MAI TAFIYA CHAPTER 1

MAI TAFIYA CHAPTER 1

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Kudi kumbar susa, idan ba ka da su sai ya zamto ba ka da murya, ko ka yi magana ba za a ji ba!21

Kano, Nigeria

Wai me ya sa mutane ba sa son talaka ne? Har bahaushe ma kan ce wai “talaka ba aboki ba, ko kun shirya ranar biki kwa bata” Irin tunane tunanen da Hindatu ke yi kenen a wata safiyar Laraba. Ta san an ce wai Laraba ranar sa’a ce, to amma sai ta yi wa wannan Larabar taken ranar bakin ciki, ranar ban haushi.3

Matsalarta a yanzu bata wuce biyu ba;ta tashi ba ta maganin komai sai naira hamsin! kuma ta wayi gari jinjirinta wanda yayi kwana 40 a duniya yana fama da zazzabi da mura, ciwon da ya kamata ta kai shi asibiti. ‘Ya’yanta biyu Abba da Asiya su suka tsira mata ido suna ma ta kallon gasasshen balangu don yunwar da ke azalzalarsu.

Abba dan shekara shida shi ne mai wayo cikinsu ya ce11

“Mama, in yi gudu in je in siyo kosan”?

ta yi sauri ta kawar da idon ta daga kan sa, tausayi yake ba ta. Hamsin din dai ita ta ci wa buri tayi kudin mota ta kai jinjirinta asibitin Murtala tunda ba a biyan kudin kati, idan ya so in aka rubuta magani ta karba a wajen Danladi mai kemis na unguwarsu baga baya ta biya shi a hankali. To amma ya za ayi ta bar yara da yunwa?3

Da wannan tunanin da zaro kudin ta ba shi ta ce “yi maza ka je wajen karama ka siyo kosan ashirin ka ce ma ta in ji ni..kar fa ka tsaya wasa” ya fice a guje kafin ta karasa. Ya dawo ya bata canjin suka hau kan dan tsurut din kosan suka cinye har da lashe lashen takarda. Ba ta bi ta kan su ba ta saba jinjirinta a baya agogon bango ya nuna karfe takwas na safe cif.9

Ta dauki jinjirin da ta sawa suna muhammadu ba don ta yanka ma sa ragon suna ba ta saba a baya,jikinsa zafi rau! ta tarkato ragowar yaran suka yiwo waje. Ta rufo kofar gami da saqalo ta da wani kara ba don tsoron kar barawo ya shiga ya ma ta sata ba sai don cika ala’da. Ta zunkuda goyon bayanta da ke mutsu mutsu ta ce da Abba ta na nuna makotansu3

” ku shiga gidan malam wajen Iyami ku ce nace ku zauna a wurinta zan je asibiti na dawo” ba ta bar gurin ba sai da ta ga shigar su.

Ta fara kissawa ranta irin tazarar da ke tsakanin unguwarsu hausawa da asibitin Murtala, sai ta yanke wata shawara. Za ta sabi tafiyar kafa zuwa dangi daga nan ta roki dan acaba ya dauketa zuwa asibiti a naira talatin, a dawowa kuma ta biya gidan mahaifiyarta da ke Kofar Wambai ta samu kudin mota. Da wannan shawarar ta fara tafiya. Gari ne na damina dan haka tsilli tsilin mutane ne akan titi saboda ruwan da aka maka da daddare. A cikin wannan tafiyar ne ta tafi dogon tunani.

*************************

Ita yar asalin haifaffiyar kano ce a wata unguwa da ake kira Kofar Wambai. Mahaifinta ya rasu tun tana karama inda mahifiyarta Hajiya Uwani mai zuciyar nema ta cigaba da kula da su har zuwa lokacin da hindatun ta kamala diplomarta a Health Technology da ke kano. Abubuwa sun fara cabewa ne lokacin da mahaifiyar ta su ta gamu da cutar ciwon ido ta “glaucoma” har ya zamana ta daina gani.2

Fadi nan tashi nan Hindatu ta fara neman aiki da dan kwalin diplomarta amma abu ya ci tura. To bata san wani a sama ba,ba ta kuma san wani wanda ya san wani ba don haka maganar neman aiki ta rushe.

Abubakar wanda aka fi sani da Habu yana cikin masu neman aurenta kuma shi ya fi kwanta mata a rai. Soyayya aka yi irinta bugawa a jarida wacce in ba kai ba sai rijiya.9

Habu ba mai kudi ba ne,rufin asiri gare shi yana aiki a wani kamfanin robobi da ke sharada a matsayin mataimakin manaja kuma yakan taimakawa su Hindatu. Aka yi biki aka kare aka kai amarya dakinta. Wani abu da ya fara daure ma ta kai bai wuce yanda zamantakewar ta da Habu take neman sauya zani ba. Shi din da ta sani a samartaka mai wasa da dariya sai ya zamana idan ta ji dariyarsa to kallon ball yake inda yan club din su suka yi sa’ar buga kwallo cikin ragar abokanan hamayyarsu.

Auren bai fi wata shida ba gabadaya zaman ya isheta. Dan taimakawa mahaifiyarta da yake ma duk ya watsar suka koma gidan jiya. Dama shi iyayena sun rasu a wajen kawunsa ya tashi,to su ma nan sai ya dade kafin ya je.

STORY CONTINUES BELOW

Sa’annan Hindatu ta fahimci abu guda daya, samun da yake yi yanzu ya karu wanda hakan ya sa masa girman kai . Ita tai ta san ba ta ji a wajensa ko wajen wani cewar an masa karin girma ba amma yanayin kashe kudinsa ya bala’in wuce na da. Ya sayi motarsa “volvo” ba dan ya isa saya ba yake buga abarsa yana shanawa a gari hindatu ba ta isa ta ce uffan ba!5

Lokacin da ta haifi Abba kuwa ranar suna yaron irin shagalin da aka sha aka ci mutuncin nera sai da jikinta yayi sanyi. Ta lura yanayin abokansa yanzu duk wadanda suka fi karfinsa ne ta yanda in ta lura da motocinsu da siturunsu. Abin tambaya anan shi ne ina Habu ya samu kudaden da yake facaka da su wanda daga gani sun fi karfin albashinsa?1

Ranar dai ta kasa hakuri ta tambaye shi ya yi mata mugun kallo ya ce cikin gatsali4

“fashi da makami nake”5

ya mayar da kan sa kan akwatin talabijin. Ba ta daddara ba

ta ce ” wannan rayuwar da ka daukar mana ba fa za ta kaimu koina ba. Ko ba ka gayamin inda kake samun kudi ba na san da haram a ciki ina ji maka tsoro ranar da zata tashi da mu”.2

“Ta tashi da ke dai uwar mugun fata”!

Ya fada yana kumfar baki,sanna ya nunota da dan ali2

“ke na ga fa kwanan nan kina kawomin raini. Idan hawainiyarki ba ta kiyayi rama ta ba to ungulu za tayi saurin komawa gidanta na tsamiya. To ma ina ruwanki da al’amarina? Biyayyar da aka ce ki yi kenen? Kina tuhumar mijinki..a irin haka shi ya sa mata ku ka yi yawa a wutar jahannama!”13

Jikinta yayi sanyi ta ce

” Daga shawara? Gyara kayanka ai ba ya zama sauke mu raba. Ka ari wadansu halaye ka ratayawa kan ka. Duk me ba ka shawara wallahi ba masoyinka ba ne,ka nemi masoyinka tun wuri!”3

Ya zuba ma ta ido kamar wanda zai mayar ma ta..sai kuma ya buga shaddarsa mai sitati ya shuri takalmansa ya kara gaba. Wannan kenen.

Ba ayi sati da wannan maganar ba rigima ta tashi asiri ya tonu inda aka kama Habu dumu dumu da satar kudin kamfani hade da manajan kamfanin. Masu kamfani ba sani ba sabo suka miqa su gaban kuliya manta sabo. ‘Yar motar da Habun ke fafa da ita aka sayar aka hada da gidan da suke ciki na gado, Hindatu ta hada da gadonta da ‘yan kujerunta aka hada aka kwato shi da kyar!

Ragowar kudin hannunta ne ta kama musu hayar wani dan tsurut din gida mai ciki da falo da ‘yar rumfa ta kuma ja jari tana yan kulle kulle na su gishiri,maggi da sauransu. Ya zo ya koma ba ko sisi,ba aikin yi sai buga buga duk abunda ya ganganda ya samo ya kawo ma ta ta hada da na ta a rufa asiri.

Aka cigaba da gurgura rayuwar a haka tana samun ciniki sosai har ta sayi gadonta na fameka a wajen wata dillaliya a unguwar ta kuma sayi shimfidediyar tabarma ta shimfida a falo. Ta dauki Naira dubu biyu ta bawa Habu ta ce ya kafa tireda a kofar gidan ko sa dan dunga rage wani abun. Da ya karbi kudin washegari sai ganinsa tayi da katuwar rediyo mai manya manyan sifiku ya zo ya kima mata a falo,ya zuba mata manyan batira yana sauraren labaran duniya. Har ma ya kan ce13

” Au har mutum zai iya zama bai ji labarin abinda duniya ke ciki ba? Idan mutum fa ya saki jiki a haka a haka arzikinsa zai zo ya wuce bai sani ba!”11

Ido bai fara raina fata ba sai da shekara ta zagayo mai gida ya fara batun kudin haya har ma ya bayarda notis Habu ya dubi Hindatu ya ce

” kam bala’i wallahi tallahi talaucin nan ya isheni. Wai kasar nan ina za ta da mu ne? kullum cikin babu muke.

Muna nema kamar ba ma yi gwamnati ta bi dukiya ta handame mu talakawa an bar mu da hamma. Kyaun kasar nan a rushe wani abu wai shi gwamnati,a raba kudin kasar gabadaya kowa ya dau kason sa in ya so kowa tashi ta fisshe shi.”21

Duk wannan maganar da yake yi Hindatu na talgen tuwo bata juya ba mamaki ya gama mamaye ma ta zuciya tana jinjina maganganunsa. Ai gwamnatin kowa tana farawa ne daga kan sa shi yanzu gwamnatin ya shiga har ya samu ya handame dukiyar kamfani? Shi ya fara yiwa kan sa fada mana. Ba irinsa irinsa ba ne a gwamnatin suke handame dukiyar kasa? Lallai laifi tudu. Ta share korafinsa don ta san tana magana cibi zai zama qari ta ce4

STORY CONTINUES BELOW

“to yanzu ya za ayi game da kudin hayar?”

Ya watsa hannayensa a iska ya ce

“yo ni me kuwa zan yi? Kur’anin Allah da naira ashirin na tashi,shekaruna kike so na cire na biya kudin hayar da su?”12

A sanyaye ta ce

“wai da tunani na ko zaka je gurin kawunka” ya ja tsaki ya ce

” kawun da nayi wata bakwai rabon da ko gaishe shi na je?ai ina tsammanin idan bai kira ubana na kabari ya zaga ba to kuwa ba zai dauki kwandalarsa ya bani ba”5

Ya cigaba da sauraren rediyonsa yana shan iskar karkashin bishiyar dalbejiya. Da sauke tuwonta ta sabi mayafi ta tafi gidan Hanne uwar adashe bayan dogon roko ta samu aka bata daukan watan. Da dan cinikinta na cikin gida ta hada aka biya kudin hayar wannan shekarar. Wannan ta wuce.

Hindatu ta kuma dagewa da sana’arta har ma ta soma yin lamurje da kunun zaki ana siyo ma ta kankara a zoo road tana dorawa tunda ba ta da firji. Akwai wani Mai kudi a unguwarsu ta je ta roki matarsa da ta taimaka ta sa baki wajen maigidan a bawa Habu aikin shara da ban ruwan fulawa sai ake biyansa wata wata.Aikin ya samu cikon ikon Allah shi ma ya karba ya yarda zai yi. Idan ya dawo maganganunsa ba sa wuce2

” kin kuwa san tazara tsakanin mai kudi da talaka kamar tazara ce dake tsakanin sammai da kassai? Ai ma su abun suna shanawa! Dan arzikin namu sun hada sun tura bankunansu na kasashen waje daga su sai matansu da ‘ya’yansu. Mai kudi bai san zafi ba saboda yana cikin “ac” bai san sanyi ba saboda yana cikin “heater”. Ke idan kasar ta ishe su sai su kwashi iyalansu su tafi ingila ko amurka ko saudiyya. Su je su roki Allah ya yafe masa zunubansu. Shin wai ba kya ganin kamar sun fi kusanci da Allah? Kamar dan su aka halicci duniyar? Kamar za su ri ga mu shiga aljanna??22

Ta yi sauri ta ce

” Auzubillahi.. wai so ka ke kayi sabo? Ai babu wani makusanci da Allah sai wanda ya fi bauta ma sa. Wai ya ka ke nema ka yarda imaninka?”

Jikinsa yayi sanyi ya ce

“kuma fa haka ne ,banbancin kawai daular. Don ke kan ki kin san kudi su ne jin dadin rayuwa su ne kumbar susa wanda ba shi da su ya zama sorry! Dubi dazu dazun nan Hajiya ta miko min ragowar abincin Alhaji wallahi da na bude kwanon miyar kin ga nama zuqu zuqu? Na rantse miki da Allah yadda kika san yana aurar da diya wai a haka ci yayi ya rage”12

Hindatu ta kwashe da dariya shi ma kuma ya biye ma ta suka yi tare har yana karawa da

“wallahi”

Ta ce ” kuma shi ne ka kasa ragomin”?2

Yayi ma ta hararar wasa ta nuni da yau yana cikin nishadi ya ce

“Inaa… ai anan na sude na lashe ban bar ko dan kankani ba don kar ma ‘yan wanke wanke su samu sudi”

Canje canje sun fara aukuwa ne bayan ta haifi ‘yar ta Asiya da shekara daya lokacin ne Alhaji ya kori Habu daga aiki saboda rashin bawa aikin muhimmanci. A kuma lokacin ne hindatu ta zo ma sa da wani zance da yayi wa laqabi da zancen banza marar dadin sauraro , wai tana dauke da ciki. Cikin da ya zo ma ta da masifar laulayin da ko sana’ar ta bata iya yi. Cikin jikinta na da wata bakwai ta wayi gari da wani mummunan alamari na ban mamaki na an nemi Habu ko sama ko kasa an rasa. Aka shiga cigiyarsa gidajen rediyo da unguwanni amma ba labari.

Hankalinta ya fi raja’a akan ‘yan mafiya ne suka sace shi ,amma kuma ba ta karyata tunaninta ba sai da aka yi kwana bakwai da batansa.1

Daidai matsatsin yaloluwar katifarta da gadonta ta tsinci wata takarda mai jimla biyu. Ga abunda ta kunsa

“Ni Habu na saki matata Hindatu saki daya,domin bazan iya jure zama da ita a halin talauci ba. Kar da ta neme ni don baza ta ganni ba.”20

STORY CONTINUES BELOW

Yan hanjinta ta ji sun murda dan cikinta kamar zai hudo ya fito. Sai ta ji kamar numfashinta zai dauke hawaye wani na riga wani a fuskarta, yaya Habu zai mata haka? Wani abun ban haushin ma ko maganar ‘ya’yansa bai yi ba balle cikin da ya bar ta da shi. Wato ma wai ka da ta neme shi kamar bai bar ta da wani nauyi ba.

Ta cigaba da jujjuya takardar a hannunta tana maimaita ” Habu Allah ya isa ..Allah ya ma ka abunda ka min..”15

*******************************

Ruwan da aka fara kamar da bakin kwarya shi ya katse wa hindatu dogon tunaninta. Cike da tsananin mamaki ta tsaya cak don har ga Allah bata lura da hadari ba. Jinjirinta ya fara tsala kuka na fitar hayyaci yana mimmikewa nan ta shiga diriricewa tana neman wajen fakewa.2

Ta fara gudu tana hange hange har sai da ruwa ya taba su sa’annnan ta samu wani wajen rubabben rumfar langa langa ta fake. Hakoranta suka cigaba da kaduwar sanyi kaf…kaf tana mai dana sanin fitowarta a wannan bahaguwar larabar.1

Sai da aka yi kusan minti talatin sannan ruwan ya tsagaita, muhammadu yayi shiru a lokacin tsammaninta ya samu bacci. Tsiraran motoci da babura da wasu a kafa sun soma wucewa bisa titi don gudanar da uzurirrikansu. Har yanzu ba ta kai Dangi ba kawai sai ta tsallaka gefen titi da niyyar ta roki dan achaba da ya taimaka ya kai ta asibitin murtala a naira talatin.

Can sai ta hangi wani daure da hankicif shudi a kan sa ta sa hannu ta tare shi ya tsaya hade da fadin

” Hajiya ina za ki”?

Ta fito da talatin din da ke jikinta ta karyar da murya ta ce

” Dan Allah bawan Allah ka taimake ni yanda Allah ya taimake ka, yaro na ne ba shi da lafiya ka taimaka ka kai ni bakin asibiti a naira talatin. Dan son ma’aiki”

Dan achaban baki wuluk mai faffadan lebe da katon hancin da ya mamaye kusan rabin fuskarsa ya kura ma ta kwala kwalan idanuwansa masu kama da jan gauta ba tare da ya ba ta amsa ba har tayi zaton taimakonta zai yi. Amma me? Sai ta ga ya sa kafarsa ya burga babur din bayan ya jeho ma ta wata murdaddiyar tambaya1

” Yo Hajiya mashin din na uwarki ne?!”19

Ya cilla kan titi ya bar ta anan. Duk wannan abun da suke yi akan idon wani dan achaba da ya tsaya a gaban mai tireda ya sayi sigari. Ya cigaba da kallonta bayan ya dora sigarin akan lebensa ya cinna ma ta wuta. Gangarowa yayi gabanta ya kalle ta bayan ya zuki hayaki mai yawa ya fesar akan fuskarta. Wani abu mai kama da ashar ya zo ma ta iya wuya kafin ta furta ta ji ya ce

“kawo talatin din”

Cikin rawar jiki ta mika ma sa ta dane kan babur din ya cilla da ita bisa titi har asibitin murtala.

Tana isa ta wuce miltara babu cikowar mutane saboda ruwan saman da aka yi sai ta samu benci ta zauna ta kama layi. Ta tamabayi ta kusa da ita

“ya na ga layin baya motsi”?

matar ta ce

” tun dazu muke jira wai kati ya kare sai an kawo..to jiran ya zama na gawon shanu”3

Ta ja dan karamin tsaki tana mai cigaba da ba wa wani dan yaro awarar da ke hannunta. Hindatu tayi shiru ta san ba yadda za tayi sai dai ta jira.

Wata mata mai dauke da farin bokiti cike da alala kullin leda ta zo wucewa ta na cewa

” alala alala ashirin ashirin”

Sai ta ji cikinta ya bada kululu ta bi alalar da ido ga ta lubu lubu , jajir daga gani ta sha manja. Ta hadiyi yawu makwat tana mai tuna rabonta da cin alala irin wannan. Mai alalar har ta bace wa idonta tana binta da kallo kamar ta kwata. Daga bisani ta kau da ido ranta a bace da ta tuna ba ta maganin ko ficika.2

Ta yanke shawarar komawa gidansu tun da zaman na ta bana kare ba ne,dama a gajeran tunaninta ta dauka Habu ba nisa yayi ba zai waiwaye su. Hakan ya sa ta share ta zauna zaman jiransa ya dawo duk da zunden da mutane ke ma ta.

Aka kawo katin ta karba har aka zo kan ta a layi ta shiga dakin likita. Wata nas na zaune a gefensa , ta gaishe shi ya amsa ba tare da ya dago ya kalle ta ba. Daga bisani ya karbi katinta ya dago kan sa ya ce

” menene matsalar?”

Tayi ma sa bayani ya ce ta miko yaron. Ta kunto shi a kunshin zanin goyo mai damshi ya karba a daidai lokacin yayi sauri ya dago ya kalleta jin yaron sakab sannan a jike ya ce

“yaya na ji shi a jike??

Ta ce a sanyaye

“Ruwan sama likita,ruwa ne ya dake mu”

Likita ya maida kallonsa kan jinjiri muhammadu a wani yanayi da ya sa hindatu shan jinin jikinta. Ya shimfidar da shi akan gado yana ta dudduba shi da kayan aiki. Cikin kasa da minti daya ya juyo ya ce ma ta

“Hajiya ai ya rasu”!8

Duniyar Hjndatu ta fara juyawa da ita jikinta na kyarma..me take ji haka? Ba ta iya cewa komai ba karbar gawar jinjirin kawai ta yi ta fice a guje. Sai ta kankame jiririnta tana gudu, tayi gudu tayi gudu amma fa ba ta san takamaimai inda tayi ba. Haka mutane suka dinga binta da kallon mahaukaciya sabon kamu.2

Lokacin da Allah ya taimaka ta isa gida har an idar da sallar laasar. Malam mai almajirai makocinsu mai taimakonsu har ya sa an baza tabarmi na karatun yamma. Ta fado gabansa cikin gigita ta zube ma sa ta fashe da kuka cewa yake

” lafiya? Hindatu lafiya? Shiga cikin gida gani nan zuwa”

Ta kasa ce masa komai saboda kuka sai kawai ta miko ma sa gawar ta dora ma sa, kamar numfashinta zai dauke ta ce

“Ya rasu malam”. A jikina ruwan sama ya taba shi aka zare mishi rai ba tare da na lura ba. Ina ma ni aka dauke na je lahirar da ta fiye mini duniya! Malam akwai wasu mutane wanda ba a halicce su dan su ji dadi a duniya ba,wadanda duniya bata karbe su ba..ina ga ina cikinsu malam! Malam ya mike tsaye a cikin tashin hankali ya ce15

“Auzubillahi..wannan kalamai ne na wadanda suka fitar da rahama daga ubangiji, na wadanda suka bata ne, ke kuma ba batacciya ba ce”

Ta ce “

Ina ma na tashi a cikin batattun watakila da na san menene dadin duniya”!1

Malam ya lura sumbatu take don haka ya karashe zancen da

“garin yaya wannan kaddara ta auku”

Yana mai nuni da gawar. Ta nisa tana jinjina kai zuciyarta cike da kissa ma ta abubuwa ta ce

“Rashin kumbar susa..Allah ya tsinewa rashin kumbar susa”!Ina aka je? Ina za a dawo?+

Saudi Arabia

“Hajiyya goro”? Balaraben ya tambayi wata mata da ke fitowa daga harabar “airport” din Jidda a cikin gurbatacciyar hausarsa. Matar ta girgiza kai tayi gaba cike da takaicin goronta da aka kwace a wajen screening . Ranta ya cigaba da raya ma ta dama a gida Najeriya ne, ta bada cin hanci ta wuce da shi ta ci kazamar riba.9

Wannan abun da ya faru akan idon Lubabatu wacce ta sha bakar abaya da nikabi baka hango komai sai fararen idanuwanta. Can ta hango wata mata lukuta ta fito da sassarfa tana tafiya da kyar kamar kwai ya fashe ma ta a ciki. Luba tayi sauri ta mike ta cafki hannun matar ta ce

“Salam ya ukhti..Hajiyya barka da zuwa barka da zuwa na ga alama akwai goro ko?”

Hajiyar ta kalli Luba da mamakin yadda ta gane yayin da takari maza da mata suka yanyame ta da rokon ta siyar musu. Amma sai ta ki, ta tsayar da Luba akan dalilin ita ta fara taryo ta. Suka sauke goron ta na mai bawa Luba labari

” Ai duk cikin ‘yanuwana ni kadai na samu na ketaro da shi yau sa’ar a kaina take. Abokanan tafiyata an kwace musu har da masu kwarya goma! Amma kin ganni nan sai da na haye da kwarya takwas!”1

Luba tace ” Mashallah mashallah”

Sa’annan ta daga baki ta kwalawa Hajiya ‘yar Sakkwato kira ita kuma tayi ma ta alama da hannu cewar ta na zuwa. Suka yi ciniki ta biya ta kwashi goronta tayi gaba suka hade da Hajiya ‘yar Sakkwato tana murmushin mugunta ta ce

” ai halin na ma ta ,na ga sabuwar hajiya ce ko kan lisafin riyal din ba ta sani ba”

Suka kwashe da dariya. Hajiya Yar Sakkwato ta ce

“Kwanda da kin kai ma ta haka. Duka nawa an ka saida huhun goro ga kano? Amma dan Allah ya bisshe su ga sa’a sunka hawo da shi ,sai su lumka mishi kuddi su saida shi da tsada bayan mu abun kai baka kawai munka bida” .

Luba ta gyara nikab dinta tayi murmushi ta ce

” Kin ko samu kin sayi man bilicin din kin san fa kwanan nan shi ke kawo kudi.”

Hajiyar ta saka hannu a ledar hannunta ta nuna ma ta ta kara da cewa2

” har atanhwa ta jikka bibbiyu ni ssiya sai mu siyarta ga uwani mai tuwo na ji tana bida”

Suka rankaya za su fita Luba tayi sauri ta ce ” au ki tsaya mu duba ko an kawo maggi star kin san fa yanzu zuwan ‘yan umara ne, su in ba su ji maggin nan zai! a abinci ba babu magana”. Da kayan da suka siya daga hannun matafiya ‘yan Najeriya suka koma Makkah. Nan da nan fa sai kasuwa ta bude, suka raba goron nan bari bari suna siyarwa larabawan nan mayun goro su kuma suna rububi.11

Idan da mai karatu zai ga inda su Luba ke kwana a unguwar Sharu mansur da Sharu sittin sai abun ya bashi mamaki. Anan za ka ga mai siyar da tuwo, waina, shinkafa har da danginsu gyada da aya. Dakin kwanansu Luba wani tsukakken daki ne a can saman bene su goma sha uku ne a dakin kowa akan ‘yar yaloluwar katifarsa. Daukacin jama’ar wannan daki ba sa dauke da takardar shaidar zama ta dan kasa igama, a takaice dai bakin haure ne.

Luba da Hajiya kan yi tuwo,suna kuma sayar da kayan sare saren da suka samo daga ‘yan Najeriya. Sa’annan Luba kan dauki kayan yara da dan kananan siturunsu masu saukin kudi ta kulle a zani ta kai bakin “Harem” .Duk inda suka ga askar to fa sai su fyalla a guje ita da ire irenta , don idan aka kama ka yanzun nan ka sha zaman” sijjin”daga nan sai kasarka ta gado.3

Idan lokacin Ummara da Hajji ya wuce sukan yi aiki a gidajen larabawa kamar su wanke wanke, shara, raino da sauransu. Wadannan aiyukan da bakaken fata kan yiwa larabawa shi ke sawa suke musu kallon kaskanci a ganinsu kowani bakar fata matsiyaci ne, boyi boyi ne. Don haka kyara ta dalilin banbancin launin fata (racism) yayi yawa yayin da aka samu rangwame na rashin sanin darajar kai a wajen bakaken.8

STORY CONTINUES BELOW

Wani abu da Luba kan yi wanda ma fi yawan ‘yan kano to jidda ke yi shi ne karuwanci. Hakan zai iya zama tsakanin bakaken fata mazauna can ko kuma mazan larabawa. Hakan ba karamin kudi yake kawo musu ba domin kuwa mazan larabawa ba su kyashin fitar da ko nawa ne idan har bukatarsu zata biya.2

Luba ta kalli Hajiya a wani dare da suke shirin kwanciya ta ce

” wai ko hajiya don munafirci kin san ‘yar Gombe fara lekawa tayi wajen Balaraben nan mai gwal na Jidda wanda ki kai min hanya? Shegiya tsinanniya! kin san kuwa cewa Hajiya Zulai kawarki ita ce ta ma ta hanya dan ta ga yana barin kudi? Duk sai sun ci ubansu ‘ya’yan matsiyata, ‘ya’yan bakin ciki!” Ta dauko ashar ta maka!11

Hajiya tayi salati ta sanar da ubangiji cike da mamaki ta ce “wacce Hajiya Zulai kinka nihi? Wagga da na yiwa hanya ta zo garin ga tana tsumma gaba tsumma baya? Hal ita ce akan gama baki da ita ai mana zalumci?”14

Luba ta tsuke baki kamar irin yanda yara kan yi, yanayin halayyarta kenen. Ta saki bakin a hankali sannan ta ja karamin tsaki. Ba ta tanka Hajiyar ba illa ma ta shiga warware gashin kanta wanda ya zubo har gadon baya ta sa mataji ta soma taza.

Hajiya Yar Sokoto ta lalace wajen

duban Luba da irin nata kyawun sai kace barbarar yanyawa. Wasu irin idanuwa gareta manya manya farare da ta da take iya yin wani kallo da su ta kafe mutum kamar tocila. Bakin kwayar idonta da gashin girarta kan rikita yawa yawan maza da suka kauce hanya a irin hilata da jan hankali irin na ta. Yanayin jikinta daidai yake da yanda mazan da ke kara kaina akanta ke bukata. Tana da kowacce irin halitta da mace ke bukata a kira ta da mace ta kuma amsa da babbar murya.13

Tana da tsayi daidai ita da kibar da bata wuce misali ba sai dai me? Duk cikar halittar Luba dafi ce ga wanda bai san ta ba, zinariya ce ga wanda ke cikin duhun jaraba haka guba ce ga wanda ya sake ya rabe ta.8

Hajiya yar sokoto tayi firgigit ta dawo daga duniyar tunaninta lokacin da Luba ta daka mata duka a cinya. Ta ce “Hajiya yaya dai?” Hajiyar ta janyo kwananta da kubz da yar miyar dankali ta ce

” To ke me ma yaka damunki? Su fa larabawan ga irinki sun ka hi so har wani manemi za ki qi yi? Ni fa shekarata ishirin kasar ga , wallahi ki tsumayi aikin hajjin ga mai zawwa Alhazawan da na ka gama ki da su..K’ ..kya yi mamaki”1

Budar bakin Luba sai cewa tayi

” Kutumar! Hajiya rainawa kan ki hankali ina ce bara ma haka kika ce da ni amma da aka kawo yara kanana kasuwarki ta bude da su ban ko ji duriyarki ba! Ke ma kika samo naki abokin harkar Alhaji mai goro ko kwana gida ba ki yi”

Hajiya ta kule matuka da kalaman Luba. Dama ita matsalarta kenen shegiyar fitsara da tantiriyar rashin kunya.idan ban da don tana samun kudi ta hanyarta ba da tuni ta yarda kwallon mangwaro ta huta da kuda. A kule ta ce

” Luba ni ki ka dannawa ashariya?

Luba ta ce ” yo Hajiya ni…ni…karya nayi? tsofai tsofai da ke wai har kin san dadin maza?” ta yi sakaka da baki cikin tsabar rashin mutunci.

A fusace Hajiya ta ce9

” Tun kahin a haihi uwalki na san maza!kin ji ni ko? Ganin kin zo Saudiyya kin waye na ‘yan shekaru hal kin ka isa ki mini ragaita? Sa’ilin da kike kudin cizonki har na bisshe ki ga daudar dakin uwalki ba ki ki min ragaita ba! Sai yanzu da kin ka hwara kama kudi bisa hannunki shi ne za ki tasamma zagina?”11

Luba ta gintse dariyarta ganin ran Hajiya ya baci. Ita ta san cewa Hajiyar na cutarta tana mata wayonsu na tsofaffin kilaki don haka ta dade mata a makogwaro. Ranta na raya mata Hajiya ita ta yiwa yar Gombe hanya wajen balaraben nan don hadama amma ta ke nema ta ninke ta baibai.2

Amma sai ta tuna cewa ba yanzu ne lokacin da ya kamata a bata ba , da sauran lokaci. Sai ta share ta shiga bawa Hajiyar hakuri. A ranar ta kwanta da burirrika iri iri a ranta.

STORY CONTINUES BELOW

**************************

Ga duk wanda ya kwana ya tashi a unguwar Birget ya san Luba a zamaninta. Gidansu wani tsukakken gida ne mai mata hudu da ‘ya’yan da ko mai gidan farat daya ba zai ce ga yawansu ba.

Duk macen da mahaifinsu ya aura ya saki sai ta dangwarar da ‘ya’yan ta kara gaba ba don akwai takamaimai wanda zai iya daga ido ya kalle su da rahma ba. Haka zai ta gararamba duk inda ya wuce matar uba tana bin sa da alkaba’i3

“shege tsinanne dan gidan ta maqwalle mai gani har hanji” ,

“gantalalle da micin ido irin na uwarsa”

Wadannan kalaman su ne ruwan dare akan ‘ya’yan tsakar gida. Kazar gidan ta fi dan da ke yawo a tsakar gida daraja domin kuwa ita watakila a watsa ma ta hatsi ko don ta girma a ci moriyarta.

A tsawon zaman Luba a gidansu bata taba ganin mahaifinta ya shigo da leda da sunan cefane ba sai lokaci daya tak!wato idan ya yiwo sabuwar amarya. A ranar da ta zo a ranar ne za a gwangwajeta da dankwaleliyar gasasshiyar kaza daga nan kuma sai ga ji dif! Kamar an dauke ruwan sama sai kuma zuwan wata amaryar!5

Baban na su an fi saninsa da “Baban yara” kuma talaka ne tilis bai ajiye ba bai ba wa wani ajiya ba bai kuma damu da hakan ba. Mutane na mamakin yadda aka yi mata ke amincewa su aure shi ,har ma wai suka yi hasashen cewa yana da wata laya ta farin jini da babu macen da ta isa ta musa ma sa. Yar sana’ar ta sa ba ta wuce sayar da danginsu tumatir, tattasai da attaruhu amma aure aurensa ko tattabara albarka.

Idan ka ga an dora tukunya a gidan to uwar kowa ce ta nema ta baiwa ‘ya’yanta su kuma ‘ya’yan tsakar gida idan an ci a sude su samu na lasa.3

Wani iri zama ake yi a gidan irin na marina , zaman ban san ka ba..kowa tashi ta fisshe shi. Kowa burinsa ya nema ya samu ya hana danuwansa. Ga tsananin kishi tsakanin matan kowacce so take a ce ita da ‘ya’yanta sun fi.

Mahaifyar Luba ita ce ta biyu kuma ita da uwargidan a yanzu su ke da zaunannen gurbi a gidan. Hakan ne dalilin da yasa suka zama dadaddun abokanan hamayya. Dukanninsu suna da yara maza da mata.10

Iya Asabe uwargida tana da ‘ya’yanta bakwai wanda akwai biyu mata wadanda suke kusan sa’anin Lubar.

Iya tamadi mahaifiyar Luba ‘ya’yanta maza uku da autarta Luba.

Ragowar gurbin na mata biyu wanda akan iya canja su a kowane lokaci na da ‘ya’ya barkatai wanda kirga su ma tsatsar rashin aikin yi ne. A zuciyar Iya tamadi ba komai sai tsanani kwadayi, kullum Allah Allah take wani ya kawo abunsa ta lashe ko da kuwa yayan cikinta ne. Halin da ya sa kenen ‘ya”yanta maza suka guje ta ba ma sa son shigowa gidan saboda jarabar bani bani. Ita a son ran ta , ta fi iya asabe komai dangane da abun duniya. ‘Ya’ya mazan data kwallafawa rai suka ki tsinana mata komai ,kawai sai ta kafa murhu take suyar kosai safe da yamma.

Iya asabe na ganin haka sai ta nunawa iya tamadi ranar haihuwar ‘ya’ya mata. Sai take yin alawoyin yara take dora musu talla.3

A tun tasowar Luba ta saba da rayuwa irin ta kashin dankali na sama ya danne na kasa, da kuma kowa tashi ta fisshe shi. Sai ta taso a yarinya yar kanta ba mai fada ma ta ta ji. Da fari ta takura wa uwar ta sa ta a makarantar firamare ta gwamnati da ke unguwarsu saboda kawai ta banbanta da sauran yan gidansu da take kira ‘yan kauye. Luba ta fi ganin karatu a matsayin hanyar bunkasa da birgewa ba wai wata hanyar samun ilmi ba.

Da fari uwar ta ki ta ce zata kashe mata jari. To amma da yake Luba uwar naci ce kuma auta shalelen Iya Tamadi sai ta yarda amma da sharadin daga nan ba cigaba. Da ta gama firamare lokacin tana da shekara goma sha biyar sai ta ci common entrance ta kuma dage ita fa sai ta je sakandare.

Iya tamadi ta hau ta fado kasa ta ce ba da jarin kosan ta ba karya da ciwo mari da zafi. Luba uwar giggiwa da tsaurin ido sai cewa tayi

” yo ni ma sana’ata zan kafa na huta da wulakancinki. Ranta min dubu biyu billahillazi kafin karshen sati zan maido miki kudinki”2

Iya tamadi ta mika ma ta kudin ta hada da rantsuwar sati na zagayowa idan bata maido da kudin ba ,za ta siyar da atamfarta mai tambarin gidan Sarki da saurayin ita Lubar ya saya ma ta ta ci sallah. Luba ta ce1

STORY CONTINUES BELOW

“eh na ji”.

Washegari kuwa ta yi cefenenta ta ta dafa shinkafa da taliya tayi miya da naman saniya. Ta sa yaro ya siyo ma ta salak da tumatir ta yanka siri siri ta saka a farin bokiti mai suna fallasa. Kayan abincinta ta kwasa ta dora a kai ta fice abunta ba tare da ta ce wa kowa ga inda ta je ba.1

Da yammaci lis ana shirin kiran sallar magariba sai ga ta da fararen bokiti komai ya kare. Iya tamadi ta rike haba cike da mamaki ta ce

” ke…auta! Ba dai wai har ya kare ba?”2

Sai ta yi wa uwar kallon galala na ina ruwanki ta ce

” yo ku dai ku zuba min ido ba kowa ya ki ya taimake ni ba? Ai kuwa ni zan taimaki kaina”1

Iya tamadi ta cigaba da cewa ba tare da ta damu da kallon banza ko maganar da tayi ba2

” Auta kenen. Ke dai da yake kina da tagomashin arziki dole ki ce haka. Mata nawa ke saida shinkafa da taliya a bakin kasuwa kuma suke bandaron kayarsu? ke..ni ko dai juye aka miki?”14

Luba ta kada kanta ta tafi bakin rijiya ba tare da ta bawa uwar ansa ba ta janyo ruwan wanka. Ta shiga bandaki ta sallo wankanta. Bayan sallar isha’i ta ci kwalliyarta cas ta baza turare .Iya tamadi tana ta yashe baki ganin diyar ta ta tamkar zinariya. Ta sa kai ta fice abunta ba tare da ta cewa kowa kanzil ba. Kullum haka Luba kan yi karshen sati na zuwa kuwa ta lalo dubu biyu cas ta mikawa iya tamadi ,ragowar kudin dumus a hannunta riba ce ta fara kokarin turawa a ‘yar pos. Iya tamadi ta ce

” Haba haba auta..ai ido guba..ai kya dan lasa min irin wanna uban kudi haka?”4

Luba ta ce ” Tabdijam! Dubu biyun ma na ga da kyar kika ranta min, da ace ban samu riba ba da yanzu kin daga min hankali kin ce na ba ki abarki. Kin ga wannan kudin? To kudin kayan makaranta ne zan sai abuna da ‘yan littafai Alkur’ani sai nayi bokon nan in ga uwar meye a cikinta da masu zuwa suke daga mana kai!”

Iya Tamadi ta fara zazzaro ido ta ce

” Au ke yanzu wannan uban kudin asararsa za kiyi a karatun boko? Ni ca nake ma taro za ki fara tunda dai kin san halin ubanki ko cokalin shan shayi bai siya miki in aurenki ya tashi. Ni ce dai komai kuma so nake na yankawa su Hafsi da Rahila sakwaninki. Kin ga wannan fita tallar da suke billahillazi samari kashe musu kudi suke. Karkashin gadonsu kuwa kamar kantin kalau kalau. So ki ke yi mu ji kunya?”3

Luba kuwa sai buga cinya tayi ta gatsina baki ta ce

” yo ke iyannan ina ruwanki? Su sayi kasuwar kwari su hada da ta bakin asibiti. Ke ba kya ganinsu ne wai ‘yan kauye ba wani aji yanzun haka har wani saurayin kirki ne zai aure su? Daga mai tireda sai mai gurasa me na sama ya ci ballantana na kasa ya dangwala? Ni fa dan boko zan aura mai aikin ofis ko so kike yanda kika kare nima na kare? “2

Cikin tsananin sauri Iya tamadi ta buga a’uziyya ta ce

” Allah ya kiyashe ki auren irin ubanku. Haihuwar guzuma ‘ya kwance uwa kwance” sai ta kama haba ” ni na rasa wani tsautsayi ya kai ni auren ubanku ba ci ba sha auren matsiyaci” ta karashe da watsa hannaye a iska cikin saduda ta ce ” rabon haihuwarku ne auta in ba don haka ba ai na fi karfin ubanku!”4

Luba ta ce ” A to. Ki bari ni dai nayi bokon nan na goge. Miji kuwa sai na zaba na darje ban yin auren wahala Alkur’an!Idan banda abunki ma ke ba da kudinki za a je bokon nan ba, ba kuma na uban wani ba me zai dame ki?”6

Iya tamadi ta ce “Ai fa..to ban dari biyar auta ladan ganin ido”2

Luba ta zaro ‘yan dari biyar biyu ta mika ma ta sabbi kar, ta yi saurin karba kamar ta kifa don d’oki.1

” Duk cikin ‘ya’yana ba mai kaunata irinki auta, daga gani ke za ki fitar da ni cikin kangin talauci. In banda abunki ma wlh da mun hada jari” inji Iya tamadi.1

STORY CONTINUES BELOW

Luba ta kwashe da dariya ta ce ” ka ji iyannan ta ji zancen kudi. Ban ki ba dai tunda yanzun zan shiga makaranta sai kike min girkin da safe, ni idan na dawo da rana sai in fita talla. Idan ya so duk abunda aka samu sai na ke ware miki ladan ki. Amma fa ni miya ta ba ajino kadai nake sa ma ta ba, ina saka dunkule kin ji dai na gaya miki”.3

Iya tamadi ba musu ta ce ta yarda.

Litinin na zagayowa Luba ta shiga makaranta abunta ba tare da kowa ya damu da ya aka yi take zuwa ba. Idan ta dawo kuma sai ta dauki abincin tallarta tayi gaba. Sau dayawa har takan kai bayan ishai ba ta dawo ba. Babu wani abu da ya damu iya tamadi illa dai kawai idan ta dawo komin dare za a ja lissafi.

Abu kamar wasa abincin Luba ya bunkasa har ta kai tana yin doya, wake har da kajin gidan gona. Tana kama kudi sosai kuma ita din ‘yar jin dadi da son kwalliya ce. Idan ka gan ta ba zaka ce daga cikin gidansu ta fito ba. Cimar ta ma daban ce a gidan. Idan suna shiri da iya tamadi ta sammata idan ba sa yi ta cinye kayanta. Sai dai ka ji Iyar na cewa

“um’um..uhmm auta..ido guba!”14

Samari ‘yan sha’awa suka yi wa Luba caa tamkar ita kadai ce mace budurwa a layin su. Sau dayawa idan ta dauki tallar abincinta kafin ta kai inda take siyarwa wani yake mata juye. Dan Luba ta wanki saurayi ko ya taba ta ya bata abun duniya ba komai ba ne. Ita dai a rayuwarta ta tsani talauci kuma ta rantse ba zata rayu a cikinsa ba ko da kuwa zata yi yawo tsirara.

Tayi matsanancin sabawa da maza a karancin shekaru irin na ta. Kafin ta shekara sha takwas ta kara cika, ta fara shafe shafe tana walwali sai kuma ta iya taku, tana kuma zuwa makaranta tana dan tsintar turanci.5

A wata ranar asabar ba makaranta Luba ta dora wa almajirai kayan abincinta tinkis tinkis har zuwa kofar shagon Olu inda take da tebur. Duk cikin kasuwar ba mai iya ajiye tebur a gaban shagonsa sai Luba. Olu wani bayerabe ne da ke da shagon siyar da kayan masarufi. Katoton shago ne da shi wanda babu abunda baya siyarwa, hakannan kuma mayen Luba ne.

Luba tana yiwa Olu kyau, tana ba shi sha’awa idan ya gan ta jikinsa har bari yake. Hakan ne ma ya sa ya barta take kasa abinci a kofar shagonsa kuma duk ranar da tayi bandaro yakan siye duka ya rabar don kar ta dau asara. Luba nayi da Olu cikin samarinta ba wai don yana birgeta ko da da kwayar zarra ba ,sai don kudin da take samu a hannunsa da kuma kayan da take dauka a shagon gaba gadi ba tare da ta biya ba.

A rayuwar Luba bata san so ba, kuma ba wanda ya isa ta so shi sai dai ta so abun hannunsa. Sai dai kuma Luba na da kyauta, abun hannunta baya rufe ma ta ido.

Da isowarta ta fara jera kayanta akan tebur a tsaftace. Ta sha atamfarta mai tauraro da kuma gyalenta mai suna “rakani gantali” dan karamin bakinta ya dau jambaki tana taunar cingam kas kas. Ya fito daga shago sanye da wandonsa “three quater” da “vest” hannunsa daya a cikin aljihu dayan kuma ya kama hannun ta yana matsawa ya ce

” Haba Lulu na, ka zo kuma shi ne ba zaka ce min ka zo ba? “

ta dalla masa harara cike da cike da jin haushi ta warce hannunta ta ce

” eh..ai dama yanzu zaka iya zuwa ka min dadin baki ni kuwa na riga na dawo daga takiyarka tunda dai har zaka iya nunamin iyakata akan dubu biyar”

Olu a rude ya ce ” haba haba now..dont say that..luluna you know now..market dis day..e..no sabi good woo..ehn. But ba na gaya maka ka zo monday ba, monday..monday if ka zo..i go get money..i go carry five thousand give you. Wetin be five thousand self..mami water like you i go even give you six thousand ..oh my lulu” ya fadi bayan ya rungumota yana kokarin saka hannunsa a rigarta.

Ai kuwa ta wancakalar da shi sannan ta murguda masa baki ta ce

” kan uba! Mayar ni wawiya, ‘yariska rainon tasha ma! Kai kudinka ne kudi ni jikina ba jiki ba ne? Ai wallahi ba ma zan bar gurin nan ba sai ka bani ko ka zata ban san kana kula halira ba? Mai kawo danwake, rainawa kan ka hankali”

Olu yayi tsuru tsuru har ga Allah baya son bacin ranta domin ya jarrabi kan sa da shaawarta kuma har yau ta ki ta bashi hadin kai sai yawo da hankali take masa tana lashe kudinsa. Tsakaninta da shi bai wuce ta bar shi ya taba wani sassa na jikinta ba daga nan kuma sai ta doje. Tunani sa na gaya masa watakila isassun kudin ne baya ba ta,shi ya sa yake ta barinsu.

STORY CONTINUES BELOW

“Haba lulu” ya fadi yana shafa gefen fuskarta ba tare da ya nuna jin haushi ba ya zaro dubu uku ya ce

” ka gani ba, daga wannan ba ni da komai sai an yi kasuwa yau”

Cikin azama ta warce ta cusa a kirjinta ta ce5

” ai kuwa na raba ka da su”

Anan ne fuskarsa ta dan canja ya ce

” ka dan ba ni guda daya mana lulu ko sigari na sha”

ta bude ‘yar pos din ta, ta zaro murtala ta danka ma sa ta ce7

” in dai sigari ce ishirin ma ta ishe ka”

Kamar abun magani sai yayi kus. Daga karshe ya ce ” to ka zo mu je ciki mana lulu, 2days ba ka yi da ni” . Ta share shi kamar ba ta ji ba ta cigaba da harkar sayar da abincinta.

Shekaru suka ja yayin da tantirancin luba ke karuwa amma ko yaya takan je makarantar ta. Lokacin rubuta jarabawar kammala sakandare ta kawo kai ana bukatar naira dubu gima sha biyar. Dama ita kudi ba sa zama a hannunta sayi banza sayi wofi. Hankalinta ya tashi . Ta bi shawarar zuciyarta ta rankaya wajen Olu wanda suka dade ba sa tare. Ta wassafo ma sa bayani ya galla ma ta harara ya ce1

” Ka bani abunda zan baka kudi ne? Chegen yaro mai yaudalan tsiya”1

Ta ce kai dai ka kawo ka gani mana ” ya ce

” In dai zaka bani kan ka sai na baka mana”

Ciniki ya fada. Olu yayi abunda ya ga dama da Luba a shagonsa ya lalo kudinta ya bata ya ce

” kana ta min yanga ashe ma ba ni ne farko ba”

Ta linke kudinta ta cusa a bakin zani ta kada ma sa idanu ta ce1

” shege, dan akuya dan kasa da wutar jahannama!” Ta ranta ana kare.3

Da sakamakon jarabawarsu ya fito ta ci credit bakwai da pass biyu duk da dai duk jarabawar kusan satar amsa ce. Ta ci “maths” ta ci “English”don haka take doka tsalle ta ce da iya tamadi

” na ci jarabawata da a ce son samu ne da har jamia za ni”

Iya tamadi ta auna ma ta mugun kallo ta ce ” gaskia auta ba ki da hankali. Kina lissafa bana shekarunki ashirin da daya kuwa? Ba za kiyi tunanin aure ba? Ga su hafsi nan sun fitar da mazaje so kike ayi mana dariya ace kin yi kwantai?”

Luba tayi dariya mai isarta ta ce

” yo ka ji iyannan wallahi. Na gaya miki ki daina hada ni da wasu kucakai can su hafsi..ai wannan har mazaje ne suka fitar? Ni fa har yanzu babu wanda ya kwanta min”

Iya ta ce ” uwar ruwan ido, ina wanda ya zo ranar har ya bani kudi? dan gayu mai sabon babur..billahillazi kar ki wuce shi”2

Luba ta kada baki ta ce

” tun yaushe na ba shi jan kati . Ke kin ga ni fa makarantar aikin koya jinya ma za ni, in zama nas”

haushi ya kama Iya ta ce a fusace

” to ke da ubanki!!Dan jiya a tsakar gida ya ce Alhajin kyalli zai bawa ke.”

Luba ta wani ja da baya cikin gatsina ta ce1

” ka ji baban nan da kankanba. Bai san ci na ba balle sha na sai lokacin aure na ne ya san zai bawa Alhajin kyalli? Kuma na gayawa Alhajin kan sa tun farko kar ya nemi babana don wadanda suka fi shi ma sun ganni sun bari. Iya ta ce

” gane min hanya wai makaho ya so tsegumi. Ai shi babanku wani iri ne wallahi. Ai kuwa shekaran jiya na gan shi da sabuwar shadda wacce Alhajin ya gwangwaje shi da ita. Ke dadin ki ma Alhajin akwai nera, ko banza kya ci”

Haushi ya rufe luba ta ce

” to in kin hadu da baban namu kawai ki gaya ma sa kar ya soma don ba lallai sha’anin yayi dadi ba”

STORY CONTINUES BELOW

Daga fadar haka ta ja lallausan bargonta tayi kwanciyarta abunta.

Luba na ganin abu kamar wasa aure dai yake nema ya tabbata da Alhajin kyalli. Gidan shi a bayan layinsu yake yana da mata uku da ‘ya’ya ashirin da bakwai ,da yawansu sun girme ta. Ya dade yana makahon son ta amma tayi kememe ta ki. A cewarta wai ya cika gajarta da baki kamar shuni, hakoransa jage jage saboda tsabar cin goro sannan leben baki sidik saboda tsabar zukar sigari.

Aka dunga tafka rigima, iya tamadi da take bayanta ta samfe saboda Alhaji yayi mata ruwan kudi. Wata zuciyar ta ce da ita ta gudu amma sai take ganin asarar hakan tunda ba ta da isasshen kudi a hannunta ,wahalar banza kawai za tayi.1

Wata zuciyar ta ce ta kale su su aura ma ta Alhajin da kan sa zai sako ta. Zuciyarta ta kissa ma ta , ta lallaba kamar ta yarda ta , ta samu ta warci abunda zaga warta a gidan ta ware tunda ko banza ya fi gidansu.

Alhaji yayi barin nerar da ya dade bai yi ba a wannan biki. Bangarenta daban komai ya siya ya saka ma ta. Da bikin kuwa kowa ya sha gorin iya tamadi, auta tayi goshi mutan gida ta hana su sakat da sakin maganganu .

Abinda ba ta sani ba shi ne baya fa ta haihu domin a daren farkon Alhaji da Luba ya diro daga kan gado tulun cikinsa na rinjayarsa ya narko wani ashar tun na zamanin maguzawa ya aikawa Luba ya ce2

” dama ke yar iska ce? Yawon titi ki ka gama shi ne za a lullube ni a bani ragowar bakin kwalbati?”

Luba na daga kwance ko motsawa bata yi ba hankali kwance tayi sakaka da baki abinda ya zame ma ta dabi’a ta ce

“haba? “

cikin tsananin rainin hankali ta kara da

” ni fa ba na son sharri irin na tsofaffin najadu”.1

Ya ware ‘yan yatsunsa duka goman ya aika ma ta da daquwa ya ce

” ubanki shi ne zai miki sharri ba ni ba! Ni zaku ninke a baibai? Ke da matsiyacin ubanki ku lullube ku cuce ni. To ai kuwa cikin daren nan ba sai gobe da safe ba za ki koma inda kika fito”.

Tayi zumbur ta tashi ta ce

” A’a Alhaji..zagi ubana in ka so amma kar ka sake ka hada da ni don baka cikin ‘yan kayana”.4

Ya bude baki cikin tsananin mamakin yarinyar da tsaurin idon. ta ya ce

” ke ni ki ke gayawa haka? To na haifi kamarki”

tayi caraf ta ce

” tsohon banza ka san ka haifi kamata ka aure ni? Kuma don zalunci ka zo zaka bini da sharri ni dana san budurwa sabuwa fil na zo a leda?” Sai ta fashe da kuka.

Takaicinta ya kama Alhaji ya shaka sosai kawai sai ya ware ‘yatsunsa ya tsinka ma ta mari! bai kuwa mayar da hannu ba Luba ta damki murfin mai ros din ta da aka ma ta jere ta wurgi Alhaji ta kuma same shi a daidai tsakiyar goshi ji ka ke ..kwam! Sai ga jini na malala.9

Cikin azama irin ta maza Alhaji ya ziro hannu ya shako ta ‘yar tazugensa da bai kulle ba ta tade shi ya fadi rikica!

Luba ta tsallake shi ta shiga bandaki ta kulle abunta bayan ta bar shi jina jina. Ya daure ya mike hannu rike da goshi yana aunowa ita da iyayenta zagi kwando kwando.Har ya gaji don kan sa ya nufi sashen sa don samowa kai taimakon gaggawa,da niyyar gobe iyayen luba ko da tsumburbura suke tsafi ba abunda zai hana ya daure su.

Bai kuwa kwanta ranar ba sai da ya rubuta ma ta saki uku ras!5

Alhaji bai yi awa da fita ba luba ta zari karamar akwatinta ta cusa tsadaddun kaya da Alhaji ya saya ma ta da kudaden da yayi ta barnatar ma ta , ta sulale ta gudu abunta. Ba ta je ko’ina ba sai gidan Ilu -Ilu wani dadden saurayinta dan kano to legas

Shago gare shi na sayar da atamfofi na legas a kasuwar kwari don haka garin legas ba bakonsa ba ne. Tun kafin luba tayi aure ya dunga zugata su gudu zuwa legas ta ki saboda rashin isasshen kudi. Yanzu da ta je wurinsa dama zani ce ta tadda mu je mu kawai sai suka tafi abunsu.1

STORY CONTINUES BELOW

A can gida kuwa neman duniya an yi ba a gan ta ba, Alhaji bayi wata wata ba ya daure Baban yara. Rigima ta ki ci ta ki cinyewa Iya tamadi tayi kuka har ta gode Allah. Da kyar manyan unguwa suka sa baki aka saki Baban yara damma fa Alhaji ya dage sai an biyashi komai.

A Ikko luba ta kara gogewa da wayewa sai ta ga ashe ma ba komai take yi a kano ba? Ilu ilu bai yi wani zurfin karatun boko ba amma dan gaye ne daidai da zamaninsa, don haka duk wani club club na casu sai da ya kutsa da Luba. Wani daki ne suke zaune a unguwar obalande na wani abokin ilu ilun da ya tafi aiki makurdi suke sheke ayarsu.2

A tunanin ilu ilu da shi kadai luba ke ta’ammali amma a rashin saninsa ta riga ta hango wadanda suka fi shi komai! A cikinsu babu gwaninta irin wani Dpo na wata police station da ke unguwarsu. A lokuta da dama idan ilu ilun ba ya nan yakan dauketa su je “bar beach” inda kan luba ya fara fasuwa. Duk yawonta iyakacinta kano sai a legas ta lura ashe iskanci suna ya tara?

Ta ga mata na yawo daga su sai “pant” da “bra” . Kan luba ya daure, ashe ita bata waye ba? Ashe ita yar kauye ce? Ashe ana irin wannan rayuwar a gida Najeriya amma ta nade kan ta a garin Kano kamar kifin rijiya. Son duniya da jin dadinta suka rinka dibanta ta ji ina ma ta cinye rayuwarta a garin legas. Dpo ya bala’in shagwaba ta ya dunga kashe ma ta kudi kamar ba gobe.4

Watansu hudu cur da zuwa legas Luba ta fita fit a ran Ilu ilu. Shi lokacin ma hangen wata yarinya Bianca yake. Bai yi kasa a gwiwa ba ya tunkari Luba kan sa tsaye da batun ta bar masa daki dan zai kawo sabuwar yarinyarsa. Kan Luba ya kulle ta tsaya tana yiwa ilu ilu kallon tsananin mamaki . Idan ita ba ta ce za ta rabu da shi ba, har shi ne zai koreta saboda wata basamudiya can!4

Ta karewa dakin kallo ta ga yawancin abubuwan ciki ma ita ta saya da kudinta. Yana gama fadin abinda zai fada ya wuce bandakin tsakar gida yana fito ya fara wanka. Takaici ya kule ta har ta raya ma ranta za ta nunawa Ilu ilu ta fi shi bariki. Ta tattara abun da take so ta sa a yar jaka da kudadenta. Kawai sai ta cinnawa dakin wuta ta gudu abunta. Ba ta zarce koina ba sai gidan hutawar DPO.9

Da kyar Ilu ilu ya sha da taimakon makwabta da suka kawo caffa har wutar nan aka samu ta mutu. Hakan ne ya sa ya baza mutanensa neman Luba ko a ita ko a shi. A rashin saninsa Luba na boye cikin gidan shakatawar DPO tana sha’aninta. Washegari kuwa ya sai ma ta tikitin jirgi zuwa kano yace idan bincike ya lafa zai biyo baya.5

Gaban Luba ba ko dar ta shiga unguwarsu ta Birget ta kuma nufi hanyar gidansu da matsattsen siket din ta da daurinta mai tocila. Baban yara ya hau kanta yake jibga kamar an aiko shi ya ce sai dai ta bar ma sa gida, Luba ko gezau.4

Da kyar aka kwace ta ta shiga dakin uwarta ta yi mata gashin ruwan zafi. Washegari ta danka wa yayanta Iro wasu ‘yan kudade a cikin wanda DPO ya sallameta da su ta ce ya siyo wa Baban yara yadudduka da takalmi sau ciki. Ba ta tsaya anan ba ta bayar aka siyo kayan abinci kala kala aka rabawa kowa. Tun ana jin daga muryar baban yara sai kuma aka ji tsit!4

Iya Tamadi tun tana korafin ta tozartata da ta ga irin kudaden da ta zo da su kuma take kashewa yan gida sai tayi kus, kar ta ja zancen ya zamana ba rabonta.1

Duk yawan kudi idan dai ba kara nemansu ake ba to zasu kare, haka ce ta faru ga Luba. Anan sai ta fara tunanin mafita ta ga dai wannan zama haka ba zai fissheta ba.2

Kwatsam rannan sai ga Hajiya ‘yar sakkwato wata aminiyar iya tamadi da suka yi ‘yanmatantaka tare. Hajiyar ta dade a Saudiyya don tun lokacin da aka ma ta auren fari ta kaso auren ta gudu can. Ta kawo ziyara gida Najeriya ne sai ta biyo gidan iya tamadi a sada zumunta.

Daga zuwanta kuwa tayi ido biyu da Luba ta ce

” Tamadi shin ina kin ka samo wagga budurwa tsaleliya?”

Iya tamadi tayi dan murmushi ta ce

“Diyarki ce fa Lubabatu” .

Hajiyar tayi salati ta sanar da Ubangiji ta ce

” Luba ce tayi girma hakan ga? Hala ba ta kai ga aure ba?

Iya Tamadi ta kwashe labari kaf ta gaya ma ta. Ita kuwa Hajiya ta ji wani sanyi a ranta, hanyar neman kudi ta samu. Ta ce

“Ke mi ya kai ga damunki? Ai diya mace ita ajjari. Ki ban ita kawai mu tahi Saudiyya. Wallahi idan Allah ya bissheta ga sa’a kya sha mamakin arzikin da zata yo ga can”1

Iya Tamadi ta riki baki ta ce

“Saudiyya? Mu ina muka ga arzikin zuwa can muna fama da kan mu?”

Hajiyar ta murmusa ta ce

” Ke dai bammin wuka da nama hannuna ,ai ni yaruwa ni dauke ki. Lubabatu diya ta ta. Ke dai bari a ji ta bakinta in ta yadda sai mu tahi ayi ma ta fasfo da biza. Zuwa sati biyu sai in sayi tikiti mu tahi”.

Da aka tuntubi Luba da zancen dama zani ce ta tarda mu je mu, ta ce ta amince. Shi kuwa Baban yara ji yake Luba ta zame ma sa nauyi, tana jawo ma sa zagi a unguwa sai ya ji kamar ya rabu da kaya. Haka kwanaki suka cika aka gama shirye shirye Luba ta daga sai Saudiyya.So ai ruwan zuma ne, idan ka sha ka ba masoyi!5

Niamey, Niger Republic2

Rokaiyatou ta cigaba da kallon hanya yayin da take wasan kasa a kofar gidansu ta ga ta inda Momodou zai bullo ta ruga. Can ta ji an kwalla ma ta kira “Rokaiyatou”! daga kan da za ta yi sai ta hange shi ba ta yi wata wata ba ta fyalla gida a guje. Yarinya ce da ba za ta wuce shekara 8 ba jikinta ku san duk tsummokara. Ba ta yi wata wata ba ta fada bayan babarta ta kwakumeta ta ce7

” Momma, frère Momodou shiddawo ya tardoni ina wasan kasa”2

Uwar ta tunkude ta daga jikinta cikin hausarta ta zallar kananci ta ce

“Ke kaleni, ku je can ku karata”

Momodou ya shigo da riga “long sleeve” fara da shudin wando bayan sa goye da jaka irin ta yan makaranta, ya sa safa da kambos. Ya nufi bayan Momma ya janyota da kunne ya murda ya ce

“Mi na gani kina yi waje?”

Ta na ta jan kunnen kokarin yakicewa shi kuma ya kalli momma kamar me neman bayani ta dago daga tsintar shinkafar da take ta ce

” Rokaiyatou, K’…ai kadan ka gani..kamar mai aljanu..ai duka kawai zaka ma ta sai ta ji a jikinta”

Ya kura ma ta ido hawaye kwance male male a fuskarta, gashinta mai tsawo da yawa ya cukurkude ga kasa kamar an yi yaki. Kafafuwanta butu butu kamar tayi hakan rijiya. Sai kuma ya ji tausayinta ya kama shi da ga rigar jikinta yar yaloluwa da yawan wanki ya sa ta kode ta jeme. Abubuwa dayawa suka cigaba da yawo a kansa duk da karancin shekarunsa dan yanzu ma yake aji shida yana neman gama makaranta.

Ya janyota suka zauna akan tabarma yana kakkabe ma ta gashi ya ce

” kin yi abinci dai ko?”

Yana so ya ji ko ta ci abinci.

Ta girgiza kai ta ce

” yanzu dai Momma za ta dahwa”

Ya juya ya kalli shinkafar da ake tsinta ‘yar kut a faranti wacce ya san bai wuce a ci ta da mai ba. Ya bude jakarsa mai dauke da yar ” cooler” na abinci ta yan makaranta , dankali ne ko tabawa bai yi ba ya sa a gabanta. Ta fara ci da budu budun hannayenta ba tare da yace ta je ta wanko ba, ya cigaba da kallonta. Momma ta dube su tayi murmushi ta ce1

“Kai dai baka son cin abincinka, sai dai ka kawo wa kanwarka”

Murmushi yayi. Sai ya sa hannu ya zaro biskit da wani dan lemo ya ce

“Wannan kuma sai kinyi wanka, ba ki son wanka ko?”

Ba ta kula ba cin abinci kawai take. Ya kalli. Momma ya ce

” Ina ruwan da za tayi wanka?”

Ya kama haba tace

” Au har wani ruwan wanka zan ke ajiye ma ta? To sau nawa zan ajiye”?

Murmushi kawai yayi ya nannade hannun rigarsa ya doshi inda rijiya take. Ya jefa guga ya fara jan ruwa har ya cika wani dan karamin bokiti. Sai ya yafito yarinyar da hannu ya ce

” je ki dauko sabillo”2

Ta shiga daki ta dauko ya ce ta tsugunna ya fara wanke wannan kan na ta dikin dikin har sai da ya fita tas. Ya kalli Momma ya ce

” Dan Allah Momma ki kai ta bayi ki ma ta wanka”17

Ta yi murmushi ta mike tana cewa

“Tou momodou na Rokaiyatou ai idan ban taso ba ba zaka kaleni ba”

Ta zo ta karbe shi. Ya dauki jakar makarantarsa tana kallo ya zaro kudi ya cusa a karkashin farantin shinkafar nan yayi tafiyarsa ba tare da ya waiwayo ba. Ta gyada kai a hankali a cikin ran ta tana tunanin irin kaunar da momodou ke yi mu su sai ta raya a ranta ko dan Rukaiyatou jininsa ce? Ta kawar da wannan tana mai la’akari da cewar duk ‘yan gidan ma ai yanuwanta ne to amma wa ta ishi kallo? Momma ta cigaba da dirzar Rokaiyatou da sabulu ta na mai ayyanawa a ranta , ko ya rayuwa za ta yiwu ba Momodou?

Washegari da safe Rukaiyatou na tsaye a kofar kangon gidansu tana hangen wani tsararren bene mai bakin gate tana so ta ga fitowar frère. Gida ne tangameme wanda kallo daya za ka masa ka san an zubar da dukiya. Can aka bude tangamemen gate din motar da take kai yan makaranta ta fito. Tun daga nan ya fara kwalla ma sa kira tana daga ma sa hannu. Da ma ya san tana tsaye domin al’adarta ce yin hakan. Yana isowa zasu wuce shi ma ya daga ma ta hannu suna ta dariya.2

STORY CONTINUES BELOW

***********************

Iliyasou Tillaberi mahaifin Momodou yayane ga Ahmadou Tillaberi mahaifin Rukaiyatou. Wadanan yanuwa suna zaune ne a garin Niamey suna gudanar da kasuwancinsu. Tafi tafi sai suka bude kamfanin hadin gwiwa na sarrafa shinkafa , taliya, flour da mafi yawancin nau’in abinci. Kasuwancunsu ya bunkasa tsakanin Nigeria, Niger, togo , Mali , cameroon da senegal. Daga baya suka kafa babban kamfani da reshensa biyu Nigeria da Niger. Aka sa wa wannan kamfani suna I and A and sons.

Maganar irin tarin kudi da kadarori da suka mallaka wani abu ne da mai karatu zai sha mamaki. Kasuwanci ya karbe su , su ma kuma suna dagewa game da bunkasar arzikinsu. Iyayensu duka sun rasu sai baffaninsu da ke Tillaberi, wani karamin gari a yankin Niger.

Iliyasou wani irin murdadden mutum ne mai bakar zuciya. Ya fara da auren uwar Mommodou anan Niamey wata zabarmiya me suna Hajiya Khulsomou. Ta haifa masa ‘ya’ya biyar mata sai namiji daya wato Momodou. Sai kuma Allah ya jarabce shi da son wannan yaro.

Daga baya yayi aure a Nigeria da wata mai suna Hajiya Hadiza bakanuwa ce ya usul ta haifa masa da guda daya tal Al Mustapha. Wani irin tsananin kishi ke tsakanin wadannan mata biyu har ya zamana daya ba ta zuwa kasar da daya take. Amma me? Wani irin zumunci ke tsakanin Mustapha da Momodou da suke ku san sakwannin juna. Sun shaqu ta inda takanas daya kan bar kasar sa ya ziyarci daya duk da halin da iyayensu mata kan nuna na tsanar hakan.4

Ahmadou Tillaberi kafin ya hadu da mahaifiyar Rukaiyatou mai suna Ramlatu ‘yar kano yana da matan aure guda uku. Suk cikin matansa ba wacce ta taba ko batan wata. A matsayinsa na attajiri mai tarin dukiya zai so wataran in ya fadi ya zamo yana da magaji. To amma ya zai yi?

Wannan rashin haihuwa na Ahmadou yana yiwa Iliyasou dadi a rai duk tunaninsa bai wuce yau in ba ran kaninsa to komai ya zama na sa. Ana cikin hakan kwatsam rannan kasuwancinsu ya kai su kano duba wani sabon kanfani a lokacin. To anan ne fa ya ga wata kawar Hajiya Hadiza matar yayansa mai suna Ramlatu ya makale ma ta. Ba yanda Iliyasou bai yi ba akan ba ya so amma ya jajirce sai ya aureta.2

A sanin Iliyasou Ahmadou neman haihuwa yake, shi kuma ba ya fatan hakan dalilin da ya sa ya tsani auren kenen. A bangaren Ramlatu kuwa dama marainiya ce a hannun yayanta take, ta kafe ta tsare ta ce sai Ahmadou yayanta ya rantse ba zai ba wa wanda ba dan kasa ba. Aka dunga tafka rigima daga karshe yayan ya ce in dai ta yi auren nan to ba shi ba ita, ta ce ta amince. Aka yi aure Ahmadou ya tafi da amaryarsa Niamey.4

Tun Momma na amarya babu wani dan gidanta da ya wuce Momodou. Yaron na kaunarta ita ma haka. Hakan na kona ran Hajiya khulsomou a ganinta an zaqewa danta ga kuma karin abun kawar kishiyarta. Sai wata gaba ta kullu, sai gore gore na rashin haihuwa ganin cewa har a lokacin ita ma bata samu ciki ba. Ganin an yi shekaru Ramlatu ba ta samu ciki ba sai hankalin iliyasou ya kwanta su kuma kishiyoyinta suka hau ta da habaici. An auro ta daga Nigeria dan ta nuna musu iya haihuwa ashe duk kamwar ja ce.

Lokacin da Ramlatu ta samu ciki har ya fara fitowa sai fa hankalin kowa ya girgiza, sai aka fara kallon kallo. Ahmadou kamar zai yi hauka don murna. Nan fa kaunarta ta kara azalzakar zuciyarsa aka shiga tattalin ciki ana ririta shi. Sai kuma wani abun al’ajabi ya faru.

Al’amuran dukiya na Ahmadou suka fara ja baya. Duk a abunda ya taba sai ha zamo asara. Nan da nan fa yayansa da matansa suka fara nuna Ramlatu da cewar ita ke da farar kafa kuma wai zata haifa musu bala’i. Da aka haifi yarinya sai abubuwan suka kara tabarbarewa amma me? Shi bai wani damu ba farincikinsa kawai ya samu abun kauna Rukaiyatou. Ya so Rukaiyatou irin son da ake yiwa da guda daya tilo da yayi jinkirin zuwa. Sai matansa suka fara ganin haukarsu ta zama da shi ba abun duniya ba da ba jika..me zai zaunar da su? Sai suka watse abunsu suka bar shi da Ramlatu.

To amma yawa yawan kudadensa suna hannun Iliyasou na kanfanunnukan hadin gwiwa da suka bude. Zaman iliyasou babba sai ya zamana ya fi karfi akan dukiyar don haka sai ya tuntube shi da batun kudinsa. Sai ya nuna ma sa cewar ba fa zai iya fitar da komai ya sa a hannunsa ba hakan kamar ganganci ne yayi hakuri zai cigaba da juya musu. Ahmadou mutum ne mai hakuri sai ya jure hakan ya cigaba da juya dan abunda ke hannunsa.3

STORY CONTINUES BELOW

Tun haihuwar Rukaiyatou Momodou ya kalli Momma ya ce

” shikenen kin haihwa min mata, ni ina kamnar ta! “4

tayi dariya ta ce

“Allah Momodou? To inshallahu in ta girma kai ne mijin”

Sai ya kama tsalle irin na yara har ya tafi da gudu ya gayawa babarsa . Ita kuma ta ce a fusace

” Ba ka amren mayya, ita ta lashe dukiyar Ubanta!”7

Kamar abun almara, Rukaiyatou na da shekara biyu Ahmadou Tillaberi ya yanke jiki ya fadi a bayi ko shurawa bai yi ba. Ai tun daga nan sai fa nuni ya koma kan su, lallai Ramlatu da diyar ta sun tabbata mayu masu lashe dukiya da kurwa. Daga nan sai rayuwa ta musu kunci. Iliyasou ya rantse da cewar Ramlatu ce ta jefe shi da asiri ya fadi ya mutu don ta gudu da ragowar dukiyarsa, don haka sai ya hau kan dukiyar Ahmadou ya danne babu ma batun rabon gado. Da kyar aka samu ya basu wani kangon gida anan kusa da shi wancan tsararren gidan na su ya siyar ya ce shi zai rikewa marainiya dukiyarta.1

Momma tayi kuka ta gode Allah ganin yadda aka musu fin karfi ita da diyarta. To amma ina zata je? Wa zata gayawa? Babu. Yayanta da take da shi ma sun riga sun raba hanya, tun da tayi aure bai taba neman ta ba. Sai kawai tayi zamanta a wannan gidan take dinkin fata na takalmi da jaka take kaiwa kasuwa suke cin abinci.3

Iliyasou ya watsar da su ya ma manta da wasu iyalan Ahmadou. Baffaninsu sun sa baki ya samu ko diyar ce ya kula da ita amma ya shashantar da batun. Wani irin mulki na zallar zalunci yake gwada musu da asalin fin karfi.1

Momodou yaro ne amma ya taso da tsanar wannan dabi’a ta mahaifinsa yana matukar jin takaicin hakan. Mahaifin ya kwallafa rai akan sa a matsayinsa na babban dan sa namiji hakan ya sa tun yana karami ya fara dora shi akan harkar kasuwanci. Shi kuma sai ya taso da kauna da tausayi na wadan nan bayin Allah ta yanda duk abunda ya samu to nasu ne.

A shekarun girman Rukaiyatou ta taso ba ta shaku da kowa ba sama da yayanta frère, wannan shakuwar da ko iliyasou Tillaberi ya gaza rabawa. Al’adarta ce kullum ta tsaya a hanya ta ma sa bye bye idan za shi makaranta ba don ita tana zuwa ba.1

Ganin hakan ne yau ya ga bai gan ta ba sai ya shiga gidan don a zatonsa ko ba lafiya ba. Da shigarsa ya tarda ta tana wasan ruwa, shigowarsa tayi fatali da ruwan ta ruga daki. Momma ta fito daga wajen wani kewayayyen langa langa inda take tukin tuwo tana share hannayenta a jikin kodadden zaninta. Tayi murmushi ta ce

“Mutuniyarka ta gudu ko”?

Ya mayar ma ta da murmushin sannan ya ce bayan sun gaisa

“Na ji ta shiru bana ganinta a waje, nayi zaton ko bata da lahiya ne, lahiyarta lahiya?”

Ta kwalla mata kira, ta zo tana rabe rabe. Ya zaunar da ita kan tabarma ya ce

” Me ya hwaru ba na ganinki waje da sahe?”

Cikin kasa kasa da murya ta ce

” Ba kowa yana zawwa L’ècole amma ban da ni ba”8

Yayi shiru kamar mai nazari sai can ya ce

” kina son zuwa L’ècole ko?”

Ta gyada kai. Ya ce

” Ba ina zuwa ina koya miki ba har kin ka iya karatu ba?” Ta ce

” Ai naka ba irin na L’ècole ba ne, ba a sa kayan L’ècole” ya ce

” To shikenen kamnata, in dai ina raye sai kin je kin ji ko?2

Ta fara tsalle. Ya fito da wasu yan kudi a hannu ya manna mata yana dariya.

Duk abinda suke Momma na kallonsu. Ya mike zai tafi ta kira shi cikin damuwa ta ce

” Kana dan makaranta ka ke wa wani alkawarin sa shi a makaranta?”

Ya sosa keya yace

STORY CONTINUES BELOW

” jiya ne fa muka gama gwajinmu na karshe sai jiran sakamako kawai”

Ta ce

” Alhamdulillahi, dana ya girma. Amma ina fatan ba mahaifinka zaka gayawa ba, ka san bana son kuna samun matsala akan Rukaiyatou”

Shiru yayi na wasu dakiku sannan ya ce

“Kar fa ki sa komai a ran ki Momma na san yanda za a yi na samu kudi. Ba ki san yanzun haka Abba ya bude min shago a Grand Marchè ba? Nan zan ke zuwa kafin sakamakon gwajin mu ya fito. Babana ke da alhakin kula da ita kuma ya ki. Wallahi idan ki ka ga ban kula da Rokaiyatou ba, to ba yadda naka iyawa”.

Kwallar cikin idon Momma ta tsiyayyo. Yau ta ga bakar tukunya mai fidda farin tuwo!2

Kawar da kai yayi..ya fita da sauri. Ta cigaba da kuka a hankali ranta ya kasa ayyana ma ta irin kaunar da momodou ke musu. A hankali ta ce

“Ba mu da tamkar ka Momodou, ba mu da!”

Abu kamar wasa sai Rukaiyatou ta fara zuwa makaranta. Abinda ba su sani ba shi ne shagon da aka budewa wa Momodou to duk ribar ranar a karatun Rukaiyatou yake karewa. A lokacin shekarunsa ba za su wuce ashirin ba, amma zurfin tunaninsa da hankalinsa ya fi na dan shekara talatin. Hakan ne ma yasa uban ya dada jan sa a jiki da nuna ma sa harkokin kasuwanci dan ya ji a ran sa shi zai gaje shi.

Daga nan ya shiga Universite Abdou Moumouni de Niamey ya fara karanta harkar kasuwanci kamar yanda mahaifinsa ya ke so. Lokacin da ya gama a sannan ne Rukaiyatou ta gama ta gama karatun primary da aka sa ta daga aji uku har ta fara zuwa wata makarantar sakandare ta yanmata je ka ka dawo.

A mafarkin Rukaiyatou ba ta da kamar Momodou kuma shi zata aura idan sun girma. Kuma shi zai sa ta a universete tayi karatun aikin jarida. A lokacin ne kuma Iliyasou Tillaberi ya ke son aika Momoudou kasar faransa domin ya je yayi digiri na biyu a harkar kasuwanci. Wannan wani tsari ne da bai so saboda tunanin wa zai bar wa su Rukaiyatou?

Dan haka sai ya fara zamewa batun3

A irin haka ne ya shiga gida wajen mahaifiyarsa Hajiya Khulsomou ta kira shi ta ce

” Yo kai bakka kishin kan ka ko? Ba zaka tahi karatun kirki ba ka tsaya anan kamar marar gata. Ka hi son ubanka ya dora sobanka Mustapha ko?”

Har yau ya kasa gane irin kishin da babarsa take da Mustapha. Ba ma haka ba kowa a duniya abokin kishi ne a wurin mahaifiyarsa. Ba a gari daya ba , ba kasa daya ba amma ta uzzura ma ranta. Ga shi ita Hajiya hadiza ba ta ma cika nuna masa tsangwama ba. Kai tsaye a faransan sa ba wata rufa rufa ya ce3

” Ai na hwadi miki, ban iya tahia na kyale Rukaiyatou”

Ta kalle shi a tsanake, maganar da ya fada ta taba ta ba dan kadan ba don haka sai ta kalle shi ta ce a tsaurare

” Idan ma son ta ka ke, ba ka amrenta..in ni da ubanka muna da rai baka aurenta!”

Wani abu ne ya ji ya gifta ta gabansa mai tsananin duhu saboda bacin rai. Duk duniya bai ga mai hana ma sa aurenta ba, abinda ya ayyana a ran sa kenen.

Da daren ranar ne yana zaune a gaban Momma tana dinkin takalmi da taimakon fitilar aci bal bal. Suna hira kamar yadda suka saba, Rukaiyatou na kishingida can gefe akan tabarma. Yanzu ta fara zama yar budurwa ta rage halayenta na kiriniya ta ce

“Frere ka ci tuwo in zubo maka? Ni na dahwa”

Sai ya fara dariya ya ce

” yanzun yar dul da ke anan har kin iya dahwa tuwo”?

Ta ce

” Ai na dan iya saboda Momma ta ce kana son tuwo in mun yi amre sai in dunga tuka maka ko?”2

Ya rasa wannan hali na ta na rashin jin kunya ga Momma a zaune. Ya yi sauri ya ce

” Ni na ce miki zan amre ki”?

Ta dago kai cike da mamaki har ga Allah ta ce

“Ba Momma ta ce Kai a mijina ba? Wai tun ina zanin goyi ta ba ka ni?”

Haushi ya sa Momma ta mako ta ta na cewa

” uwar surutu”

Cikin basarwa ya ce dauko takardunki na Lecole mu gani ko kina kokari. Ta dauko ya duba ya gyara ma ta wasu abubuwan. Yayi shirin tafiya Momma ta ce

” zo nan in tambayeka”

” ya ba ka tafi ba”?

Ya ce

“In tafi? Rukaiyatou fa? Wa ke gareta”?

Ta nisa a hankali ta ajiye dinkin takalmi ta kalle shi a hasken fitilar aci bal bal ta ce

” A kan ta sai ka fasa karatu? Ai muna hannun Allah ko? baka yarda da ikon Allah ba? Da ba dan ikonsa ba da taimakon ka zamu kai yanzu? Ka je kayi karatunka ka ji”

Shiru yayi, ba mai yawan magana ba ne. Abinda ba ta sani ba shi ne shi ya san babansa na son tura shi faransa ne dan yayi nesa da su. Ya san tsarin uban ,ya gaya ma sa ya je ya karo karatu a can sannan nan ya zame ma sa ido akan wani karamin kamfani da yake son budewa a can. Har wani tsawon lokaci hakan zai dauka? Amma kuma shi kan sa ya san ba shi da zabi.

Sai yayi murmushi har ya taba rashin kunyar ya ce

“Bari na je na dawo ko Momma? Kafin nan na yi kudi sai na zo na amri kamnata” iyaka gaskiyarsa kenen bai kuma iya boyewa ba. Momma kamar wata abokiyar shawara ya maida ita tun tasowarsa.2

Ta tsaya tana duban yaron, har yanzu da yarinta a jikinsa amma duk tsarinsa na su ne. Tayi ma sa kallon nutsuwa ta ce

“Rukaiyatou dai! Rukaiyatou dai! Akwai wani shirinka na duniya da babu ita? Wanene ya ce sai kayi kudi zaka aureta?” Ta girgiza ma sa kai tana ma sa kallo irin na uwa sannan ta ce

“Ko ba ka da ko dala ni zan baka Rukaiyatou”!!

“Momodou ka tafi kamar yau ne zaka je ka dawo” cewar Momma

Ya gyada kai a hankali. Ya yiwa Rukaiyatou inkiya da ta biyo shi daga gani wani abun zai ba ta. Ta bi shi a baya. Momma ta kare musu kallo tayi murmushi ta ce

“So, ruwan zuma”

About AIS

Check Also

MAI TAFIYA CHAPTER 5

MAI TAFIYA CHAPTER 5                  Www.bankinhausanovels.com.ng  Son kasancewarmu …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *