UMM ADIYYAH CHAPTER 60 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 60 BY AZIZA IDRIS GOMBE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Mun tsaya 

Oh Yaya Salisu, yaya gida da su Aunty Mashkura?” “Alhamdulillah! Suna Kalau, uhm na shigo Bauchi ne jiya da dare, ban sani ba ko ki na gidan yar kin nan ne na (Airport Road)? Akwai maganar da na ke so na zo mu tattauna.” Ummu Adiyya ta yi shiru tana Www.bankinhausanovels.com.ng nazari, to ita kuma? Wace irin magana ce hakan
kenan? “Wani abu ne ya faru?” “A’a ba komai, idan dai ki na nan ko za ki ba ni lokaci sai na zo anjima?”
Eh ina nan.” “To shi kenan na gode. Allah ya kai mu.”
Ameen.” Ta fadla, sannan ta cire wayar a kunnenta cikin nazarin ko menene hakan? Surutun Safiyya ne ya dawo da ita daga guntun nazarin da take yi. Dakin Adda Zubaida ta shiga, ta samu ta idar da karatun Al-Kur’ani. “Adda ga ta,
bari na yi wanka, idan na bar ta a aki, aiki za tai min da turare ko jambaki.” “Ki rinKa dorawa a sama ai kawai, idan ba haka ba, haka za ku rinKa fama.”

“Cab! Yarinyar da ta iya darewa kujera ta za-
una kan madubin? Har cikin wardrobe
shiga take yi, naku kawai zan fara dauka,
tunda ba ta bata maku nawa ta raina.”
“Me za mu yi ne yau kam?”
“Kawai Adda koma meye, kullum ko mun yi
time table sai ya rushe. Yawwa dazu
Salisu ya kirani, wannan abokin Yaya Zaid da
suke zuwa nan taren nan wasu
lokuta.”
“Wai me?” Www.bankinhausanovels.com.ng
“Cewa ya yi wai akwai wasu ababen da yake
so ya zo mu tattauna, gaba daya kaina
ya kulle, na rasa meye ne wadannan
abubuwan.”


A cikin zuciyar Adda Zubaida har tsallen
murna take yi. Allah sa abinda take tunani
ne. Murmushi ta yi ta ce, “Tunda ya ce zai zo,
sai a saurara aji ko ma meye ne ko?
Yanzu kam muna da baki kin ga shirin girki naa
musamman za mu yi.”
Ummu Adiyya ta dan turo bakinta tana kallon
yadda a take Adda Zubaida ta za ku
daga jin an ambaci Salisu na zuwa.
Haka dai suka hau aiki, bayan ta shirya suka
dan hada ababen tarar baki dan
daidai. Karfe biyar kuwa sai ga Salisu ya iso.
Mai-gadinsu ya yi sallama ya fada,
suka shigo da shi falon Baban Walid.
“Sannu da zuwa.” Ta fada, bayan ya zauna,
fuska a sake ya amsa. Nan ta ajiye
masa abubuwa, sannan ta zauna suka gaisa da
kyau. A hakikanin gaskiya sai da
ranta ya dan yamutse, da ta gan shi, shi kadai.
“Hajiya ai da kin bar duk wannan, ba ma zama
zan yi ba, kamar yadda na fada miki,
magana ce mai muhimmanci na zo mu yi da
ke.”
Ina jin ka Yaya Salisu.” Ta fada hade da dan
gyara zaman ta, kanta a kasa.
“Har ga Allah ba sai yanzu na so na zo mu yi
wannan zancen da ke ba. Amma
abubuwa sun yi ta faruwa da ba sa cikin ikona,
sai yanzun dai Allah ya kaddara.
Batun aboki na na zo mu yi.”
Ba shiri gaban Ummu Adiyya ya fadi, ta dago
ta kalle shi.
“Batun abokinka?’ Www.bankinhausanovels.com.ng
“Eh, na san abubuwa da dama sun faru marasa
dadi a tsakaninku, amma yadda na
sanku, sam ban ji dadin hakan ba, ban kuma
zaci za a kai warhaka ma ba ku koma
ba. Har ga Allah komai na rayuwar nan dan
hakuri ne, idan ana kwatanta shi, sai
komai ya tafi yadda ya dace.
Ina so na tuntube ki ne, na ji yaya abin yake a
wurinki? Ban san me ya faru daga
baya ba, ko kun tattauna da shi, ko ba ku samu
zantawa ba, amma abin da na sani,
shi ne a halin yanzu Zaid yana gaf da tafka
kuskuren da ni na san zai zo ya dame
shi daga baya, sannan a zo ana da-na sani.”
A hankali Umm Adiyya ta dago idanu ta dube
shi. “Me ya faru?”
“Zaid zai yi aure.”
Cak! Ummu Adiyya ta ji numfashinta yana
nema ya gaza fita, daga idanunta, ta dubi
Salisu ta ce, “Aure?” Tamkar ba ta jiyo da
kyau ba.
“Eh, a takaice ma da kansa ya wakiltani nayi
masa ja gaba kan shirye-shiryen bikin.
Yana maganar a sa nan da wata daya. Ni na
san kuskure zai yi.”
Sunkuyar da kanta ta yi, ta maida ruwan
hawayen da ta ji ya taba idanunta, “Hmm!
Wace ce?”
“Wata ce kanwar abokinmu.”
Murmushi ta yi mai ciwo, “Tunda zance ya kai
ga aure kam, ai ina ga zuwa yanzu
sun kammala duk shirye-shiryen da suka dace.
Ba abinda zan iya yi, ba zan iya
tsayar da shi ba.” Ta fada tana dan girgiza
kanta, “Wata kila kuma ba ni ma da zabin
da ya wuce nayi masu fatan alkhairi.”
“A’a Hajiya kar ayi haka mana, sam ba haka
abin yake ba, na takaita miki zance ma,
saboda ke zai yi wannan auren, shi ya sa na zo,
don na sameki.”
Kwafa ta yi ta ce, “Domin ni kuma? Me yake
so ya gwada min?” Ta fada muryarta na
rawa. Www.bankinhausanovels.com.ng
“A tunaninsa, ba ki damu da ku koma tare ba,
tun farko kuma ke ki ka nemi ku rabu,
bayan ya yi hakan, aka zo sulhu, ya yi zaton za
ki ba shi manuniya akan ku gyara
aurenku a gidan Baffa, amma ki ka nuna ba ki
shirya hakan ba, ta hanyar dauke
kanki, wannan ne yayi masa zafi har ma ya yi
tunanin ya nisanci inda ki ke.”
“Me yake so na yi? Yaya Zaid da kansa ya
yanke hukuncinsa, so yake yi ni na bi shi
na ba shi hakuri na gyara zamanmu, na yi ko
mai ni kadai da kaina? Idan zama da
rabo ya kare, ai ba yadda aka iya dole a rabu.”
“Hajiya, ki yi hakuri. Har yanzu yana matukar
sonki, kuma Wallahi alama daya ki ka
ba shi na son ku gyara al’amura, ina tabbatar
miki zai janye batun wani neman aure
da yake yi.”
“Yaya Salisu, shi fa ba karamin yaro bane, da
zan sa shi ko na hana shi, idan ya ga
daman yin komai da rayuwarsa ma, ai sai ya
yi, wannan bai shafeni ba, tunda ni dai
ba matarsa bace, ko ni matarsa ce, ba hurumina
bane na hana shi yin wani aure,
bare yanzu. Ku bar shi ya yi aurensa, ai kullum
ci-gaba ake so a rayuwa.”
Salisu dai ya yi tsam! Ya rasa a tsakanin
wadanne irin mutane aka matse shi. “Ki yi
kokari dai ki yi nazari akai, domin muddin
hakan ta faru, alakar ku za ta karasa
warwarewa.”
Dariya ta yi ta ce, “Alakar da babu ita ka ke
magana a kai fa. Ai wannan ta dade da
karewa tuni. Na gode da ziyarar da ka kawwo
min, a gaida su Aunty Mash.”
Tana fadan haka ta mike daga falon cikin
kokarin danne tashin hankalin da ta tsinci
kanta a ciki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Yana barin gidan Adda Zubaida, sai ga wayar
Zaid ya shigo, ajiyar zuciya ya yi ya
daga.
“Ina jin ka.” Ya fada a dakile.
Zaid ya dan yankwana fuska cikin tunanin ko
me ya faru, leka wayar ya yi ya kara
dubawa “Kai kuma ina ka bace ina ta neman
wayarka ba na samu? Za mu hadu
anjima din ko?”
“Malam me zan zo na maka, tunda kai ba jin
shawara ka ke yi ba? Ba ka damu da
kowa ba idan ka tashi yanke hukunci, kanka
kawai ka sani,”
Hucin numfashi Zaid ya sauke, an kuma.
“Yanzu dai koma meye ne ka shigo ofis sai
mu yi magana ko mu hadu a Wuse mu zauna.
And yes akwai wasu shirye-shirye da
ya kamata mu karasa game da bikin nan.”
“Ba zai yiwu ba saboda ina Bauchi.”
“Bau… Shi ne ka tafi babu sallama?”
“Ni fa ka cireni tun wuri a wani batun aure-au-
ren kan nan.”
“Wai me yake damunka ne? Bayan na yi maka
bayani kuma ka san komai wace irin
magana ce wannan?”
“Lokaci ya yi da idanunka za su bude.”
Iya abinda Salisu ya fada masa kenan ya kashe
wayar. Zaid ya dade rike da wayar
a hannunsa.
%**** ******
Har ya yi shirin kwanciya a ranar da dare yana
azkar dinsa, wayarsa ta yi kara. Yana
ganin sunan kan wayar ya ji wani iri, haka dai
ya daure ya amsa.
“Hello, ki na lafiya?”
“Alhamdulillah! Na kira ne mu gaisa, na ji ka
shiru kwana biyu.”
Murmushi ya yi dan kadan, sannan ya ce, “Kar
ki damu ba wani abu bane, kawai na
tarar da ayyuka sosai a gabana ne tun da-
wowata, amma zan samu lokaci na zo mu
gaisa da kyau. Ranar na zo a tsatsaye.”
“To sai yanzu hankalina ya kwanta, da na yi
tunanin wani abin ne daban.”
“A’a ba komai, sai da safe.”
Yasmeen ta dan yi shiru, a daya bangaren, da
alama ba ta so ya katse wayar da
wuri ba, “Allah tashe mu lafi ya a huta gajiya.”
“Na gode, ki kula da kanki.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Shiru ya yi yana nazari, shin yarinyar yake
yaudara ko kansa? Shafa fuskar wayarsa
ya yi, nan take fuska mai dauke da mafi
kyawun lobewar kumatu ta dube shi, yana
Kara shafawa, wata fuskar ta kalle shi, dariya
take yi ta dan sa hannu ta kulle
bakinta.
A kitchen dinsu ne, da katon kwanon corn-
flakes a gabanta, ya tuna lokacin da ya
dauketa wannan hoton. Bayan ya gama mata
tsiyar ta zama cereal addict, ta ce
sharri yake mata, shi ne ya dauketa ya ce, “Zan
adana kar ma ki musa a gaba. Don
na ga alama kin zama Sarauniyar rinto.”
Hoton da ya fito na gaba shi ya fi so duk
cikinsu, gashinta ya bazo kan kafadunta
zuwa bayanta, ya tare gefen fuskarta, ta dago a
razane saboda ba ta san ya shigo
dakin ba, shi kuwa ya dauketa hoto, ranar shi
ya zauna ya shafa mata mai a
gashinta baki sidik mai laushi, ya yi mata
damsasa mata shi da abin feshinta, ya
kuma bata lokaci ya taje mata gashin. Za ta
kama ne ya ce, “Ki tsaya, na iya dai ni
ma.
“Za ka sa na yi kuka kawai, ka kukkulla min
gashina.”
“Juya ki gani, kin san na yi wa giginya kitso da
muke wasa da su Adda Sadiya ko?”
Hararsa ta yi kasa-kasa, “Na yi maka kama da
giginya ne?”
“Ina, sai dai ki gwada mata ja da mulmulewa.
You’re just too adorable (ke abar so ce, har ma
kin kure).” Www.bankinhausanovels.com.ng
Da ya gama ta kalli kanta, a madubi ta tuntsure
da dariya saboda guda biyu ya
kukkulla mata, suka yi kama da kahon rago.
Har yanzun da yake tuna wannan lokacin, sai
dai ya ji gudun zuciyarsa ya karu.
“Kin faye shiga rai Twinkle.” Ya fada hade da
shafe kan wayar, nan ya shiririce da
kallon hotunanta, wasu ya yi dariya, ya girgiza
kai wasu kuma ya yi tsam zuciyarsa
ta cika dam! Da abubuwa masu nukurkusa

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE

UMM ADIYYAH CHAPTER 89 BY AZIZA IDRIS GOMBE               …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *