UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 19 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 19 BY SHATU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Bayan Malam ya Gama sauraron duk bayanan zainab se ya sakata a gaba Suka tafi police station Dan ita kadai ce zata saka ayi bailing Junaidu. Tunda dama it’s din ta hada husumar so seta Zama wadda zata warware ta. Lokacinda Suka Isa gaba daya Junaidu ya canja kammanni saboda dukan da ya Sha, tunda Suka shiga DPO yace a lallasa masa shi har se ya gane baa dukan mace. Ga Junaidu da bakar zuciya haka yaki Basu hakuri se amsar dukan yake. Malam na Isa yayi ma officers din dake tsaye a reception bayani,  daya daga ciki yace Masa+

” Malam kawai ka tafi Dan bansan ranar belin wannan gaggararren Dan naka ba”

Malam ya gyara tsayuwan shi yace

” Idan ba zaku damu ba Ina son magana da DPO din ku”

Daya daga ciki yace

” DPO baya gari yaje headquarter acan Dutse”

Malam ya gyada Kai yace

” Idan ba zaka damu ba ko Zan samu num…”

” Baya cikin aiki, kaga Malam Muna ganin girmanka a gurinnan, tunda munce ka wuce kawai ka tafi”

Malam ya Kama hannun zainab Suka fita a station din, haihuwa kenan sanadin ta Babu abinda bazai same ka ba walau sharri walau khairi, shi Bai taba zuwa police station ba Amma dalilin Junaidu yau shi ake cewa ya fita duk girman shi da darajar shi.

” Ai da ka sani ka tatse shi wallahi, malaman nan kudi be dasu, yaran Yan siyasa ne fa”

Dayan yace

” A’a gwara dai a kyaleshi saboda wannan Yana da connection da manyan mutane kada mu jawa aikin mu”

Yana zuwa gidan ya tarar da fada ya barke tsakanin Fatima da Hasiya, Hajja nata kokarin raba su Amma sunki, sede suka hi sallamar shi sannan cacar bakin da suke ta lafa, Bai ce musu komai ba ya nufi dakin shi, Amma kowacce Tasha jinin jikinta, Hajja ta bi Bayan shi ta sameshi zaune ya kurawa guri daya idanu, he looks disturbed. Zama tayi tana fadin

” Malam kayi hakuri kada ka Bari abin Junaidu ya dameka, adduar shiriya ita ce zata rabamu dashi”

Ya gyada Kai Amma Bai ce komai ba hakan ya tabbatar Mata ba zaiyi magana ba, se ta tashi ta fito dukda tana son taji yadda aka Kare a station din Amma Bata son damun shi, Kuma alamu sun nuna baayi nasara ba, tunda ya shigo babu Junaidu. A tsakar gida taji zainab na fadawa Hasiya yadda sukai a station da officers din, hankalinta ya Kara tashi to Amma ya zatayi? Sai dai ta zubawa sarautar Allah idanu. Wasawasa magana se ta Zama babba tun Malam yana zuwa wajen police din suna Masa yawo da hankali har ya kyalle su, Fatima Kuma sunyi magana da DPO akan se Malam ya Bata hakuri sannan zai sake Junaidu. Ko fahimtar abinda take nufi yayi se ya kyaleta Bai ce da ita komai ba Amma se ya kaurace Mata, kwana biyu da tayi a dakin shi magana ta fatar Baki Bata hada su ba, hankalin ta yayi mummunan tashi, washegari wajen azahar se ga Junaidu an sako Shi, fuskar shi ta kumbura saboda duka, ga jikin shi da duk shatin bulala a jiki. Hajja Huwaila ta daura ruwan zafi tasa yayi wanka, ta gasa Masa jiki sannan ta shafa Masa man zafin da Hasiya ta kawo Mata. Yaci abinci ya kwanta a ranshi Yana saka next abinda zaiyi!

Na karasa gaban gadon tareda jijjiga Abbu, Amma a hakan nan dai yake kwance lifeless, Babu digon numfashi dake jikin shi, gaba daya jikin yayi sanyi, kwayar idanun shi a rufe tamkar me bacci, hakan ya tabbatar min daga baccin aka zare Masa Rai. Naja baya da sauri tareda rufe bakina da hannuna Ina jin ilahirin jikina Yana rawa kamar ana kada min mazari. Hajiya na kuka ta fita yayinda ni banyi kukan ba sede Ina tsaye a gaban shi Ina fatan Nanny ta buga min gefen gado na ta tashe ni tace min na tashi zanje makaranta, Amma ba mafarki nake ba, idanuna biyu it’s happening in reality Abbu is no more.  Nayi shiru ban masan me zuciyata ke sakawa ba a wañnan lokacin, bazan iya Baku labarin yanayin da na shiga ba nasan dai I was more than shattered. Babu wata kalma da Zan muku amfani da ita ta nuna bayyana muku halin da na shiga, Wanda kadai ya rasa iyaye shi zai fahimci me nake nufi. Ina nan a tsaye na fara jin koke koken mutane, Ina tsaye na tsira Masa idanu, Kawu Sa’idu da wasu daga cikin Yayan sarki Suka shigo, duka Ina tsaye aka fara kokarin shiray shi, nasan an ja hannuna an fita Dani, but bazan iya cewa waye ba, kowa kallon shi kawai nake na Zama tamkar statue. Gidan kafin wani lokaci ya cika dam da mutane,  se kuka suke Amma gani nake duk yadda suke ji ba zai Kai yadda nakeji ba. Mummy Maryam da Rooks Naga sun shigo, ta rike hannun Mummy dake wani irin kuka tamkar ranta zai fita Amma Ina nikam nawa idanu ne. Seda aka fito dashi cikin makara sannan na Mike tsaye, Kawu Tijjani yazo ya rike hannun na idanun shi se hawaye ke fita yace

STORY CONTINUES BELOW

” So ki Masa addua”

Haka na bi bayan shi na zauna gaban gawar, my Father,my love, Abbuna, abokina, uwata da ubana? Shi ne a cikin makara ya tafi, ya mutu Kuma bazai dawo ba. Se na kankame shi na saki wani kuka me daci Ina fadin

” Abbu why will you leave me? Bansan kowa ba, you’re my everything Abbu ya zanyi rayuwa yanzun…”

Na kasa karasawa saboda gaba daya na shide, ban Kara farkawa ba se Bayan awoyi goma da wasu abubuwa sannan na farka a firgice Ina Kiran sunan Abbu, Nanny dake gefena tayi saurin rungume ni a jikinta tana kuka, tana rungume ni nasan ita ce Dan haka na saki jikina na fara kuka bance komai ba Amma radadin da nakeji a cikin zuciyata ya wuce gaban na rubuta muku. Allah sarki Abbu ya tafi ya barni se nake jin inama Nima na mutu na huta, Babu abinda ke tsoratar Dani shi ne na tuna Wai Dole Zan rayu Kuma Babu Abbu.

A cikin gida an kaishi makabarta a wañnan yammacin, itama Hajiya tunda aka dawo da abinda aka lullube shi ta mike se kuwa ta yanke jiki ta Fadi, Babu shiri aka dauke ta se Kano asibiti, kafin suje ta rasu itama, Dan hakan mutuwar se ta hade Mana, ga ta Abbu ga ta Hajiya, kowa ka kalla kasan ba karamin blow sakon ya bashi ba, a lokaci guda Allah ya nufi tafiyar su! Rayuwa kenan. Kwana uku gida ya watse Nima aka sallamoni a asibiti , na dawo gidan kowa ya kalleni yadda na rame na lalalce lokaci daya se hawaye ya fita a idanun shi, fada min rasuwar Hajiya ta Kara daga min hankali Amma ban nuna ba Dan ko magana banayi, bana kuka se idan Babu kowa na zauna nayi kuka na share hawayena, a Rana ta biyar Yan maiduguri suka zo, suka Mana gaisuwa, Mummy da Nanny ke kaina wajen tabbatar da naci abinci Kuma Ina nan, wani lokacin ji nake kamar na gudu na fada ruwa Nima ace na mutu da wannan kuncin da nakeji a cikin Raina. Da zasu tafi sukace suna so su tafi Dani nan Mummy ta nuna musu ita zata tafi dani Dan hakan se suka Mana sallama suka tafi, wani lokacin Ina jin inama na bisu may be da duk haka Bai faru ba, to Amma idan na kara wani tunanin se Naga duk abinda ya faru Dani dama is already written in my book, Dole ne ya faru Dani. Ranar sadakar bakwai aka watse ranar nayi kuka Dan Ina zaune kowa ya dinga bajewa sede su shafa kaina su ce min nayi hakuri, nayi kuka na rashin gata, na rashin madafa na rashin sanin yadda rayuwa zata zo min. Abinda kadai ya rage min shi ne Nanny da Rooks. Nanny ta zauna gefena tace

” Ki ci abinci kinji, ko so kike kiyi rashin lafiya?”

Ina kuka nace

” Meye amfanin naci abincin, Abbuna ne ya mutu fa Nanny, banida kowa Nanny”

Ta rungumeni tana shafa min baya hawaye itama na bin fuskarta, tausayi na na dawainiya da ita, shigowar Mummy da Uncle Babawo yasa na Mike na nufe shi, ya rike hannuna Yana lallashina, se akai saa nayi shiru har Nasha tea. Fita sukai Shi da Mummy tace

” Ina ganin Zan tafi da ita kawai, kallonta is breaking my heart”

Ya shafa kanshi Yace

” Ita ce abin tausayi Kam, da nayi aure ni Zan dauke ta Amma Zan bar Miki kawai”

Washegari Suka zauan meeting akan fate Dina, Mummy ta dubi kawu Sa’idu da mamaki tace

” Yaya Sa’idu ni Zan tafi da Afiyya tunda kaga dama ta Saba da Rooks”

Ya dago idanu ya kalleta yace

” A’a ba zata je gidan wani ta zauna ba watarana ayi Mata Gori ni Zan rike ta”

Kawu Tijjani yace

” Eh da wannan dukda nasan Daddyn Rooks bazai taba haka ba, dama mafi Dadi ace mu mazan muka riketa. Sede Yaya ka Bari na tafi da ita kawai”

Ya Kara Bata fuska yace

” Ni Zan rike ta anan Ringim, magana ta kare”

Mummy ta hade Rai tace

” Yaya Sa’idu in har bazan dauki Afiyya ba to kaima ba zaka dauketa ba, Allah ya gani sede Tijjani ya tafi da ita, ya zaayi yarinya ta tashi a Abuja a dawo da ita Ringim”

” Ke wawiya ce Maryam, ke baa Ringim din aka haife ki ba? Mutuwa kikai da Kika girma anan. Kunji maganar banza”

Haka dai sukai ta musu aka tashi Babu dadi, Mummy tace musu Dole suyi fighting din Kawu Sa’idu ita Bata yadda dashi ba, washegari da suka je aka raba gadon Abbu, sannan aka raba na Hajiya nan ma yace se de a bashi nawa anan ne Uncle Babawo ya fito da will din Abbu kan dukiya ta ya damka ta a hannun Uncle Babawo haka kawu Sa’idu ya hakura. Bansan me ya faru ba kawai se dawowa sukai sukace Wai a gidan Kawu Sa’idu Zan zauna, Nanny ta bi Mummy dake ta kuka ganin Ina kuka Dan taji me yasa bazan zauna hannun daya daga cikin su ba, Mummy tace itama ba yadda zatayi she can’t fight him. Ina ji Ina gani aka tattara kayana duka aka maidani gidan Kawu Sa’idu Kuma yace Nanny ta tafi maiduguri!

Cikin kiftawar idanu na rasa koma, mahaifina, gatan da nake dashi da komai na tashi banida kowa da Zan kalla na Kira a matsayin Wanda zanyi kuka a kafadar shi. Ina zaune Nanny ta Gama hada kayanta taxo ta zauna gefena ta rike hannuna cikin barbarcin da take koya min Kuma na dauka sosae Dan duk maganar da zakai Ina ji, Kuma Ina mayarwa sede ba can sosae ba.
” Kiyi hakuri nasan komai zai canja, Amma kiyi hakuri kiyi addua, n samu kawun ki Tijjani jiya na tambaye shi tunda Anty Maryam Bata bani amsa ba, yace Yallabai yace su amince da duk hukuncin da kawun ki Sa’idu zai yanke, shiyasa suke Masa biyayya. Ki sani zamanki a gidan shi kamar biyayya kike ga Yallabai, kiyi musu addua Zan dinga zuwa duk lokacin da na samu dama. Ki rike maraicin ki kiyi amfani da illimin ki, kiyi hakuri Allah Yana tare dake…”
Nayi ta kuka da hannunta cikin nawa Amma ko sau daya ban manta abinda Nanny tace ba, haka Ina kallo ta tafi ko waiwaye babu, dukda ta hada min kayana tsaf tace da Mummy ita ba zata iya ganina na koma wannan gidan ba. Mummy da yamma ta Gama hada kayan su da Rooks Dan washegari zasu tafi NY, Muna daki na idar da sallar laasar, Rooks ta zauna gefena mukai shiru se can tace
” I’m going to miss you Afeey”
Na Dan Mata murmushi Amma bance komai ba, ta Kara gyara Zama tace
” Promise me duk halin da kike ciki Zaki fada min?”
Na Mika Mata hannuna nace Mata na Mata alkawari, shigowar Mummy tasa mukai shiru, ta zauna ya nade kafafun ta sannan tace Rooks ta fita zamuyi magana, haka ta mike ta bamu guri. Mummy ta Jima ta na yimin nasiha wadda na rike ta tsaf sannan tace duk abinda nake so na Kira su zasu bani. Nace Mata to , Bayan maghrib muka shirya se gidan Kawu Sa’idu, na taka zauren da kafata Ina jin kuncin a cikin zuciyata, tun a lokacin na fahimci duniya zancen banza ce, Babu wani Abu da zai daure. Suna zaune an kunna wasu kwayaye Yan kanana an sakale sun haska tsakar gidan, suna zaune akan tabarma Hafsa nata kuka, yayinda Mino ke wanki se Ummaah su na raba abinci, akwatina na da aka kawo tun Rana suna aje a gefe yadda aka barsu, mazan Basu nan. A hankali kamar kwai ya fashe min a ciki na tako na zauna gefen Siyama inda Rooks da mummy Suka zauna, ni na fara gaida Ummaah ta amsa tana cewa Mummy Bari ta karaso. A cikin su Babu Wanda yayi min magana Nima haka, seda ta gama sannan ta dakko kujera ta dawo gefen Mummy ta zauna, nayi jugum Ina bin gidan da kallo, Ina ayyana wacce rayuwa zanyi Kuma a gidan, gidan Kato ne sosae, sede anyi rashin basira a ginin, an bar katon tsakar gida Amma Kuma anyi dakuna biyu kawai se kitchen Wanda bama amfani take dashi ba se bayi guda daya, ta can gefe wajen zauren gidan shi ne dakin dasu Yaya suke ciki, gidan mu na Abuja ya fado min, my spacious bedroom, parlon mu, garden da komai na jin dadin rayuwa. Ina wannan tunanin har bansan sun Gama magana ba se da naji  ta taba ni sannan na kalleta ta min alamar na tashi , na kuwa Mike na bi bayanta, Mino ta raka mu dakin, Babu komai se katuwar katifa an gyara ta da bedsheet, daga nan Babu komai, Mummy ta gyara min zaman akwatina na, ta nuna min komai inda yake sannan ta dakko kudi tace min na boye inda ga amfani dashi kadan kadan idan ya Kare zata Aiko min da wani. Ta Kara min nasiha sannan ta tafi ta barni a tsaye a tsakiyar dakin nayi shiru Ina tuna Abbu. Bansan iyakar lokacin da na dauka a tsaye ba seda naji  muryar Mino tace min nazo Ummaan su na Kirana, na fito a sanyaye naje na tsaya nace
” Gani!”
” Dallah samu guri ki zauna”
Na koma na zauna aka Miko min Yar karamar silver da tuwo a ciki, na kalla tuwon ban ma gane miyar dake ciki ba saboda abinda aka haska gidan dashi ya fara disashewa, na wanko hannu na saka hannu na tasting miyar first se naji kuka ce, na Dan saki jiki naci Amma se half way naji cikina ya koshi, Dan hakan na tsame hannuna Amma tsoron cewa nake na koshi, se na ta juya hannuna a ciki, se can naji Hafsa da Siyama dake bayana sun fara fada, hankalina haya kansu Amma Ina jin fadan sede ba zance ga dalilin fadan ba, Ina zaune naji Mino tazo kaina tace
” Ummaah Bata cinye ba”
” Karba ki bawa Hafsa, ni abinda ya rage anan na babanku ne dasu Baba”
Nayi saurin cire hannuna tace min
” Kin koshi?”
” Kar ta koshi Mana,  tun karfe nawa na zuba Mata abincin, Wasa ake?”
Haka Suka karba abincin Suka bawa Hafsa, na mike na wanke hannuna ina share hawayena na tuna yadda Abbu zai ta lallaba ni har se naci abinci, na wanke fuskata nayi alwala nazo nayi sallah, Ina cikin sallahn naji sallamar Yaya, daga yanayin yadda yake fadin
” Ina Afiyya?”
Nasan Yana cikin farin ciki, Amma response din Ummaan su ya Sagar Masa da gwiwa
” To uban shishiggi, daga shigowar ka ko ni baka tambaya ba se kanwar uwarka Afiyya, gaba daya ku tsaya ki jini man, Afiyya tazo ta zauna bance kowa ya zurfafa muamula da ita ba, bana son kawance ko shishigge mata, ba wata bace, itama ya ce kamar kowa. Ka dauki abinci kaci”
Yayi shiru duka suna sauraron ta, Yaya yace
” Kai Ummaah, Afiyya abar tausayi ce fa, ya zaai ba zamu jata a jiki ba”
” Mhmm kanwar uwarka ba, Dole Ina fada kana mayar min”
Baice Mata komai ba ya dauki kwanon shi ya fita, na Jima a zaune sannan nace da Mino dake zaune gefena,
” Zanyi bacci, Ina Zan kwanta?”
Ta kalleni sannan ta kalla gefen Ummaan su tace cikin kasa da murya
” Ko fadawa Ummaan mu”
Nayi shiru Ina tsoron tunkarar ta, anan nayi ta guangyadi sauro ya samu ya cije ni son ranshi, se Susa nake, can Siyama ta tashe ni tace naje mu kwanta, haka na Mike nabi bayanta, Ina ayyana yadda zamuyi bacci akan katifa mu hudu, lucky enough Ina zuwa na tarar an Yar min da Yar karamar katifa irin 6×6 dinnan, net ta Mika min na daura, na rike net din Ina tunanin to ya Zan daura, Mino ganin Ina tsaye ta min bayani tana jin motsi tayi shiru, se na fahimci they all want to be nice tsoron iyar su suke. Wani irin dauri na Masa na Shiga na kwanta, gaba daya ya kwanta a fuskata Dan haka da asuba na tashi nayi alwala naji fuskata kamar an zuba Mata barkono, na cije bakina Ina kokarin danne azabar da nake ji, a hakan nayi sallah duk suna bacci Basu tashi ba, gwara Yaya Ina ban daki naji motsin shi. Anan bacci ya daukeni se fadan Hafsa da Siyama ya tasheni, na tashi na cire net din fuskata na azaba kamar zata kwakwabbo, na gaida Mino dake cemin na tashi na kwashe kayan shimfida ta, nace Mata
” Kinga fuskata zafi take min”
Na fada Ina yatsina fuska, da a gidan mu ne da tuni na tada hankalin kowa kilan se an kaini asibiti, ta taba fuskar tace
” Net ne, zai warke kinji”
Na gyada kaina, anan ta nuna min yadda Zan saka yau sannan na kwashe kayan muka fito, ta bani tsintsiya Wai nayi shara, na kalla tsintsiyar na kalla tsakar gidan na saki ihu a kaina, Ina neman agaji a gurin Allah!
Na Kara kallon shafcecen tsakar gidan sannan Kuma na kalli tsintsiyar hannuna, nifa bazan iya tuna last da nayi shara ba, kada ma nace ban taba ba aga kamar karya nake, nayi shiru Ina ayyana yadda zata kasance. Mino tuni ta wuce ta Kama aikin wanke wanke, ita Kuma Siyama tana hura wuta, a raina nace Allah kar kasa watarana ace Zan huta wannan itacen, inaga makancewa kawai zanyi. Ina nan tsaye rike da tsintsiyar Mino tace min+
” Wai me kike jira ne”
Nayi raurau da idanuna nace
” Ban iya ba”
Tace
” Tab! Gwara ki koya Dan daga yau shi ne aikin ki, kada ma ki Bari Ummaan mu ta leko taga Baki Gama ba”
Jin haka se na duka na fara Amma yadda kukasan bayana zai balle, numfashi na har cicciko was yake, idanuna Suka kada sukai jawur, a Haka nayi tayi, dukda kawai Yi nake bawai Dan na iya ba, saa ta daya Babu datti tunda su mutane ne masu tsafta, ban taba zuwa Naga gidan su day datti ba, kullum a share yake. Nayi rabi na Kuma Bata wajen minti talatin inayi Ina dagowa Ina hutawa, naji dum! A bayana, nayi saurin sakin tsintsiyar na dago Ina rike bayan da nake lallabawa, Ummaan su ce a tsaye tana min wani mugun kallo
” Haka ake shara a gidan ku, koma baya ki fara daga farko”
Kallon da take min ma Bai Isa ya bani damar rokon ta da nake Shirin Yi ba, haka na dauki tsintsiyar Ina share hawayena na Kara tisowa daga farko, a kalla na Tisa sharar nan tafi say biyu, da kuka na karasa ta wajen karfe goma na safe kenan, Ina cikin sharar Yaya da Baba suka fito, seda ya kalleni na wasu mintuna kafin ya gyada kanshi kawai ya nufi gurin Babar shi, na aje tsintsiyar na gaishe shi ya amsa min fuskar shi a sake, Baba dama girman Kai ne dashi you can mistaken him for Dan gwamna, Yana ji da kanshi irin sosae dinnan fa, ya kalleni ya dubi Yaya dake tsaye yace
” Who’s she?”
Na dago na kalleshi, haka yake ya kuma Saba min hakan, idan Ina gurin Abbu yazo zai gaida shi zaice me sunan tsofi Amma idan Ina gaban ko Hajiya indai bana tareda Abbu zaice Wai wacece wannan, idan aka fada Masa se yace Wai shi baya gane mu. Ko magana ban Masa ba seda Yaya yace na gaishe shi sannan na gaishe shi. Ina Gama sharar nayi wanka, wata Yunwa nake ji Dan hakan Ina saka Kaya nazo nace Ummaan su Yunwa nake ji, wani Koko ta Miko min a bude duk kuda sun Gama binshi se fanke a flask, naci fanken Babu laifi Amma kokon ban Sha ba, ganin hakan yasa Yaya fita, can Babu dadewa ya kwalla min Kira, Ina zuwa zaure ya bani tea me kauri yace na shanye cikin farar Leda, na karba nasha sannan na Masa smiling na godiya na koma ciki. Wajen azahar tace naje na kunna wutar girki ni da Siyama, ta nuna min yadda akeyi, gabana ya fadi ga ciwon jikin shara, ga radadin fuskar net ga wata azaba da zaayiwa idanuna. Haka mukaje muka hura wutar girki, idanuna sukai jawur, numfashi na ya cunkushe muna Gama daurawa aka bani dakan yaji, ranar haka na wuni kana kallo na kasan a gigice nake, kafin yamma wata sabuwar mura ta balle min, saboda hayaki, shara da Kuma abin borkono, ga dama nayi Rama a mutuwar Abbu yanzun ma se na fara akan ta da. Duk wannan abin da ake Banga Kawu Sa’idu ba, seda nayi sati daya, har na fara hakura da saka ran wani zaizo yaga halin da nake ciki ya tausaya min ya tafi dani, idan nayi wani tunanin se Naga waye ma zaizo, Mummy na NY, Uncle Babawo na UK, Kawu Tijjani na Kano, Nanny na maiduguri. Dama su dinne, se na hakura na fawallawa Allah na saka a raina am stuck a cikin gidannan kila sede a fitar da gawata. Wannan kwanakin bakwan na tashi tsakar dare nayi kukan da ban San sau nawa ha, nayi addua Allah yasa Nima na mutu da bakar wahalar da nake Sha, Amma kullum jiran mutuwar nake Taki zuwa. Ummaan su ta takura min kowanne aiki zaayi se Dani idan aka gwada min sw tace su tafi su barmin, abincin ba irin Wanda na Saba ci bane, kullum Mai da yaji har ciki na ya fara ciwo. Tunda nazo sau daya akai shinkafa da Miya, shima seda kowa ya samu sannan ta difana min, na rasa me na tare Mata, me nayi Mata na kasa sani. Amma ko kallon da take min na tsana ne. Da yammacin kwana na takwas Ina zaune takure a tabarma, Mino na karatu ita Kuma Siyama na tilawar karatun islamiyya. Tunda ta fara Qadsami suratul mujadala take bata, na matso inda take nace
” Na iya, na Kara karanta Miki”
Ta harareni
” Nace Miki ban iya bane ko me, ke din me Kika iya?”
Na koma gefe naja bakina nayi shiru, Bata san nayi izu talatin ba a karatun da kullum Abbu ke fadan bana maida hankali. Sallamar Kawu Sa’idu tasa na kalla kofa, ya shigo se Naga dukkan su Basu tafi sun rungume shi kamar yadda na Saba ba, kowa yace Masa sannu da zuwa, se ni ce karshe nace Masa
” Kawu Ina wuni? Sannu da zuwa”
” Uwata, sannu ya bakunta?”
Na cije lebe bance Masa komai ba, ya wuce dakin shi, Abbu ya fado min idan yayi tafiya ya Dade haka idan ya dawo na dinga bin shi kenan se ya rokeni na jira shi a parlor zaiyi wanka tukun nake hakura. Muna Gama cin abinci, Yaya ya shigo ya zauna Yana ta min Hira, na saki jikina Ina bashi labarin random abubuwa, mostly magana daya biyu zance
” Allah sarki Abbu da Yana nan, da tuni kaza ya faru, Abbu yace kaza”
Haka hirar tamu ta kaaance se yace min yaji ance mun koam makaranta, nan na tuna ai tun last week an riga an koam, yace gobe na fadawa Kawu Sa’idu. Nayi tunanin tunda ya dawo zaa rage min aiki, se Naga akasin haka, musamman ranar kowa ya tafi makaranta se ni daya na rage Dan hakan ni nayi komai a gidan, har na daina jin zafin dundun saboda yadda ake sauke min shi a bayana akai akai. Na fito daga wanka na dakko skirt Zan saka kawai na rike shi na fara kuka, I remembered lokacin da mukaje wani top boutique a Abuja muka siya da Abbu, se na fasa sawa na dakko wasu kayan na saka nasa hijab kamar yadda nakeyi kullum tunda nazo, kayana ma sun taru bansan yadda zanyi dasu ba, Dan ni ban iya wanki ba. Jin muryar Kawu Sa’idu yasa nayi saurin fitowa, Yana tsaye suna magana da Ummaan su, na gaishe shi na Kara gaishe ta, ignoring harar da take banka min.
” Kawu dama an koma makaranta tun last week”
Ya kalleni da kyau yace
” Daga yau duk abinda Zaki fada min ki fara fadawa Zinatu ita zata fada min”
Na gyada kaina, ya cigaba da fadin
” Makaranta Kuma Zan dawo dake nan Ringim tunda can Babu inda Zaki zauna”
Tamkar saukar aradu haka naji zancen makaranta, nayi sauri nace
” Kawu se na koma boarding…”
” Dallah wuce ki tafi marar kunya, Yana magana kema ki nayi”
Na juya jikina a mace na koma daki, na saki kuka gefen katifa, Ringim Zan dawo da makaranta. Na bude kayana na Ciro tab dita na kunna ta dama a boye nake amfani da ita na Kira Rooks, Babu jimawa yayi connecting, tana dauka ta fara complain ramar da nayi, ban Mata magana ba se kuka, tayi sauri ta koma dakinta tayi locking kofar ta ta fara tambayata abinda ya faru, na fada Mata tace yanzun zata fadawa Mummy, nayi saurin dakatar da ita nace
” Rooks please no! It’s out little secret. Kinga abinda kike tunani zaman gidannan ya wuce haka, tun yanzun idan na fara Kai Kara zaa samu matsala, Babu komai ko Ina makaranta ce zanyi karatu, kawai na fada Miki ne saboda naji dadi. Promise me Babu Wanda zai sani?”
Haka mukai wannan alkawarin Ina jin motsi na kashe na share hawayena na boye tab din. Na leko naji tana cemin zata je makwabta na hura wuta, cikin kudin na cira nayi sauri naje na siyo kifi, shi ne karon farko Dana fita, wani irin nishadi naji da yancin wucin gadi, kamar tantabara haka naji ni Dana fita, it’s been a while! shima ba sanin gurin nayi ba, Mino naji tana zancen kifin na rike a raina, Kuma ban Sha wahala ba. Da na dawo kamar mayya  ko mage haka na dinga ci sannan na wullar da takardar na wanke hannuna nayi brush, Ina hada itace ta dawo ta dinga fada banyi abinda tace ba, nidai nawa shiru ne Amma shima Bata Mata Rai yake!

About AIS

Check Also

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 16 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 16 BY SHATU To meye matsalar ki da abinda ta Haifa, …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *