TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 3 BY AUFANA

TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 3 BY AUFANA

Ganin MUJAHID tareda Rayyan suna k’ok’arin fitowa a cikin dalleliyar motarsu yasa suka gane cewa su d’inne take kallo,, dasauri Nusy tarik’ota suka zauna cikin b’acin rai da masifa tace “haba feedom mekikeyi hakane so kike kibamu kunya ne”  shuru tai takafe idanuwanta gu d’aya sai kawai sukaga kwallah sunfara zubomata daga idanu,,,….+

Mamakine har yanzu cike fam a zuviyoyinsu dakuma tarin tambayoyi ga MUFIDA, ahankali tad’ago ta kallesu sannan tace “friend’s ina cikin matsala ina cikin damuwa” subhanallah feedom  meke faruwa dake ne…?? Nusy ta tambayeta,,,….

Shuru tai can kuma tafara magana kwallah nabin kuncenta “ina cikin matsala friend’s abunda Amira tafad’a naga laifinta hadda fushi nai da’ita yau yazama gaskiya ya tabbata akaina” murmushi Amira tai saboda tini tagano kwanan zancen takuma fahimci inda yadosa, “mekenan feedom?” sake kallo nusy tai tace “Nusaiba zuciyata ta tsunduma tsundum acikin kogin k’aunar MUJAHID bansan ya akayi hakan tafaruba wallahi bansaniba” tak’arasa cikin fashewa da kuka, dasauri nusy tajanyota ta rungume tana rarrashinta,,,….

Shuru yad’an ratsa wurin sai she she kar kukan MUFIDA kake jiyowa kasancewar wurin kowa sha’anin gabansa yake yasa basuwani damuba, Amira ce tace “tin farko dakuka fara wannan rigimar naji a zuciyana akwai wani abu dazai shiga a tsakaninku shiyasa namaki magana akan ki sausauta tsana dakuma irin tarin rigimarda kika shirya kiyi da shi saboda irin haka tasha faruwa daga k’arshe saikiga ankoma dana sani” Nusy tace “yanzudai dik abar wannan zancen mufara neman mafita akan matsalarda take shirin fuskantomu”  wani irin murmushi Amira tai batareda tasake cewa komaiba saidai dagani kasan akwai magana acikin bakinta tadaiyi shuru ne kawai,,,…..

Yaukam basu wani jimaba suka wuce 5pm tawuce gida saboda rashin jin dad’in jikinta datake ga wani a zababben zazzab’i datakeji,,,….

               *****  *****

Kwance yake akan gadonsa yad’aga kansa sama hanunsa d’aya akan kansa, yalula sosai yai zurfi acikin duniyar tinani idanuwansa sunyi jajir saboda tsananin zazzab’inda yakeji, Rayyan ne yashigo tareda mubashir dakuma wani doctor Ayman,,,….

Suna shigowa suka zauna MUJAHID yagaisa da doctor sannan likitan yafara duba lafiyarsa,, bayan y’an gwaje gwajenda yamasa sannan yahad’a injection yamasa yakuma doramasa drip saboda yalura yanada buk’atar su,,….

Saida yagama komai sannan yazauna yadubi su Rayyan yafara magana “am to nayimasa gwaje gwaje sosai bawata cuta dake damunsa kawai yawan damuwa da yawan tinani dakuma yawan zama acikin kad’aici shine yamasa yawa yakekuma nema ya haddasa masa hypotention yanzu hakama jininsa yahau yakai 70% shiyasa ma namasa wannan injection d’in saboda jinin yasauka yakoma normal but idanfa bai rage yawan damuwa da tinani ba jinin zai sake hawa zai kuma iya fin hawanda yai yanzu idan kuma hakan tafaru tofa komai zai iya faruwa wallahi saboda haka dole a kiyaye” shuru sukai suka rasa mema zasuce dakyar Rayyan yace,,,….

“Ok Thanks doctor insha Allah za’akiyaye mungode sosai” nan yahad’a kayansa yafita mubashir yabisa domin masa rakiya,, juyo da kallonsa izuwa ga MUJAHID rayyan yai cikin b’acin rai yace “kaga abunda kake nema ka janyowa kanka ko to wallahi idan baka daina wannan damuwar ba Allah saina kira mai martaba nafad’amasa” murmushi yai sannan yajuya fuskarsa yace “hmm rayyan kenan wallahi dan bakasan irin yanda nakeji acikin zuciyata bane shiyasa kake wannan maganar”  murmushin gefen lebe rayyan yai saboda shifa tini yagano damuwar MUJAHID acikin zuciyarsa kuwa tsintsar farinciki ne fall saboda tini yadad’e dayiwa MUJAHID sha’awar auren MUFIDA saboda sunmatuk’ar dacewa da juna to yanzu tinda abunda yake rok’o yatabbata wato MUJAHID yatsunduma a k’aunar MUFIDA dole yayi iya yinsa domin ganin yahad’a su fatansa Allah yataimaka masa yashawo kan abun cikin sauk’i har Allah yasa aure yashiga a tsakaninsu,,,…..

Saida mubashir yadawo sannan rayyan yadawo daga tinaninda yake,, bayan drip d’in yak’are aka cire sai suka had’amasa ruwan d’umi yai wanka yai sallah sannan yashirya sai rayyan yace yazo sufita domin yad’an mik’a kafa saboda yarage tinani, haka kuwa akayi bayan yasaka kaya sannan suka fita,,,….

                *****  *****

Yau kimanin kwana biyu kenan MUFIDA bataje school ba hakan yasa tai missing exam’s biyu, saidai su Nusy sunyi matuk’ar mamakin abunda yasa MUFIDA batazo school ba dasuka tambayi munira saita fad’amasu batada lafiya ne,,,….

Bayan sungama exam saisuka shirya suka nufi gidansu MUFIDA, koda suka isa tana cikin d’aki a kwance itakad’ai, dasauri Amira tahau kan gadon tad’agota tana tambayar abunda ke damunta, mamakine ya bayyana a fuskarta ganin wata iriyar muguwar rama da tai a y’an kwana biyunnan,,,….

Subhanallah Amira tafad’a “MUFIDA meke damunkine haka kwana biyu kikai wannan muguwar rama” bataiya cemata komaiba sai kwallah datake zubarwa daga idanuwanta masu zafin gaske, cikin tsintsar tausayi tazaunar da’ita koda tabud’e cikinta yayi tamkar babu ciki a jikinta da’alamu yunwace takeji dasauri tace “nusaiba je kitchen kihad’o mata tea mai zafi yanzi yanzinnan” nusaiba tace toh tafita da sauri,,,….

Cikin y’an mintina nusaiba tahad’o tea d’in takawo nan Amira tad’aga ta tabata, dasauri takarb’a tafara sha dikda zafinsa amma haka taita shansa saida ta shanye gaba d’aya sannan tasauke nannauyan ajiyan zuciya tareda lumshe idanuwanta,, can kamar 5mnts saita tayunk’ura gefe d’aya kan gadon nantafara shek’a aman jini, tsoro yakama su Amira sosai dasauri Amira tarik’ata taita shek’a aman jinin saida tagama sannan takamata suka wuce toilet,,,….

Wanke mata jikinta tai tabata ruwa ta kuskure bakinta sannan tarik’ota suka dawo d’akin, koda suka dawo har nusaiba tacire wannan bedsheet d’in tasaka wani, kwantar da’ita tai sannan tabud’e wardrobe tad’akko mata wata doguwar riga ta taimaka mata tacire wacca ke jikinta sannan tasaka wannan d’in,,,…..

Zama tai kusa da’ita nusaiba kuma na a gefensu tarik’o hanunta d’aya cikin kulawa tace “MUFIDA waimeke damunkine….?” Amira ta tambayeta, shuru tai dakyar tabud’e bakinta tace “tin shekaranjiya damuka rabu daku a school bansake yin lafiya ba dama koda naje banajin dad’i bayan nadawo ne abun yakaru” shuru sukai bawanda yasake cewa komai,,,….

Can sai Amira tace “MUFIDA kodai har yanzu baki cire MUJAHID a rankibane?”  kwallah ne sukaga sunfara gangaromata sai kawai tafashe da matsanancin kuka, bata hanataba ta kyaleta saida tai mai isarta, ahankali tafara magana cikin muryar kuka “wallahi Friend’s inacikin mawuyacin hali inacikin Matsananciyar damuwa son MUJAHID nanema yazameman baraza a rayuwata nayi iya yina amma nakasa ciresa a zuciyata sonsa saima dad’a k’aruwa yake a zuciyata nakasa ciresa yafi k’arfina” tana kawowa nan tasake fashewa da sabon kukan,,….

Wani irin tausayinta ne sukaji yakamasu nusy kasa jurewa tai har saida tazubda kwallah, Amira ce tace “hak’ika nasan irin halinda kike ciki MUFIDA nasan irin rad’ad’inda kikeji saboda nima natab’a tsintar kaina acikin irin halinda kike ciki a yanzu shiyasa tin farko nafara tsoron irin wasanda kuke a tsakanink….” amanda MUFIDA tafarayi ne yakatse maganarda take,,,….

Dasauri tarik’ata takamata suka wuce toilet, abun kamar wasa sai cigaba yake aman jinin ne yanzuma take tintanayi da k’arfinta hartafara gajiyawa can kawai saita zube a jikin Amira somammiya……….Tsintsar tashin hankaline yak’ara  bayyana a fuskar Amira, dasauri takwallawa Nusy kira a rikice tazo, tana ganin irin halinda MUFIDA take ciki hankalinta yak’ara tashi,,,….+

Cikin sauri Amira tace “nusaiba wannan abun yayi zafi sosai mud’auketa mukaita asibiti kar tasamu matsala” toh nusy tace fuskarta cike da tsintsar tashin hankali,,,….

Cikin sauri suka d’auketa suka saka a motar nusy nan suka wuce a wata private hospital dake kusa dasu,, dazuwansu kuwa ana ganin irin halinda take ciki akai saurin karb’an ta domin bata taimakon gaugawa, I.C.U aka wuce da’ita kai tsaye, cikin gaugawa suka fara taimakamata domin dawo da numfashinta, tajima sosai kan numfashinta yadawo sannan suka sakamata oxygen domin taimaka mata wajen cigaba da numfashi da kyau bayan sunsakamata oxygen suka had’a wasu injection suka mata tareda d’ora mata drip a hanu d’aya d’ayan kuma jini saboda tazubarda jini sosai lokacinda take amai,,….

Acikin drip d’in ma saida suka saka wasu medicine’s aciki waenda zasu taimaka mata domin tasamu k’arfin jikinta,, ….

Tinda aka shiga da’ita d’akin Amira takira munira a waya tashaidamata halinda MUFIDA take ciki hakama mubina takirata ta fad’a mata amma saitai kamar bata damuba tad’aga kafad’a irin ko’ajikinta dinnan,, munira kuwa suna gama exam bako tsattsayawa tahawo taxi tazo hospital d’in, ganin dak’in da akace MUFIDA take ciki dakuma ganin yanayin fuskokinsu Amira yasa hankalinta yak’ara tashi saita fashe da kuka saida Amira tajanyota jikinta ta rungume tana rarrashinta,,,….

Saikusan 4pm sannan akamasu izinin suganta koda suka shiga kuwa har yanzu bacci take oxygen yana a hancinta hannayenta dika biyun sanye da jini dakuma ruwan jiki, cikin tsintsar tausayi sukai zaune suna jiran farkawarta munira sai kuka take,,,….

Around 6:30pm bayan sunyi sallar magrib Amira na zaune munira da nusy sunje siyomasu abinci, ahankali tafara juya fuskarta tana karanto kalimatush shahada tana bud’e idanuwanta, dasauri Amira ta taso cikin murmushi tazo kusa da’ita, bayan tabud’e idanuwanta Amira tace “sannu MUFIDA” tad’aga mata kai yunk’urin tashi tai sai takasa Amira tai saurin rik’eta saigasu munira sundawo, dasauri sukayo gunta cikin fara’a sunamata sannu ta amsa nan munira taje tashaidawa doctor farkawar ta,,,….

Atare suka shigo nan yafara y’an gwaje gwajenta yacire mata drip d’inda yak’are saura jini sannan yasake mata wasu injection sannan yajuyo garesu “to Alhmdllh komai yazo da sauk’i yanzu sab’anin d’azu jininta yadawo normal sab’anin d’azu dayahau sosai wanda hawarda yaine ma yai sanadinda take aman jinin,, dik waennan matsalolin dasuka faru gareta sunfaru ne a sanadin tention d’inda yamata over damuwa yawan tinani gakuma saka abu a ranta wanda yake k’ara haifarmata da damuwa dakuma yawan tinani, zaman kad’aici yana bada babbar gudumawa wajen wanzuwar yawan tinani dakuma shiga damuwa, damuwa da yawan tinani shike kawo hawan jini wanda idan jinin mutum bayada k’arfi sosai saiyafara aman jini kokuma yafad’i b’arin jikinsa yamutu yadawo baya aiki wato paraliasation mutuwar b’arin jiki d’aya, so gaskiya bazan b’oye makuba  tana gab da kamuwa da ciwon hawan jini wato hypotention matuk’ar jininta yasake irin wannan hawar da yai to komaima zai iya faruwa so saboda haka dole a kiyaye tadaina shiga damuwa da yawan tinani saboda gujewa matsala domin kuma kariyar lafiyarki Allah yabaki lafiya” dakyar suka iya amsawa da ameen saboda dik jikinsu yamutu sosai,,,….

STORY CONTINUES BELOW

Bayan yafita norse taciremata oxygen da jinin da aka doramata yak’are, brush tai tawanke bakinta sannan suka had’a mata tea tasha bayan tasha sannan akabata magani tasha takwanta, bayan ta kwanta suma sukaci abinci sannan sukai sallar isha,,,….

Suna zaune sai Amira tad’auki phone d’in MUFIDA takira PC d’insu koda yad’aga cikin farinciki yad’aga wayar azatonsa itace gogar saboda kullum saidai yakirata ko plss call me bata masa saikuma gashi yanzu yaga kiranta, bayan yad’aga tareda rangad’a mata sallama had’e da kiranta da sunanda yasaba kiranta wato baby,,,….

Dasauri Amira tai saurin katseshi da “sir barka da dare nice Amira Nasir Aji k’awar MUFIDA nakira ne nafad’a ma halinda MUFIDA take ciki a yanzu haka tana a private hospital dake kusa da School dinmu” bayan tagama fad’a masa yace “subhanallah ok ok ganinan zuwa” saiya kashe wayar, kallonta MUFIDA tai tace “meyasa kika kirasa da wayana Amira kinfasan banasan hakan bana sonsa haka kuma bana san kiransa a wayana kuma bana son komai nasa”  murmushi Amira tai tace “nayi hakan ne saboda wata manufa, kinsan kinyi loosing exam’s biyu yanzukuma gaki kwance akan gadon asibiti kinga ko gobe bazaki iya zuwa School ba so nasan idan yazo dik yanda za’ayi zaiyi saboda yaga kin rubutasu” murmushi kawai tawai batasake cewa komaiba,,,….

Haka kuwa akayi bayan yazo yamata sannu tareda kawo kayan jinya sai yace badamuwa insha Allah zata rubutasu tai masa godiya su Amira ma sukamasa,, washe gari saida suka shirya komai tai wanka taci abinci tai sallah sannan suka fita suka barta tareda norse, lokacin exam nayi saiga malaman School d’insu da jamian tsaro har uku sunzo anan aka bata Question’s  paper ta karb’a da  laptop tai exam d’in tagama sannan tai submitting suka wuce,, saida tai kwana biyu anamata haka aranar na uku ne aka sallameta suka koma gida,,,….

A kwana biyunda tai Amira da nusy sunyi matuk’ar k’ok’ari sun nunamata su aminaine nagari dan ko y’ar uwarta batai mata abunda sukaimata ba, tin ranar farko da mubina taje batasake zuwaba shima bawani jimawa taiba tawuce abunta, munira kuwa dik abunda akai atare da’ita, acikin kwanakin sunyi matuk’ar k’ok’ari wajen ganin sun sakata acikin nishad’i saisuyita mata fira mai cike da barkwanci taita dariya suna nishad’i dikdan kawai tad’an samu tarage damuwa kuma Alhmdllh tasamu sauk’i sosai saidai tarame sosai daman bawani k’iba ne da’ita ba bare kuma yanzu datai ciwo,,…

              *****  *****

Yau kimanin kwana biyu kenan da dawowarta daga hospital taji sauk’i saidai har yanzu takasa daina tinanin MUJAHID dik lokacinda tazauna itakad’ai to zaka ganta tai tagumi tana tinani ko tai shuu kamar mara lafiya,,,,….

Zaune take itakad’ai akan kujera cikin class saigasu Amira sunshigo, fira sukad’anyi kan lokacin shiga exam yayi, bayan sunyi exam sungama suka wuce restaurant domin cin abinci,,,….

       Bayan sungama sai suka tashi domin sud’an mik’a kafa anan acikin School d’in,, suna cikin zagayawa saisuka hango MUJAHID da Rayyan suna tafiya suna fira sai dariya suke suna wasa da’alamu sunajin dad’in firarsu,,,….

Tsaye tai tadazk’are anan tai tagumi tana kallonsa tana murmushi kamar yanda shima yake murmushin saikuma kawai taji kwallah nazubomata, nusy ce tai saurin rik’o hanunta tajuyo da’ita gefe d’aya lokacinda sukazo zasu wuce ta gefensu kusa dasu karsugane sune suke kalla, saida suka wuce tai saurin kwace hanunta tajuya tana kallon bayansa, wani irin kyau taga yak’ara mata saidai taga yarame sosai kamar wanda yakwanta jinya, murmushi take sosai har fararan hak’oranta suna bayyana saidai kuma kwallah nazuba daga idanuwanta,,,….

Tsintsar tausayinta ne yamamaye zuciyoyinsu nusy tace “MUFIDA kiman izini naje na bayyana soyayyarki a gun masoyink….” bakinta da MUFIDA tai saurin rufewa ne yahanamata k’arasa maganarta tace “hakan bazata tab’a faruwaba nusaiba koda kuwa sonsa zaima ajalina amma bazan tab’a iya tinkaransa nafad’amasa cewar ina sonsa ba koda kuwa sonsa ne zaizamto ajalina abunda kawai nake nema agareku amatsayinku na aminaina shine kucigaba da tayani da addu’a Allah yarageman zafin k’aunarsa acikin zuciyata yakuma bani juriyar cigaba da b’oye k’aunarsa har izuwa lokacinda rai zaiyi halinsa amma fa bazan tab’a iya tinkaransa nafad’a masa ina sonsa ba” janyota nusy tai tarungume cikin tsintsar tausayinta,,,….

Kasa yin yawon sukai kawai suka wuce izuwa gida,,…

               *********

Yau takasance Thursday ranarda suka kammala zana exam y’an class d’insu MUJAHID sunfito sai murna suke suna nuna tsintsar farincikinsu da Allah yanuna masu wannan ranar dasuka kammala degree d’insu,,,….

Hamma faruk na gefe d’aya tareda abokanansa dasu MUFIDA suna tayasa murna, acan wani gu tahangosa zaune shikadai yana danne danne phone nasa, wani irin murmushi ne yakub’e ce mata batareda sanintaba saikuma tai sauri tajuya kar yaganta,,,…

Yana a zaune saiga Rayyan yazo fuskarsa dikta baci da kala wacca sukaita shafawa jikinsu, murmushi yai tareda zama sannan yace “MUJAHID gafa y’ar gidanka nan smole baby a kusa dakai mezai hana kasameta kafad’amata sak’on zuciyarka saboda wannan itace damar k’arshe agareka idan kabari ta kub’cemaka to bazaka sake samun irintaba”  murmushi yai sannan yace “aikuwa saidai ta kub’ceman amma bazan tab’a aikata abunda kaceba” shuru rayyan yai yayi tagumi yana kallonsa shi tinda yake a rayuwa baitab’a ganin miskilin mutum kamar MUJAHID ba, yanda yai abun saima yabama MUJAHID dariya yai dariya yamik’e tsaye tareda buga shoulder d’insa irindai yanda gyaiz sukeyiwa junansu yawuce abunsa,,,…

Kallo rayyan yabisa dashi can saikawai wata dabarar tafadowa rayyan, dasauri yatashi yaje yanemo paper d’aya da ink yazauna yafara tsara letter irin wacca ada maza keyi idan namiji zai fara neman tayin soyayyar mace yakuma fad’a mata cewar yana sonta,,,….

Saida yatsarata tsab harda kalaman soyayya masu dad’in gaske masu sanya zuciya tai taushi sannan yalinketa yasaka acikin wani gu mai kyan gaske yahad’a da flower red colour had’e da zobe na zinare mai shegen kyau yai murmushi sannan yatashi yawuce,,,….

Wajen yacika sosai sai farinciki da murna suke, nan yakutsa yafara neman MUFIDA saidai ina iya ganinsa yaduba bai gantaba, can kawai saiya hango mubina tareda k’awayenta saiyaje gunta yamasu sallama suka amsa sannan yace dan Allah tad’an bashi 10 mnts yanaso yai magana da’ita nan tace ba komai suka keb’e,,,…

Bayan sun keb’e yamata bayanin abunda yakeso tamasa tace ai bakomai saiya bata yace takaiwa MUFIDA MUJAHID ne yace abata, karb’a tai a fili tana murmushi amma a cikin zuciyarta tsintsar bak’inciki ne da haushi dakuma takaici, bayan takarb’a yamata godiya yawuce………..Wani mugun tsaki tai tareda binsa da harara, k’awayentane suka k’araso kusa da’ita, bud’e takardar tai tafara karanta abunda ke k’unshe acikinta saida suka karanta komai tabuga wani mugun tsaki zuciyarta namata kuna tace “aikin banza aikin wofi to sak’on bazaije guntaba bare har taji dad’i tayi farinciki” sai kawai tayaga takardar tayaga flower d’in shikuma zoben tabud’e jakarta tasakashi acikin,,….+

Hmm wallahi sunma rainamaki wayoi wato kece y’ar aikensu ko yafa kamata kifara d’aukan mataki akan yarinyar nan ki nunamasu kemafa big lady ce. cewar anisa k’awar mubina, “eh wallahi dan daga MUFIDA har k’awayen nata sunmugun rainaki” inji najma k’awar mubina,, wani mugun murmushi mubina tai tace “karku damu lady’s nakusa kawo k’arshen wannan iskancin nasu domin nafara gano sirrin abun wato yanzu dai gaba d’aya MUFIDA taluuuula acikin kogin soyayyar d’an samrayi MUJAHID” tai maganar cikin kyalkyalewa dawata muguwar dariya suma k’awayen nata suka kyalkyale da dariyar “so kunga nasami makamin da zanyi yak’i da MUFIDA” of course my k’awa muk’arasa gida domin sanin yanda zamu tsara abun. cewar najma nan suka wuce izuwa gidansu mubina,,,….

Rayyan nabata yawuce suka cigaba da celebrating d’insu,,”….

Around 4pm akafara gudanarda shagalin bikinsu MUJAHID domin tayasu murnar kammala karatunsu, cikin shiga mai kyan gaske ta alfarma MUJAHID da rayyan sukashigo acikin k’aton holl d’inda ake gudanarda shagalin sanye da graduation gown, tamasu kyau sosai idan kagansu kai kace jinin Arab’s ne sak kirarsu da siffarsu kamanninsu gaba d’aya na arab’s ne musamman MUJAHID,,,….

Bayan manyan bak’i professers da dai sauran manyan shuwagabannin k’asar sunzo sai akafara gudanarda bikin, anjinjinawa shugaban makarantar sosai irin namijin k’ok’arin da yake wajen ganin ansamu cigaba ga d’alibbai hakama d’aliban anjinjinamasu sosai saboda irin jajircewarda suke wajen karatu domin fitowa da result mai kyau, bayan nan sai akabada kyaututtuka ga gwarazan d’alibbai wanda hadda MUJAHID aciki yakarb’i kusan kyaututtuka uku da kyautar littafai guda biyar waenda wani professor yarubutu, rayyan ma yakarb’a, bayan angama sannan d’aliban suka fara nasu shagalin,,,…..

A can gefe d’aya MUJAHID yahango MUFIDA tareda k’annenta da hamman su cikin wata iriyar shiga mai d’aukan hankali, tai masifar yin kyau Arabian gown ce ajikinta tai rolling da veal d’in rigar k’afafuwanta sanye da wasu hills shues d’an k’aramin bakinta yasha janbaki red color, dariya take sosai fararan hak’oranta sai bayyana suke dimples d’inta sai lotsawa yake, murmushi yai yashafa sumarsa saboda wani irin shauk’i dayaji jiyake kamar yaje yarungumeta yafara tsotsar lips d’inta gasu pink sunsha janbaki gwanin birgewa da d’aukan hankali, saidai ina girman kai bazai bariba hhhh Lol,,,”…

Saikusan 6pm sannan aka gama akai pic’s domin tarihi sannan kowa yanemi yafiyar d’an uwansa aka watse,,….

Zaune yake akan gado yai shuu yad’ora kansa akan pillow yana kallon sama mubashir na harhad’a masu kayansu, rayyan ne yashigo d’auke da jakar takalman MUJAHID,,,….

D’ayar jakar takalmansa yajanyo yasakasu aciki sannan yacigaba da taya mubashir, har suka kammala had’a komai baisanma rayyan yashigo d’akinba saida yatab’a shoulder d’insa sannan yai firgigit yadawo daga duniyar tinaninda ya lula, murmushi yai yashafa sumarsa yatashi yawuce toilet, binsa da kallo rayyan yai batareda yace komaiba yafita,,,….

Washe gari tin 6:30pm basu sake kwanciya ba, bayan sunshirya sannan suka fito sukai breakfast, sunacikin cin abinci rayyan yadubesa yace “prince yau itace damarka ta k’arshe karka bari ta kufcemaka” shuru yai nayan wasu second’s kan yace “ban fahinci inda zancenka ya dosa ba” wani kallo rayyan yamasa na mamaki shikam yana mamakin hali irinna MUJAHID kana suma kana farfadowa akan abu amma kuma saboda girman kai ka kasa samarwa kanka wannan abun,,,….

“Hmm ina nufin kaje kasanarda MUFIDA kanasonta” Murmushi yai yahad’iye ruwan tea d’inda yakurba sannan yakallesa yace “rayyan kenan ayanzukam tabbas na tabbatar zuciyata tariga takamu da son smole baby saidai kasani bazan tab’a tinkararta na fad’amata ina sonta ba wannan maganace dana fad’a a baya yanzu kuma nasake maimaitawa, zan iya hak’uri nacigaba da binne sonta acikin zuciyata nakuma cigaba da rok’on Allah daya mantar dani k’aunarta yacire man ita acikin zuciyata amma bazan tab’a furtamata kalmar so ba koda kuwa son natane zaizamo ajalina” kallonsa rayyan da mubashir keyi har yagama maganarsa,,,….

Nannauyan numfashi rayyan yasauke hakama mubashir suna jinjina girman wannan al’amarin dandai tinda suke basu tab’a ganin irin saba basukuma san mezasuyi akaiba, saidai fa har yanzu k’udurinda rayyan yai bai mantaba yakuma d’auki alk’awarin cikasa kodon ya jadadda k’arfin abotakarsa da MUJAHID,,,”….

Haka suka kammala cin abincin batareda kowa yasake cewa uffan ba, bayan sungama sannan suka kwashi kaya suka saka acikin mota sannan suka fito aka rufe gidan sukabama gateman Key’s tareda masa bankwana sannan suka shiga mota rayyan yajasu suka kama hanyar airport kasancewar flyt d’in 10am zasubi,,,…..

***** *****

Munira da Amira ce zaune akan dining suna break itakuma tana kan kujerar parlor a zaune tai shuu tak’urawa littafe idanu,, nusaiba ce tashigo da gudu suna ganin yanayinda tashigo bako sallama saisuka taso da sauri sukayo gunta,,,….

Cikin haki tafara magana “ga MUJAHID can nagani a airport suna jiran flyt d’insu ya’iso yanzu munje raka yayan k’awata nagansa shi da abokinnan nasa, MUFIDA dan Allah kitashi muje kibayyana masa sak’on zuciyarki kokuma kimana izini muje musanardashi” wasu irin zafafan kwallah ne suka zubomata a lokaci d’aya tareda murmushi mai zafin gaske “ahalin yanzu inaji ajikina tabbas narasa mr man har abada soyayyarsa takusa tazama tarihi agareni zancigaba da b’oye ta acikin zuciyata inkumayi k’ok’arin binneta saidai na tabbata aduniya zuciyata bazata tab’a son wani d’a namiji a duniya kamar mr man ba koda kuwa shine number 1 acikin masu kud’in dik duniya kuma koda shine yafi kowa kyau a duniya” juyowa tai takalli nusy tai murmushi sannan tace “nusaiba tabbas ku k’awayene nagari masu damuwa da damuwar wani amma nusaiba kiyi hak’uri wallahi bazan iya tinkarar mr man nafad’a masa ina sonsaba i can’t i can’t nusaib…a” saitafashe da matsanancin kuka mai tsintsar ban tausayi mai raunana zuciyar mai karatu,,,”….

Carkey Amira tad’auka afusace takalli nusy tace “tashi muje nusaiba” nan nusy ta tashi munira ma ta tashi suka fita suka barta kwance akan kujera,,,….

Kai tsaye airport d’in suka nufa cikin sauri Amira sai gudu take sosai da motar, suna isa sukai parking suka fito da sauri nusy tajasu izuwa gunda taga MUJAHID da rayyan da mubashir zaune saidai kash koda suka isa basugansuba suntashi,,,”….

Tsaye sukai suna dube dube nusy tad’ora hanunta d’aya a goshinta d’aya kuma tarik’e k’ugunta saboda damuwar da take ciki, Amira tadubesu tace “inaga mushiga ciki muduba watakil suna ciki saboda sai 10am jirgi zai d’aga kamar yanda naga sun rubuta acan” tanunamasu wanu k’aton allo fari da akai rubutu akansa,,,”….

Wucewa sukai ciki suka fara dube duben inda zasu hangosa, sunkai kimanin 30mnts suna zaga wajen harsuka gaji sukai tsaye kusa da wasu jamian tsaro dake kula da wajen,,,….

Can kamar ance nusy ta waiga tana waigawa kuwa tahangosu suna tafiya izuwa gun flyt yasakko domin sushiga suwuce, dasauri tajuya tacewa su Amira “Amira gayacan zasu shiga jirgi” dasauri harda gudu suka kama hanyar zuwa gunsu………

About AIS

Check Also

TSINTACCIYA CHAPTER 4 BY NIMCY LUV

TSINTACCIYA CHAPTER 4 BY NIMCY LUV Www.bankinhausanovels.com.ng  Ƙamshin haɗaɗɗan turarensa ne ya daki hancinta wanda …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *