OGA HABEEB COMPLETE BY FADEELA SANI

OGA HABEEB COMPLETE BY FADEELA SANI

                Www.bankinhausanovels.com.ng 


GARIN ABUJA. 
Wani tabkeken Company ne, asamansa ansa,: SANAT YOGHURT.  
Daga k’asan sunan kuma ayi rubutu da k’anan bak’i,  kamar haka, :sanat yoghurt company , zone e apo Abuja. 
tsaye nake ina kallan tsaruwar SANAT YOGHURT company, ina nan tsaye, sai naji wani yana cewa, “Barka da fitowa Oga Habib “. koda na juya dan ganin wannan wanda aka kira da Oga Habib. 
Na makara sai dai  motar da yashiga nabi da kallo, koda na duba motar da kyau sai naga, corolla S ce. 
Motar nabi da kallo, motar black ce, mai pure white glass. 
Gudu sosai motar ke yi. 
Sunyi tafiya mai nisa sosai, dan har sun shiga garin kaduna. 
Tafiya suke sosai, su biyu ne a motar Oga Habib, sai driver shi. 
Habib cikin siririyar muryar shi, mai cike da izza, ya ce, “Bilya tsaya!. 
D’an tsawa ce ya yi maganar, wanannan nature ne na Habib haka yake abisa lurar da nai me. 
Bilya, cikin girmama Ogan shi, ya ce, “Oga Habib Lafiya zamu tsaya anan? kabari mushiga gari mana, kasan yanzu ba ko’ina ake parking ba”. 
Habib cikin tsawa, ya ce, “Bilya na ce kayi drup d’ina anan kana kawo min wasu Questions”. 
Bilya tsayawa ya yi, Habib ya d’auki  faron da yasha ya rage ya fita da shi.  
Bilya driver da mamaki, ya bi Habib da kallo, ya ce, “Oh wai dama gayannan fitsari zai yi ya ke min wani muzurai. 
Habib da sauri ad’an tsorace ya dawo ya na haki alamun kamar yaga wani abun tsoro. 
Bilya driver da sauri ya bud’e ma Habib burfin motar ya shiga. 
Bilya cikin girmama ya ce, “Oga Habib lafiya kuwa? “. 
Habib kamar ba zai magana ba, sai kuma ya ce, “Bilya gawar mutum nagani anjefar”. 
Bilya cikin tsoro ya ta da motar zasu ta fi. 
Habib ya da ka mai tsawa yace, “meye   haka?, baka ji abinda na ce bane!? “.Bilya driver cikin bin umarnin Ogan shi Habib, ya tsaya da motar, ya kalli Habib, ya ce, “Oga Habib zamu d’augawa ne a mota?, kasan fa yanzu rayuwa ba kamar daba, gaskiya ricks ne Oga mu d’auki gawar da…… “. 
Tsawar da Habib ya yi ma Bilya ne, ya sa ya yi shiru. 
Habib cikin d’aga murya, ya ce, “ka fita ka duba min ka gani”. 
Bilya fita yayi kawai dan bashi da yadda zai yi, amma a ainihin gaskiya a tsorace ya fita. 
Bilya cikin tsoro ya fita ya dudduba amma bai ga wata gawa ba. 
Bilya dawo wa ya yi, ya kalli Habib cikin girma, ya ce, “Oga Habib banga gawar kowa ba fa”. 
Habib tsaki ya ja, ya fito daga motar. 
Habib na ta fiya, Bilya na binsa aba-abaya. 
Habib kallan Bilya ya yi, yana nuna mai abinda ya gani, ya ce, “Can me ye? “. Da d’an k’arfi ya yi maganar. Yana nuna gawar mutum da yagani kwance agun. 
Bilya cikin tsoro ya ce, “Oga Habib zamu fa jefa rayuwarmu cikin had’ar…… “. 
Tsawar da Habib ya yi ma Bilya ce tasa ya yi shiru, ya kama bakinsa bai k’arasa fad’in abinda ya ke fad’aba. 
Habib cikin b’acin rai dan ya tsani arik’a jayayya da shi, cikin fushi ya ce, “Your very stopped, ina maga kana quarrel da ni, Bilya baka da wani amfani Wallahi”. 
Idan da sabo Bilya yasaba da fad’an Habib. Hakan yasa Bilya cikin bin Umar nin Ogan shi yak’arasa inda gawar ta ke. 
Bilya cikin al’ajabi ya ke, kallan gawar matashiyar budurwar, Bilya matsawa ya yi kusa da ita sai yaji kamar tana numfashi kad’an-kad’an.Hakan yasa Bilya dawo wa inda Habib ya ke tsaye. 
Cikin girmamawa Bilya ya ce, “Oga Habib ba gawa bace,dan da alamun tana numfashi”. 
Habib batare da ya kalli Bliya ba, ya ce,”ka d’akkota ka shigo mu tafi”. 
Bilya da mamaki ya kalli Habib, amma gudun kar ya yi laifi yasa baice ko mai ba ya bi Umarnin Ogan nashi, ya je ya d’akko ta. 
Habib tashi ya yi ya koma site d’in driver ya zauna. 
Ita kuma Bilya ya shimfid’ar da ita a mazaunin baya. 
Tafiya kad’an ta idasa da su Oga Habib kano. 
Suna shiga kano sun yi tafi bawani sosai ba. Habib ya ce, “Bilya samu gu kai parking”
Bilya tsayawa ya yi, kamar yadda Ogansa ya Umar ce shi, ya ce, “Oga Habib mun tsaya”. 
Wata private hospital Habib ya nuna ma Bilya ya ce, “Bilya ka shiga hospital d’in nan ka kaita”. 
Bilya kamar zai yi kuka, dan shi a ganinsa idan ma tai mako Habib d’in ya ke son yi tom shi yi yi mana da kanshi ba sai ya bashi wahala ba. 
Baliya badan ya soba ya d’akko wannan baiwar Allah da ke kwance kamar matatta ya shigar da ita hospital d’in. 
Bilya na shiga aka amsheta. 
Bilya kallan likitar ya yi, ya ce, “Likita dan Allah tare da Ogana muke, ki bata duk wata kulawa da ya ka mata zan dawo yanzu”. 
Likitar cikin mamaki ta  kalli Bilya ta ce, “Haba bawan Allah  ya za ai bamu sanka ba, ka kawo mana yarinyar da bamu san taka mai-man abinda ke damunta ba, kuma ka ce mana wai za kaje ka dawo. Gaskiya ammana irin haka da yawa anan kano kuma basu dawowa.  gaskiya haka ba zai yuwuba “. 
Bilya cikin rok’on likitar ya ce, “Karki damu Insha Allah ni zan dawo nai miki alk’awari”. Likitar kallan Bilya ta yi ta ce, “sure”. Bilya cikin tabbatar wa ya ce, “Yess am very sure insha Allah “. 
Bilya number shi ya ba likitar ya ce zai dawo ba da dad’ewa ba. 
Bilya fitowa ya yi inda ya yi parking d’in motar Oga Habib, ya shiga. 
Habib bai tambayi Bilya ya sukai ba, shin tana da rai ko bata da rai make damunta, bai tambayi komai ba. 
Shima kuma Bilya ganin bai tambaye shi ba yasa shima yaja bakinsa ya yi shiru. 
Direct inda Oga Habib keda Meeting Bilya ya kai shi. 
bliya na yi parking Habib ya sauka,   hotel d’in da za su yi meeting d’in. 
Lokacin da Habib ya shiga har sun gaggaji da jiran shi, dan harma sun fara fidda ran zai zo, in da  shi Ka d’ai su ke jira dama. 
Habib be fi hour d’aya da shiga taron ba ya fito ranshi a b’ace. 
Habib cikin jin haushi ya bud’e murfin motar ya shiga ranshi da alamun b’ace ya ke. 
Habib na shiga ya kalli Bilya cikin jin haushi, ya ce, “Jamu bar gurin nan aikin banza ai kin wofi”. 
Bilya da sauri ya sa  ma motar key suka bar gurin. 
Bilya cikin jin tsoro ya kalli Habib ganin ranshi kamar ab’ace ya ke, ya ce, “Oga Habib ina zamu”. 
Habib shiru ya yi  ya yi banza da Bilya. 
Bilya cigaba da tafiya ya yi batare da yasan ina zasu ba, so yake ya k’ara tambayar Habib amma kuma yana jin tsoro.   
Wayar Habib ce ta yi ringing, Habib da sauri ya yi picking call d’in, dan ringing tone d’in mommy shi ce. 
Habib cikin sakin fuska da murmushi, dan indai kaga Habib na waya yana murmushi tom mutum d’aya ce, wato Mahaifiyarshi. 
Habib cikin sweet voice d’in sa, ya ce, “Mommyna kina lafiya”. 
Banji mai akaje ba daga can b’angaran sai dai naji Habib ya ce, “Mommy ina hanya fa, na kusa dan Allah kijirani mana”. 
Banji mai Mommyn Habib ta kuma cewa ba, sai ji nai ya ce, “Mommy ki barsu kawai, ni dama nasan bawai maganar kirki bace dan dai ma kin matsamin ne shiyasa nazo, Mommy wai fasaha suke so mu saida masu, suma su rik’a irin yoghurt d’in mu ak’asarsu, Wallahi Mommy tsabar haushi ko magana ban musuba nabar gun, dan dana san  wannan maganar ce Allah Mommy da banje ba”. 
Can b’angaran bajin me ake cewa nake yi ba, sai dai naji Habib nai mata fatan Allah ya dawo da ita lafiya, kuma dan Allah karta dad’e kamar yadda ta yi wannan karan. 
Bilya ko jin wayar Oga Habib ce ta sa ya fahimci, Habib yagama abinda ya kawo shi kano, yanzu Abuja zasu nufa.About AIS

Check Also

A DAREN FARKO COMPLETE

 A DAREN FARKO COMPLETE  Www.bankinhausanovels.com.ng  DOWNLOAD HERE?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *