JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 3 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI

JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 3 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI

                Www.bankinhausanovels.com.ng 

tana zuwa ta sare sarkokin da suke jikinsa ta dora shi
akan wani ingaraman doki lokaci guda tayi masa kaimi
suka nausa cikin daji a guje kamar fitar kibiya daga
kwari.
Ganin haka ya sa sarki mazwan ya dakawa
dakarunsa tsawa da zumar su bi bayansu su kamo su,
nan mahaya doki suka hau suka rufa musu baya
amman sun makara domin tuni Hasma tayi nisa a cikin
daji.
Haka suka yi ta yawon nemanta, amma basu
samu ikon ganinta ba, suka koma cikin tsananin
fargaba na tunanin abinda za su fadawa sarki mazwan
saboda sun san halinsa na bakin zallunci.
A haka suka koma suka same shi yana tsaye
a kofar shiga birnin Hindu fuskarsa tayi baki kamar an
sassako daga itace ransa ya yi matukar baci, tunda
suke basu taba ganin fushi irin na yau a fuskar sarki
mazwan ba. Hakan ya saka tun daga nan suka soma
fargabar abinda zai faru. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ina fatan kun saro min kawunansu sannan
kuka dawo? Suka yi shiru suna kallon juna ganin
haka yasa ya zare takobi cikin fushi ya yi kansu da
sara da suka sai daya ga babu ko guda daya da yake
numfashi a cikinsu sannan ya kwarara wani uban ihu
da ilahirin birnin Hindu sai daya amsa.
Ya yi saurin komawa cikin birnin ransa a
matukar bace, yana shiga cikin gidan sarauta a lokacin
Bokan shi ya bayyana a gare shi sarki mazwan ya
tsaya yana kallonsa cikin tsananin bacin rai.
Da wane bayani ka zo min? Bokan ya
dubeshi ya yi shiru yana nazarin fuskar sarki mazwan
sannan yace masa.
Babu dama na
gyara maka wannan da
yankaken kunnen da aka yanke tunda saran da
tsafaffiyar takobinka aka yi maka, ka kuma san duk
abinda aka sara da ita yake kasancewa Ya yi shiru
yana nazarin fuskar sa sannan ya ci gaba da magana.
“Babu shakka ya zama dole ka saka sarkin
yaki da mayaka su bi su a baya zuwa birnin nur yanzu


suna daf da shiga cikin wani kauye da ake kira da
Yadama shi wannan kauyen yana karkashin ikon sarki
Nur kuma babu shakka idan suka karasa birnin nur to
sarki lambu na kasar nur zai mallaki tsafafiyar
takobinka idan kuma ya mallaka zai iya cinka da yaki
ya rusa birnin nan.
Sanin kanka ne tun tsawon zamani akwai
gagarumar gaba a tsakaninku da sarki lambu kuma
babu abinda yake fargaba a game da kai sai wannan
tsafafiyar takobin, idan har ya mallaketa to kasar
Hindu tana cikin wani hali na kunci da tashin hankali
kuma mulkinka yana gaf da zuwa karshe” Wannan
maganar da Boka ya fada masa ba karamin daga masa
hankali ta yi ba. Www.bankinhausanovels.com.ng
Mene mafita? Boka ya kalli yankaken
kunnen sarki mazwan ya yi murmushi sannan yace
masa.
Rashin sani ya fi dare duhu, shi yasa suka
yaki wannan macen don lokacin ina cikin halwa ta
tsafi kuma babu ikon na tashi amman dana hana ku yin
wannan fafatarwa saboda tana da wani sirri da babu
wanda yake da ikon cin nasara akanta idan ya yaketa.
Ita kadai da kake gani zata iya karar da
dakarun Birnin Hindu ta kuma rushe duka ganuwar
garin. Wannan matar da kake ganinta Macen sirri ce,
wani boka daya shahara a duniyar bokanci shi ne ya
kirkireta, kana tsamanin mutum ce kamar mu?
Amman ba haka bane Wannan maganar ta boka ba
karamin daure kan sarki mazwan ta yi ba.
“Kamar ya ya macen sirri?
Wannan macen da kake gani kamar yadda
na soma fada maka kuma ka ganta kyakkyawar gaske,
matace ta wani mashahurin boka wanda ya hardace
kalaman sirikan tsafi guda miliyan dari duk duniya
babu boka kamarsa. Yana da mace guda daya wacce
duk duniya babu abinda yake so sama da ita, sun dauki
tsawon lokaci suna soyayya, kwatsam sai aka wayi
gari matar tashi ta kamu da ciwon ajali har ta mutu, ya
wanzu tsawon lokaci yana kukan bakin ciki, haka ya
wanzu tsawon lokaci ba ci ba sha saboda bakin ciki da
begen matarsa kullum yana zaune a gefen kushewarta
yana kallon kushewar cikin tsananin bege na soyayya
da kaunarta.
Haka ya wanzu tsawon lokaci yana zaune a
gefen kabarinta. bayan shekara uku yana cikin wannan
halin na zama a gefen kushewar duk yabi ya lalace ya
rame ya kanjame ya koma kamar ba mutum ba saboda
idan ka ganshi sai ya baka tsoro.
A rana daya cika shekara uku yana wannan
zama sai ya tashi daga wajen kabarin nata a wannan
lokacin sulasainin dare ya soma shiga kai tsaye ya
shiga cikin dakin tsafinsa ya zauna akan buzun tsafi
zuwa wani lokaci sannan ya tashi daga wajen da yake
ya soma dauko wasu robobi masu kama da kirgi yana
hadasu waje daya. Www.bankinhausanovels.com.ng
Bayan sa’a shida sai gashi ya harhada gabai
na dan adam ya ci gaba da hada roba sashe zuwa sashe
kafin wani lokaci ya hada surar matarshi da wannan
roba bayan ya kammala ya zuba mata idanu yana
kallonta, sak matarshi babu abinda ya rabasu kamar an
tsaga kara sai dai wannan bata motsi.
Kuma ta rob ace aka hadata bata da jini taba
da kashi, haka kuma shima yasan bashi:da ikon busa
mata rai ta tashi tayi motsi, a zaman daya yi a gefen
kushewarta matarsa, yana cikin halwa ne na son gano
har
yadda zai busawwa wannan sundukın ra amman har
shekara ukun bai gano ba.
Abinda ya gano a cikin halwarsa duk abinda
yake so ba zai samu ba, mafita daya ce idan yana son
ta motsa, sai dai ya samo wata budurwa macen aljanu
ya sakata a cikin jikin robar mai sifar matarsa sai ta
rika motsawa.
Wannan abin daya gani shi yasa ya zauna
yin halwa tsafi har sai daya nemo budurwa Aljana
mafi kyawu a cikin yankin aljanu ya kamota ya sata a
cikin butar tsafi ya dauki butar tsafin ya saka a jikin
wannan gangar jikin roba. Da wannan ya tashi gangar
jikin ya zama tana iya motsi tana iya tafiya tana iya
magana.
Ganin wannan nasarar daya samu ya saka
ya dauki sirrin tsafi dubu dari tara ya saka a cikin
jikinta, ya kuma saka mata karfin sadaukai dubu ya
saka mata hikima da balaga ta magana, wannan ita ce
irinta ta farko da wani boka a duniya ya kirkira kuma
mafi hatsari a duniya.
Duk lokacin daya so ita kadai yake turawa
wani gari taje ta yaki duk girman daular daya ga dama,
haka kuma idan ta saka dakaru a gaba bata gajiya tana
Iya yin shekara guda tana yaki bata gajiya ba, tunda ita
bata ci bata sha bata da wani aiki sai yin biyayya ga
boka, idan aka koma fanin tsafi idan tana fadar
kalaman tsafi sai ka yi tsamanin duk duniya babu
kamarta, hatta a wannan zamanin banda ni babu wanda
ya kaita sanin sirrin bokanci, wannan fafatawar da
kuka yi don na baiwa kasar nan kariya na tsafi shi yasa
bata yake ku kuma tayi galaba akan ku ba, amman ba
don haka babu shakka da kaga azaba irin wacce baka
taba ganin irinta ba” Ya yi shiru yana kallonsa.
Sarki mazwan ya yi shiru yana kallonsa
Boka marmasi ya saukar da ajiyar zuciya ya kara cewa
da shi. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Yanzu ya kake ganin za a yi yadda za mu
kara mallakar takobinmu data karba kuma ka sanar da
ni cewar kar na sake takai birnin Nur saboda sarki
Lambo zai iya mallakar wannan takobin tawa Boka
marmasi ya bushe da wata dariya sannan ya dafa
kafadar sarki mazwan yace masa.
Naga hankalinka ya tashi ka kwantar da
hankalinka bisa wannan bukatar da ka zo min da ita,
don haka zan aika sako gareta bisa tafarkin tsafi kuma
zan dawo maka da takobin taka domin na faranta maka
rai jin wannan kalamin ba karamin faranta ransa ya yi
ban nan take fuskarsa ta washe zuwa ga murmushi.
Daga nan suka yi sallama Boka marmasi ya
bace daga cikin gidan sarautar.
*******
Lokacin da su macen sirri suka nausa suka
shiga cikin daji tana kan ingaraman: dokin data hau
ganin tafiyar bata yi musu sauri sai ta tsayar da dokin
ta dauki sham ta saba akan kafada ta ruga da gudu,
kamar wacce take gudu akan iska kafin wani lokaci ta
yi nisa da birnin Hindu.
Wannan karon kana ganin fuskarta kasan
ranta a matukar bace yake, saboda babu anuri ko farin
ciki hakan ya faru ne saboda ganin irin raunin da sarki
mazwan ya yi wa sham. Tasan sham sadauki ne wanda
baya tsoro ko fargaba, amman sarki mazwan ya
shamace shi ya kafta masa sara wanda tun sanda aka yi
masa bai kuma motsawa ba.
Hakan yana nuni cewar akwai sirrin tsafi a
tattare da takobin, don haka ta kara azama ta shiga
cikin dajin a lokacin ta karasa wani waje mai yawan
rairayi da kuma ruwa mai kyau yana gudana a wata
Korama gefe guda kuma ga wasu ‘ya ‘yan itatuwa jere
reres gwanin ban sha’ awa.
Tana karasawa ta samu waje ta ajiye shi
akan rairayi mai sanyi ta zauna tana kallonsa, har zuwa
lokacin banda idanu babu abinda yake juyawa nan take
tausayinsa ya kamata ta mike ta komo kansa ta tsaya
tana kallonsa da idanunta masu haske fari kal.
Zuwa wani lokaci ta soma karanto wasu
dalasimai na tsafi kala-kala take abubuwa suka
bayyana garai-garai gareta cikin gaggawa ta bude
idanunta daga rufewar data yi takai dubanta zuwa ga
wajen da yake ga mamakinta babu shi sama ko Rasa.
Ta juya ta kuma Juyawa ta duba ko zata ga
wata alama da zata nuna mata sawun wani abu amma
sam babu wata alama, wane wannan ya aikata wannan
zunibin gareta? Tabbas ko wane sai ta azabtar da shi
da irin azaba irin ta yaki, nan take ta takarkare ta
kumarma ihu wanda sai daya saka duwatsun da suke
cikin dajin amsawa. Tsuntsaye da suke bakin ruwan
suka bazama suka tashi sama, igiyar ruwa ta somna
ambaliya kafin kace kwabo tuni launin wajen ya sauya
saboda wannan ihun da macen sirri ta kurma.
Idanunta suka kada suka yi ja, saboda
tsananin fusata da tayi kamanita suka sauya daga
kyakkyawar mace zuwa wata kalar ta daban. Lokaci
guda ta soma nazari akan abinda ya shafí babi na
tsafinta kafin wani lokaci duk wani abu daya faru ya
bayana a gareta. A gaba da wajen da yake nesa kadann
akwai wasu arnan daji da suka kasance suna bauta ga
wani dodon gunki da suka sassaka shi daga itace.
Wannan abin bautar na su ya kasance suna yi masa
hadaya duk karshen wata da jinin bakon matafiyi
wanda hanya ta biyo dashi, hakan ya saka suka kafa
wajen wannan korama a matsayın tarko da suke kama
baki. Www.bankinhausanovels.com.ng
Hakan ya saka suka sace sham suka nufi
birin nasu na arnan daji domin yau kwana uku kenan
ba su samu wanda za su yi hadaya da shi ba, wannan
birnin ya kasance shi ne kusa da birnin Hindu kuma
shekara da shekaru babu basa ga maciji da masarautar
birnin Hindu, wannan gabar ya saka jama’ ar birnin
Hindu basa iya shiga cikin dajin yin farauta ko kuma
yin itace domin gudun gamuwa da tarkon arnan daji.
Sarki mazwan yana sha’awar fita farauta
amman saboda bakar gabar dake tsakaninsu hakan ya
saka ya hakura, ya aika kashen da suke kusa da su aka
sayo masa duk wani nau ika na dabbobin daji ya zuba a

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 1 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI

JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 1 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI Www.bankinhausanovels.com.ng  JARUMI DAN BAIWAYaro ne …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *