UMM ADIYYAH CHAPTER 64 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 64 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 


kwakwalwarsa take fada masa kenan, amma
idan ya yi haka, ya bata goma ne,
daya ba ta gyaru ba, tabbas yaran suna da
fasaha, sai dai rashin samun kula mai
kyau da kuma saurinsu na son su yi kudi ta ko
wane hali, ya sa sun zama yan Www.bankinhausanovels.com.ng
yahoo yahoo.
“Banda hustling’ me ka ke sha Fa’iz?” Zaid
ya jefawa Fa’iz wannan tambayar., yana
Kare masa kallo.
*** *****
BABI NA ARBAIN
“Wallahi Yaya, banda sigari ban taba shan ko-
mai ba. Shi ma sau biyu kawai na taba
sha. Maami za ta tsine min idan ta ji abinda na
yi, don Allah kar ka fada mata.”
Fa’iz kam kuka yake yi wee-wee.
Yanzu abu na gaba, ya dace ina dakin taro
mintuna goma da suka shige. Ina
tattaunawa da ma’assasa (N-Bit Links). Abinda
na ke so da ku, shi ne za mu shiga
da ku wurin taron, za ku maimaita abinda ku
ka fada min yanzu, za kuma ku nemi
gafara da kuma yarjejeniya. Zan kira lauyanmu
mu tattauna, kafin nan ku je nan
Reception ku jirani.”

Yaya Zaid, za su sa a daure mu. Yaya Zaid na
shiga uku Wallahi su Abba ba za su
bar ni ba.”
Waye zai fada masu?” Yana fadin hakan ya
mike, ya dauki wayarsa a kan teburin
tsakiyar ofishin nasa, sannan ya bude kofar ta
sa, sumui-sumui jiki a mace suka fice,
wayarsa ya latsa, ya nemi Barrister A.I Mahdi.
“Mun shirya, mu hadu a (Conference Room
A).”Www.bankinhausanovels.com.ng
**********
Tunda suka dauki hanyar gida motar shiru take.
Fa’iz ya sargafe hannayensa cikin
juna tamkar mai jin sanyi.
Ka na jin sanyi ne?” Zaid ya tambaya.
Da sauri Fa’iz ya girgiza masa kansa.
Ganin shiru ya mika har suka isa Maitama sun
sha kwanar gidansu ne. Fa’iz ya ce,
“Yaya Zaid, na gode, Allah ya biyaka da gidan
aljanna, ban san me zance maka ba.
Amma yau ka ceci rayuwata.”
Ba komai Fa’iz, mun yi wa Allah ma laifi, ya
yafe mana, bare dan Adam, na dade da
sanin yafiya ya fi riko fa’ida. Kawai dai mu-
tane ne ya kamata su fahimci hakan.” Zaid
ya fada hankalinsa ya bar cikin motar.
Fa’iz ya dan kalli dan-uwansa, sannan ya ce,
Idan ba za ka damu ba, na fada maka
wani abu?”
Zaid ya dan yi murmushi ya ce, “Ina jinka.”
“Ka san ta damu da kai ko? Har yanzu tana ke-
warka, ba ta son nunawa ne wata
kila.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Dai-dai lokacin suka isa bakin gate din gi
dansu. Zaid ya taka birki da karfi.
“Kayi hakuri, da ban ce komai ba.” Fa’iz ya yi
saurin fada hade da hadiye yawu,
lokacin da ya ga hadarin da ke fuskar Zaid.
Ana bude masu suka shiga ciki, ya sa hannu
zai bude kofarsa, Zaid ya tare shi da


hannunsa, Fa’iz ya dubi hannun Zaid akan
cikin sa ya dago ya kalli Yayan nasa.
Ina son ka san idan zan yi aiki da kai, ba za ka
shiga rayuwata ba, kar ka sake
dauko min maganar ‘yar-uwarka.”
Shiru ne ya ratsa motar, yayin da Fa’iz ya ji
tsikar jikinsa ta tashi tsabar tsoro. “Na ji
Yallabai.”
Ya fada, sannan Zaid ya sake shi ya fice daga
motar. Aviator glasses dinsa ya cire
lokacin da ya zo shiga cikin falon, don su gaisa
da Maami, idan ta dawo. Sai dai
bakin takalmi da ya gani a bakin kofa ya sa ya
shiga da niyyar ganin su da baki.
Falon Abba ya shiga kai tsaye, saboda a zaton
sa bakin suna babban falo ne.
Idanunsa na sauka kansu, ya juya ya koma
babban falon, sannan ya fito da wayarsa
ya danna lambar.
Ki zo mu yi magana.” Ya fada kai tsaye a
cikin wayar, bayan an daga.
“Maganar ba zai jira sai anjima ba? Ina da
bako.” Ta fada kasa-kasa, tana jin sautin
gudun jini a kunnuwanta.
Za su iya jira bakin naki, na ga ba na sauri
bane ai.”
Yana fadin haka ya kashe wayar ta sa, ya tsaya
dai-dai wundon falon yana hango
ranar da take shirin faduwa a magangararta.
Bayan minti daya ya juya, ba tare da ya
ji takunta ba, sansanyar Kamshinta ya ji.
Wanda duk wanda bai san kamshin ba zai
yi wuya ya ji kamshin, amma shi da ya san
kamshin dole ya gane.
Wane irin abu ne da ba zai iya jira ba, na bar
baki suna jirana.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Kallonta ya yi daga sama har kasa kamar mai
fedeta da idanunsa, ya takure
fuskarsa. “Idan bakin zafi ne za su iya tafiya,
saboda abin da na ke so na fada miki
yana da muhimmanci, sannan ki kwantar da
hankalinki Ummu Adiyya ba abinda ki
ke tunani bane, saboda haka stop with the eye
batting (Ki daina fari da idanunki).”
Bakinta ta bude cikin tsantsar mamakin kala-
mansa. Ta kara rufewa ta kara budewa,
amma ta rasa wace amsa ya kamata ta ba shi.
Ina saurarenka.”
Za mu iya gaisawa kafin nan?” Ya sassauta
fuskarsa.
*”Mun riga mun wuce wannan wurin a tunan-
ina, ka fada min saboda na koma ciki, ka
ga ba kyau barin mutum yana jira.”
Hmm!” Ajiyar zuciya ya sauke, ya sauke han-
nayensa da suke jingine da jikin windon
falon, sannan ya samu wuri ya zauna.
Za ki bukaci ki zauna, idan ba dai ki na shirin
ki fadi bane.”
Zan iya daukar koma menene.
Kafadarsa ya daga sannan ya ce, *An gane su
waye suka saka Mr. Akim tattara
data din kamfaninmu.”
Shiru ta yi tana kallonsa, tunda a tunaninta dai
yanzu ta bar aiki da kamfanin, to
kuma wani abu ne maganarta da su? To abinda
ya wuce shekara daya da rabi da
suka shige, meye na tonowa?
Ganin ta kura masa idanu ne, ya sa ya kalli
cikin idanunta ya ce, “Ummu Adiyya, ki
zauna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ajiyar zuciya ta yi ta dan samu gefen kujera ta
jinginu. Fa’iz ne da abokansa suke
wannan aikin.” Shiru ya yi ya bari ta gama
zukan zancen da kyau.
“Wani Fa’ iz?” Ta fada tana kyafta idanu.
Daidai lokacin Fa’iz din ya shigo falon.
Idanun Adiyya suka sauka a kansa.
Fa’iz! Fa’iz?” Idanunta suka kankan ce akan
kanin nata.
Wallahi Adda Ummu sharrin shaydaan ne, ba
zai sake faruwa ba.”
“Amma ka ba ni kunya Fa’iz, abinda za ka
yiwa su Maami kenan? Kowa yana maka
kallon yaron kirki, ba ka damu da sha’ anin mu-
tane ba. Ka san me ka janyo a dalilin
shirirtarka na neman suna da kudi kuwa? Ka
san barnar da ka aikata? Inna-
Lillahi’ wa-Inna-llaihir-Raji’un!.” Kanta ne ta
ji ya yi wani sarawa.
“Yanzu ka kyautawa kanka kenan? Yaya ma
aka yi har ka fada irin wannan
rayuwar?”
Hawaye ya share da hannun rigarsa ya ja
hanci.
“Yaya Zaid ya ce zai daukemu a wurinsu,
amma don Allah kar ki fadawa su Abba,
kin ji?.”
Ya fada yana kallon Zaid, tamkar mai neman
ya taya shi rokonta. “Ni yanzu me ka
ke so na ce?”
Ba komai, ya wuce, mun yi magana da shi.”
Ta ji muryar Zaid ya kwararo cikin amo
mai zurti.
“Yaya za ka yi ka bar su haka, idan gobe suka
yi abinda ya fi haka kuma fa? Kullesu
ya kamata ayi, kuma ni kam sai Abba ya sani,
ai masa duk abinda aka ga dama,
yaushe ya zama haka?” Ta fada yanzu kam ita
ma ta gama kulewa can.
Fa’iz da ya zaci yar-uwarsa za ta taya a bada
hakuri sai ga shi tana cewa me ya sa
akayi masa hakuri. Www.bankinhausanovels.com.ng
Adda Ummu ba kowa bane yake da riko dai
irinki, da za a biyewa abinda ki ka yiwa
Yaya yau da bai rufa min asiri ba.”
Fa’iz!” Zaid ya fada a fusace yana kallonsa,
lokacin da idanun Adiyya suka ciko da
hawaye. Zaid ya dube shi ya ce, “Ka ba ta
hakuri yanzun nan.”
Ummu Adiyya kam girgiza kai kawai take yi,
cikin takaici. Dai-dai lokacin Fa’iz din ya
furta mata kalmar hakurinsa, sannan ya juya ya
bar falon, don ya san Yaya Zaid din
ba zai bar shi ya gama amayar da cikin sa ba,
amma ai gaskiya ya fada.
Kafafunta ne suka hau girgiza, suna neman su
gaza daukarta. A dalilin nauyin
zancen kaninta a gareta. Tafiya ta yi za ta fadi.
Ya Subhaanallahi, so ki ke yi na rike ki yanzu
ko meye? Na ce miki ki samu wuri ki
zauna!” Ba shiri ta zauna.
Ban san kuskurena ba a kaina ya tsaya kadai
ba, ashe har kan zuri’a baki daya ne sai yau, ban
taba tsammanin Fa’iz… Fa’iz zai taba fada min
abinda ya fada ba yau.
I’m such a bad influence, ba ni da kirki ko
kadan.” Hawaye ne suka fara malala a
fuskarta, nan da nan fuskarta ta dawo kamar
jan tumatur.
Yaya Zaid, ya fito da kyallen hankici daga
cikin aljihun gogaggen suit dinsa ya mika
mata hade da kau da kansa gefe, saboda kar
ma ya ga hawayen nata. “Ki daina
damun kanki, haka yaran suke yanzu, addu’a
kawai za mu sa a gaba mu yi ta nuna
masu hanyar da ta dace.”
Hawayen ta goggoge, ta sa a hancinta ta share
majinan da ya zo tare da hawayen
nata. Ta kara nade hankicin, sai kuma ta rasa
yadda za ayi ta ba shi kayansa, Www.bankinhausanovels.com.ng
bayan ta goge komai da shi. Kamar ya karanci
abinda ke ranta kuwa ya ce, “Ki
ajiye.” Sannan ya juya bayansa.
“Sai ki kimtsa ki koma, kin bar bakonki yana
jiranki.” Yana gama fada ya yi waje, nan
ta zauna a daskare kamar an dasa ta, wai yau
Yaya Zaid ne har zai ganta da wani
ya share ta, ya nuna halin ko in kula akan
sha’aninta.
Wato yanzu koda zai ji labarin an sa ranar au-
renta da TJ. Ba abinda ma ya dame
shi kenan, ita ce take ta duma kanta akan me
zai kasance yake gudana a cikin
ransa idan ya samu labarin tana shirin bawa TJ.
kofar neman aurenta.
Ajiyar zuciya ta yi da ta tuna ta bar TJ. A ciki
yana jiranta.
Da fatan dai komai lafiya, kin ce ki na zuwa
yanzu, na ji kuma shiru, saura kiris! Na
je na ga ko kin bata ne hanyar ki ta dawowa.”
Murmushi ta yi sannan ta ce masa, “Kan batun
ofis ne, amma mun gama magana.”
Ofis kuma?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Eh, wurin da na yi aiki da, akwai abinda suka
tambayeni, shi ne na tsaya masu
bayani.” Ta rasa dalilin me ya sa ta yi karya ba
ta fada masa da Yaya Zaid suka yi
magana ba.
Murmushi ya yi mata ya ce, “Muna magana
dazu.”
Tana kallon kan carpet din falon Abban ta ce
masa, “Uhmm?” Ya kula da hankalinta

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE               …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *