MAI TAFIYA CHAPTER 4

MAI TAFIYA CHAPTER 4

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Duniya budurwar wawa…kowa ya daka ta tata ya sha kuka!4

Kano, Nigeria

Ahayye..yau ana shagalin duniya a gidan nan” cewar ‘yar Modu ” gaskiya ku din nan an yi ‘yan kwal uba! Kamar lokacin da uwarku take da cikinku ta zagi ubanta! Wannan balbalcewa haka.2

Ko da yake zaman duniya ai ta gaji haka..in dai da ranka ai dole sai kayi motsi. Rayuwa idan ba ka daga ‘yar kwalbar nan kana dan zuke zuken nan ya kwakwalwarka za tayi kiliya? Ai sai dai bakin cikin duniya ya yasarka a gindin kwalbati irin yadda ya yada uwata da tayo cikina a kwararo. Billahillazi bata mike ba sai da ta sankato ni! Ahayye Allah raba mu da takaicin duniya…cas!6

Rukky ce ta kalle shi tana dariya

” Dama ‘yar maduwaye kai shege ne? Katakatan uba! Haba dole tambadewar tayi yawa ka ce tsotso kayi a nono..hahaha” ta kwashe da dariyar ban haushi5

Yayi sakaka da baki

” Yo ke uwar taki da tayi cikinki ta hanyar halas alfahari tayi da ke? Ku ji ni da karamar ‘yar iska. Me kika fasa?kwanan gida ko sane? Ko kuwa idan kun hallara a gaban Allah ana gobe kiyama za ta nuna ki a cikinmu ta hada ubangiji ya jefa ki jahannama? A billahillazi Rukky yanda na san zan mutu haka na san sai mun dandani wuta! Duniya gidan dadi! Allah kar ka kashe mu bamu tuba ba…ahayye nanaye! Gargadi na karshe kar ki kara sani a jinsin da ba nawa ba..To kin ji!”5

Hindu tayi caraf ta ce

” Amma ‘yar moduwaye an yi dan tselan uwa Rukky ka ke cewa za ta shiga jahannama? To kai gida Allah zai gina maka a aljanna? Akwai abunda ma ya kai daudu zunubi?”1

Maimakon ya kula ta sai ya dauko karan tabarsa ya kunna ya fara zuka ya ce

” ke Hindu shi zunubi yana da kankani yana da mai yawa ne? Yo Allah na tuba ko da sata a ka bar ku ai sai dai ku hango mu a karshen siradi mun tsallaka mun bar ku. Ai wuyarta kan ka mutu kayi taubatan nasuha cikakkiyar tuba kenen. Ka kuma shaidawa Allah ba zaka koma i zuwa wannan aikin zunubin ba. Yo ke ‘yar nan ba ki je islamiyya ba? Dan ahalarin nan ma ba ki haddace ba?”

Hindu ta zuba masa ido da mamaki ta ce

” Ta ce wai kai anan din nan har islamiyya ka je? Amma a bige da daudu? Wanda ya sani ya take shi Allah ya fi hukuntawa!”1

Ya kalleta yayi sakkaka da baki karan taba na reto a lebensa ya ce1

” Allah jikar Alaramma wacce aka yi cikinta aka haife akan dandamalin masallaci! Aka yiwa uwarta wankan jego da ruwan alwala! To duk yadda aka kai ga tofe ki da kul’a’u zai idan ba ki shuka khairan ba ba ki tadda shi gaba! Ehe kin ji na gaya miki.18

To ‘yar ni din nan da kika raina izifina 20 cif! Hadda kuwa tun daga alhamdu abunda yayi izza sama’u zuwa kulu hiya babu wacce ban iya ba! Kin ga kuwa ina da na sallah wacce muke dan jejjefa ta haka kar abun yayi mana yawa. Babun badiluhu..mu ba tsinana abun arziki ba mu ba mu zauna a musuliluncin ba. Kin ganni nan Alquran Hajiya nike don bara biyu da ta wuce na je aikin hajji na sauke farali..ai aljanna ta mai rabo ce! Ahayye…cas!”16

Hindu ta karkace kai ta rangada guda ‘yar Modu ya bata hannu suka kashe. Ran su tas suna ganin duniya ba a bakin komai ba.1

Duk wannan shagalin da ake a Gidan Hajiya Kububuwa ne a wani tangamemen falo kuma ba su kadai ba ne a ciki. A can gefe kowa shagalinsa yake..yawa yawansu wasan karta suke. Wasu suna gefe suna shaye shaye.

In da su Hindu ke zaune su hudu ne. Hindu, Rukky , Luba sai ‘yar Modu. Duk wannan hirar da suke ita Luba bata sa baki ba. Ba ta da wani aiki sai zukar wiwi dama gwanace amma tana saurarensu tsaf. A lokacin ne ta ga Rukky jikinta yayi sanyi da maganar da ‘yar Modu ya dankara ma ta. Kawai sai ta tashi ta nufi inda take ta cusa ma ta tabar wiwi a baki ta ce

STORY CONTINUES BELOW
” wayyo Allah na sukari…ai tunani ba naki ba ne! Kin ga duk duniya babu abunda ke yakice tunani irin wannan abar. Ki sha ta ki more ki ji kamar yau aka nada ki sarauniya..ki ji duniyarki fes! Yi ma ta zuka daya tak sukari..wataran idan kika kamata ba kya barta ba!”1

‘Yar Modu ne ya sa baki ya ce2

” wallahi! Ai idan zaka sha giya ka sha ta dubu! Kowa ya tuba don wuya ba lada! Duk wanda bai fasa ba ni ‘ yar moduwaye na ce tsinannne dan gaba da kasan wuta!! Yarinya ki sha wanda bai sha ba ya bar dadin duniya…ahayye..nanaye..yau ana shagali!!”2

Rukky ta kafa kai ta zuka sau daya.

Luba ta ce

” wannan ai ba zuka ba ce. Ja za kiyi sosai ta shiga hanjinki da huhunki ta koro miki tarin matsaloli. Gobe idan an ce ga damuwa ko hanyar inda kike ba ta bi ba. Ja sukari..ma za ja”2

Rukky ta kama ta ja da kyau..wani tari ya sarkafe ta ta fara malelekuwa a kasa tana surutan banza. ‘Yar Modu da Luba na mata daria. ‘Yar Modu ya ce1

” Da kyau ‘yar gidana ai da koyo akan iya. Ai abun ban haushi bai wuce na ganni a layin ‘yan wuta ba ke ba, ina zan sa kai na? In je in shiga uku ga miji barawo ga kishiya mayya!”14

Hindatu ce ta buga tsaki ta gyara zama ta cigaba da danna waya. Chatting suke da wani maneminta tana so ta lallaba shi ta wanke shi tas! Wani tunanin kuma yana kan yaranta tana tuna dadewarta bata je dubo su ba amma dai aiken kudinta baya yankewa. Ta fara tunanin ta sayi gida na ta na kan ta ta kwaso yaranta abunta ta ajiye masu kula da su. Budar bakin ta ta ce

” Allah ya kiyaye. Ni duk iskancina wallahi bazan yi shaye shaye ba. Da me zan ji? Ko na tuba kaina ya kwarkwance..iya shege ya iya shege amma shaye shaye har abada! “3

‘Yar Modu ne ya karkace kai ya rangada guda. Ya ce

” An ki cin biri an ci dila…da sannu dai! Ai masomin hauka soshe soshe”7

****************************

Yanzu Hindatu tsarin da kika daukarwa rayuwarki hanya ce mai bullewa? Yanzu wannan rayuwa ce da ya kamata ‘ya’yanki su taso su gan ki a ciki? Kin girma amma kina cin kasa? Gaskiya kin yi karkon kifi daga ruwa kin koma wuta!”

Hindu ta daga kai ta kalli makauniyar mahaifiyarta ranta a cushe, gabadaya ranta ya gama baci. A nata hangen ai yanzu ta wuce nan, a wani zauna ana mata fada kamar karamar yarinya. Da can babu ce tasa take jurewa yanzu kuwa ba ta ga abunda ta tarewa wani ba.1

Zaune take akan wata kujera ‘yar tsugunno sanye da wani ubansun leshi mai ruwan shashanbali. Bata ko yafa mayafi ba ta turo daurinta gaba daidai da zamani. Ta na danna wata tsadaddiyar waya a hannunta hade da tauna cingam kas kas.1
Hindu na kallon duniya wani fage na ‘yancin kai. Ranta na raya mata ta isa don rayuwa ma yanzu ta fara. Ta kalli uwar ta ce3

” wai Hajiyarmu me nayi? Babu dama in shigo gidan nan sai ki ta min fada. Na san ba zai wuce zantukan mutane ba, su yanzu mutane da kike ganinsu fatansu a kullum su bata ka ko sukai suka. Bakin ciki ake mun an ga Allah ga daukaka ni alhalin da can an ga na zama liability. Wannan aikin dana samu ne fa yake tsonewa mutane ido”

Hajiya Uwani ta kama baki cike da mamaki ta ce

” Hindatu ni ce me miki bakin cikin?” Sai ta fashe da kuka1

Hindu ta ce

” Aah Hajiya ke ma kin san ba da ke nake ba da ‘yan gulma nake irinsu Safara. Ba tayi aure ba ba a huta ba tayi aure ba a huta ba. Su suke zuwa suke kawo miki zancena. Na ga duk wani abu da ake bukata daga ku har yara ina kawowa. To na samu aiki sai na bar aiki na zo na tsugunna muna zaman warrabbuka? Haba i cant “2

STORY CONTINUES BELOW
Hajiya tayi shiru yanzu hindatu tsoro take ba ta ce1
” Aiki dai aiki dai wannan wani irin aiki ne na shekara da shekaru da kamar ke kwanan gida ya gagare ki? To shikenen ya maganar aure? Yanzu dai autarku ce kadai a gabana sai ke da kika fi karfina. Aure dai shi ne mutuncin diya mace”

Budar bakin Hindu sai cewa tayi

” Na farkon dana yi Hajiya da me ya qare ni? Ai da muguwar rawa gwamma kin tashi”2

Kafin Hajiya ta ce komai sai Abba da Asiya suka yi sallama suka shigo. Suna ganin mahaifiyar su sai suka rugo da gudu suka rungume ta.

Ta kankame su a jikinta tana jin wani irin nishadi na tsirga mata. Yinifom ne a jikinsu amma sai taga sun zame mata abun kallo sun yi fes da su. Da yanzu sun mutu ko kuma suna cikin ha’ula’i saboda zafin talauci, abinda zuciyarta ke gaya mata kenen.

Abba ya kara tsawo yayi wayo ya kai shekara goma sha daya. Ya kura ma ta ido har ta tsargu ya ce

” Mama na dauka ke ma kin mutu ne kamar babanmu. Muna kwana dayawa bamu gan ki ba. Kar ki tafi ki bar mu kin ji mama”

Sai taji kwalla ta tarar ma ta. Ta kankame su a jikinta kamar zata maishe su cikinta. A lokacin ne Abba ya fadi wata magana da ta nemi ta tarwatsa.ma ta kwakwalwa. Ya ce

” Mama wai menene karuwa?”4

Ai bata san lokacin da ta fizge shi daga jikinta ba ta wancakalar da shi a gurin . Wani irin kallo take ma sa na tsananin mamaki. Cikin zafin rai ta ce

” Abba a gidan uban wa ka ji wannan kalmar!”

Shi ma jikinsa yayi sanyi ganin yadda uwar tayi. A marairaice ya ce

” Mama zagi ne ko? Ba ni ne na fada ba. Su munkaila ne ‘ya’yan gidan Hajiya Mari suke fada. Idan muka je makarantar allo ta Malam dogo sai su ce wai ba zasu zauna a kusa da ni ba ko baza su sammin alewarsu ba wai inji mamansu ni dan gidan karuwa ne!!”2

Wani abu ya soki ran Hindu ba da wasa ba wai duk yadda take tunanin tana boye rayuwarta daga kan idon wadanda suka san ta ashe abun ba haka bane? Har ma wai an fara yiwa yaranta gori? Ah lallai yau mai raba ta da Hajiya Mari sai Allah. Kawai sai ta tashi a fusace za ta fice. Hajiya Uwani ta gane fita za tayi ta ce

” Zo nan! Dawo nan sakarya ana mata hannunka mai sanda idanunta sun rufe! Dawo ki zauna”

Ta dawo sai huci take na bacin rai. Yaran sun kura mata ido suna kallon uwar ta su kamar bakuwa. Ta ce

” Hajiya wai ba ki ji yanda ake zagi na ba? Wai ‘yan unguwar nan me suke so da ni ne? Habu ya gudu ya bar ni akaita yamadidi da ni yanzu na samu na dogara da kai na abun kuma ya zama kazafi. This is nonsense!”

Uwar ta ce a sanyaye

” Hindatu, kin ga rayuwa ? Ba a mata shigar sauri! Kin ga duniya? To budurwar wawa ce duk wanda ya daka ta tata to zai sha kuka! Kin girma ba sai an zauna ana gaya miki daidai da ba daidai ba sai dai ke ki gayawa wani.

Yanda kika dau rayuwa wasu dayawa sun dauke ta fiye da ke sun kuma ajiye ta a lokacin da basu shirya ba. Ni dai kin ga karfina ya kare abunda zan muku na yi. Wanda na gaza Allah ya sani ba don son raina ba ne sai dai bazan iya ba. Ki kama kan ki kiyi aure Hindatu lokaci bai kure miki ba.1

Hindatu idan ni ce sanadin jefa ki a wannan rayuwa..ki yafe min..ki yafe min hindatu”6

Kawai sai ta fashe da kuka. Maimakon ta ji ma me take fada sai ya kara kulewa. Matsalarta da Hajiyarsu kenen abu kadan ta saka a gaba tayi kuka. Tana ce ita ma haka tayi kukan? Wa ya cece ta?

Tayi aure to wa zata aura? Tayi tsaki a hankali kwata kwata maganganun ma basu shigeta ba. Tayi nisa ba ta jin kira. Ta ce1

” Ni dai Hajiya ba ki min komai ba ni ban ce kin min wani abu ba. Kawai dai zancena na karya da ake kawo miki ki hau ki zauna nake rokonki dan Allah ki daina. In don yara ne ma kawai zan zo na kwashe su akwai wani shiri da nake yi. Maganar aure ki sani a addua Allah ya fito min da nagari”

STORY CONTINUES BELOW
Uwar bata sake magana ba, abun ya sha mata kai.

Hindun ta kalli Abba ta ce

” kar in kara jin wannan kalmar a bakinka. Karya suke maka ka ji ko?”

Yaron ya gyada kai ahankali. Ta ce tana murmushi don su saki jiki

” ku zo ku ga abubuwan dana siyo muku na kayan wasa kala kala. Abba kai har da kwallo Asiya ke kuma har da ‘yar bebi”

Abinka da yara sai suka fara tsalle suna murna. Siyayya ce tayi musu baja baja. Ta kira kanwarta maryam da take kula mata da su ta bata na ta da na uwar. Hajiya uwani dai bata kara cewa komai ba a zuciyarta ta ji kamar ta ce ta kwashe kayan bata so. Amma sai taji kamar tsoron Hindatun ma take ji. A ranta ta raya Allah ya shiryeta idan mai shiryuwa ce.2

Tana gama abunda za tayi ta tashi tayi tafiyarta bayan ta yiwa yaran alkawarin dawowa nan ba da dadewa ba. Ta isa gurin motarta ‘yar madaidaiciya kirar corolla ta bar unguwar. Tunane tunane ke dawo mata rai na ganin yanda aka sa mata ido, ko ina ruwansu oho?

Tana da appointment da wani Alhaji Bala wani tsohon ministan gwamnatin da ta shude. Sun yi da shi zasu hadu a wani joint ta san yau ranar arzikinta ce.

Ita komai take yi tana yi ne don yaranta zuciyarta ta raya mata hakan. Kuma kafin su Abba da Asiya su girma za tayi sauri ta tuba ta tara abunda ta tara sai kawai ta bude kasuwanci. Tana son yaranta tana kaunarsu. Ba ta dalilin Abba ba ne don ta ceto ransa ta fada wannan harkar? Da irin wannan tunane tunanen ta tuka motarta ta bar unguwar.1
Ina ma Hindu ta san cewa Abba zai kyamace ta! Irin kyamatar da tayi wa talauci! Ina ma ta san zai yi fatan dama ace bata haife shi ba! Ina ma ta hakura! Ina ma lokaci bai yi halinsa ba!2

Lokaci sakarai ne, ya kan tafi ba tare da ya waiwayo ba, ya kan tafi da burirrika ya kan tafi da imani. Ina ma ana dawo da hannun agogo baya..kaico!!2

*********************************5

Aminan uku Hindu, Rukky da Luba ma fi yawancin abunda za suyi tare suke yi. Amma babu wanda ya san ainihin cikakken labarin danuwansa. Sukan yi hirarrakin duniyarsu su kuma yi zantukan samarinsu da hanyoyin da zasu bi don su wanke su.

A wannan shekarar suke shawarar barin gidan Hajiya Kububuwa ba don wani abu ba sai don cewar su ma sun giga sun bunkasa. Hindu na da sha’awar ta ware gidanta daban don ta kwaso yaranta da me kula da su. Suk wasu harkokinta na iskanci za ta yi su a waje don ba ta son yaran su gane ko ita wacece. Kafin su kara girma su mallaki hankalin kan su zata watsar da wannan sanaar ta tuba. Tunaninta kenen.1

Kowacce a cikinsu tana da mabanbancin halaye.
Hindu ita ce me dan hankali kuma ta fi su kaifin tunani. Yawa yawan dubarirrukansu Hindu ke tsarawa da yake ta fi su zurfin ilmi. Hakannan duk cikinsu ta fi su magana da son jan mutum a jiki da kuma rashin tu’ammali da kayan maye. Tana son yawan saka turanci a maganganunta.

Ko taba sigari ba ta sha bata da wani buri irin yaranta su girma cikin gata da jin dadi. Ita kuma ta yi rayuwa cikin baja baja da annashuwa, watakila ma gaba idan ta tuba har tayi aure.3

Luba dama yar gararamba ce. A duniyarta bata taba wasu cikakkun kawaye ba sai a yanzu, kuma hakan yana mata dadi. Ashe dama ba duka kawaye ba ne maciya amana? Don gaskiya hankalinta ya kwanta da Hindu da kuma Rukky.
Duk cikinsu ta fi kowa shaye shaye ba abunda ba ta sha. Ta sha giya, taba wiwi roci babu wanda Luba ta bari. Tana yawan saka larabci kadan kadan a maganganunta.Hakannan ta fi son kudi da abun duniya. Ta fi su kaifin wayo da son kai. Luba ta fi gane komai a duniya a ce ta fi wani kuma nata ne ita kadai.2

Ta fi su gogewa a barikanci da sani yanda ake tafiyar da maza. Bata da wani buri irin ta girma ta buwaya ta zama gawurtacviyar yar siyasa ta wawashe kudin gwamnati.5

STORY CONTINUES BELOW
Ma fi kankantar shekaru a cikinsu ita ce Rukky. Ba ta da yawan magana ba ta da yawan fada. Duk cikinsu babu wacce samari ke kaiwa caffa kyawunta yake ruda su irin Rukky. Ta gwanace da hilatar da namiji da kwakular kudi. Tana yawan saka faransanci a maganganunta.1

Sannan tana da kwanta kwanta maciji sari ka noke a fuska kamar mutuniyar arziki a zuci kuwa ita ta san tuggun da take kullawa. Duk duniya bata da wani buri irin ta girma ta bunkasa ta kai wa makiyinta hari. Da hakan take kwana take tashi.1
A cikin kwanakin nan ma da Luba ta koya mata shan wiwi bata da aiki sai ta samu guri tana zuqa Kamar Allah ya aiko ta. Sai ta ji ranta fes! Tunaninikanta sun tafi.2

A wata ranar lahadi da misalin karfe shida na yamma ‘yar modu ya fado musu daki suna baccin asara. Ya fara yayewa kowacce bargo ya na cewa2

” kai ku ji min sakalci. Lallai na yarda mata suna suka tara. Yo ai duk inda mace me zaman kanta ta isa da kanta duk inda 6 tayi ta shiga ta tsala wanka lokacin neman kudi yayi. Wallahi ni ‘yar moduwaye tun da uwata ta sallo ni duniya ban taba gani tabararru irinku ba!”2

Hindu ce tace

” Look ‘yar Modu ya zaka fado mana daki haka kawai ba wani neman excuse? “1

“Eskis din uwaki!” Ya ce da Hindu yana aiko mata dakuwa ” ka ji almura kamar gidan ubanta! Yo ni ai ko dakin uwaki na fada ba eskis! Menene banbancina da ita?”3

Babu wacce ta kara kula shi don idan da sabo sun saba da halinsa. Kawai sai ya fada bandaki ya tara ruwa ya fito ya ce3

” Ni fa akan aikina nake don ko sojojin da aka aika dajin sambisa ba zasu nuna min aiki ba..ehe! Kowacce yar iska ta shiga ta sallo wanka yau bamu da wajen zuwa sai La Mirage.1
Wani hadadden gurin ‘yan caca ne na kasaitattun masu kudi. An ce duk karuwar da ba ta je La mirage ta baza hajjarta ba, ta kasa an samu mai saye da tsoka to ta cika mai bakin jini! Ni kuwa na kara da tsinanniya ce da aka kade uwarta dauke da cikinta da bakar mota da daddare!!ahayye..ras!”3

Ai jin samuwa ce sai suka tashi zumbur suka fara shiri. Kowaccensu tayi irin tata shigar da ta fito da irin na ta kyawun.

‘Yar modu cikakken kawali ne da yake aiki da Hajiya Kububuwa sama da shekara 10. Babu wani wanda ya girma ya gagara da iskanci da ‘yar modu bai san shi ba. Duk wata kulla kulla ta gidan Hajiya da shi ake yi. Duk wata mai son a hada ta da wani gawurtacce to sai ta bi ta yar modu don ta samu abunda take so.1

La Mirage wani katon wuri ne na holewa na wadanda suka ci suka ta da kai da nera. Babu abunda aka gwanance a wannan gurin sai caca. Duk wani rikakken dan caca da ya giga ya gagara to za ka same shi a la mirage.

Tun da suka je ba abunda ake sai sharholiya. Wani fitaccen mawakin kasar Ghana aka gayyato yana wasa a gurin. Dama haka suke idan sun yi nishadi sai su gayyato manyan mawaka daga kasashen duniya su zo suyi wasa. Maganar shan giya da sauran kayan maye kuwa ba a magana. Wani abun ban haushi shi ne yawa yawan mazan gurin masu iyalai ne da suka mayar da nan wajen badala.1

Duk cikin yanmatan kowacce ta kama saurayinta. Wani balaraben kasar lebanon shi ya makalewa Rukky ita kuma Hindu wani Alhaji Tanimu mutumin jahar katsina. Luba na tsaye da nata manemin wani matashin yaro da ake kira Zayyad.

Irin lalatattun yaran masu kudi din nan ne da ba sa jin kwaba. Mahaifinsa babban attajiri ne ya sangarta shi yaron ke yin yadda ya so. Ba shi da aiki sai caca da shaye shaye babu mai ce masa don me.

A kan tebur din su ne yau ake dabdala ake buga wasan karta kamar ba gobe. Mutum zai iya shiga da mota la miraj ya fito daya shi sai kayan jikinsa saboda an cinye su a caca! To daren yau ana buga wani wasa ne tsakanin matsahin yaro zayyad da wani mutum magidanci Idi Maina.

Ihu kawai ke tashi kowa da magoya bayansa. Wani abun mamaki Idi Maina ya yiwa zayyad kankat. Tun daga motar da ya zo da ita har agogon hannunsa sai da ya ciwo su. Za a tashi wasa zayyad ya ce bai yarda ba a buga wasan karshe. Idi Maina ya ce ya ji amma akwai sharadi. Ya ce masa ya fada a ji.1

Idi Maina ya dago ya karewa Luba da ke tsaye akan zayyad kallo, hannunta rike da tambulan tana kurbar lemo a hankali ya ce

” wannan yarinyar taka za ka bar mun..in dai na kayar da kai to ni zan tafi da ita”

Cikin zafin rai zayyad ya ce ya ji! Ya ma fizgo ta ya kawo ta tsakiyar fili gani yake kamar abun ba zai yiwu ba. Ita kuma Luba sai dariya take ganin ai yau ta isa har mazan fama na fada akanta. Ba a tashi wannan wasan ba sai da Idi Maina ya ciwo Luba a CACA!!3

Idi Maina a ranar ya zamewa Luba wani tsani…tsanin da yayi sanadin da ta fada wani tarko. Tarko irin na so.. bai ban mamaki!

Soyayyar da ta zo da alakakai da yayi sanadiyyar tarwatsewar amintar kawayen guda uku. Shin wannan wata irin soyayya ce?????

Tarkon so….tarkon kauna.4

Kano, Nigeria

Ayye mama ayye mama, mama ye iye
Ayye mama labo labo, mama ye iye
Da aure ya kan raba aure, mama ye iye
Da na biki mun tafi tare, mama ye iye3

Kandala ta cigaba da rera wakarta tana jefa danwake. Dirkekiyar mace ce da ta doshi shekara 50 a duniya. Fuskarta na dauke da fashin goshi, yanayin fatar jikinta tayi haske irin na bilicin da kuma dabbare dabbare na tabubbukan da bilicin din ya bar ma ta. Lebanta sun yi baki sidik saboda shan taba.4

Jikinta sanye da wata atamfa code vore da aka yiwa dinkin zurmemiyar riga mai aljifai na saka kudi. Fuskarta ba yabo ba fallasa tana jefa danwakenta na siyarwa da yayi suna. Daga wajaje daban daban ake zuwa saya a wani kango data kama. Tana da kananan ma’aikata masu zubawa mutane da mika musu.2

Kandala wata tsohuwar karuwa ce da duniya ta yi mata atishawar tsaki daga karshe ta qarke da sana’ar danwake. Ba wai ta daina kananan iskance iskance ba ne, kawai dai yanzu duniya bata ta tata.16

Daga gefenta kadan Rukky ce kwance akan wata tabarma tana ta bushe bushenta na iska. Sanye take da wani wando tiri kwata da ya kame ta tsam, ta sa wata riga marar hannu. Duk wanda ya shigo kangon nan yakan zuba mata ido cike da mamakin rashin kunyarta amma ko a jikinta.9

‘Yan iska kuma zauna gari banza su ke jifanta da fito ko yabo amma babu wanda ta kula.2

Sai ma ta kara mikewa ta dago kafarta tana karkadata a hankali. Duk na mujiyar mutanen nan ma su siyan danwake su fice bai dada ta da kasa ba.2

Wajen danwaken kandala wani waje ne da Rukky ta mayar wajen nishadi. Anan ta kan zauna idan bata son magana da mutane tana so ta kadaice tayi tunane tunanenta na duniya. Haduwar jininsu da Kandala ya sa ta mayar da gurin wajen zuwanta ko banza ta mata hirar duniya.3

Tana wannan kwanciyar ta lissafa yawan wakokin da kandala ta rera a zamanta na kasa da awa biyu. Ta rera sama da 20..tana kan ta ashirin da daya. Shin wannan matar na da matsala kuwa? Ta dauke tunaninta daga kan wakokin kandala ta koma tunanin abunda ya shafe ta.1

Burinta a duniya bai wuce ta kai wa makiyanta farmaki ba..to amma ta yaya. Ta zata i yanzu ta gawurta ta kai matsayin da za tayi fito na fito da su to amma abun ya gagara. Ga shi ba ma ta da wani takamaiman labari a kan su. Idonta idon Iliyasou Tillaberi ko wani da ya dangance shi, to kashinsu ya bushe.

Muryar Kandala tana aiken wani yaro shi ya tsayar ma ta da tunaninta.Ta ji ta ce

” kai ajiye kwanonka a nan in aike ka”

Ta zira hannu a daya daga cikin aljifan rigarta ta zaro N20 ta baiwa yaron ta kara cewa
” maza maza je ka shagon Namadi ka siyo min taba rotmans..idan ka siyomin benson sai na ci uwarka…”9

Ta karasa tana nuna masa danyatsanta sabbaba alamar gargadi. Sai daga baya ma ta karewa yaron kallo ta washe hakora ta ce

” Au…au..ashe ma isuhulle ne na wajen tabawa….ai ga idon nan irin na uwarka..maza je ka kafin ka dawo an zuba maka”15

Yaron ya fyalla a guje. A wannan lokaci ta gama jefa danwaken ta dauraye hannunta ta goge a jikin atamfarta. Masu saya sun fara raguwa dan isuhulle ya kawo mata tabar ya dauki kwanon danwakensa ya tafi.
Mutane suka watse saboda danwake ya kare sai masu taimaka mata da ke wanke wanke. Zaune take aka kujera ‘yar tsugunno ta kunna wannan tabar ta fara zuka a hankali. Sai ta karkato da jikinta gaba daya tana kallon Rukky ta ce da ita

” Yarinya ki bar zuke zuken nan..kar ki je ki haukata kan ki a banza a wofi!”6

A hankali Rukky ta taso daga kwanciyar da take ta kurawa mata ido da lumsassun idanunta. Kallo ne take mata na ‘ke me kike yi’. Kandala tayi murmushi ta ce

STORY CONTINUES BELOW
” Kin ga waccan mahaukaciyar tabargazuzu ta bakin rawul din can? Billahillazi a gabana ta zo garin nan shekarun baya. Babu irin tashen da bata yi ba. Idan kika ga yadda maza ke rububinta za ki sha mamaki! Har ‘yan bani na iya kan ce wai ta dalilinta ne wani gwamnan lokacin ya shimfida mana wannan titin da ya shigo unguwarmu.1

Ita ma ta kafa wannan bushe bushen da shan kwaya..to kin dai ga karshenta nan. Tun tana haukarta a cikin gida har ta fara yawo.Ni abunda ya sa kenen daga taba ban dara ba, ita ma dan ta zame min jiki ne”1

Rukky tayi wani murmushin takaici ta ce

” To ita taba kin san illar da take yi? Dagargaza huhu take. Ba ki ga ko jikin kwalin ba..masu yin ta ma sun aibatata da cewar mashayanta za ta iya kawo musu mutuwa a kananan shekaru. Taba ita ma ai balai ce!”4

Maimakon Kandala ta kula ta sai ma ta cigaba da zukar tabarta tana fitarwa ta hanci ta baki. Suka yi shiru na dan mintuna har suka daina jin kwaramniyar masu wanke kwanuka. Su ma sun gama kandala ta sallame su. Ya rage daga ita sai Rukky a wannan waje.

Ta murje tabar a kasa ta kurawa Rukky ido ta ce

” Ke ‘yar wani gari ce?”

Rukky tay caraf ta ce
” Ni asalina ‘yar kazaure ce..acan jihar jigawa babana dan wani kauye ne mai suna karkarna. Bahaushiya ce ta usul!”

Kandala ta buga tsaki ta yi mata kallon uku saura kwata ta nuna ta da danyatsa ta ce

” Ke yarinya kallo daya na miki na san ke jinin zabarmawa ce! Ba ki wuce maradi ba ki wuce zinder da kewaye! Ni kuwa kin ganni nan uban da ya haifi uwata ma cikakken dan damagaram ne!”7

Rukky bata kula ba ,kandala ta gyara zamanta ta ce

” kin ganni nan bana shekarata 30 cif a bariki! Ba wani abu ya fito dani ba sai sanadin fyade. Na taso ina marainiyata a hannun wata gwaggo na to mijinta shi ya fara lalatani!1

Tun da uwata ta kawo ni duniya ban taba ganin azzalumi irin Alhaji Isa ba. Ina kankanuwata ban fi shekara goma sha biyar ba ya fara min fyade a cikin gidansa! Ga shi lokacin akwai karancin shekaru da karancin wayewa a lamarina. Sai ya shigo da zarmemiyar wuka ya ce idan na fadi ma gwaggo na sai ya yanka ni!1

A lokacin babu wani abu da nake tsoro sama da shi haka kuruciya ta sa na ja bakina nayi gum, amma kamar an tarwatsa zuciyata. Dana gaji ranar na samu gwaggo na na gaya mata ko da zata cece ni daga wannan rayuwar kin san me ta ce?”

Rukky ta girgiza kai tana tuno abubuwa da dama. Idanunta suka fara hasko mata Ali. Kandala ta ce

” Sai cewa tayi ina yi wa mijinta sharri. Ta kafa duka na da kyar makota suka cece ni. Ba irin tsinuwar da bata mun ba a ranar. Har da ce da ni butulu na zama kaza ci ko goge bakin ki.6

Ba a fi kwana biyu ba ta kuwa kama shi da idonta yana kokarin haike min. Amma kin san saboda tsabar son zuciya sai kira na tayi daki ta ce wai nayi shiru kar na fadawa kowa saboda Alhaji Isa babban mutum ne. Idan na tona mishi asiri kamar na tonawa kai na ne saboda uban ‘ya’yanta ne. Amma za ta dauke ni ta kai ni aikatau birni.1

Da kin san tarkon da fyade ke jefa zuciyar wanda aka yiwa to da ba kiyi fatan ya faru ko da ga makiyinki ba Rukky. A irin wannan bakin cikin na fara rayawa rai na na kashe Alhaji Isa! Barin irinsa a doron kasa ai ba karamin fitina ba ne!1

Kandala ta daga kai tana kallon sararin samaniya na wasu ‘yan daqiqu sannan ta mayar da idonta kasa ta ce

” Ina ma za a ji labarina iyaye su hankalta! Ina ma za a ji labarina a ke bi wa ‘ya’ya hakki! An jefa rayuwata a cikin haula saboda maraicina, tun daga lokacin na kudurta a raina sai na gurgunta rayuwar duk wanda ya kusance ni.8

STORY CONTINUES BELOW
Tun da ta kai ni aikatau ba ta kara bi ta kai na ba ni kuma ba marmari nake ta ce na zo na koma gida ba. Na riga na kudurta ni da gidanta har abada! Don haka daga gidan aikatau gaba kawai na kara ina ‘yar kankanuwata na tsinci kai na a karuwanci!3

Ba so nayi ba , ba kuma so nayi na balbalce ba amma rayuwa ta fi karfina ba ni da yanda zan yi ba ni kuma da inda zan je.2

Kin ganni nan?A yanzu na fi shekara guda cur dauke da cutar kanjamau! Amma fa shan maganina nake akai akai ba tare da kowa ya sani ba. Kuma har yau ban fasa tu’ammali da maza ba. Yanda na kwasa kowa ma ya kwasa! Ai kowa ya kwana lafiya shi ya so dan uwatar!”17

Rukky ta kurawa Kandala ido ta rasa matakin da zata dora ta a zuciyarta. Maganar fyaden nan ta tsaya mata a rai.

Fyade…ina ma wadanda aka yiwa fyade na da murya…ina ma..ina ma…..7

*********************************

Irin soyayyar da ake bugawa tsakanin Idi Maina da Luba dan kallo sai ya rike baki. Luba ta makalkale shi ta yi masa dabaibayi a cikin salo, hilata da yaudara irin tata. Har ya zamana bai iya zuwa koina sai ya ratayo luba a jikin sa ta masa rakiya. Sosai shedan ya shiga al’amarin nasu yayi rawa yayi juyi har ya zamana ba sa komai sai diban albarka.5

Idi maina mai samu ne don kuwa duniya na yayinsa a lokacin akwai yan kwabbai a aljihunsa. Sai da Luba ta tabbatar tana tatuke shi fiye da zatonsa. Shi kuma ya makance a a jarabar karuwa ya watsar da matansa na gida. Da yake duk abun bautar shedan ne sai suka gamtse suka zama tif da taya.3

Har ‘yar Moduwaye kan ce

” Ki tatuke shi ki masa kat! Ai duk wanda yace bariki zai..ai ba uwarsa ta turo shi ba!..kar ki tausaya masa ko na miskala zarratin! Kowa ya ci dubu ai sai ceto! Kowa ya tuba don wuya ba lada! A dade ana yi sai uban da ya sa kan sa..tun da yace zai hadiyi gatari to sai a sakar ma sa kota! Duk shegen da ya fasa baya kaunar uwatar!”8

Wannan nema na su da Idi ya sa Luba ta kara wayewa don Ya san ta kan duniya. Kacokam ma sai ya dauke ta ya kai ta Abuja suke sheke ayarsu. Yawa yawan lokuta sai ya kashe wayarsa kar matansa su dame shi da kira. Yayi nisa kadangarun bariki sun daura masa laya.4

A abuja irin mahaukatan kudin da yake kashewa Luba ba a magana. Ba su joint joint ba su club club.Daga baya ma har ya dalle ta da mota sabuwa fil ‘yar yayi. Ranar da suka dawo ta taho da motarta gidan Hajiya Kubuwa su yar modu aka siyo lemon fanta aka fara mata wanka suna shewa! Cewa yake4

” Da kyau Luba shegiyar wutsiya..kowa ya hango ki ya taya to dama uwarsa ta ce da shi je ka ka gani..tsinanne ne! Ahayye…yau ina ganin abun da ya ishe ni..abun zama ya mutu ya bar zani!”10

A ranar wata alhamis Idi Maina ya dauki Luba a mota suna yawan ta zubar. Yau ma wani wajen cin abinci suka je suka cika tumbinsu. Suna kan hanyar dawowa ta ce ya biya da ita wani shagon sayar da kayan kwalliya sun dauki hanyar kenen sai wayar shi tayi kara.

Bai cika son ansa kiran waya ba idan yana tare da Luba musamman ma da ya san ba zai wuce matansa ba. Don haka sai yayi kamar ya share sai kuma ya duba sunan. Cikin sauri ya rage karan sautin redio da ke tashin wata wakar p square ya dubi Luba ya gaya ma ta ogansa ne ke kira.

A hankali ya daga wayar da
” Hello Sir”

Ba ta ji mai ake cewa ba ta dai gane kamar fada ake masa. Bayan ya ajiye wayar ne ya kalleta rai a bace ya ce

” Oga na ne yake nemana a ofis yanzu yanzu..kuma ya zama dole na ansa kiransa na gaggawa. Don gaskiya shi in dai akan aiki ne ba ya wasa”

Luba ta tabe baki irin na shagwababbun ‘ya’yan tabara ta ce2

STORY CONTINUES BELOW
” To baby ni yanzu ya zaka yi da ni..ka san fa gobe ina da bikin kawata hannatu kuma da kayan zan yi amfani..gaskiya ni..gaskiya..” Sai ta fara buge buge da kafafunta2

Ya dan fara rikicewa..a rayuwarsa ya tsani fushin Luba. Yana kaunar yarinyar kamar ba gobe. Ransa ya fara raya masa abubuwa dayawa game da ita. Shin ko dai ya aureta ne ya ajiyeta a Abuja? Idan ya so ragowar karabitin matansa ya bar su acan garin da suke sai yake leka su loto loto.2

Da irin wannan tunanin ya shafa fuskarta a hankali ya ce

” Haba gimbiyata, kin san fa in ba don dole ba ba zan je kiran nan ba. To amma maganar aiki ce ogana kuma baya wasa da aiki. Ni fa so nake ki zamo tawa ni kadai! Ki kwantar da hankalinki i’m all urs”

Cikin shagwaba ta fara cewa
” To yanzu yaya za a yi..sai dai mu je na raka ka daga nan sai mu wuce”

Ba zai iya musu ba ya ce mata to..suka wuce ma’aikatarsu. Da suka isa yayi pakin ya ce ta jira zai je ya dawo ta ce zata bi shi . Suka fito gabadaya.

Ba dai hakan ya so ba amma ba yadda ya iya. Tunanin ogansa yake ko yau kuma da wacce ya zo ya ga sai zazzaga masa masifa yake. Sa’annan baya so ya shiga da Luba ofis din sa amma ya san ba zata amince ba.

Ya san ogan nasu dan hannu ne don ko da can ya san wani kawali da ke kawo masa mata jefi jefi. Bai tsumduma a harkar ba amma dai ya san yana tabawa.

Ba ma wannan ba shekarun baya wanene ya kai ogansu tashe a La mirage? Hadadden wajen cacan nan da yayi karin suna. A dan shekarun nan ne ma ya ga ya bace bat! Baya ganinsa kwata kwata ko me ya sa? Oho

Yanzu da suka doshi ofis din da Luba sai ya ji zuciyarsa ta cika da waswasi. Ba wai don zubewar mutuncinsa ba sai don kar fa ogan nasa ya gani ya kyasa. Ko da yake shi fa ogansa mai taste ne mai dan banzan ra’ayi. Sai a kawo masa mata 10 ya ce ba su masa ba..ba lallai ma Luba ta birge shi ba. Da wannan tunanin suka doshi ofis din.2

Tun da Luba ta shiga katafaren ma’aikatar jikinta yayi sanyi. Dama anan Idi Maina ke aiki lallai ashe arzikinsa ya kai haka? Ashe ma bata tatsi komai ba! Da sauranta dole ne ta san yadda za tayi ta raba shi da komai. Daga karshe ta kora dan banza! Amfaninsa ya kare.6

Sakatariya ce tai musu iso suka shiga. A jikin kofar ta ga an rubuta ” The Chairman, A. I. T”. Shigar Luba wannan Ofis sai ta ji kamar ta suma. Tun da take shige shigenta ofisoshi yawon ta zubar bata taba shiga wanda ya kai wannan haduwa ba. Komai na cikinsa ruwan toka ne. A wani bala’in sanyi da ke busawa ka ji ka kamar ba a kasar ka ke ba. Lallai wannan ogan ba karamin tsoho ba ne da ya tara kudi tsababa!

Idi Maina yayi mata mazauni a wasu kujeru da ke ofis din shi kuma ya karasa tebur din gaba suka fara tattauna abunda ya shafe su.

Ogan ta ji yana cewa

” You have to be careful, very careful”

Dago kan da Luba za tayi idonsu yayi caraf ya hade. Wani irin shock ne ya ziyarce ta wanda saura kiris ta fadi daga zaune. Ya dauke idonsa suka ci gaba da maganarsu ita kuma ta zuba masa na mujiya.1

Menene haka? A zatonta zata ga tsoho tukuf kawai sai ta ga matashi mai jini a jika da ba zai haura shekara 35 ba!. Baki ne daga gani dogo ne ya ajiye wani gemu da ake wa laqabi da na kwata miliyan a fuskarsa.5

Yana sanye da wata bakar kot da takalmansa sau ciki kallo daya za kai mu su ya fallasa tsadarsu. Jikinsa ya nuna alamar hutu da jin dadi..kai daga ganinsa young miloniya ne!

Kan ta ta ji yana juyawa da ta kare masa kallo da wassafa tunaninsa. Tun da take a duniya take haduwa da maza kala kala bata taba ganin wanda ya kai haduwar ogan idi maina ba! Komansa sha’awa yake ba ta, ta rikice ta dimauce a cikin wani TARKO! Tarko irin na so!9

Ashe dama haka so yake? Ashe da mutane suke cewa “so” ashe da gaske su ke? Ashe akwai shi? Haka yake dama? A yau ta tabbatar so gaskiya ne domin ya dana mata tarko kuma ta kamu har iya wuya!5

Tun da take shanawarta bata taba tunanin yin aure ba. To amma yau da idonta ta ga miji. Ta ga miji na nunawa sa’a. Ko ana ha maza ha mata sai ta mallake shi. Sai ya so ta kamar yanda take son sa. A yau ta ga abun so abun kauna! A dalilin son wannan gayen da son aurensa har suka bar wannan ofis da tunani daya ranta!9

” Zan mallake ka, ko da abunda na mallaka a duniya zai kare! Ko da duk mutanen duniya suna so ko da basa so!”4

Ko bayan sun fita daga ofis din ,Luba na waiwayensa a sace da tunanin zata masa zuwan bazata. Daga nan ta yi masa kamun kazar kuku.

Shi kuma ya cigaba da aiyukansa dama gwanin aiki ne. Wayarsa tayi kara ya daga da sauri ganin mai kiran. Wani private detective din sa ne. Ya ce

” Yaya ake ciki? Any progress?”2

Daga jin amsar da ya bashi ba ta masa dadi ba ya ce

” Har yanzu? Ba wani information? Idan nan da sati biyu ban ji wata cikakkiyar magana ba mai amfani i’ll fire u!”

Kit ya kashe wayar yana huci dama zafin rai ne da shi. Wani irin damuwa ya ji tana taso ma sa ,ran sa ya gama baci. Tunani ya masa yawa ya zai yi da ransa ne? Yana jin kan sa a matsayin wani wanda ya gaza! A rayuwa ya tsani ya gaza, gazawa ai ta raggon maza ce! Shi juwa ai jajirtacce ne!

Wasu irin maganganu ne suka cigaba da kuwwa a kunnuwan ALMUSTAPHA ILIYASOU TILLABERI…36

An damra………Mustapha ……..an damra amrena da Rokaiyatou!9

Daga nan ya ji dif! Komai ya tsaya cak!!!

A hankali ya ce

“Ina ki ke?… Ina ki ke???????”

Almustapha gwani….makwafin gwani!2

( ina so mai karatu ya gane cewa momodou na cikin labarin rokaiyatou ya mutu! Wanda ya mutu kuma, baya dawowa. Almustapha danuwan Momodou ne, babansu daya. Ku duba babi na 6 don karin bayani. Kalamai da ake amfani da su mararsa kyau a labarin an yi haka ne dan nuna ainihin yadda alamarin yake, ba don a habbaka su ba. Ayi hakuri da hakan)

Kano, Nigeria

Sau dayawa a rayuwar dan adam mutane kan aikata laifuffuka da suke gani ba a bakin komai ba. Zamani ya zo mana da wasu halaye da suka zama ruwan dare. Zinace zinace, shaye shaye, tsubbu da sauransu.

Ka dauka cewa a rayuwarka kai matafiyi ne duk tsawon tafiyarka akwai inda zaka kare. Za kuma a tambayeka abubuwan da ka aikata a hanyarka ta zuwa wannan guri. Wani tanadi ka yi? Ka tabbata lokacin da aka nuna maka tafiyarka cikin majigi za kayi alfahari da kan ka?4

Ga duk wanda bai san Almustapha Iliyasou Tillaberi ba to a anan ya gama cutarsa. Yana da fuskar kamala da za kayi zaton mutum ne mai tsantseni wajan aikata zunubi. To sai dai me? Sau dayawa mutane na sanyawa jikinsu wata riga mai badda kama. Akuya da fatar kura!1

Da ne ga Hajiya Hadiza da iliyasou Tillaberi. Ya taso cikin gata da tsananin soyayyar uwa da take ganinsa da daya tilo.

Almustapha da Momodou ‘yanuwan juna ne kuma aminan juna. Sun yi zumunci ba tare da iyayensu sun damu da suyi hakan ba. Momodou ba shi da wani abokin shawara sai Almustapha musamman akan soyayyar shi da Rokaiyatou. Almustapha ya ba shi goyon baya dari bisa dari abinda ya rasa a duk cikin yanuwansa.

Almustapha yayi wa Rokaiyatou ne sani tun tana zanin goyo don haka har yau ba zai iya tantance ta ba a cikin mutane. Momodou ya sha masa mitar ya zo su gana abinda ya sa ya ce zai zo Niamey kenen. Zuwan da aiki ya rike shi suka yi da momodou zai taho shi kuma momodou din ya wuce Tillaberi a daura musu aure sai su hadu a Niamey. Daga nan zasu taho da shi, momodou, Rokaiyatou da Momma. Yana taya danuwansa murna yana taya sa samun abinda yake so. Sai a lokacin shi ma ya fara tunanin aure.

Momodou da Almustapha sun riga sun gane halin mahaifinsu sun kuma rantse ba za su goya masa baya ba. Suka yi ajandar cewa amarya da angon zasu karasa shiri a Nigeria su wuce nairobi inda momodou ya samu aiki. Shi kuma Almustapha ya cigaba da kula da harkokin biznes din su da zasu bude babbar hedkwata a kano.

A wannan shirin na shi na zuwa Niamey ne ya ji wayarsa tayi kara. Yana duba ya ga momodou ne dariya ta subuce masa ya san ba zai wuce zancen aure ba, inshallahu su ke da nasara. Daga jin alama Momodou din akan hanya yake don yana jin karar iskar mota. Ya ce

” Hello..Frere”

Network ke yanke maganar sai ya ji baya jin sa. Ya kara cewa

” Heloooo…”

Muryar momodou kawai ya ji yana cewa

” An damra..Mustapha an damra…. amrena da Rokaiyatou” sai ya ji wayar ta dauke.5

Dariya ya kama yi, ya ji abunda yace sai yake ta kara kokarin kira. Wayar ta ki shiga. Sai ya hakura ya fara shirye shiryen wucewarsa Niamey. Ya san dole ya je don wannan fadan da suka tarko da mahaifinsu ba mai karewa ba ne. Shi dai yana bayan danuwansa ko ana ha maza ha mata bai ga dalilin da zai sa a hana masa abunda yake so ba!

Abu daya ne ya sa bai je da wuri ba, daga Abuja ya hau jirgi za shi Niamey sai yayi missing flight. Har a lokacin yana gwada nambar momodou bai samu ba. Sai ya fara wani tunani kar ya tafi niamey shi kuma momodou da Rokaiyatou sun taho nigeria a samu sabani. Sai yayi tunanin bari ya kwana in ya so washegari sai suyi waya su tsara yadda abun zai kasance. Ya riga ya kira wani abokinsa a immigration ofgice da zai yiwa Rokaiyatou fasfo a kwana 2 daga nan sai ya shigar musu da biza. Da wannan ya kwana a rai.

STORY CONTINUES BELOW

A wannan daren ne gabanni asubahi mahaifinsa ya kira shi yana rusa wani irin kuka. Ya ba shi labarin da ya girgiza duniyarsa wai momodou ya samu hadari a hanyar dawowarsa daga tillaberi, Allah ya masa rasuwa. Jirgin farko ya bi zuwa niamey cikin tashin hankali. Ya kira mahaifiyarsa hajiya hadiza da cewar su hadu a can.

Irin rudanin da wadannan iyali suka shiga ba cewa komai. Duk irin rashin jituwar mutapha da hajiya khulsumou kawai sai ya rukunkumeta yana kuka. Mutuwar ta dake shi ba da wasa ba. Sai yake ji a zuciyarsa ya kullaci mahaifinsu a ganinsa da ya bar Rokaiyatou da momodou sun yi aure tun farko to da hakan bata faru ba.

Sai a lokacin yake jin wani labarin kanzon kurege. Wai mahaifinsu na zargin wannan yarinya da uwarta da kashe momodou. Wai har ma an so kashe su an kona musu gida an kore su. Yanzu haka ba a san ma inda suka yi ba.

Wani irin kallon tashin hankaki Al mustapha ke wa uban. Ya kan kasa gane me mahaifinsu ya mayar da duniya. Ai alkawarin Allah baya tashi, duk yanda yaki auren ai sai da aka daura. Sai yakan tuna maganganun momodou1

” kamnata amanarmu ce ni da kai.. marainiyar Allah marar gata..ba ta da wanda ya hi mu duk duniya.!”

Ya yarda ya amince har ya ji yana kaunarta kauna ta zumunci. Zai nemo ta zai kuma inganta mata rayuwa kamar yadda momodou ya so. Zai yi hakan ko mahifinsu yana so ko baya so. Ya san nemanta ba zai masa wuya ba watakila ba za su wuce can niamey ba, watakila sun samu wani gida sun boye..watakila..watakila…Neman da ya shayar da Almustapha mamaki.5

Mahaifiyarsa Hajiya Hadiza wata irin mutum ce da ba abunda ta sa a gaba sai duniya. Ita in dai tana cikin daula to bata damu ba da kowa ba sai dan ta tilo. To yanzu da yake ma shi kadai ya rage momodou Allah ya masa rasuwa to ai danta yanzu shi zai zama akan komai. Momma kawarta ce tun ta yarinta amma bata damu da ta bincika akanta ba. Ita dai tun da duniya ta samu shikenen. Ko da Almustapha ya nuna mata nemo su sai ta nuna ba ruwanta ta kuma yi masa gargadi da kar ya sake ya shata layin gaba da ubansa don abun ba zai masa kyau ba.

Duk cikin halayensa ya san shi ba azzalumi ba ne shi din kuma mai tausayi ne. Sai yake jin wani nauyi a ransa da bai sauke ba muddin bai nemo yarinyar nan ya sa ma mata ‘yanci ba. Neman da ya wuce tunaninsa saboda ko hotonta ba shi da shi. Sai wani hoton momma da ita tana jaririya da ya samu a binciken da yayi a dakin mahaifiyarsa.

Bayan mutuwar momodou ne mahaifiyarsa tayi masa auren hadi da wata yar kawarta, auren gata. Auren da bai dade ba ya kare saboda wani mugun hali na Almustapha..CACA. Daga baya duk yanda aka so ya ki kara aure ya tsunduma harkar bariki.

Shekarun da suka gabata sun zo da canje canje dayawa mafi yawansu ta habbakar I and A group of companies. Hakan na da nasaba da Almustapha da ya jefa dukkanin rayuwarsa akan tabbatar da hakan. Mahaifinsu tun lokacin da mutuwar momodou ta dake shi sai abun ya zame masa kamar ciwo yau da lafiya gobe babu. Sai ya zaman komai yana hannun Almustapha.1

Komai ya bunkasa fiye da zaton mai karatu. A karancin shekarunsa ya zama babban mutum mai madafan iko. Ba shi da wani abu da yasa a gaba sai I and A group of companies.

Daga baya ne ya fara hiring detectives da za su cigito masa Rokaiyatou da Momma sai ya bada hoton Momma a matsayin shaida. Yayi yayi da mahifiyarsa ta nuna masa asalin gidansu momma watakila ko zai samu labarinsu amma ta ki. Tsoronta daya mahaifinsa ya ji tana da hannu a almarain yayi watsi da ita. Taurin kai irin na Almustapha ya ki saduda. Yakan ce3

” Sai na nemo ta, sai na inganta mata rayuwa. Zan yi abunda danuwana zai yi farin ciki, zan cika masa buri!”

Abinda Al mustapha bai sani ba shi ne, wasu abubuwan suka faru ne a kurarren lokaci. Wasu abubuwan mafarkai ne. Lokaci sakarai ne..yakan tafi da burirrika…yakan tafi da imani!3

STORY CONTINUES BELOW

*********************************

La mirage wani waje na da Al mustapha ya mayar da shi wajen nishadi. Ba wai don ya dauki hakan a matsayin wani babban laifi ba sai a matsayin wata hanyar nishadi. Sukan nemi matansu suyi wasan karta na caca a gurin kuma bai dauki hakan a bakin komai ba.4

Ba ma’abocin shaye shayen wiwi da sauran kayan maye ba ne ya kan dauki masu yin hakan wawaye. Idan ya fara shaye shaye ya je ya haukace a banza wa zai kular masa da dunkiya? Ai shaye shaye na marar dubara ne wanda bai ajiye ba bai ba wani ajiya ba kuma ba shi da wata madogara a gaba.1

Amma idan yayi nishadi suna cacarsu a la mirage akan kawo musu kofunan whisky suna zuka a hankali. Ya kan sha kofi daya ya wadace shi ya tunda dai ba shiga halin maye ba a ganinsa hakan ba laifi ba ne.4

To wataran daga nan ne zasu kwashi yanmatansu da suka yi daidai da raayinsu. Almustapha ba wai mayen mata ba ne amma zama cikin abokanai masu irin halin ( dan Allah mu kiyayi abokai da kawaye bata gari) ya sanya suka fara nuna masa a bin mata ba komai ba ne. Kamar wani abu ne ma da zai yiwa rayuwarsa ado da shi. Tun da ga shi mai kudi mai madafan iko ai kowacce mace ya ga dama zai zara.2

Da irin wadannan hudubobin ya zama yana neman mata jefi jefi. A cikin matan ma dan ra’ayi ne sai wacce ya ga ta masa ga zabin masifa. Tun da yayi aure suka rabu da matar ya mayar da gidansa inda yake shigo da mata. Iyayensa sun san wasu abubuwan da yake yi amma sun kasa daukar mataki akai. Son sa da kaunarsa ya rufe musu ido daga baya ma sai Hajiya Hadiza ta fara shiga malamai na cewar makiya sun yi masa asiri ya ki aure ya balbace. Ya zama bata ga gidan boka bata ga gidan malam.1

Jin dadin duniya wani abu ne da Almustapha ya ganewa saboda bai rasa komai na rayuwar duniya ba. Ya girma ya gawurta a karancin shekaru irin na sa ya na zama da manyan da suka isa su juya duniya. Tun yana tunanin ya kara aure har abun ma ya fice a ransa tun da kadangarun bariki suka daura masa laya. Aure takura ne a wajensa yakan hana bawa ya wataya ya ji dadin duniya.5

Iyayensa sun yi sun yi akan ya kara aure amma abun ya gagara. Yanzu mahaifinsa ba shi da wani karfin jiki da mulki komai Almustapha ke juyawa idan ya tasamma masa zai masa fada sai ya nuna zai ajiye komai na kamfani ya nemi na yi. Abunda ke tayarwa mahaifin hankali kenen, baya so a ce guminsa na shekara da shekaru ya tashi a banza.

Akwai wani abu da Almustapha ke ji a ransa game da ubansa da ya kasa yafewa. Gani yake shi ne silar rasa momodou kuma ba zai taba yafe ma sa ba. Yakan kalli mahaifinsa a matsayin azzalumi mai danniya. Anya ba shi yayi sanadin mutuwar Ahmadou Tillaberi ba? Almustapha ne kadai ya san iya adadin dukiyar Ahmadou Tillaberi da mahaifinsa ya hade da tasa. Sai mahaifinsa kan ba shi tsoro, ina za shi da hakki. Irin wadannan tunani kan sa ya ji yana neman wannan yarinya ko banza a mallaka mata dukiyarta.2

A halin da ake ciki ya hadu da manyan kasa sun kafa wata jamiyya ta siyasa ta DSP. Ba takara yake so ba ba kuma mulki yake shaawa ba. Sai dai a rayuwarsa shi capitalist ne. Duk wani abu da zai kawo habakar dukiyarsa to ya san ta. Ya gane cewa gama kai da manyan gari manyan kasa shi zai dada karo bunkasarsa da kuma kanfanunukan sa.2

Haka rayuwar take, ka daga ni na daga ka. Hakan ba karamin taimaka masa yayi ba wajen shige da fice da kayan masarufi na kamfaninsa. Ana wannan halin ne suka tsayar da dan takarar gwamna. A kuma lokacin ya tafka wani kuskure da ya zame ma sa abun bibiya.2

*********************************

Zaune yake a ofishinsa a wata ranar litinin aiyuka sun cabe masa. Suna da kaddamar da wani kamfanin man gyada da karfe biyu na rana ga shi har karfe daya ta gota amma yana zaune a ofis.

Ya tuno abunda ya faru yau da safe da ya biya wajen mahaifiyarsa har ya sa shi ya dan makara.

Tana zaune a wani tangamemen falo mai dauke da kayan alatu sanyin ac yana buso ta.

STORY CONTINUES BELOW

A hannunta remot ne tana caza tasho shi a tv ya gaisheta ta dube ta ce

” ka ga text dina jiya da daddare, ba ka ji ina maka neman gaggawa ba? Tun da yanzu idan an kira ba a isa ka dauka ba”

Sai ya iso har inda take ya kama kafafunta ya rukunkume ya ce

” Mummy kenen ai na san zancen guda daya ne shi yasa na ki zuwa. Wai kin gaji da ganina hakan ne da kike so na kara jajibowa kaina wani auren?”

Ta shafa kan sa tana kallonsa cikin kauna irin ta uwa. Tana so ta gaya masa abubuwa dayawa da zai gyara a rayuwarsa amma sai ta ji kamar ta kasa. Yaron yana mata kwarjini sannan bata so yayi fushi ( karshen duniya baiwa ta haifi uwargijiyarta).kuma ma ai da kuruciya a jikinsa wataran zai daina. Maimakon ta yi masa fada kan kwashe kwashen yanmatan da yake yana kaiwa gidansa sai cewa tayi5

” Ni na fi so ka nutsu waje guda kayi aurenka ai ya fi mutunci. Ba ka so na ga ‘yan jikokina?”

Dariya yayi. Ya saba da irin zancenta. Ya ce

” To ai matsalar yanzu za ki ce sai zabinki. Ba haka aka yi da Fadila ba abun ya zo bai yi dadi ba”

Tayi sauri ta ce

” Aa, wannan karin dai ka zabo wacce tayi maka. Amma kar ka manta ka zabo yar babban gida yanda ka ke dan babban gida. Ka san ni mutum ce mai shiga kawaye bana son abunda zai jawo min raini ko a ga gazawata”6

Kallonta kawai yake. Zancen dai kenen. Ita dai ta shiga ko’ina ta kece raini. Da haka ya amsa da to kawai ya shigar da zancen da ke ransa don ya ga yau tana nishadi. Ya ce

” To ya maganarmu? Yanzu mummy ya kamata a ce a neman nan na kawarki da diyarta ki kasa sa hannu?”

Nan da nan ta gintse fuska. Ta nuna masa danyatsa ta ce

” wai mustapha wannan zancen bai kare ba? An gaya maka su suna so a gan su ne? Da suna so ai da kan su zadu bayyanar da kan su. Ka ga alamun rashin gaskiya kenen.A irin wannan turbar danuwanka ya rasa ransa shi ne kake nema ka salwantar mun da kan ka?”

Tsayawa kawai yayi yana kallonta. Idan da sabo ya saba da halinta na ko in kula in dai ba akan hamshakan kawayenta ba ne. Yanzu duniya ta koma sai da mai shi ake yi. Ya san idan ya tsaya ma bata lokacinsa zai yi.

Ya mike yana gyara kot din sa ya rasa me ke damun iyayensa. Ya ce

” To Allah ya bayyanar da su”

Cikin kosawa ta ce

” Amin”

Ya mike yayi mata sallama. Har ya zo bakin kofa ta ce

” kun yi magana da mahaifinka kuwa? Daga zuwansa Niamey jikinsa ya motsa ba zai samu damar dawowa yau ba. To Allah na tuba zama da wannan matar tasa ma kadai ai ya isa ya tayar masa da hawan jini. Khulsumou..khulsomou ai matsala ce”3

Wani abu ne yazo ya tokare masa a makogoro. Dama duk zancen da take masa dazu babansa ba shi da lafiya ta kasa gaya masa.Ya share korafinta akan Hajiya Khulsomou yayi sauri ya fara laluben wayarsa yana cewa

” Bari na kira na ji..idan jikin ya matsanta kawai Indiya zamu koma. Na kasa gane wannan wani irin ciwo ne”

Da haka ya fita bayan ya kira baban yace masa da sauki a satin ma zai shigo kano. A haka ya zo ofis aiki ya sha masa kai. Ya katse aikin suka tafi wajen kaddamar da kamfaninsu na man gyada. Ko lokacin da ya gama aikin ranar ya gaji likis. Wani sashe na ran sa ya ce ya wuce la mirage ya barje gajiyarsa ta yau.

Da misalin karfe 10 ne na dare harabar gurin a cike take da mutane manya da kanana. Tebur din su Almustapha na sashen Vip suna zaune da shi da waau abokansa 4 suna tattauna al’amuran siyasa.

A kan teburin akwai kwalayen taba da wasu gajerun kwalabe na giya masu tsada. Da tambulan a hanunsa yana kurbar abinda ke ciki a hankali.

Tun daga nesa ta kura masa ido ta fi sati daya tana bibiyarsa. Komai yayi sha’awa yake bata ta rasa wani irin abu take ji game da shi. A hankali ta taka har teburin da suke.

Sanye take da wata riga irin gown dina mai masifar tsada fara kal. Ta kwanto gashinta da ta yiwa kari zuwa kafadunta. Babu abunda take yi sai kamshin turare. Kowa a gurin ita yake bi da kallo saboda kyaun da tayi. Ta zauna a wata kujera kusa da shi ta rangwada kai ta ce

” Ranka shi dade…kar ka ce dani baka gane ni ba”

Kallo ya kare mata a hankali so yake ya tuna inda ya san fuskar. Ya ce

” A mafarkai kike zuwa ko?”

” Mafarkan ido biyu ko?” Tace da shi

Ya bude ido alamar mamaki ya ce

“Su kuma wadanne ne hakan?”

” Irin mafarkan nan da mutum ba zai so ya farka ba” ta bashi amsa

Kallonta kawai yake akwai wani abu na kyaunta da ke fizgarsa, ya rasa menene.1

Ta dauki kofin da ke gabansa ta kurbi abunda yake ciki ta kalle shi cikin idonsa ta ce

” Ana ahabak ktheer…ktheer habiibi”2

(Ina son ka sosai da sosai masoyina)

Kun ji haduwar da ta zama silar bankadar sirri. Sirrikan Almustapha.6

Wasu sirrikan ba su boyuwa wasu sirrikan bibiya suke yi, su yi naso suyi rassa su tarwatsa mamallakinsu! Irin hakan ce ta faru ga Almustapha Iliyasou Tillaberi!!

About AIS

Check Also

MAI TAFIYA CHAPTER 5

MAI TAFIYA CHAPTER 5                  Www.bankinhausanovels.com.ng  Son kasancewarmu …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *