UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 20 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 20 BY SHATU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Seda Junaidu yayi kwana uku baya zuwa ko kofar dakin Hajja indai ba wanka zaiyi ba ko Kuma dai wani Abu zai kaishi bayi din,  abinci ma har daki take kawo mishi yaci, sede yayi ta juyi Alan gado, kannen shi ma har adduar ya samu sauki suke Masa ko ya fita a dakin su samu sararin zama, Amma da sun shigo kwakwaran motsin da Bai gamshe shi ba zasuyi ya dinga zaginsu, ko ya wurga musu abinda ya fi kusa dashi. A kwana na hudu ya fito daga daki zai je wanka, Hajja sake zaune tace+

” Junaidu dawo Ina son magana da Kai”

Ba tareda ya juyo ba yace

” Wanka zanyi ki jira na fito”

Ya saka kanshi ya nufi toilet, Fatima ta Gama hada ruwanta me zafi ta Kai toilet zata yiwa Yara wanka, ta manta Bata matsa musu toothpaste a brush dinsu ba, shikuwa Yana zuwa ya wuce ciki ya turo kofa ya fara wanka, Babu jimawa ta dawo hannunta dauke da bar of soap, ta Dan tsaya ganin toilet din a rufe tace da zainab dake kusaa da gurin

” Waye ya shiga toilet dinnan?”

” Mama Yaya Junaidu ne!”

Take ta Bata Rai ta Isa kofar ta fara bugawa tana fadin

” Dallah malami ka sauri ka fito Kuma wallahi karka taba ruwan da yake ciki”

Bai ce Mata komai ba ya cigaba da wankan shi, Babu jimawa ya zura jallabiyyar jikin shi ya fito, ta mike Bata ko kalleshi ba ta leka bandakin sede Babu ruwa cikin bokitin, ta fito da sauri ta biyo bayan shi tana fadin

” Junaidu waye ya baka damar amfani da ruwan daka tarar cikin bokitin”

Nanma Bai kalleta ba balle tasa ran zai Bata amsa, wannan halin nashi ke batawa Fatima Rai, ta zauna ta dinga bambami tana fada, Babu wanda yace Mata ci kanki, sede ya girgiza Kai kawai ya Mata shiru to hakan ke Bata Mata Rai a cewar ta ya maida ita mahaukaciya. A dakin shi ya shirya daga nan baima Kara shigowa ciki ba ya fita daga nan. Hajja na daki tana jiran ya dawo Dan ita se lokacin ta tuna tunda yayi jinyar man baifi say biyu taga yayi sallah, ita Dana tasan baya zuwa masallaci. Jin shiru Bai dawo ba, se ta fito ta samu salama tana Wasa tace Mata yaga Junaidu tace ai tuntuni ya fita, ta girgiza Kai kawai ta nufi dakin ta.

Junaidu garejin su ya wuce, Yana zuwa ya samu an Kama aiki sosae, wajen oga yaje Suka gaisa ya tambaye shi jiki sannan ya canja Kaya ya fito ya Kama aiki, se wajen hudu Suka tashi sannan yaci abinci ya wuce can sha’iskawa wajen abokan shi. Suna zaune gaba daya gurin ya turnuke da hayakin zuke zuken da suke, Kuma ka kalle su Yara be sosae tunda shima Junaidu a lokacin shekarun da Basu for Sha shida ba. Ya zauna bayan an mika Masa tashi Jason, seda ya zuka sosae sannan ya amsa jarma da ya tambayeshi ko abinda yaji gaskiya ne cewar abokiyar zaman Babar shi ce ta saka yayi kwana uku a station

” Itace, har yanzun tunanin abinda Zan Mata nake”

Halilu dake gefe yayi dariya ya buga kafa yace

” Amma fa ka Bata kofa da yawa, Taya zata maka wannan abin?”

Junaidu ya shafa kanshi Yace

” Kawai ku bani shawarar abinda Zan Mata”

” Ni ai babata ma da Naga zata min katsalandan gurin teacher na zaure na kaita, aka rufe bakinta sede ta kalleni amma Bata Isa tayi magana ba”

Junaidu yayi shiru yana tunani kafin yace da Malam

” Waye teacher na zaure”

Suka bushe da dariya, Malam har da kwarewa saboda dariya, seda sukaga ya Bata Rai kafin Suka daina dariyar, Jarma yace

” Tashi muje mu Kai matar can gurin teacher  Allah nan gaba ko ance tayuwa wani sharri ba zata iya ba”

Aikuwa Suka tafi can wani jeji ga yamma tayi Amma ko tsoro basayi haka Suka dinga Shiga daji sannan suka hango wani zaure an saka fitilar kwai, ni kaina tunanin inda Young boys kamar su Jarma Suka San gurin malamin tsubbu. Gaba daya gurin yayi dubu se wani candle kwaya daya da yake ci, ga zafi ga kauri na abubuwan da yake konawa, Suka shiga malamin na zaune saman fata, hannun shi rike da zungureren carbi me beads dubu, Yana ja Yana fadar Abu da ba lallai kaji ba sede motaswar da bakin shi yakeyi. Guri Suka samu Suka zauna seda yayi wajen mintina biyar kafin ya dube su yace

” ‘Yan samari ya akai? Me ke tafe daku”

Jarma ne y fara Masa bayanin abinda yake tafe dashi seda suka Gama sannan yace Junaidu ya fada Masa da bakin shi

” Matar ta takura min tana shiga min hancina, so nake ayimin maganin ta”

Malam yayi dariya yace

” Wannan shi ne Abu mafi sauki ma da zamu iya maka”

Ya Ciro was kulle kulle ya bashi yace ya dinga turarrawa a gida na kwana uku, na farko ya tuarara a dakin shi na biyu yayi a zaure na uku Kuma ya turara idan biyu da rabi na dare yayi. Suka ma Malam godiya, Jarma yace

” Allah ya gafarta Malam me zaa baka na sadaka”

Naira dari biyu kawai ya bukata, Suka bashi sannan Suka fito, da farko jikin Junaidu yayi sanyi yace ma Jarma

” Anya Zan iya kuwa?”

Malam yace

” To tsayawa zakai ka dinga barin ta tana naka abinda take so? Kayi maganin ta kawai yafi”

Da hakan sukai convincing dinsa ya yadda, seda suakje  gidan su Jarma shi ya bashi kaskon da shima yayi turaren dashi lokacin. Yana karba ya wuce gida ya samu an Gama abinci ana kokarin kashe wuta a mangal, dake yawanci anan suke Miya. Salama ce ke kokarin zuba ma wutar ruwa, ya dakatar da ita, tayi saurin matsawa tace

” Yaya sannu da zuwa!”

Ko kulata baiyi ba balle tasa ran zai Bata amsa ba, har ya dauki garwashin se ya fasa ya Bari akan washegari se yayi da safe. Aikuwa washegari Malam ya same shi a daki, Yana zaune malam ya shigo, seda gaban shi ya Fadi yaji tsoron kada malam fa yasan yaje gurin teacher na zaure, in jisu da fada.

” Junaidu yaushe rabon da kaje makaranta, principal dinku ya kawo min karar ka”

” Zanje yau!”

Ya bashi amsa a takaice, Malam ya Mike zai fita se ya juyo yace

” Ya kamata ka dinga zuwa masallaci kana sallah, ita sallah tana sanyaya zuciya”

Daga haka ya fita, Junaidu ya fito rike da kasko ya sauke ruwan zafin Hajja Huwaila ya kwakule duka garwashin dake ciki ya wuce dakin shi, Fatima dake dakan yaji a gefe ta kwashe da dariya tace

” Dara taci gida, dadin abin na uwarka ne ba ni na marainiyar wayon ka ba”

Yana shiga daki ya kulle ko Ina ya fita wutar se da ta ruru sannan ya fara jefa itacen daya raba gida uku, saboda yadda garwashin ya ruru se wuta take ci, hayakin ya fara fita zuwa tsakar gida Wanda yayi daidai fitowar Hajja Huwaila, sauri ta fara fadin

” Wannan menene yake hayaki daga dakin Junaidu, kada dai gobara ce?”

Ta tambaya Amma Kuma kanta take wa tambayar Dan tasan Fatima ba amsa zata Bata ba, cikin daurewa saboda ciwon kafar ta nufi dakin shi, Yana zaune yayi daidai Yana ta Kona itace da saiwa, Banda hayaki da tukuki Babu abinda ya cika dakin, Hajja ta yaye labulen tana fadin

” Junaidu me kake Yi haka?”

Ya Kara hade fuska cikin muryar shi da ba amo ne da ita ba yace

” Ni bana son ana shiga min cikin rayuwa ta gaskiya”

Hajja ta cije leben ta zuciyar ta Babu dadi ta juyo, Fatima tayi dariya tace

“Da haihuwar wasu gwara barin su!”

About AIS

Check Also

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 16 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 16 BY SHATU To meye matsalar ki da abinda ta Haifa, …

2 comments

  1. Pls if possible it should be daily post, the novel is interesting.thanks

  2. Hey how are you doing? I just wanted to stop by and say that its been a pleasure reading your blog. I have bookmarked your website so that I can come back & read more in the future as well. plz do keep up the quality writing

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *