NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 10 KARSHE

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 10 KARSHE

Www.bankinhausanovels.com.ng 

_______bayan wasu shekaru. Zaman aure na nike mai kyau da tsafta da kuma tsantsar so da kulawa da junan mu, alhamdu lillah na kammala secondary school di na , amma ban samu na cigaba ba, saboda yah Sadeeq irin mazajannan ne masu bukatar iyalan su a kusa dasu, kuma yace “mai zanyi da karatu mai zurfi indai zan karanta na rubuta kuma na fadi a fahimta nima idan an fada min na fahimta ai shikenan” .+

Mun samu fahimtar juna sosai tsakani na da yah Sadeeq zan iya cewa tundaga ranar da aka kaini har kawo yanzu da nike magana baiyi abunda zai cusguna min da gangan ba, saida bisa rashin sani da kuskure wanda dama dan Adam tara yake bai cika goma ba, yah Sadeeq mutum ne mai saukin kai da tausayin na kasa dashi yanzu haka mun bude gidauniyar da ake temakawa marayu da gajiyayyu. Ya rike mukamai da dama a bangaran aikin sa yanzu haka shine kwamishinan yan sanda na nan jahar kaduna, mun haifi yara yan biyu duka maza shekarun su uku yanzu, Sunan Abba da Daddy aka sa musu, saboda haka muke kiran Abba da Sudais Daddy kuma muke ce mai Taufeeq

Anyi auran Khadija da Yah Mubarak inda suke da yara biyu duka mata, kuma sun koma zama a Dubai, karkashin wani kamfani da suka dauke shi

Sai Ummi da ta auri wani ma’aikacin Jarida, itama ta haifi dan ta namiji

Fadeela kuwa yah Farooq take aure sun haifi yara uku maza biyu mace daya

Sai Jiddah da take auran Maheer wanda sun hadu ne a wajen bikin wata kawar Jiddan yayin da Maheer din shine babban abokin ango sun haifi diya mace

Tsaye muke a filin buga ball din. NI DA YAYA SADEEQ ne sai yaran mu da muke ta guje guje cikin so da kaunar junan mu yah Sadeeq na wurga ma kallon ya cafe da hannu yana dariya ya iso gareni ya shiga raira min wakar “zan rayu da ke zan mutu dake a abadan dani da ke zamu zauna” . ✍️

 * * * * * * * * *

Tammat bi hamdulla Alhamdu lillah duka duka anan na kawo karshen littafi na mai suna NI DA YAYA SADEEQ ina rokon Allah ya yafe min abunda na rubuta bisa kuskure wanda kuma nayi dai-dai Allah ya bani lada

About AIS

Check Also

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 7

NI DA YAYA SADEEQ CHAPTER 7                  Www.bankinhausanovels.com.ng  …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *