UMM ADIYYAH CHAPTER 66 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 66 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


Mun tsaya 

Ban fahimci a matsayin wa ka ke min magana

ba.” TJ ya fada lokacin da ya

Kankance idanunsa.

A matsayin Yayanta na ke fada maka, kar ma

ka bari na fara akan matsayina na

daya bangaren. Amma saboda adalci, zan fada

maka ka shirya samun wasu tsaiko,

ba ka tsammanin na bar maka ita haka kawai

ko?”

“Ina ga da ace akwai wani abu makamancin

hakan da ba ma wannan maganar a

yanzu, saboda ta kasance ta ka a wata gaba. Ka

yi sake da damar ka. Ina ga ko ka

tsaya ka ga iya yina ko kuma ka sameta, ta

fada maka abinda ba ka sani ba.”

Maganar ta kona Zaid ba na wasa ba, amma
bai yi mamakin abin da ya ce ba,
saboda a hakikanin gaskiya shi ne ya yi sake
da damar sa kamar yadda TJ Ya fada
masa, amma shin ya shirya nade hannu ya sa
masu idanu? A’a ba zai tsaya ba, har
sai ya ga abinda ya turewa buzu nadi, zai
kwato Twinkle dinsa!
Wasu lokutan abu kalilan muke bukata da za
su bude mana idanu su ingiza mu
zuwa hanyar da ta dace, na yarda da cewa
hakan ka ke yi a rayuwar Umm Adiyya.”
Murmushi TJ. Ya yi ba tare da ya tanka shi ba.
Turirin da ke tashi a cikin motar, tamkar ta ki-
far da motar, amma ba wanda ya kara
furta komai har suka dawo gidan Www.bankinhausanovels.com.ng
An bar Adiyya a gida tana ta kada Kafa cikin
tunanin me ya tsayar da su suka dade
har haka? Tun tana kallon agogo har ta bar
kallo, lokacin da ta ga sun cikata
mintuna arba’ in.


Suna isowa nan cikin harabar suka samu ku-
jeru suka zauna, sun samu Yaya Saadikma da wani abokinsa a wurin, suka kafa hira,
kowa abinda ke ciki yana ciki. Tun
Umm Adiyya tana leka su tana tsaki, har ta
daina.
Ta fashe da kuka, haka kawai don fin karfi an
zo an hanata zantawa da bakonta.
***********
BABI NA ARBA ‘IN DA DAYA
TJ Ya yi dariyar maganar Saadik ya ce, “Ni
zan wuce.”
Zaid na goye da hannayensa a saman kirjinsa
ya sa masa idanu, “Ba za ka jira mu
yi sallah ba?”
A’a ana jirana, za mu yi a can.”
“To ba damuwa,”
Saadik ya ce, *”Yallabai zuwan nan dai ba
namu bane, ka shiga ku yi sallama, mu dai
suruka nan zamani ne, kar ka zo ka ce ka ga
yayyin Karanta.”
TJ. Ya yi dariya ya ce, *In don sallama ne, ba
damuwa bace, idan kun ce mu yi a
waya ma, sai mu yi tunda yanzu kam nema
muke yi.
“Allah Ya bada sa’a to.” Na lokaci kankani
idanunsa suka sauka a kan Zaid da ya
daga robar ruwa yana kurba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Zaid dai mukamukansa kamar za su karye don
tauna, ji yake yi kamar ya bubburma
fuskar TJ. Ko zai cire wannan shegen fara’ar
fuskarta sa. Koda yake idan ya runtse
idanu, ya ga yadda Umm Adiyya take dariya
da shi, abinda yake ji ya yi ya fi karfin
burma fuska.
Yake ya yi masa ya ba shi hannu suka yi sal-
lama, sai bayan ya fito ya tafi ne. Zaid
ya yanke shawarar abin yi.
Cikin gidan ya shiga.
“Yaya Zaid, don Allah me ya sa ka ke haka
ne? Karfi da yaji fa ka yi kane-kane ka
hanani ganin Unle TJ.”
Kallonta yake yi hade da murmushinsa na gefe
sannan ya ce, “Meye? Kin ji zafin
hakan ne?””
“Ka koma gida, ba zan iya magana da kai
yanzu ba.” Ta fada hade da juya fuskarta,
hawaye ne ta ji sun ciko mata idanu damdam!
Duk da ba ta san ma dalilinsu ba.
“Me ya sa? Saboda ni ba ni da muhimmanci a
wurinki? Ko kuwa ki na so ki ce kin
manta komai ne? Me ki ke so daga gareni? So
ki ke yi ki san me na ke ji game da
duk wannan abinda yake faruwa? Ke ki na kula
bawan Allah, ki na dora shi a zuwan
cewa shi ki ke so, yana da iyali, ashe ko don
wannan ba za ki tausaya ki rabu da shi
ba?
Ban san me ki ke ji ba game da ni ba, tunda
ban san gaibu ba, amma yau ina son ki
san cewa l’am not alright with you seeing
Someone (bana jin dadin ganinki da wani),
yana min ciwo fiye da zatonki, raina ya yi
kunci lokacin da na rabu da ke, ban yi
cikakken barci ba, shekarar nan shaf da ta
wuce ba tare da tunaninki ba, ko
mafarkinki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nayi matukar kewarki Twinkle, na yi kewar
yadda na ke kiranki, haka na ga idanunki
sun yi kyalli. Nayi kewar murmushinki, da
kukanki, da shagwabarki, da fushinki. I
miss every. single. thing. about you.
Ta kai ga ina muradin na ji muryarki koda
Hypocrite za ki kirani. I miss us. Hakan ya
miki? Ga shi na fada miki abinda yake raina.”
Ya karasa muryarsa kasa-kasa tana
rawa.
Ya Salaam! Sau bila adadin ba na buktar
wani ya fada min, ji na ke yi kamar
abubuwa za su tarwatse cikin kaina, na zaci na
haukace ne da gaske a cikin kaina.
Na yi addu’ar Allah ya yaye min matsalar da
na ke ciki, na yi addu’ar zabin Allah, na
yi komai har gobe ina kan yi, ba zan daina ba,
muddin ina raye.
Adiyyah ba ki san halin da na ke shiga ba,
muddin na rufe idanu na ga kina farin-ciki
da wanina, na kan tunassar da zuciyata na rar-
rasheta akan cewa wata kila
kasancewarmu haka shi ya fi mana. Na yaki
wannan matuka. Na yaki soyayyar da
na ke ji game da ke. A rashin sanina, mutum
baya yakar kaddararsa, saboda da ni
da ke anyi mu ne domin juna.
Ba zai taba zama min daidai ba, koma da waye
zan kasance, saboda duk duniya
Umm Adiyya ke kadai ce Adiyyar Zaid. Don
Allah ki daure mu mance komai, mu faro
daga farko. Ki ba mu dama a karo na biyu.
Please be my wife again, Adiyyah.”
Habar ta na rawa, saboda kukan da take sha a
tsakanin wani makoko da ya makale
mata a wuya ne ta ce. “Yaya Zaid, wani sati za
a kai kayan aurenka. Nan da wata
daya za ka auri wata yarinya, ‘yar gidan mu-
tumci, wacce ta ke sa ran ta samu
soyayyar mijinta, ta samu dukkan kulawar da
ta dace, don ta gudanar da ibadarta
cikin sahihanci, bazaka fada min wannan kala-
man ba. Ba daidai bane.”
Hannu ya sa ya shafo fuskarsa. “Babu auren.
An janye.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Idanun Umm Adiyya ne suka bullukko waje,
“Yaa Salam! Me ya sa ka aikata haka?
Me zai sa ka bari a dalilin abinda ba ka da tab-
bas ka warware rayuwar mutum? Ka
maida hakan wasan ne? Zukata nawa ka ke son
ka tarwatsa, duk don son ranka?”
“Ba ni na warware ba. Duk da ina gaf da yin
hakan, saboda ko anyi, ba abinda
hakan zai haifar, domin ba zan taba sauke
nauyin da suke kaina ba.” Ya fada hade
da taba hancinsa kadan.
Kau da kanta ta yi gefe, don yanzu ba ta san
yaya al’ amuran suke ba kuma. Dago
idanunsa ya yi, ya ga tana kallonsa a tausashe,
tamkar yanzu ne take ganinsa da
kyau.
“Ita ta roki iyayenta a warware, saboda ba na
ba ta kulawar da ta dace tun yanzu, ba
na kirarta a waya, kuma ko ta kira ba na
dauka.”
Umm Adiyya ta yi shiru tana kallon kasa, a
hankali ta dago kanta tana dubansa,
“Wai ne ko haka ne?”
“Wasu wai ne wasu haka ne, ni dai kawai na
san ba ni da dalilin rayuwa, idan ina
tare da ita, ke kuma… ke kanki… Idan ina tare
da ke, ina sanin ababen da na ke son
yi da rayuwata. Kamar na so-ki har gaban
abada.” Ajiyar zuciya ya yi, ya ce,
Twinkle don Allah ki ba ni damar na gwada
miki matsayinki a gareni.”
Girgiza kai ta yi, sannan ta daga kanta sama
tana hadiye hawayen da suke kokarin
zubo mata. “Ina ga ka makara kadan Yaya
Zaid.”
Tsuke ganinsa ya yi yana dubanta. “Me hakan
yake nufi?’
Magabatan Uncle TJ. Sun yiwa Baffa mag-
ana.” Da sauri ya matsa baya, yana
dubanta kamar ta canja halitta. Sannan ya
gyada mata kai.
I am sorry.” Muryarsa ta fito babu karsashi,
babu amo.
Juyawa ya yi jiki ba kwari ya bar wurin. Tana
kallonsa ta taga, ya yi kusan minti
goma bai motsa ba a motar, kafin daga bisani,
ya tada motar ya bar harabar gidan.
A durkushe a nan Maami ta sameta, ita dai
nata idanu, don ba ta san me za ta ce ba
a lamarin yaran. Haka ta karaci kukanta, san-
nan ta shiga.
***** ****** **
Kai tsaye Maami ta samu Abba a daren.
Sha’anin Ummu na daure min kai. Gaba
daya ba ta da alkibla, an taba yin mutum
wanda bai san me yake so ba?”
Abba bai ko bude idanunsa ba bare ya tanka.
Maami ta shiga jero masa ababen da
ta kula da su. “Tunda ita ba yarinya bace, duk
yadda ta zaba ai shi kenan, matsawar
ba wai mun ga zabin nata zai taba addininta da
mutunci mu bane ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Haka ne kam.”
“Don haka ki cire kanki a damuwarta, ita ta san
daidai ai.” Abba ya Karasa, ita dai ko
za ayi yaya da ita, ta san cewa Abba ya yi mag-
anar nan ne kawai.
“To Allah sa hakan ya fi alkhairi.”
Tana shirin kwashe kayan shayin Abban ne,
wayarsa ta yi kara. Ya daga ya amsa,
duk da cewa dare ya dan yi kadan.
Jin ya ce, “Subhaanallahi.” Ya tashi zaune
daga kishingidar da ya yi, ya sa Maami ta
jinkirta har ya kammala.
“Lafiya Abba?”
Shiga ki shirya ki zo mu tafi.”
Ina za mu je?” Ta fada tana bin bayansa da
tiren kaya a hannunta. “Asibiti, yaron
nan ya yi hatsari.”
Inna-Lillahi’ wa-Inna-Ilaihir-Raji’un!
Garin
yaya?”
Abba bai ba ta amsa ba, ya san duk cikin rudu
take. Haka suka shirya suka nufi
hanyar asibitin da aka kai Zaid din. Can suka
tarar da Salisu kasancewar bayan abin
ya faru shi aka fara kira a waya.
Yana ganinsu ya daure ya yi masu fara’a, aka
gaisa a tsaye, lokacin ne ya ce, “Har
yanzu dai ba su gama duba shi ba, amma kai
tsaye ma ICU suka shiga da shi.”
Wata mummunar faduwar gaba ne ya riski
Maami, sai da ta jinginu da bangon
bayanta, take kuma ta shiga salati a zuciyarta
tana karanto addu’o’i. “Ya Allah ka ba
shi lafiya mai albarka, ka tashi kafadarsa”
Abba ma da bai cika nuna damuwa ba, yau
kam ya kasa zaune bare tsaye. Can sai
ga Fa’iz ya shigo, bayan Faruk ya masa waya,
ya sanar da shi suna asibiti da su
Abba.
%************
Bayan sallar Asuba ne Umm Adiyya ta kama
hanyar dakin Maami don ta gaishesu,
sai dai ta ji mamakin rashin ganin Maami, inda
ta saba zama, bayan ta idar da
sallah. Wannan ya sa ta ja kofar ta juya zuwa
dakin Abba, nan kam a kulle ma ta ji
shi. Tana zuwa daki, ta daga wayarta za ta ki-
rasu, nan ne ta samu missed calls Www.bankinhausanovels.com.ng
guda goma sha hudu a wayarta, har da asub-
ahin nan ma, an kirata. Tabbas akwai
abinda yake faruwa, koma ya faru. A gurguje
ta danna lambar Maami.
“Wane irin bacci ki ke yi ne haka?”
“Maami lafiya? Ku na ina, na tashi ban ga
kowa ba.”
Ga mu nan a asibiti, ina so na ce miki ki
kimtsa komai da komai, ki ce Innayo ta yi
abinci mai dama. Don duk a tsaye muka
kwana.”
Maami waye ba lafiya, ba ku tashen ba?”
Ba komai, ke dai ki shirya ki taho da duk
abinda ya kamata, idan kin zo, sai na koma
gidan.”
“To muna fitowa yanzu, wane asibiti ku ke?”
“Yanzu dai na ji Abbanku yana kokarin mnu
koma Nizamiye, amma idan ba mu tafi
ba, zan fada maku kafin zuwa ku fito. Faruk
zai zo ya daukeki.”
Maami Fa’iz ne ba lafiya?
Zaid ne ya samu hatsari jiya da dare.”
Wani shuuu! Ta ji kunnenta suna mata, tamkar
mai nemo tasha a gidan Rediyon da
suka tashi aiki.
“Na’am? Yaya… Hatsari kuma? Jiya fa ya bar
nan lafiya.”
Baya ba ta kadan ai, ki je ki kammala.” Daga
nan Maami ta kashe wayar. Gaba
daya kafafunta sagewa suka yi, ta ji ba za ta
iya tafiya ba, sai bin bango ta yi ta
fadawa Innayo abinda za ayi.
“Za mu kai asibiti ne Yaya ya yi hatsari jiya.”
Subhanaallah. Allah ba shi lafiya ya tsare
gaba.”
Ameen Ya Rabbi.” Ta amsa sannan, ta koma
sama, bandaki ta wuce ta watsa
ruwa. Safiyya kam ba ta tsaya yi mata wanka
ba, ta dauketa suka yi kasa, cikin minti
talatin sai ga Faruk ya iso, fadawa motar ta yi
don su tafi, tunani goma da ashirin ne
suka addabeta. Tabbas bayan ya bar gidan
Abba ne kenan, ya yi hatsarin nan.
“Faruk yaya… yaya jikin nasa?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ba za dai mu ce komai ba tukun. Likitan ya
ce dai babu karaya, amma ya ji rauni
sOsai, don haka ba za su ce komai ba, sai sun
gama gwaje-gwajensu, za mu san
komai.”
Shiru kawai ta yi, tana goge zufar hannunta a
jikin zaninta, duk da sanyin
iyakwandishan din da ke fita a cikin motar.
Sun yi kusan awa guda kafin Likitan ya ce,
Mun samu mun tsayar da bleeding din
da yake yi, yanzu ya dan daidaita Za a iya
ganinsa, amma da daddaya.”
Wata irin ajiyar zuciya Maami ta yi, ta rinka
hamdala. Ita ta fara shiga, sai Abba ya bi
bayanta. Haka dai suka shiga sama-sama ba
zama.
Umm Adiyya kanta na Kasa, ta buga tagumi ne
ta ji idanu caa a kanta. Tana,
dagowa ta ga ita suke kallo gaba dayansu.
Ware idanu ta yi, suna nufin ita ma za ta
iya shiga?
Amma Docto…
Maami ce ta ba ta wani zazzafan kallo tukun,
ba shiri ta samu kafafunta na cilluwa
gaba. A hankali ta tura kofar.
Yana kwance shame-shame a dakin, har
lokacin bai san inda kansa yake ba, idan
ka dauke kumburin da ke gefen habarsa, ba za
ka ce ya ji rauni ba. Sai dai mutum
irin Zaid da tashin hankali ka gansu ba sa iya
koda motsi.
Wannan ya kara kashe mata jiki, ta san dan
Adam ba a bakin komai yake ba, nan ta
tsaya ta shafe mintoci, tana kallon abubuwa
suna motsi, suna kara a kewaya da shi.
Goshinta ne ya tattare cikin tunani.
A dai-dai lokacin abin ya fado mata. Da sauri
ta juya ta fita daga dakin, ba ta tsaya Www.bankinhausanovels.com.ng
inda kowa ke jira a waje ba, fita ta yi can farfa-
jiyar asibitin, ta gangara wurin da wasu
dan
shuke-shuke suke, ta yi zamanta akan dan
dakalin da ke gun.
************
Washegari Ummu da Mama suka taho duba jikin
Zaid, nan aka bar Umm Adiyya da
raba idanu. Ta rasa me yake mata dadi a
duniya, abin da ya rage mata kawai, shi ne ta ba

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE               …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *