NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 9

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 9

Www.bankinhausanovels.com.ng 

a bangaran su Zuby  abinda ya faru kuwa shine,

+

kwatsam wata rana suna cikin gidan da suke yin mitin, kamar kullum yadda aka saba, manyan mata suka zo suka zabe su suna tsaka da sheke ayar su, mai gadin su taji ana buga get koda ta bude matan yan sanda ta gani da bazata iya shaida a dadin su ba, ture ta sukai suka kutsa cikin gidan kai tsaye, har cikin katon falon suka shiga inda suka ganewa idan su zahiri take suka shiga jibgar su, ko wacce sai da taji saukar kulki a jikin ta tasan cewa an musu cune, haka yan sandan suka tarasu a guri guda, can na hangi Zuby da Lubancy sai raba ido suke, koda suka fito motocin yan Sanda ne sunkai goma Sha biyar da DSP Sadeeq ya ke jagoran ta, haka aka tarkata su aka kai su sell, koda labari yaje kunnen Abban Zuby ba karamin cikin tashin hankali ya shiga ba duk da alokacin baya Nigeria gashi bikin ta da Maheer a lokacin bai huce saura wata uku ba, ba shiri ya dawo nigeria, bai zarce ko ina ba sai gidan sa, da zuwa direct dakin Mama ya nufa koda ya buda kofa take kansa ya fara juya masa, saboda abinda ya gani, Mariya ce kwance bisa kan gado ga kartai har biyu suna kwanciya da ita, take ya fara ambatar innalillahi wa’inah ilaihi rajiun, haka yai ta ambatar sunan Allah, Mariya

kuwa bata ji shigowar kowa ba sai alamar fita da taji, hakan yasa tace ma abokan shashan cin nata “su dakata, kamar taji alamar mutun” amma sukai burus da ita suka cigaba da aika aikan su, tuni Abba ya kira yan sanda kiran gaggawa, ba’a dauki wani lokaci mai tsayi ba sai gasu, nan ya nuna musu dakin da su mariya suke haka suma aka tarkato su sai police station, anan Abba ya sake ta kuma ya mata Allah ya isa, saboda ta cuce shi kuma ta cucu rayuwar yarsa, yace taje ta gani taci amanar aure, shiko Sadeeq koda yaga Zuby a cikin su baiyi mamaki ba Saboda abokin sa Maheer ya fad’a masa, kuma dama tun sanda sukai fadan-nan bai kuma koma mata ba, hakan yasa da Maheer yace mai ita zai aura bai ji komai ba, Maheer abokin Sadeek ne tare suka gama secondary school din su dake nan Abuja, abunda ya jawo to nan asirin su shine, Sumayya da ake cewa yar leken asirice, ashe kanwar Maheer ce kuma shi yaturo ta tun kamin ya dawo kasar Kamal makocin su Zuby ya fad’a mai abunda yake zargi akan Zubyn, hakan yasa yace kanwar sa tayi basaja taje, abunda basu sani ba har Video tai musu alokacin kuma ita ce wacce ta jefar da takadda a gurin wannan shakatawar, hakan yasa Maheer sanar wa Sadeeq shi kuma ya hada rundunar yan sanda, yayin da Sumayya ta musu jagoranci ta kai su har bakin get din, kunji ta yadda asirin jigagan yan luwadin ya tonu.

koda DSP Sadeeq yazo yana tambayar matan Dalilin dayasa suke yin wannan mummunar dabiar saboda yanaso ya gama hada bayanai ya mika su kotu,

Daga wacce zata ce kawar tace tai sila sai wacce zata ce mijin ta ne baya bata hakkin ta, haka dai ko wacce da abinda zata ce, abinda ya qara bama Sadeeq takaici harda matasan yan mata da bazasu wuce 18 to 19 ba, Zuby dai ba bakin magana saboda yadda take jin kunya ji take kamar ta ha’ka rami ta burne kanta, acikin su wanda yafi tsayawa Sadeeq a rai shine abinda daya daga cikin su tace wai ita da kishiyar ta ne suke yi a gida, har suka shiga cikin wani group na yan madugo zallah, daga nan aka kara buda musu ido, sosai Sadeeq yaji maganar ta dake shi tsoron matan yanzu ya kara kama shi, Allah abin tsoro mata abin tsoro, lalacewar har ta kai ga kishiya ta nemi kishiyar ta, saboda sun maida aure ba  a bakin komai ba, sunyi Fatali da darajar sa sunci mutuncin sa, badon Annabi Muhammad ya roka kar a halakar damu ba, da tuni an dade da kifar damu, saboda duk wani abu da aka halakar da mutane akai muna aikatawa, an halakar da wata Al’umma akan tauye mudu da suke, ku fada min shin yanzu bama tauye mudu? An halakar da wata Al’ummar, akan luwadi, shin ku fada min yanzu bama aikatawa, an halakar da Al’umma da dama saboda yawan sabama ubangijin su, amma ku duba fa maye ba’a aikatawa a wannan zamanin, shan giya caca zina luwadi madugo, tauye hakkin wani zagin shuwagabanni cin amana, rashin yiwa iyaye biyayya, zagin malamai, cin dukiyar maraya, da dai sauran su, Allah ya bamu ikon gyarawa, idan muka gyara muma sai muji dadin rayuwar, haka dai yai ta jinjina lamarin yana yin rubuce rubecansa, a farar takarda, shi wallahi mamakin masu luwadi da madugo yake yi ko mai suke ji a jikin juna, ace wai mace da mace namiji da namiji, masifar tayi yawa dole annoba ta damemu shin ko kun sar masifar da yake haifarwa? Wallahi duk wanda ya mutu yanayi bai tuba ba wuta ce Makomar sa. Dan yanzu abin yayi yawa, iyaye ku saka ido akan yayan ku ku lura da tarbiyar su, ko kawa ce idan tazo wajan yarki kika ga ana shiga daki a rufo kofa wallahi ki bincika, zamani ne Allah ya kawo mu dole sai mun dage mun tashi tsaye akan tarbiyar yaran mu, saboda zaki tabawa yarinyar ki tarbiya rana daya wata shegiyar kawa tazo ta rushe.

STORY CONTINUES BELOW

To bayan kwana biyu kotu aka mika su, inda Alkali ya yanke musu hukuncin shekara goma sha takwas-takwas a gidan yari tare da horo mai tsanani, akace duk wacce hukuncin bai mata ba zata iya daukaka kara.

ita kuwa Mariya da abokanan fasikancin ta hukunci jifa aka yanke musu har sai sun mutu kasancewar su masu aure kuma sukai Zina, oh ni rayuwa ina zaki damu wai kina matar aure wace irin jaraba ce da bazaki kama kanki ki rike mutuncin ki ba, saboda ki samu Aljannar ki Allah dai ya ganar damu.

* * * * * * * * * *

Bayan wasu shakaru haka Rayuwa ta cigaba da tafiya  cikin hukunci Allah gashi har  mun rubuta jarabawar mu ta JSCE,, aminci da shakuwa mai karfi ya cigaba a tsakani na da Fadeela, sosai muke kyautata wa junan mu, dan Ammi komai tare take siyo mana, haka nima komai tare yah Sadeeq ke kowo min idan zai zo min bizitin, haka idan nice naje gida idan zan dawo hutu komai biyu nike zuwa mana dashi, dan sau biyu su Momy da Inna suka zo min, na kyara girma na ban mamaki ni kaina mamakin yadda nai girman nike, idan ka ganni sai kace na kai irin shatakwas din nan, ga wayau na masifa da nai, sosai kama ta da Ammi take kara bayyana, dan dalibai da dama ce min suke diyar firinsifal.

na hadu da Sadiya kanwar yah Farooq a lokacin da yaya Sadeeq yazo min bizitin yasa aka kira ta, itama tun daga ranar muke zumunci amma ita ba hostel dinmu take ba, duk inda ka ganni zaka ga Fadeela da Sadiya haka ake cemana yan ukun Firinsifal, dan da angama karatu muke zuwa ofishin ta, sosai yanzu nike jin turanci dan ko magana da hausa ban fiye yi ba, dan jina nike babbar yarinya.

Senior Jamlah kuwa sun bar makarantar, sunyi candy, kuma koda tana nan ma, ban bari ta dake ni ba, dan kuwa karar ta nakai staff sai dai zagi da tsangwama idan mun hadu, sosai school Momy na Saudat take kula dani, shiyasa ban wani sha wuya ba gashi yanzu har zan barta.

Yau ne muke zana fefar mu ta karshe kuma cikin azumi ne home economy ne ya bada wuya gaskiya, duk wacce ta fito hol zakiga tana goge gumi, bayan na gama na fito na iske Sadiya zaune na jiran mu, nan muka shiga farar yadda fefa tai zafi, muna cikin firar sai ga Fadeela nan itama tace, “wash rabon da fefa ta bani wuya irin na yau wallahi na manta ku tashi muje mu shirya, dan da alamar wasu daliban ma sun fara tafiya”.

hostel muka mufa inda a hanya muke ta haduwa da class mate din mu da akazo daukar su , dama duk munyi musayar numbers saboda dayawan wasu daga cikin mu ba nan zasu yi senior ba,

Ahaka muka karasa hostel muka shiga hada kayan mu bayan mun gama muka raka Sadiya itama ta hada nata.

Office din Ammi muka je, da sallama dauke a bakin mu muka shiga inda muka same ta a tsaye tana hada takardu, bayan mun gaishe ta, tana dariya ta kalle ni tace Yata duk kinfi kowa kosawa ko duk zumudin za’a Dande ne? tunda kince acan zakiyi Sallah”

Dariya nai kasa kasa nace, “Allah Ammi ba haka bane kawai kewar gida nike”.

Tace “ai na gama ku tashi mu tafi gida daga can sai mu dauki hanyar Abuja”

Dama tuni nayi waya da Yah Sadeeq nace ba sai yazo daukar mu ba, Ammi zata kawo mu, dan tace “tana son zuwa ta gaida Inna saboda ina yawan bata kabarin ta”

A tsakar gidan su Fadeelah muka tarar da kannen ta yan biyu wato , Aysha suna kiran ta da little easha sai Aliyu suna ce mai Dady, haka yaran suka taho suka rungume mu dama mun saba dasu dan ina zuwa gidan idan anyi mana hutu yaya bai zo daukana da wuri ba, muna wasa da dariya muka karasa falon gidan, ciki Ammi ta shiga dan ta shirya haka ma Fadeelah, ya rage da gani sai Easha da Dady da Sadiya sai wasa muke, ahaka Ammi ta fito ta iske mu tace “ina Fadeelan?”

Sadiya ce tace “bata fito ba”

“Fadeelah Fadeelah” Ammi ta kwala mata kira, sai gata ta fito itama tayi fes da ita cikin shigar wata atamfa mai tsadar gaske, atamfar tana da kaloli da yawa a jikin ta mai digo digo, yayin da ta yafo mayafi brown, haka jakar ta da takalmin ta duk brown soboda akwai brown a jikin atamfar, duk da Fadeelah ba fara bace amma tayi mutukar kyau, yayin da Ammi ke sanye da doguwar riga yar dubai mai ruwan kasa ta yana mayafin ta fuskarta sanye da siririn gilashin ta na lura bata rabo dashi, dan ga little Easha nan duk sanda zan ganta itama dashi nike ganin ta,

STORY CONTINUES BELOW

Ammi ta kalli Fadeelah tace “dadi na dake nawa duk sanda aka shirya tafiya kece a baya”.

Fadeelah tace “haba Ammi yanzu haka na dade?”.

Ammi bata kula ta ba tace “ku tashi mu tafi rana na dad’a yi”

Dama su little Easha a shirye suke saboda haka muka dauki hanyar Abuja, a hanya muka tsaya a restaurant muka siya abinci mukaci, da misalin karfe biyar na yammacin ranar juma’a muka isa makekyan gidan su Khadija, yayin da Ammi tai hon mai gadi ya bude mata ta sulala ciki, gurin faking din motoci tai faking kana ta bude mana kofa, da gudu na fito ina ihu na nufi cikin gidan Momy da Ummi na tarar zaune suna cin kayan marmari a falo, fadawa cinyar Momy nai, itama kamani tai tana min oyoyo, ban tashi daga kan cinyar ta ba sai ga Ammi ta shigo bakin ta dauke da Sallama, koda Momy ta dago kai da Zimmar amsa sallama, sai tai maza ta tureni ta Mike tana fadin “Amina” ita ma Ammi idon ta zaro tace “Aisha” kollon kallo muka fara bin su dashi, ganin kowannen su idon sa na zubar da kalla, a dai dai lokacin Yah Sadeeq ya shigo gidan ganin Momy da Ammi na zubar da kwalla yasa yai turus yana jimami ya karaso falon.

Ganin basu san ma ya shigo ba yai gyaran murya yace “Ammi Momy ku zauna mana lafiya”

Momy ce tai karfin hali tace “dan Allah ku fada min mafarki nike ko kuwa ido na biyu ne Amina ce fa kanwar Daddyn ku goggwan ku Amina ce fa”

Ni kuwa da naji an ambaci Amina mikewa nai zunbur ina dad’a kare mata kallo, a cikin wannan yanayin Daddy da Umar suka iske mu, koda Yaga Ammi take yashiga murza ido yana fadin “Aisha Aisha kina ganin abinda idona yake gani ko kuwa gizo din take min kamar yadda ta saba?”

Momy tace “ba gizo take maka ba Aminan ka ce ita ce”

Take muka ga Daddy ya fadi yana mai sujja ga Allah, bayan ya dago yazo ya rungume Ammi, nan fa dakin ya kaure da koke koke baka jin karar komai sai shash-shekar kuka, harda su little Easha mukai ta kuka wuy-wuy shi kuwa Sadeeq ba hawayan amma idon sa yai jajur, mun dauki lokaci mai tsayi muna yi daga bisani yah Sadeeq ya shiga bamu hakuri, to bayan komai ya lafa Ammi ta samu guri ta zauna,

ni kuwa tashi nai na haura sama, dan na samu nai wanka na canza kaya, dakin Khadija naje dan na amsa mukulli na amma sai naji kofar ta a rufe, hakan ne yasa na nufi ban garan yah Sadeeq, nayi sa’a a bude na samu kofar, koda na shiga ban zarce ko ina ba sai bathroom din sa, ina shiga na hada ruwan wanka, koda na fito kamshin turaran sa dana ji ne ya tabbatar min da yah Sadeeq ya shigo, ina waigawa na gansa zaune a bakin gado, ya kura min ido, kunya ce ta kamin saboda tawul din dana daura dan karami ne ko cinya ta bai gama rufewa ba, na kasa dago kai na kalle shi, shi kuma ya kasa dauke kai daga gareni, hanyar fita bedroom din nayi amma sai naji kofar a kulle gam, jiyowa nai na kalle shi yana Murmushi yace “ina zaki bayan na rufe kofar ai tun na shigo na fahimci kina ciki da naji alamar ana wanka, nasan babu mai shigo min daki sai ke, shiyasa na rufe kofar dama a yunwace na dawo, ashe zan samu mai kore min kishin ruwa na”

Gaba na ne ya shiga buguwa dan yanzu sarai nasan maye aure kuma nasan abinda yake faruwa a tsakanin miji da mata, ji nai kamar an samin shokin na kasa gaba na kasa baya, haushin kaina ya kamani dana shigo bangaren sa, taku naji anayi da sauri na juye tsaye na gansa gaban madubi yana cire kayan jikin sa, gabana ya cigaba da faduwa, na shiga yi masa magiya, amma ko kala bai ce min ba, ya shige bayi abin sa, ya dauki lokaci mai tsayi can sai gashi ya fito da tawul daure a kugun sa, ba karamin kunyar sa bace ta kamani amma shi sai naga ko a jinkin sa, gefe na kawar da kaina saida ya gama shiryawa yazo gabana, kama hannu na yai yazo ya zaunar dani akan bakin gadon, shima ya zauna muna fuskantar juna yace “nasan yau rana ce ta farinciki a gareki, saboda Allah ya amsa adduar da muka dade munayi, ina tayaki murnar haduwa da mahaifiyar ki Siddeeqerh” ni dai ban ce mai kala ba, ya daura da “gashi kuma kin zana JSCE din ki shima ba karamin nasara bane”. hannu na ya kama ya fara murza tafin hannu na, nai sauri na kwace ina fadin “maye haka yaya ka buda min kofa na fita kada aga na dade, nasan yanzu sun fara nema na ga yunwa inaji, yace ” to ai banga magana ba amma ya jarabawar da dadi ko?”

Nace “eh Alhamdu lillah”

Kirjina naga ya kurawa ido nai sauri na sa hannu na ka kare nace “wai yaya maye haka kasan dai matar wani ce ni amma duk kabi sai kura min ido kake”

Banyi aune ba naji ya hada baki na da nasa yana tsotsa nayi ta kokarin kwacewa amma na kasa saboda yadda ya matseni a jikin sa. Saida ya gaji dan kansa ya sakeni yana maida wahalallan numfashi

Ni kuwa nayi tsuru-tsuru kamar wacce ruwa yaci ta.

Idanuwan sa sun kada sunyi jawur yace ” wannan shine Punishment din da zan dunga miki aduk sanda kika kara ambata min wani” yana gama fada ya mike a kasalance ya bude kofar, ina ganin haka na zura a guje, yai saurin kamo ni yace “ke wai har yanzu baki yi hankali bane? Banason naga mace na gudu ki kama kanki baki san kin girma bane?”

“naji” na fada ina kunkunai nace “sakeni to”

Naci sa’a ban hadu da kowa ba direct dakin Ummi na zarce, ina shiga dirowar kayan ta na bude na dauko doguwar riga yar kanti mai ruwan madara, da sauri da sauri na kintsa na fito. Saboda na kosa na kara ganin Ammi a matsayin Mahaifiyata…______Koda na sauko zaune na samu su Easha da Dady karami da Umar afalo suna wasa, bayan na zauna, na shiga tambayar su Ina su Ammi Little Easha tace “suna dakin Momy”.

+

“to” nace na mike na nufi part din Momy baki na dauke da sallama na kusa kai, a zaune na same su cikin dan karamin falon ta. Da alamar tattaunawa suke, nan kasa na zauna gurin Daddy nace “Daddy ina yini bamu gaisa ba “

Yace “lafiya lau Siddeeqah ya makarantar?”

“lafiya lau Daddy”

Yace “an kare ko yanzu sai cigaba?”

Nace “eh Daddy amma gaskiya ba makarantar kwana zan koma ba na gaji”

Yace “to shikenan nima nayi tunanin haka, kuma lokaci yayi da zaki tare a gidan mijin ki in yaso sai ki cigaba da karatun acan” kaina a kasa ni dai ban

ce komai ba, na mike ina tambayar Momy Khadija, tace ta aiketa gidan kawar ta Hajiya Nafisa ,” to” nace nan na bar su na fito, kitchen na shiga dan na taya Suwaiba aikace-aikacen kayan shan ruwa dan naga kamar aikin zai mata yawa ita kadai, munayi ina mata firar makaranta, a haka Ummi da Fadeela suka isko mu.

Muna nan kitchen din Sadiya tazo tai mana sallama direban su yazo daukar ta, nace mata “sai mun hadu a Dande”

“to” tace tana dariya ta tafi

da dare misalin karfe 10:00 pm dukkanin mu zaune muke harda yah Sadeeq, da yah Mubarak wato yayan Ummi, kuma shine zai auri khadija, tun wata biyu da suka wuce ya kare karatun sa a harkar computer, yanzu haka aiki yake a karka shin wani company, kowannen mu kagani fuskar sa dauke da annuri, Ammi ce tace “Yaya Ali wai yaushe zamu je Dande ne dan na kosa naga Inna na wallahi nayi kewar ta” yana Murmushi yace “ki kwantar da hankalin ki nan da Jibi ma sai mutafi in yaso dukkan ku sai kuyi sallah acan tunda sallar saura kwana biyar, dakanan ma ayi maganar tarewar yarinyar nan da kuma bikin Su Khadija”

Ammi tace “to shikenan Allah ya kaimu”

Da lokaci bacci yai nace “dole Ammi a dakina zata kwana”

itama dama tana son kebewa da diyar tata, yayin da Fadeela tace ita A dakin Ummi zata kwana saboda jinin su ya hadu , Jiddah kuwa tace ita da Little Easha zata kwana dan itama jinin su ya hadu, Dady karami kuwa cewa yai tare da Umar shi zai kwana, Khadija na dariya tace yanzu ni ba Wanda zai kwana dani ai shikenan, sai mun hadu da asuba “

Tana gama fadar haka ta haura sama, muma da daidai da daidai mukai ta watsewa.

Nida Ammi a daki fira muka dasa ta tsakanin ‘ya da uwa ina kwance kan cinyar ta nike ce mata” Ammi wallahi Abba na bai da mutunci kamar bashine ya haife ni ba” Ammi tai saurin toshe min baki tace “ki daina fadin haka koma yaya ne dole ki bashi kima da daraja saboda shi din mahaifin ki ne” na ce amma fa Ammi tun nataso ban sanshi ba ban taba ganin shi ba, bai taba turo dai dai da naira goma yace a saimin sabukun wanki ba, Daddy ne ya tsaya min tsayin daka akan komai na rayuwa ta, sai Momy Allah yai mata Albarka wallahi tana kula dani, ko ita ta haife ni sai haka dan ba’a taba nuna min banbanci a gidan nan ba, haka fa lokacin Aure na da Daddy yaje kar kiga yanda Abba na yaci mai mutunci nan dai ta kwashe labarin komai ta fada mata, idon ta cike da kwalla take ce min “nayi hakuri ba yin kansa bane asiri ne amma Abba na yana mutukar so da kauna ta insha Allah nan bada jimawa ba komai zai zo karshe”.

Bayan kwana biyu ya kama ranar zamu je Dande lokacin Sallah sauran kwana Uku da misalin karfe goma na safe dukkanin mu a farke muke kowa sai shiri yake bayan mun gama shirya wa, mota uku mukayi da Ammi da Momy da Daddy babba da Umar da karamin Daddy mota guda suka shiga, yayin da Khadija da Jiddah da little Easha suka shiga motar yah Mubarak, ni da Ummi kuwa motar yah Sadeeq muka shiga inda na zauna gidan gaba Ummi na gidan baya muka dauki hanyar Dande sosai yah Sadeeq ke tsulala gudu ahanya, na lura dashi yana son gudu a mota, mu dai Allah ne ya sauke mu lafiya, duk da idan nai hutu ina zuwa Dande amma ba laifi ta dan samu canji dan yanzu haka ana basu wutar nefa kuma asbitin bayan gari an dan gyara shi, a kofar gidan Inna mukai farking da futuwar mu yaran unguwa akai ta kallon mu ana ga yan Indian nan sun zo, sau tari dama ni haka suke ce min yar indiya, dayin fakin din mu, sai ga motar yah Mubarak nan shima ya danno kai, muna kokarin shiga saiga motar Daddy nan ita ma ta kunno kai haka muka dunguma gunin ban sha’awa da burgewa yaran layi kuwa sai kallon mu suke,

STORY CONTINUES BELOW

Bakin mu dauke da sallama muka shiga, babu kowa a tsakar gidan saboda haka muka dunguma cikin falon Hajiya Inna, a zaune take tana kallon talabijin “tsohuwa mai ran karfe” na fada yayin da na isa gare ta na fada kan cinyar ta.

Tana dariya ta baka min duka tace “dagani ja’ira kada ki karasa ni”

Turo dan karamin baki na nai nace “inna ki dai ji tsoron Allah yanzu ni ina naga nauyin da zan karya ki”

Kallon mu inna ta shiga yi daya bayan daya kana tace “Karami wa nike gani wannan kamar Amina na? Ko ido na ne kuma wa’innan yaran na waye?”. Wato su little Easha da Fadeela take nunawa.

TA dora da cewa “ko tsufan nawa ne yake rudar dani Karami?”. Ta ambaci sunan Daddy 1

Da gudu Ammi ta isa ga Inna ta rungume ta tana cewa “nice Inna nice Aminan ki ce”

Sai hawaye shar-shar yai ta zuba daga idanun inna jikin su Daddy yai mutakar sanyaye suka samu guri suka zauna

Inna sai sumbatu take tana cewa “ashe da rabon mu gana ashe da rabon zan sake ganin ki, bayan wa’innan shekarun, dama ni ban fidda rai ba kullum cikin addua nike ina rokon Allah idan kina raye Allah ya bayayyana mana da ke, Allah maji rokon bayin sa gashi ya amsa mana, jikin kowa yai sanyi nan mukai ta taya Inna kuka ba mai lallashin wani saida mukai mai isar mu, sannan mukai shiru,

Cikin kuka mai tsuma zukata, Ammi tace “Inna ku yafe min nasan na tafi na barku cikin matsanancin tashin hankali nima ba a san raina nayi ba, alokacin ban san inda hankali na yake ba, ni dai nasan kafin faruwar abun Habiba kiyasha ta tazo daki na, ina hada ido da ita naji gabana yai mummunan faduwa daga nan tace min “dauki shegiyar yarinyar ki ki kaima uwar ki banason na kara ganin ki arayuwa ta ki tafi nesa da wannan garin, sai na same ni da bin umarnin ta ban dauki komai ba sai mayafi na, na saba Siddeeqah a kafada na fito, a harabar gidan naga Alhaji Sulaiman, kallo daya na masa naji na tsane sa, haka na wuto shi yana so yai min magana kuma ya kasa, idon sa cike da kwalla na bude get na fito, ban zarce ko ina ba sai gidan ki Inna kina gani nana ki ka shiga tambaya ta lafiya? Me yasameni amma ban ce miki uffan ba na aje miki Siddiqah na fito, tafiya nai mai nisa da kafa ba tare da nasan inda na dosa ba, yamma ta fara yi saboda haka dare ya fara lillbe yini nagaji ga yunwa ga kishin ruwa, nan na zube a kasa gefan kwalta, wani mai mota ne yazo wucewa da ya ganni ya taimaka ya dauke ni, bayan ya sakani a mota asbiti ya kaini, bayan sun gama duk wani gwaje gwajen su basu ga komai a tare dani ba illah yar yunwar da ta galabaitar dani, kwana na biyu a asbiti aka sallame ni, wannan mutumin ya dauke ni kamin nan tun a asbiti yake tambaya ta, akan ya suna na kuma ina ahali na, amma babu uhm babu uhm uhm, sai dai nai ta bin sa da ido, hakan yasa ya fahimci ba kalau nike ba, da yike babban malami ne, shine fa ya dauke ni ya kaini gidan sa gurin matan sa anan garin katsuna, inda sukai ta nema min magani har Allah cikin ikon sa ya bani lafiya, bayan na dauki tsayin sheru bana ko magana, to bayan na warke na dawo hayyaci na ya tambaye ni ahali na ko suna ina, sai na tsinci kaina da ce mai bani da kowa sai Allah sai kuma kai, to bayan kwana biyu yazo min da maganar aure, nace masa ni da ba fita nike ba ina zan samu muji?” yace” indai wannan ne bashida matsala zai samo min mijin aure na kirki wanda zai rike ni amana “

Bayan sati guda ina zaune a daki na sai gashi yazo yake cemin” ya daura min aure, yanzu haka tare da mijin nawa yazo kuma dani zai tafi saboda haka na tashi na shirya “

Haka dai na baro gidan Mlm liman ba dan raina yaso ba nabi Alhaji Imran, wato baban yarannan

Ammi ta fada tana nuna su Fadeela

TA dora da cewa, nayi zama na amana da margayi, yana yawan tambaya na Ahalina amma sai nace” ni bani da kowa “.

Na rasa kuma dalilin da yasa nike cewa haka dan ko tunanin wani nawa ma banayi, cikin ikon Allah na haifi yarana yan biyu mace da namiji masu kama da Daddyn su, ya tambayeni shawara akan sunan da zamu sa musu nace” Asa min Aisha da Aliyu “.

Haka rayuwa ta cigaba bayan wasu shekaru ina zaune a office dina saiga Sadeeq da Siddeeqah nan sun shigo, tunda na kalle su na fara tuno da iyali na kuma naji ina kwadayin na sake haduwa dasu, tunda naga Sadeeq naji a jiki na dana ne haka itama Siddeeqah, sai naja ta ajiki na ta yadda take yawan bani labarin ku, hakan yasa na kara tabbatar da tabbas ita din jini na ce, amma sai ban taba nuna mata ba, nasha tambayar ta ina mahaifiyar ta? ” sai tace min” mahaifiyata ta bata tun ina yar karama kuma har yanzu bamu san inda take ba ” hakan yasa na kara jin kwarin gwuiwa shine fa da akai hutu nace ta bari zan kai ta”.

Ta numfasa tace “wannan shine takaitaccan abun da ya faru bayan rabuwa ta daku”.

Inna tace” wannan fa?”

Fadeela take nufi

Ammi tace” marainiya ce mahaifiyar ta ta rasu wajan haihuwar ta, kuma yayar su Easha ce da suke uba daya”.

Daddy yace “naji kina cewa margayi yanzu shi Alhaji Imran din ya rasu?”.

Wasu hawaye ne masu zafi suka zobo wa Ammi tace “eh ya rasu a sakamakon hadarin mota da yai”.

“Allah ya jikan sa su Daddy suka ce”

Wannan kenan

Bayan ko mai ya lafa Ammi da Momy suka tambayi inna abinda za’a sha ruwa dashi?

Tace su bari Garba ya siyo tunda yanzu yamma tayi, ga gajiyar mota

Bayan kwana biyu ya kama jajibari, mayafi na na saba nace “Inna zan fita” tace “zuwa ina kuma keda ba kya iya zama a guri daya?”

“gidan Ladiyo man tun nazo ban leka ta ba fa”.

“to a dawo lafiya” inna ta fada ni kuma na fice a buna

A soro naci karo da Yah Sadeeq, bayan ya kare mun kallo yace” ina zuwa?”.

nace” gidan kawata Ladiyo zani “.

” kuma da izinin wa” ya jefo min tambayar

“inna mana” na fada a takaice

“to bazaki ba ki koma”.

Kallon in ka isa na mai na fice a bi na

karasawa cikin gidan yai ransa a mutukar bace ya fara masifa saboda duk suna tsakar gidan, fadi yake “wai Inna akan me zaki bama yarinyar nan dama ta dunga gantali, da aure na a kanta”.

Momy ce tai caraf tace “eh lalle ma Sadeeq, yanzu ne kasan da ita din matar ka ce yanzu ne kaje jin haushin yawon da take yi? To tun wuri ka fita ido na bazaka takura ma yarinya ba”.

Ammi da ke wanke wakan da za’a kosai dashi tace “Haba Momyn yara ai da gaskiyar sa, tunda shi ba sakaran na miji bane taya zai bar iyalin sa sakaka a gari? Ina goyan bayan sa kuma bari ta dawo sai naci mutuncin ta, na kara ganin ta fita ba da izinin sa ba _______zaune nike a dakin Ladiyo muna firar mu gunin ban sha’awa sai wasa da dan ta Mamman nike yi, tace “wai ke Siddeeqah yaushe zaki tare a dakin mijin ki ne?”+

Nace “waya gaya miki zan tare? Nida nike jira ya bani takarda ta naje na auri wanda yake kauna ta”.

Bakin Ladiyo bude tace “amma dai baki da hankali, a wannan zamanin ka samu miji irin yah Sadeeq ai ka more, ke sune fa irin mazan da ake bada labarin su a novel, amma kike nema kiyi fatali da damar ki”.

Nace “bazaki gane bane, mubar maganar kawai” bayan na bata kyautar kudi nai mata sallama nace “taya kuri nazo mata da kaya sai na bude a kwati na zan kawo mata”

Gadiya tai min har bakin zaure ta rako ni

A hanya na hadu da wani mai naci tun na fara tafiya yake bina yana min magana amma ban kula shi ba.

Har bakin kofar gida ya rako ni inda yah Sadeeq da Yah Mubarak ke zaune suna fira, da gani na Sadeeq ya hade rai kamar ya hangi mutuwa, tasowa yai ya nufo mu kan ya karaso na shige gida ban san ya ya kare da mai bin nawa ba.

Koda shiga na gida Ammi ta hau yin sababi Momy na kare min nan na barsu nai cikin daki na inda na samu Fadeela na ta sharbar baccin ta. Jiddah na zaune na chat Khadija kuma na ninke kaya.

Bayan na cire mayafina na zauna kusa da Khadija ina taya ta ninkin kayan

Jiddah ce ke cewa “yau fa aunty Bilkeesu zata zo”.

Khadija tace “au haba na dauka sai ranar Sallah”

“A a yau ne” ta bata amsa

* * * * * * * * *

Yau take sallah bikin daya rana gidan mu cike yake da yan uwa da abokan arziki da makota, anci ansha yara nata har kokin su. Wa’inda suka san inna da dadewa suna ta taya ta murnar bayyanar diyar ta.

AUNTY balki sai tsokana ta take wai yayan su zai kamani.

Little Easha ce ta shigo tace “aunty Siddeeqah yah Sadeeq na kiran ki”

“To” nace amma ban tashi a lokacin ba sai da na gama shan kanshi na

Ina ta raba mutane har na wuto falon. Shima tsakar gidan cike yake da mutane suna cin abinci gunin burgewa.

Dakin yah Sadeeq na nufa bayan nayi sallama ai min izinin shiga na shiga.

Tasowa yai ya maida kofar ya rufe kana ya kama hannu na ya zaunar dani bakin katifar sa yace ” na gaji ne shine na kira ki ki mun tausa”.

Dago kai nai muka hada ido ya daga min gira gajeran wando ne a jikin sa sai rigar shan iska wato bes fuskar sa kuwa dauke take da saje ga dan gemu ya aje gunin burgewa.

Kwanciya yai yace ” fara nana ” ido na zaro waje nace “yaya me zan fara kuma? Wallahi ban iya ba”

Tashi yai ya zauna yace “to shikenan bari na gwada miki inyaso sai ki min yadda nai miki “.

Da sauri nace na iya ba sai ya min ba amma yace “Allahn kashe sa sai ya gwada min”

Ya na iya haka ya Sadeeq yai ta jagwalgwala ni, tun yana yi cikin hankalin sa har ya fara fita hayyacin sa dan kokari yake ya rabani da kayan jiki na.

Kuka na sa masa ina magiya akan ya rabu dani ” ganin haka yasa ya sauka daga kai na yai gefe idon sa a rufe yana jin marar sa na murda masa, take ya fara juyi yana kiran sunan Allah, yanzu na fahimci dalilin wannan ciwan na yah Sadeeq da tun ina karama naga yana yi, amma gaskiya bazan iya basa kaina a wannan halin ba, ganin ciwan nasa na kara tsanan ta yasa na mike da hanzari na fita daga dakin, a tsakar gida na hadu da Ammi, ta ganni kamar bana cikin hayyaci na tace “lafiyan ki kuwa duk kin sukurkuce?”

STORY CONTINUES BELOW

Nace “Ammi ba lafiya ba yah Sadeeq ne gayican a daki sai hankoran mutuwa yake”.

Ban gama rufe baki ba Ammi ta nufi dakin sa da sauri.

Ni kuma cikin hanzari na karasa falo, lokacin mutane sun ragu sosai a falon Cikin tashin hankali nace “Momy yah Sadeeq fa baida lafiya gayi can cikin wani hali”.

Duk da tausayin Sadeeq ya kamata amma sai tace “shi ya sani ita babu ruwan ta “

Inna ce tai ta mata fada da kyar taje dakin sa, amma tana ganin sa taji yayi bala’in bata tausayi.

Mubarak Ammi ta kira ya kama shi akasa a mota Ammi da aunty Balki suka shiga don su kai shi asbiti. Suna zuwa aka amshe su cikin kulawa aka kai Sadeeq dakin da ake duba mara lafiya kai ka ce baya numfashi ne, bayan komai ya lafa Likatan yazo inda su Ammi ke zaune yace ta same shi a office.

Zaune take kan kujera likitan yai mata bayani kamar haka “Hajiya gaskiya idan ba so kuke ku salwantar da rayuwar yaron ku ba to kuyi masa aure dan banga dalilin da zaku aje matashi kamar wannan babu mata ba, ina tunanin ma ya girmeni, amma ni yanzu haka ina da mata da yarana guda biyu, kuma ba wannan ne karo ne farko da yake yin irin wannan ba, magunguna yake sha da zaran yaji irin yanayin, to ahalin yanzu ya ruga ya kai makura wa’innan magungunan sun daina masa aiki, aurar dashi ne mafita gaskiya “.

Kalaman dakta ba karamin rikita Ammi sukai ba, abinda yafi tsaya mata arai shine da doktan yace” zasu iya rasa shi” tabbas dole ta dauki mataki dan bazata zura ido haka ya faru ba, ta gama yanke hukuncin tana komawa gida zata kira Daddy ayi maganar tarewa.

Haka kuwa akai Ammi na zuwa gida ta kira sa a waya ta sanar mishi, ba tare da kowa ya sani ba yace “to shikenan zai shigo nan da kwana biyu su fara shirye shirye”

Bayan kwana biyu Sadeeq ya murmure sai dai ya dan fada kuma yayi wani iri dashi, yasha aiko Samaheer ta kirani sai nai watsi dasu, dan badani za’a dunga tsanan cewa ba

Yau ne Daddy zai zo sai shirye shiryen hada Abinci Ammi keyi Momy na taya ta.

Bayan Daddy yazo sun tsaida magana akan nan da sati buyu zan tare, sunce daga baya a saka ranar bikin Khadijan, amma kuma Ammi ta roki Alfarma akan tanaso ta kaini naga mahaifina kamin lokacin bikin, sosai Daddy yaji dadi kuma yayi farinciki da kanwar sa tayi wannan tunanin.

Wata ranar Juma’a muka shirya, Ammi tace naje na fada ma Yah Sadeeq dan shi zai kai mu, koda nagan sa ba karamin tausaya masa nai ba saboda yadda ya zama wani iri kamar ba yah Sadeeq dan gayu da kwalisa ba, nesa dashi na tsaya nace “Ammi tace idan ka shirya kazo ka kai mu”

Ban jira amsar sa ba nayo waje abi na

Unguwar barnawa a bakin wani katon farin get yah Sadeeq ke danna hon can mai gadi ya leko ganin bakin fuska ya ce su waye anan, koda yaji Muryar Ammi tayi magana tace “Nice Hajiya Amina ce” take ya shaida ta yana fadin “Allahu akbar Hajiya ashe zamu sake haduwa”.

Bude mana get din yai muka sulala ciki

A dai dai lokacin wani dattijon mutum mai sanye da manyan kaya ya fito daga motar sa ganin bakuwar mota a cikin gidan sa yasa yai turus, Jim kadan ni da Ammi da Sadeeq muka fito, ido na ya sauka akan kyakkyawan dattijon da nike kyauta ta zaton shine mahaifina, nuna mu ya shiga yi yana daga hannu sai ya bude baki yai magana sai ya kasa, addu’ar neman tsari yai ta karantawa a cikin zuciyarsa kamin ya ce “Amina”

Ido cikin ido Ammi ta kallesa tace “Suleiman”.

A kuma dai dai lokacin wata bushash-shiyar mata ta fito ganin mu tare da Abba na yasa ta cire dan kwalin ta ta fara ihu tana kururuwa cewa take “ta shiga uku yau asirin ta ya tonu Amina da Sulaiman sun hadu”. kuma boka yace ” muddin suka hadu to fa asirin kanta zai koma haka dai tai ta simbatu sai yaran gidan duk gasu sun fito, sunji uwar su na hauka.

STORY CONTINUES BELOW

Koda na daga kaina wa zan gani senior Jamlah ce rike da wannan me haukar tana daura mata dan kwalin da ta kwance.

Kallon Abban mu nayi sai naga yana kama da Jamlah, a cikin zuciya ta nake cewa “kenan Jamlah blood sister na ce shiyasa tun a makaranta naji na tsane ta, ashe ba banza ba mamar su ce ta tarwatsa min farinciki na ta hanani tasowa a gaban iyaye na”

Take Abban mu yai waya da masu kama mahaukata yace “an sumu a gidan sa”.

Babu bata lokaci sai ga masu tafiyar da ita su zo, yaran ta guda biyar sai kuka suke Abba yace “duk wanda zai bita ya bita ga hanya nan” yana gama fadar haka ya ce “Amina kuzo mu shiga daga ciki “

NI DA YAYA SADEEQ kuwa kamar wa’inda ruwa ya cisu dan mamaki, wato dai inda ranka baka daina kallon abun al’ajabi ba, kuma Allah ba Azzalumi bane sai dai bawan da ya zalincin kansa.

A wani kayataccan falo muka zauna da ganin Abban mu yana cikin faran ciki dan ya kasa zaune ya kasa tsaye.

Jamlah ce ta shigo da yan kannan ta na biye da ita sai kuka suke kamar wa’inda akaiwa mutuwa, Abba ne ya daka musu tsawan yace “wai bana ce muku duk wanda bazai zauna ba ya bita? abinda ta Shuka ne ya koma kanta, kunga dole ta girbe shi. kuma dama ramin mugunta ka gina sa daidai da kai saboda wataran kaine zaka fada”.

Sai a lokacin Jamlah ta lura dani, da alamar tayi mamakin gani na tace “Siddeeqah kece”

Ban bata amsa ba Abba yace” kunsan Juna ne?”

Ammi tace” eh duka daliban mu ne a makarantar Jibya “.

Kallon Jamlah Abba yai yace” gata nan kanwar ku ce sa’ar Sajida ce “.

Da mamaki ta kalli Abban mu dan ita tun da take a cikin gidan nan bata taba jin anyi labari ko makamancin wannan ba.

Ya nayin ta ya nuna bata fahimta ba don haka Abba ya gyara zama ya shiga basu labarin duk abun da ya faru, sunji babu dadi kuma sunji mahaifiyar su bata kyauta ba, hakuri suka shiga bawa Ammi harda Abba akan ta yafe musu tace “kada su damu komai ya wuce”.

ABBA ya bukaci yaji labarin abinda ya faru lokacin da yaga ta fito zata bar gidan.

Take Ammi ta shiga labarta masa bata boye masa komai ba har labarin auran ta da Alhaji Imran ta basa.

Yaji babu dadi amma basu isa su gujema kaddarar ubangiji da tazo a rubuce ba .

Da zamu tafi Abba ya bukaci a barni amma nace “ni bazan zauna ba sai da Ammi na”.

Abba yaji babu dadi hakan yasa yace “to shikenan Kuje zan zo da daddare insha Allah “

Da daddare Abba na yazo kamar yadda yai alkawari, anan cikin baranda akai mai shimfida ya zauna inda suke tattaunawa da Daddy yai ta basu hakuri akan abinda ya faru, kuma Daddyn ya hakura saboda sun san ba halinshi bane kuma Ammi tai musu bayanin abunda ya faru da ta dawo.

Bayan Inna tazo suka gaisa nan ma hakurin yai ta bata tace “babu komai ya wuce tunda ba’a cikin yaiyacin sa yai ba”.

Bayan Inna ta koma ciki Abba ya kara gyara zama yace “dama kuma alfarma nike so na kuma roka”

Daddy yace “alfarma kuma Alhaji Suleiman ai ka wuce neman Alfarma fadi kawai kanka tsaye”

“dama inaso na maida Amina dakin ta ne”

Daddy yace “madallah haka akeso naji dadi sosai, amma nan da yaushe kake so ka maida ta?”

ABBA yace “ai ba wani lokaci za’a dauka ba nan da kwana biyu ma yayi, sai aiyi bikin Siddeeqah tana dakin ta itama Siddeeqan nasan zatai farinciki matuka”

“dan dakata ina zuwa” Daddy ya fad’a kana ya Mike, wurin kanwar tasa yaje suka shawarta kana ya dawo gurin Abba na suka Kare magana, a take a gurin Abba ya biya Sadaki, aka tsaida daurin aure ranar litinin.

Da ranar litinin tazo aka daura auran Ammi da Abba kuma a ranar Ammi ta tare da yaran ta, wato little Easha Dady karami Fadeela Jiddah dan ita ma tace Ammi zata bi sai kuma ni.

Gidan Abba na gida ne mai girman gaske bangare-bangare ba ruwan wani da wani, bayan wasu yan kwanaki a cikin gidan mun dan fahimci Juna da su Jamlah sukan zo bangaren mu ayi fira, ga maganar biki na ta taso gadan gadan dan bai wuce saura kwana goma ba. Sosai Ammi ke bani magun-guna ga wanka da lalle da ake min akai akai, ana saura sati daya Momy ta aiko mubarak yazo ya tafi dani gurin wata Hajiya kamshi aka kaini, kwana na uku a gurin ta ana gyara ni, kar kuso kuga yadda na koma, duk da abubuwa sun zo min a kurarran lokaci, ban samu gyaran da ya dace aiwa amare completeba amma na hadu in ka ganni bazaka gane ni ba, indai ba kamin farin sani bane dan na hadu nayi kyau iya kyau fatar jiki na tayi laushi ga haske da sheki gunin ban sha’awa.

Zaune nike da su Sadiya, magana suke akan dinner din da zasuyi ga kamu da Arabian night ni dai duk jin su nike, saida suka gama tsaf na ce “kun gama?”. Kanwata Sajida ce ta daga min gira Alamar “eh”.

Nace “lalle kam kuna ruwa danni wallahi babu wata bidi’ar da za’ai, idan bacci kuke gwara ku farka, dan walima ce kawai za’a ita ma kuma sai bayan na tare”.

Ina gama fadar haka na tashi na barsu suna ta surutu wai ban isa ba. Su wannan ka kalan basu sanshi ba

Ana saura kwana biyu tarewa Yah Sadeeq yazo gidan mu, inda ya aiko kanwata Hannatu da muke uba daya  ta kira ni,

A falon saukar baki na same shi har yanzu bai gama murmurewa ba, tausayin sa ya kamani, sai naji zan zauna dashi kuma zan masa biyayya ko dan farincikin iyayen mu ya daure, bayan na gaishe shi na zauna dan nesa dashi.

tashi yai ya matso kusa dani yana cewa “ke wai dodo na koma miki ne kike gudu na? dama nazo ne na tambaye ki naji ko akwai wani events da zakuyi”.

Kai na a kasa nace “babu wata bidi’ar da zanyi, walima ce itama sai bayan an kaini za’ia”.

“to” yace yana mai jinjina wannan tsarin nawa.

Washe gari mai fulawa tazo ta mana amma ni ja nace ai min tayi kyau sosai abinka da farar mace, kuma a daran ranar aka sani a lalle.

Wa shegari ta kama asabar kuma yaune tarewa ta gidan mu cike yake makil da jama’ar Ammi har yan Katsina da suke mutunci da Ammi sunzo, haka dangin mahaifina suma sunzo gidan dai ya cika makil masha Allah amma babu wani kida da akai kaya kuwa na canza wannan na saka wancan ga sarkar gwal da Abba na ya siya min mai tsadar gaske, biki yayi biki. Ammi ma sai shiga take tana fita, abun dai ba’a cewa komai sai masha Allah anyi komai cikin tsari da burgewa. Harda yan makarantar mu sunzo, nayi mamaki da na gansu harda senior din mu, ashe duk Aunty Jamlah ce ta gaiyato su.

Da dare yai da misalin karfe 8:2 pm durkushe nike gaban Abba da Ammi nasiha suke min mai ratsa zuciya, kaina a lullube cikin alkabba mai ruwan danyan gwall kayan da nasa na ciki kuma farin leshi ne mai kyau da tsadan gaske ga kamshi sai tashi yake ni kaina nasan na hadu.

Bayan an gama min nasiha kannan Abba na da wasu kawayan Ammi suka tasani gaba sai kerarran gidan Sadeeq da yake a nan cikin sabuwar unguwar mu’azu, ginin gidan na zamani ne haka adon gidan ma. Ban gare ne guda buyu wato daya nasa daya nawa. Goggo Abida tace “nayi bismillah na shiga da kafar dama “

Har bedroom room dina suka kaini wanda ya gaji da haduwa komai na cikin dakin pink ne hatta da fentin dakin ma ga wasu akwatuna lodi lodi dana gani a here. wannan pink guda goma sha biyu wannan ja guda shida wannan me ruwan kasan guda ba kawai, nayi matukar mamaki dana gansu ko duk na waye?

Basu wani jima ba akace su fito a maida su dare na yi harda su Khadija aka tarkata aka tafi ya rage sai ni kadai ji na nike wani iri,

Tambayar kaina na shiga yi, Wai yanzu sabuwar rayuwa ce zanyi fa da Wanda bai so na da kauna ta, nasan bani yake so ba gangar jikina yake so, kuma nasan daya samu abunda yake so zai rabu dani, hawaye ne masu zafi suke zubar min, tunanin maganar sa ya fado min arai na cewa” na fara tunanin yadda zan rubuta littafi mai suna NI DA YAYA SADEEQ aduk sanda na tsinci kaina a gidan sa” tabbas lokacin yayi yanzu Allah yasa farinciki zan rubuta.

About AIS

Check Also

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 7

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 7                  Www.bankinhausanovels.com.ng  …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *