UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 17 BY SHATU

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Taken mu a kullum shi ne ” Jinin dabo ringimgim da ka garin karamci” mun amsa wannan taken Dan mu mutane ne masu karamci da dattako, masu riko da alada, garin me ruwa, me kifi Wanda suka San kansu a wajen noma. Bari na barku hakan kada kuce na Koda garin mu da yawa, believe me idan kuka je ringim zaku San ba karya nake ba.+

Sunana Amina Abubakar Salihu, Amma anyi min lakani da AFIYYA kasancewar na ci sunan kakata data haifi babana ne. Kakana Alhaji Salihu shi ne wazirin sarkin ringim kunga kenan na hada jini da sarauta. Na kanyi tunanin Anya infertility wato rashin haihuwa baya running cikin zuriar mu? Ko Dan ba hakan ya kamata nace ba , zance tabbas infertility na yawo cikin familyn mu. Dukda haihuwar ana yinta sede batada yawa, da anyi daya shikenan, se ta tsaya. Hajiya Amina ita ce kakata, asalinta mutuniyar Ganjin gebi ce. Ita kadai ce matar daya aura Bai Kara Kuma wani auren ba. Yaranta su biyar ne. Mahaifina Abubakar shi ne babba se Wanda ke bi Masa kawu Sa’idu, se Yar tsakiyar su Mummy Maryam, me bi Mata se kawu Ahmad ana ce Masa Tijjani  autansu Uncle Salihu amma Babawo ake Kiran shi, my very own savior.

Kamar yadda muka sani lokacin da westerners Suka kawo karatun boko an fara dauka ne daga gidajen masarautu Dan a bada misali ga sauran alumma su biyo baya. To mu dinma hakan ce ta kasance lokacin da yaran sarki zasu tafi se aka hada da Babana da Kuma Kawu Sa’idu aka kaisu. Hajiya Bata so saboda tana ganin kamar wani Abu ne ake son koyawa Yara Dan a dauke hankalin su akan turbar musulinci. Da kyar aka samu akai convincing dinta ta amince Suka tafi makaranta, sede kawu Sa’idu fur yaki idan an kaishi se ya gudo ya tafi gidan Gwoggon su dake kyarama, duk kuwa da tsakanin Ringim da kyarama akwai tazara Amma hakan zai gudu. Idan mahaifina ya dawo yayiwa Hajiya complain tayi fada Amma a banza tunda ita Baso take ba Amma tana ganin Dole tayiwa waziri biyayya, Kuma ba zata so yayanta Suki Masa biyayya ba. A haka aka Gama karatun Babu abinda kawu ya tsint, da waziri ya fahimci hakan se kawai ya kaishi kasuwa yace gwara ya nemi abinyi kada ya ja Masa magana a gari. Nanma Babu wani abinda yake illa yaje yayi shawagi ya tafi yawon shi, sede a wañnan shekarar baya ga waccan budurwar baya ga gidan wane, Kuma kowa saboda darajar waziri yake kyale shi.

Daddy a kings college dake Lagos anan yayi secondary School din shi, Yana gamawa aka bashi offer Amma se yaki karba akan shi fa se yaje ya Karo karatu. Hajiya Babu yadda batayi dashi ba Akan yayi aure Amma yaki. Haka ta kaishi Kara wajen fulanin sarki se ta nuna Mata itama fama take da nata dan maslaha kawai su kyalesu suyi masu addua.

Mahaifiyata sunanta Halima, ban taba ganin ta ba, asalin ta Yar shehun borno ce, akai alliance Akan zaa hada auren yayarta da Baba Mustapha Dan sarki Wanda yake saan Abbuna ne Kuma tare suke karatun acan UK. Yayar ta ita Kuma Mariya, da zasu zo aka saka mamana ta Mata rakiya, bayan an gama komai se sarki yace ai tunda Halima tazo se a hadata da da Abbuna tunda Suma Yan uwa ne. Haka akai aka daura aure mazan na can wata duniya, kowanne se gani yayi an aika Masa da matar shi. Abbu yace min Bai taba ganin mace kyakyawa kamar mahaifiya ta ba, me hakuri da juriya irinta ba. Ya fada min zamansu Zama ne sukai Akan fahimtar juna da soyayya.

Shekara na zagayowa Ummin Istanbul kamar yadda muke ce Mata ta haihu Amma mamana shiru ko Bari babu, wannan haihuwar daidai Gama karatun su Suka dawo Nigeria, precisely Ringim, sosae aka tarbesu aka nuna jin dadi musamman haihuwar Ummiey ta dada musu. Anan suka cigaba da rayuwa, Abbuna ya samu aiki a Lagos ga damuwar da mamana ta saka a ranta na rashin haihuwa se aikin yazo Masa da Dadi yasan zata Dan ji Dadi idan tayi nisa dukda bawai takura Mata ake ba, Hajiya me tsananin Kara ce Kuma ta fada min Bata taba suruka ta gari ta kirki me Kara da kawaici who owns a golden heart irin mahaifiyata ba. Baba Mustapha da Ummiey se Suka bar kasar gaba daya, a hakan rayuwa ta cigaba da tafiya.

Bangaren Kawu Sa’idu yayi aure matar shi Zinatu, a yawon shi ya samo ta Yar Kano ce Muna kiranta Ummaah, a yanzun bazan ce muku komai akanta ba Amma nan gaba kadan zaku gane irin rawar data taka wajen lalata rayuwata, idan Babu Ummaah cikin labarin AFIYYA to labarin bashi da amfani. Kawu ba karatu yayi ba , shi ba Sanaa yake ba sede standing order da Abbuna yayi Masa duk wata akwai amounts din da yake bashi, dukkan yayan shi Abbuna yake daukar nauyin karatun su. Shi ne kadai Wanda ya haihu da yawa, Ina tunanin kamar ma ya riga Abbuna yin aure. Danshi na farko sunan sarkin Ringim gareshi shi ne aka Kiran shi Baba, na biyu shi ne Yaya, sunan waziri gare shi, bazan taba manta Yaya a rayuwa ta ba, mutum me alkhairi Wanda yaci sunan me sunan shi. Ta uku sunan Hajiya ne da ita ana kiranta Mino, se Siyama se Hafsa. Banda saa a gidan na girmi Hafsa Siyama ta girmeni. Haka yaran shi suke. Mummy Maryam tana auren daya daga cikin yayan sarkin Ringim tana zaune a NY yarinyar ta daya Rukayya muna kiranta Rooks. Kawu Tijjani yana Kano da matar shi Anty Salma, yarsu daya Basma se Uncle Babawo shi ne a UK precisely a Lancashire yake. Shi Bai ma tana haihuwa ba.

Abbuna seda sukai shekara ashirin Basu haihu ba, Abbuna yayi kudi,ga ilimi gashi successful business man Amma Babu haihuwa har ya gaji da zuwa asibiti suka fawwalawa Allah. Se at the last minute da suka fitar da Rai sannan kamar Wasa mama ta fara laulayi suna zuwa asibiti akai confirming ciki gareta. Bayan kwana biyu Suka tafi Germany rainon ciki. Kowa yaji labarin cikin se yayi farin ciki Banda Wanda suke adduar Allah yasa kada ta haihu idan Abbuna ya mutu gado nasu ne. Saura sati daya a haifeni waziri ya fara rashin lafiya kamar zai mutu. Dole Abbu ya tafi Nigeria Dan sadawa dashi, Ashe rashin lafiyar ba ta tashi bace kwanan shi daya da zuwa ya rasu. Wanann sakon da ya samu Mama se ya sata ta fara labor, dama tasan cs zaa Mata tunda ta Dade Bata haihu ba. Take aka shiga da ita ot baa fito ba seda sabuwar halitta wato ni! Seda mukai sati daya sannan Abbuna ya dawo jikinta yayi sauki muka dawo Nigeria, a wannan dawowar  gaba daya Babu wani dadi, Mama taso waziri ya ganni ya rike no kamar yadda yake Mata nasiha kullum cewar watarana zata hahihu zata dauki danta a hannunta. Se gashi lokaci yayi Amma baya da Rai. Abbu ya saka min Amina, Mummy Maryam ta saka min AFIYYA lokacin tanada tsohon cikin Rooks. Mama Bayan zaman makokin ya lafa ta tafi borno seda ta zubar da wanka sannan ta dawo. Rasuwar waziri ta girgiza mutane sosae nan akazo tunanin Wanda zaa bawa sarauta kowa ya nuna Abbuna yake so Amma se wasu suka nuna ai baya Zama balle a bashi, why not Kawu Sa’idu. Shi dinma so yake a bashi Kuma ace Yana cikin council members na emirate ai yayi gaba kawai. Hakan Bai kasance ba aka bawa Abby shi Kuma se ya wakilta kanin waziri kamar yadda Hajiya ta fada Masa. Wannan abin ya Kara Bata ran Ummaah da kawu Sa’idu.

Satin Mama biyu da dawowa muka koma Lagos muka fara sabuwar rayuwa, idan ka kallesu ka kalleni zaka Yi tunanin ni din jikar su ce ba Yar su ba, Dan sunyi girma ace ni din Yar su ce. Na samu gata na samu tarbiya na Kuma samu jin Dadi sede Bai daure ba, Allah ya yanke min hakan ya jefo min wata hanyar da zanbi Dan ya gwada imanina. Shekarata daya Mama tayi rashin lafiya kwananta biyu a asibiti Allah ya Mata rasuwa.

Junaidu sunan shi, mahaifin shi Malam Ibrahim Wanda yake haifaffe Kuma zaunannen Kazaure ta jigawa. Mahaifin shi babban malami me Wanda yasan alqur’ani da litattafai. Ko Ina zakaji anyi kwatance da tsoron Allah irin nashi. Sede bawai a malimtar ya tsaya ba shi din manomi ne haka Kuma Dan kasuwa ne Wanda yayi karatu sosae a ilimin zamani, shiyasa malumtar ma take tafiya yadda ya kamata. Allah Yana da hanyoyi da dama na jarabtar bayin shi, duk imaninka baka wuce kaddara,
Matan auren shi hudu, Babbar wadda ita ce uwargida Yar Roni ce Hajja Huwaila, ita ta Haifa Junaidu Wanda a yayanta shi ne na uku. Gaba daya yaranta biyar. Me bi Mata ita ce Hasiya wadda Yar nan cikin garin kazauren ce, se ta uku Yar Daura sunanta Fatima, amaryar shi Kuma Yar wani abokin shi ce ya bashi ya aura me suna Sadiya. Gaba daya yaranshi sun tasar ma goma Sha biyar. Yadda aka San gidan malamai gida ne Wanda zaman lafiya da kwanciyar hankali ya yawaita,nan dinma hakane sede idan Mata suka taru Dole akwai abubuwa na kishi da Dan rashin jituwa. A alaadar gidan tun kafin ka Gama primary zakai izu talatin, kana zuwa js3 kayi sauka seka tafi boarding ka cigaba do littatafia. Karatu ana idar da asuba zaa fara, Bayan sallar Isha a daura, Dole kowa se yaje ko ya hadu da fushin malam.+
Wasu iyayen sun iya banbance yadda yaran su suke tun daga yanayin kukan su suna jarirai da Kuma yadda suke muamula da Yara sa’o’insu idan sun fara girma. Junaidu yaro ne me kuka Yana yaro, kukanshi ya baci, Kuma duk abinda Hajja take ya fara kukan nan se ta katse shi, Yana da zuciya Dan ko an daura shi a po yace ya Gama baa zo da wuri ba to idan akazo tsarki zai ce bazai tashi ba. Cikin dare idan ya tashi Shan ruwa kafin a dakko a bashi yayi fushi bazai karba ba. Wannan halayen nashi yasa ake cewa Hajja tafi son shi saboda gudun zuciyar shi yasa dukkan attention dinta take Kansa, shima Baban wato malam daya fahimci hakan se kullum kafin ya fita se yayi rubutu ya kawo a bashi. A hakan ya fara girma har Yana fitowa waje yayi Wasa da Yara saanin shi dukda ba sosae yake hakan ba Amma duk ranar da ya fita wasan to se ya daki yayan mutane, a gidan su ma idan kannenshi da yayun shi suna Wasa Yana zuwa kowa zai kwashe kayan wasan shi idan ba hakan ba ta kansu zai bi ko Kuma ya dinga wurgi dasu. Kowa tsoron shi yake he’s a villain and also a rogue!
Primary aka Kai su Amma baya zuwa se ranar da ya ga dama, shi ne shugaban bad gang na cikin makarantar kullum rana idan har suna cikin makarantar to tabbas zasu daki wani ko su sumar da wani. Kullum ana filing complain office din headmaster, har ya gaji ya fadawa Malam halin da ake ciki. Malam ya dawo gida ya aika a Kira Masa Junaidu, ya shigo a nutse saboda haka yake, idan ka kalleshi zakaga zallar nutsuwa a tattare dashi Amma idan ka kalleshi ko ka zauna dashi zaka San Allah ya Masa hallittar nutsuwa shi Kuma ya bijire. Ya tsaya a tsaye Yana cewa Malam gashi yazo,yayan shi Suleiman ya kalle shi ya kalla Malam sannan yace Masa ya nemi guri ya zauna, ko kallon shi baiyi ba balle yasa ran zai zauna hakan ya batawa Suleiman Rai, Yana tashi ya dauke shi da Mari, Amma ko gezau Junaidu baiyi ba se huci kawai da yake Wanda ke nuna ranshi yayi mugun baci, seda malam ya Masa magana sannan ya tsugunna shima yadda tsugunna din kawai se yasa kunyi dariyar takaici.
” An kawo min Kara cewar baka zuwa makaranta, idan Kuma kaje kana dukan yayan mutane…”
” Inji wanne Dan shegiyar?”
Ya fada Yana Kara Bata Rai tareda mikewa tsaye, Suleiman ya Mike yakai Masa naushi a take bakin shi ya fara jini, yasa hannun shi ya lakuto Yana ganin jinin yayi Kan Suleiman ya cakumi wuyan shi ya fara naushin shi, Malam ya Mike da kyar ya raba su, yana sakin Suleiman ya zube a kasa saboda yadda ya karbi naushi a jikin shi, tabbas jikin shi ya fada Masa. Malam ya dafe Kan shi ya kwallawa kanin shi sarki Kira, Babu shiri sukai asibiti da Suleiman. Baa Kara tada maganar ba Amma Malam ya dage da kaiwa Allah kukan shi.
Tun daga wanann abun gaba me karfi ta shiga tsakanin Suleiman da Junaidu, Kar kuyi tunanin me sauki basa magana Koda zasu bangaji juna, wannan ya dagawa Hajja Huwaila hankali ya bar Mata abun Fadi wajen kishiyoyi. Lokacin da ya kusa Gama primary se ya fara Shan taba, bakin shi ya fara nunawa, ya daina zuwa karatun da suke na Bayan sallar asuba, ya daina zuwa gaida kowa a gidan, abincin gidan Banda na dare to baya ci. Can wajen kanti akwai wani garejin gyaran mota nan yake zuwa da yamma anan yake samun kudi anan Kuma ya fara Shan taba, da Abu yayi gaba we aka fara bashi Wiwi Yana zuka, baka taba shi da robb da yake shafawa a leben shi da Kuma namijin goro Dan kada kaji warinta. A hankali Malam ya fara gajiyawa da halayen Junaidu se ya fara fita daga alamuran shi. Tun ranar da ya daki Suleiman a ranar Malam ya fara tsoron Junaidu Amma dukda haka yana Masa fada Hajja Huwaila na ma na kokari sosae Akan shi shiyasa ya daina zuwa gidan. Akwai lokuta da iyaye suke samun matsala, itace tun Yana karami ake tankwara shi idan ya bushe zai karye, lokacin da Junaidu ke fatali da kayan wasan Yan uwan shi ya kamata a tsawatar Masa Amma idan yazo ya nayi se Hasiya ta dinga tafi tana cewa ga gwarzo yazo, yanzun zai baza yaran da basa son yin karatu se Wasa kawia Suka sani, ko sun Kai kararshi Huwaila ce kawai zata lallashe su Amma sauran matan se suce ai maganin fitsararru yakeyi. Wannan shi ne abinda ya bashi lasisin yin duk abinda yakeyi, a unguwa ko ya daki Dan wani saboda Malam se kauda Kai, a makaranta baya zuwa Amma form teacher batai reporting ba saboda tana ganin irinsu Junaidu rashin zuwansu yafi zuwan su alkhairi. Kowa ya taka muhimmiyar rawa wajen lalacewar shi, tarbiyyar Bata iyaye kawai bace, ni na yadda cewar tarbiyyar duniya ita ce tarbiyyar, duniya makaranta ce kowa se ta bashi ilimin da yake bukata.Mutuwar Mama ta girgiza mutane da dama saboda rashin lafiyar da tayi ma ba kowa bane ya San batada lafiya, it was very brief Amma da yake karar kwana ce se gashi ta rasu ta barmu ni da Abbuna. He was completely shattered beyond imagination, har ya koma ga Allah Babu ranar da baya cewa ” da Halima nada Rai, Allah sarki Halima” maganar shi kenan, kullum Rana se ya bani labarin ta sede idan baya gari ko bana nan. A luth ta kwanta aka Gama duk wani cike cike da ya kamata sannan yayi booking flight within few hours suka dakko gawar zuwa Kano, kafin mu karaso an turo Mana motoci daga Ringim Emirate council Wanda zasu tafi da gawar zuwa inda dubban mutane ke jira a sallace ta. Abbuna yana rike Dani a kafadar shi tunda muka taho nayi bacci bayan Nanny ta bani oat nasha. Muna zuwa danginta da suke nigeria duka sun biyo flight zuwa Kano sun karasa Ringim, ita mamanta Bata gidan Kuma ita daya ta Haifa, asalin ta Yar Ethiopia ce, so Bayan sun rabu da shehun borno ta koma kasarta, acan Bata wani Jima ba ta rasu, so nidin jini da yawa ke bin veins dina. Ina baccin Nanny ta shiga Dani ta goya ni a wañnan yammacin aka kaita makabarta aka binne ta. Abbu was devastated, kallon shi kadai zai baka tausayi kowa yabin halayen kirkinta yake. Mutane da yawa kallon Abbu Dani ke saka su kuka na tausayin mu. Tunda na farka a baccin aka bani abinci naci se na kankame Nanny dama ni me kowa ce saboda ban Saba ganin mutane a gidan mu ba.  Idan Naga mutane Kuma to se na nanike mamata ko Abbuna, idan Babu daya se na nanike Nanny. Kwana uku mutane suka baje yawancin zaman makokin Ina jikin Abbuna a kofar gida Dan naki Zama ciki, kowa se yaji tausayi na. A Rana ta bakwai Bayan an gama adduaa aka raba gado, a cikin dangin Mama Babu Wanda yace zai tafi Dani shima Kuma Abbu Bai yiwa kowa tayi ba, sun tafi suna ta jin rashin dadin rasuwar Yar uwarsu. Duk yadda rayuwa zatayi Dole mutum ya cigaba da rayuwa, duk wani bakin ciki da zaka dandana akwai ranar da zai wuce kaji kamar baayi ba. Bayan gidan ya watse Hajiya tayiwa Abbu nasiha sosae Amma se yace Mata shifa tayi hakuri aure daya ne Kuma yayi Amma baya tunanin zai Kara wani. Mummy tace to ita zata karbe ni ta hada Rooks Amma yace ya gode zai rike ni Yana ganina yaji Dadi. Daga nan muka koma Abuja saboda transfer da akai masa zuwa can. Gidan daga ni se shi se Nanny se Kuma maids din dake Mana aiki, da Nanny ke Mana komai Amma tunda ita ce sabuwar uwata Abbuna ya maida ita kawai kula Dani su Kuma sauran suyi aikin gida. Akai akai yake kaini Ringim Dan na Saba dasu, Yan uwan Mama Babu Wanda ya taba zuwa ya ganni Dan haka Abbu yace shima bazai kaini ba, har na Isa yaye aka daina feeding Dina da Madara se aka koma solid food. Ban Jima da yaye ba na cika shekara biyu, Abbu ya kaini creche, so ni dai as far as am concern tunda nayi wayo a makaranta nake, karatu nake, Dan hakan karatu a cikin Raina yake, shekarata ta farko bani ma da wayo bazan iya tuna komai ba, seda nayi shekara biyar sannan na fara sanin kaina, mutum daya na gane matsayin uwata da ubana Abbu, shi kadai na sani kowa as preliminary nake ganin shi,duk Wanda na Kira da Baba to Kara ce kawai,Dan Babu Wanda ya yimin abinda Abbu yayi min.
Saboda yadda na Shiga makaranta da wuri yasa kankanin lokaci na gama. Munje Ringim Ina kwance akan cinyar Hajiya Abbuna ya shigo Dan tun isowar mu fada ya fara zuwa ya gaishe da sarki sannan ya fito mutane Kuma suka tareshi kowa na fada Masa financial complain dinsu Dan ya taimaka musu. Da kyar na yadda na shigo gida shima Yaya na gidan Kawu Sa’idu ne ya lallaba ni muka shigo cikin gidan dashi, Ina ganin Hajiya se na saki hannun shi na nufi inda take zaune ta mike kafafun ta na kwanta Ina ce Mata
” I was waiting for you, you didn’t come to my house and I missed you!”
Ta dungure min kaina tace
” Ni bana jin wannan yaran nasarar da Baban ki yake koya Miki, yimin hausa”
Yaya dake gefe yayi ta Mana dariya sannan ya fassara Mata abinda nace, ta rungume ni Yana cemin ita ta tsufa ba zata iya zuwa har can capital wajena ba. Tana ta tambayata abinda zanci ne Abbuna ya shigo, nayi saurin tashi na koma kan cinyar shi, murmushi yayi ya zaunar Dani Yana gyara min hular kaina suka gaisa da Hajiya, Yaya ya Mike Dan yasan ya kamata ya Basu guri, hannu ya Mika min yace
” So muje na kaiki gidan mu”
Na kalleshi sannan na kalla Abbu, ya gyada min Kai tareda mikar Dani tsaye, har na tafi na dawo na rungume shi nace
” I’ll mish u”
Yayi dariya yace
” My Princess go”
Na wuce hannuna cikin na Yaya muka nufi gidan su dake can gefe duka a cikin Ausar ne. Muna zuwa duka suna zaune ita Ummaah na gaban murhu tana rabon shinkafa da Mai da yaji, su Kuma suna zaune an shimfida katuwar tabarma na bogaji suna jiran a Gama kowa ya dauki nashi. Muna sallama suna ganina Mino ta mike tana fadin
” Afiyya oyoyo! Ummaah Kinga Afiyya tazo”
Ta juyo ta kalleni ni Kuma naje kamar yadda Abbu yace min idan Naga babba na gaishe shi na tsugunna nace Mata Ina kwana, ta tabe baki ta fara fadin
” Kanwar uwarki ce Afiyya da Zaki dinga wannan ihun? Shashasha kawai”
Jiki a sabule ta zauna, shikam Yaya Zama yayi yace
” Ummaah Baki amsa Mata gaisuwar ba”
” To uban shishiggi Kai Kuma, Wai ita wannan Afiyya din Yar gwal ce, bazan amsa ba”
Sanin halinta yasa ya guntse bakin shi ya Mike yace min na zauna yanzun zai dawo, na Mike na Kama hannun shi Dan kada ya tafi, Mino yasa ta daukeni haka na Dan zauna a dadare saboda rashin sabo, abinci kowa yaje ya dauki nashi, Nima aka Miko min wani Dan mitsitsi cikin karamin roba, na karba na aje Amma naki ci saboda bana ma jin Yunwa, suna Gama ci Siyama ta janyo nawa ta cinye, Mino na Mata magana Ummaah tace ta barta dama ni na xo na datse musu abincin su. Yaya ya dawo da kifi a Leda ya dauki abincin shi yace nazo naci me kifi, ni Kuma since from childhood bana ketare tayin kifi saboda yadda Abbu ya Saba min cin kifi kullum se mun ci a dinner. Ina ganin Kifin naje na zauna Siyama ma ta taho ya dinga bamu muna ci har ya Gama naje nace ma Ummaah ta wanke min hannu, ruwa kawai ta zuba min na cuda tace naje, nace Mata ai se an saka detergent sanann zai fita, se ta koreni Wai Ina Mata iyayi. Ban wani Kara sakewa ba saboda karnin da hannuna yake na dameshi ya maida ni gurin Abbuna.
” Jarabar ka tasa ka dakko ta,seka maida ita ai”
Ya Mike ya Kama hannuna muka tafi, Ina zuwa na samu Abbu ya fita, se na zauna wajen Hajiya Ina Mata hirar school, se dare ya dawo da Kifin shi. Naci nayi bacci, bayan fita ta Hajiya ta nuna Masa lallai ya kamata ya kaini maiduguri Koda su Basu neme ni ba to shi ya kamata ya Kai ni na gansu, idan sun cigaba da nemana kansu idan Basu Kara ba shi dai ya sauke wannan nauyin. Washegari muka tafi Kano muka bi flight zuwa maiduguri, ya kaini na gaida kakkani na duk sunata borin kunyar Wai Basu San min koma Abuja ba, se zuzzuta yadda na girma nake Kama da Mama suke. Akazo zau tafi na dinga kuka bazan zauna ba hakan shima ya hakura muka tafi tare. Kawata Dana fara Yi a school namesake Dita ce, sunan ta Amina Abubakar Rogo, gari kadai ya banbanta sunan mu. An tashi school drivern mu duka Bai zo daukar mu ba, muna zaune inda muke Zama mu jira na Bata book Dina Wanda tsayin shi bazai Shiga cikin backpack Dita ba haka itama, inda water dispenser ke aje naje na tsiyayo ruwa nasha sannan nayi discarding cup din sannan na dawo na karba book Dina, kafin na zauna Nanny ta shigo cikin sauri, nayi sauri na nufe ta Ina rungume ta nace
” Nanny!”
Ta shafa kaina ta karba book Dina, da food box dina da Kuma backpack Dita nayi waving Amina muka tafi. Tun cikin mota nake Mata complain Yunwa nake ji, tace ai ta Gama abinci, nace Mata Abbuna ya dawo tace ai yace se dare zai dawo. Muna zuwa gida na wuce dakina da gudu na dauki waya nayi dialing wayar office din Daddy, Yana picking nace Masa yaushe zai dawo yace nayi hakuri naci abinci zai dawo da daddare, ba yadda naso haka na yadda mukai sallama. Akazo wanka nace ni fa da kaina zanyi da kyar na yadda Nanny tayi min.
Ina zaune Bayan maghrib a dakina na tasa drawing book a gaba dasu pencil colors da water color Dole se na zana picture Mama da Abbuna dake rungume Dani on my first birthday,
” Where’s my princess?”
Naji muryar Abbu Yana tahowa dakina, na yadda drawing book din na taho a guje gurin shi na rungume shi, ya daga ni sama ya wulla ni ya cabe nayi dariya na rungume shi. Tare mukaci abinci sannan na raka shi yayi Dan walk cikin compound dinmu sannan Muna dawowa Nanny ta min wanka yazo ya zauna gefena Yana tambayata yadda school ta kasance a hakan nayi bacci sannan ya tafi. Haka yake min kullum indai Yana gida to zai zauna side bed Dina har se nayi bacci. My father my world!

About AIS

Check Also

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 16 BY SHATU

UWAR GIDAN BAHAUSHE CHAPTER 16 BY SHATU To meye matsalar ki da abinda ta Haifa, …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *