin ido hudu da Hajiya Fadimatu ta fada jikinta ta saki wani kukan, 

Hajiya Fadimatu ta shafa bayanta a hankali ta ce” wa ya kuma batawa y’a ta rai?  Wa ya saka min yarinya take kuka?

Yar Mahaukaciya tamkar wata baby ta turo dan bakinta ta ce” Mamana kin ga Yaya ne da matar sa”

Hajiya Fadimatu ta zaro ido tace ” wani abu suka Yi miki?  Su suka ji miki ciwon nan?  Suna ina?

Yar Mahaukaciya ta ce” aa mamana ba fa su suka ji min ba, faduwa nayi,  su sun hanani baci na,

Hajiya Fadimatu ta Kama hannunta suka nufi dakin ta,  ta dauko kada ta goge mata wajen da jinin ya digu,  ta shafa mata Magani wajen da ya kumbura sannan ta zauna ta fuskanceta Cikin nutsuwa ta kirayi Sunan ta, ta ce” Rahma

Yar Mahaukaciya tayi gagawar kalon ta domin ta san tabas abinda zata fada Mai mahinmanci ne Dan kuwa bata taba kiranta da sunanta ba, Cikin mutuwar jiki ta amsa da na. Am,

Hajiya Fadimatu ta ce ” *kina son sanin ainahin sunan ki Wanda abanki ya dasa miki?*

Yar Mahaukaciya ta dago kanta a Karo na biyu gabanta ya kuma faduwa ta Kali Hajiya Fadimatu Cikin gargadar murya ta ce” mama kin yarda shi ya haife ni?

Hajiya Fadimatu ta ce” tabas Elhaj Muhhamad Mahaifinki ne, na yarda da hakan,

Yar Mahaukaciya ta kawar da kanta gudun kar Hajiya Fadimatu ta ga hawayen bakin Cikin dake shirin zubo mata,

Hajiya Fadimatu ta dago habarta ta ce” Shin ba hamdallah ta fi dacewa ki Yi na ganin Mahaifinki?  Kina fushi da jarabawar ubangijin ki ne?  Shin baki duban Wa’inda kika fi?  A rayuwar bola da kika Yi Allah ya Kare ki, sanan da kika fito daga bola Allah ya kasance Cikin baki Kariya, kinga rayuwa kin sha wuya,  Aman Hajiya Rafi’at ta fi ki Shan wahala du da haka banban burinta ta ganki, balatana Mahaifinki Wanda aka Raba shi da ke a lokacin da Allah ya bashi ke, a lokacin da yake cike da burin ganin kin taso, ya GA girman ki ya ji maganar ki,  ya GA dariyar ki,  ya ji dumin jikin ki a matsayin ki na y’a kwaya daya da ya malaka a duniya,  aka raba shi da matar sa wace suka yi auren soyaya, aka juyar masa da kwakwaluwar sa ya manta kowa sai yau da Allah ya hada shi da ke komai ya karye aman zaki kasa kalon sa y’a ta?  Shin wannan ni’imar bata isa kiyi ta murna Kina yiwa Allah godiya ba?  Haba *Fadimatul Islam Mai baban suna*

Yar Mahaukaciya dake zubar da hawaye ta tsurawa Hajiya Fadimatu ido Tana sauraron abubuwan da take fada Wanda tamkar da ita take to Aman sunayen da take kira ita ko daya bata Sani ba hakan ya sa ta ce” *wanene Elhaj Muhhamad? Wacece Hajiya Rafi’at?  Wacece Fadimatul Islam?*

Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta dago habarta ta ce” *Elhaj Muhammad shine Mahaifinki,  Hajiya Rafi’at shine sunnan mahaifiyar ki,  Fadimatul Islam shine Sunnan da Mahaifinki ya dasa miki*

AI kuwa Yar Mahaukaciya ta fada jikin Hajiya Fadimatu ta kuma sakin wani kukan,  da Kyar ta lalashe ta,  tayi shiru ta samu ta fada mata labarin da Hajiya hafsat ta fada mata,

daidai wannan lokacin Yar Mahaukaciya ta yarda da maganar Hajiya Fadimatu sannan ta yarda Elhaj Muhammad mahaifinta ne, to aman ina mahaifiyarta take?

Hajiya Fadimatu ta kamo hannunta ta ce” zo ki gani,

Yar Mahaukaciya ta Mike Tana biye da ita,  daidai sun fito, Su Mubasshir ma sun fito sahla sai kuka take shi kuwa idannuwansa sunyi jajajir yana tafe Tana binsa a baya tana rantsuwar sai ya saki wanan mahaukaciyar yarinyar,

Hajiya Fadimatu ta Kare musu Kalo ta ja Hannun Yar Fadimatu suka sauka inda ladidi Mai aiki ta Sanyo su Hajiya Rafi’at ta cika su da kayan marmari Aman sun kasa taba komai,  Sunyi zuru cike da zunlumi Suna ta tinani Hannun Hajiya Rafi’at Cikin na Elhaj Muhhamad sai murzawa yake yana karawa ko sun sami kwarin guiwa,

saukowa suke su hudun domin shi Mubasshir biyo su ya Yi,  itama sahla Tana biye da shi Dan ta ci alwashin sai dai ya zabi guda a Cikin su ko kuwa wly kowa ya rasa shi har uwar tasa (to Kaji )

Suna saukowa su duka suka mike Suna hango Yar Mahaukaciya da ta labe a bayan Hajiya Fadimatu,

kasa daurewa Hajiya Rafi’at tayi ta matso a hankali ta ce”  *Islam*

Gaban Yar Mahaukaciya ya fadi domin wanan muryar bazata taba mantawa da ita ba,

da sauri ta fito daga buyar ta zaro ido bakinta na rawa ta ce” *Mahaukaciyata ke ce ko Mai Kama da ke ce?*

Hajiya Rafi’at ta lumshe idannuwanta ta buda hannayenta,  AI kuwa da gudu Yar Mahaukaciya ta fada jikinta suka kankame juna inda suka saki wani irin kuka na farin ciki,

elhaj Muhammad ya kasa Hana kansa isawa garesu,  ai kuwa shima ya isa ya rungume su sai kuka(?? )

gaba daya falon kukan suke banda sahla dake kalon wani sabon salon rainin hankali,  sai Mubasshir dake lumshe ido kukan abin sonsa da mahaifiyar sa na taba masa zuciya, 

wasa wasa sun ki daina kukan kuma sun ki sakin junan su,  ganin Daman kukan nan shi ta wuni tana Yi, kuma idan ya zuba mata ido sai tayi ta Yi har wata cutar ta Kama ta ya sa ya matso  Kadan ya daidaita murya ya ce” *Am Dad ( kuma kai?), am maman Mubasshir, am aunty* kukan ya isa hakanan kar a kamu da rashin lafiya,

Elhaj Muhammad ya Fara tsagaitawa sanan suma suka Yi shiru,  aka zazauna,  nan Hajiya Rafi’at ta bukaci Yar Mahaukaciya ta fada mata irin rayuwar da suka Yi a bola da kuma yanda aka Yi suka rabu,

Yar Mahaukaciya ta lumshe idannuwanta tamkar a lokacin take rayuwar ta fada musu komai abinda ta Sani har haihuwar Mahaukaciya ita ce sanadiyar rabuwar su,

Hajiya Rafi’at ta zaro ido ta ce” inalilahi Wa’ina ilaihi Raj’une,  harda haihuwa nayi a Cikin haukan?  To a ina na hadu da Cikin?  Ina abinda na haifan?

Yar Mahaukaciya ta kuma rintse idanuwanta ta ce” abinda kika Haifa bayan na Baro bola mun hadu da jarabawa kalakala Allah ya Amshi abinsa, …………… Nan ta ci gaba da basu labarin bayan fitowarta daga bola saceta da akayi aka nufi Lagos da ita,  matar da ta so lalata mata rayuwa Mai sunan  Falmata a yanda ta ji inyamurar nan tayi kiranta da oga,  Allah ya ceceni mijinta ya dawo a lokacin, nan na samu na fice.

Elhaj Muhammad ya  dago kansa da sauri ya ce” Falmata?  Hajiya Falmata?  Inyamura a gidan?  , nan ya zaro wayarsa ya ciro hoton matarsa Hajiya Falmata ya nuno mata

ai kuwa Yar Mahaukaciya  ta mike dafe da kirjinta ta ce” tabas ita ce,  wannan matar ce,  lokacin da ta shigo tana fadin kar na damu ba zata jima ba Dan ma boka ya ce dole dole sai mai da kar asirin da tayi shekara 15ya karye,  tana kokarin aikata nufinta akace mijinta ya zo,  nan ta ce a fitar da ni ta baya yanda bazai gan ni ba

Elhaj Muhammad ya shiga maimaita inalilahi Wa’ina ilahi raj’une, tabas matarsa ce kuma Yar uwarsa wace Hajiya Rafi’at ta saka baki ya aureta Ashe ita ta ruguza masa farin Cikin sa?  Kai duniya abin tsoro abin a bi a sanu ce, ya dube su ya ce” ga sakayar Allah nan tun ba. Aje lahirar ba domin yanzu haka Tana psychiatric na shine tana hauka har ta kashewa likitan Karen sa sai fada yake kan aje a daukota  tun kafin ya sake ta,

gaba daya suka shiga jimami Suna Al’ajabi,  rayuwa kenan ko an zalince ka idan kayi hakuri Cikin ruwan sanyi Allah zai saka maka,  tsoro da kaunar musulunci ya Kara darsuwa a zukatan su, kowa tasbihi yake a Cikin zuciyarsa yana wasa Sarkin da shine Sarki Wanda buwayarsa take a bayane gagara misali, ubangijin samai da kansai, Mai wuta mai aljannah, Mai bada umarnin abu ya kasance ya kasance, Mai kowa Mai komai,  Wanda bai haifa ba, ba’a haife shi ba, wannan dai gagara misali,, *Allah* kenan☺,

muryar Sahla ce ta katse musu wanan shauki da suka shiga inda ta matso Kusa da Elhaj Muhammad mai gidan mahaifinta a wajen aiki kuma mijin kawar mamarta ta ce” Aba, ban gane ba,  shin mainene hadinka da wannan mahaukaciyar Yar Mahaukaciya wace uwarta MA tayi Cikin shege balatana ita gashinan Tana fadi da bakinta ta wani zo tana Yi maka karya ka yarda har kana zubar da hawayenka,  da ganin zagar idanuwan yarinyar nan ka San Yar bariki ce ba karama ba Aman har a iya sauraron ta harma a aurawa mijina ita bayan ba a San asalinta ba? 

wani irin kalo ya watsa mata Wanda ya sa yata hadiye sauran maganar ta, yana Al’ajabin daman haka take?  Bata da kunya har ya dauketa tamkar Yar sa ya Cikin sa yake kyautata mata?  Daidai da rigimar mota da ta Dora mahaifiyarta ta kawo Karar MahaifinTa ya ki saya mata da yayi masa magana ya nuna bashi da Hali hakan ya saka aka kawo mata ashe bata da kunya?  Ransa ya Kai kololuwar baci ya buda baki ya ce”””””””””””””””””””””””””””::::::::::::::::::::::::::::::::::::””””””””””””””??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*_Na SAJIDA_*

                        65

Cikin wata irin murya mai cike da mamaki da haushin kalaman bakin Sahla Elhaj Muhammad ya ce” ashe baki da nutsuwa?

Cikin sauri Yar Mahaukaciya ta ce” a yau na hadu da abanna, ina son ya wuni Cikin farin ciki, bana son Wani abin komai girmansa ya daga masa hankali, please abanna Kar ka mayar da bacin rai Cikin bacin rai,

Sahla da ta Gama harzuka ta ce” ke ki Kali kanki ki kirayi kanki y’ar dad?  No baki Kai wannan matsayin ba, ke fa almajira ce, mabaraciya ce, Mahaukaciya ce, sanan Yar Mahaukaciya,

Mubasshir Cikin bacin rai ya ce” sahla ya ishe ki haka,

Sahla ta juyo Cikin bacin rai idannuwanta sun fara rufewa ta ce” to Kai kuwa shanyaye,  Da aka Koreta daga gidan namu shine ta shanye ka,  ka kwaso ta ka kawo ta nan kana kawar da jarabar ka har ka goga min cuta ko?  To walahil azim Baku isa ba, ni da ku mu zuba mu gani,  Idan takamarta karuwanci,  iya bariki ni na fita iyawa, kuma ka Sani ni sahla Dan ni kadai aka halice ka Kai Mubasshir,

Hadiye maganar tayi sakamakon dauketa da mari da ya Yi,  ya Kara mata wani,

Gaba daya ido suka zaro,  Da sauri Hajiya Fadimatu ta nufo shi haka Elhaj Muhammad suka rike shi inda ita kuwa ta silale nan jini ta hancinta yana zuba,

Hajiya Fadimatu ta ce ” why son?  Why zaka taba lafiyar jikinta bayan an Hana ka dukan koda namiji ne bare mace?  Shin ka manta ne? 

Elhaj Muhammad ya ja Hannun sa ganin yana kokarin sume masa ya kasa furta komai jikinsa sai rawa yake,

Hajiya Fadimatu ta sauke ajiyar zuciya tana adu.ar Allah ya tsagaita fushin sa,

Hajiya Rafi’at ta nufo sahla ganin tana habo harda yawu na diga daga bakinta, da sauri ta mika hanu zata taimaka mata, Aman karfin Hali da muguwar zuciya suka saka ta ja jikinta a haka har ta fita da kyar ta shiga motar ta , ta nufi asibitin yayanta tana gursheken kuka,

Dakin Yar Mahaukaciya ya nufa da shi ya zaunar da shi sanan Ya shiga bayi ya hada masa ruwan wanka Mai mugun sanyi ya taimaka masa yayi wankan,  har a lokacin bai ce ufan ba, Shima Elhaj Muhammad bai ce masa komai ba,  , Suna fitowa ya nufi gadon da shi ya konta  , ya kuma laptop ya saka masa karatun alkur.ani mai girma sanan ya fito ya rufo masa Dakin

Yana saukowa Hajiya Fadimatu ta mike ta ce” Yaya dai?  Ya suman ko?

Elhaj Muhammad ya ce” aman da kina da Cikin sa Sarki ya baki wanan tsumin ko?

Hajiya Fadimatu ta ce ” haka,  domin a ranar da aka shaida mana namiji ne, ya turo min da tsumin nan, to run yana yaro nake iya yina Dan gudun bacin ransa, dan idan ransa ya baci bai huce haushin sa ba suma yake, daga ya farka sai kurmancin kwana biyu

Elhaj Muhammad yayi murmushi ya ce” tsoho ya hada min yaro da rigima,  Ai zamanin yaki ne ake irin tsumin nan,  gashi shi kuwa baya son harkar sarautar MA, bare har yayi yaki,

Hajiya Fadimatu ta ce” haka, 

Hajiya Rafi’at ta ce” wanan wani irin tsumi ne haka?  Kar dai ya suman?

Elhaj Muhammad dake kalonta da mayatacen kalo tunda ta rukunkume shi a asibiti ta tayar da zaune tsaye ya ce” no akoy wata hanyar,  ana saka mutun a ruwan kankara, sai a bashi abinda zai saka masa nutsuwa da yardar Allah idan ya farka zaiyi magana aman fa ba kamar da ba,  sai ya kwana biyun nan sai ya saku,

Hajiya hafsat ta gyada kanta Tana ta shafa gashin kan Yar Mahaukaciya wace tayi zuru tsoron Mubasshir ya darsu a zuciyar ta, Wanda bata taba jin irinsa ba, ta kawar da kanta ya sauke ajiyar zuciya Tana tuna zako ta iya Jan ajin nan?  Kar taje ta ja ya jaza mata duka(hhhh) , wata zuciyar tace mata “wani Jan ajin kuma ke da baki Kai wannan wajen ba, ke fa a kalon Yar bariki yake miki,

Hajiya Fadimatu ta katse mata tinaninta inda ta ce” Yar Fadimatu tashi ki dauki abinci ki ci please,

Yar Mahaukaciya tayi murmushi ta mike ta ce” to mamana,  ta nufi kicin

bayan tafiyarta Hajiya Fadimatu ta gyara zama ta zayane musu komai tun ranar daurin auren Mubasshir da ya kawo mata Fadimatul Islam har zuwa shawarar da suka yanke na daura musu aure da Mubasshir Dan tsoron halaya irin na mahaifiyar su sahla tana tsoron taji cewar tana nan ta kuma yin yunkurin wani abin, hakan ya sa muka yanke wanan hukunci Wanda su kansu ba. A jima da muka sanar musu ba bayan mun tabatar da eh yana sonta,  da fatan zaku Yi min kyakyawar fahimta

Hajiya Fadimatu tayi murmushin jin dadi ta Sada kanta inda Elhaj Muhammad ya karanci farin ciki a fuskar ta,  ya ce” Kaji Hajiya da wani zance kuma,  Dan kin yanke hukunci a kan y’ar ki har zaki zauna Kina bamu labari?  No Mu haihuwar Islam kawai muka Yi aman Maman Fadimatul Islam Fadimatu ce.

Cikin yanayin farin ciki Hajiya Fadimatu ta rungume Hajiya Rafi’at tana murna tana godiya, 

Ita dai Kara Sada kanta take Dan kuwa abin kunya yake bata wai itace da aurar yarinya,  Allah Mai iko,

Elhaj Muhammad ya dago kansa ya ce” sister mana,  wai dole sai anyi wani bikin tarewa?  Tunda an daura a bani matata

Hajiya Rafi’at ta zaro ido ta mike da sauri tana neman wajen buya,  shi daman haka yake da fadin abinda yake ransa ba tare da dar ba

Hajiya Fadimatu ta riko hannunta tana dariya ta ce” aa yayanA gaskiya sai munyi bikin tarewa

itama Hajiya hafsat dariya take tana cike da farin cikin ganin Yar uwarta farin cikinta ya dawo

          Sahla

tana isawa hospital din ta Dana kanta ta fito ko kashe motar bata tsaya Yi ba ta nufi ofishin yayanta,  Gaban rigarta du jini ne Da yawun wahala,  Tana shiga ta zube a kasa ta saki wani kuka tana fadin ta mutu ta lalace

Da gudu ya ajiye takardar gabansa wace ya zauna yana rubuta irin yanda yayi missing din Rahmar sa sai GA kanwar sa ta shigo a wannan yanayin, 

Cikin faduwar gaba ya talafo ta ya ce” Sahla lafiya?  Yaushe kuka dawo daga tafiyar?  Mai ya Faru?  Hatsari kuka Yi?  Ina mama?  Wani ya mutu ne?  Tell me sahla kar ki saka zuciyata ta buga,  ya karashe zancen Cikin karaji

Sahla Cikin kuka har tana kokarin shidewa ta ce””””””””””””””””””””””””””……………………”””””””””””””””””??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                        *66*

Sahla cikin kuka har tana kokarin shidewa ta ce” sun cuce ni, sun wulakanta ni, ashe dama Mubasshir macuci ne ?  Azalumi ne ?  Allah ya isar min,  sanan sai na halaka su daya bayan daya

Idriss ya zuba mata ido yana rike da ita, cikin muryar tausayi ya ce” mai yayi miki ne ?  Sahla ki dena irin maganganun nan ba kyau, ki dena please, ki tashi na wanke miki jinnin nan, ki nutsu sai muyi maganar

Sahla ta kara fashewa da kuka ta ce” Yaya Idriss zaman dadiro fa yake yi da ita, karuwar sa ce ashe, shi yasa ya  nacewa zuwa wajen hajiya da nufin shan fura ashe da abinda suke kulawa ?

Daidai wanan lokacin gaban Idriss sai dukan tara tara yake, da sauri ya  matse hannunta ya dagota cikin kakausar murya ya ce” ki dena, ki dena kokarin kayar min da gaba, ki dena kokarin ganin bugun zuciyata ya tsananta, ki fito ki fada min inda zancen ki ya nufa, shin Wa kike nufi ? Da Wa Mubasshir ke cin amanar ki ?

Sahla ta dago idannuwanta ta kali yayanta ganin yanda yake Bari, ta ce” eh wannan mai kama da aljannun, da ita nake, ita na kama da Mubasshir à dakin sa a saman bed dinsa

Da sauri ya ja baya yana girgiza kai ya ce” no,  no Sahla,  Rahama *Tawa ce* ni kadai, abinda nayi mata bazai saka tayi fushi da ni ba har ta kula wani na, sanan kudin sa KO kyan sa bazai saka ta juya min baya ba domin ni din nan ni zan fadi irin halayar Rahama na, bazata taba yin taraya da wani namijin da ba muharaminta ba, yana dai lalabarta ta yafe min ne na aureta muyi rayuwar mu cikin SO da kaunar juna, baki gani da kyau ba,  ya karashe yana langwabar da kansa irin ta bashi karin haske à abinda ta gani,

Sahla ta Mike tsaye ta dafa hannun yayanta ta ce” idannuwana basu yi karya ba, tabas kusancin da na tarar yafi karfin aminta, ka Sani indai da boka KO malan sai inda karfina ya kare, na haramtawa wannan yar mahaukaciyar mijina,    ta juya ta banko kofar

Idriss ya zauna dabas yana fadin “no Mubasshir ba mazinaci bane, haka Rahama, to mai Sahla ke nufi ? Ganin yana kokarin fadawa wani tunanin ya saka shi mikewa yana kokarin kamala aikin da ya fara sai ya je gidan su Mubasshir din ya ji yanda suka kaya ta amince ta aure shin KO aa ? (? eyah Idriss)

Karfe hudu da rabi sun gama cin abinci, Hajiya Hafsat ta kali yar mahaukaciya ta ce” Yar aunty tashi ki leko min yayanki KO ya farka ?

Da sauri yar mahaukaciya ta dago kanta gabanta ya yanke ya fadi, tsoro ya shiga zuciyar ta,

Hajiya hafsat ta kawar da kanta dan ta karanci tsoro à fuskar y’ar Tata,

Yar Mahaukaciya ta Mike gwuiwa à sace ta nufi sama , tana zuwa kofar dakin da ya zama malakinta bugun zuciyarta ya tsananta, rintse idannuwanta tayi tana karanto duk abinda ya Zo mata bakinta,

Cikin ikon ALLAH ta samu kwarin gwuiwa, ta tura dakin ta shiga kanta à kasa tana harde kafafuwa,

Mubasshir da fitowarsa kenan daga Wanka dalilin ruwan sanyi da elhaj Muhammad ya saka shi anfani da shi da kuma sanyin AC ga daman mutumin ba dama, hakan ya hadasa masa shiga wani yanayi marar musaltuwa, wannan shigarsa Wanka na uku ne yana sakarwa kansa ruwa aman sai kara mumurdewa yake,

Kalonta yake tamkar sabuwar halita, ganin ita Bata karaso ba, sanan ita Bata juya ba ya saka shi yin gyaran murya,

À hankali ta dago kanta, idannuwanta suka sauka à kan Mubasshir dake tsaye daure da tawul, ido ta zaro tana dafa kirjinta tayi saurin tsugunnawa kasa ta rufe idannuwanta ta dora hannayenta biyu saman kanta ta ce” na shiga uku,

Mubasshir ya zaro ido yana kalonta, tamkar wace ta ga wani dodo,  à hankali yake takowa sai da ya ISO Daidai ita ya ce” malama kin Zo karbar hakinki ne ? Mai yasa baki da hakuri ne islam ?

yar Mahaukaciya ta dago kanta da haushi haushi ta mike da niyar ramawa wata kunyar ta kuma darsun mata bazata iya jure kalonsa à haka ba, ta juya da sauri zata bar dakin

Mubasshir yayi taku biyu ya riko hannunta ya juyota da karfi ta fado kirjinsa, gaba daya gashin kanta ya rufu à kirjinsa, ya saka hannunsa na dama ya dago habarta idannuwanta à rufe ruf, bugun zuciyarta na bugawa tun karfi tamkar nasa,  à hankali ya saki murmushi ya ce” *u love me yarinya*

yar mahaukaciya ta bude idannuwanta da suka tara kWallah à cikin su ta zubawa fuskar Mubasshir ido,  gabanta ya kuma faduwa ta rintse idannuwanta ta kuma budewa tana Jin wani abu na ratsa sasar jikinta tun daga kanta har kafarta,  cikin karfin hali ta ce” *No, bana sonka AA*

Kafin ta rufe bakinta ya hade bakinta da nasa ya shiga kissing,  kis din da bai san ya iya shi haka ba,  kis din da bai san haka ake ji ba,  yayi haka ne da niyar ya hukunta bakinta da ya furta abinda baya cikin zuciyarta, yayi haka ne dan kar ta kuma furta abinda zai iya halakashi sai dai kash ya kasa control din kansa, ya kasa hana kansa dena kissing din Islam, ya kasa raba jikinsa da nata,   gaba daya jikinsa Bari yake ya dagata yayi saman bed da ita,  cikin rawar jiki ya kama rigarta ya………………. ?????????????????????????????????????????????

*Dan Allah ku gafarceni na jinkirina, abin ne yayi yawa, insha ALLAH na kusan gama shi, sanan Wa’inda suka tambayeni farkon sa KO karshen sa kuyi hakuri zan nemo muku cos na canza wayar ne nima banda shi,  rashin sanin amsar da zan baku ya saka banyi muku replay ba, Ina kara godiya masoya ALLAH ya sa ku yi min uzuri, love u all*         *SAJIDA*??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                       67

*My Aïcha, aishata, tawa Ina mugun yin ki, irin da yawa din nan, wannan page naki ne gabaki dayansa lv u*

Kokarin sabule mata rigar yake gaba daya hankalinsa ya fara barin jikinsa, jikinsa sai bari yake, gashi bakinta à nasa yana ta kissing bai Bari ba,

Yar mahaukaciya sai kicikicin din kwace kanta take domin wannan lamarin ya girmi tunanin ta, yafi karfin kwakwaluwarta da gangar jikinta, sai zare ido take jikinta na Bari,

Dagewa tayi, tayi wani motsi hade da nishi nishi domin ta kasa ihu sadaniyar rike mata bakin da yayi,

Idannuwansa ya dago Wa’inda suka rine suka yi jajawur da su ya sauke à cikin kwayar idanuwan yar mahaukaciya wace nata sun cika da kwalah, sai jujuya su take tana kokarin isar da sakonta ta hakan,

Cikin yanayin bukatuwa ya cika mata bakin ta, ai kuwa ta fashe da kuka tun karfinta tana shasheka

Mubasshir ya tsareta da ido yana kalonta, karfa ta raina Masa hankali, ai bazata ce kuka rashin sabo ne ba dan kuwa koda jama’a zasu taru à kansa bazai yarda cewar Bata saba da wannan ba,   KO du wannan kukan na Bata son sa ne ?  Shi bai ce baya sonta ba sai itace zata yi irin haka ?

Cikin kukan ta ce” ni karka kuma taba min jikina ni ba yar ? , ta hadiye maganar ta sakamakon tunawa da tayi da Wa take magana,

Kokarin saukowa take daga bed din ya jawo hannunta ta fado saman kirjinsa ya dagota ya ce” baki gama yi min kashen ba kuma zaki tafi ?

Yar mahaukaciya ta sada kanta bugun zuciyarta na tsananta, ta kasa magana

Yaci gaba da fadin” mace bata gindaya min sharuda, nine namijin ni zaki bi komai matsayinki dole ki duka min, dole ki gaishe ni, dole ki bi umarni na, sanan wannan yayi Nuni da jikinta y’ace” gonata ne, à koda yaushe, à KO wani irin yannayi inada iikon shigarsa na fita à shi ba tare da wani KO shi kansa sun yi min iyaka ba, da ke da jikinki malaka ta ne, ki guji juya min baya KO kokarin tsayar da ni idan na bukace shi, i’m i clear ?

Yar mahaukaciya ranta ya gama baci wannan shine à dakeka à hanaka kuka,  Taya zai mayar da ita tamkar wata propriété  ??‍♀, ta rintse idonta cikin wata irin murya mai Shegen dadi ta ce” ni na san zan zamto ne tamkar   baiwa à wajenka Yaya AA, har yanzu ni ba kowa bace face mai neman kanta, Ina neman kaina sosai, karka damu KO don gudun kar na kuma tsintar kaina à wacen rayuwar zanyi kokarin kaucewa bacin ranka,

Gaba daya jikinsa yayi wani irin sanyi ya rasa mai zaiyi kawai sai ya jawota jikinsa ya rungume ta tsam à jikinsa yana Jin yanda sonta yake bin sasar jikinta yana ratsa KO’ina na jikinsa,

Wayar sa dake ajiye à saman bed din ta kwashi tsuwa tun karfi tana shaida Idriss ne ke Kira,

à tare gabansu ya fadi tayi saurin mikewa shima ya mika hannu ya dauko yana wani kawar da kai uwa yana gabansa,

Da kyar ya samu ya daga wayar ya kara à kunnansa

Idriss ya ce” mutumina ya garin ? wai kana inane Ina ta nemanka ✌? days ?

Mubasshir dake kalon  Islam ta juya baya tana tafiya bayanta sai juyawa yake har ta bar dakin ya saki ajiyar zuciya

Idriss ya ce” llafiya nake Jin muryarka wata iri ?

Mubasshir ya ce” Lafiya lau likita

Idriss ya sauke ajiyar zuciya ya ce” gani fa kusan gidan zan biyo naji yanda kuka yi da kakus ta fada maka inda princess take ?

Mubasshir ya Hadiyi wani yawu kafin yayi magana Idriss ya katse wayar,

Da sauri ya mike yabi jikinsa da kalo ya kali kofar dakin ya kuma kalon wayarsa à hankali ya furta chuiiiiiiiiiiiiiiiiiit ya zanyi ?

      Na sani????????????????????????????????????????????????????????????????????????Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                         68

Tafe take tana adu’ar ALLAH ya sa kar à gane AA ya taba mata jikinta, tana saukowa ta tarar basa nan sai auntyn ta, cikin sauri ta nufi kofa dan gudun kar ta gane abinda ya faru da ita,

Tana kokarin bude kofar Idriss ya turo ya shigo, ido ta zaro tare da wata faduwar gaba

Shi kansa saï da gabansa yayi wani mugun faduwa Wanda bai san Dalili ba,

Hakoransa ya washe da alamun murna à fuskarsa ya nuna Yar mahaukaciya ya ce” Princesse,  ke ce ? daman kina nan ?  daman abokina ya taimakeni ya kilace min ke ? 

Yar mahaukaciya ta fara ja da baya cike da tsoron sa da kuma tinanin lokacin da ta kamo rigarsa tana kukan ya taimaketa kar à kore ta daga gidan su ya bige mata hannun sannan ya tunkuda ta, raurau take da idannuwanta tana girgiza kai

Gaban Idriss ya ci gaba da Faduwa tsoro da fargaba suka darsu à zuciyarsa, cikin  kalar tausayi ya ce ” haba Rahama ta, karki ji tsoro na KO ki guje ni, kar abinda nayi à rashin sani ya saka ki guji zuciyar da ta ginu da kaunar ki, kiyi hakuri ki saurare ni dan Allah,   ya mika hannun sa da niyar ya riko nata hannun domin yakan rike hannunta ba tare da wani tunani ba

Yar mahaukaciya ta rintse ido ta ce” don’t tuch me Idriss, karka yarda ka taba min hannuna

Daidai lokacin hajiya hafsat ta taso don ganin wannan ikon ALLAH, shi kuwa wannan wanene ? Mai kalamansa ke nufi da baby ?

Tana isowa ta ce” malan Lafiya ? Wanene kai ? Mai kake SO ?

Idriss ya juyo yana kalonta, gabansa ya fadi haka kawai, ya kaleta tsananin kamarta da Rahama har ya baci, ya juya yana yi musu kalon kurilah, Daidai nan Hajiya Rafi’at suka fito ita da elhaj Muhammad tana rike da banban plat da kwanoni à sama, shi kuwa yana rike da assietoci da cokula da dan kondon fruits sai murmushi take zuba masa shi kuwa yana ta labari

À tare suka juya suka zuba musu ido, inda suma à lokacin suka lura da mutanen dakin,

Cikin nutsuwa Hajiya Rafi’at ta ajiye abincin, ta karbi na hannun mijinta ta ajiye , daidai nan Idriss ya kara matsowa kusan su hajiya Rafi’at dan ganewa idanuwansa wata mai kama da yar mahaukaciyarsa kuma,

Yana karasowa sai ya ga ai wannan elhaj ne uban gidan mahaifinsa, Wanda Tunda abansu ya hadu da shi hanyar arzikinsa ta budu  , shi ya bada goyon bayan karatun sa ma da kuma aljihunsa har ya samu ya cimma burinsa na zama Baban Docter,

Cikin yanayin rudu ya ce” aba, kaine à nan ?

Elhaj Muhammad da har yanzu gaisuwarsa sai ya dan rungume mutun banda mata ya matso yayi masa irin gaisuwar larabawa ya ce” son daga Ina haka ?

Idriss ya juya yana kalon kwayar Idon yar mahaukaciya ganin iri daya da na elhaj ya ce” Aba Ina cikin rudu, naga Rahama na kama da Wa’inan, yayi nuni da su hajiya Rafi’at, ya ci gaba’

Sanan saï naga hasken fatar ta da idannuwanta

Elhaj Muhammad ya karasa fadin” da yatsunta, da hancinta, da tsayinta, da yannayin maganarta duka nawa ne, son kaga *Kanwarka*, *Y’a ta daya da na malaka à nan gidan duniya*

Idriss ya zaro ido ya juyo yana kalon yar mahaukaciya da alamun tambaya à bakinsa

Daidai zata yi magana Mubasshir da saukowansa kenan kuma ya fahimci yannayin Idriss ya ce” *Freind* sunanta *Fadimatul islam* sannan yaron da ya rasu à asibitin ka kaninta ne, ga mahaifiyarta, ga kanwar mahaifiyarta ga mahaifinta sannan ita ba zawara bace ,

Idriss ya ce” Freind please ka kuma wayar min da kai, nasan baka taba yi min karya ba, sannan aba bazai yi min karya ba, ya juya ya kali Yar mahaukaciya da tayi tsuru ya ce” sannan ban ga dalilin da Princess zata yi min karyar rayuwarta ba

Mubasshir ya rintse ido, wai wani Princess, ya kawar da kansa,

Hajiya fadimatu ta ce”mu zauna na fayace maka komai game da y’a ta,

Haka suka dugunzuma suka zauna inda hajiya fadimatu ta gyara zamanta tana yiwa Idriss bayanin duk abinda aka fada mata yan awani da suka shude, Wa’inda Idriss kawai ya kurawa yar Mahaukaciya ido cike da tausayin rayuwar ta,  ashe ita mai mugun gata ce haka ?

Tinaninsa ya tsaya daidai lokacin da kunuwansa suka jiyo masa mugun labari mai rikitarwa mai tsoratarwa Wanda yayi imanin kawai sakarkarun kunuwansa ne suke jiyo abinda ba’a fada musu ba,  toh inba hakan ba à labarin Princess dinsa mai ya kawo cewar an daura mata Aure da amininsa AA Mubasshir ? 

Cikin wani irin yannayi ya juyo da kalonsa wajen Mubasshir yana wani dan murmushi ya ce” Freind wai kaji kunena saï gizo yake yi min KO ?

Mubasshir ya kawar da kansa yana kalon Yar Mahaukaciya,  cikin kakausar murya ya ce” Islam ki je daki ki saka hijab saï ki sauko

Yar Mahaukaciya ta kale shi,  à maganar sa babu alamun wasa à cikin ta, hakan yasa ta Mike a nitse ta nufi matatakalar benen don aiwatar da umarnin AA,

Idriss ya zaro ido ya Mike tsaye yana binsu da kalo ya ce” Mama kina nufin an daurawa Rahama Aure da Mubasshir ?

Hajiya Fadimatu ta zuba masa ido tana kalon sa,

Elhaj Muhammad ya ce” son What’s happen ?

Idriss ya ce” Aba dan Allah kar ku yi min haka, wly ni nake son ta, dan Allah karku huce abinda Nayi mata ta haka, wly wly à rashin sani na aikata haka, aman ni Nafi kowa son zama da ita, ban san ya akayi na kasa sauraronta ba ku yi min rai karku rabani da ita,

Ya juya wajen Mubasshir dake kalonsa yayi saurin rike hannunsa ya ce” broth kafi kowa sannin Ina sonta dan Allah ka ce ka barmin ita

Mubasshir ya kawar da kansa zuciyarsa na bugawa, tabas da ace ba’a rigayi daura masa Aure da Islam ba da ya hakura ya barwa Idriss koda hakan zaiyi sannadiyar rasa farin cikinsa KO rasa nunfashinsa gaba daya, domin Idriss dan uwa ne à wajen sa

Dafa kafadarsa aka yi ya juyo ya sauke Idannuwansa à fuskar wace ta dafa shi, ba Wanda ya san da ta shigo domin hankalin su du ya tashi, dan kuwa Idriss d’à ne,

Hajiya hawau kenan tsohuwa mai ran karfe, Tunda aka gama rikicin iyayen Fadimatul islam hajiya fadimatu tayi kiranta kan tazo ta ga abin mamaki

Tun lokacin da hajiya fadimatu ta fara bada labarin  yar mahaukaciya ta shigo falon domin a bude Idriss ya barshi yana dokin ganin yar mahaukaciya

Cikin nutsuwa ta ja hannunsa suka zauna

Ya jima jikinsa na Bari kansa à saman cinyarta tana tofa masa adu’a har ya daidaita numfashin sa,

Hajiya hawau ta ce” alhamdulilah, alhamdulilah, Idriss ka dawo cikin hayacin ka Tunda har ka tina ta,

Idriss Kasan cewar wani baya auren matar wani sannan wani baya haifan d’an wani, tabas mun hada auren nan dan gujewa Islam rigimar mahaifiyarka aman ka Sani kafin mu hada shi sai da muka yi listahara mun saka anyi mana tsakanin ka da ita, da kuma tsakaninta da Dan Aljannah, cikin ikon ALLAH ALLAH ya dora mu kanta da dan aljannah domin shi muka barwa zabi ,shi ya san abinda ke boye

Ka dauki wannan abin à zuwan kadarar ubangiji Idriss, karka manta wani ransa ya rasa, wani ya rasa mahaifiyarsa KO mahaifinsa KO matarsa KO dansa aman yayi hakuri, Idriss Tunda kuwa Bawa yana iya jure rashin mutun dungugun à gidan duniya lale zai iya rasa komai ya dangana da ikon ALLAH saï ALLAH ya jikansa ya jagoranci lamuransa,

*Ya kai jikana Ina yi maka gargadi da kawar da kai daga hukuncin ALLAH saï kaga ka gama da duniya lafiya*

Ba Idriss ba elhaj Muhammad kansa saï da zuciyarsa ta karaya da wannan gargadi na wannan tsohuwa mai hangen nesa da yarda da adinninta wato *Musulunci*

Idriss ya share hawayen sa ya dago rinanun idanuwansa ya ce” na gode hajiyata, Allah ya kara Lafiya, insha ALLAH daga yanzu na dena wannan maganar, Allah ya bani Wanda zata maye mini gurbinta

Gaba daya suka amsa da ameen, inda ya mike suka gaisa da Mubasshir ya ce” hei freind ka kula min da kanwata,  kar Inji kar in gani abinda zai saka ta hawaye cos da Sahla da Islam Ina jinsu à jinnin jikina

Mubasshir ya jawo shi suka rungume juna suna dan bubuga bayan juna (Maza kenan da manyan ne da anga kuka lol)

Bayan ya dawo daga rakiyar Idriss ya tarar suna cin abinci su duka sai dariya suke, suna labari harda hajiya hawau, ya nemi waje zai zauna Hajiya Fadimatu ta ce” kai, tashi ka sauko min yarinya ta ci abinci mana

Mubasshir ya Mike ya haura sama, yana Isa ya tura dakin ya shiga,

Hangota yayi zaune ta hade kanta da gwuiwarta tana rusa kuka,  gabansa ya yanke ya fadi à ransa ya ce” na shiga uku, kardai kukan rabata da Idriss ne take, tana nufin tana sonsa kenan ? Idan ba haka ba Tunda ta hayo take kukan nan ? Bazai yuwu ba,  cikin bacin rai ya nufeta………………………………………………………………………………………………………………

wai Ina Sahla ne ?  Fadimatul islam Wa take SO ne ? ??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀??‍♀ mai kuka Dauka darasi à wannan novel ?  Daga taku yar mutan Niger??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                          69

Cikin kakausar murya ya ce” ke,  kukan me kuma kike ?

Da sauri yar mahaukaciya ta dago kanta tana kalonsa, à ranta ta ce” oh ni *Yar Mahaukaciya* an hadani da bahagumen mutun, shi bashida aiki sai fada, hum dan baya sona ne da yana SO na da ya tatale ni,

Mubasshir ya ce” kalon fa ?

Cikin sauri ta ziro kafarta tana goge hawayenta tayi tsaye kanta à kasa

Ya lumshe Idannuwansa ita kam akoy Kira,  à fili ya ce ” mu je ki ci abinci KO ?

Ya juya yayi gaba, yar mahaukaciya ta biyo bayansa

Hajiya Rafi’at ta ce” aunty yaushe ne y’ar taki zata tare ne ?

Hajiya fadimatu ta ce” da Nayi niyar karshen satin nan, To da kika Zo da uzurin nan à yanzu kam ban Sani ba

Elhaj Muhammad ya ce” ni wannan sha’ani naku na mata ban san kansa ba, please ku bani matata muyi tafiyar mu tare chainar nan dan ganin wannan matar yanda zanyi da ita, sai ku shirya y’ar ku, madame a shirye take, ya karashe zancen yana kalon hajiya hafsat,

Tayi saurin sada kanta kasa, ita dai bata san yanda zata yi da elhaj ya dena saka ta kunya ba

Hajiya fadimatu tayi dariya ta ce” to Yaya kika gani kanwata hakan yayi ?

Hajiya hafsat ta kara sine kai ta ce” ni fa ku dena tambayana na please du yanda kuka tsara hakan za’ayi

Gaba dayansu suka kwashe da dariya domin yanda take maganar uwa ta zura da gudu, Hajiya Hafsat kenan sarkin kunya

Karshe dai sai tsakanin hajiya fadimatu da hajiya Rafi’at aka yanke shawarar inda fafur hajiya Fadimatu ta kafe à kan Hajiya Rafi’at ta zauna à gidan ta saboda ba kowa à gidan su dan su elhaj Muhammad da hajiya Hafsat tafiya zasu yi kasar chaina wajen hajiya Falmata,

Washe gari Mubasshir ya tashi ya tafi gidan sa bisa umarnin mahaifiyarsa KO dan yayi nisa da Fadimatul Islam su samu su tsumata da kyau domin tun daga sokoto suka dauko aunty Habibu M Shehu ta gyara  Fadimatul islam inda ta dage ka’in da na’in tun daga kanta har tafin kafarta gyara suke sha kala daban daban,

Yau à dama wannan à Bata ta sha, in an jima ta shiga cikin ruwan tirare, Idan ta fito ta tsuguna à na tsuguno,  da kanta take shafe mata jikinta da mayukan da ta hada masu kara santsin fata, da laushi, da kyali,  harda rami aka yi daidai da jikinta Wanda Aunty habiba take rufeta da bargo ta shiga tirara mata wasu magungunan,  ita kanta Yar Mahaukaciya mamakin kanta take domin har kara kalon kanta take à madubi, gashin kanta kuwa an hada mai wani mayen hadi na tirare an daure shi tamau har wani dan kaikayi yake mata aman fir aunty habiba ta ki ta kunce shi har sai ana Yau tarewa tukunan, dan ma tana cikin fashin sallah,

Mubasshir Tunda ya koma gidansa abin mamaki ya tarar da Sahla,  sannan da kanta ta kawo masa kanta yayi yanda yake SO da ita ba tare da tayi masa korafin komai ba

wata dawowa da yayi daga gidan Hajiya Fadimatu,  ya dawo da takaicin hana masa ganin Islam da suke yana shigowa yake shinkayo zance kasa kasa, hakan ya sa ya raba kadan yana sauraro

hajiya Marhaba ta ce” dadina da ke gajen hakuri,  Ina SO ki shige masa sosai da shi da matar da uwar tasa, ke KO yau ya dawo ki je dakinsa da kukan kissa da komai kiyi masa nunin mai yasa bazai hada kanku tun kafin ta iso ba, kina SO ya kaiki ku saba tun wuri dan zaman duniya ne zaman waje daya kina SO ku saba da yar uwarki,  ke kiyi masa nunin ke da za’a taimake ki ma da dankaren bukatar sa ai ke aka kamawa

Mubasshir ya rintse ido na takaicin sirikarsa ce ta san sirinsa ?  Ya kuma kashe kune  dan Jin karshen tugun sirikarsa,

Sahla ta ce” haba mama, yanzu haka baki ji irin yanda nake kalonsa ba, Jin haushinsa nake har cikin raina, ya cuce ni ya cuce ni, gashi dan cikin da na samu garin matse matsen naki kin matsa min abinda ya tafi,  à ace baki matsamin komai ba ai da yanzu mun samu abinda zamu ci gadon KO ?

Mubasshir ya dafe kansa sauran kadan ya kurma ihun kuka, harda cikinsa sirikarsa bisa goyon bayan matarsa aka zubar ?

Hajiya Marhaba ta ce” dadina da ke ana nuna miki gabas kina yin yama,  To ki saurareni da kyau ki ji abinda boka ya ce” Ya ce idan kika kawo masa zobon da maganin à ciki kiyi iya yinki da kisar ki à ranar da zai konta da amaryar ki nuna masa ke zaki raka shi, ki tabatar da ya sha wannan zobon to zaki sha mamaki, domin harda bindin kare da na jaki aka markada maganin, idan mazakuntarsa ta Mike sai ya kwana biyu cir yana hauka à samanta kinga kuwa mutuwa zata yi, idan ta mutu shikenan ayi masa daurin rai da rai shikenan arziki namu domin har uwar sai na saka an rufe mata baki sannan à saka matsananciyar gaba tsakaninsu ita da iyayen na mahaukaciyar,

Sahla ta ce” mama kisa fa ?

hajiya Marhaba ta ce” ke sakarya ce, du irin rashin mutuncin da suka shuka miki shine zakiji tausayin aikasu lahira ?  Idan bakya SO sai nayi tafiyata kiyi ta zama ki zama abinda zaki zama

Sahla tayi saurin rikota ta ce” aa mama zan aikata karki damu

Da kyar yake iya daga kafarsa ya nufi motar sa ya tada ya fita,  biyu biyu Idannuwansa suke gani tuki yake yana cije lebensa burinsa ya ganshi à jikin mahaifiyarsa

da kyar ya samu ya iso inda yana sauka daga motar ya fadi nan kofar gidan su domin shi du ji yake har ya shiga cikin gidan

Masu tsaron kofar suka nufo shi da gudu suka cicibe shi su wajen biyar suka yi cikin gidan da shi inda da sauri daya ya tura suka shiga da shi

hajiya Fadimatu, Hajiya Rafi’at, Aunty Habiba, Fadimatul islam (Yar Mahaukaciya)  suna zaune Suna ta hira suna dariya suka ga an shigo da AA rigija rigija tamkar ba numfashi à tatare da shi,

à tare suka Mike suna rige rigen tambayar Lafiya ?

hajiya Rafi’at ta ce”accident ba yayi ?  Mai ya same shi ?

Daya daga cikin securitien ya ce” ma’am yanzu ya ISO har ya fito kawai saï ya fadi

Daidai nan Yar mahaukaciya ta dauko Bokici da ruwa da hankici  fari mai laushi ta mikawa hajiya Fadimatu wace jikinta banda Bari ba abinda yake, ta ce” KO don mun hana shi ganin matarsa ne ransa ya baci haka ? 

Aunty Habiba da Bata san kan abin ba ta ce” Aunty à tafi asibiti da shi man ?

Hajiya Fadimatu ta ce” ba accident yayi ba, ba na asibiti bane ku mu kama da ada’a domin irin haka na jima ban ga irin haka ba,  Allah ya sa ya tashi domin ban ga alamu ba sai tsayin kwana

gaba dayansu suka zaro ido inda yar Mahaukaciya ta fashe da kuka ita Sam idannuwanta sun rufe ta zauna ta dago kansa da kyar dan kuwa jikin nasa ya saka ta dora saman cinyarta suka shiga adu’a tun karfin su ( kun manta abinda Elhaj Muhammad ya fada na ayi masa wanka KO ba mai yi à kirawo sisterna? ??)

toh fa shin AA zai farka kuwa, karfa kuyi la’akari da du à film da novel acteur yana tashi ku dai kuyi fatan ya tashin,??, wani irin mataki zai dauka ne idan har ya farkan ?  Shin Sahla ta cancanci yafiya kuwa ?  Shin idan har wannan tugun bai ci ba zasu kuma shirya wani ? Ya labarin yan honymoone lol, kumuje zuwa??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                      70

Adu’a suke tun karfin su, aman jikinsa sai kara daukan zafi yake,

Hajiya Fadimatu ta daga hannunsa ta saki hannun wani irin nauyi, tayi saurin kawar da kanta ta rintse idannuwanta gabanta na mugun faduwa

Yar mahaukaciya ta ce” mama Lafiya ?  Ba alamun sauki ?

Hajiya Fadimatu ta tataro dukan KOkarinta ta ce” ba komai y’ar Fadimatu,

Yar Mahaukaciya ta ce” KO na Kira Yaya Idriss ne ?

Hajiya Rafi’at ta Gyada mata kai, hakan yasa ta ajiye kansa à hankali ta nufi wayar falon ta danawa ofice dinsa Kira domin ta san kawai yana ofice

Jin abinda ke faruwa ya saka shi barin Ofice dinsa ya kwaso yan kayan aikinsa ya nufi gidan su abokinsa domin ceto ransa

Yana zuwa ya tarar still sun dukufa sai adu’a suke masa zuwa lokacin Yar Mahaukaciya kam ta fara zubar da hawaye domin hannun sa baya KO karyuwa

Yana zuwa ya shiga tambayar abinda ya faru, inda hajiya Fadimatu ta fada masa komai na idan yayi irin haka harda na Karshe da yayi bai kai hakan ba

Idriss ya ce” Mama na karshen da yayi mai akai masa yaki yin nisa ?

saï à lokacin suka tuno jawabin mahaifin Fadimatul islam (Yar Mahaukaciya)  kan idan hakan ta faru à tabatar da an saka shi à ruwan kankara sosai cikin ikon ALLAH zai kawo hankali

Nan ta kwashe ta fada masa yanda Elhaj Muhammad ya fada,

Idriss ya ce” to wankan za’a yi masa ai mama

Hajiya Fadimatu, Aunty Habiba, Hajiya Rafi’at da Islam gaba daya suka zuba masa ido suna kalon sa

Hajiya Fadimatu tayi karfin hali ta ce” wankan KO ?  To ya zamu iya kai shi dakin ?

Idriss ya Mike gannin yanda duk suka wani tsure ya nufi kofa yayi Kiran securitiesn suka taho suka cicibi AA suka yi dakin Yar Mahaukaciya da shi inda ta Mike ta bi bayan su domin hada ruwan wankan

Baban bokici ta cika da kankara ta shiga bayin ta zagine tana sauyewa à cikin bahon wankan Daidai nan Hajiya Fadimatu ta shigo ta kama mata suka juye kankarar,

Suna gamawa su Idriss suka shigo da shi à talafe da dan gajeren Wando à jikinsa Yar Mahaukaciya tayi gagawar lafewa à bayan Hajiya Fadimatu , suka saka shi à cikin bahon ruwan da yayi mahaukacin sanyi

Suna saka shi securities suka juya suka fita inda su Hajiya Fadimatu ma suka yi niyar fitar dan barin Idriss da AA ya zuba masa ruwan à jikin sa

Idriss ya ce” Mama ku dakata ku matso mu yi masa tare

cikin sagewar gwuiwa suka juyo islam na biye da ita tamkar jela kanta à kasa suka shiga daban ruwan suna zuba masa har à cikin sumar kansa

Basu dau wani lokaci suna hakan ba ya ja wani dogon numfashi ya bude idanuwansa tamkar gauta dan ja à fuskar mahaifiyarsa domin ita kawai ya fara tozali

ido ya rintse yana Jin yanda kankarar nan ke ratsa masa jijiyoyin jikinsa, kokarin zama yake aman sulbin abin wankan ya hana shi,

Ya damki hannun mamansa ya kafe ta da ido saï ga hawaye wasu na korar wasu

hajiya Fadimatu ta kasa jurar ganin hawayen yaronta Bata san sanda ta jawo shi jikinta ba du da tsananin sanyin ruwan nan ta ce” Hasbunnalahu Wa ni’imal wakim, Ya Salam, shin yaushe dan Fadimatu zai daina daukan bacin rai da zapi haka ?  Shin yaushe zai lazumci fadin Inalilahi Wa’ina ilaihir’raj’une à duk lokacin da yaji ransa ba Daidai ba ?  Dan Fadimatu irin wannan zuciya ba’asan musulmi da ita, Tunda ka yarda da kalmar La’ila ha ilalahu MUHAMMADU’rasululah salalahu alaihi Wa Salam ka gama komai, Tunda ka yarda da shi kadai ya Isa yayi kuma shi kadai ya Isa ya hana mai yasa zaka kuma saka damuwar wani à ranka ?  haba dan Fadimatu yanzu fa girma ya hau kanka, Dan mai bazaka gyara shi ba ?

Kalaman mahaifiyarsa na sauka à kunan sa tamkar warware masa kalmomin bakinsa ake cikin ikon ALLAH ya fashe da kuka mai tsanani ya kara rike mahaifiyarsa yana tunanin da mugun nufin su sahala ya kasance da an halaka masa mahaifiyarsa dan kuwa bazata juri hakan ba,

yana kuka tana hamdallar Jin muryar sa domin Bata sakawa ranta zata ji muryar sa a kusa kusan nan ba,  hakan yasa ta barshi yayi mai isarsa sannan ya shiga ajiyar zuciya, du wannan abin bai lura da Idriss da Yar Mahaukaciya dake zaune dirshen à cikin bayi suna nasu hawayen ba

Cikin yanayin tausayi ta ce” fada min Wanda ya bata maka haka ?

AA ya lumshe Idannuwansa, da ace zai iya da ya boyewa mamarsa wannan lamarin, saï dai Ina bashida sama da ita, damuwarsa damuwarta ce,  Dan haka ya bude bakinsa yana hawaye yana fada mata gaba daya abinda kunuwansa suka jiyo masa à gidan sa wato tataunawar Matarsa ta suna da Sirikarsa

Idriss dake saurare yafi kowa firgita inda ya rushe da kuka tamkar mace ya hada kansa da garun bayin ya shiga buga kansa da garun yana tir da halayen mahaifiyarsa da Kanwar sa

sai à lokacin AA ya lura da mutane à bayin bayan mahaifiyarsa,  da sauri ya Mike ya nufi Idriss ya jawo shi da hanu guda ya ce ” Idriss, baka da hankali ne ?

Idriss cikin kuka ya ce” banga anfanin rayuwata ba Mubasshir, Ba yau ba nake yiwa su mama à kan duniya aman abin har ya tsalake baiwar ALLAH (Hajiya hawau) ya fito kai ? Shin Mamana Bata kaunar saduwarta da rahamar ubangiji ne ?  Ta raba d’a da mahaifiyarsa, ta kyamaci nakasasu, ta wulakanci talaka, yanzu tana kokarin halaka rayuwar jama’a da dama dan kudi?

why ? 

Hajiya Fadimatu ta karaso gabansu ta ce” ya ku yayana ku saurara, ku kasance masu yiwa iyayen ku adu’ar alkhairi à duk halin da kuka tsince su, Idriss tsananin ka da mahaifiyarka adu’ar shiriya da ita da kanwar ka,

Ta juyo wajen AA ta ce” ka Sani da 1 ALLAH ya kawo ka har ka tsinci wannan tataunawar ya saka da Rahama, abinda nake SO da kai shine kayi ta adu’a ba dare ba rana à duk halin da ka tsinci kanka à ciki kan ALLAH yayi maka jagora, sannan idan ta baka karka sha, ta kali Idriss ta ce” Kayi hakuri Idriss kayi hakuri Haka Taka Kadarar take, yanzu Baban abinda ya dace muyi shine mu kwatanta musu cikin nutsuwa idan da halin kubutar su cikin ikon ALLAH zaku ga sun kubuta

Idriss ya sada kansa, shi yanzu wata irin kunyar su yake ji ya zaiyi da iyayen sa ne ?  Ina zai saka ransa ?

Hajiya Fadimatu ta juya jikinta à matukar mace ta nufi waje tana mamakin wannan lamari

Yar mahaukaciya ma ta juya da sauri zata fita AA ya ce” Islam dakata

Cak ta tsaya tana kalon kasa inda Idriss ya juya à nitse ya silale daga bayin ya fito matatakalar benen ya zauna yana kalon kasa

Aunty Habiba Y’ar sokoto ta kali Hajiya Rafi’at ta ce ” sister banga fitowar amarya ba fa, kar aikina ya koma baya, ta karashe tana murmushi

Hajiya Fadimatu da gaba daya jikinta yayi mata nauyi ta ce” au ai mantawa Nayi na barota à dakin, please sister tashi maza ki sauko min da ita domin yaron nan sai adu’a

Hajiya Rafi’at ta Mike tana murmushi ta nufi matatakalar benen tana hawa kunuwanta na jiyo mata sheshekar numfashi inda tayi tsai gabanta na faduwa tana son gane kukan waye ?

Cikin sasarfa ta karasa daga kusan mai kukan gaba daya jikinta ya mutu cikin wata irin murya ta ce” komai yayi zapi ka barwa sarki ALLAH, shi zai sanyaya maka Idriss,  kadarar ka mai sauki ce Idriss domin da ranka da lafiyarka to sai ka barwa ALLAH komai shi zai warware maka damuwar ka

Tunda ta fara magana ya tsayar da kukan da ya Zo masa yana sauraron duk wata Kalma da zata furta Har ta dasa Aya, ji yayi inama Bata rufe bakinta ba domin wata iriyar nutsuwa da take sauko masa lokacin da Take maganar, dago kansa yayi ya zuba mata ido, tana maganar ashe Bama shi take kalo ba, tana kalon kasa, saurin kawar da kansa yayi daga kalon kurular da ya kafeta da shi yana furta a’uzubillah haka kawai ya kare matar mutane da kalo, cikin yanayin sauri ya Mike yana gagawar magana ya ce ” na na na gode,

Da sauri ya raba ta gefenta ya fice tamkar tana biye da shi dan ta kama shi,

Hajiya Rafi’at ta lumshe idannuwanta maimakun ta nufi dakin AA sai ta shige dakin Hajiya Fadimatu ta Konta à gefen bed ta rufe idannuwanta tana tunanin irin rudanin wannan family da kuma shi Idriss Da Allah ya tsame daga halayen mahaifiyarsa

Kalon bayanta yake yana takowa à hankali har ya ISO Daidai inda take tsaye Tunda ya kama sunan ta, a nitse ya dan rage tsawon sa ya dora kansa à wuyanta yana sinsinawa

Yar Mahaukaciya tayi saurin juyowa tana kikifta ido cikin inda inda ta ce” Yaya  Lafiya ?  Mainene kuma hakan ?

Mubasshir ya rintse Idannuwansa ya kuma budewa gaba daya jikinta wani irin santsi da wani shegen kanshi yake, kara janyota yayi ba tare da ya Bata amsar tambayoyinta ba ya hadata da jikinsa,

Gaba daya jikinta Bari yake domin har à lokacin jikin AA banda gajeran Wandan nan ba komai, Yar Mahaukaciya ta dimauce ta rasa  mai yasa yake sha’awar hada jikinta da nasa,

Katse mata tinaninta yayi sanadiyar jan dan kwalin kanta Wanda à dole aunty Habiba ta konce mata shi dan al’adarta ta dauke dole ta wanke mata shi tayi wankan sallar Azahar, hakan ne ma ya saka aunty habiba sakawa a kirawo Yar Mahaukaciyar dan tana gudun kilu ta jawo bam,

Yana jan dan kwalin ya fadi kasa gashin ya zubo da dan danyatar sa ta mayukan wankin kan da aka yi anfani da su wajen wanke kan, Hancinsa ya kai à hankali ya sisina ya lumshe Idannuwansa cikin nutsuwa ya shiga cusa hannunsa à cikin gashin yana kara lumshe ido

yar mahaukaciya ta zaro ido da sauri ta dago idannuwanta tayi arba da fafadan kirjin sa Wanda à Yau ne ta fara ganinsa à fili haka, gabanta ya fadi ganin irin baiwar ni’imar da Allah yayi masa gashine konce yayi sidik da shi s kyalin ruwa yake,  dago da kanta tayi dan Jin bugawar zuciyarsa ya tsananta kan na da,

Tana dago da kanta tamkar Jira yake ya hade bakinsa da nata ya shiga kissing,

Yar Mahaukaciya ta zaro idonta ta shiga kokarin kwacewa, aman Ina karfin ba daya ba, ganin zata Bata masa lokaci ya saka shi yayi sama da ita ya fito daga bayin yayi saman bed da ita

wutar dakin ya mika Hannu ya kashe sannan ya ci gaba da kissing din Fadimatul islam wace daidai wannan lokacin tana kokarin fita daga hayacinta dan ita kanta à Yau tana Jin dadin tabatan da yake sakamakon tsumin Aunty Habiba  Mai Abin Mamaki Y’ar sokoto,

Zuwa wani lokaci AA yayi fatali da Rigar Yar Mahaukaciya wace ita kadai ce à jikinta sai zani da ta Daura,

Arba yayi da yan biyu sunai masa hello, bai san  sanda ya kai bakinsa domin kawo musu agaji ba,

Su duka nunfashin wahala suke saukewa Daidai nan AA ya ce fa yana bukatar isar da sakonsa banban birnin,

Saï à wannan lokacin Y’ar Mahaukaciya ta bude idannuwanta ta zuba masa ido inda ta lura da gaske fa yake,

Tura shi ta shiga yi tana Kiran sunansa aman Ina aikinsa yake ba sasautawa, kukan wahala ta saki tana tura shi tun karfinta aman Ina baya Jin duniyarta bale ya saurara mata,

Kuka take tana yakushinsa domin ji take tamkar zata bar duniyar, tun tana yi da karfinta har ya kasance KO hannunta ta kasa dagawa tana ta zubar da hawaye saï da bukatarsa ta biya dan kansa sannan ya kyaleta ya koma gefe yana sauke ajiyar zuciya( ? Leila ba ruwana)

Ganin shirun yayi yawa gashi wayarsa saï ringin take Sahla na kiransa mai yiwuwa dan taga dare yayi ne bai dawo ba take kiransa ya saka Hajiya Fadimatu ta Mike ta haura sama dan ganin tataunawar mai suke haka da yar aiken, da Fadimatul islam din, da kuma Oga AA din da suka shantake suka kasa fitowa har magariba ta kawo kai ( Jama’a ku mu taro Maman Mubasshir karta sume mana?????????????????????????????????????????Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                          72

Tana karasa hawa matatakalar Hajiya Rafi’at ta fito daga dakinta tana hama da alamun baci à idannuwanta, Hajiya Fadimatu tayi galala tana kalonta ta ce” Madame Ashe baci kuka shiga ?

Hajiya Rafi’at ta zaro ido domin sai à wannan lokacin aikin Hajiya Fadimatu ya fado mata à zuciyarta , da sauri ta dafa kirjinta ta ce” Ya Salam, kardai har yanzu Bata fito ba ?

Hajiya Fadimatu ta kwalalo ido ta nufi dakin da sauri ta shiga konkwasawa,

Yana zaune saman salaya ya kurawa bed din ido yana son ya tashe ta yana tsoron Jin kukanta, gashi magrib har tayi, ya lumshe ido yana ta adu’ar ALLAH ya tsagaita fushinta shi har ga ALLAH da ya san cewar Islam budurwa ce da baiyi gigin samun nutsuwa da ita à wannan yanayin ba, sannan à cikin gidan nan ba, no da shi kadai ya san irin yanda zai kawatar da farkon daren su shi yasa akayi hani da zargi, zargi ba kyau, zato zubine koda ya kasance gaskiya ne, Ya bude idanuwansa ya furta ” i love you wifey, i really love you, insha ALLAH zan sadaukar da dukan farin cikina gare ki, 

Shi Sam haduwar sa da mahaifiyarsa bai daga masa hankali kamar fushin Angel dinsa, bai san ta yanda zai warware irin yanda ya rinka jifanta da maganganu mararsa dadi, harda hadata da Zina ba,

Bubugawar kofar ya dawo da shi daga duniyar nadamar da ya afka da kuma begen matarsa , da sauri ya Mike ya nufi saman bed din ya hau ya yaye mata rufar bargon da yayi mata, cikin magagin bacin wahala ta bude idannuwanta ta zuba masa su ai kuwa saï ta barke baki ta saki kuka

Mubasshir ya rintse ido ya dagota ya rungume à jikinsa à hankali yana furta” shiiiiiiiiit baby is OK, daina kukan haka please,

Yar Mahaukaciya ta ce” zapi jikina, ciwo à jikina , wallah naji ciwo baba, ka Kira min mama

Mubasshir ya ce ” Bara na taimaka miki sai na Kira miki itan Kin ji ?

Yana gama fadin haka ya dagata cimak ya nufi bayin da ita stilll ba’a daina buga kofar ba, harma an shiga danna Kira à waya, yana sane yayi bilis da su,

Suna shiga ya direta à bahon wankan cikin ruwan zapi , Yar Mahaukaciya ta rintse ido ta rike hannayansa hawaye na zirara daga idannuwanta, yana yi yana canza mata ruwan zapin har ya gamsu da gashin nata sannan ya koma gefe ya ce tayi wankan tsarki,

Yar Mahaukaciya ta kawar da kanta domin ta san KO mai zata yi bazai yarda ya fita daga bayin ba, hakan yasa kawai ta zagine tayi wankan ta duk da har à lokacin da zafin dan dai bai kai na dazun ba

tana gamawa ta Daura banban tawul a kirjinta tayi kokarin fitowa,

Da gangan ya tsareta da ido har ta fito daga bahon wankan, ta fara tafiya à hankali tana cije lebe, karasowa yayi ya dagata yayi tsakar dakin da ita,  ita dai ba abinda ta ce masa shi kuwa sai leken yanayin fuskarta yake,

Haka ta zumbula doguwar rigarta ta saka hijab ta kabarta sallah,

Saï à sannnan tunanin karfa suyi tunanin KO wani abin ne ya same su ya saka shi mikewa Sam bai dauke zanin gadon da suka kwonta samansa ba,

Yana budewa ya gansu à tsaitsaiye, abin mamaki harda su Hajiya  Hafsat maman Yar Mahaukaciya, Idannuwansa ya zaro ya ce” Au su aba kun karaso ? Dama kuna hanya kenan

Hajiya Fadimatu ta ce” son suna gidanku dai ba suna hanya ba, Ina yarinyata take ?

Elhaj Muhammad ya ce” Kai Hajiya ni dama tsorona KO jikin nasa ne Tunda naga kun daga hankali haka, ashe lafiyarsa lau, Dan haka ni kunga tafiyata, son Zo mu je akoy Yar tataunawar da nake SO mu yi

Mubasshir kuwa ya raba ta gefen mamarsa yana dan sine kansa dan kuwa tana iya zabga masa mari a kan y’arta,

suna sauka Su Hajiya Fadimatu suka nufi dakin inda Hajiya hafsat tayi gaba abinta duk da irin yanda zuciyarta take cike da mararin ganin y’arta aman wani abin da kunya,

suna shiga suka tarar da Islam à konce saman salayar da sauri suka karasa wajenta suna tambayar Lafiya ?

Hajiya Fadimatu ta dagota ta ji jikinta zapi rau,  ta ce” subahanalah Yar Fadimatu zazabi ne KO meye jikinki zafi haka ?

Ita dai Yar Mahaukaciya Bata ce komai ba idannuwanta à rufe tayi lamo à jikin Hajiya Fadimatu tana sauke numfashi

hajiya Rafi’at ta matsa kusan bed din dan ta dauko abinda take hange à yashe, ido ta zaro ganin abinda yake saman bed din, à hankali ta furta ta faru ta kare, da ido ta yafito Aunty Habiba ta taso ta ISO itama Idon ta zaro aman ita tayi magana ta ce” Eyah AA ba’ayi hakurin ba kenan

hajiya Fadimatu ta dago ta zuba musu ido, yanayin fuskarsu kadai ya fasara mata abinda suka gani, tsam ta rungume Islam à jikinta, à ranta ta furta she is virgin, ya zama wajibi à mikata gidanta à gobe gobe dan haka al’adar take, ta kawar da kai cike da takaicin Mubasshir,

À hankali ta Mike da Islam ta nufi kofa da ita dan ta kaita dakinta ta kula da ita, su kuwa suka zagine dan gyara dakin

Sahla ce sai kai kawo take a tsakar tamkamemen falonta da waya à hannunta tana bugawa tana tsaki,

Dakin taji ana dannawa ta tashi da sauri ta nufi kofar dan budewa, tana budewa taga wani sécurite ne dan soja tsaye ya ce” Madame oga ne ya ce à sanar da ke Yar tafiya ta kama shi wayarsa à rufe aman ba zai jima ba

Sahla ta ce” What ?  Kan uban cen karfa ya je ya ruguza min tsari, ba shiri ta nufi dakinta ta dauko dan gyalenta ta nufi gidan mahaifiyarta,

Daidai ta ISO Idriss ya ISO suna hada ido yaji wani irin haushinta da tsanar halayenta sun darsu à zuciyarsa, toh uban me ya fitar da ita daga gidanta à wannan tsohon daren, cikin Jin Haushi ya bude matarsa ya nufi tata da mugun bacin rai

to fa kardai garin bacin rai Idriss ya tona abinda AA ya ji ????? ????????Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                          73

*Manzan Allah sallallahu alaihi wasallam ya ce wanda ya karanta subhanallahi wabi hamdihi subhanallahil azim,,, sau dari a rana za’a yafe masa zunubansa koda sun kai yawan kumfar kogi*

Yana karasowa ya tsareta da ido ya ce” Sahla mai kike à nan gidan da tsohon daren nan ?

Sahla ta yatsina fuska ta ce” wajen Mom na Zo,

Ta raba ta gefensa tayi shigewarta

Idriss ya sauke ajiyar zuciya ya ce akoy ALLAH,

Tana shiga ta ce” Mom Ina ta Kiran wayarsa tana ringin baya dagawa

Daidai zata yi magana Mubasshir ya Kira ta, cikin rawar jiki ta daga ta kara à kunenta

Mubasshir bisa umarnin elhaj Muhammad da ya tsare shi da ido ya ce” Wifey, kiyi hakuri Ina wajen aiki wata gagarumar kongila ce ta sameni daga wajen sarki,  so ki kular min da kanki, sannan ki tanadar min Abu mai dadi ki tsumayi tukuicin ki

Sahla da tayi Shiru tana sauraron zazakar muryar mijinta ta rausayar da kai ta ce” i miss u my man sai ka sauko

Mubasshir yayi murmushin yake ya ce” miss u too wife, bye-bye, kit ya kashe Kiran ya dora kansa saman kujerar da yake zaune

Elhaj Muhammad ya yunkura ya ce” Saki, Saki ?  No saki ba shine solution ba, ka tsunduma matar ka à tsananin kaunarka, idan har da rabon ta tsira da ita da mahaifiyarta to zasu daina mumunan nufin su, idan kuwa basu da rabo ne, To ka Sani ALLAH baya baci, shi ya san yanda zaiyi da su,

Mubasshir ya Gyada kansa irin ya gamsu da bayanan mahaifin matar sa,

Elhaj Muhammad ya ce” ka huta son bara na leko madame

Mubasshir ya yi murrmushi, yanayin soyayar Sirikan nasa yana matukar birge shi, yana son yin koyi da su, à hankali ya lumshe Idannuwansa yana tuna moment dinsa da Islam, islam cikakiyar budurwa ce, yarinyar da tayi rayuwa à bola, gardawan maza suka sauketa, lale ya yarda Allahn nan shi ne mai karewa, domin ita Yar gatan ta shigo à bude ita kuwa Yar bolar ta shigo à rufe, à hankali ya furta da banbanci tsananin ku à zuciyata, Zanyi iya yini dan ki ringa jina à jinin jikin ki my Islam

Maman Mubasshir ce zaune tana Jiran Aunty Habiba ta gama hada ruwan dumin da zata kuma gasa Yar mahaukaciya, gefe guda su Hajiya Rafi’at ne zaune suna labarin tafiyar su,

Maman Mubasshir ta juya ta kale su ta ce” na kula ba mai kama min y’a ta KO ?

Hajiya Rafi’at da ta san ita ce da Laifi tayi saurin tasowa ta ce” Eyah maman islam ai na Zo na kama miki kika kiya kuna fushi kan dan Aljannah,

Hajiya Fadimatu ta kawar da kai ta ce ” lale fa dan Alhannah, Ai yau KO Aljani yake idan ya shigo sai na hadu da shi

aunty habiba ta fito ta ce” Aunty na hada aman kiyi hakuri mu yi mata aikin ni da Rafi’at

Hajiya Fadimatu ta dago ta kan Yar mahaukaciya wace du tana Jin su, su basu san abinda ya sameta bane zasu ci gaba da sakata à ruwan tiraren nan ?  (Wa ya fada miki ?)

Da sauri ta Mike tana kakawar da kanta ta ce” Mama zan iya fa,

Ta juya tana kokarin yin sauri idannuwanta sai rufe su take tana cije lebenta, har ta shige bayin suka Mara mata baya

hajiya Fadimatu ta zauna Kusa da Hajiya hafsat ta ce ” sister ya zakina nunawa y’ata halin KO in kula ne haka ?  Kin ga fa irin wahalar da ta sha na rashin ki aman sai Ina ga bakya Bata kulawar da ya dace da ita

hajiya hafsat ta zaro ido ta ce” Lah aunty, wace kulawa kuma zan baiwa islam wace ta fice Wada kike Bata ?  Kin tarbeta à lokacin da kowa yake hantarar ta, kin zauna da ita ba tare da kyama ba, kin sakata à hanyar samun ilimi, kin koyar da ita girki, kin koyar da ita tsaya, kin aurar da ita ga miji mafi daukaka à rayuwarta mai kuma zanyi mata ?  Aunty ki Sani wly wly islam kece mahaifiyarta domin ni haihuwarta kawai Nayi, har kunyarta nake ji a zuciyata, Ina Jin dacin irin rayuwar da na gana mata,

Ta karashe zancen tana kokarin mayar da hawayenta

hajiya Fadimatu ta ce ” karki ringa tuna baya, abinda kika aikata ba à cikin hankalinki ba kike yiwa nadama ?  Haba sister ai bai dace irin haka ba, na Sani sarai islam Ina bata kulawa aman ki Sani ya zama wajibi kema ki ringa sakata à jikinki domin ba komai zata iya fada min ba, KO daman can islam akoy zurfin ciki bale yanzu da yaron nan ya yi mana haka, kina gani fa irin saurin da ta kwasa du dan kar à gane baiwar ALLAH, Dan haka muna barar hakan

hajiya hafsat ta kawar da kanta tana murmushi à fili ta ce” korafinku ya karbu

à gaskiya na san Ina jinkiri wajen posting, aman Ina neman afuwarku kun san yau da gobe sai ALLAH, abubuwan ne sai à slow, thanx à lot??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                          74

*Uwa Tana Iya Kula Da ‘ya’ya Sama Da Goma Amma A Wasu Lokutan Sai Ka Tara ‘ya’ya Goma Sun Kasa Kulawa Da Uwarsu Guda Daya!!! Yakamata Musan Cewa Abubuwa Masu Mahimmanci Da Daraja Basu Cika Maimaituwa A Rayuwar Mutum Ba… Shi Yasa Kowanne Mutun Uwa Daya Kacal Gareshi!!!

Kuma Watarana Zamu Wayi Gari Babu Ita A Duniyar Nan… Dan ALLAH Mu Kara Kulawa Da Mahaifanmu Musamman Ma Uwa Wacce Babu Kamarta A Duniyan Nan!!!

Ya ALLAH Ka Bamu Ikon Yiwa Mahaifan Mu Biyayya Ka Jikan Iyayenmu, Ka Basu Aljannatul Firdausi, Allah Ya Sakawa Iyayenmu Da Mafificin Alkhairinsa Duniya Da Lahira*

bayan ta ajiye wayar ta shaidawa mahaifiyarta aiki ne ya rike shi ashe

Hajiya Marhaba ta ce” jibi ne tsinaniyar yarinyar zata tare KO ?

Sahla ta ce”Eh mama

Hajiya Marhaba ta ce” toh duk yanda zanyi zanyi na kawo miki hadin maganin kinji ?

Sahla ta amsa mata ta Mike tana fadin bara ta juya kar aje yayi safiyar dawowa gidan Bata nan

Hakan kuwa hajiya Marhaba ta barta cikin tsohon daren nan ta juya ta koma gidanta tare da dumbin muguwar hudubar mahaifiyarta

Tunda ya juya ya fita bai sake saka Islam à Idannuwansa ba, domin Hajiya Fadimatu ta kasa ta tsare ta hana shi hawa saman balatana ya ganta, duk irin yanda yake fakewa da Bara ya dauko wani abin sai ta tare shi ta ce lala ba zai hau ba, hakan na matukar mahalar da shi,

Da kansa ya je gidan su Fati kawar islam ya shaida mata Auren islam aman ya boye mata mijin domin ya fi son ya zame mata surprise, auren kansa tayi mamakin sa domin Bata taba kawowa à ranta rashin zuwan islam school na kwana biyun nan haka ne ba, kuma ai suna waya Bata taba Shaida mata ba, Jin ya ce à washe gari zata tare ya sanya ta shirya da yama ta nufi gidan su AA Mubasshir,

Konce take tana baci, wannan bacin ya zame mata tamkar na rashin Lafiya, ta fiya baci à yan kwanakin nan,

Hajiya Hafsat ta shigo dakin ta Nemi gefen gadon ta zauna ta rasa ta Ina zata fara, à hankali ta saka Hannu tana dadaba bayanta

Firgigit Yar mahaukaciya ta farka tana adu’ar tashi daga baci, idannuwanta ta sauke à fuskar mahaifiyarta, da sauri ta zauna tana kalonta

Hajiya hafsat ta kawar da kanta à ranta tace ” wannan ido na mahaifinki ai sai mutun ya tsorata, à fili ta ce” ni islam bacin Lafiya kike ?

Yar mahaukaciya ta ce ” *Mahaukaciyata* da sauri ta rike baki ta gwalalo ido tana dan girgiza kai

Hajiya Hafsat ta jawota jikinta ta rungume ta tsam, kawai sai suka fashe da kuka irin mai tsananin nan, Wanda KO ranar da suka hadu basu yi shi ba,

Sai da suka yi mai isarsu sannan hajiya hafsat ta fara tsagaitawa tana shafa gashin kan Yar mahaukaciya, à hankali ta ce” sunan da kike kirana da shi ne à da KO ?

Yar mahaukaciya ta dago kanta ta ce ” Eh, sunan da yara suke fada miki ne, nima da na tashi sai nake kiranki da shi

hajiya Hafsat tayi murmushi tana share mata hawaye ta ce” shin Ina dukan ki à cikin hauka KO ?

Yar mahaukaciya ta lumshe idannuwanta ta bude ta ce” duk da à cikin hauka kike à lokacin mama, idan zaki yi baci sai Kin jini à jikinki idan kuwa bana nan na tafi nemo mana abinci har na dawo kina zaune kina duba hanyata

Hajiya Hafsat ta rintse idannuwanta ta ce ” ki yafe min *Islam*

Da sauri Yar mahaukaciya ta ce ” Mama, karki nemi gafarar abinda baki da laifi, ba abinda kika yi min, Dan ALLAH ki dena tinawa

Hajiya hafsat tayi tsai tana kalonta, can ta ce ” tell me, kina Son sa ?

Yar mahaukaciya ta zaro ido tana kalon mamarta

Hajiya hafsat ta ce ” eh fada min,

Yar mahaukaciya ta e” wane ?

Hajiya hafsat ta girgiza kai tana murmushi ta ce” mijinki nake nuFi, kina son sa ?

Yar mahaukaciya tayi saurin rufe idannuwanta gabanta na faduwa, tabas idan ta buda makaryacin bakinta ta furta cewar Bata son Dan Aljannah sai à nada mata sarauniyar makaryatan duniya baki daya, Dan haka gwara tayi shiru shine mafi aala à gareta, sai dai tana mugun Jin tsoronsa, tana Jin tsoron haduwarta da shi, sannan tabas idan abinda ya faru da ita da shi ne Aure ta san zata wahala, Karshe ma ta mace domin ta ji azabar da Bata san akoy irinta à nan gidan duniya ba

hajiya hafsat ta katse mata tunanin da ta afka ta ce” my islam, ki buda kunuwanki da kyau ki saurare ni, ki dago muyi zancen fahimta da ke à matsayina na wace tafi kowa sanin sirinki, shin kina son Mubasshir ???

Yar mahaukaciya ta dago kanta still idannuwanta à rufe kanta à Sade kasa cikin wani irin yanayi ta gyadawa mahaifiyarta kai tana nufin eh

hajiya hafsat ta ce ” Alhamdulilah, kin san mai zan fada miki ?  Aljannarki zaki je nema, ki Sani islam akoy da babu mijinki shugabanki ne, Lafiya da rashinta kyautatawa à gare shi ya zame miki wajibi, da fara’a KO babu kokarin kwontar masa da hankali na rataye à wuyan ki, yi Nayi Bari na Bari islam, à yanzu yanda mijinki yake da iko à saman ki KO mu da muka haife ki Bamu da shi, ki Sani idan kin gyara auren ki kin gyara lahirarki, shi kuwa gyara aure shine biyaya ga mijinki, Islam baki da sama da mijinki duk abinda ya saka ki yi kiyi shi banda Wanda ya sabawa adinin musulunci, Tsafta, girki, tsaftar gidanki, komai ki rike da hanu bibiyu, tsananin ki da kishiyarki kyautatawa, *Islam,  Islam,  Islam* sai da ta kirayi sunan sau uku taci gaba *Islam* duk ranar da kika je gaban boka KO malan kika durkusa da bukatar kan mugun nufi ga abokiyar zaman ki KO à kawar da hankalin mijinku à kanta KO wani mugun nufi ni mahaifiyarki ban yafe miki ba, ki Sani babu wani makami KO kariyar da ta fi kiyi alwallah ki tsarkake kanki ki fadawa ubangijin ki, ke kece shaidar abinda ya faru à kanki kinga à yanzu Allahn nan shi dai ya ga bayan ta, sannan yaci gaba da kare ki, kiyi ta hakuri da zaman gidan miji domin yau da gobe sai ALLAH,

haka mahaifiyar islam tayi ta Bata shawarwari kan rayuwar aurenta, da mahinmancin hakuri da barnar shirka, har lokacin jikonta yayi, da kanta ta karba ta jika islam tana kara koyar da ita yanda zata kula da kanta tun tana Jin kunya har ta sake sai dai tayi dariya KO ta rufe idannuwanta

suna fitowa suka zauna tana caje mata kai Fati kawarta ta shigo da gudu tamkar karamar yarinya

rumgume juna suka yi suna ta murnar ganin juna,

fati ta ce” kawata yanzu mamanki take fada min wata magana, Dan ALLAH yanzu AA ne mijinki ?  Daman ba yayanki bane kika ce yayanki ne ?

Yar mahaukaciya ta ce” ke hajiya bakya zama sai tambayoyi ?  Kinga mamana nan tayi mata nuni da Hajiya hafsat dake murmushi tana kalon su

Fati ta ce” Lah kinga kuwa kuna kama wallah, ta duka ta ce” mama Ina yini

Hajiya hafsat ta amsa fuskarta cike da fara’a, Daidai nan Elhaj Muhammad ya shigo da salamarsa yana fadin jama’a Ina cigiyar My princesse nd my wife

Hajiya hafsat ta dago kanta ta ce” du sun bata

da sauri ya ce” ALLAH ya kiyaye, plz koda wasa kar ki kuma ambatar sunan Bata à gabana plz, koda wani abina ne ba’a gani ba ki ce” aban islam wannan abin ka sayi wani plz maman islam

Hajiya hafsat cikin murmushi ta ce” Aban islam kaga kawarta fa,

sai à lokacin ya juya yana kalon su ya Mika hanu ya kamo islam Ya jawota yana gyara mata gashin kanta ya kali Fati da tayi sharan tana bukatar karin haske à sunan *Islam* da kuma wannan mutumin da farin su iri daya shi da *Rahma* harda kwayar idannuwansu,

???????????????????????Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                          75

*Watarana manzon Allah S.A.W. ya gama ibada yana addu’a Yana cewa Allah ka yafema sayyada Aisha R. A. zunubbanta da wanda ta sani da wanda bata saniba Da wanda tayi yanzu da wanda zataiyi nan gaba duk Allah ka yafemata ashe sayyada Aisha tana ji sai taji wani irin dadi sai tace: Ya RASUULULLAHI (S.A.W.) na gode sai Manzon Allah yace wannan addu’ar dana yimaki. Itace nake yiwa AL ‘UMMATA A kowace Sallah. Allah ya karawa ANNABI daraja tare da wasila da farila à aljanar firdausss*

Ganin kalon na fati ya saka shi yin dariya ya ce” i’m Muhammad, nine aban islam, yayi nuni da Yar mahaukaciya

Fati ta ce” abanta fa ? Sis ???  Ta kali Yar mahaukaciya

Islam tayi murmushi ta ce” yeah, ni ba marainiya bace, wannan shine abanna, sannan wannan momyna,  ni kuma sunana na gaskiya Fadimatul islam,

Fati ta ce” waouh, kenan hakane, waouh sister inai miki murnar ganin iyayenki, yanzu maman AA ta fada min komai to du sai nake Jin zancen tamkar wani Sabon zance,

Islam tayi murmushi ta kama hannun fati ta ce” haka Allah ya tsara, kinga Zo ki ga

Suka yi gaba, inda su Hajiya hafsat da mijinta suka ci gaba da tataunawa kan tarewar y’arsu kwaya daya da suka malaka à gidan duniya

Tunda garin ALLAH ya waye ake ta shige da fice a cikin gidan, masu gyaran dakin amarya na kanfanin Imran spécial aka dauko suke gyaran bangaran Islam, gado uku akayi mata kowani daki da nasa, kujerunta seti biyu na arabian da kalar na sarakai, adon ash da fari ne ake tsara dakin da shi, komai ya ji zanzan,

Tunda yama tayi mahaifiyar Sahla ta Zo à sadade ta kawo mata maganin wajen bokan inda suka hada hadaden j’yaourt mai cike da na’a na’a sai kanshi yake ta dauko sabon caraf mai kyan gaske suka zuba dan madaidaici ta zuba maganin ta girgiza ta saka à firij Hajiya Marhaba ta juya bayan ta kara jadada mata ta tabatar ya sha fa,

Bayan salar magarib gaba daya familyn na zaune inda na hango wani a

hasken yadi fari kar sai Sheki yake, sheshekar kuka na tashi sai muryar namiji na adu’a , Yar mahaukaciya ce tsugune à tsakiyar falon inda Hajiya hafsat, hajiya Fadimatu, hajiya hawau, hajiya Rafi’at, Aunty habiba, Sai Elhaj Muhammad dake adu’o’in neman tsari ga Y’arsa, wace zai sadata da gidan mijinta à wannan lokacin,

sosai sukai mata nasiha, suka kuma nuna mata mahinmancin Hakuri da kuma ilar rashinsa,

Kuka suke su uku à bayane wato *Fadimatul islam, Fati, da kuma hajiya Rafi’at* su kuwa iyayen suna share hawayen su,

Makota da abokan arziki suka fara cicika motoci inda mahaifin Islam ya murje Idannuwansa ya dauko sabuwar motarsa ya kama hannun y’arsa tana kuka ya nufi mota da ita akayi amaryar koko da Fati kawarta,

Su suka fara isowa inda Elhaj Muhammad ya damka mata alkur’ani mai Girma ya kama hannunta ta shiga Gidanta da adu’a à bakinta,

Sai da ya sadata da dakinta ya kuma yi mata gargadin karta yi sake da adu’a sannan ya juya ya baro gidan zuciyarsa cike da raunin kukan Islam

duk irin azarbabin masu rakiyar amarya Hajiya Rafi’at ta kasa ta tsare ta hana kowa shiga bangaren islam, haka kowa ya hakura ya juya da santin falonta da sauran dakunan da suka leka,  aka bar islam da fati da hajiya Rafi’at kanwar mamarta

konce yake saman makeken bed din dakinsa yayi rigingine Idannuwansa a lumshe, yana matukar mamakin irin yanda zuciyarsa ke azalzalarsa da ya je wajen islam tun kafin yan rakiyarta su juya, yana mamakin dokin da yake, cijewa yake tun karfinsa

Cikin takun yanga take takowa cikin dakin takalman kafarta na fitar da sauti kwos kwos kwos, uwargida kenan wato Sahla sai zuba kanshi take ta sha make up din yaudara,

Tafiyar tsutsa ta shiga yi masa tun daga wuyansa har kirjinsa, sosai sakonta ya fara caza shi domin daman à dane yake,

Idannuwansa ya buda ya sauke su à fuskar Sahla gabansa ya fadi, domin à lokacin mumunan aikin da ta shirya masa ya fado masa à ransa,

Murmushi ta sakar masa sannan cikin yatsina ta ce ” wani irin ango ne mai baci karfe takwos bayan an kawo masa amarya à dakinta ?

Mubasshir ya tataro dukan kokarinsa dan ganin ya ja Sahla à sabon salon barikin da ta fido dan tunkuda shi à rami,

Jawota yayi ya hade bakinsa da nata ya shiga tsotsa Idannuwansa à lumshe

Gaba daya ya kashe mata jiki, ita kanta ta san à wannan fanin ita din ba kowa bace wajen AA,

Hudubar mahaifiyarta ta fado mata à ranta, hakan yasa ta zare bakinta da sauri tana fadin” Ya Salam, huby plz tashi na raka ka bangaren matar ka bana son ka shiga hakinta KO kadan

Mubasshir ya kuma jawota ya ce” mai yasa zaki katse min rabar jikinki ne ? I need u, plz matso gareni

Sahla ta Mike da sauri tana fadin kai Hiby baza’ayi haka da ni ba, so plz bara na kawo mata dan yaourt din na tarban amarya da na Adana maka rabonka ka sha ka Isa ga amarya domin yau darenta ne,

Tana gama fadar haka ta juya da murmushin yaudara à fuskarta

,

Mubasshir ya rintse Idannuwansa ya ce “tabas yau daren amaryana ne, sai dai kin cuce ni Sahla

Bata dauki wani lokaci ba sai gata dauke da caraf din da kuma kofi kwaya daya

tana zuwa ta cika kofin ta zauna ta mika masa tana fadin” oya daga bakinka na baka ka koshi mu tafi na raka ka

mubasshir ya sakar mata murmushi ya daga bakinsa yayi bismillah ya rufe Idannuwansa ya ya…………………………..???????????????????????????????Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                    76

*Ya UBANGIJI ALLAH ka karbi tubanmu,Ka wanke zunubanmu,ka amsa addu’o inmu,ka tabbatar da hujjojinmu,Ka shiryar da zukatanmu,Ka tsayar da harshenmu akan gaskiya,kuma Ka cire duk wani mugun tunani daga zukatanmu.Mun sani, kuma munyi imani, shiriya, kariya da rahama duka naKa ne.Ya Allah,Ka samu acikin inuwarka alokacin da babu wata Inuwa sai taKa, Ya Allah Amin,summa Amin*

    Rintse Idannuwansa yayi tare da yin bismillah ya fara shan yaourt din da Sahla ta kawo masa yana tunanin yanzu koda gubar ce haka zata didika masa ya sha,

Har ya kusan shanyewa sai ya gumtse à bakinsa ya tare da hannunsa ya cire kofin ya jawota jikinsa ya hade bakinsa tamkar zaiyi kissing dinta

Idannuwanta ta zaro Jin ya zuba mata yaourt din da nufin itama ta sha,

Da sauri ta janye kanta tayi bayi da gudu tana kokarin amai domin har ta hadiye wani,

Murmushi ya saki ya Mike a nitse ya bi bayanta ya jingina kansa da jikin bayin sai da ta gama amanta sannan ta juyo,

Gabanta ne ya fadi ganninsa à tsaye yana kalonta

Mubasshir yayi yannayin damuwa ya ce” Sahla Lafiya ?  Kyankyamina ne kike ?

Da sauri Sahla ta zaro ido ta ce” kyankyaminka fa ?  No wly KO daya

Mubasshir ya tsareta da ido ya ce” to ya akayi kike kakari haka ?  KO dai kin hadiye wani Abu à ciki ne ?  KO da wani abin à ciki ?

Sahla ta kuma zaro idannuwanta tamkar mujiya ta ce” wani irin da wani abin à ciki ?  Kana nufin zan saka maka wani Abu da zai cutar da kai ne ? ( abinka da marar gaskiya)

Mubasshir ya yatsina fuska ya matso kusanta, sai da ta dan ja da baya domin duk ta tsargu da kanta, hakan ya sa ya wayance ya kamota gaban miror din bayin ya dora kansa saman wuyanta da wata murya ciki ciki yana shafa mararta ya ce” relax, relax, nifa du ba can nayi va, Ina dai mamakin yanda à Yau kike guduna,  Ina mamakin daga na zuba miki abin bakina Kin zabura Kin tofar, dole tsoro ya shige ni kar aje KO kin rage sona ne, KO kuwa bakina yake wari ban Sani ba ?

Sahla da wata irin kasala ta gama rufeta har lumshe idannuwanta take ta ce” bana son shiga hakin Yar uwata ne,  husband ita ce da kai, bana son ka tashi da shanyayen jiki gobe kiyama

Mubasshir ya lumshe Idannuwansa yana sauraron tatsuniyar munafukar matarsa, à hankali ya ce” are u prégnant ?

Da sauri ta bude idannuwanta domin tamkar ya buga mata guduma ne, Yau du wani iri take ganinsa tamkar ya san abinda ta aikata sai faman kawo mata sirin da daga ita sai mahaifiyarta suka Sani, cikin wani irin yanayi ta janye jikinta sannan ta kakaro murmushi ta ce” bafa zan biye maka ba, mu shiga hakin baiwar ALLAH, dan haka mu tafi Nayi maka rakiya kar lokaci ya kure

Mubasshir shima ya mayar mata da murmushin ya ce” ban taba gani KO Jin labarin matar da aka yiwa kishiya take zumudin raka mijinta dakin amaryar tamkar Wanda take fatan ta rabu da su ?   My baby kiyi kokari ki samo cikin bebyna Nayi miki alkawarin gaba daya dukiyata da na malaka ta nan Lagos da sunan ki, kafin yarona ya Zo sai na dawo da dukiyata ta makah nan

Sahla ta zaro ido ta ce” Da gaske ??  Sai kuma ta wayance ta ce” ai yanzu ni bazan yarda ayi haka ba Tunda mu biyu ne, dan haka muje Nayi maka rakiya, sannan Ina son raka angona ne dan na samu rabauta sannan na kafa tarihi

Mubasshir yayi murmushin yake ya taba kuncinta ya ce” Tabas kin kafa tarihi, sannan ya shige Sahla na biye da shi tana ta yauki

suna shiga bangeren Yar mahaukaciya sai da gaban Sahla ya fadi, domin fadin tsaruwar falon ma Bata baki ne,

Mubasshir ya mika hannunsa ya kamo na Sahla domin sai wani dari dari take, haka suka ratsa falon na farko suka nufi dakunnan, daki na uku ne nata ya saka hannunsa à hankali ya bude kofar

abin mamaki maimakun su tardo amarya à lulube cikin rufa na amare, à tare suka wangame baki Wanda ya saka nima na waiga wayan nawa ya kufce ya fadi kasa da sauri na rarumo wayar don na dauko muku dalilin firgitarmu

Fadimatul Islam ce tsaye tana dadage tana faman sai ta dauko wani Abu à saman werdrob dinta  , ta sha damamen bakin wando sidik mai santsi sai daukar ido yake, da Riga mai kamar jikin mage gashishikan jikin rigar sai kyali suke, gashin kanta à sake yake har gadan bayanta sai kyali yake ya sha gyaran Amare, du burar da zata yi sai mazaunanta sun motsa tamkar an cika balanbalan da ruwa ana girgizawa, haka na shanunta idan ta bura dai sunyi sama domin ba abinda ta saka daga ciki, ai tana Jin sun shigo din nan bisa hudubar auntynta wato Hajiya Rafi’at tayi wata irin juyowa ta nufo su tana buga kafa aman abin mamakin tamkar Bata ga da Sahla à wajen ba,

tana isowa ta shiga dire kafafuwanta tamkar Yar baby karama tana juya idannuwanta nan nata tamkar na mage tana dan kikifta su haka sai yarfe hanu guda take ta mika hannunta ta kamo hannun Mubasshir da ya zama tamkar gunki nunfashi kawai yake fitarwa aman komai na jikinsa ya tsaya ya daina anfani, kalonta yake kwakwaluwarsa ta tafi caji domin Tunda yake da ita bai taba ganinta da shigar kakanan kaya ba, KO ranar da ya bareta à Léa a duhu komai ya wakana , du ganin da zai yi mata da doguwar rigarta KO zani da atamfa aman koda atamfa bai taba ganinta ba,

Yan hannunsa da Yar mahaukaciya tayi ne ya fargar da shi cikin shagwaba ta ce”nurulkalbi plz kazo ka dauko min CD na Gaza daukowa, yayi min nisa gashi Ina son Nayi kalo

Sahla dake tsaye Bata san sanda ta ce” tap, tun karfinta ba

à tare suka juyo suka kaleta,  Islam ta ce” Lah auntyna yaushe kika shigo ?  Kinga Ina ta my one ban lura da ke ba i’m SO sorry yayi mantuwar tasa ne kafin ya fito KO ???

Sahla ji tayi uwa ta make bakin Yar mahaukaciya dan Haushi , ita zata nunawa bariki ?  Aman zata fada,  ta danyi murmushi ta ce” ikon ALLAH,  amaryar nan anya kuwa ?  Kai kanwata ba KO irin kukan za’a rabu da su mama din nan du da ba’a jima da haduwa da su ba,  ba’a wani shaku ba, aman ai amarya koda zawara ce ranar tarewarta ya dace à bude mata lulubinta ba ta bude ba

Yar mahaukaciya tayi dariya harda dan rike cikinta ta ce” Lah yanzu aunty à tinaninki yaune tarewar ? Ai an dade da sanin wannan hanyar yauma Nayi niyar na dawo kusa da mijina ne dan na ringa dama masa dakan hanu na fura cike da ada’ar soyaya

Sahla ta juya da sauri ta kali AA dake tsaye yana kalon ikon ALLAH, irin yanda islam ke mayar da du bakar maganar da Sahla ta yaba mata, maganganun da take Ramawa haussa ne cikin haussa,  Sahla ta ce cikin bacin rai” Daman ka dade da tarawa da ita ?  Toh à matsayin matarka KO dadiro ?

Yar mahaukaciya ta ce ” matarsa ai dadiron sa ce, sai dai mata suna suka tara sanan akoy dadiron mijinta bayan Aure kuma akoy dadiro kafin Aure da kuma bayan Aure,   ta juya wajen wata akwati Karama mai shegen kyau ta ce” Aunty kinga kyautar budurcina Wanda yayi min ni tawa kirar Dubaï ce harda dan gwal à ciki,  taki ma irin haka ya baki ????????

Sahla tayi tsit ta kasa Bata amsa kawai sai ta juya da gudu ta fita daga dakin inda suka rakata da ido,  Islam ta dan saki murmushi ta juya tana kokarin saka Baban hijabinta dan ta kwonta baci

AA  yayi tsam yana kalonta ya juyo yana tambayar kansa mai kenan ?  Mai hakan ke nufi ?  Wai shin duka wannan abin da Islam tayi wasan kwakwayo ne ????????? No  bazai yiwu ba ba zai yiwu ba

zai yiwu kai AA ???????????????????????????????????????Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                          77

*Manzan Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata agareshi yace: duk wanda yai min salati a rana sau dubu {1000} to bazai mutu ba har sai nai masa bishara da Aljanna. Wanda ya yada wannan hadisin to hakika yana sona, wanda kuma ya boye to hakika yayi nadama*

Kalonta yake cike da al’ajabinta, wai daman tana magana haka ? Toh Wa ya koya mata irin hakan ?  Au yanzu fa wuta ce ta kuna masa KO ? Yayi murmushi ya zauna bakin bed din yana kalon yanda take kiriniyar daure gashin kanta

À hankali ya ce ” baki ci nasara ba, domin fushin bai dameni ba

Yar mahaukaciya ta waigo ta dan kale shi ta juya ta ci gaba da shirin bacinta,

Shima kyaletan yayi yana nan zaune har ta gama ta juyo tana kalonsa, domin à saman bed din yake ya tankwashe kafafuwansa

Juyawa tayi tana kalon tsakar dakin nata sai lalausan kafet à shinfide, ta nufe shi da niyar konci

Mubasshir ya ce” Islam

Cak ta tsaya Bata waigo ba, ya lumshe Idannuwansa ya ce “ki dawo saman bed dinki ni zan kwana à kasan, yana gama fadar haka ya buda jerin kayansa da aka zuba à dakinta ya dauko tawol ya nufi bayi

Yana shiga ta juya harda dan gudunta ta haye bed dinta ta ja lalausan bargonta ta rufa ta tofe jikinta da ada’o’i ta lumshe idannuwanta sai barci

Can cikin dare ta farka dan gyara konciyarta ta jita à jikin mutun, hakan ya matukar firgitata ta mika hanu à hankali ta kuna fitilar jikin bed din mai dan duhu

Fuskar Mubasshir ta tsurawa ido da kontacen sajensa Idannuwansa a rufe sai bacinsa yake hankali konce, à nutse ta tsurawa kirjinsa ido yanda gashin ya konkonta alamun nutsuwa à tare da shi,

“idan kin gama kalon ki kashe fitilar my islam, haka kawai kalo da tsakar daren nan ? 

Muryar Mubasshir ta tsinta Idannuwansa a rufen nan aman yana fadin haka, da sauri ta shiga zare ido tana kokarin tashi daga kirjinsa ta ce” ni, ni ba wani kalo da nake nini

Kara jawota yayi sannan cikin muryar mai baci ya ce” shiiiiiiiiiit, Ina bukatar ki à jikina SO kiyi min hakurin hakan, ya kara rumgumeta da kyau à jikinsa

Luf tayi cike da kunya tana kara sine kanta à kirjin nasa nan da nan kuwa baci yayi awon gaba da su

Karan wayarsa ta tayar da su à tare ya mike à hankali ya lalubo wayar, sunan umina ya gani à jikin screen wato Hajiya Fadimatu cikin Bari ya daga ya kara à kunansa ya ce” Maman islam Lafiya ? 

Ajiyar zuciya ta sauke ta ce” Dan Fadimatu Ina yarinyata ?  Hop lafiyarta lau ? 

Mubasshir yayi murmushi ya juya yana kalon Yar mahaukaciya da tayi tsuru cike da tsoron Jin ba’asin Kiran domin karfe biyar ma Bata cika ba, ya ce” ga yarinyarki zaune ta tankwashe kafa tana zare idon tsoron Jin kiranki à karfe Hudu maman Mubasshir,

Hajiya Fadimatu ta kali hajiya hafsat dake ta murmushi ta ce” bani yarinyata kaji ko

Mubasshir ya mikawa Yar mahaukaciya wayar sannan ya tsareta da ido,

Tana amsa tayi salama

Hajiya Fadimatu ta ce ” my Daughter lafiyanki lau ?  Ba abinda yayi miki ?

Islam kunya ta cika ta, kawai sai ta kasa magana ta shiga sisine kai, ganin haka ya karbi wayar ya ce” Maman Mubasshir ki kontar da hankalinki plz, y’arki tana cikin koshin Lafiya, kunya ta hanata baki amsa,

Hajiya Fadimatu tayi murmushi ta ce” na kasa baci ne, du da Elhaj Muhammad ya fada min yanda kuka yi, aman sai nake jina bana tare da nutsuwata, plz karka cutar min da yarinya

Mubasshir ya ce” Maman Mubasshir kin san wani Abu ?

Hajiya Fadimatu ta ce ” aa

ya ce” Maman Mubasshir Ina tsananin son Y’arki,

Hajiya Fadimatu ta zaro ido, hajiya hafsat ma ta zaro ido ai ba shiri ta datse Kiran, Hajiya hafsat kuwa ta bushe da dariya domin yanda hajiya Fadimatu take dan zazaro ido abin à daran ne, hajiya hafsat ta ce ” aunty plz ki konta ki huta ni kam kinga Nayi nan, ta shige bargo tana ta dariyar Mubasshir da islam da mamansu

Mubasshir ya saki murmushi Jin ta datse Kiran, ya juya ya kali islam yanda ta dukunkune à cikin bargo ya san kunyar abinda ya fada ne ya saka tayi hakan, ya matso à hankali yayi mata kis à kuncinta sanan ya ce” kinsan mamanki tana tsoron kar à maimaita abinda ya faru ne kar à jima yarta ciwo

Yar mahaukaciya ta zaro ido ta kara matsowa can karshen bed din à ranta tana tunanin daman haka yake Sam kunya Bata ishe shi ba,

Ya Mike yana murmushi ya nufi bayi ya dauro alwallah ya shiga nafilfili

Karfe takwas na safe wayar hajiya Marhaba ta tayar da Sahla daga baci,

Hajiya Marhaba ta ce ” baby Ki tashi haka mana da barcin nan naki kiyi ki leka ki ga yanda suke ciki

Sahla ta diro daga bed dinta ta ce” bara na wanke idannuwana na leka kinga abin nan na jiya ya kona min rai zinariyar nan ba karamin kudi aka kashe mata ba, abinda ni bai ban ba ita ya Bata, aman su suka ja ma kansu, nasan yanzu ta dade da mutuwa Bara na hanzarta na kwashe su zinariyar kafin yan sanda su zo

Hajiya Marhaba ta ce ” yawa Yar Gari maza hanzarta

Sahla idannuwanta kadai ta wanke ba KO tunanin Wanka KO alwallah dan rama sallar asuba haka ta hanzarta wanke fuskarta ta bude bangarenta ta nufi na Yar mahaukaciya har tana harde kafafuwa wajen sauri

tana isowa Bata yi tunanin yin salama ko wani abin ba kawai ta tura kofar Baban falon ta shige

Gabanta ne yayi mugun faduwa inda kafafuwanta suka Gaza daukarta ta zube nan tana kare musu kalo su Mubasshir da islam sun sha wata farar Shadda bugagiya ta sha aiki kala daya, saï Aunty Rafi’at da fati suna zaune saman table suna cin abinci sai anuri ke fita daga fuskarsu

wani ihu ta saki ta ce…………………………,,,,,,,,,,,,,………….??Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                          78

*Yaya Hayat Admin na hayat haussa novel, haussa novel nd fashion cool novel….. Patati nd patata sako zuwa gareka, kayiwa girman ALLAH ka barmin novel dina yanda ka ganshi cos nawa ne ba naka ba, haba taya zakana hada document da novel dina da numbobin wayarka da sunayen Grup dinka kuma ba tare da izinina ba ?  Ka manta y’ar mutan Niger da na nemi alfarmar ka saka ni à grup Ina bin novel din auntyna matan Ali ka bukaci kudin shiga ni da nake Niger Ina zan ga naira hakan yasa kaki sakani sai yanzu zaka yi anfani da naya novel din ?  Kai walahi idan ka kuma anfani da novel dina dan kayi document da shi ban yafe ba ka barshi yanda yake idan na gama abina zan hada abina à document na gode*

Wani ihu ta saki da ya saka suka Mike a tatare, da hanayenta ta daga tana nuna su tana kokarin yin magana da gudu ta Mike ta fice ta nufi dakinta tana zuwa ta danna Kiran mahaifiyarta,

Hajiya Marhaba na daga wayar Sahla ta rushe da matsanancin kuka

Hajiya Marhaba ta ce ” ke pretending kike KO kukan gaske ne ?

Sahla ta ce “mama lafiyansu lau, suna zaune suna karyawa cikin annuri, KO dan ta saba da shine ya sa Bata gaji da shi ba, ya sa bai halakata ba, mama mai yake faruwa da ni ne ?  Daga wannan sai wannan, KO duba fa ki gani tun kafin ta tare yake like mata kenan yafi sonta da ni KO ?

Hajiya Marhaba cikin tashin hankali ta ce” wani irin mutun ne kika aura Sahla ?  Shi asiri baya cinsa ne ? Bara Nayi Kiran tsinanan bokan nan Naci kutumar….. Don kuwa bazai yiwu na barshi ya cinye min kudi kuma aiki bai ci ba, KO kontar da hankalinki kiyi musu basaja tamkar ta kirki, ni na fisu zama hatsabibiya,  zasu ga abin mamaki, da ni suke zancen

Sahla ta saki ajiyar zuciya ta ce” à da Ina tunanin sasauta masa aman à yanzu na tsane shi mama, dalili kontawa da yayi da wannan yarinyar har ta kare min kalo ta gwada min abinda ya siya mata,

Hajiya Marhaba ta ce “barni da su, Tunda kika gane hakan ai da kyau

Suna katse wayar hajiya Marhaba cikin bacin rai ta danawa bokanta kira

Cikin magagin baci na mutumin da bai tashi ba har karfe tara boka ya daga wayar hajiya Marhaba,

Rufe shi tayi da fada tana fadin ita zaya yaudara aikinta yaki ci

Wata uwar ashar ya dura mata sannan cikin yannayin mashaya ya ce” ke kika Bata aikinki Yar akuya, dan haka li jirayi sakamakonki na zagin aljannu da kika yi,  dif ya kashe Kiran

Hajiya Marhaba ta bi wayar da kalo ta Mike tayi Kiran kawarta azumi,

Tana dagawa ta shiga zayane mata abinda ya faru, ta dora da fadin” kinga kuwa shine yayi min aikin Elhaj na daga bayan nan da ya fara warwarewa, yanzu haka yanzu zanyi Kiran uwar tasa Ina kuka idan ta taho ta tsalako shikenan hauka har kabarinta, sai sauran tsinanun, To aman na fara kokonto

Ji tayi an warce wayar daga hannunta ta dago da kanta da sauri idannuwanta suka sauka à fuskar mijinta da lokaci daya kamaninsa na tsare gida tun suna samartaka ya dawo masa, daga bakin kofa kuwa Baban danta ne ya dora hannu biyu à kai yana rusa wani matsanancin kuka, fitowa yayi ya jawo dansa suka zauna suna Jiran isowar su Sahla domin su hajiya Fadimatu har sun karaso inda yayi Kiran Mubasshir ya bashi umarnin KO à daure ne ya kawo Sahla wace ya yana shiga ya tsorata ta ta hanyar fadin mamarta ba Lafiya

Ai da Gudu ta fito suka kama hanyar gidan mahaifinta gaba dayansu banda fati

Suna karasawa ta fita da gudu tayi falon umanta, tana zuwa ta tarar da jama’a à falon inda suka taru kowa yayi jigum, shi kuwa Idriss sai rusar kuka yake

Ihu ta saki ta dora hannayenta biyu à kanta ta nufi Idriss tana tambayar ta mutu ne ? Mai ya sameta ? Wani ne ya kashe min uwa ? Ina maman a…..

Dim kake ji ta hadiye sauran maganar à bakinta, sanadiyar wani wawan mari da abanta ya zabga mata, kafin ta dago ta kali mai marin nan nata ya kwasheta ji kake kush karar faduwarta à kasa, kafin ta gama dandace abinda ke faruwa da ita ya bita kasa ya shiga nausarta

da gudu suka ririke shi suna fadin haba Elhaj, idan rai ya baci ai hankali baya gushewa,

Sahla dake zubar da jini ta goshinta ta kasa daga hanunta da alama ya karye fuskarta kuwa har ta canza kala, ta ja jiki ta rike kafar Idriss tama kasa kukan du irin azabar dake tsigarta, idannuwanta ta dago har jini ya dan konta ta zuba masa su ta ce” mai ke faruwa Yaya Idriss ?

Idriss shima ido cikin ido ya ce” Sahla asirinku ne ya tonu,

Sahla ta zaro ido ta ce” wani asirin mu ?  Ni da Wa ?

Idriss ya ce” asirinku na shirin ku na halaka rayuwar bayin ALLAH da suka yi muku rana dan ku malake abinda ba naku ba, ke harta asirin da mama ke yiwa dady na ta juya shi yanda ta ga dama ya karye Sahla, yanzu haka ta bine wani à kofar dakin dad Bata tsoron yayi dawowar bazata dan kawai ta tsoratar da Hajiya (hawau)  cewar dad ya mutu yana dakinsa idan ta tsalaka ta haukace à cewar bokanku, Allah ya taimaka muna shigowa dakinta muka nufa dad cike da mamakin za’ayiwa mama sherin bin bokaye sai gashi yaga haza domin shaida ta kirarin mutun da kansa KO ta Zina ta shaidu,

Sahla zuwa wannan lokacin ta gama tsurewa,  tsoro da fargaba da tashin hankali da kunya suka mugun lulubeta, cikin nauyin harshe ta ce”  Wa ya fada muku ?

Abanta cikin wata irin murya mai cike da kunci ya ce” Wanda ya boye mana dan ya kare mu, Wanda ya zuba muku ido dan yaga imanin ku, Wanda à cikin ruwan sanyi ya dago ku à fili *ALLAH* kenan, Wanda baya baci,

Sahla ta waigo ta zubawa fuskar Mubasshir ido a ranta tana tunanin ashe ya ji komai shi yasa yayi tayi mata tambayoyin nan ?

Idriss ya Mike ya nufi kofar dakin mahaifiyarsa ya bude dakin, tana jingine da kofar tana sauraron komai, ta dora hannunta à kai tana tunanin yanda aka yi hakan ta faru ai kuwa Bara ta kirayi boka ta fada masa ta bashi hakuri ya kuma shirya mata wani sihirin ( oh wai Kin manta rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya ?)

Budewar da yayi tana tsaye, ya zuba mata ido itama shi take kalo, ai kuwa ta shiga zaro ido hango mutanen falon, ta fito tana inda inda ta ce” aa fa, aa fa, wannan duka karya ne, ni ban aikata ba, aban Sahla karka yarda à hadani da kai, kai kasan à yanda

Nake kula da hajiya bazan iya cutar da ita ba, kai kafi kowa sanin hakan KO ? Ta juya wajen Idriss ta ce” Docter kaima ai shaida ne matso nan ka furta mahaifiyarka ba abinda tayi kowa ya tashi ya fice gidansa,

Sahla ta ce” mama.

Hajiya Marhaba ta juyo gabanta ne yayi wani irin faduwa, fuskar Sahla ta Haye tayi sindim, jini ya shigar mata ido ga hannunta ta kasa daga shi

Hajiya Marhaba ta ce ” ubanwa ya taba lafiyar jikinki ? Fada min ubanwa ya dake ki ?

Mahaifin Sahla ya ce” ni ne, ni na daki y’ar da nake tir da…… Da sauri Elhaj Muhammad ya ce” kul na haneka da yin mumunan furuci Wa y’arka, SO kake ta shiryu KO ta baude ?  Rashin tunani dana sani, kaucewa hanya ya tabata ga iyayen da zasu aibata y’ayansu dan sun kaucewa hanya, To mai zaka yi kenan ? Mala’iku suna gagawar amsar adu’ar iyaye Wa y’ayansu da amin KO wace kala ce dan haka ka kiyaye kar danasani yayi yawa rayuwarka

Hajiya Marhaba ta karewa Elhaj Muhammad kalo cikin kunan rai ta ce” ai dole ka fadi haka, kai ka kilace taka sakaryar y’ar zaka yi mana bariki à nan, toh wly baka Isa ba

Mahaifin Idriss ya juya dan yiwa Idriss magana sai dai abin mamaki bai ganshi à inda yake tsaye ba

Kiriniyar bude dakinsa yake domin idan za’a bude dakinsa sai an sha fama da kofar

Da sauri suka nufe shi aman kafin su Isa har ya bude kofar da gudu hajiya Marhaba ta rike shi aman da yake karfin ba daya ba zai kufce mata Mubasshir ya damko shi, kokowa suka shiga suna kokarin turo shi, garin ta tura shi karya shiga dakin da ta bine abinda zata haukata  hajiya hawau da shi, ita kafafuwanta suka shiga, abin ikon ALLAH kawai sai ji suka yi ta kwashe da wata muguwar dariya

À tare suka furta inalilahi Wa’ina ilaihi raj’une, hanayensu à saman kansu

Mubasshir ya saki Idriss Wanda ya juyo jiri na kwasarsa ya zube à nan sumame

Ita kuwa sai dariya take babakawa, haukan dariya hauka mai wuyar warkewa, haka suka yi jigum jigum inda suna waigowa itama Sahla ta suma ( to fa wanzam baka SO à jikinka)

To fans tambayana à nan shin Sahla zata ci gaba da zama à matsayin matar AA ?  Haukan hajiya Marhaba ya dace da ita duba da irin abinda ta aikata ?  Bawan ALLAH Idriss ya tasa makomar ba masoyiya mahaifiya ta haukace, kanwa ta kauce hanya ?  Shin labarin Yar mahaukaciya na kayatar da ku ?  Cos ance wai banida masoya ???????????????????????Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                          79

*Wayo dadi, daukaka abar gudu abar nema, ni kam na rasa bakin magana sai jazakumlah,*

da gudu ya nufe shi yana jijigashi, inda Yar mahaukaciya ta nufi Sahla saï kuka take dan kuwa ita abi kankani ke rikita mata lisafi, tana kuka ta dago kanta ta kale su zata yi magana kenan sai ga abanta ya shigo da gudu yace ” ku kama su mu je asibiti

Mahaifin Idriss wato Ilyas ya dago da kansa ya ce” baza’a kaita asibiti ba, sannan ba zan bisu asibiti à yanzu ba, kawai zan rufeta à daki ne naje wajen tawa mahaifiyar,

Elhaj Muhammad ya zuba masa ido ya SO ya takura sa sai dai yayi wani tunanin kawai ya kamawa Mubasshir suka dauki Idriss suka shiga motar da shi,

Elhaj Muhammad ya kali Mubasshir ya ce” kaje ka dauko matar ka domin kaine muharaminta

Mubasshir ya dago Idannuwansa cike da hawaye ya ce” ka yafe min aba, na saki Sahla saki daya

Elhaj Muhammad ya zaro ido ya ce” why Mubasshir  zaka yanke danyan hukunci haka saki cikin fushi ?

Mubasshir ya kawar da kansa ya ce” banyi saki cikin fushi ba, na gama nazarina kafin Nayi sakin nan domin da à lokacin da nake walafawa Sahla soyayata gareta ta canza tunani Bata bani yaourt din nan ba da lale lale bazan saketa ba, aman à cikin zuciyar Sahla kiyayata tafi soyayata yawa dan haka ka yafe min,

Elhaj Muhammad ya rasa ma mai zai ce masa kawai sai ya kada kai ya koma dakin inda ya tarda Elhaj Inyass ya fitar da du abinda ya san zata iya raunata kanta ya rufeta à dakin sai falasa irin aika aikar da tayi take tana busasa dariya,

Elhaj Muhammad yayi gagawar kawar da kansa dan kuwa sai yaji ba dadi,

Su hajiya Rafi’at da hajiya hafsat suka kama suka dauko Sahla wace kitsonta na atch sai yawo yake tsananin tsayinsa a kanta,

Suna sakata irin motar nan ce jeka da iyalinka, lxus suma suka shiga Mubasshir ya tayar ya kama hanyar asibitin idriss

Suna zuwa da gudu aka karbesu BQ tare da tambayoyin abinda ya faru ba suka dukufa domin ceto ransu,

Zaune suke Yar mahaukaciya ta dora kanta saman cinyar auntynta tana ta sauke ajiyar zuciya, itama Rafi’at din du tayi wani iri da ita sai tunani take na rayuwa,

Hajiya hafsat ta kasa zama sai kai kawo take tana dan leka hanyar dakin da aka shiga da su,  kuma sai ta kali AA da yayi wani irin ja na Wahala, kansa à kasa yana kalon yatsun kafarsa,

Elhaj Muhammad ya zuba mata ido yana kalonta, wani irin tausayinta da kaunarta suka kara darsun masa à zuciyarsa, ya kuma kali y’arsa dake konce q cinyar Rafi’at, ya juya ga Mubasshir dake kalon kasa, ya girgiza kai à hankali ya Mike ya kamo hannun hajiya hafsat, har yanzu abin nan bai barta ba na idan hankalinta ya tashi ta kasa zama, yayi murmushi ya jawota jikinsa ya Bata kyakyawar runguma, hakan ya saba yi mata idan har yana son ta shiga cikin nutsuwarta, hakan kuwa aka yi sai ta dora kanta à kirjinsa tana sauke ajiyar zuciya, tana karawa,

Ta kusan minti biyu à haka ta tuna su Mubasshir fa na wajen da sauri ta kufce daga rikon da yayi mata tana kara jan zumbulelen hijabinta tana kokarin rufe fuskarta,

Mubasshir ya kawar da kansa yana girmama soyayar sirikansa

Docter Halima ce ta fito ta nufo su

da sauri suka Mike har suna hada baki wajen tambayar ya jikin su,

Mubasshir ya kali Yar mahaukaciya da ta ce” ya jikinsa ? Gabansa ya fadi, Muryar docter ta dawo da su inda ta ce” alhamdulilah jikinsu da sauki cikin ikon ALLAH,

An daidaita lunfashinsu, shi an saka masa ruwa aman munyi masa alurar baci wace tana iya daukan awa uku zuwa Hudu yana baci dan ya samu hutu, sai ita an dora hannun, aman tana bukatar kulawa KO ku dauki nurses masu kula da wannan harkar KO ku dauko Wanda zata tsaya tsayin daka dan lafiyarta ta samu cikin sauki da yardar ALLAH

Mubasshir ya ce” docter muna iya shiga mu ganshi KO ?

docter ta ce” eh sosai ma, kuna iya zama ma ai docter ne, ba wata damuwa,

Elhaj Muhammad ya girgiza kai Jin bai damu da rashin Lafiyar sahlan ba, ya ce” docter Ina bukatar à daukarwa kanwar Idriss nurses uku da mai kula da tsaftarta, da mai kula da abincinta, da mai kula da addininta à kan lokaci, du wata kulawa Ina son à Bata kafin ta dan warware

Docter ta ce” Elhaj akoy tsada fa

Elhaj Muhammad ya kaleta ya ce” ba wannan ba, aikinsu shine biyan bukatarmu

Mubasshir suka yi gaba su hudun suka nufi dakin Yar mahaukaciya kafin ya gama ya tarda su,

suna shiga suka tarar yana konce hanunsa jone da karin ruwa, yana baci aman da ka kale shi sai ka ga ya fada,

hajiya hafsat ta nufi gadon Sahla tayi mata ada’ar samun sauki,

Elhaj Muhammad suka shigo da nurse aka ja gadon Sahla dan à canza mata daki domin jinyar namiji da mace bazai yiwu à daki daya ba

Elhaj Muhammad ya kare yi masa kalo ya ce” da ace inada wata y’ar da na Isa da ita da na aurawa Idriss bisa sharadin idan ta Bata masa ban yafe mata ba

hajiya hafsat itama ta zura masa idon ta ce” ya ALLAH yanda ka yaye mana damuwarmu bisa Imani da muka yi da kai ka yayewa wannan Bawa naka cikin ruwan sanyi sannan ka bashi ikon cinye jarabawar

gaba daya suka amsa da amin, Mubasshir dai na kalonsa kuma sai ya saci kalon Yar mahaukaciya da ta zuba masa idon itama ba tare da wani tunani ba sai tsantsar tausayawa gare shi balatana idan ta tuna Tata rayuwar da ta shude ba’a dade ba

Elhaj Muhammad suka yiwa su hajiya Rafi’at da Mubasshir da Yar mahaukaciya Salama suka nufi gidan su Idriss dan su tarda hajiya Fadimatu dake wajen hajiya hawau suna ta jajantawa da kuma murnar dawowar tunanin Elhaj ilyassssss

bayan tafiyarsu Mubasshir sai ya daina kalon Idriss din gaba daya sai ya dawo da tunaninsa wajen islam da tayi zuru ita da aunty Rafi’at suna ta kalon lumfashin Idriss, wani haushi da mugun kishi ya rufe shi, à ransa ya ce, Tunda ta zura masa ido Bata dauke ba, mai hakan ke nufi ? Tana tsoron ta kawar da kanta ne wani abin ya sami masoyinta ( toh fa eh din Inji ni )

Gani yayi bazai iya jure wannan abin ba, ya Mike yana dan sosa keya ya ce” auntyn mu plz mana bara mu samo muku dan abin matsa baki kafin ya farka

hajiya Rafi’at ta kale shi ta ce” haba freind (domin shekarunsu daya abinka da yan gayu shima idan yana bukatar wata alfarmar ce yake kiranta da aunty)  ya zaku barni à nan ni kadai kuma ?  Idan ya farka fa ya Zanyi da shi ?

Mubasshir ya ce ” ai ba zamu jima ba

hajiya Rafi’at ta ce ” toh ka je kai kadai mana

Mubasshir ya zaro ido ya ce” Ina bazai yiwu ba fa hajiya kinga tafiyar mu dan Ina dan yi miki Yar murya aa bye, 

Ya ja hannun Yar mahaukaciya wace tayi murmushi diramar auntynta da mijinta na birgeta matuka

Bayan fitar su aikin nata da ta saba ta ci gaba wato kalon sa, Kiran salar da aka yi ne ya saka ta Mike ta cire hijabinta dan taga yana baci kuma zata shiga bayi, ta ajiye à saman kujerar da ta tashi ta nufi bayin

alwallah ta dauro ta fito,  tana fitowa ya mayar da Idannuwansa ya rufe ta dauki hijabinta ta dora saman Riga da siket dinta ta jawo dardumar da docter ta Miko ta kabarta sallar la’asar,

Bayan ta gama sallah tayi ta adu’o’inta da ta saba sannan ta daga hannunta sama cikin bayananiyar murya ta fara yiwa ALLAH kirari da shi da fiyayen halinta, ta nemawa iyayenta gafara da Wa’inda suka rigaye mu gidan gaskiya, ta kara nemawa y’ar uwarta kariyar ubangiji da ahalinta baki daya, ta roki gamawa da duniya Lafiya, sannan ta gangaro kan Idriss ta ce” Ya  ALLAH  alhamdulilah,  Allah mun gode maka da wannan rana ALLAH muna rokon ka ka sanya ta zamto alhairi à gare mu, ya ALLAH ga bawon ka nan, kafi kowa sanin dalilinka na ciro kamili daga tsatson Wanda ba kamili ba, ya ALLAH kafi kowa sanin abinda ya dace da wannan Bawa naka domin kai kadai ka san gaibu, ya ALLAH ka sanyaya masa damuwarsa, ka yaye masa kuncin sa, ka bashi ikon kula da mahaifiyarsa da kuma kanwarsa, ka bashi juriyar cinye wannan jarabawar, ka shiryar da kanwarsa, ka baiwa mahaifiyarsa Lafiya, kai kayi komai kai kake da komai ya ALLAH,

*sai da ta gama yiwa kowa adu’a sannan ta fashe da kuka mai tsanani, ta kara daga hannunta sama ta ce” ya ALLAH ka kawo min abokin rayuwana koda da an daura min aure zan koma gareka, ya ALLAH idan wani abin na aikata KO nake aikatawa ka nusar da ni ka yafe min ka bani miji na gari komai talaucinsa, ya ALLAH idan kuwa lokacin Nayi auren ne baiyi ba ALLAH ka kara min hakurin jiran lokacin domin na san da mutuwa da arziki da Aure lokaci ne, ya ALLAH idan….. Ta kuma fashewa da wani kukan ta ci gaba idan kuwa banida raban yin auren ne har na koma gareka ka saka min dangana ka kuma kare ni da sharin Zina ka kara nutsa ni à kogin tsoronka ya ALLAH ka cika min burina amin*

bayan ta gama adu’ar ma sai da ta ci kukanta sannan ta Mike a nutse ta nade salayar ta juyo dan ta ajiyeta

Gabanta ne yayi mumunar faduwa sanadiyar ido Hudu da suka yi , wato Tunda ta fashe da kuka ya zabura ya zauna yana kalon ta kuma yana sauraronta,

wayancewa tayi tana dan murza ido kamar wani abin ya fada mata à ciki ta nufi dan kusa da gadon tana dan inda inda ta ce” “””””””””””””

garigajin ganin ji ganjin kara Kaka kara ????????Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                          80

Tana murza ido ta ce” au ka farka ?  Yaushe ka farka ?  Ya jikin ?

Shiru Taji yayi bai ce komai ba hakan yasa ta dago da kanta suka yi ido Hudu, gabanta ne taji ya yanke ya fadi ta shiga kikifta ido

Idriss dake kalonta yana kokontan anya kuwa shekarun da aka ce ta kai kuwa ?  Kamar wata Yar budurwa mai shekara 25 haka, ya lumshe Idannuwansa ya ce” shekarunki nawa ?

Hajiya Rafi’at ta dago kanta ta zuba masa ido tana mamakin tambayar sa, yaro karami da shi yana tambayar shekarunta ita tayi imanin ta bashi wata shekara biyu KO uku, ta kawar da kanta ta ce” ban gane shekaruna ba ?

Zaiyi magana kenan Mubasshir ya turo kofar ya shigo da ledodi manya bakake à hannunsa, Yar mahaukaciya na rike da wayoyinsa,

Suna shigowa ya saki murmushi Ya ce” marar lafiyana ya farka ?

Idriss yayi murmushin shima ya ce” ALLAH ya tashe ni broth

Mubasshir ya Mika masa hanu suka gaisa ya zauna yana kokarin bude dan abin motsa bakin,

Idriss kuwa banda kalon hajiya Rafi’at ba abinda yake, gaba daya ta tsargu, tana tsoron karfa aje yaron nan ya saurari adu’arta, ta girgiza kai à ranta ta ce ” da kuWa ya cuce ni sosai,

Muryarsa ta katse mata tunani inda ya ce” tashi ki dauko min kofi na sha magani

À tare suka dago, Yar mahaukaciya ta Mike domin dai ta san bazai aiki auntynta ba duda bashi da Lafiya, ga mamakinsu sai ji suka yi ya ce ” No ba ke ba,  da *Yarinyar* nan nake

À tare suka zaro ido harda Mubasshir, Hajiya Rafi’at ta waiga ta kali Mubasshir ta ce” Freind KO kwakwaluwar yaron nan ta tabu ne ?  Cos yana Farkawa ya shiga tambayana shekaruna, ni kuwa anya ba za’a Kira docter ta duba lafiyarsa ba ?

Mubasshir ya ajiye abarbar da ya wanke ya matsa kusan gadon ya ce” broth are u OK ???????

Idriss yayi murmushi ya ce” tabass lafiyana lau broth, i’m Idriss Ilyass, i’m 31 old, ni Docter ne, sannan à wannan lokacin Ina cikin tashin hankalin mamana mai suna Hajiya Marhaba da ta samu tabin hankali da kuma sisterna mai suna Sahla da ta karye sannadiyar son zuciya da kuma son abin duniya, kuma alhamdulilah na yarda da kadara

Mubasshir ya ce ” hajiya Rafi’at ce fa kake Kira da yarinya,  to mai zaka yi da shekarunta ?  Mai ke damunka ?

Idriss ya lumshe Idannuwansa ya bude ya leko fuskar Rafi’at dake kalonsa tana jiran Jin amsar bakinsa, ya dawo da Idannuwansa wajen Mubasshir ya ce” nima Ina son sanin abinda yake damuna broth, Ina son sanin rigimar dake kokarin dosoni à wannan lokacin, ina rokon ALLAH ya kama mini domin wannan tashin hankalin zai fi rikitani, zai kara kawar min da nutsuwata

daidai wannan lokacin gaba dayansu sun sare du sun kara matsowa kusan sa, harda islam sun zuba masa ido, Mubasshir ya riko hannunsa ya ce” what happen, mai ke damunka broth ka fada min da yardar ALLAH zamu samo mafita

Idriss ya tsare shi da ido ya ce” kayi min alkawarin zaka samo min mafita ?

Mubasshir ya ce ” bi’izinillah Zanyi iya yina idan har hakan bai kaucewa hanya ba,

Idriss ya sauke ajiyar zuciya ya zuyo ya kali Rafi’at da tayi tsuru tana kalon sa, ba zato ba tsamani ta ji ya ce” Ina son auren Rafi’at, Ina son Rafi’at, Rafi’at tayi min ita nake son rayuwar Aure da ita, sai dai Ina fargabar KO zata ki *Dan Mahaukaciya ?*

Yar mahaukaciya ta zaro ido ta rike baki, Mubasshir ya saki murmushi ya juyo yana kalon Rafi’at da ta zama tamkar mutun mutuni tana kalon sa, Mubasshir ya ce ” shikenan sai ayi tuwona maina

Hajiya Rafi’at ta kuma zaro ido ta ce ” Da Wa za’ayi tuwanka manka ?  Au KO kunya baka ji ka kali idona ka ce Ni Rafi’at kake SO ? Ni KO auren ne ai sai Wanda ya girme ni nesa ba kusa ba, idan kaji adu’ana ne ka tausaya min to ka tayani da ada’ar ALLAH ya bani Daidai ni ba wai yaro karami ba, ka shiga Ina da ni ka fada min mai ?  Ai Nafi karfin Auren kanina

Idriss ya rintse Idannuwansa ya ce ” stop, ya Isa haka, Ki dena kalon tsabar idona kina fada min zancen nan, Ki Sani *Namiji baya kadan* kuma da kike maganar wai kin girme ni fada min shekarar biyu da kika bani ne zaki fadi haka ? To ya kike kalon tarihin auren fiyayan halita Wanda akayi duniyar dominsa ? Aure suna ne, ba tausayinki da naji kawai sonki nake, sai dai idan kalmar nan daya zata hannaki aurena wato *Dan Mahaukaciya*

hajiya Rafi’at jikinta yayi sanyi tsoronsa ya darsun mata à zuciyarta ta zuba masa ido tana sauraron duk wata kalma tasa, wai shekara biyu ta bashi, no shekara uku ne, to aman taya zata yarda da wannan abin kunyar ai har Sahla ta goranta mata, itafa har yanzu gani take Idriss baya cikin nutsuwarsa, domin wannan abin da ya dage yana fadi, ta juya ta kali Mubasshir ta ce” ka saka à caje kwakwaluwar kanina kuma abokinka, idan kuwa à cikin hankalinsa yake ka fada masa lale ya cika dan dirama, aman Ina rokonsa ya tsayar da diramarsa haka domin ni kam na cika rauni, tana gama fadar hakan ta juya zata bar dakin da gudu sai ga kofar ta bude an shigo *Elhaj ilyass ne da Elhaj Muhammad* suka dawo da kwondon abinci, gaba daya abinda suka fada à kunayensu,

hajiya Rafi’at tayi saurin sada kanta kasa dan kar su gane hawayenta

Elhaj Muhammad ya ce” where are u going ?

Rafi’at ta ce” zan Kira docter ne ya ya farka

Elhaj Muhammad ya gyada kansa ta juya tana tuna fita ta tari Adaidaita tayi gidan su Mubasshir,

bayan yan gaishe gaishe da karin jawabi kan Idriss yayi hakuri da kadararsa ya ce ” ba komai ALLAH ya bani ikon cinyewa

suka amsa da amin, shiru ya biyo baya na dan dakiku

A

Elhaj ilyass ya dago kansa ya ce” son abinda na saurara à kofa kana fada da gaske kake KO kuwa maganar ta Rafi’at ce baka cikin nutsuwarka ?

Idriss ya sada kansa ya ce” dad, Ina cikin nutsuwata, tun ranar da na je gidan su Mubasshir ta bude min kofa na tsinci kaina à wannan yanayin, Rafi’at ita ake Kira da matar rufin asiri domin du irin abinda ya faru tana yi min adu’a da kuma iyayena, nan ya kwashe adu’ar da ya saurara daga bakinta, ya ci gaba” idan har zata juri zama da ni à halin da na tsinci kaina à ciki à yanzu tabas da sai Nafi kowa murnar hakan

Elhaj Muhammad ya ce” Alhamdulilah, barni da ita, ni nasan yanda zan bilowa al’amarin da yardar ALLAH,

Bayan wani dan lokacin Elhaj Idriss ya kali Mubasshir ya ce” yarona tashi ku tafi gidanku kaji,

Mubasshir ya dan sada kansa ya ce” ai aba Bazan iya barinsa haka shi kadai ba

Idriss yayi murmushi ya ce” broth tashi ka tafi da sister baiwar ALLAH ta gaji da yawa, ai nima yanzu zan tashi mu koma gidan

Mubasshir ya ce” tohm sai munyi waya, suka Mike suka yi musu salama

Tafiyar minti talatin da dan dori ne suka yi kafin su Isa gidan su, kowanen su da abinda yake sakawa à ransa, ita dai Yar mahaukaciya tana fatan auren nan ya tabata domin Idriss mutunan kirki ne, shi kuwa yana tunanin gaskiya an shiga hakinsa da yawa,

Tsayar da motar yayi ta bude ta fice, ya bita da kalo à ransa yana tunanin Bata san tafiyar kawarta fati ba,

Yar mahaukaciya ta tura falonta ta shiga da ada’a à bakinta, karo tayi da farar takarda ta buda ta karanta sakon fati ne na ta tafi gida sai an kwana biyu zata dawo da yardar ALLAH

Yar mahaukaciya tayi murmushi ta ce” My fati,

Dakin ya sha gyara sai kanshi yake ta shige dakinta tana ta murnar yanda fati ta gyara mata dakin kafin ta tafi

Wanka ta fada, kafin tayi sai da ta shiga ruwan dumi ta fito ta sala Wanka ta dauro alwallah ta fito daure da tawul, ta zumbula doguwar Riga ta kabarta sallar magariba, bayan ta gama ta cire ta bude cikin kayanta ta saka wasu Riga da wando masu shegen kyau ta daure gashin kanta Bata tsaya yin Wata kwaliya ba ta nufi dan karamin frij dinta ta bude ta dauko jikon kabewa da madara no sugar da mamanta ta dadafa ta cicika biduduna aka jera mata à frij, guda ta dauko ta girgiza ta shanye tana tande baki, haka ta bude zumuwar da aka yi mata Hadin amarya aka ce ta ringa sha kadan kadan, ta kuwa zauna ta aniya sha sai da taji ta koshi ta rufe sauran ta Mike ta ajiye, sannan ta fito ta nufi Baban falonta ta kuna TV,

Kalonta take hankali konce ba abinda yake damunta, ta jawo wayarta ta danawa fati Kira, suka shiga labari sai kyakyata dariya suke

Cikin farar jalabiyarsa ya turo kofar ya shigo da salama aman Bata ji ba dalilin hankalinta ya dauku wajen wayar da take,

Ajiye ledar hanunsa yayi ya zuba mata ido yanda take labari tana dariya, ita Sam ba abinda ya dameta, ya lumshe Idannuwansa yana tunanin first night dinsa da ita du da yana cikin halin bacin rai aman abin nan yaki fita à ransa, ya sada kansa à ransa ya ce” anya kuwa zan iya hakura har sai ta yarda dan kanta,

Ya girgiza kai à hankali ya furta ” Islam

Dago kanta tayi da sauri sai à lokacin wata kunya ta dirar mata, to yaushe ya shigo dakin ma ?  Da sauri ta kali kayan jikinta ai kuwa ta diro da gudu zata nufi dakinta

Mubasshir ya saka hannunsa ya kamota ya janyota jikinsa ya rungumeta

Yar mahaukaciya ta shiga sisine kanta, aman kanshin turarensa na mugun birgeta, haka kawai ta shiga cusa kanta à jikinsa tana shakar kanshin turaran

Hakan ba karamin rikita shi ba yayi, domin sai yake Jin hakan tamkar tafiyar tsutsa take yi masa à kirji, à hankali ya dago da kanta ya zuba mata ido,

Yar mahaukaciya ta bude idannuwanta Jin an rabata da kanshin nan mai dadi ta kale sa, gabanta ne ya fadi wata irin soyayar mijinta ta kara tsarga mata jikinta, da sauri ta sada kanta kasa

Mubasshir ya saki murmushi ya kuma rungumeta, à hankali ya ce” kaunar Mubasshir ne nake hange à kwayar idanuwan islam ???

Yar mahaukaciya tayi shiru Bata bashi amsa ba, to mai zata ce masa ? Ita Kam lamarinsa ya girmimi tunaninta, gashi tun karfi ya koya mata kaunar kasancewa à kirjinsa

Mubasshir ya  dauki ledar hannunsa ya ja hannunta suka nufi dakinta, ya ce ” dauro alwallah muyi nafila

Jin yace nafila ta nufi bayi ta kuma yin Wata alwallar ta dawo, ta zumbula hijabinta na sallah, Mubasshir ya ja su suka yi raka’a biyu

Bayan sun gama ya dafa kanta da harshen larabci ya rufe Idannuwansa yana ta kwararo mata ada’a, sai da ya gama yayi mata yan tambayoyi bisa kan adinin musulunci Wanda cikin ikon ALLAH ta bashi amsoshi gamsasu, har zuwa wannan lokacin Yar mahaukaciya Bata dago inda Mubasshir ya nufa ba,

Mubasshir ya ce ” AM dauko plate mu ci abinci KO ?

Yar mahaukaciya ta ce” ai na sha jus din nan bana Jin yunwa KO kadan bara na dauko maka dai, tana gama fada ta nufi kicin ta fito da Baban plato ta ajiye ta bude gasasun zabi har Hudu ta juye ta ajiye masa jus din biyu ta zuba sauran à frij ta fitar da ledodin ta dawo ta shige bayi tayi brosh, ta dawo ta bude kayanta ta dauki wata Yar rigar baci ta dauki hijabinta ta nufi bayi ta saka ta zumbula hijabinta ta dawo ta dauki turarukanta na humrar ne, na fesawar ne, har ta juya zata konta ta ga turaren da aunty habiba ta Bata ta ce mata ta tabatar da ta zama mata cikakiya à gidan mijinta ta shafa shi, ta bude ta bulbula à hanunta ta shashafa à kowani sashe na jikinta tana Jin dadinsa à ranta, ta juya tayi bismillah ta gyara shinfidar gadon duda ba wani abin tayi ba, ta Haye tayi konciyarta

Du abinda take yana kalonta, mamakinsa ne ya karu ganin ta Konta da wannan katon hijabin dan yana dakin KO ?  Yayi mrmushi ya Mike ya dauki sabon tawul ya nufi bayinta dan yin wanka

Ya dauki lokaci kafin ya fito daure da tawul ya fita ya rurufo kofofin ya dawo ya rufe dakinta ya nufi gaban miroir ya fefesa tarare,

Yana gamawa ya kashe fitilar dakin ya Haye gadon

Yar mahaukaciya ta tashi da sauri tana zazaro ido ta ce” Yaya Mubasshir ka kuna fitilar nan mana, kana ganin duhu, Yaya Mubasshir mai zaka yi à dakina kuma bayan sun tafi su aunty ka koma naka dakin mana, y a ta y y y y y y y y y y y y y y y y y   hadiye sauran maganarta tayi sakamakon janyota da yayi ya hade bakinsa da nata ya shiga aika mata zazafan kisssss

Cikin kankanin lokaci Mubasshir ya wular da hijabin Islam yayi mata runfa yana sarafa harshenta, sakin harshen yayi yayo kasa da kansa inda ya shinshino abinda ya fitar da shi daga hayacinsa bai san lokacin da ya cafke na………………. Ya shiga sarafasu cikin kwarewa

Abinda da Wanda ta sha tsumi ta sha jiko ta bulbula tarare nan da nan ta maida hankali tana karbar sakon AA cikin na’am da sakon da yake Bata, Jin dadin hakan take, shi kuwa banda Bari ba abinda jikinsa yake, adu’ar saduwa da iyali ya yi hakan yasa Nayi baya Inaiwa Yar mahaukaciya adu’ar juriyar mijinta

I’m sorry iya hakan nake iya rubutawa☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹☹ sauran na samu mazga?????????Belles écrivaines du Niger

*’YAR ??*    

         *MAHAUKACIYA?*

*Na*

             *Sajida*

                          81

*Aunty Zainab kiyi ki gama min Docter deejart plz ?*

*Sister Dee ya haka ? Gaskiya page daya yayi mana kadan, kawai ki karo mana page din bintalo domin ya dauko sugar?*

wayarsa dake ajiye kasa ta kwashi ruri, à tare suka zabura, Mubasshir ya diro daga bed din Yar mahaukaciya tayi saurin mayar da kanta cikin bargon, yayi murmushi yana daga wayar

Idriss ya ce” kai wai ya haka Tunda safe Ina kiranka har karfe tara tayi  mai kake ne ?

Mubasshir ya zaro ido yana fadin ” what karfe 9 fa ?  Ya Salam abokina bara muyi sallah

Idriss ya zaro ido ya ce” Ina gidanka

Mubasshir ya ce” gidana fa ?  Haba bawan ALLAH da safiyar nan ? 

Idriss ya ce ” kasan ALLAH ka bude min KO Nayi maka aika aika à cikin gida

Mubasshir ya ce” aa yi hakuri, Bara na wurgo maka ky din falon kafin na sauko

Hakan kuwa akayi Mubasshir ya wulowa Idriss ky din falonsa ya bude ya zauna ya kuna TV domin yayi niyar fa bazai bar gidan nan ba sai da shi

Cikin nutsuwa ya dauki matarsa yayi bayi da ita inda ta dan sake da shi domin ta lura idan da taci gaba da nonokewa Mubasshir sai ta rame irin yanda yakeda takuran nan da son komai sai yayi mata,gashi ya mayar da lips dinta filin saukarsa du motsinsa sai ya mana mata kis

Haka suka gama ya jasu sallar asuba à karfe 9?,

Bayan sun gama Yar mahaukaciya ta duka gabansa cikin muryarta uwa ta yara ta ce” morning yayana

Mubasshir ya zuba mata ido yana kalonta yaki amsa gaisuwar tata,

Dago da kanta tayi tana kalon sa, yanayin kalon da yake mata sai da taji kunya, hudubar aunty habiba ce ta fado mata cikin ranta inda take fadin” karki baiwa mijinki damar wata ta waje ta birge sa, kiyi iya yinki dan ganin kin Wadata mijinki da dukan abinda yake bukata idan dai bai kaucewa hanya ba, sannan ki Kula da yannayin fuskar mijinki, Idannuwansa lebensa komai nasa yana iya yi miki magana da su, ki kasance mai gane kurmancin mijinki,

Yar mahaukaciya ta Mike ta cire dogon hijabinta, ta kuma cire abayar da ta dora saman Yar karamar rigarta fara tasss,  tana sane ta duka kamar zata cire wani Abu à akaifunta,

Mubasshir dake zaune ido ya zaro yana kalonta, kafin yayi wani yunkurin ta Mike,, ta juyo gabansa, cikin dabara ta dan ja rigar tata kasa, saman mamarta suka dan bayana à fili, nufo shi take, shi kuwa ya tsura mata ido yana son ganin abinda zata aikata

tana isowa daidai shi ta mika hannayenta biyu ta zagaye wuyansa da su,  ta Haye saman cinyoyinsa ta hade idannuwanta da nasa tana kashe shi da wani Shu’umin kalo, à hankali take matso fuskarta da tasa har ta ISO Daidai lebensa, inda Idannuwansa ke rawa ya kali idannuwanta ya kuma kali lebenta, gaba daya ya kunce ya zama wani sususu, maimakun ta mana masa Kiss sai ta fitar da harshenta ta lashi gefen fuskarsa wajen sajensa sannan ta Isa Daidai kunnansa ta hura masa iska cikin wata murya wace ni kaina sai da na zaro ido domin ban san Islam da ita ba ta furta” *Morning My Blood*

Mubasshir bai san lokacin da ya rintse Idannuwansa yana Jin saukar leben islam à kunansa da kuma sunan da ta nada masa, gaba daya tsikar jikinsa tayi wani irin tashi, bai san sanda yayi saurin jawo ta gaba dayanta jikinsa, jikinsa na mugun Bari ya lalubi lips dinta ya shiga kissing dinsu cikin zafafan Kiss,

wayarsa ta Kuma kwasan ruru tamkar an kara mata sautin kidan

Bai saki bakinta ba ya lalubo wayar sannan ya saki cikin kasalaliyar murya ya ce” Haba Idriss, haba Idriss ya zaka yi min haka, haba mana, shin mai Nayi maka da farar safiyar nan kazo kana shigar min haki haka ?  Ka tausaya min mana kana katseni

Idriss ya ce” la la la,  lale ma Mubasshir jarabarka tafi karfinka, toh wly au ka bude kofar nan ka fito ka raka ni zance au na hanaka koma meye kake bazaka yi shi ba wly

Yar mahaukaciya banda dariya kasa kasa ba abinda take, ta Mike a hankali daga jikinsa tayi gaba abinta

Mubasshir ya ce ” baby plz karki tafi

Idriss d’à bai katse wayar ba ya ce” tafi ke karki kula shi

haka dai à dole ba dan ya SO ba ya bude kofar bayan ya saka shadarsa maroon ya sauko inda ya bar Yar mahaukaciya tana shafa mai

yana saukowa ya nufe Idriss d’à maseefar taya zai adabi rayuwar amare, ba’a yiwa ango sauko haka

Idriss yayi murmushi ya ce” nawan wly ban rintsa ba, dama na samu Nayi hajiya traitement dinta na dawo dakina dan yin baci abin ya gagara, dole na tashi na shiga fadawa ALLAH kan ya kwata min zuciyar Rafi’at

Mubasshir ya ce ” abokina baka da dama, yanzu dan iya shege ka tsalake ka diro kan auntyna ?

Idriss ya ce” au yaushe kuma ka yarda da auntynka ce ?

Mubasshir ya ce” Tunda ta haifi My Islam

Idriss yayi dariya ya ce” ai kuwa nima na zama uncle dinka daga yau

zaiyi magana wayar Idriss ta kwashi kara,  ya daga da sauri yana salama

Elhaj Ilyass  ya ce” kaga fa abin arziki Idriss insha ALLAH yau za’a daura aurenka, yanzu haka zancen da nake maka muna gidan à zaune, ga su elhaj da mamana, da su hajiyar, Elhaj ya ce Tunda yau juma’a ne kawai mu je gidan liman mu shaida masa sai à daura idan an gama sallah

Idriss ya Mike da sauri yana ta wara ido murna ta cika masa ciki ya rasa ma mai zai ce hakan yasa ya mikawa Mubasshir wayar yana ta hamdallah,

Mubasshir yayi godiya ya ce” su din ma gasu nan tafe gidan

hakan kuwa akayi islam banda murna ba abinda take

Suna Isa ta bude ta fice da gudu inda Mubasshir ya zaro ido ya ce” ya Salam, islam no karkiyi ki fadi

Ina bata ma jinsa ta tura kofar ta shige tana ta murna sai dai Bata kai ga karasawa ba ta ja ta tsaya tana kalon ikon ALLAH, Aunty Rafi’at ce sai kuka take shekawa an kewaye ta

Turo kofar suka yi suka shigo inda suma suka ja suka tsaya suna kalon ikon ALLAH

Rafi’at ta ce” haba aunty, haba hajiya, kawai dan yaro ya ce ” ga abinda yake SO sai à biye masa, haba dan Allah yanzu da girmana à hada ni Aure da yaro karami ?  Nafa girme masa fa kuma wly tausayina ne yake ba wani sona ba

hajiya hafsat ta ce ” sister wai meye haka ne ?  Haba taya za’a zauna ana nuna miki gabas kina kalon yama ?  Sunar ce bakya SO ?  Idan har baki godewa ALLAH kan ni’imar da yayi miki à yanzu mai zaki yi ?  Taya zaki fasara kyautar da Allah yayi miki adu’arki da ya amsa da wata fasarar ? Rafi’at à da inai miki kalon kinyi hankali ashe dai da sauran ki,

hajiya hawau ta ce ” aa hajiya ku tashi ku barni da y’ata mu zanta kun ji ?

Hakan kuwa akayi sai da suka tashi suka ga su Mubasshir sunyi cirko cirko da hanu suka yi musu nunin su fice karta gansu

hakan kuwa suka shige inda hajiya hawau ta dage wajen kontarwa da hajiya Rafi’at hankalinta kan auren ta da idriss

ya kasa tsaye ya kasa zaune, du labarin da suke yana dai jinsu ne aman baya fahimtar abinda suke fada,

Hajiya hafsat ce ta fito da faranti da abinci à ciki,  ta ajiye ta dauko ta shiga zubawa kuskus ce ta sha muryar jan nama sai kanshin kayan yaji ke tashi, ta mimika musu,, har ta kai kan Idriss ta mika masa ta ce” Idriss ka dawo cikin hayacin ka mana,

Idriss ya juya à hankali ya shiga cacakar abincin

Yar mahaukaciya ta shigo da jus jus ta ajiyewa kowa à gabansa, ta juya ta dauko nata farantin ta zauna Kusa da hajiya Fadimatu tayi bismillah ta debo ta kai bakinta

Wani irin Abu taji ya bigeta à hancinta na kanshin kayan yajin nan da tafarnuwa, kafin ta Ankara tayi wani abin sai kawai taji cikinta ya fara hautsina mata sai ga amai

da gudu ta mike zata nufi Bayi aman Ina dole ta duka à nan tana kwara amai tun karfinta, dan kwalin kanta ya fadi kasa haka mayafinta domin wani irin tukota aman yake

da gudu Mubasshir ya rigayi kowa isawa wajenta ya kamata yana tambayarta Lafiya ?  Mai ya sameta ?  Wani abin ta hadiye ?

Da kyar ta samu ta gama aman du ta galabaita ya dauketa yayi bayi da ita dan ya wanke mata wajen da ya baci à jikinta, ita kuwa hajiya Fadimatu sai sintiri take tana tambayar ta shigo ne bayin ? inda hajiya hafsat ta shiga gyara wajen

Idriss ya Mike ya fice dan dauko kayan aikinsa domin yana Docter gida har uku hakan ya sa baya tafiya ba malet dinsa mai dauke da yan abubuwan da ya dace domin aikinsa

Daidai zai fita suka yi karo da Hajiya Rafi’at, da sauri ta zaro ido tana yi masa kalon mamaki domin Bata san shigowarsu ba, ido Hudu suka yi inda gabanta ya fadi, tayi saurin sada kanta kasa shi kuwa yaki dakin hanyar balatana ta fice,

Hajiya hawau ta taho tana fadin lafiyarku kuwa yayanan ?  Naga kun tsare hanyar ficewa

hajiya Rafi’at ta ce ” hajiya shine ai ya tsare hanyar fa

Idriss ya ce” to hajiya ta shige mana ?

Hajiya hawau tayi murmushi ta juya tama daina shigan balatana su fake da ita

Rafi’at ta juya itama zata bar wajen da saurinsa ya riko hannunta ya jawota tamkar wata beby ya hadeta da garun dakin

Idannuwanta ta rintse tana mutsukmutsuk da baki, Idriss ya tsurawa bakin nata ido Yana kalonta

Jin yayi shiru ne t’a bude idannuwanta ta sauke su à cikin Idannuwansa, ta kasa janye idonta daga NASA

Idriss ya saki murmushi à hankali ya ce” hei *I Love u*

Aunty Rafi’at ta zaro ido ta kasa dauke idannuwanta daga fuskarsa gabanta na dukan uku uku

Idriss ya kashe mata ido daya ya ce” Yaya dai madame, kalon fa ?????

Da sauri ta sada kanta tabi ta kasa hannun NASA tayi dakin da gudu tana ajiyar zuciya

Yayi murmushi y’a ce ” she love me too,  yayi gaba abinsa

Yana dawowa dauke da kayan aikinsa ya shiga aune aunensa inda ya bukaci fitsarinta, bayan tayi ta bayar ya kuma daukan jininta ya fice, ita kuwa tayi lamo à cinyar hajiya Fadimatu, inda Mubasshir yake zaune rike da hannunta daya yana dan murzawa, hajiya Rafi’at tana dan shafa gashin kanta ita kuwa hajiya hafsat sai cin abincinta take domin juna biyu ne da ita mai shegen sakata kwadayi du da ba Wanda ta fadawa har shi kansa mai abin,

Hajiya hawau ta kare mata kalo ta ce” wai y’ata watansa nawa ?

Hajiya hafsat ta zaro ido domin ta san da ita hajiya hawau take, ba shiri ta Mike tana fadin ” Wa ?,  tayi gaba ba tare da ta tsaya an fada mata Wa din ba,

ai kuwa hajiya Fadimatu tayi dariya ta ce” haba kin rigani à fili na rigaki à badini hajiya, Allah ya raraba Lafiya

Yar mahaukaciya ta zaro ido zata Mike Idriss ya shigo da result yana ta murna ya ce” an daura auren

Hajiya Fadimatu ta ce” oh yaren zamani idriss to barka

Idriss ya dan sine kai yana mikewa Mubasshir takardar gwajinsa yana hangen Rafi’at da ta sada kanta kasa tana share hawaye, wannan karen kam kukan dadi take( Wa ya fada miki)

Hajiya hawau ta shigo tana fadin” an daura Aure ba ango, ya akayi baku je masalaci ba ?

Mubasshir da ya buda takardar bayan ya yiwa Idriss barka yayi saurin cewa what ?  Yana zaro ido ya kali Idriss yace”docter baka fasara min abinda nake gani ba ?

Idriss ya ce” congratulation, abinda ka gani hakane

Mubasshir yayi saurin kai kansa kasa yayi sujada yana ta murna, yana dagowa ya dagota ya rungume à gaban su hajiya Fadimatu wace itama murnar ta hanata zama, à tare suka yi gaba suka bar masa dakin domin kara rungumeta yake yana lalubar cikinta dake shafe yana fadin”beby boy or girl hi, dadyne, how are u ?  Kana cin abinci ?  Kana jina ?

Yar mahaukaciya sai sine kai take a ranta tana mamakin rashin kunyar AA

Alhamdulilah , Alhamdulilah, dukan godiya ta tabata ga ALLAH buwayi gagara misali da ya bani ikon ganin Karshen novel dina *Yar Mahaukaciya* Ina fatan du Wanda ya karantashi ya karu da abin karuwar dake ciki sannan Ina neman gafarar du Wanda na batawa sanadiyar wannan novel nawa na biyu bayan *Duk karyar kada na ruwa ne* , Allah ya hada mu à novel dina na gaba mai suna *Daga tafiya daukan soja* Na gode taku y’arku, kanwar ku, yayarku *Sajida* Y’ar mutan Niger,.

About AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *