TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 12 BY AUFANA

TSINTACCIYAR MAGE CHAPTER 12 BY AUFANA

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Cikin sauri yake driving ganin halinda take ciki, wani irin nishi take hanunta dafe da maranta tana fad’in “innalillahi wainna ilaihi raji’un, hazbiyallahu wani’imal wakiil, wayyo Allah na MUJAHID mutuwa zanyi marana zata tsinke MUJAHID cikina wallahi mutuwa zanyi ka taimakeni MUJAHID” tana fad’in haka kwallah nazubarmata tana yarfarda hanunta ‘daya d’aya kuma yana kan maranta ta dafe, MUJAHID kuwa dikya rude yarikice dasauri yake driving d’in,,,….

+

Dakyar cikin gaugawa suka iso hospital d’in Ustaz Shuraim, yana isowa baijira komaiba yazo yabud’e murfin motar yad’auketa yakama hanyar shiga cikin hospital d’in, tinda yad’akko ta nurse’s suka biyo bayansa wata kuma taje tasanarda doctor’s kasamcewar YARIMA Biryama mutum ne na mutane dikda darajarsa ta d’an gidan mulki kuma inda ake ji da mulkin da sarauta had’e kuma da shahararriyar dukiya wacca tafi k’arfin tinanin mai karatu amma sam bashida girmankai, yakan sauya kama yai shigar talakawa yaje kasuwa da asibitoci domin ganin yanda mutane ke gudanarda rayuwarsu daga baya kuma yazo yabasu tallafi yabasu kyaututuka domin suma suji dad’in rayuwa, wannan asibitin ma mallakin sarki ce wacca yagina yabada sadaka domin Allah ataimakawa talakawansa to kasancewar ustaz shuraim babbar likita kuma shine shugaba a asibitin yasa ake kiran asibitin da sunansa,,,”….

Yana isa da’ita cikin gaugawa Nurse’s suka karb’eta suka shiga da’ita emergency, suna shiga da’ita saiga doctor’s d’in sun iso danhaka suka shiga domin bata taimakon gaugawa, wani doctur Akram ne yatsaya MUJAHID yamasa bayanin iya abunda yasani sannan shima yashiga ciki suka fara aikinsu,,,,……

Har kusan 12pm ba’ace ba’afito da MUFIDA ba, likitoci uku suka hau kanta domin bata taimako tayanda bazatasha wuya sosai ba wajen zubewar cikin,,,….

MUJAHID kuwa yakasa zama yakasa tsayi sai zarya yake a k’ofar shiga emergency d’in gaba ‘daya hankalinsa atashe yake saiya zauna kuma yamik’e tsaye addu’oi barkatai kowacce karantowa yake batareda yak’arasa dayar ba, sai can kusan 12:30pm saiga doctor’s d’in sunfito sauran suka wuce sai doctur Akram ne yatsaya yamasa magana cikin harshen larabci yace suje office d’insa yamasa bayani nan suka dunguma suka wuce,,,….

Bayan sun isa sun zauna ne doctur Akram yake masa bayani acikin harshen larabci kamar haka “Yarima hak’ik’a dik abunda Allah yabamu nasane kuma dik abunda yakarba shima nasane saboda haka godiya kawai zamu masa dakuma addua da fatan Allah yasake bamu wani, inaso dan Allah karka damu karka daga hankalinka, tabbas juna biyun dake cikin sarauniya yab’are yafita saidai muyi addu’ar Allah yasake bada wani mai albarka” idan ran MUJAHID yai dubu toya baci, yanzu shikenan sunrasa d’an babynsu dasuketayiwa shirye shiryen zuwansa, ‘dagowa yai yakalli doctur yace “shikenan Allah i bada wani rayayye mai albarka” doctur yace ameen sannan yacigaba da magana “saidai yarima bafa miscarriage bane Abortion ne, cikin yazube ne tasanadin wani magani mai k’arfi da’akayi amfani dashi ta hanyar sha acikin ruwa ko juices wanda yake b’ararda ciki cikin gaugawa koda kuwa cikin yakai wata biyar ne to maganin zai iya narkarda abinda ke cikin ya nunnugesa sannan yab’arardashi, kasancewar ita jininta bayada k’arfi sosai kuma maganin yamata k’arfi shiyasa ta zubarda jini sosai jinin ne yafara zuwa kamin cikin yafara b’arewa”,,,,….

Mamakin duniya yacika MUJAHID tsabar mamaki dayake yasa yasake baki da hanci da ido yana kallon doctur har yagama bayaninda yake masa, bayan yagama sannan sukai musaba yafita yabar office din zuciyarsa cike da mamaki dakuma tinani barkatai akan Abortion d’inda doctur yace MUFIDA tai dakuma kalar maganinda yace akai amfani dashi wajen b’ararda cikin,,,….

STORY CONTINUES BELOW

Koda yaje d’akinda aka mayarda ita har yanzu bata farkaba bacci take amma daganinta kasan taci wuya idanuwanta sun kumkumburo saboda kukanda tai jikinta sanye da rigar hospital d’in an rufemata jiki da blanket,zama yai kusa da’ita yakura mata ido yana kallonta, tinani yake acikin zuciyarsa anya kuwa MUFIDA zata iya aikata wannan abun kai ina dolene yai kwakkwaran bincike akan wannan abun, toma taina zaifara ne?,, haka yaita zancen zuci shik’adai,,”….

Sai kusan 3pm sannan MUFIDA ta farka tana karanto kalimatusshahada tareda karanto addu’ar farkawa daga bacci, waigowa tai gefenta saita hango MUJAHID zaune a gefenta, murmushi yasakarmata sannan ya taso yazo kusa da’ita, shafa sumarta yai sannan yaduk’o ya sumbaceta a goshi yace “sannu my only na harkin farka” shuru tamasa batace komaiba tanabin d’akin da kallo, can sai komai yadawomata abunda yafaro acikin kwakwalwanta, dafe kanta tai sannan takai hanunta tashafa cikinta, dasauri tabud’e fuskarta tazaro daran daran idanuwanta tad’ago takalli MUJAHID tace “MUJAHID ina cikina kardai kacemun baby na yafita” duk’owa yai yakamo hannayenta yasumbacesu sannan yashafa sumarta yak’uramata ido sannan yace “come down my only one karki daga hankalinki inaso ki kwantarda hankalinki kinji dik abunda kikaga yasami bawa to tabbas mukaddari ne daga ubangiji, MUFIDA Allah yafimu son wannan cikin shiyasa ya karbi abunsa” tanajin yafadi haka saita fashe da kuka mai tsuma zuciyar mai karatu mai cike da tsintsar ban tausayi, rungumeta yai yafara rarrashinta yana bubbuga bayanta cikin tausayi yana fad’in “is ok is ok MUFIDA kidaina kuka mana insha Allah, Allah zaisake bamu wani kinjiko” batai shuruba haka tacigaba da kukanta yana rarrashinta,,,”…

Kasancewar tazubarda jini sosai yasa saida sukamata karin ledar jini uku d’aya na MUJAHID ne sauran kuma siya yai, kwanansu uku anan hospital d’in nurse’s da doctor’s suna bata cikakkeyar kulawa dakuma MUJAHID, daga baya ganin tasami lafiya ta warke sai suka sallameta,,,….

Aranarda suka koma gida MUJAHID yakira hadimanda aka kawowa MUFIDA mata yafara tambayansu waye acikinsu yazubawa matarsa magani acikin ruwa cikinta yab’are, nanfa kowacce tafara rantse rantse tana kare kanta, ganin sunki fad’a yasa yatsoratasu akan zai koresu gaba ‘daya kuma idan suka kuskura sukaki fad’a haryai bincike yagano wacca tai aikin to suduka sai laifin yashafesu kuma zaimasu hukunci mai tsauru, amma dikda hakan dayai baisa wata daga cikinsu tafadi komaiba saidai yana zargin humaida wacca takowa MUFIDA ruwa tasha shekaranjiya a parlor wacca kuma itace keyiwa MUFIDA girki, yahango razana da tsoro tsintsansa a fuskanta danhaka nantake yashirya yanda zaiyi, sallamarsu yai yace sutafi saisuka wuce daga nan yafara bincike akan abun yahad’a da wancan na baya na wannan gardin,,,….

              *****  *****

Rayuwa tacigaba da tafiyar masu cikin farinciki da k’aunar junansu, a kullum karajin suke k’aunar junansu nakara shigarsu soyayya kuwa tazamarsu al’ada wacca take dole suyita,,,….

Kwanaki natafiya watanni na shudewa yau kimanin wata goma kenan da aurensu, wani abun mamaki da MUFIDA ke gani shine cikinta sai girma yake har yanzu bobbs d’inta basu huceba basu daina cika ba sannan tinda tai bari har yanzu bata al’adartaba tazo ( period or menstruation) abun yana bata mamaki kuma yana d’agamata hankali saboda ko lokacinda tana budurwa taba tsallaken wata dik wata saitaga al’adanta amma yanzu har kusan wata uku amma shuru, a zuciyarta tace “dolene nasanarda MUJAHID muje asibiti inba wata matsala bace”,,,….

Tana cikin wannan tinanin sai wayarta tai kara nanta d’akko, tana dubawa saitaga sunan (my Lil Sis M ) akan secreen d’in wayar aikuwa dasauri tadaga tak’ara a kunne cikin zumud’i,  daga ‘dayan bangaren akai sallama sannan akace “haba my big Aunt haka akeyi dankina makale da masoyinki shikenan saiki manta da y’an k’annenki” dariya MUFIDA tai sannan tace “habadai my Little Sister munira wace ni dazan iya mantawa da y’an kannena abun k’aunata wallahi kullum kuna raina yanzu hakama kullum cikin maganarku nake kwanan nan harma nayiwa yayanku magana muzo mu gaidaku to shinedai baice komaiba shiyasa kukajini shuru amma insha Allah acikin kwanannan zaku ganni”  murmushi munira tai sannan tace “to shikenan da har munyi fushi mundauka kin manta mune amma yanzukam munyi hak’uri” saitai murmushi tace “yawwa y’an kannena ina sonki ina alfahari daku wallahi ina my Lil bro musty” munira tace “yanzu suka fita tareda uncle hashim yazo kinga aunty MUFIDA kusan time by time sai musty yaita tambayana momy da aunty mubina sainarasa amsarda zanbashi wallahi”,,,…

Shuru MUFIDA tai sannan tasauke nannauyan ajiyan zuciya, ganin haka yasa munira ta kauda zancen da fad’in “am aunty dama nakirane nafad’a maki gobe insha Allah zamuzo BAGDAAZ su Abbu ne sukace kar afadamaki abari muyi surprising naki shine nikuma nazo a boye nakiraki nafad’a maki”  wani irin dad’i MUFIDA taji tace “kai dan Allah munira dagaskiya kike” munira tace “Allah kuwa gobe zamuzo” aifa nan MUFIDA taita tsalle tana murna,,,….

Sunjima sosai suna waya daga bisani sukai sallama, sunayin sallama takira MUJAHID tafad’amasa nan shima yaita murna sannan yamasu addua da fatan sauka lafiya,,,…

A daren ranar bayan MUJAHID yadawo daga office saiya d’auketa sukaje gida, koda sukaje saisuka tadda ana shiryen shiryen taryan mutan k’asar Cyprus wato MA’ARUF kanen MUJAHID dake can yana karatu yanzu yagama shine zai dawo gobe, kasancewar har yanzu ummin MUJAHID batasake mata fuskaba yasa tai zamanta a sashen jaddati bataje sashentaba hakama MUJAHID baitarukataba akan taje saboda shi bayaso yaga anawulk’antamasa ita shiyasa yanzu kosunzo bayacewa taje sugaida ummi saidai shi yaje dikda koya gaidata d’in ba karb’amasa takeba dan har yanzu fushi take dashi saidai ya zauna suyita fira da k’anensa idan suka gama yadawo sashen jaddati, su Nasmat ma sunaso suje gun MUFIDA ko kwana d’aya suyi amma ummi tahana,,,….

Sunjima sosai anan kasancewar idan ana wani biki a gidan to kowa nagidan baya bacci any time kamar ba dareba mutane sai zirga zirga suke hadimai kuma kowa na nasa aiki, sai kusan 11pm sannan suka koma gida,,,”….

Washe gari around 10am dot akaje dauko Ma’aruf airport dasu munira kasancewar jirgin lokaci ‘daya suka shigo sai aka raba biyu MUJAHID da sauran dakaru sukaje dauko ma’aruf mai martaba da wasu dakarun sukaje d’akko su munira su MUFIDA kuwa aka fake gida ana jiran isowarsu,,,….

Su munira ne suka fara isowa nanfa su MUFIDA aka had’e sai murna ake ana tsalle, bayan sun iso ne su ma’aruf suka iso nan gida yacika da mutane y’an uwa dakuma abokan arziki, abban MUFIDA ma yazo tareda matansa,,,,….

Tinda ma’aruf suka iso yakyalla idonsa ga munira yakasa d’auke idonsa sai kallonta yake, shi abunda ma yafiso yasani akanta shine ya zumuncinsu yake dasu,,,…

Ma’aruf kyakkyawane kamar MUJAHID amma MUJAHID yafisa tsayi da fad’in fuska kuma yafisa fari sosai amma shima dai very handsome gyai ne gashi d’an bokone yanaji da boko sosai d’an gayune nabugawa a mujallah,,,”….

Bayan sunhuta angama gaisawa da juna sai sarki ya shiryamasu kasaitacciyar walima ta murnar dawowan ma’aruf da kammala karatunsa wacca zaagudanar a babban parlonsa na taryan manyan bak’i, zaagudanarda walimar 2:30pm bayan angama sallan azahar,, daganan MUFIDA takwashi su munira suka wuce gidanta, acan sukai shirin zuwan walima bayan sunshirya sannan suka fito domin suwuce, harsun fito suna jiran isowar driver saiga ma’aruf yadanno hancin motarsa shi da friends d’insa, bayan yaiso yai parking saiyafito cikin fara’a da dariya suka gaisa da MUFIDA sannan yakalli munira itama suka gaisa yana mata wani irin kallo da’ita saida tadan ji ta tsargu, ganinsu sunfito kuma yasan can gun walimar zasuje yasa yace suzo mana yakaisu shima can zasu,,,…

MUFIDA batamasa musuba kuwa suka shiga suka wuce, acanma ma’aruf sai kallon munira yake dik inda tai saita gansa dazasu zauna ma kujerardake kusa da’ita ya zauna, bayan angama komai MUJAHID yazo yadaukesu yawuce dasu gida…………. 

Suna isa wanka su MUFIDA sukai shikuma MUJAHID yawuce bedroom d’insa, bayan sunyi wanka sannan sukafito parlor humaida takawomasu abinci nan suka zauna sunaci sunashan firar yaushe gamo,, bayan sungama sannan sukai zaune munira tafara bama MUFIDA labarin abubuwanda suka faru bayan tafiyanta, sunjima sunashan fira har kusan 7pm ganin ankira sallar magrib yasa suka tashi suka shiga ciki domin gabatarda sallah,,,….+

Bayan sungama sai MUFIDA tafita tabar munira anan, kai tsaye d’akin MUJAHID tawuce,,,”….

Cikin sallama tabud’e k’ofa tashiga, zaune yake akan gado yana tsara kaya acikin traveling bag, yanajin sallamarta yad’ago fuskarsa cikin fara’a da murmushi yakarb’amata, k’arasowa tai itama cikin murmushin tazauna kusa dashi tana fuskantarsa sannan tace “barka da hutawa habiby na” yai murmushi tareda rik’o hanunta sannan yace “barka dai my only one da harnace yau my only anhad’u da k’anwa anmanta da habiby” dariya tai tace “laa a,a wallahi kasan anjima ba’ahad’uba shine muketa shan fira amma kana raina dama so nake nai sallah sannan nazo gunka”,,,…..

Murmushi yai sannan yamatso dab da’ita yalakuci tsinin hancinta cikin tsokana yace “to me za’abani yanzu kishi nakeji amma na matana” murmushi tai tasinne kanta k’asa cikin yanayin kunya batareda tace komaiba, shima murmushin yai yace “hmm only na badai kunya ba bansan lokacinda wannan kunyar zata fitaba gabadaya amma nasan dik laifinane daban cireta ba gaba ‘daya tin a first night” hararansa MUFIDA tai sannan tace “a first night ai mugunta kai” dariya ya kyalkyale da’ita sannan yace “my only ashe dai haryanzu baki mantaba” “inafa zan manta kuwa idan mai tutu ya manta ai wanda ke kwasansa bazai mantaba” gyara zamansa yai yana kallonta yace “nimafa naci wuya aranar” hararansa tasakeyi tace “bawani dad’i dai kasha” yai dariya sannan yajuya yacigaba da aikinsa,,,,…..

Kan gadon tahau dakyau tana fad’in “am habiby wai inazakaje ne naga kanata harhada kaya haka” mikewa yai tsaye izuwa wardrobe d’insa yana fad’in “wallahi wata tafiyace takamani” cikin mamaki tace “tafiya kuma zuwa ina?” “Nigeria, zamuje neman aure Amira ne wa Rayyan” zaro daran daran idanuwanta tai ta firfito dasu waje tace “Ehhh….!!!” cikin tsintsar mamaki, yanda tai sai abun yabasa dariya yace “yess insha Allah kuma munada hope d’in baza’ahanamu ba kinga nanda after sallar azimi saimusha biki”,,,,…

Tsintsar mamaki da farinciki yagama cika MUFIDA tama rasa mezatace kawai tasakko daga kan gadon tazo tarungume MUJAHID tareda bashi hot kiss a hab’a sannan tace “wallahi naji dad’in wannan abun nai matuk’ar farinciki sosai” janyota yai yatallafo fuskarta da dika hannayensa cikin murmushi yace “ai nasan zakiji dad’i kuma zakiyi farinciki shiyasa nai k’okarin hada wannan abun domin kiyi farinciki, jibi insha Allah zansauka Nigeria zanyi kwana uku a can sai angama komai sannan zan dawo” wata iriyar dariyar farinciki tai tasake rungumesa tana fad’in “ina sonka ina matuk’ar k’aunarka mijina” yai dariya yace “nima ina k’aunarki matana”,,,….

Daganan cigaba tai da had’amasa kayan dakanta saida tatsara komai ta harhahada komai sannan tagyaramasa d’akinsa sai shan fira suke suna barkwanci da junansu, bayan tagama sannan sukafito atare suka dinner tareda munira,,,….

Washe gari bayan sunshirya sai MUJAHID yadaukesu yakaisu can gida, koda suka isa ma’aruf na harabar gidan yana buga game shi da friend’s d’insa cikin game were’s, yana ganinsun fito yazo cikin fara’a da murmushi suka gaisa da MUJAHID sannan yagaida MUFIDA, bayan sungaisa sannan yakalli munira itama suka gaisa, atare suka wuce ciki yabar friend’s d’insa,,,….

Saida MUJAHID zai fita sannan suka fito atare, basuko gama buga game d’in ba yace atashi nan suka wuce side d’insu, wanka yatsala cikin English were’s had’addu sai kamshin daddadan tirare yake, bayan yagama shirin yakalli kansa a mirror ya tabbatar yagama had’uwa sannan yafita,,,….

STORY CONTINUES BELOW

Kai tsaye side d’in jaddati yawuce koda yaisa dik suna zaune sunashan fira, cikin sallama yashigo yana fara’a yazo ya zauna kujerardake kusa data munira akacigaba da firan dashi,,,….

Sunjima sosai anan anansuka wuni sunashan fira dasu Abbu musty sai tsalle yake ajikin MUFIDA tamkar itace mahaifiyarsa koda yake hausawa sunce babbar yaya uwa ce, saida MUJAHID yadawo daga office sannan yazo yad’auki MUFIDA suka wuce kasancewar munira anan suka barta,,,”….

________________

Around 7:40pm MUFIDA na a zaune bayan tagama sallan magrib saiga kiran munira yashigo a wayarta, ahankali tad’auki wayar sannan tadaga tareda kara wayar a kunnenta, bayan sungaisa munira tace “am aunty MUFIDA inataso muyi wata magana d’azu amma yaya MUJAHID yahana” cikin kulawa MUFIDA tagyara zamanta sannan tace “Eyyah menene hala” itama gyara kwanciyarta tai sannan tacigaba “wallahi aunty tinda mukazo ma’aruf yamanneman kaman cwingom narasa yanda zanyi dashi, yauma d’azu bansan a’ina yasami number na ba saigashi yakirani wai yananemana a lambu, bayan najene yake fad’aman wai shi sona yake kuma da aure yake sona dan Allah karnace a,a wallahi tinda yaganni yaji sona yashiga zuciyarsa” tak’arasa maganar cikin dariya, MUFIDA ma dariyan tai sannan tace “ai tinda naga yana wani sinne sinne yana sadda kai idan zai gaidani hadda wani d’an risinawa nasan dawata ak’asa, to munira naji dad’in hakan kuma nayi farinciki sosai, saidai munira gaskiya ni ban amince ki amincewa tayin soyayyar sa ba saboda banaso ki auresa” jin abunda MUFIDA tafad’a yasa dasauri ta tashi daga kwancenda take tace “meyasa aunty MUFIDA” d’an shuru MUFIDA tai sannan tacigaba “munira nikaina dakikagani ummi mahaifiyar MUJAHID bataso MUJAHID ya aureni ba hakan yasa yanzu haka fushi take dashi saboda kin bin umarninta dayai yaki aurar y’ar uwarsa y’ar kanwarta ya auren” nandai takwashe komai daya faru tafad’amata sannan tak’arasa dafadin “a yanzu haka ummi bata k’aunar ganina bataman magana tahana kowa nata yakusanceni hatta k’annen MUJAHID dasuke uwa ‘daya uba ‘daya sai ma’aruf ne kawai shima kuma nasan batasan yana zowa nanbane, saboda haka munira banason kema kishiga acikin halinda nake kuma banason kiyi saurin shiga acikin soyayyar ma’aruf saboda inatsoron kar mahaifiyarsu tace bazai aureki ba,, munira kawai kibama ma’aruf hak’uri yaje yanemi wata kema kuma Allah yabaki wani”,,….

“Hmm….!!!” munira tasauke numfashi sannan tace “shikenan Aunty dama banbashi amsa ba yanzukuma tinda haka abun yake zanbasa hak’uri yaje yanemi wata kawai” MUFIDA tace ” shikenan Allah yabaki wani nagari shima kuma Allah yabasa wata tagari” tace ameen sannan sukai sallama,,,….

Waigowarda zatai sai kawai MUJAHID a tsaye yana kallonta, juya fuskarta tai cikin jin kunyar maganarda tafad’awa munira abunda ke tsakaninta da ummi saboda tasan yaji dik zancensu”,,,…

Ahankali yak’araso fuskarsa d’auke da fara’a wacca tabama MUFIDA mamaki saboda a zatonta zataga tsintsar b’acin rai ne a fuskarsa amma saitaga akasin hakan, zama yai dab da’ita cikin sakin fuska yace “MUFIDA sam baidace kifadawa munira abunda ke tsakaninku da ummi ba ma’aruf yaganta kuma yaji yanasonta itama kuma na tabbata kila tanasonsa to meyasa zakiyi haka amatsayinki na yaya agaresu, hakan dakikai baidaceba sam” shuru tai tana kallonsa cikin mamaki baidamuba yacigaba “ma’aruf yafad’aman yana son munira kuma nai na’am dahakan nai farinciki sosai kuma insha Allah zanyi tsaye da kafafuwana har sainaga wannan auren ya tabbata” dasauri MUFIDA ta taresa dafadin “MUJAHID karkai hakan wallahi banason munira itama tashiga acikin halin rayuwarda natsinci kaina aciki inaso naga munira nafarinciki inaso naga sirikar munira tana alfahari da’ita kuma tanasonta dan Allah narok’ek’a kabar wannan zancen please….!!!” takarasa cikin magiya kwallah nabin fuskarta,,,,….

Juya fuskarsa yai sannan yace “MUFIDA kidaina fadar waennan maganganun kema insha Allah ummi zatasoki watarana kawai dai raunine da ummi irinna mata bata fahimceki bane kidauka aranki wata rana zata soki sannan kadace zaki hana ma’aruf y’ar uwarki idan kikamana hakan sam baki kyauta mana ba kuma bazanji dad’i ba shima kuma haka saboda yariga daya fad’a tarkon sonta kuma kinsan zafi da rad’ad’in rasa masoyi” shuru kawai tai batasake cewa komaiba sai yacigaba “abunda kawai nakeso dake shine, kimasu addua dakuma fatan alkhairi arayuwarsu sannan ki rik’o Allah yafahimtarda ummi tagane gaskiya dakuma matsalar raba masoya ko shiga atsakaninsu” ganindai har yanzu takasa sakewa yasa yamatso dab da’ita cikin murmushi yajanyota tadawo jikinsa tareda yin kissing nata,,”….

D’agota yai cikin murmushi yace “pleace my only ki saki jikinki mana banaso inganki acikin irin wannan yanayin dan Allah” y’an kwallanda suka zubomata ta share sannan ta k’ak’aro murmushi tace “shikenan nadaina” yai dariya yace “yawwa my only one Allah i maki albarka” tace ameen itama cikin murmushi, jin kiran sallar isha yasa yamik’e yafita izuwa masjid,,,….

Washe gari tin 8am MUJAHID yashirya yafito tareda MUFIDA, atare sukaje airport saida jirginsu yad’aga sannan suka dawo cikin kewar abun k’aunarta,,,…

Kimanin kwanan MUJAHID biyu da tafiya su munira suka koma Nigeria sukabar MUFIDA cikin tsintsar kewa,, MUJAHID kuwa ranarda yasauka washe gari akai baikon Amira da Rayyan tareda saka ranar bikinsu, abun yamatuk’ar yiwa MUJAHID dad’i Rayyan kuwa farinciki tamkar yakashesa, bayan anyine MUJAHID yakira MUFIDA yafad’amata, farinciki da tsintsar murna baya misaltuwa agun MUFIDA nantake takira number d’in Amira, tana d’agawa nan taita tsokanarta suna dariya daga bisani ta tayata murna sosai, sunjima suna fira daga bisani sukai sallama,,,”….

Kwanan MUJAHID uku a Nigeria sannan yadawo gida BAGDAAZ, koda yadawo saiya tadda MUFIDA na zazzabi, cikin kulawa ya zauna sannan yad’orata kan cinyoyinsa, tallafo fuskarta yai saiyaji jikinta yai zafi sosai, kallonta yai sannan yace “my only one meke damunki ne?” dakyar tabud’e idanuwanta sannan tace “najima sosai lokaci bayan lokaci zazzabi yana tasoman saidai danasha magani yake kwantawa to yanzuma dai nasha magani” ganin yanda takeyi alamar tanajin zazzabin sosai yasa yakwantar da’ita sannan shima yakwanta a bayanta,, hanunsa tarik’o ‘daya tadora kan cikinta sannan takallesa tace “habiby tin bayanda nai bari bansake ganin period dinaba kuma nasan banida ciki amma kuma abun mamaki wani lokacin idan na kwanta sainaji abu yanaman motsi aciki nidai habiby ka kaini asibiti inajin tsoro” murmushi yai yashafa fuskarta sannan yak’ara matsota acikin jikinsa yace “karki damu my only one insha Allah bawata matsala bace gobe zankira doctur Aysha tazo saitadubaki kinji ko” saitai murmushi tace to,,,”….

_______________

Washe gari kuwa kamin yafita office yakira doctur Aysha d’in tazo nan tafara yiwa MUFIDA y’an tambayoyi tana bata amsa, bayan tagama sannan tamata y’an gwaje gwaje, abunda dai doctur ke tsammani shine yake tabbata, murmushi sukaga doctur d’in nayi, bayan tagama sannan tacewa MUJAHID tanaso suje hospital nasu domin tayiwa MUFIDA wani babban gwaji wanda zai tabbatar mata da abunda take tinani,,,….

MUJAHID kuwa baiyi musuba yace MUFIDA tashirya nantashirya suka shiga mota suka wuce, bayan sun isa saita d’ora MUFIDA kan wani gado acikin babban dakinsa sukeyiwa mata masu ciki awo, na’urori takunna sannan tad’ora wani abu akan cikin MUFIDA nantake saiga d’a baby ya bayyana a naura kwance acikin mahaifar MUFIDA, tsintsar mamakine ya bayyana a fuskokinsu wanda yasaka MUJAHID yakasayin shuru saida yai tambaya, acikin harshen larabci yace “doctur ya akayi wannan rikitaccen al’amari yafaru mai cike da ban mamaki da al’ajabi” murmushi likitar tai sannan ta zauna tafara masu bayani “sau dayawa irin waennan matsalolin suna faruwa wanda idan likita baiyi kwakkwaran bayaniba hakan na’iya zama matsala atsakanin ma’auratan biyu, lokacinda matsalar tafaru cikin bai zubeba tadaiyi zubar jinine sannan suma likitocin basuyi kyakkyawan bincikeba koda yake irin wannan matsalar bakowanne likitane ke iya magancetaba saboda haka dai babyn ku bai bareba yana nan saidai yana buk’atar kulawa sosai” wani irin farincikene yarufesu sai aka rasa wanda zai fara magana acikinsu dik sai dariya kawai suke suna fara’a,,,….

MUJAHID ne yace “mungode sosai doctur amma yanzu watansa nawane” saida taduba tamata awo sannan tace “yanzu watansa bakwa ne da kwana hud’u” yai murmushi, nandai sukamata godiya yabata kudin aikinta sannan yad’akko MUFIDA suka wuce gida,, ranar wuni sukai acikin tsintsar farinciki musamman MUFIDA, tindaga wannan lokaci MUJAHID yad’ora daga inda yatsaya na bama MUFIDA kulawa ta musamman yanzuma saiyafi da d’in dan yanzu aikin komai yahanatayi saidai shi yamata kokuma tasaka hadimai sumata itakuwa ma batason hakan saitakejin dikta takura ba dad’i amma dole take hak’ura saboda MUJAHID yace a,a,,,”….

***** *****

Rayuwa tacigaba da tafiya inda MUFIDA da MUJAHID ke rainon cikinsu cikin kulawa ta musamman yanzu yashiga wata takwas yaturo fiyeda da yafito kuma saiyamata kyau sosai,,,….

Saura sati ‘daya afara azimi MUJAHID yazowa MUFIDA da daddadan albishir sarki yace zasuje suyi umrah atare dashi da ummi, MUFIDA taji dad’i sosai nantaita yiwa sarki kyakkyawar addua saidai dayace da ummi zaaje sai murnarta taragu har MUJAHID yafahimci hakan a fuskarta,,,…..

Saura kwana uku afara azimi jirginsu yad’aga izuwa Saudi Arabia domin gudanarda UMRAH…………

*kumin afuwa najina shuru kwana biyu NEPA namuce tasami matsala shys amma yanzukam komai normal insha Allah*2pm dot jirginsu yasauka k’asa mai tsarki, suna sakkowa dakaru sukazo da dalla dallan motoci suka d’aukesu izuwa masauki, kasamcewar sarki babban mutum mai gudanarda gaskiya wanda aka sansa da tausayi dakuma son talakawansa, girmansa dana kujerarsa yasa kowa ke girmamasa kuma yake martabasa data kujerarsa hakan yasa dik kasarda yaje a yankin arab’s ake bashi girma ake martabasa sosai,,,”….

+

Kai tsaye wani k’ayatacaccen gida aka kaisu mai d’auke da part uku sai sarki da ummi suka shiga d’aya MUJAHID kuma da MUFIDA sukashiga d’aya ‘dayan kuma a rufe yake, suna isa MUFIDA tawuce toilet tasakarwa kanta ruwa tai wanka sannan tafito, kasamcewar a gajiye take yasa wata gown kawai tasaka tabi lafiyan gadon kankace me har bacci yai awon agaba da’ita, MUJAHID kuwa yanacan gun sarki koda yadawo tini tai bacci,,,….

Murmushi yai sannan yazauna yad’akko k’afafuwan ta yad’ora kan cinyoyinsa yafara mata tausa cikin tausayi yana murmushi, wata iriyar mika tai tareda gyara kwanciyarta tacigaba da bacci saboda dad’in tausanda yakemata, murmushi yai saboda yanzu wani irin tausayinta yake Kara shigarsa tinda cikinnan yakai wata takwas yanzu batada juriyar zirga zirga sosai nantake take gajiya k’afafuwanta suyita ciwo sai anmata tausa,, saida ya tabbatar baccinta yai nisa sosai sannan yatashi yacire kayansa shima yashiga toilet, bayan yafito yasaka jallabiya da hula tab’a kasha hadisi sannan yazo ya sumbaceta a goshi sannan yafita,,,”…..

Kimanin kwanansu biyu dazuwa akafara gudanarda UMRAH donhaka MUFIDA da MUJAHID sarki da ummi suka raba hanya, MUJAHID yakoma side d’insu ummi tareda sarki ummi kuma tadawo side d’insu MUJAHID tareda MUFIDA saidai fafur tak’i yarda tazauna d’aki d’aya da MUFIDA tashiga ‘dayan d’akin dake kusa dana MUFIDA, ran MUFIDA bai baciba saboda yanzu inda sabo tasaba,,,,…..

Ahankali suka fara gudanarda ibadarsu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, dawowar ummi side d’insu yasa tai amfani da wannan damar tafara cusa kanta agareta tahanyar yimata hidima batareda tasaniba, da asuba idan zasuje masjid bazata tafi itakad’aiba saita jira ummi sannan sutafi dikda kuwa bamagana takemata ba idan kuma gama sallah har gunta take zuwa tamata barka da safiya dole badan tasoba take karbawa,,”…..

Ahaka ahaka ahankali ahankali tin ummi bata kulata harta fara kulata saboda irin hidimarda take mata dikda bakulata takeba, ganin haka yasa MUFIDA tak’ara himma wajen cusa kanta agun ummi, y’an kayanta idan sukai datti saita dauka batareda sanintaba taje tawanke saidai kawai taga takawomata a wanke sannan idan suka dawo gida domin cin abinci sai tai amfani da wannan damar tashiga kitchen tamasu girki, abun yanabama ummi mamaki wani lokacin saitarasa shin aka wane daliline ma yasa take k’in yarinyar nan, itadai d’an zamannan dasukai bataga aibintaba yarinyace mai nutsuwa hankali dakuma uwa uba tarbiyya da ladabi, dikda k’aton cikinda take d’auke dashi amma baihanata yin ayyukanta ba amatsayinta na mace komai itakeyiwa kanta bata tarshe ba tace komai sai ammata tinda cikine da’ita ba dikda kuwa tasan irin sonda sarki da MUJAHID kemata komai takeso zasumatashi amma hakan baisata tazama raguwa ba wajen kula da kanta harma da wani sab’anin asma’u wacca ko wanka badan yazamemata dole ba dazatace shima adingamata,,,….

Nantake acikin k’ank’anen lokaci raayin ummi da k’iyayyarda takeyiwa MUFIDA tafara sauyawa akan MUFIDA yanzu tafara sakewa MUFIDA fuska harma idan tagaidata tana amsamata acikin fara’a da sakin fuska, hakan yabama MUFIDA mamaki matuka acikin k’ank’anen lokaci Allah yakarb’i adduarta wacca tajima tanayi, hakan yasa tak’ara yin d’amara dakuma Kara k’aimi kozata samu fada agun ummi,,,….

STORY CONTINUES BELOW

Tacigaba da cusa kanta agun ummi yayinda kuma take Kara samun shiga agunta yanzu har zama sukeyi gu d’aya dikda bawata fira sukeba, MUFIDA takan baro d’akinta tazo d’akin ummi tazauna tamata shara ta gyara mata gado sannan tazauna tai karatunta idan dare yai tamata saida safe tawuce,, ahankali ummi tasake da’ita yanzu har fira suke, idan zasuje masjid har Qur’an MUFIDA ke rik’amata sai insunje sannan tabata takarba cikin fara’a da murmushi,,,”…..

              *****  *****

Alhmdllh yau saura kwana d’aya kacal sukammala ibadarsu wanda yau kuma itace daren sallan azimi, around 12pm bayan sundawo tai wanka tashirya tawuce d’akin ummi, koda taje tana zaune tana karatun Qur’an, cikin sallama tashiga tazauna saida ta kammala sannan tagaidata ta amsa cikin fara’a tareda tambayarta kwarin jiki tace Alhmdllh,,,….

Suna nan zaune dakyar cikin in ina tafad’amata abunda yakawota, murmushi ummi tai sannan tamata na’am da abunda tazo dashi, tsefa tamata sannan tazauna tamata kitso, bayan sungama sannan tamata lalle ja, wani irin dad’i ummi keji yanda MUFIDA ke kula da’ita tamkar yarta data haifa acikinta, bayan tagama zata wuce sai tadubeta cikin murmushi tace “kai nagode sosai MUFIDA sannu da k’okari Allah imaki albark……”  saikuma tai shuu bata k’arasaba, murmushi kawai MUFIDA tajuya tawuce abunta,,,,……

Washe gari tin 5am tafarka tashiga kitchen tafara girki, abinci tagirka nagani na fad’a wanda kuma tasan ummi da sarki sunfiso dan yanzu ma batadamu data farantawa MUJAHID ba kamar yanda tadamu ta farantawa ummi da sarki, girki tai har kala uku sannan tahada juices kala biyu, bayan tagama sannan takoma ciki tai wanka tashirya cikin wata tsadaddiyar jallabiya black color ammata zanen flower’s da red color saikuma wasu Stone’s da’aka manna silver color, veal d’in rigan tai rolling dashi sannan tasaka nik’ab da takalmanta tad’auki jakarta da phone d’inta sannan tafita,,,”….

Kai tsaye d’akin ummi taje koda taje itama tashirya nanta gyara mata bedsheet d’inta takwashe kayanda tacire nan ummi tak’arasa shiryawa sannan sukafita izuwa masjid domin yin sallar eid_el_fitr,,,  sai kusan 11am sannan  suka koma gida koda suka koma su MUJAHID basu shigoba danhaka sai MUFIDA tajuya domin tafiya d’akinta, harta juya sai ummi takirata tace tazo su zauna anan mana harsu MUJAHID sushigo, batamata musuba kuwa tadawo tazauna, ahankali ahankali kad’an kad’an suked’an tab’a fira harsu MUJAHID suka dawo,,,….

Cikin farinciki da fara’a da nishad’i suka gaisa sannan sukayiwa junansu barka da sallah dakuma fatan ubangiji yakarbi ibadunsu, bayan su MUJAHID sun zauna saitamike tsaye tafita, jim kad’an saigata tadawo d’auke da food flask akan faranti, dasauri MUJAHID yazo yakarb’amata saboda sunmata nauyi kayan hanunta har rawa yake, yana karbawa tasake komawa tad’akko wasu har biyu da plate’s da cup’s da lemonda tahada sannan tazo tasaukesu,,,….

MUJAHID ne yabude abinci nantake wani irin daddad’an k’amshi yadaki hancinsa yai murmushi, tsintsar mamakine yakama ummi saboda sam batasan lokacinda MUFIDA tai wannan girkin mai yawaba “kai lallai wannan yarinyar akwai k’okari akwaita da hak’uri aiki bata gajiya dikda cikinda take d’auke dashi amma kamar bata d’auke da komai kamar batajin wahalar aiki” ummi ke fad’a acikin zuciyarta,, haka suka zauna suka kwashi daddadan girkin MUFIDA sarki da MUJAHID sai sanyamata albarka suke ummi kuwa murmushi kawai take amma zuciyarta cike take da tsintsar mamakin kanta yanda ta tsani MUFIDA batareda tatsaya ta zauna da’ita taga yanda halayenta sukeba,,,”….

     

*________________*

Bayan kwana hud’u dayin sallah sukafara shirin dawowa gida nan suka shiga kasuwa domin yin tsaraba, k’udi sarki yabama MUFIDA masu yawa yace tak’ara tasiyi abunda takeso nan taita masa godiya dakuma kyakkyawar addua,,,….

Washe gari rana ta biyar jirginsu yad’aga izuwa BAGDAAZ, 3:30pm dot jirginsu yasauka, ma’aruf da mai martaba da dakaru ne sukazo tarbansu ma’aruf sai tsokanar MUFIDA yake yana fad’in “gaskiya babbar yaya kink’ara kyau muma gaskiya next year damu zaaje” nan akaita dariya, kai tsaye su MUFIDA gidansu aka wuce dasu aikuwa suna isa tai wanka tai sallan la’asar taci abinci saita kwanta nantake tai bacci saboda gajiya,,,”…

STORY CONTINUES BELOW

Bayan kwana uku da dawowarsu sannan suka shirya sukaje gida, ma’aruf sukafarayin karo dashi zaune tareda dakarunda ke kula da k’ofar shiga sunashan coffee kasancewar ma’aruf mutum ne maison mutane tin yana yaro inkagansa gida to yunwace tamaidashi amma idan bahakaba to yanacan waje tareda mutane sunashan fira shiyasa yasaba dasu har girmansa sab’anin MUJAHID da daga gida sai gida saikwa gun sarki ko mai martaba,,,…

Yana ganinsu cikin fara’a yazo ya taryesu tareda masu barka da zuwa, bayan sungaisa kuma yakoma gun abokanan firarsa sukuma suka wuce ciki, sashen jaddati suka wuce kamar yanda suka saba suna isa MUFIDA tai zamanta anan, hartai kwanciyarta sai MUJAHID yace “my only na tashi muje mugaida ummi ko” shuruu tamasa tana tinani can dai ta tashi tareda fad’in “toh” tasaka hijab d’inta sannan suka wuce,,,…

Koda suka isa sashenta tana zaune kan sallaya tana jan carbi saboda haka suka zauna itadai MUFIDA diktasha jinin jikinta cike take da tsoro tarike hanun MUJAHID gam, bayan tagama saita juyo cikin fara’a da sakin fuska nan suka risina suka kwashi gaisuwa saisukaga tana amsa masu cikin fara’a da murmushi, abun yabama MUFIDA mamaki matuka harsaida mamakinta yakasa b’uya ya bayyana a fuskarta, zama sukai ak’asa sai MUJAHID yatashi yaje yadiboma MUFIDA kayan itatuwanda takesha yazo yafara fere mata yana yankamata tafara sha, suna zaune saiga su Nasmat sunshigo ganinsu MUFIDA a zaune har sunashan fruit’s yabasu mamaki sosai nan suka gaisheda MUJAHID sannan suka kama hanyar shiga d’akinsu,,,…

Har sunjuya sai sukaji ummi tace “a,a bazaku gaisheda yayar takuba ko bakugantabane?” aikuwa sunajin haka sukazo da gudu suka rungume MUFIDA cikin farinciki, aranar anan sashen ummi MUFIDA tawuni saida dare sannan MUJAHID yazo suka wuce,,,”….

Tindaga wannan lokacin MUFIDA tasamu sakewa da ummi saidai har yanzu bawata doguwar fira sukeba sosai amma ita MUFIDA hakanma yamata dadi sosai tinda yanzu su Nasmat har gidanta suke zuwa suwuni kuma su kwana toko ahaka aka tsaya Alhmdllh,,,”….

           *****  *****

Kimanin satinsu biyu da dawowa ma’aruf yadami MUJAHID dan Allah yaje yayiwa sarki maganarsa da munira, MUJAHID kuwa baiyi k’asa a guiwaba yaje yasami sarki yamasa bayanin komai, sarki yaji dad’in zancen matuka yanuna farincikinsa nan yacewa MUJAHID yaje zaije gun mai martaba yafada masa dik yanda sukai zai kirasa shima yafad’amasa nan MUJAHID yai godiya sannan yawuce, kai tsaye sashen ummi yawuce itama domin yafad’amata saidai itakam yana shakku yana tsoron fad’amata saboda yanatsoron yanda zata karbi zancen,,,….

Baiyi sanyaba cikin girmamawa kamar yanda yasaba yarisina yagaidata ga mamakinsa saiyaga ta amsa masa bakamar da ba, hakan yabashi mamaki matuka nandai dakyar cikin in ina yasamu yafad’amata, murmushi yaga tayi sanna tace “ai ma’aruf yafadaman komai Allah i kyauta i sanya alkhairi” tsintsar mamakine ya bayyana k’arara a fuskarsa wanda yakasa boyewa har saida ya bayyana fuskarsa, baki sake yace “ameen” sannan yatashi yawuce,,,….

Bayan sarki yasami mai martaba yafad’amasa, mai martaba ma yai farinciki sosai yanuna jin dadinsa sosai nantake suka yanke shawarar yanda abun zaikasance,,,, acikin kwanakin maganar ta bayyana ta bazama kowa yaji, lokacinda MUFIDA taji tai matuk’ar mamakin yanda abun yakasance musamman dataji abunda ummi tafad’a, tai mamaki sosai yanda ummi tasauya acikin k’ank’anen lokaci,,,….

Acikin kwanakin mai martaba yakira a gida Nigeria yasanarda Abbu zasuzo kuma ga abunda zai kawosu, shima abbu yai matuk’ar jin dad’i ganin zumuncinsu zai Kara k’ulluwa,,,”…

Kimanin satinsu MUFIDA biyu da dawowa su mai martaba suka shirya sukaje Nigeria, tarba ta musamman akamasu wacca basuyi zatoba nan abbu yasaka aka kira masa munira yatambayeta shin dagaske tanason ma’aruf, dafarko shuru tai ganin haka yasa abbu yasake tambayarta nan tafara basa labarin komai, tabbas tanason ma’aruf saidai tanatsoron aurensa, cikin kulawa abbu yasake tambayanta saboda me, nan takwashe labarin yanda ummi keyiwa MUFIDA sam bata k’aunarta tahanata kowa nata ya kusanci MUFIDA hatta MUJAHID dake danta batamasa magana fushi take dashi  kawai saboda ya auri MUFIDA yaki aurar wacca takeso ita ya aura wato asma’u,,,….

Murmushi abbu yai sannan yace “y’ata munira wannan dikba matsala bace indai har dagaske kinason ma’aruf saboda gimbiya zainab ba’itace zata zauna dakeba ba’itace zata aurekiba kuma bataisa tahanamu yin abunda mukesoba saboda itama a karkashin ikon wani take saboda haka ki amsa man eh kinasonsa kokuma a,a bakyasonsa” duk’arda kanta tai takasa cikin yanayin kunya tace “EHH” sai abbu yace “to Alhmdllh dama abunda mukeso muji daga gareki kenan shikenan tashi kije Allah yamaku albarka” ta amsa da ameen sannan tawuce,,,….

A ranar abbu ya’aika d’an aike yaje yafada a gidansu momy mahaifiyarsu munira gobe za’ayi baikon munira saboda a fitarda hakkinsu, haka kuwa akayi washegari around 10am akai baikon munira da ma’aruf dakuna sadaki naira dubu d’ari a kudinmu na Nigeria da jajayen rak’uma biyar da dawakai dakuma d’aurin dabino goma, anan MUJAHID yaroka da’ataimaka asaka lokacin bikin dai dai danasu Rayyan, baamasa musuba kuwa abbu yace ai shima uban d’ane zai iya sakalokacinda yafi so nan aka saka k’arshen wannan watan wanda kuma yake 15th na watan turawa, bayan angama aranar su MUJAHID suka wuce gida BAGDAAZ,,,….

              **********

Rayuwa tacigaba da tafiya inda MUJAHID da MUFIDA sukacigaba da bama cikinsu cikakkiyar kulawa doctur Aysha ma tana nata k’okari sosai wajen kula da lafiyar MUFIDA dakuma abunda ke cikinta,,,”….

Alhmdllh yau sati ‘daya kacal yarage afara gudanarda shagalin bikin ma’aruf da munira, Rayyan da Amira, tini MUFIDA taje taciro kud’inda dadynta yabarmata a accaunt naira dubu d’ari biyar domin yin hidimar biki dayiwa munira dik abunda takeso saboda yanzu itace uwa agareta, bayan tacirosu kuma MUJAHID yasake bata wasu naira dubu dari uku yace tak’ara yayiwa munira dik abunda takeso aikuwa nantaita masa godiya da kyakkyawar addua,,,….

Washe gari takeso tawuce Nigeria saboda kiranda munira da Amira keta kwala mata tazo tazo gashi kuma tanaso taje da munira kasuwa, bayan tashirya komai saita shirya taje masarauta domin tamasu bankwana zata wuce, kwatsam koda taje saita tadda asma’u tazo, wani irin wulak’antaccen kallo asma’u tabita dashi kamin tawuce tareda buga wani mugun tsaki da kallon “zaki gane kurenki nan kad’an”, itakuwa ko kallon inda take bataiba taje gun ummi tacemata gobe zata wuce Nigeria nan ummi tamata Allah kiyaye hanya tareda kyakkyawar addua sannan tawuce,,,…

Washe gari hartagama shiri tana jiran MUJAHID yagama suwuce kasamcewar shine zaikaita airport saitaga kiran wata new number a wayarta, al’adar MUFIDA ne bata daga kiran new number saboda haka tacilla wayar tafita abunta, koda tadawo har kusan 6 miss call’s akamata da wannan number d’in kasancewar tana sauri yasa batamabi ta kan kiranba tafita,,,….

Saida jirginsu yad’aga sannan MUJAHID yadawo gida cike da kewar abar k’aunarsa dakuma d’an babynsa dakullum yake manne dashi………….

Aslm reader’s kuman afuwa dan Allah jiya bakuga posting ba bayan kuma namaku alkawari wlh harnayi har kusan 6 read more kawai ina hawa online message’s suka fara shigowa daga grps dayawa sai kawai wayar tai restored komai ya goge, kuyi hkr dan Allah wlh banso hkb nima ??

About AIS

Check Also

TSINTACCIYA CHAPTER 4 BY NIMCY LUV

TSINTACCIYA CHAPTER 4 BY NIMCY LUV Www.bankinhausanovels.com.ng  Ƙamshin haɗaɗɗan turarensa ne ya daki hancinta wanda …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *