TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 7 BY AUFANA

TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 7 BY AUFANA

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Tasowa tai dasauri hanunta rik’e da wuk’ar idanuwanta na zubda kwallah tayo gun momy sai suka ja da baya da sauri momy nafadin “a,a wannan yarinyar nan anya tanacikin hayyacinta kuwa security’s kukamata mana kar muma tahad’a damu takashe” itakuwa kuka take tana fad’in “momy waya lashe hamma faruk momy waya kasheshi” cikin matsanancin kuka take maganar,,,…..

Security’s hud’u suka kamata suka rik’eta momy tazo ta wanketa da kyawawan marika sunfi a kirga tana fad’in “kin cucemu MUFIDA kin yaudaremu kin rabani da mijina abun k’aunata sannan kuma kin kashe faruk wallahi bazan barkiba saina kema saina kasheki” tana maganar tana marinta kuma tana dukanta, dakyar mubina da d’aya dagacikin security’s d’in suka jata,,,…..

Tsintsar mamakine ya bayyana a fuskar MUFIDA kwallah nazubarmata cikin mamaki tace “momy kina nufin kice dady na ma yamutu” mubina ce tai magana cikin kuka tace “to wazaki tambaya bayan kece da kanki kika kasheshi sannan kuma kikazo yanzu kika kashe hamma faruk kokina nufin kice rainama hankali zakiyi bayan ankamaki dumu dumu” cikin mamaki tace “ni kuma kina nufin kice nice nakashe dady da hamma” mubina tace “kece za’ayiwa wannan tambayar ba kece zakiyi tambayar ba saboda amsar tambayar tana gunk..” batako k’arasaba sukaga MUFIDA tazube k’asa somammiya, cikin tsintsar b’acin rai momy tace “kukira I.G da D.I.G da commissioner of police kufad’amasu sannan ku tsareta anan kamin su k’araso karku yarda tad’aga izuwa konan da toilet ne itakuma gawar za’aturo a d’auketa” suka amsa da “yes ma angama” saita juya ita da mubina suka wuce,,,,…..

Acikin y’an dak’ik’u kad’an zancen yakarad’e ko’ina da ko’ina acikin k’asar kebbi tini momy tasaka aje adakko munira school adawo da’ita, dika gidajen biyu banda koke koke da tsinuwa ga MUFIDA ba abunda akeyi momyn faruk kuka momy kuka su bilkis da mubina kowa kuka yakeyi gida dikya rikice sai koke akeyi, har and’akko gawarwakin sai Abbu yace ajira har gobe dai dai y’an uwa na nesa dana kusa sun iso sannan a sallacesu akaisu makwancinsu,,,”…

       Haka kuwa akayi, washe gari around 10am kowa ya’iso kusan dik rabin familyn gaba d’aya sun iso sai waenda ke nesa sosai ne kad’ai suka rage suma kuma sunakan hanya, Governor da PA d’insa I.G da D.I.G da commissioner of police da sauran shuwagabannin gomnati dik sunzo,,,….

      10:30am dot aka fito da gawansu, gidan sarki akamasu sallah sannan aka kira su momy sumasu addu’a sannan awuce akaisu makwancinsu na gaskiya, koda sukazo ma komai basu iyayiba banda kuka abban ammar ne kawai ya’iya tsayawa yamasu addu’oi shima sai zubda kwallah yake, Abbu da hajiya ma sunmasu addu’oi sannan akadaukesu akawuce mak’abarta aka binnesu,,”….

Allahu akbar kullu nafsin zaa’ikatul maut dady da hamma faruk anrigamu gidan gaskiya Allah yamaku rahama ya kyautata tamu idan tazo ameen,.

A b’angaren MUFIDA kuwa tini ta farfado sai kuka take matsananci idanuwanta dik sun sauya launi sunyi zajir sun kukkumburo saboda kuka ita bama kazafinda akamata yasa take kukaba a,a mutuwar dady saboda tasan yanzu tabbas tarasa gata har abada rayuwarta saidai wani iko na ubangiji,, gidan kuwa gaba d’aya ansakamasa tsaro gaba da baya ko’ina police ne da sojoji,,,….

           Bayan andawo daga mak’abarta su governor suka shigo gida sukayiwa su hajiya dasu momy ta’aziyya sannan suka wuce, suna wucewa I.G yawuce gidan faruk suka d’auki MUFIDA suka wuce da’ita izuwa station d’insu,,,….

Suna isa kuwa yasa akashigar da’ita wani d’aki inda suke magana da mai laifi kan su hukuntashi, bayan anshiga da’ita tana zaune itakad’ai saiga I.G yashigo tareda wata police mace k’atuwa, zama yai a kujerardake fuskantarta sannan yad’ago jajayen idanuwansa masu ban tsoro yakalleta fuskarsa tamke yafara mata magana “ke meyasa kika kashe mahaifinki da mijinki…? wane laifi suka maki…?” haka yajeromata tambayoyin atare,, wasu zafafan kwallah ne suka zubomata bakinta na rawa tace “Wallahi wallahi Allah banina kashesuba shin wace riba zanci idan nakashe mahaifina haba kudinga tinani mana kan kuyi magana mahaifinane fa shi kuma wanda banida kamarsa a duniy…” bata k’arasaba yadaka mata tsawa saida ta razana cikin kakkausar murya yace “ba wannan na tambayekiba kifad’aman meyasa kika kashesu waya sakaki ki aikata hakan” cikin kuka tace “nafad’a maka wallahi Allah banina kashesuba ni ko kiyashi bantab’a kashewaba bare mutum kuma ko mutum ma dady na da yayana” wani kallo yamata sannan yace “ohhkk bazaki fad’aba kenan Good A.S.P hafsat” matar dasuka shigo atare tace “yes sir” yace “kishiga da’ita kumata dik yanda yadace har saitafad’i gaskiya tai magana sannan kufito da’ita” matar tace “ok sir angama, ke tashi muje sha sha wacca batasan ciwon kantaba barin irinku acikin al’umma bala’i nema wallahi” MUFIDA tamik’e tsaye jiki ba kwari suka fita atare,,,,….

STORY CONTINUES BELOW

    Sai kusan 1pm sannan munira suka iso tin a k’ofar shigowa dataga y’an zaman makoki tafashe da kuka dakyar ta’iya k’arasawa cikin gidan, tana shiga tafad’a jikin momy tana kuka mai tsuma zuciyar mai karatu cike da tsintsar tausayi, da akafada mata wai MUFIDA ce takashe dady da faruk k’in yadda tai tace “kai ina wallahi k’aryane wannan sharri ne wanine kawai yakeson yasaka aunty MUFIDA acikin tashin hankali bayan wanda tashiga na rasa dady amma wallahi sam Anty MUFIDA bazata tab’a iya aikata wannan laifin ba” wata muguwar harara momy tawatsa mata batareda tace mata komaiba hakan yasa dole munira takama malamin bakinta,,”….

Wani d’aki mai duhu tashiga da’ita tana ganin cikinsa tagane gunda suke horasda masu laifine nantake k’irjinta yafara bugawa da k’arfi da k’arfi, wasu mata taga sunshigo su hud’u manya masu girma sosai kuma karfafa dan idan kagansu ma zakace maza ne kuma da’alamu dikansu ba musulmi bane A.S.P ce kawai musulma acikinsu, suna shigowa tacemasu “ku tub’eta kusakamata riga yanzu” nan suka kama MUFIDA tana kallonsu suka ciremata kaya suka maidata daga ita sai brez da pant saisuka sake d’akko wata y’ar best bak’a suka sakamata girmanta iya cinya sannan suka rufemata fuskarta da wani kyalle bak’i,,,…

Bayan sun rufe fuskarta sannan suka kamata suka d’ora akan wani abu suka d’aureta sannan suka d’akko wata bulala irin wacca ake dukan doki da’ita ba ice bace ita bulala ce nan suka fara dukanta su biyu suna zabgamata ita tako’ina na jikinta musamman cikin k’afafuwanta da tafukan hannayenta, kuka take tana k’ara mai sauti saboda azabarda takeji amma haka sukacigaba da dukanta tintana ihu tana k’ara har muryanta ya disashe, saida suka gaji sannan suka kyaleta suka kwanceta suka maidata zaune, A.S.P tace dai dai fuskarta tace “kifad’amana meyasa kika kashesu? waya sakaki?”  cikin shesheka tana haki tace “wallahi banina kashesuba bani bace dan Allah kudaina cutardani banmaku komaiba bani bace” wani murmushin gefen leb’e tai sannan tace “ok da’alamu har yanzu baki shirya fad’ar gaskiya ba gyaiz zaku iya cigaba da aikinku”,,,….

Wasu karafa suka d’akko masu baki biyu sukazo suka kamo hanunta suka saka yatsunta bibbiyu aciki suka matsesu sosai, wata iriyar k’ara tai mai sautin gaske tareda fad’in “dadyyyyyyyyy……!!!” saisuka kyalkyale da dariya sannan suka koma a kafafuwanta suka sake saka yatsunta na kafa suka matsesu sosai da iya karfinsu tasakeyin wata k’arar sai kawai tasome saboda bak’ar azaba,,,”…

D’aukanta sukai suka dora kan wani table wai fad’i sosai suka watsa mata ruwa a fuska dole ta farfado numfashinta yadawo tafara tari tana numfashi sama sama, kyaleta sukai saida takusan 30mnts tahuta amma har yanzu yatsunta basu daina mata zafiba gashi sai zubda jini suke,,,”…

A.S.P ce tazo tasaka hanunta tadamko bakinta cikin mugunta tace “kin shirya fad’ar gaskiya ko har yanzu” yanzukam tariga data galabaita ko magana bazata iyaba danhaka shesheka kawai take sai matar ta tashi tsaye, matan sukazo suka danneta anan kan table d’in sannan suka rufemata fuska da wani towel k’arami sai suka d’akko ruwa cike da bucket suka fara kwararamata a fuska, juyi take tana neman d’auki amma ina haka sukacigaba da kwararamata su saida sukaga numfashinta nanema ya dauke sannan suka kyaleta tafara tari tana jan numfashi da k’arfi tana fitarda ruwanda suka shiga a hancinta da bakinta, ganin ta galabaita yasa suka barta haka amma badan sun k’are mata ponishment d’inba,,,..

Haka sukacigaba da gana mata azaba kala kala amma har yanzu tak’i tace itace takashesu yanzuma ko magana bata iyayi saboda bakinta ya kumbura sosai saboda dukanda suke mata jikinta dik tabo ne jini kam ba’amagana gashi har yanzu y’ar wannan best d’in itace ajikinta gashi tanajin sanyi saboda zazzab’inda take fama dashi gakuma yunwa da k’ishi saboda yanzu sau d’aya suke bata abinci ruwa kuma sau biyu kawai tini tafita hayyacinta dan idan kaganta sam bazakace MUFIDA bace fuskarta dikta sauya,,,”…

                *****  *****

Yau kimanin kwana hud’u kenan da mutuwarsu dady angama zaman makoki kowa ya watse saidai har yanzu gidan cike yake saboda bak’inda ke zowa daga nesa,,,….

Around 3pm momy tace akaita gun MUFIDA nan munira tace itama zataje saisukaje atare, suna isa aka kaisu gun MUFIDA munira tafashe da kuka saboda ganin halinda MUFIDA take ciki, dakanta tad’auki key tabud’e k’ofar dagudu tashiga ta tallafo ta tarungume tana matsanancin, MUFIDA kuwa “ruwa ruwa” kawai take fad’a ganin alamun kishi takeji saboda bakinta dikya bushe yai fari alamar dai kishi takeji, tashi munira tai taje tabud’e wani k’aramin fridge tagani tad’akko ruwa acikin gora tazo ta dagata tafara bata ruwan aikuwa zokuga yanda take karb’an ruwa tana hadiyewa kamar wacca tai shekara d’aya batasha ruwaba saboda tsabar kishinda takeji,,,”…

Batako gama shan ruwanba saiga A.S.P tashigo ta karbe ruwan ta watsar sannan takama hanun munira tafitar da’ita tarufe k’ofar, cikin masifa munira tace “wai ke matarnan anya kuwa musulma ce saboda ina kokonto akan musulincinki, wane irin rashin imanine wannan zaki kama baiwar Allah kudinga azabtar da’ita bayan kuma tafad’a maku ba’itace ta aikata wannan abunb…” bata k’arasaba momy tawanketa da mari sannan tace “amma dai wallahi munira kinji kunya dumu dumu aka kamata da wuk’a ahanu tagama kashe faruk sannan tabbas itace takashe Alhj amma dikda haka wannan bai isheki ki tsinewa wannan muguwar ba wato kenan ke bakya bak’inciki akan kashe maki mahaifi datai” d’agowa munira tai tareda fad’in “to amma momy” sai momy tai saurin dakatar da’ita dacewa “dakata munira bana buk’atar sake jin komai daga bakinki tinda ke kin nuna bakiji zafin kashe maki mahaifi dataiba” tana fad’ar haka takalli I.G tace,,,….

“I.G tinda tak’i tafad’i gaskiya kukawo d’in nasaka hanu sai shigarda case d’in court inaga acan zaifi tafad’i gaskiya cikin sauk’i” I.G yace “ok madam” sai yaje yad’akko yakawo mata tai signing sannan tace “bana buk’atar kukai file d’in gunsu hajiya harsaikungama komai lokaci kawai ake jira nafara shiga court” I.G yace “dik yanda kikeso haka za’ayi ur Excellency”  suna gama maganar tajuya suka wuce munira na kallon MUFIDA badan tasoba haka suka wuce sukabarta acikin wannan halin,,,,…..

Komai ya kammala nafara shiga court lokaci kawai ake jira sadai abunda yamasu matsala shine MUFIDA batada lawyer,,,….

24/3/2019 ~ 10:00am dot akafara gudanarda wannan shari’a a babbar cotun dake cikin k’asar KEBBI State, bayan lauyoyi sun gabatar kansu sai akafara sauraron k’ara, lauyan gomnatin shine yafara tambayoyi ga MUFIDA bayan yagama sai mai shari’a yace “idan lauyan wacca ake tuhuma yana kusa yazo yafara gabatarda shaidunsa domin kare wacca yake wakilta” nan aka shaidawa mai shari’a cewar batada lauya,,,….

Bayan mai shari’a yagama y’an rube rubensa sai yad’ago yace “duba da rashin lauya da wacca ake tuhuma batada andaga wannan shari’a har izuwa 27 ga wannan watan sannan tayi gaggawar samo lauyanta domin yakareta agaban kotu kan lokacinda aka d’iba yacika sannan acigaba da tsare wacca ake tuhuma” yana gama maganar yamik’e tsaye sai kowa yamik’e tsaye yafita,, police ne sukazo suka rik’e MUFIDA zasu fita, suna fitowa waje saiga y’an jarida kowanne sai jefowa MUFIDA tambayoyi yake itakuwa banda zubda kwallah ba abunda take takasa amsa kowa daga cikinsu tambayarsa, dakyar police suka samu suka wuce da MUFIDA,,,”….

Zaune take akan kujera tana kallon TV, wayartace a hanunta tana danne danne jin an ambaci sunan MUFIDA AHMAD SHITU wacca ta kashe mahaifinta da mijinta dasauri tad’ago kanta tamayarda hankalinta kan TV d’in, MUFIDA ce dai tagani an hasko tana kuka police sun rikota ‘yan jaridu sun rufeta sai tambayoyi suke mata, dasauri tafara kiran “ummi ummi ummi kizo mana” wacca takira da ummi tafito daga kitchen dasauri tazo tana fad’in “haba Amira wannan kiran mafarautan fa” tace “ummi zo kiga k’awata MUFIDA gatanan wai itace takashe mahaifinta da mijinta”,,,….

Zama tai ummin saida aka gama hasko abun sannan suka nannauyan numfashi atare Amira tace “wallahi insha Allah na tabba ummi wannan abun sharri ne saboda na tabbata MUFIDA bazata iya aikata wannan abunba” kallonta ummi tai sannan tace “Amira yanzu wani zamani yazo da ko iyayenka bazakayi shaidarsuba bare kuma aboki” cikin damuwa Amira tace “ummi nazauna da MUFIDA tsawon shekara hud’u nasan halayyarta mai kyau da mara kyau MUFIDA ko fad’a mukayi itace ke saurin sakkowa daga gadon fushi saboda bata iya gaba ko k’anwarta mubina data rainata wallahi kosunyi fad’a itace ke fara mata magana ummi na tabbata wannan sharri ne akamata kuma wallahi koma waye yamata wannan muguntar sai Allah ya toni asirinsa cikin gaugawa”,,,….

Numfashi ummin tasauke tace “to Allah yafitar da’ita yakuma toni asirin wanda ya’aikata kada a yankemata hukunci batareda itace ta aikataba” Amira tace “ameen ummi gobe dole nayi sammako k’asar KEBBI kuma dan Allah ummi kitayamu da addu’ah Allah yatoni asirin dik wanda ya aikata wannan abun” ummi tace “insha Allah Amira kuma zansaka a masallatai atayamu da addu’ah” nan Amira ta tashi tashige ciki,,,….

Washe gari tin 8am dot tashirya tai’sa airport 10am jirginsu yad’aga izuwa k’asar KEBBI…………..

Kwance take a k’asa tarufe idanuwanta dasuka mata nauyi sosai saboda kuka, makyarkyata take alamar tanajin sanyi, wani police ne yashigo d’aya dagacikin masu tsaronta saboda yanzu ba hanunsu I.G da A.S.P takeba tana gidan tsaro na kotunda ake shari’ar, yanzu tadaina shan wuya andaina azabtar da’ita saidaifa ankara mata tsaro sosai ko d’akinda take ma soja shida ke gadinsa,,,….+
Police d’inne yazo yabud’e k’ofa yakalleta yace “kizo ankawo maki ziyara” jikinta ba kwari ta tashi tamik’e tsaye kafafuwanta bako takalma, ita yasaka a gaba tana tafiya yanabin bayanta har suka isa, suna isa saitaga mubina ce tai mamaki sosai dan bata tab’a zaton mubina zata tina da’ita ba,,,…
Zama tai batareda tace uffan ba sai mubina takalli police d’in tace “plss malam kad’an bamu wuri inaso nayi magana da’ita ne” sai yace mata “toh amma 10mnts kawai nabaku” tad’aga kai alamar toh, juyowa tai takalli MUFIDA ta tsuke fuska sannan tafara mata magana “MUFIDA nazone naji dalilinda yasa kika kashemuna mahaifi da d’an uwa, MUFIDA meyasa kika kashe dady meya maki nawa aka baki danki kasheshi, hmm wallahi MUFIDA kinbani mamaki yanzu dik irin alkhairinda dady yamaki abunda zaki sakamashi dashi kenan ki d’auki wuk’a da hanunki ki kasheshi wallahi MUFIDA kinbani mamaki kuma kisani dik abunda kika shuka saikin girbesa nan bada jimawaba” zafafan kwallah ne suke zuba daga idanuwanta takasa ciwa uffan zuciyarta sai kuna take mata kalaman mubina sai k’ara tafarfasa mata zuciya suke, d’agowa kawai tai takalleta batareda tace mata k’ala ba,,,….
Ganin tamata shu yasa ranta yak’ara baci “MUFIDA kifad’aman memuka maki kika maidamu marayu dady yamaki komai a rayuwa yamaki abunda ko iyayenki bazasu tab’a iyamaki shiba shin ko dukiyarda yamallaka maki ce bata makiba shine kika kasheshi danki kwashe dukiyar gaba d’aya MUFIDA kinzama butulu kiyi abunda duniya gaba d’aya saita zageki daga k’arshe kuma kema kije inda kika kai mahaifinmu da d’an uwanmu hmm tabbas hausawa sunyi gaskiya dasukace *TSINTACCIYAR MAGE* BATA MAGE gashinan mungani acikin gidanmu” zuwan police ne yakatseta da cin mutuncinda takeyiwa MUFIDA saidai hartagama kalma d’aya MUFIDA bata mayarmata ba, haka ta tashi tawuce tana matsar ‘yan kwallan da sukaki fitowa MUFIDA kuma ta tashi suka koma ciki,,,…..
   
                 *****  *****
Around 2pm dot jirginsu yasauka k’asar KEBBI suna isowa kuwa tanemi taxi tashiga, kai tsaye hotel tawuce takama d’aki bayan tahuta tai wanka taci abinci tashirya sannan tafito, tana fitowa tanemi taxi tashiga kai tsaye tawuce gidansu MUFIDA,,,….
Cikin sa’a kuwa koda tai’sa munira nanan nan munira ta taryeta suka shiga tayiwa su momy ta’aziyya sannan munira tashiga ita da’ita d’akinsu, cikin nutsuwa Amira takalli munira tace “munira wai abunda akace MUFIDA ta aikata gaskiya kokuwa?” shuru munira tai kwallah suka zubomata tajuyo takalli Amira tace “Aunty Amira wallahi ni koda dik duniya zasu taru suce gaskiya ne ni bazan yardaba kawaidai ba yanda zanyine yanzu hakama wallahi tanacan agidan tsaro na kotunda ake gudanarda shari’ar kuma kan sukaita can saida suka wahaldaita yanzuhaka idan kika ganta bazakice ita bace” hmm….!!! Amira tasauke numfashi sannan tace “shikenan Allah i kyauta yanzu kitashi muje naganta sannan muje mufara neman lauyanda zai tsayamana”,,,….
Wani irin murmushin jin dad’i munira tai tace “abunda naketa tinani kenan yazanyi nasami lauyanda zai tsayawa Aunty MUFIDA saboda har yanzu bawanda yai zancenta kowa harkan gabansa yake momy kuma batun had’a shaida kawai suke basu zancenta” murmushi Amira tai tadafa shoulder d’inta tace “to ki kwantarda hankalinki insha Allah komai zai tafi dai dai daikon Allah sai asirin dik wanda ya’aikata wannan abun ya tonu mucigaba da addu’ah kawai” basuwani jimaba suka fita,,,….
STORY CONTINUES BELOW
Koda suka isa Court d’in sai sukai rashin sa’a akace bazasu ga MUFIDA ba saboda yanzu ba lokacin ziyara bane sujira har 5pm tayi, ganin zasu b’ata lokaci yasa Amira tace zasu tafi amma zasu dawo idan 5pm d’in tayi, munira bataso hakanba amma dole tasa suka juya suka wuce,,,,….
Wunin ranar gaba d’aya yinsa sukayi atsaye saida suka tabbatar dikwani abu na cike cike akan shari’ar sunyisa har lawyer sun d’auka Amira tabiya kud’i sunyi signing gobe 10am zai iso k’asar KEBBI domin fara bincike akan shari’ar, sai 6:30pm suka koma gida danhaka basusamu komawa gun MUFIDA ba, saida Amira tai sallar magrib sannan takoma masaukinta,,,”…
Washe gari tin 9am Amira tashirya taje ta d’auki munira suka wuce, kai tsaye office d’in lauyoyin suka wuce domin jiran isowar lauyanda suka d’auka,,,, 10:35am ya’iso wani abun mamakinda suka gani shine ashe lauyanda suka d’auka Rayyan ne abokin MUJAHID, ai saboda tsabar farinciki Amira da munira kasa magana sukai sai dariya kawai suka dingayi,,,….
Bayan yahuta sannan akamasu izini dasu shiga office d’insa, bayan sunshiga Rayyan yai murmushi sannan yace “ashe Allah yayi zamu sake ganin juna” Amira tai murmushi sannan suka gaisa sukamasa barka isowa lafiya, daga nan suka kara masa cikakken bayanin yanda case d’in yake, dikda wannan bashine farko agaresa ba dayai irin wannan case d’in amma abun daya kasance ga MUFIDA saiyai mamakinsa sosai,,,….
Bayan sungama komai sai yace yanaso suje yaga MUFIDA domin yamata waensu tambayoyi nan suka tashi suka wuce Court d’in,,,”….
Suna isa akai caking d’insu sannan akamasu umarni dasu shiga, zaune take akasa tai tagumi itakad’ai tana kallon sama, d’aya daga cikin masu tsarontane yashigo yace “kifito ankawo maki ziyara” jiki ba kwari tamik’e tsaye tafita, tana isa tahango Amira da sauri hadda d’an gudu taje tarungume Amira tana kuka itama Amiran kuka take saboda ganin yanda MUFIDA tadawo tamkar wacca batada gata wacca kuma batada kowa a duniya, kuka take sosai dakyar Amira ta rarrasheta tadaina kukan tadubi Amira tace “Amira kinga yanda duniya tajuyaman baya ko bayan auren dole yanzukuma ga kazafin kisan kai Amira bansan wane laifi nayiwa ubangiji ba yake jarabtana da waennan mugwayen kaddarori…” bata k’arasaba Amira tarufemata baki tana juyamata kai alamar tai shuru sannan tace “MUFIDA kidaina fad’ar haka dik abunda kikaga yasami bawa to *MUK’ADDARI* ne daga ubangijinsa, yanzudai mudaina wannan zancen wannan shine lauyanda muka d’auka wanda zai tsayamana jibi a gaban alkali” saita nuna Rayyan tasake cewa “sunansa barrister Rayyan Al-mustapha inafatar kin shaidasa”,,,….
Murmushi tai sannan tace “eh Rayyan abokin mr man” Amira tai murmushi sannan tace “eh shine lauyanda muka d’auka lauyane mai zaman kansa ba lauyan gomnati ne ba” kallonsa MUFIDA tai ta gaidasa ya karb’a sannan suka zauna suka fara tattaunawa yana mata tambayoyi tana bashi amsa,, saida suka gama sannan security d’in yazo yakoma da ita,,,….
Acikin kwanakin Rayyan yadinga bincike akan wannan case d’in a b’oye batareda momy tasaniba tindaga masu aikin gidan security’s gateman da dai sauran masu aikin gidan, acikin k’ank’anen lokaci yafara samun kwakkwarar shaidarda zai gaba tar a kotu,,”…
Saura kwana d’aya ashiga kotu Rayyan ya ziyarci gidansu MUFIDA, bayan anmasa iso ankawomasa ruwa sai momy tashigo tazauna suka gaisa sannan yagabatarmata kansa “hajiya sunana Barrister Rayyan Al-mustapha lawyer mai zaman kansa nine lauyan MUFIDA nazone nad’anyimaki wasu tambayoyi” tinda momy taji yace shine lauyan MUFIDA ta tamke fuska tasha kunu,,,…
Wani mirmushi Rayyan yai sannan yace “hajiya lokacinda MUFIDA tashigo harta kashe Alhj shin kina inane sannan dawa dawa ne acikin gidan?” juya fuskarta tai sannan tad’ora k’afarta d’aya kan d’aya tamasa wani kallo sannan tace “ni lokacin ina kitchen gidan kuma bakowa munira na school mubina kuma na office sai mustapha yana bacci masu aiki kuma dik suna ghost house” yan rubuce rubuce yai sannan yacigaba “ok to kince kina kitchen to ya akayi kikaga lokacinda takasheshi ko wanine yagani yazo yafad’a maki?” a,a lokacinda tashigo bangantaba amma lokacinda zata fita na ganta lokacin kuma zanshiga gun Alhj ne. “ok to ya akayi kikasan itace takasheshi dakanki kika kamata kokuwa ya akayi ne?” a,a bankamata ba amma lokacinda take fitowa naga jikinta dik alamun mara gaskiya bandai yarda da’ita ba sai kawai nashiga ciki koda nashiga kuwa sainagansa kwance akasa tacafkamasa wuk’a acik….i” saita fashe da kuka,,,…
Kyaleta yai saida tad’an tsagaita sannan yamik’a mata ruwa takarb’a tasha sannan yacigaba da “hajiya lokacinda kikaga tafito kinga alamar jini ajikinta ko zufa?” nankam shuru tai tafara rabon idanuwa sannan tace “a,a banga komai ajikinta ba” rubutu yai sannan yace “ok nagode sosai hajiya amma dan Allah inaso nacire CCTV cameras dake cikin parlon nan dakuma d’akin Alhj” dasauri tad’ago idanuwanta tana zarosu, sam brain d’inta baitab’a kawo mata tinani akan camera’s d’indake cikin gidanba amma badamuwa zansan yanda nai, yanayinda yaga tashiga hakan yak’ara bashi kwarin guiwa, badan tasoba tace “O….K…Ok toh” yai murmushi sannan yatashi yafita jim kad’an yadawo tareda masu cirarsu nan suka hau suka kwancesu suka bashi sannan yayiwa momy godiya yawuce,,”…
Aiki yake tukuru har kusan 2am yana binciken camera’s d’in shiga da ficenda akai aranar, hankalinsa yad’auke yana kan aikinda yake kamar ance ya waiga saiyaga wani mutum yawurga ta k’ofar parlor, tashi yai yaje yad’auki wuk’a yafara tafiya ahankali sadaf sadaf domin,,,….
Har ya’isa cikin parlon baiga kowaba nan yafara dube dube har yabud’e k’ofar fita baiga kowaba yafita yadudduba ko’ina har bayan gidan amma baiga kowaba saiyadawo ciki yarufe k’ofar yakoma d’akinsa,,,….
Koda yazauna yajanyo laptop d’insa domin cigaba da aikinsa saiyaga anmasa delete all komai ya goge har abunda yad’akko acikin camera’s d’in gidansu MUFIDA, mamakine yakamasa nan yacigaba da bincike amma haryagama baiga komai yadawoba tabbas yagoge nan ya tabbatar da wanine yashigo yad’auki hankalinsa “ohhh….shet!!!” yafad’a tareda kaiwa iska naushi cikin takaici da b’acin rai………..
Wayarsa ya d’akko yai dialing number na Amira cikin saa kuwa tadaga kasancewar itama takasa bacci sai nafiloli take tana kaiwa Allah kukansu daya taimakeso yatonu asirin dik wanda ya aikata wannan laifin kuma yacuci MUFIDA yasaka acikin wannan sarkar mai wahalar kwancewa,,,…+
Tana dagawa batareda yamata ko sallama ba saboda yanda ransa yabaci yafara magana “Amira wallahi komai yajagule yanzu aka shigoman gida aka dauki hankalina naje naduba wanda yashigo koda nadawo saina tadda dik evidence d’inda nahad’a tin shekaranjiya izuwa yau komai angoge” Subhanallah. Amira tafad’a tai shuu tana jinjina wannan al’amarin can tace “tabbas dik wanda ya’aikata wannan abun olready dama bibiyarka yake saboda haka yanzu dole kakiyaye kanka” hmm….!!! yasauke numfashi sannan yace “tabbas hakane amma idan sunsan wata ai basusan wataba insha Allah bazan kwanta harsaina samu evidence d’inda zan gabatar gobe a kotu” murmushin jin dad’i Amira tai sannan tace “to Allah yabaka nasara ya taimakeki muma insha Allah bazamuyi bacci ba munanan muna kaiwa Allah kukanmu itama MUFIDA nakaimata Qur’an da sallaya tanacan tanayi” nandai suka gama sannan sukai sallama,,,….
Daren ranar gaba d’aya suduka hud’un, MUFIDA, Amira, munira dakuma Rayyan ba wanda yai bacci, acikin daren Rayyan yaje gidan marigayi Faruk sannan yaje station d’inda suka karb’i case d’in, saida ya tabbatar yahad’a kwararrun evidence sannan yakwanta lokacin kuma yai dai dai da 5am,,,….
Washe gari tin 8am Amira da munira suka zo Court gun MUFIDA suka kwantar mata da hankali akan karta d’imauce ta kwantarda hankalinta dik abunda aka tambayeta tabada amsarsa dai dai yanda tasani karta kuskura tafad’i abunda batasaniba saboda lauyan gomnati kwararre ne sosai zai iya rikitata har tafad’i abunda bashibane daga baya kuma abun yarikice saboda haka ta kwantarda hankalinta Barrister Rayyan zaiji da komai, saida ta sallar nafila raka’a biyu sannan suka fito suka barta,,”…
9:30am Barrister Rayyan yak’araso nan sukaje gunsa suna tattaunawa, su momy ma sun iso mubina ji take kamar ta daki munira saboda haushinta datakeji wato ita tafisan wannan *TSINTACCIYAR MAGE* akan mahaifinta, momy tace barni da’ita kawai mubina maganinta zanyi wallahi,,,”….
10am dot mai Shari’a yaiso akashiga, lauyoyi suka fara gabatarda kansu lauyan gomnati yafara “am ni sunana Barrister Sadiq Abubakar lauyan gomnati” bayan yagama Rayyan shima yamik’e tsaye yace “nikuma sunana Barrister Rayyan Al-mustapha lauya mai zaman kansa nine nake kare wacca ake tuhuma” yagama saiya zauna,, wani nan nakusa da mai shari’a yamik’e rike da wata takarda yafara karantata kamar haka “A yaune zamu cigaba da sauraran kararda ake shari’a akanta ta MUFIDA Ahmad Shitu wacca ake tuhuma akan takashe mahaifinta dakuma mijinta wanda wannan shine zama na biyu zai kuma dauke mu tsawon awa biyu kacal” yana kawowa nan yajuya yamikawa mai shari’a takardar sannan yakoma ya zauna,,,….
Bayan wasu y’an dak’ik’u sai mai shari’a yad’ago yace “lauyoyi zaku iya fara gabatarda shaidun ku” lauyan gomnati yamik’e yace “ya mai shari’a inaso kotu tabani dama nai waensu tambayoyi ga wacca ake tuhuma wato MUFIDA” sai mai shari’a yad’ago yace “kotu tabaka dama Barrister” olready dama tana nan tsaye an iso da’ita saiyamatsa kusa da’ita yakalleta sannan yafara mata tambaya kamar haka “MUFIDA meyasa kika kashe mahaifinki da mijinki da mijinki? Miye dalilinki nayin hakan? Ko dai wanine yasakaki aikata hakan? Kud’i yabaki? Ko akaran kanki kika kashesu domin ki mallake dukiyarsu kotu tana sauraronki” dasauri Rayyan yamik’e tsaye taredafadin “objection mai Lord yakamata Barrister yasan yanda zai rik’a jefawa wacca ake tuhuma tambaya saboda idan yai duba da wannan shine karo na farko da tafara zuwa kotu sannan yanayinda yake mata tambayar kamar yanasone tafad’i cewa eh itace takashesu bayan kuma tuhumarta yake bashida tabbacin itace ta aikata ko ba itace ta aikataba inafatar za’adubi k’orafina my lord”,,…
STORY CONTINUES BELOW
Daga momy har mubina ji sukai kamar suzo su shake Rayyan yamutu, hakama Barrister sadiq, su Amira kuwa wani sanyi suka faraji a ransu,,,….
Mai shari’a yadubi Barrister sadiq yace “barrister a kiyaye” yace “ok my lord za’akiyaye nagode” sannan yacigaba “MUFIDA kotu tana sauraronki” basmala tai sannan tafara magana “ni dai banice nakashesuba sannan bawanda yasakani koya bani kud’i abunda nasani dai wallahi banice nakashesuba” murmushi yai sannan yace “MUFIDA wannan kalmar itace kiketa fada amma taya kike tinanin zaki rainamana hankali mu yarda da hakan bayan kuma dubbannin mutane sunkamaki dumu dumu rik’e da wuka a hanunki lokacinda kika kashe faruk sannan dika dika tazarardake tsakanin kisan Alhj Ahmad da faruk batafi 30mnts ba sannan kuma lokacinda kika kashe Alhj kika fito uwargidansa taganki fitarki dakusan 5mnts tashiga koda tashiga ta tadda kinkasheshi” saida ta sauke numfashi sannan tace “bazan daina cewa ni banice nakashesuba, eh tabbas anganni rik’e da wuk’a saidai tinaninda sukai bahaka yakeba, dama akwai sab’ani tsakanina da faruk saboda koda akamana aure bana sonsa bashine zab’inaba kawai nayi biyayyane na auresa, tsanarsa takarda ruruwa acikin zuciyata tin lokacinda nasan shi mashayi giya ne kuma manemi mata ma’ana mazinaci, dikda haka nai biyayya nai auresa, nayi nayi yadaina shan giya amma yaki, nacigaba da zama dashi kwatsam kuma wata rana saina taddashi yai raping d’in ‘yar aikina harira,, da’abun yafaru yayi nadama sosai har fushinda iyayenmu sukai akansa yasauka danhaka akace nayi hakuri nakoma gidansa”,,,….
Kwallanda suka zubomatane ta tsaya ta share sannan tacigaba,,”…
Bayan nakoma da kwana d’aya kacal kuma nadawo daga gun aiki saina taddasa shi da abokanansa Suhail da Nazir acikin parlor sunyi tatil da giya sai wari suke, raina yabaci sosai sai kawai najuya naje gida nafadawa dady na, a maimakon yad’auki mataki saiyace naje nai hakuri kowacce mace da tata kaddara rayuwa ni tawace ahaka amma naje gashinan yanzu zaizo, badan nasoba haka nafito, to lokacinda nafitone raina a bace saina hadu da momy zatashiga d’akinsa kasancewar raina yana a bace yasa bantsayaba nawuce,,,….
Koda naje gida saina tadda faruk kwance akasa ancaka masa wuk’a aciki, tsintsar tashin hankali yasa narasa yanda zanyi cikin bacewar dabara saina saka hanuna nacire wukar” saita dago kwallah nazuba daga idanuwanta takallesa tace “to kaji iya abunda nasani” murmushi yai sannan yace “to munji wato kinaso kice koda kika auri faruk nakyasonsa kenan wannan dalilinne yasa kika kashesa saboda kije ki auri wanda kikeso” Rayyan yamik’e tsaye dasauri yace “my Lord inason nayi tambayoyi ga MUFIDA inafatar kotu zata bani dama” sai mai shari’a yace “Barrister Rayyan kajira har Barrister sadiq yagama nasa tambayoyin” sai Barrister sadiq yace “nagama my lord zai iyayin nasa” saiya dawo ya zauna,,,….
Matsawa Rayyan yai kusa da’ita yakalleta yace “malama MUFIDA kince koda kika shigon gidan faruk shi da abokanansa kika iske to amma koda kika dawo kika taddasa ankashesa shine kintaddasu abokanansa kokuma shi kadai kika tadda” a,a koda nadawo shi kad’ai na tadda su bangansuba. “ok to ina sukaje kuma bakya tinanin anya basune suka kashe faruk ba” eh to hakan zata iya faruwa saboda gaskiya ba mutanen kirki bane dansunma taba yin fada har Suhail ya yankawa faruk wuk’a a hanu. “Good” Rayyan yafada sannan yajuyo yace “my lord ina rokon kotu ta daga wannan shari’a izuwa wani lokaci sannan tasaka akamo suhail da nazir domin su amsawa kotu tambayoyinda take dauke dasu agaresu, daga wannan karar kuma zai bamu damar sake samo kwararan hujjojinda zamu gabatar agabanta inafatar za’a karb’i k’orafina” yana gamawa yakoma ya zauna,,,…
Shuru yaratsa kotun natsawon wasu yan mintina, can mai shari’a yadago yace “andage wannan shari’a har izuwa 2 ga watan apirilu sannan laiyoyi suyi kara kwazo domin samun kwararan hujjojin” yana fadar haka yatashi kowa yamik’e sannan yafita,,,….
Wani irin dad’i was Amira taji hakama munira ganin nasara tafara tinkarosu, tasowa sukai suka rungume MUFIDA suna dariya itama tana dariya sannan Rayyan yazo, kallonsa MUFIDA tai tace “Rayyan banida abunda zan sakamaka dashi Allah yabiyaka da mafificin alkhairi yacikamaka burikinka na alkhairi yasa kagama da duniya lafiya” murmushi yai yace “ameen MUFIDA karki damu Allah dai yabamu saa yasa muyi galaba akan wannan shari’a” suka amsa da ameen munira tace “nasara tafara tinkaromu insha Allah komai yakusa zuwa karshe” Rayyan yace “yanzu zaaje neman su suhail sannan zanje na karb’o wuk’arda akai kisan da’ita sannan kuma sainayi scanning na hannayen dik wani wanda ke cikin gidan dady da faruk saboda hakan ne zai sauk’ak’amana wajen gano wanda ya’aikata kisan” murmushi sukai suduka sannan sukace “Allah yataimakeka yabaka nasara yakuma kareka” yace ameen sannan yawuce security’s sukazo suka wuce da MUFIDA ciki sukuma su munira suka wuce,,,”….
STORY CONTINUES BELOW
               *****  *****
Ahalin yanzu komai yai zafi bincike ake sosai, tini Rayyan ya karb’o wuk’ak’enda akai kisan dasu kuma yasaka anyi scanning hanun dik wani dake cikin gidan dady da faruk saidai har aka gama ba’asamu wanda hanunsa yai dai dai tambarin hanun wanda yai kisanba daga baya ma koda Rayyan yakula ashe waennan wuk’ak’en an sauya su ba ainihin sune akai kisan dasuba, murmushi kawai baice komaiba,,”….
Tini aka kamo Suhail da Nazir nan aka dinga gana masu azaba fiye da wacca akayiwa MUFIDA domin su sufadi gaskiya amma sukaki,saida sukaci wuya sannan Nazir yace  “wallahi basu bane suma sunfita su siyo masu abinci koda suka dawo saisuka taddasa ancaka masa wuk’a a ciki tsoron kar a zargesu yasa suka gudu amma akwai wacca suke zargi” jin haka yasa Rayyan yacemasu “matukar kuka fadaman gaskiya za’akyaleku bazaa maku komaiba amma idan kukai hmm kunsan karshen” sunsan irin azabarda aka masu danhaka nantake Nazir yace matso nafada maka sai Rayyan yamatsa dab dashi shikuma yaduko dai dai kunnensa yafada masa,, wani irin murmushi Rayyan yai sannan yacemasu “nanda anjima za’a sakeku amma idan inaneman wani abu zan kiraku” sukace toh sannan yafita,,,”….
Yana cikin bincike a gidan faruk saiyaga tsinin takalmi na mace yana d’auke da jini a jikinsa, daukansa yai yaduba sannan yasakasa acikin leda yafita,,,….
Yana fita yakira Amira yace su had’u yanzu kuma tazo tareda munira tace toh sannan yakashe wayar, kimanin 30mnts kuwa saigasu sun iso a gidansa nan yaciro tsinin takalmin yanuna masu sannan yace “nasami wannan ne a gidan faruk munira wakika sani acikin gidanku da irin takalmannan” tana dubasa ta tina tace “wallahi na mubina ne naga takalmanta d’aya tsininsa yacire dana tambayeta saitace musty ne yamata b’arnan” murmushi Rayyan yai sannan yace “wannan shari’a tana gab da kai karshe wannan shine evidence na biyu dana samu akan mubina na uku nake jira sannan nasaka akamata” munira tace “kenan akwai hanun mubina acikin aikata wannan kisan” Rayyan yace “bama da hanunta ba itace ta aikata saidai banida tabbacin dika kisan biyu itace ta aikatasu sai idan munkamata zamusan hakan” hmm….!!! Amira ta sauke nannauyan numfashi tateda fad’in “Allah i kyauta” suka ce ameen sannan suka tashi suka wuce,,,”….
                ******  *****
Yau saura kwana biyu kacal akoma kotu danhaka yanzu kullum Rayyan acikin aiki yake ba zama ba tsayi, Amira kuwa dabino ta siya da Qur’anai masu yawa ta bada a masallatai domin amasu addu’ah sannan suma kullum cikin yinta suke ba dare ba rana,,,….
Around 2am zaune yake acikin parlonsa yana aiki da system d’insa, kamar motsin mutum yaji saiya share yacigaba da aikinsa,, can kuma saiya sake jin motsi saiya tashi yasakawa laptop d’insa password tayanda bayanda za’a iya bud’eta amasa b’arna sai yatashi yabarta yashige bedroom d’insa,,”….
Kamar 15mnts haka saiya fito yana fitowa kuwa saiyaga mutum tsaye yad’auki laptop d’in yanata k’ok’arin yabud’eta, dasauri yadamk’o wuyansa yajuyosa yanunasa da bindiga, fuskarsa a rufe take da bak’in abu sai yace “bud’e fuskarka” k’in bud’e fuskar yai saiya fara matsowa danufin yafara kokuwa da Rayyan sai kawai Rayyan yaharbesa a k’afa aibashiri yazube k’asa yarik’e k’afar yana ihu nan shikuma yazo yabud’e fuskar,,,….
Kujera ya janyo yakamasa ya yazaunar akanta sannan ya d’akko igiya ya d’auresa, bayan yad’auresa sannan yace “waye kai? Waya aikoka?” shuru yai yana ihu yaki yin magana nan Rayyan yadaga bindigar yace “zaka fad’a ko saina sake harbe k’afar ne” da sauri yace “hajiya Fatima ce uwar gidan Alhj Ahmad shitu da dan Allah kabarni natafi karka illatani” wani murmushi Rayyan yai sannan yad’auki wayarsa yakira police cikin y’an dak’ik’u sukazo suka d’aukesa suka wuce dashi,, wani irin farinciki Rayyan yaji saboda yaga yakusa cin nasara dakuma kai karshen wannan case d’in,,”….
Washe gari koda yaje police sun cicci uban yaron yasha duka da bakar azaba nan yaita fad’awa Rayyan dik irin tuggu da makircinda momy kesakasu sunayi ciki hadda suje sushiga kotu su kashe MUFIDA bayan sun kasheshi shi rayyan, dik abunda yaron ke fad’a Rayyan recording nasa har yagama sannan yace sudaina azabtardashi yawuce,,,”….
STORY CONTINUES BELOW
                  ********
2/4/2019~ 9am dot
Tin cikin daren ranar ake ana raya masallatai da karatun Qur’an domin neman samun nasara dacin galaba akan wannan shari’a, hakama MUFIDA da Amira da munira kwana sukai suna karatun Qur’an suna kaiwa Allah kukansu kuma Alhmdllh dan sunji acikin zukatansu insha Allah zasuyi nasara dan tinda safiya tawaye MUFIDA takejin kanta acikin yanayi mai dad’i,,,…
9:30am kowa ya hallara amma banda su momy harsu hajiya da Abbu da Abban ammar dik sunzo amma momy da mubina basuzoba, hakan baisa su MUFIDA sunyi mamakiba shi Rayyan dama yayi tinanin bazasu zo ba dansunsami labarin yakama yaronsu,,,”….
10am dot akashiga kotu mai shari’a ya’iso, bayan lauyoyi sun gabatarda kansu sai aka fara sauraron karar, mai shari’a yadago yace “lauyoyi zaku iya fara gabatarda shaidinku” nan Barrister Sadiq yai saurin mik’ewa tsaye yace “my lord inaso zanyi waensu tambayoyi ga wacca nake tuhuma wato MUFIDA inafatar kotu zata bani dama” mai shari’a yace “kotu tabaka dama barrister” nan yamatsa kusa da MUFIDA yakalleta yace “malama MUFIDA kince bake kika kashe Alhj Ahmad da Faruk ba amma a bincikenmu damukai a na’urorindake gidan Alhj da faruk wato CCTV camera’s dinsu nuna kece kika kashesu sannan tambarin hanunda ke akan wuk’arda akai kisan da’ita tambarin hanunki ne saboda haka kidaina wahalarda shari’a ki karb’i laifinki saboda tabbas kece kika aikatasa” cikin nutsuwa MUFIDA tace “wannan wallahi dik karyane ba gaskiya bane ni bani nakashesuba saboda haka bazan taba amsar laifinda bani na aikatasaba” dole ki karb’esa MUFIDA saboda kekika aikatasa. Barrister yafad’a dak’arfi tareda dukan kan table d’inda take tsaye harsaida ta tsorata,,,….
Dasauri Rayyan yamik’e tsaye tareda fad’in “objection my lord yakamata barrister yasan yanda zai rik’a yin tambayoyinsa saboda yana nemane ya tirsasa wacca ake tuhuma data karb’i laifinda ba’itace ta aikatasa ba” mai shari’a yad’ago yace “barrister kasauya salon tambayarka” sai yace “zan sauya my lord” sannan yacigaba “MUFIDA kin dad’e kina takon yanda zaki kashe Alhj Ahmad munsan hakan ne ta tambayoyinda mukayiwa ma’aikatan gidan, saude d’aya daga cikin masu girki ce kin bata wani k’ullin magani kikace tasaka acikin girkin Alhj tace maki to bayan kin wuce taki sakawa tad’auki maganin ta b’oye yanzu da wannan abun yafaru saita fidda ta bamu gama maganin aduba” saiya je yakai gun mai shari’a sannan yace “ya mai shari’a ina fatar kotu zata dubi waennan kwararan hujjojin nawa domin ta hukunta MUFIDA dai dai dai da laifinda ta aikata” yana maganar yamik’awa mai shari’a laptop d’insa wacca ke d’auke da videon lokacinda MUFIDA taje tai kisan sannan yaje yazauna,,,”…
Yana zaunawa Rayyan yamik’e yagyara sannan yace “my lord inaso kotu tabani damar gabatarda kwararan hujjojina agaban kotu” sai mai shari’a yace “kotu tabaka dama barrister” nan yajuya yace “inason Nazir usman da Suhail Manir da Aryan Abdul-k’adir sufito agaban kotu” wani dagacikin waenda ke kusa da mai shari’a yamik’e yace “kotu nabuk’atar ganin Nazir da Suhail da Aryan su bayyana agaban kotu idan sunanan” nan suka taso suka fito nan yataso yazo ya rantsardasu sukai rantsuwa akan zasu fadi gaskiyar abunda suka sani sannan yakoma ya zauna nan Rayyan yamatso kusa dasu domin fara masu tambayoyi,,,….
Murmushi yai sannan yace “Nazir da suhail bara nafara daku, dafarko da kufadawa kotu alak’ardake tsakaninku da marigayi faruk” Nazir ne yace “mu abokanansa ne tin muna secondary School” Rayyan yace “good” sannan yacigaba “lokacinda MUFIDA tashigo ta taddaku taredashi acikin parlor kunashan giya saita fita amma koda tadawo sai bata gankuba shi kad’ai ta tadda ankashesa shin koda aka kashesa ku kuna inane kokune dai kuka kashesa kuka kugu” dasauri suhail yace “wallahi a,a bamu bane abunda yasa tadawo bata ganmuba munfitane musiyo abinci waje koda muka dawo sai muka taddasa ancaka masa wuk’a a ciki tsoron kada a zargemu yasa muka gudu saidai lokacinda zamu gudu munga mubina zata fita mun dauka taganmu kartayi zaton mune muka kashesa sai muka gudu amma wallahi bamu bane muka kashesa” murmushi Rayyan yai sannan yajuyo kan Aryan yace “nadawo kanka Aryan, kwanan baya ankaimin hari a gidana danaji motsin mutum nafita domin duba waye banga kowaba bayan nadawo saina tadda komai na cikin laptop dina dik evidence d’inda na hada angoge amun delete all, shekaranjiya kuma ina zaune parlor ina aiki sainaji motsi sainabar laptop dina a kunne nashiga bedroom dina, kimanin 15mnts nafito saina taddaka kana kokarin bude laptop d’in shin waya turoka waya sakaka?” dagowa yai sanna yace “bawanda yasakani nine nasaka kaina” murmushi Rayyan yai sannan yace “my lord bayan nakamasa saina kira police nadamk’asa hanunsu, washe gari bayan naje nakemasa tambayoyi sai yake fad’aman hajiya fatima uwar gidan marigayi Alhj Ahmad shitu itace tasakasa yaje yakasheni bayan yakasheni kuma yaje yakashe MUFIDA wacca ake tuhuma ga recording d’in firarda nai dashi” saiyamik’awa mai shari’a sannan yacigaba,,,….
Acigaba da bincikenda nake ne nasamu tsinin takalmi wanda kuma nake tinanin dik wacca tai wannan kisan natane saikuma tinanin yakusa zama gaskiya lokacinda su nazir sukace sunga mubina zata fita tana sauri gefen kayanta dake jikinta dik jinine, sannan Aryan dana kama acikin tambayoyinda namasa yafad’a man cewa hajiya fatima wannan bashine karo na farko datake sakasu suna mata aiki ba ko tasaka sukashe mutum kokuma suyi kidnapping nasa sai anbasu kud’i masu tarin yawa, sunce su suka kashe hajiya ummu Anwar kawarta wacca suke business atare saboda tahanamata kudinta take binta bashi sannan tadad’e dasakasu su kashe MUFIDA Allah ne dai baiyi kwananta sun kare bane amma har makarantarsu sun bita amma basusami aikata abunda aka sakasuba, a takaice dai wannan shine aikinta,,, sannan bayan an goge man shaidunda nahad’a acikin system dina nasake samun wani kwararran shaida ta wata ‘yar k’aramar camera dake b’oye acikin  parlon gidan marigayi faruk wacca suka kunna suka barta tana recording batareda sunsaniba kasancewar basa cikin hayyacinsu, wanda yai kisan ya bayyana acikin ‘yar karamar camera d’in kuma mace ce saidai fuskarta bata bayyana ba sosai amma kayan dake jikinta sun bayyana”,,….
Dikda fuskarta bata bayyana ba amma hakan baihana muka gane ko wacece ba ta kayandake jikinta, wannan bakowa bace face MUBINA ‘ya ga marigayi Alhj Ahmad Shitu, wannan sune kayanda tasaka lokacinda ta’aikata kisan gasunan ko jinin ba’awankeba” yamik’awa mai shari’a sannan yacigaba,,,….
Wannan shaidar itace zata taimaka mana wajen gano wanda yai kisan Alhj Ahmad Shitu kuma ina fatar wannan kotu mai albarka mai adalci zata dubi waennan kwararan shaidun ta yankewa wanda yai laifi hukunci dai dai da laifinsa sannan tawanke wacca ake tuhuma domin ba’itace ta aikata ba nagode my lord” yana gamawa yakoma ya zauna,,,,….
Kimanin 30mnts mai shari’a na duba hujjojin wajen kuma sai magana ake kasa kasa daji kasan dai akan hujjojinda Rayyan yabadane, bayan mai shari’a yagama duba evidence d’in saiya dago yace “kotu tana buk’atar ganin Mubina Ahmad shitu da hjy fatima” nan d’aya daga cikin ma’aikan kotu yamik’e tsaye yace “idan hjy fatima da mubina suna kusa su fito kotu na buk’atar ganinsu” nan akace dik basunan,,,….
Yan rubude rubuce mai shari’a yai sannan yadago yace “zamu dage wannan zaman izuwa nanda 3hours sannan kotu tayi umarni da’aje anemo hjy fatima da mubina dik inda suke kamin adawo acigaba da zama” yana gama fadar haka yatashi yafita,,”….
Farinciki da jin dadi agunsu Amira ba’amagana suka rungume juna suna farinciki, security’s ne sukazo suka wuce da MUFIDA, suna fitowa kuwa ga yan jarida sukamasu caaaa da tambayoyi saima suka rasa wanda zasu amsawa saboda farinciki Amira tace “kudakata yanzu dai ba’ayanke hukunciba kujira har  a yanke munmaku alkawarin zamu amsa maku tambayoyinku amma ba yanzuba” tana gama fadar haka saisuka wuce……………

About AIS

Check Also

TSINTACCIYA CHAPTER 4 BY NIMCY LUV

TSINTACCIYA CHAPTER 4 BY NIMCY LUV Www.bankinhausanovels.com.ng  Ƙamshin haɗaɗɗan turarensa ne ya daki hancinta wanda …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *