MAI TAFIYA CHAPTER 5

MAI TAFIYA CHAPTER 5

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

Son kasancewarmu tare daga zuciya ne!+

Kano, Nigeria

“A’ataqidhu inni waqa’at fil hub!”

( ina tunanin na fada soyayya)2

Luba ce ke zuba wannan zance a gaban Hindu , Rukky da ‘yar modu. Zaune suke a falon Hajiya Kububuwa ana taya Hindu kwashe kayanta za ta koma sabon gida. To amma aikin na su bai je ko’ina ba saboda abun almarar da Luba ta shigo masu da shi. Bin ta kawai suke da kallo saboda tsananin mamaki. Ta ce

” Sai ina ganin kamar ba ni ba ce. Kun ga Almustapha kuwa Wow..mashallah..mashallah. Ban taba haduwa da mutumin da na ji ina son shi farat daya kamar shi ba! Ai kwana biyun nan da ba ku ganni ba ina gidansa. Kun ga gidan? Aljannar duniya!Dole ne yau na wuce wajen Iyannan na gaya mata yau fa na samu mijin aure! Don bazan juri na ga Almustapha da wata ba! Almustapha…ya rouhi..ya habibii qalbee!”8

Rukky ta taso ta zunguri Luba ta ce

” Wai mafarki ki ke ko idonki biyu? Ko dai wani abu kika sha ya gaya miki karya? Na ji har kina batun aure”

Luba ta ce

” Garau nake ras! Ai daga nan wajen Iyannan zan je kawai ta fara shiri”

Rukky buga tsaki tayi ta koma ta zauna ta ce

” A duniyar nan dai luba, a yanzu ban ga son da za a yi masa marmarin aure ba!

Ta koma ta zauna.

Luba ta yi mata kallon sakaka. Sannan ta taso ta zungureta ta ce

” Sukari kin san wanene wannan mutumin kuwa!Uban gidan Idi maina ne fa. Ai irin wannan ba ka dangwali arziki ka bar shi ba! Ka bar shi ka je ina? Ai gwara ka samu gurbi ka dawwama anan daga ‘ya’yanka har jikoki sun huta da jaje! Me aka yi da maza in ji karya!Idi Maina ma mene ba a samu a jikinsa ba ballantana ubangidansa.”1

Rukky ta ja dan karamin tsaki ta ce

” Ai ko wanene tsakanina da shi mu rabu a hanyar da mu ka hadu. Kurunkus!Wai tukunna ma dan gidan wanene?”

Luba ta yi ma ta kallon uku saura kwata ta ce

” ji fa! Ji fa sukari da wata irin tambaya. Yo…idan kin ji ana waye ubanka ai kai ba wani ba ne! Shi fa ogan Idi Maina shi ne shugaba kankat. Shi ke da kamfani shi kuma ke juya kowa da komai. To ina ruwana da ubansa? Tunda ba shi ba ne mai kudin. Watakila ma wani tsohon matsiyaci ne can a kauye, dan ya tura masa a bunda ya sauwaka. Ni ko aurensa nayi ko inda danginsa suke bazan dosa ba!”1

Sai a lokacin Hindu ta saka baki ta ce

” This is surprising yau da bakinki Luba kike ambatar aure? Gaskiya zan so in ga wannan mutumin dan na san ya isa! Isar tasa ma ta isa!”2

Luba ta miko mata hannu suka kashe.

Sai a lokacin ‘ yar modu ya tashi yana rawa yana rera wata waka

” Ayyaraye daure jure

Zaman gidan wani tilas ne

Zaman gidan wani sai hakuri

Ai ba da kan ki aka fara ba

Ai da da kan ki aka fara ne

Da kin yi kuka kin koshi

Hindu ce ta taso ta biye masa suke taka rawa. Wai su a dole aure ya zo har ya tabbata.’Yar modu ya karkace baki ya rangwada guda suka tafa da Hindatu ya ce

” Wannan abu yana min siga! Muna jin aure a makwabta yau bana dai tamu za mu kai. Kuma dama ai abun na Allah ne budurwa da jika. Da haka da haka mu ma za a zo kan mu , ba mu fidda rai ba Alquran! Eh ai muna gayawa Azza wa jallah. Kawata lubancy ni zan miki babbar kawa. Billahillazi rabon cingan daga nan har kawayenki na kwatano. Abu namu maganin a kwabe mu! Ahayye Allah na dawo!”3

STORY CONTINUES BELOW

Hindu ce ta tunkude shi ta ce

” Babbar kawa ki ke ko ni? Ji shisshigi da kwala kai a faranti”

Yar modu ya kama baki ya ce

” Yau naga abun da ya isheni ni jikar A’i. Wannan da da ke aka shimfida duniyar da ba kya bari mu karaso ba! Yo kin zama mahandamiya. Ki ci nan ki ci can dangin makwadaita! Don kawai kin ji nace ni ce babbar kawa shi ne kike tada jijiyar wuya? Kai Hindu amma kin yi faduwar bakar tasa! Kyangarann!”3

Suka kwashe da dariya suka kara tafawa.

Luba ta ce tana fari da ido

” shirun ka nawan..ai ni kadai na san matsayin da zan baka. Ka manta kai ka fara kaimu la mirage. Ai da bazarka nake rawa!”2

“Idan kima kara sa ni a cikin jinsin da ba nawa ba..babu abunda zai yana in yi tsallen alkafira nayi kuli kulin kubra da ke!” Cewar ‘yar modu5

“Laaaa..yar modu wulakaci” luba ta fada tana masa kallon kasa kasa

Hindu ce ta ce

” Look guys..ku fa kun cika yarinta dayawa. Ke Luba wai ya ma aka yi kika san aure yake so. Kin san fa halin mutanen mu”

Ta harari Hindu da wasa ta ce

” Ai yanzu ba sai namiji na son aure ba ake aurensa. Yanzu ke ce zaki so auren sai ki bi dare ki bi rana kuma dole aure ya dauru! Zauna nan Hindu idan a tsaye kika kwana ni a tafiye na kwan! Wai kin ga gidan mutumin? Gari guda kamar wata masarauta. Da sannu zan zama sarauniya a masarautarka ya Nouri Mustapha! Kin san kuma shi ma fa na ga yana ra’ayina! Wallahil azeem faduwa ce ta zo daidai da zama!”4

“Da kyau mutuniyar” ‘yar modu ya bata hannu suka kashe.

Duk abinda suke yi Rukky ta zuba musu ido bata ce komai ba.

Luba ta fara tattara wata jakarta ta hannu tana mikewa ta ce

” Bari ku ga. Ba a bori da sanyin jiki. Bari na je wajen Iyannan. Ina ga nayi wata 3 rabo na da gidan sai aike”2

Hindu ta yi sauri ta ce

” Au ba zaki raka mu wankan sabon gida ba?”

Gaba tayi ta ce

” Hindu kiyi ta kan ki in yi ta kai na”4

Wata motar ta kirar corolla ta shiga tana tukawa tana tuno abubuwan da suka faru kwana biyu da suka wuce.

Duk yadda take tunanin masoyin na ta da arzikinsa ya wuce nan. Ta tuno irin baja bajan da ta samu a gidansa da makudan dalolin amurkan da ya cika ta da su kafin ta baro gidan.3

To yanzu da take a matar waje kenen ballantana ta shiga daga ciki! irin shagalin da za a yi a wajen bikinta abun sai wanda ya gani. Dole ne ta rarrabawa malamanta kudi su sa shi a gaba! Ina ba zai yiwu ba alewa ta zo hannun yaro sannan ya bar ta ta fadi kasa! Inaa…6

Gidansu na nan a yadda yake sai dakin Iya Tamadi da ya banbanta da na kowa. An sake masa ginin bulo an yi fenti an sa mata sabbin kaya. Shi kuwa baban yara da aka ce za a mishi gyara cewa yayi ba ya so a bashi kudinsa a hannu.

Ba ta yi sallama ba don yanzu ita ta fi karfin sallama idan za ta shiga gidan. Sannan uwar gulma Iya Asabe za ta kafa ta da habaici. An ya kuwa ba zata sa a batar da matar nan ba? Tunaninta kenen.3

Rashin sallamar tata bai sa ta kasa yin ido biyu da Iya Asabe ba daga shigowarta. Ta watsa mata harara ta ‘ba ki isa ba’ ta wuce dakin uwarta. Tana jiyo Iya Asabe na cewa

” Ah fulanin tashi yau an bayyana kenen”1

Iya tamadi na zaune tana tsintar wake tana kallon wani shiri a talabijin Luba ta shigo.

STORY CONTINUES BELOW

“Lale lale maraba da auta”

Cewar iyannan fuskarta fal faraa . Ko banza ta san yau ranar samu ce. Luba zata zauna ta ce2

” Auta kar ki zauna anan. Ga wata dadduma can dauko ki shimfida ai ta fi laushi”3

Maimakon ma ta ji tayin da ake ma ta sai ta fasa zaman kasan ta fada kan kujera. Ta buga wani uban tsaki ta ce

” Gaskiya ina da mahassada. Amma …k’ “

Iyan ta kalle ta ta ce

” Au na san ba zai wuce Asabe ba. Ai ita Asabe wannan shigar da take ganin kina shigowa da ita ta alfarma da wannan dankareriyar motar su ke ruda ta. Bar ta! ‘Yar matsiyata har ubanta ya mutu da tsohon bashi akansa! Baruma ce fa ai anan tsiya ta kare!2

Dalilin kenen da ko ‘yan unguwa nake gaya musu ba ki nan kina saudiya. Aiki ya kai ki.Yo ba sai sun gan ki ba ballantana suyi gulma? shegu iyayen sa’ido!”

Luba bata kula ba. Tunaninta yana gurin sun yi za su hadu da Al Mustapha yau da dare. Irin shigar bajintar da ya kamata ta yi. Ta dago kai da murmushi ta kalli iyannan ta ce

” Iyannan ai sai ki fara shiri. Bana dai adduarki ta kusa karbuwa. Na samu miji abinda ya rage mu samo kan sa ayi aure. Miji dai na wuce sa’a akwai shi!”4

Iyannan ta karkace baki ta rangada guda tana habaice habaice ta ce

“Da kyau! Auta ta..auta ikon Allah. Masu miki bakin ciki sa sha kuka. Allah ya kaimu..ni jikar mutum hudu ina zan saka mutane na? Ko wani dakin za ki tayar mun?” Ta karasa tana dube duben girman dakin

Tsaki Luba tayi ta ce

” ke iyannan baki gajiya da bani bani. Yo idan na samu na aure shi ai gidan kan ki zan gina miki. wannan ma ai karamin al’amari ne”

Ta washe baki ranta kal. Gwara dai Luba tayi auren a daina saka ta a waka. Ana yiwa diyarta bakin ciki an ga kudi sun zauna ma ta.

Luba ta lalo wasu kudade ta mikawa Iya ta karba tana rawar jiki ta ce da ita

” So nake ki sa malamanki su fara min aiki. Yanda duk ta inda aka bullo masa da maganar aure ba zai ki ba! Ai maganin shege karan maguzawa!”2

Iya Tamadi ta ce

“Ai kuwa dai..kin yi farar dubara. Mazan yanzu sai da haka. Da zafi zafi akan daki karfe. Daga wannan maganar can zan wuce”2

Luba tayi murmushi ta ce

” Da kyau Iyanan..shi yasa nake son ki. Ke kadai ki ke iya rufamin asiri”3

Daga nan ta hau motarta ta wuce. Ta danna wata wakar nancy ajram tana saurare tana bi. Ranta kal! Duniya sabuwa. Duniyarta da Al Mustapha.2

******************************

Sabon gidan Hindatu wadatacce ne mai sassa guda biyu. Na farkon shigowa nan ta bari a matsayin sashenta da zata dunga cin karenta ba babbaka.

Na daga ciki kuma anan ta ajiye yaranta. Ta dauko wata tsohuwa mai kula da su da mai gadi ta ajiye a gidan.

Sai a yanzu take jin hankalinta ya kwanta yaranta za su samu kulawa kuma ko banza ta huta da fadan Hajiya uwani. Yaushe ma a rayuwa zaka bari a kankameka a takureka kana da ‘yancin kan ka?

Sai dai akwai wadansu canje canje da ta gani game da Abba da yasa jikinta yin sanyi. Tun farko ta san Abba tunaninsa da maganganunsa sun fi karfin shekarunsa to amma tana mamakin irin kallon da yaron ke jeho mata.3

Yawa yawan lokuta idan ta kawo musu sabon abu sai Asiya take tsalle tana murna sai ta ga Abba bai ko nuna a fuska ba. Daga baya ma ta lura ko abubuwan bai cika tabawa ba.4

STORY CONTINUES BELOW

Jikinta ya fara yin sanyi ko zigar da ake masa a makota ya fara dauka da irin maganganun aibatawa da ake jifanta a unguwa da su. Shi ne tayi shawarar dauke su gabadaya ta kawo su gidanta. Ta sa akai musu kofa ta baya inda za suke shiga da fita yanda ba zasu takurata ba.

Ta gayawa kan ta za ta dunga taka tsan tsan da shigowar abokanan iskancinta ko don idon yaron.1

Ranar da suka tare Hindu ta shigo da su cike da doki. Asiya na ta tsallen murna musamman da aka nuna mata dakinta mai dauke da kaloli daban daban. Amma Abba bai ce kamai ba. Hindu ga dafa shi ta ce

” Yaya dai yaro na, ko kalar fentin dakin naka bai maka ba a canja wani? Ka san fa duk don ku nake yi”

Ya dago ya kalle ta a tsanake, cikin kwayar idonta ya kalla. Ta ji wata irin faduwar gaba da bata taba jin irinta ba. Sai ta ji wani irin tsoron yaron ya tsirgar mata. Abba ya mata kwarjini dayawa. Meye haka?

Ya ce

” Ni mama, mecece sana’arki?”4

Kallonsa take amma bata samu ansar da zata ba shi ba. Ba dai lokaci yayi ba? Ba dai illar lokaci zai yi halinsa ba???

Tafe suke akan titi Luba ce da Rukky a cikin motar Lubar. Luba ke tukawa a hankali sanyin ac na dukansu sai karan sautin cikin radiyo dake fitowa na wata wakar Nancy ajram.

Luba ta sa hannu ta kara volume mutuniyar ta ce kamar ‘yan tashar radiyon sun sani suka sakata. Ta ci gaba da bi tana jinjina kai kwanan nan nishadi take ji. Ta cigaba da cewa Rukky

” Sukari ba zaki gane ba, ke fa ba ki taba fadawa so ba. Labaransa ki ke ji a cikin littafan hikaya. To yaushe zaki adar?!”2

Murmushi Rukky tayi. Bata bukatar bayani. Ita ta san ba ita bace ta da. Rayuwarta ta da a shafe take ba a tuno ta bama a saka ta a lissafi. Ta yarda bata san so ba, wannan shi ya fi ma ta komai sauki!1

Ta dubi Luba a karkace ta ce

” Ai kuwa dai sai ku masoya. Ko ku ne laila da majnun?”

Dariga luba ke yi irin dariyar nan ta nishadi ta ce

” Sukari kenen. Ke fa kin dau maganata a sha- sha -gare ko?”

Murmushi Rukky tayi. Luba ta dora da bayan fuskarta ta dan canja

” Amma kin san me? Shi sai na ga baya doki na kamar yanda nake dokinsa. Kamar ma mace bata dame shi ba. Shi dai komai aikinsa. To amma idan ya dauke ni irin karuwar da ake dauka a aje a manta da babinta to da sauransa! Allah sukari zan iya yin komai akan na samu gayen nan. Hmn…k’ “

Rukky ta ce

” Ai naga alama. Ki sani dai karuwa bata zurfafa so. Dan na ga kin zira kai dayawa. Kar ya zo ya miki abinda zaki haukace. Ko da yake yanzun ma a haukace ki ke!”2

Luba ta daka mata duka ta ce

” ke ma ai don baki gan shi ba ne shi yasa kike cewa na haukace. Amma…au..au..kin ga karfe biyu ma na rana bari mu je ofis din sa mu gaisa. Daga nan sai ki kallo min shi za ki gane me nake nufi”1

Ta juya kan motar ta koma baya hanyar ofis din Almustapha.

Rukky ce ta fara fadace fadace ta ce

” Haba Luba mu da muke da AP ki bari a dawowa ma je”

Luba bata kula ta ba. Ganin haka sai tayi shiru tana gunagunai ta na cewa

” Ai fa mun shiga uku”

Harabar ma’aikatar babu mutane sosai. Yawa yawansu sun yi sallah sun koma ofishoshinsu. Rukky ta cigaba da kallon wuri cikin mamaki. Ah lallai dole Luba ta rude kyau da tsarin wajen ya baci.

Bata ga laifin Luba ba, ai kowa ya samu rana dole yayi shanya. Ita ma da zata samu wani ya taya ai da ciniki ya fada.Tinkis tinkis take bin ta a baya har suka hau lifter zuwa ofis din sa. Sakatariya dama ta san luba don haka kawai sai suka shiga.

Wata irin shiga ce a jikinsu wanda ba marabarta da tsirara sun sa wani coge mai tsini da ke bayyana kowane takunsu.

Yana danne danne akan kamfutar da ke gabansa. Aiki ya sha masa kai. Ya ji shigowar Luban ya daga kai yayi mata murmushi da alamar nuna su karaso. Suka karaso Luba ta ce

” Habibii ga aminiya ta nan na kawo ta ta kwashi gaisuwa.”

Kallo daya ya dago yayi mata suka gaisa ya dauke kai zuwan kan abinda yake kallo.

Yanda yayi matan bai musu dadi ba musamman Luban da take gani ya yabantata a bisa yanda take kambama shi a gaban kawayenta.2

Ita kuma Rukky sai ta tabe baki bata wani damu ba idan tayi la’akari da tangamemen ofis din sa na masu fada a ji. Kuma Luba ta ce shi ne mamallakin ma’aikatar gabadaya. To dama masu kudi suna da wata dabi’a banda izza da girman kai ne?

Cikin halin ko in kula ta ce da Luba zata sauka mota ta jira ta don ta dan ba su waje su tattauna, tayi musu sallama tayi takunta kwas kwas ta fice.

Taku goma sha biyar tayi kafin ta fita ya kirga a ran sa. Me yasa ya kirga ya tambayi kan sa. Me ya sa?5

Ko abin daga zuciya ne??????Abinda ke cikin zuciya ai sirri ne!4

Kano, Nigeria

Iliyasou Tillaberi ke zaune a daya daka cikin kujerun ofishin Al Mustapha na I and A group of companies. Kallo daya za kai masa ka gane ya sha jinya jikinsa ya nuna matsananciyar rama. A hannunsa wata sanda ce da yake dan dogarawa irin ta masu kudi.2

Al Mustapha ke zaune yana fuskantar sa. Ya riga ya sanar kar kowa ya shigo ofishin suna ganawa da mahaifinsa. Bayanai yake yi masa akan wasu kamfanoni da suke son siya su mayar da su masaka. Uban na saurarensa har ya gama ya ce

“Komi hwa yana yin kyau aikinka yana kyau. Ita dukiya ba a barinta ya wannan, juyata ake ta hayayyafa hal ‘ya’ya da jikoki. Tilas idan kana so hwa ka girma kayi kasaita ka buwaya sai ka zamne na kasanka ka dakusal da su ya zamana ba a kallon kowa sai kai! Yanzun wannan da danuwanka da ran shi tare za kuyi komai. Allah kyauta makwancin shi”1

Almustapha bai ce komai ba ya tabo masa abinda ke masa ciwo a zuci. Kuma bai ga dalilin da yasa zai jajanta ba bayan shi ya jawo. Wani irin abu yake ji kan uban da ya kasa fassarawa. Sai ya gwammace kawai yayi shiru.

Uban ya tsaya yana duban dan yana kallon yanayin fuskarsa ya ce

” Diba yadda cuta ke neman halakani yarona…kamata yayi ka zubal da komi ya wuce. Rayuwace fa gaba gareka ga tarin dukiya nan ubanka ya nema maka. Mi zai dame ka?”

Ya kalli uban kamar yanda zai kalli sa’ansa ya ce

” Ina gaya maka hakkin Ahmadou ba lallai ya barmu ba. A nemo yarinyar nan. Abba na roke ka a nemo yarinyar nan”

Wani irin kallo uban ke masa na tsananin mamaki. Ya rasa wannan irin bala’i da me zai ji ne wai? Shi duk ‘ya’yansa maza da yake alfahari da su ba su da magana sai ta wannan yarinya?7

Babu abinda ke damunsa irin mafarkan da yake da Ahmadou. Ya kan gan shi yana masa fushi yana tunkuda shi cikin wani rami. Babu ranar da zata wuce da bai yi shigen irin wannan mafarkin ba. Abinda ya hana lafiyarsa daidaita kenen. Ya sa damuwa da fargaba a ransa jinin sa sai kara hauhawa yake.8

Ya tuna irin shigen ficen da yayi na jawowa Ahmadou masifu na karayar dukiya da sanadin mutuwarsa. To amma kamar Ahmadou din ya bar wata halitta da take neman fito na fito da shi. A dalilin hakan ya rasa dan sa yanzu kuma Almustapha na masa zancen banza. Ya dake irin na mazan jiya ya ce cikin nuna alamar gargadi6

” Idan har kana kamnal muyi shiri da kai to ka tsaya inda nicce maka. Idan ka ce za ka shiga wannan magana kuwa..ma gamu!”2

Da haka ya kokarta ya tashi, tashi irin na jikin tsufa. Almustapha ya taimaka masa. Ya raka shi zuwa waje gurin zungureriyar motarsa ya bude masa mazaunin mai zaman banza ya zauna. Ya dago ya kalle shi a tsanake ya ce

” Na tuna. Ka je gidan abokina Abbassodor Mukhtar, mun tattauna mun yi za ka je ka ga diyal wajen shi  ku zanta. Ya kamata a ce yanzu wannan ka ajje mata hakanan. Kai da ka ke dulmiya kan ka cikin halkokin siyasa ya kamata ka ajje mace don a kalle ka da mutumci. Kal mutane su ga hakan a matsayin gazawa.1

Duniya ita ake yiwa bauta gwamma ka moreta lokacin da kake da rai. Ranar da ka zamo babu wani ne zai maye gulbinka.”

Gyada kai kawai yayi. Wasu maganganun sun shiga zuciyarsa sun zauna, ya fara hangen duniya a wani waje mai dogon zamani da zai isheka ka cika burirrikan ka. Suka yi sallama shi kuma ya dawo ofis.

Ya cigaba da juyawa akan kujerarsa tunani sun masa yawa amma akwai wani abu da ke damunsa a zuciya. Ya kasa manta fuskar wannan yarinyar da ya gani da Luba.

Shi mutum ne mai tsananin taste din yanmata. Farkon ganinsa da Luba ya ga ta masa zata cike wani gurbi a wajensa to amma kallo daya yayi wa kawar ya ji yana so ya kara kallonta. Yanayin idanuwanta ne suna masa wani irin kamanceceniya.

STORY CONTINUES BELOW

Bai damu da fadan da zai haddasa tsakaninsu ba karuwa wani daraja ne da ita da za a duba a ki abu don ita? Mai kudi kuma yana da haramiya ne balle shamaki?15

Dadin duniya kenen ka mallaki abu a lokacin da ka ke son mallaka ya kuma zo maka a yanda ka ke so. Yarinyar nan ta masa! Ai kawai yar da luba zai yi ya dauketa duk da ya ga Luban ta zarma dayawa. Amma shi gaskiya yanzu ba ya jinta kwata kwata a rai.3

Ya dauko wayarsa ya kira wani mutuminsa da yayi wa maganar yarinyar jiya. Kara daya biyu suka gaisa. Ya ce

”  ya ya bashari…ka gano gidan da yarinyar take kuwa?” 

Ya ce

“Eh yallabai…amma gidansu daya ne da Lubar”4

Yayi shiru, da zai ce ” so what” sai yayi tunanin kar ita Luban ta bata mai show. Sai ya ce

” Ka ce mata kawai ka samo mata bako, zan je gidan daga nan zan karba”

Ya ba shi amsa da

” Ok oga”

Ya kashe wayar yana cewa

“Good, very good”

Ba shi da matsala ta wannan bangaren. Sai dai ran shi na raya mishi ya kamata ya rage neman matan nan ko dan harkar siyasa kar wani ya shammace shi ya dau hotunansa. To ko yayi aure ne? Ya tuno tayin mahaifinsa ya ja tsaki, bazai je ba.

Ran sa ya raya masa

To ko yarinyar…?

Ya buga wani uban tsaki yana jin haushin zuciyarsa. Duk duniya ya rasa wacce zai aura sai karuwa? Karuwar titi da maza suka gama jagwalgwalawa! Ai tsakanin ka da karuwa kayi abinda za kayi ka watsar da ita!13

Da daddare kawai zai karasa wajen wannan yarinyar..me sunanta ma? Oho!

Zai neme ta ko na sati daya ne ya ji ko abinda yake ji akanta zai ragu. Ya san ” infatuation” ne da sannu zai neme shi ya rasa.

Da sannu zai nemi yarinya mai hankali ya aura, cikakkiyar mace.8

Da irin wannan tunanin ya tashi daga ofis.

Abinda Almustapha ya manta shi ne

Rayuwa tana zuwa maka ne a yanda ka dauketa, ba zaka taba girbar abinda ba ka shuka ba! Idan hairan hairan…idan sharran sharran!13

*********************************

” Ka san illar shaye shaye kuwa? Tabdijam!Da ka san irin illar da yake yiwa rayuwarka, to..to…tamkar ka je ka rungumi transifoma ne ana ruwan sama da daddare! Kai ma ka san ubanka zaka ci ko?”2

Cewar Iliya bakanike. Zaune suke akan benci da shi da wasu maza guda biyu sababbin daukan aiki a wani gidan mai na Total. Magana yake yana sakace da wani dan tsinke bayan wata mai abinci ta kawo masa shinkafa da wake ya siya. Da kyar ya sayi naman goma ya dora akai ga shi don jaraba naman ya zame masa kajaga.7

” Naman kirki ma ba za a sa a wa mutum ba da kudinsa, sai an hada masa da jijiya” ya fadi yana wurgar da tsinken.8

Wani a gefensa fuskarsa duk cin zanzana ya ce

” Ai oga ka gane ko? Rayuwar ce sai da haka ka gane ai..abubuwan duniya sun yi wa mutum eh..ya..ne…dole shi ma ya dan dunga afawa..yana..wullawa ko don ya ji garau. Ka gane ai.. idan ba a yi ana hawa gajimare..sai ka ga abubuwan ba sa tafiya….su na yiwa mutum eh..ya ne..”15

“Eh…eh ..eh wallashi oga” Cewar wani tsamurmuri a gefen da tabar wiwi ta zuke shi tas!

Kallon takaici Iliya ya musu ya ce

“Matsalar ku ku baku da hankali. Ina wani wali da ya zo dazu ka gan shi ai..mai farkakken wando nan nan ya roke ni abinci na ce a zuba masa na hamsin. Kwarankwatsa dubu da anan yake aiki, Oganmu ne amma da ya kafa shaye shaye ka gan sa nan kamar tuburan mahaukaci! Tun yaushe aka kore shi baya komai yanzu sai yawo da roke roke.

STORY CONTINUES BELOW

Wai ya ma za a yi mutum ya zama sakarai makiyin kan sa. Wadanda kuka taso tare ka ga suna samun cigaba a rayuwarsu ana damawa da su amma kai sakaran banza! Ko ta kai ba a yi ka kafa zuke zuke. Ka kashe rayuwarka ka kashe ta ‘ya’yanka da sauran dangi. Ka zo a gyara zaka koma a alakoro. Ka je lahira walakiri ya suburbude ka!”8

Duk wannan hirar da suke yi Rukky ta kasa kunne tana jin su. Ita ma zaune take a wani benci nesa da su kadan tana jiyo su. Wata jar atamfa ce a jikinta da aka yiwa dinkin doguwar riga. Ta daura dankwalinta daidai da zamani amma bata yafa komai ba.

Mai ta zo sha sai ta bayar da motar a mata service tunda ta ga ba wani dadewa ake ba. Suka bata benci ta zauna tana danne dannen waya amma kunnenta na kan su Iliya.

” Iya kano kawai idan ka duba adadin benelin din da ake kwankwada! Kai! Lamarin ya baci. Wallahi wani ana ce masa Raf a makotanmu taba kadai sai da ta dagargaza masa huhu a haka ya mutu..yo Allah na tuba kanwar uwarsa ce?”

” Ah..Allah oga har da laifin gwamnati ma..ai gwamnati bata yi ba oga..Allah ya tsine ma ta!….inaaa..ta bar mu ba ko sisi” cewar mai cin zanzanar nan3

Wata muguwar harara Iliya ya watsa masa ya mike yana cewa

“Tun da gwamnatin ita ta halicceka ba..wawa kawai. Gwara ka hankalta ka gyara rayuwarka kafin lokaci ya kure maka.”3

#saynotodrugabuse13

Rukky ta cigaba da bin Iliya bakanike da kallo. Ya mike ya zura hannunsa a cikin aljifansa na biri da wando shudaye. Fuskarsa kadaran kadahan.

Sai take jin kamar ta je ta ce ma sa

” Ka san irin abunda nake ji kuwa? Ka san kalar damuwar da ke zuciyata? Idan ban sha ba, ya zan yi na manta da damuwa ta?”

To amma sai jikinta yake bata Iliya bakanike ba zai bata gaskiya ba. Watakila ma ya bita da zagi ganin hakan kamar dabi’arsa ce.

To amma bata iya ce masa komai ba. Ta gabanta ya zo ya wuce yana mai daga mata hannu da cewar

” Hajiya barka da yamma”

Ya wuce abunsa. Ta bi shi da kallo. Lokaci daya a rayuwarta tayi tunanin dama ita ce Iliya bakanike, daga ganin shi ba shi da matsala irin tata.  Dama wasu abubuwa ba su faru ba. Ta na jin kewar wani nata tana so a ce ga wani na ta ko za ta ji ita ma mutum ce kamar kowa.1

Zuciyarta ta ji tana mata wani irin ciwo, sai ta mike. Lokacin kuka ya wuce, yanzu lokacin fuskantar rayuwa ne a yadda ta zo.

An gama service din motar ta karba ta hau kan titi. Ta danna wata wakar mutanen ethiopia tana bi tana gyada kai. A hankali damuwa na barin jikinta.

Wayarta ce tayi kara, ta rage volume din wakar ta dauka tana dariya ta ce

” Bashari..shegen sama! Ta samu kenen!”

Ya ce ya na dariya

” Ta samu Hajiya..ai ina gaya miki babban kifi ne ya samu”

**********************************

Luba ta ci gaba da danna wayarta a karo na barkatai amma ba ansa. Ta buga tsaki ta dubi Rukky da ke shafa Mai ta ce

” Kin san har yanzu baya daga wayata. Na je ofis din sa sakatariyar shi ta ce wai baya nan. Har fa gidan shi na je security din sa suka ce wai yayi tafiya. Mutumin da tabbas na san yana gari. Sukari wai a tunaninki menene dalilin wadannan abubuwa? Ana mushush!( na shiga rudu/ im confused)4

Sai da Rukky ta ji gabanta ya fadi. Tun da suka je ofis din mutumin nan ta gagara daina tunaninsa. Abinda ya cigaba da sa ta a cikin damuwa wannan satin kenen. Ita bata ga dalilin da zai sa ta rike shi a rai ba. To wai dan me?1

STORY CONTINUES BELOW

Sai dai ta kasa cire shi. Yana yi mata kamar wani wanda ta sani. Yana mata yanayi da wani amma ta kasa gane waye. Watakil cikin tarkacen samarinta ne amma wa? Da idonsu ya hadu sai ta gane ta ma san shi dole a wani guri watakil ko ya taba nemanta a baya. Ita fa ba za ma ta iya tuna samari nawa ta yi ba.1

Amma bata gayawa Luba wannan tunani nata ba don ta san halinta. Yanzu cibi zai zama kari musamman akan wannan mutumin mai tauraro a goshi.

Rukky ta dauki jan bakinta tana shafawa ta ce

” Luba kin kira gayen nan kusan sau hamsin kenen..dalla rabu da gara. Ke me farin jini ma wuyarta yau ki baza turare ki fita Allah kadai ya san wanda zaki samo”2

Wata muguwar harara ta dallawa Rukky ta ce

” Sukari yanzu na tabbatar baki da hankali. A tunaninki a duniya akwai kamar Al Mustapha? To a ina yake ina zan same shi? Wallahil azeem ko makwafinsa babu! Ki ga mutum kamar shi ya tsarawa kan sa rayuwa. Shi yasa nake so na mallake shi ni kadai..Almustapha nawa ne ni kadai. Kin san iya adadin kudin da nake kashewa akansa a jawo hankalin shi? Amma kina ga kamar ma ana ziga shi!”3

Rukky tayi sakaka tana kallon Luba da mamaki. A hankali ta ce

” Luba wannan son zai haifa miki da mai ido kuwa? Mutum irin wannan ko baya bariki ai zai yi yanmata dayawa ballantana. Ki hutasshe da kan ki fa!”1

Kafin Luba ta ansa Hindu ta shigo yawonta ya biyo da ita. Suka gaisa aka mayar mata da yadda aka yi. Tsaki tayi bayan ta dauko ruwa a fridge ta tsiyaya a kofi ta kurba ta ce3

”  Wai kawata yaushe kika koyi bakin naci ne? Gaskiya kin bari gayen nan ya shiga ran ki. Karuwa fa bata da hurumin so. Ki share kawai tunda kin kwashi abunda zaki kwasa”1

Luba tayi narai narai da ido , kwalla ta taru tana neman zubo ma ta ta ce

” Hindu kin san kallar son da nake ma sa kuwa?”2

Jikin Hindu yayi sanyi ganin halin da kawarta take ciki ta nisa ta ce

” To mu je wajen malamin nan mana. Wanda ziza ta kai mu farkon zuwanmu gidan nan”

Tuni Ruky ta zabura ta ce

” Gaskiya Hindu ba za mu je ba. Mutumin da ya ce za a rasa rai! Ni tun daga ranar nake tsoransa”4

Wata dariya suka kwashe da ita. Suna cewa ta cika tsoro. Wai ai ko an je wajensa ko ba a je ba, mutuwa ai dole ce.

Kawai sai suka tashi suka fara shiri Rukky bata da yadda za tayi kar Luba ta ce bata damu da halin da take ciki ba. Don ta san ita ma ko ita ce Luban zata mata kamar haka.

A motar Hindu suka fita ta ce ita ce zata gane hanyan. Anan take musu korafin dan ta, ta ce zata gayawa malam ya rufe masa baki ya daina shiga al’amuranta.1

Luba tayi tsaki ta ce

” Wannan dan dan yaron shi ne har zai firgita ki har sai kin sa an yi masa aiki hindu! Dan cikin naki!”2

Nisawa Hindu tayi ta ce

” Kawata ba zaki gane ba”

Daga nan har suka isa gidan malamin. Kamar koyaushe akwai dogon layi haka suka jira har aka zo kan su. Suka shiga.

Wannan karin ma yana zaune akan kujerar da yake zama sanye da wani shudin yadi ya masa dinkin malum malum. Ya sakar musu murmushi da alama ya gane su. Aka gaisa irin na al’ada sannan Luba ta rattabo masa bayani.

Ya ce ta gaya masa sunan saurayin sannan ta gaya masa cikakken sunanta. Duk ta fada masa. Ya ce ta zabi lamba daga daya zuwa ashirin ta zaba. Malam ya fara bude littafi.

STORY CONTINUES BELOW

Sai da ya gama ya ce

” Kiranye a yanzu ba zai yiwu ba , al’amarin babu sa’a. Al’amarin akwai rikici. Al’amarin akwai rasa rai!”4

Innalillahi wa inna ilairrajiun

Abinda Rukky ke fada kenen cikinta ya bada kululu. Sai da tace kar su zo yau ma ga shi ya ambaci rasa rai. Ji tayi gabadaya hankalinta ya tashi. Luba za ta jawo musu masifa.1

Ita ma Luban hankalinta a tashe yake . Ta ce

” Malam me ya sa al’amarin ba sa’a? Dan Allah ranka ya dade ka taimakeni ka duba min zan iya kashe ko nawa ne. Ina son karin bayani. Dan zuciyata ta mato akan mutumin nan”4

Malam yayi shiru. Ya bata wani carbi ya ce ta kama waje daya ta kama ya karbi carbin. Ya fara bude littafi

Sa’annan malam ya dago ya ce da ita

” Na ga mata guda biyu banda ke. Zuciyar shi tana ga guda daya. Daga nesa ta ke amma tana daf da ke!!”6

Daga wannan malam bai kara cewa komai ba. Luba hankalinta ya kara tashi tana rokon taimakon malam. Ya ce da ita

” Ki dawo nan da sati daya watakila kafin nan zuciyarsa ta sassauto. Za muyi aiki akansa kar ki damu.”3

Sai a nan hankalinta ya kwanta. Hindatu ta fadi bukatar ta. Suka aje masa makudan kudi suka tafi. A mota dai zancen ake ta jujjuyawa. Suna ta yiwa Rukky dariya wai ta tsorata bata karbi taimako ba. Ita dai bata ce komai ba.2

Da suka koma gidan ma hirar ce dai har bashari ya kira Rukky wai ta shirya bakon nan na hanya. Sai ta ji kamar ta ce masa ta fasa bata jin dadin jikinta. Amma sai Hindu ta nuna mata ba a haka, ina lefin mai nemanka da arziki.

Da wannan Hindu ta taimaka mata ta shirya jikin wasu jajayen kaya. Ta gyara mata dogon gashinta. Ta kalleta a tsanake ta ce

” Lallai kin ci sunanki sukari…ba kiyi farin banza ba! Cancadi!”1

Luba ita ma kwalliyar ts burgeta ta ce

” Wallahi sukari ba ki da wayo. Zuwanmu wajen malam ai da kin sani kin ce ya kama miki wannan sabon kamun tunda kuwa Bashari ya ce babban kifi ne! Ai da zafi zafi akan daki karfe!”

Ita ma Rukky anan ta ga rashin azancinta ta ce

” wallahi kuwa. Ai tsorata nayi shi yasa duk na rude”

Suka kwashe mata da dariya suna kiranta ” farar kura”. Wayarta ce tayi kara, bashari ne. Ta dauka ya ce mata mutumin yana bakin gate sannan kuma ta turo masa na shi kamashon. Suka yi dariya suka yi sallama. Ta fita kawayen nata suna ta mata fatan sa’a wai Allah sa ya dalle ta da mota.

A tsanake ta fita a bakin gate ta ga wata bakar mota ta san shi ne.Gilasan cikin motar masu duhuwa ne ba a ganin wanda ke ciki. A hankali ta bude ta shiga. Waya yake yana kallon gefen taga.  Ta zauna har ya karasa kana ya juyo ya kalleta.

Sai a lokacin ta gane ko wanene. Tayi sauri ta zabura zata bude kofa tana cewa1

” Yi hakuri kuskure ne. Luban tana ciki bari na kira maka ita. Na zata bako na ne ya zo”3

Kafin ta bude ya sa central lock ya figi motar kamar zai tashi sama. Ita kuma ta fara bin sa da kallon mamaki.1

Har suka yi tafiya mai nisa bai ce mata kala ba ita kuma ta zira masa ido tana tunanin adadin rashin hankalinsa.

Ita bakuwa ce a iskanci? Ta gane kanta ya dawo kenen. Ta tuno halin da ta bar kawarta a gida akan son sa, shi ne shi kuma ya zagayo nan. Namiji kenen kanin ajali! Idan bai kashe ka ba ya sa ka jinya! Zai kare yawonsa ya dawo da ita. Inaa..ba zata sabu ba bindiga a ruwa!

Sai a lokacin ta lura hanyar fita kano yake bi kuma ya kasa ce mata komai. Ta ce

” Ka ga malam. Ba da ni za a yi wannan cin amanar ba. Ka Karaci gudun ka ka nemi guri ka ajiyeni”1

Wannan karin ma banza yayi mata sai ma ya danna wani selection din wakoki da ya nacewa na Oumou sangare. Yana son Oumou sangare. Sautin wakarta Ah Ndiya ya fara fita daga manyan sifikun motar.

Abinda ya sa jikin Rukky yayi sanyi kenen. Ta san Oumou sangare yar mutanen Mali. Lokacin da take Niamey wakoki biyu take ji na sogha Niger da Oumou. Dan har tana jin yaren ‘yan Mali sama sama.  Tana son ta saboda irin maganganun da take fada a wakokinta na ban tausayi. Don har Momodou na yawan ce mata idan Oumou za tayi show watarana dai zai kai ta kowa ya huta. Sai ta ji kamar ya tono mata miki!5

Tayi shiru ta runtse idanunta. Wani abu na mata ciwo ta rasa ko menene. Maganar Almustapha ce ta katse mata tunani

” Ke ma kina son Oumou Sangere ko?”

Ta bude idonta amma bata ansa shi ba. Wani kullutu take ji na bacin ran sa. Zai jawo mata masifa da Luba. Ita ta san kowacece kawarta.

Ya cigaba ba tare da ya kula da shirunta ba

” Na kan ce a Africa babu mawakiya kamar Oumou. Tun tana shekara 5 take waka. Wahalhalun da ta sha a rayuwarta masu yawa ne. Ita kan ta a wakokinta tana wa kanta take da sangare kono a cikin yaren mali. Wato kamar wata tsuntsuwa kenen mai waka”

Rukky ta cigaba da kallon mutumin. Kamar yana mata kwarjini. A halinta na rashin mutunci ta kasa dura masa zagi. Yana yi mata yanayi da kamar ta san shi. A hankali ta ce

“Kono wassoulou, tsuntsuwa mai waka ta wassoulou!”

Dariya yayi. Ya ce

” Haba ni na san abu ne mawuyaci mutum ya kasa sanin oumou”!4

Murmushi tayi. Abinda ita kan ta ya bata mamaki. Ita da take tunanin yanda zata masa rashin mutunci sai ga shi ta bige da masa murmushi! Yau rana daya sai ta ji ta kamar ba karuwa ba! Farin cikin daga zuciyarta ne!3

Ya ga murmushin ya mayar mata. Sai yake ji kamar ba yadda ya tsara ba, daga zuciyarsa ne. A lokacin Oumou ta fara wata waka djorelen. Ya kalle ta a tsanake ya ce

“Djorolen kônô mi kan toula…

Tsuntsuwa mai waka, mai cike da damuwa tana kuka a daji..kin sa da wa take? Da kan ta take! Kina jin yaren mutanen mali?”

Bata ansa shi ba don tana tsoron ansar da zata ba shi. Ba ta so ta ce tana ji ya zamana ta bada wata kofa da za a san ko ita wacece. Sai tayi shiru kamar mai tunani

Ya yi dariya ya ce

” kwantar da hankalinki na san ke ba ‘yar Mali ba ce..ba kiyi kamanceceniya da su ba!”

Murmushi ne ya kuma subuce mata . Komai mutumin yayi birgeta yake. Abinda ya sa gabanta ya buga dam! Ta san tana wasa da wuta. To amma me yasa ta kasa hana kanta bayan ta san wutar akwai zafi?3

A daidai wani lokaci sun iso wani tafkeken guri yana mata kama da gidan gona. Wajewajen gari ne bata taba zuwa irin gurin ba. Sai a lokacin ya juya ya kara kallonta ya ce

” Shall we?”

Ta ce da shi

” ka san abunda muke yi kuwa? Ka san wacece Luba kuwa? Bari na baka shawara idan za ka nemi abokin gaba ka guji Luba domin bata da shamaki. Kuma kai ma ka san tana son ka. Ya za ta ji idan ta ji mun ci amanarta?”4

Dariya ma abun ya ba shi. Dama karuwa na da amana ne? Ka ji ta kamar mutuniyar kirki. Ba kudi suka fito nema ba? To ta tara ta samu!

Ya sa hannu akan sarkarta mai alamar harafin “R” ya dan juya ta ya kalle ta a cikin ido ya ce

” Tauraruwa….ai abun sirri ne!”7

Zuciyarta na raya mata kada ta fara amma ta kasa controlling din ta. Yayi wa Zuciyarsa alkawari na sati daya kacal ya daukar mata daga nan sai ajiyeta kamar yanda yake ajiye sauran tarkacen ‘yanmatansa. Amma yanzu zai mata shigo shigo ba zurfi. Alkawari da ya shayar da shi mamaki.

A satin suka dinke da wani haramtaccen al’amari. Soyayyar ban mamaki da Rukky ke tunanin ta wuce wajen saboda ta yiwa kan ta katanga.4

Haduwar da ta zama silar bankadar sirri, silar tashin hankula har daya daga cikinsu ya qarke a gidan yari!!!!10

#maitafiya

Me karatu ya kake ji a halin yanzu? Fadi ra’ayinka idan labarin nan yana burgekaRashin sani ya fi dare duhu7

Kano, Nigeria

” Ya ya aka yi ki ka fada karuwanci?”4

Tambayar da Almustapha ya wullo wa Rukky kenen a bazata. Tana rike da wani donut a hannunta ta sa baki ta gatsa kenen sai ta ji tambayar, tayi sauri ta hadiye tana mai kallon inda ta gatsa. Ba ta ba shi amsa ba ta ce2

” A ina ka sayi donut din nan? Dadin ba magana!”14

Karasowa yayi yana daura agogon hannunsa ya zauna a daidai inda take zaune kan 2 sitter. Ya kai bakinsa inda ta gatsa ya ci ya ce

” A donutfairy “22

Ta ce

” Me ke nan?”

Ya kalle ta cikin mamaki ya ce

” Ba ki san donut na donutfairy ba? Kuma kina kano? Ke kuwa wata irin ‘yar kauye ce? Ai duk wanda ke kano bai ci donut na donutfairy ba to kamar ya zo kano ne bai ga mota ba!”17

Tayi ‘yar karamar dariya. Ya sa hannu a cikin kwalin ya dauko wani mai kamar an dura abu a ciki ya kai mata baki ta gutsura.

21

Ta lumshe idonta tana taunawa kana ta bude suka hada ido suka kwashe da dariya. Ta ce

” Wallahi sai na ji ni kamar ba anan duniyar nake ba don dadi”3

Ya bude wayarsa ya nuna mata ya ce

“Kin ga shafinsu a instagram, order ake. Ki zama good girl sai a sake miki order. Ko ba haka ba?”

Ta gyada kai tana dariya dama can ba mai yawan magana ba ce. Ya kara maida hankalinsa yace

“Ina tambayarki baki bani amsa ba.”

Ta gane me yake nufi fara’ar fuskarta ta ragu ta ce

” Kaddara”

Ya ce

” Ba kya tunanin wataran ki daina”2

Ta kalle shi da alama ranta ya fara baci ta ce

STORY CONTINUES BELOW

” Na daina na je ina?”2

Da ya lura kamar ba ta so sai yayi shiru. Sun fi wata daya suna boyayyiyar soyayyarsu ba tare da kowa ya sani ba. Kuma a wannan lokacin ne ya ji kamar ba zai iya rabuwa da ita ba.

Wasu irin abubuwa yake ji game da yarinyar duk da dai ba zai iya fadawa kowa ba don a matsayinsa ba girmansa ba ne ya ce ya fada son karuwa.2

To amma sai yayi tunanin kawai bari ya aje ta suyi zaman kai. Amma da sharadin ba zata kara kula wani manemi ba. Kuma ta amince.2

Abu daya ke hada shi da ita wannan shaye shayen nata. Ranar da ya fara ganinta tana zukar wiwi ya tarar da wasu kwalaben syrup a gidan tsananin mamaki ne ya kama shi. Ashe duk yanda yake tunanin yarinyar ta wuce nan? Ashe yarinyar ba karamar lalacewa tayi ba. Ga ta nan a fuska kamar tagari a zuciya ko dafi ce!4

Ya kalle ta ya ce

” Ke kuma me ke birge ki a shaye shaye? Duk wanda ya ba ki shawarar kiyi makiyinki ne”4

Ta dube shi da kallon mamaki. Idan Al Mustapha na magana wani sai ya zaci shi mumini ne! Ga laifi akansa buhu guda ya take yana hangen na wani. Ta ce1

” Kai me ya kai ka neman mata? Shi ma wannan halin arziki ne? Da ni da kai mun san muna aikata haram amma har yanzu mun daina?”3

Ya kalle ta kamar maganar bata bata masa rai ba ya ce

” To ai dama a wannan kalar zunubin kadai kika tsaya shi ne har da tsallakawa shan kwaya! Ki lalace ki balbalce kenen”3

Ta kalle shi kamar hankalinta baya jikinta ta ce

” Dama a lala..ce na nake! Idan na bal..balce wa zai yi cigiyata! Kar ka sake ka damu da ni ko ka ce zaka canjani, ra..yu..wata ba irin taka ba..ce! Ba..za ka gane ba!”2

Kallonta kawai yake. Bai kamata ya damu ba, karuwar titi ce. Amma wani abun mamakin sai ya ji ya damu!

Duk wannan shagalin da ake yi Luba bata sani ba, ba ta kuma shinshino ba. Daga baya ma sai ya siya mata wani karamin gida. Da yake shedan ya gama yi masa fitsari a kai ya zuba mata komai na abubuwan more rayuwa ta bar zaman gidan Hajiya Kububuwa.2

Duk sanda ta rayo masa sai ya kwashi jiki ya tafi gidan da daddare don ba ya so a gane ko shi waye. Wani lokacin kuma sai ya dauketa ya bar gari da ita kamar matarsa ta aure amma fa babu tunanin auren a ran sa.

Luba ganin kowa ya watse ita ma sai ta kama gidan kan ta. Sai ya zamana dai gidan Hajiyar shi ne wajen haduwa ai zaman hira ko warware matsala idan ta taso.

Luba tana nan tana fadi tashin yanda zata karkato hankalin Almustapha amma abu ya ci tura. Saboda tsabar munafunci wani abun da Rukky za ayi a gama amma ko da wasa bata taba nuna musu tana tare da Almustapha ba.7

Rukky ta mato akan Almustapha har take ji zata iya fito na fito da duk wanda ya ke tunanin raba su. Da fari tana tsoron fitinar Luba kar balli ya tashi ta jawo musu masifa. Daga baya ma sai ta daina, a ganinta ai bariki ba zaman aure ba ne balle wani ya tada jijiyar wuya.5

Ai Almustapha tamkar allura ne a cikin ruwa mai rabo ke da shi. Ba kuma don Luba kadai aka halicce shi ba! To don me yasa zata takura kan ta? Kawai sai ta mike kafa ba tare da tunanin me zai je ya dawo ba take soyayya da masoyinta.1

A hankali ta gane ko shi waye da irin karfinsa a kasa. Sai ta kudurce a ranta za ta tayi amfani da hakan ta cimma wata manufa tata.

Me zai hana tayi amfani da wannan damar ta sa ya nemo mata Iliyasou Tillaberi , ta sa ya kwato mata dukiyarta. Ta ga ya girmama a kasa ta san karfinsa ya isa yayi fito na fito da makiyanta. Makiyan da suka jefa a wannan rayuwar.1

STORY CONTINUES BELOW

Zata kara shiga jikinsa ta ayyana a ranta. Ta ga shi ma ta shiga ransa kamar yanda ya shiga ranta. Da sannu karshen wahalarta ta zo, da sannu zata cimma buri

Abinda Rukky bata sani ba shi ne

Burirrika kamar mayaka suke a fagen daga. Wasu su kan kai labari, wasu duk yanda aka so ba zasu taba kai labari ba!3

*********************************

” Kwarankwatsa dubu na rantse da kabarin kishiyar uwata na ga saurayinki da kika mato akan nan nasa da wata a mota. Ban dai ga fuskarta ba amma Alquran ziza ce..daga gefe kamar barbarar yanyawa! Ni kuwa kin san ina dan ganin idonsa a la mirage dalilin kenen ma da na gane shi. To kin ji yadda aka yi”12

Wani abu ya taso ya soki luba a zuci jin maganar ‘yar modu. Wai wannan wani irin hatsabibin mutum ne? Ana banka masa magani amma ko gezau. Ko wani malaminta da taje gurinsa sheran jiya cewa yayi nan da kwana biyu zai zo da kafafunsa. Sai ta ke kuma jin wannan bahagon labarin!6

Wannan wata yarinya ce haka? Lallai kuwa ta tarowa kan ta aradu da ka! Ta kusanci Almustaphanta? Abunda ya fi komai soyuwa a ranta shin ita kuwa tana da makiyiya irin wannan yarinya. Ta ma san ita ta dauke masa hankali yanzu haka ma asiri ta masa. Malamin ziza ya sha gaya mata wai har yanzu duhun da ke kan sa bai yaye ba, wannan wata irin masifa ce!2

Ga shi nan tana ji tana gani ta kasa kula kowa son sa ya zame ma ta bala’i.

Da sannu zata nemo ta tayi mata gargadi mai tsanani akan ta rabu da masoyinta. Ita ai tauraruwa ce mai wutsiya ganinta babu alheri!4

Ta kalli ‘yar Modu ta ce

” wai a ina ka gan su ma? Ni fa bana son labarin kanzon kurege. Mutumin da aka ce duhu ya rufe. Ba macen ma

da zai iya tunkara”

” Yo Allah na tuba Luba duhun da ba duhun kabari ba! Yo ai duhun kabari ne ba zai yaye ba! In miki karya na ce na yi wa wa? Ko da yake je ki Allah zai hada ki da saddiqu sarkin gaskiya ya labarta miki yadda aka yi! Ni din nan dai ai turmin tsakar gida ce sha luguden mahassada! Haka nake ruwan jakara idan ba a sha ni a kauye ba a sha ni a birni!”14

Ya mike ya dauki ‘yar posar sa zai wuce. Dama ziyara ya kawo mata don duk cikin matan nan uku babu wacce ke shiri da Yar modu irin Luba. Sai su kashe su rufe sauran ma ba su sani ba.2

Ta tashi ta janyo shi tana cewa

” Haba tawan. Ke daga wasa. Duk garin nan da bazar wa nake rawa idan ba taki ba?”

Da haka yar modu ya dawo ya ce2

” Ai ca nike iya shegen naku na karuwai zaki min. In cancareki in cashe!ehe! Na san halinku sarai kaza ci ki goge bakinki! Ai muku rana ku yiwa mutum duhun dare. Kin ganni nan, ta kwarankwatsa dubu iya shege na ko shedan ya shafamin lafiya.”5

Nan dai ta rarrashe shi ta ba shi hakuri ya ce zai cigaba da bincika mata amma fa a yawan kudin da ya ji a tudun aljihunsa. Bai bar gidan ba sai da Luba ta ba shi zunzurutun kudi har nera dubu dari biyu.6

Wannan kenen.

***********************************

Abubuwan siyasa suka cigaba da karatowa, Almustapha ba shi da lokacin kan shi. Sun tsayar da dan takara komai yana tafiya yanda ake so.

Masu take masa baya suka cigaba da nuna masa cewa yanzu ne fa ya kamata ya gina sunansa a duniya. Don Watan wataran shi za a tsayar.

Idan ya gama kuciba kucibarsa ba ya qarkewa a koina sai a gidan abokiyar shashancinsa Rukky. Kallo daya yake yi mata ya ji zuciyarsa ta samu nutsuwa. Ko zai ma kan sa karya ya san son yarinyar yake shi mamakin kan sa yake. Sai ya fara tunanin ko Allah ya fara jarabtarsa ne akan irin yanmatan da ya lalata a rayuwarsa?1

STORY CONTINUES BELOW

A lokacin ne ya tashi haikan akan cigiyar Rokaiyatou. Wani abu da yake kwana da shi yake tashi. A wani yammaci sun fito yawon shakatawa shi da Rukky wayarsa tayi kara. Ya duba ya daga sabon detective din sa ne. Sai ya ba shi bayani akan an samu cigaba game da neman yarinyar nan domin an samu wani gida da ta zauna a unguwar kawo.

Abinda ya sa Almustapha paka motarsa kenen a gefen titi don sauraren wannan bayani. Suka yi zai dauke shi a hanya su wuce. Sai bayan ya ajiye wayar ya juyo ya kalli Rukky. Ya gaya mata yana da wani babban uzuri da zai gabatar. Ta ce ya ajiyeta gidan kawarta Hasina ya wuce. Hakan kuwa aka yi.

Almustapha da mutumin suka kama hanya basu tsaya a koina ba sai unguwar Kawo gidan Baban Ali. Ba su sha wata wahala ba don gidan ba boyayye ba ne sai kuma suka yi sa’ar taradda mai gidan zaune akan benci a kofar gida.

Suka yi masa sallama ba tare da bata lokaci ba Almustapha ya masa bayanin kan sa da kuma abinda ya kawo shi. Kafin kace me sai kuka ya kecewa baban Ali. Ya kuma gaya musu labarin abinda ya faru da cewar a halin da ake ciki an neme ta an rasa.

Ai kafin su yi aune Almustapha ya cakumo wuyan baban Ali ya shaqe shi. Shi dama matsalarsa kenen bai iya zuciya ba. Cewa yake

” Yar uwar tawa..kanwar tawa kowanta ya mutu shi ne a karkashin idonka dan ka ya dirka mata ciki? Mahaukaci ne kai ? Kuma daga karshe ka ce min wai baka san inda take ba. To sai ka nemo ta! Da kai da dan ka yau kwa kwana a cell! Wallahi tallahi sai nayi sharia da ku! Sai an daure dan naka ko labarinsa ba zaka kara ji ba!”1

Abun da ya janyo hankalin mutanen unguwa kenen suka kwaci baban Ali da kyar! Sai a nan wani makocin su yake masa bayanin ai dan nasa ma ya fi shekara biyu a daure sun je wani gida sata a kama su. Har yau bai fito ba.1

Tsananin bacin rai ya sa Almustapha barin gurin ya fada mota. Kawai sai ya ji wata kwalla ta tarar masa a ido. Yarinya kankanuwa, marainiya da ciki a jikinta ta bace kamar batan tattabara? Wai yana raye wadannan abubuwan suke faruwa?2

Shi ba yayi cigiya a gidan radio ba yana tsoron mahaifinsa. To ma ya ma san kamanninta ne? Yarinyar da ba zai iya tantance ta ba a cikin mata biyar.

Wani abu ya ji yana masa yawo a zuciyarsa ya rasa inda zai saka tausayin yarinyar a ransa. Yana ganin kamar da sakacinsa ma. Cewa yake1

“Momodou ka yafe min…na gaza amma da sannu zan cimma buri!”

Haka suka bar harabar gurin detective din na lallashinsa da cewar zai kara iya kokarinsa. Ya sauke shi a hanya.

Da kyar ya biya ya dauki Rukky fuskarsa kamar hadari. Tana kallonsa ta san akwai matsala. Bata taba ganin hakan a tare da shi ba. Ta so ta ji me ke damunsa ya ce ” its personal”.

Ya ajiyeta a gidanta kawai ya wuce. Ta bi shi da kallon mamaki. Hankalinsa yana kan Rokaiyatou , ina zai gan ta?1

Ba ayi sati biyu da faruwar hakan ba yana zaune a ofis din sa aiyuka sun cabe masa. Yanzu Almustapha ya lura cewa yana da mahassada sai yayi taka tsantsan. Yan adawa sun fara sako shi a gaba.

Amma yana ji a jikinsa jamiyyarsu ta DSP ita ke da nasara. Don ya bi suk wasu hanyoyin samun daukaka da nasara ya bude. Yana da mutane manya manya a sama yana da mutane a kasashen ketare masu fada a ji.

Yana zaune a ofis din ne ya ji kiran detective din sa ya ce ya shigo ya same shi a ofis. Detective sammani ya karaso. Almustapha ya ce su dan fita ta harabar balcony su sha iska sai ya gaya masa a yanzu halin da ake ciki ko ana samun cigaba.

Suna tsaye a gurin ne Almustapha ya ce

” Yaya batun yarinyar nan? Ka san fa ya kamata ka zage da aiki tukuru domin kuwa zan iya kashe ko nawa ne akan wannan binciken.”

STORY CONTINUES BELOW

Detective Sammani yayi gyaran murya ya ce

” Ai yallabai aikin ne yana da matukar wahala domin kuwa babu hoton wacce ake nema. Dadin dadawa nema ne muke yi a cikin sirri ka ce babu damar mu sanar a kafafen yada labarai. Hope dina ya ta’allaqa ne a gidan da muka je sai aka yi rashin sa’a nan ma babu labarinta”

Almustapha ya nisa. Kan sa ya daure. To ko zai fara cigiyar a gidan radio ne? Komai ta fanjama fanjam. Maganar detective sammani ta katse shi da ya ce

” A cikin satin nan ne ma da dan ji wata jita jita. Wai kamar an taba ganinta a wani gari da ke hanyar zinder”

Almustapha ya zaburo gabansa na dukan uku uku ya ce

” wani gari ne haka?”

Ya ba shi amsa da

” Matamaye”

Almustapha ya hade girar sama da kasa alamun zancen bai zauna masa ba ya ce

” Har mai zai kai ta wannan kauyen? Me take yi? “

Babu wani kwana kwana ya ce

” yanzu haka ba zai wuce karuwanci ba”

Wata irin zabura Almustapha yayi har sai da detective din ya tsorata. Sai ya ji da ma bai fada ba saboda ganin irin shakar da yayiwa mutumin nan rannan.6

Wani irin daci ya ji ya mamaye masa zuciyarsa har bai san lokacin da ya nunawa detective din danyatsa ido jawur ya ce

” Yar uwar tawa zaka danganta da wannan mummunar kalmar? Kan ka daya kuwa?”10

Ganin yadda ransa ya baci matuka ya sa detective sammani cewa

” Yallabai ina ga fa ba ita din bace. Al’amarin zai iya zama jita jita.”

Daga nan Almustapha bai kara cewa komai ba ya buga tsaki ya koma cikin ofis din detective sammani yayi ficewarsa yana mamakin irin wannan zafin rai.

Ko da ya dawo cikin ofis din ma sai da ya nemi robar ruwa ta swan madaidaiciya ya kwankwade, mamaki ya kama shi wai Rokaiyatou ake dangantawa da karuwanci! Karuwanci fa! Me aka yi aka yi wannan sana’a. A ce jinin Ahmadou Tillaberi ta kare a haka? Inaa karya ne!7

Yanzu da a ce Momodou zai dawo duniya ya ga ya bar Rokaiyatou na karuwanci ai sai ya kashe shi! Ashe ma bai kai a ba shi amana ba! Ashe ma shi ba danuwa nagari ba ne!4

Mutuwar Momodou na tsaya masa a rai shin akwai wanda ya kai shi jin ta kuwa? Ji yake kamar wani bangare na shi a cire an yar har yau ya kasa daidaituwa.

Idan ya tuna maganganun da suka tattauna saura bai fi kamar kwanaki kadan ya rasu ba sai tausayi ya lullube shi. Ya kan ce masa

” Ina kamnar ta tun tana zanin goyo. Bata da wanda ya hi ni bani da wanda ya hi ta”!

Matar danuwansa!

Allah ya cika burin momodou an daura..Allah bai yi za a zauna ba!

Rokaiyatou ashe burin naku da Momodou ba mai nisan zango ba ne?!

Abu daya yake gani kamar ya zame mi shi wajibi. Ya nemo yarinyar nan ya mata gata. Mahaifinsu shi ne silar komai ya kamata shi ya gyara.

Ina ma za a gan ta , da sai yayi mata gata irin na uba! Shi zai aurar da ita, sai ya nemi mutum kamili wanda zai rike amanarta! Idan haihuwa ta yi zai kula da yaron! Wa ya jawo? Ai su ne!4

A irin wannan tunanin ne ya ji zuciyarsa tayi baki kirin har ta kai shi ga janyo durowar teburinsa ya zaro kwalin taba. Abunda ya dade bai yi ba. Dama bai cika sha ba sai idan yana cikin bacin rai.

Ya kyastawa kara daya lighter zai zuka kenen sai ya tuno maganganunsu da Rukky. Yanda yake nuna mata ba ya son zuke zuke. Sai ya kashe ya yar. Bacin rai ne kawai ya taru ya masa yawa.

Abunda ya assasa lamarin bai wuce kiran da Hajiya khulsomou tayi masa ba na zagin kare dangi dazu. Wai dan ta ya mutu ya hau kan dukiya ya danne. Abu daya yasa bai tanka mata ba, Momodou.

Sannan ya wayi gari da son siyan wasu kanfanunnuka da suke so su hade da nasu. Dukiya bata son sanya, rassa ake mata domin ta cigaba da yado tayi mamaya yanda ‘ya’ya da jikoki zasu ci moriyarta.

Bai tashi daga ofis sai da ya tabbatar ya gama maganar siyan kanfanunnkan nan. Abu daya ne ya katse, shi shigowar sako wayar shi. Daga Rukky ne. Ya karanta

” Hi….je suis amorex!” ( im in love!)2

Ya gane sakonta domin yana jin faransanci sai ya ji kashi tamanin din kuncin zuciyarsa ya tafi! Me yasa yake jin haka game da yarinyar?

Dama tana jin faransanci?

To wai ‘yar ina ce ma?

Kamar lokaci yayi da zai san wacece ita!14

Rashin sani…shi ya fi dare duhu

Ina ma ya san waccece

Ina ma ya sani …kafin lokaci ya kure

Ina ma ya sani…kafin lokaci yayi halinsa

Lokaci sakarai ne…yakan tafi da abinda ka ke so!

About AIS

Check Also

MAI TAFIYA CHAPTER 4

MAI TAFIYA CHAPTER 4 Www.bankinhausanovels.com.ng  Duniya budurwar wawa…kowa ya daka ta tata ya sha kuka!4 …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *