JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 2 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI

JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 2 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

kowa yana gudin karya gofama kanshi
shima ya gamu da fushin sarki.
Shi kuma jariri salhim tun yana kuka da
karfi murya har murya shi ta soma dashewa amma an rasa
wani mai tausayin da zai shiga cikin konannen
gidan ya dauko shi har sai da dare ya soma kowa ya
watse sannan wata tsohuwar almajira ta yi ta maza ta
fada cikin gidan ta dauko jaririn salhim tabi duhun.
dare ta gudu da shi.
Daga wannan rana almajirar taci gaba da
rainonsa tana bashi madara shanu tunda ita ta tsufa ba
zata iya shayar da shi ba, wata rana haka zata yini tana
bara kafin ta samu dan abinda zata sayawa jariri
salhim madarar shanu da zata bashi.
Don haka yasha yini da yinwa tun yana Www.bankinhausanovels.com.ng
jariri haka zai ta tsotsar hannu idan yana jin yunwa
yana jikinta suna zagaya kasuwa suna yin bara, wani
wajen a basu hakuri wani wajen kuma zagi da bakar
magana saboda yanda suma jama’ar Hindu talauci ya
yi musu katutu, ya saba yini da yinwa amma bai taba
galabaita ba.


Rayuwar wannan yaron tana baiwa wannan
tsohuwar almajirar mamaki yanda yaron yake da juriya
da jarumtaka tun yana karamin yaro, hakan yasa take
iyakacin kokarinta don ganin ta samu abinda zata ciyar
da shi.
Wannan mulkin zallunci da tauye hakki da
ake yi a kasar Hindu yana damun kowa
sai sun kawo karshen rayuwarka, don haka jama’a
suna cikin bakin talauci da rashin tabbas na rayuwa.
Wannan dalilin yasa koda ta sha wahala
wajen yin bara bata samu ba bata damuwva saboda
tasan halin da jama’a suke ciki suma suna cikin halin
fatara da talauci a kasar.
Haka dai almajira Harsum taci gaba da
renon salhim har ya tasa ya zama dan shekara hudu.
Ta shaku sosai dashi tana masifar son shi a iya zaman
su bai taba kawowa ba ita ce ta haife shi ba. A yanzu
ko bara zata fita tare da salhim suke fita, tun yana
karami ya iya bara kuma yasan cewa uwarsa bata da
wata sana’a data wuce bara amman wajen da matsala
take mutanen kasar Hindu suna fama da tsananın
talauci na mulkin azzalumin sarki Mazwan.
Duk abinci gona da mutum ya noma a kasar
to kaso biyu cikin uku na sarki ne kuma duk da haka
ma sai ka biya haraji mai tsoka duk karshen wata
guda. Kai bama dan gari ba hatta bako idan hanya ta
biyo da shi ya zo giftawa ta kusa da birnin Hindu sai
an tsare shi ya biya harajin sarki idan kuma yaki biya
sai a kama shi da karfin tsiya a maida shi bawan sarki
kuma idan yana da mace da sauran dukiya duk sun
zama na sarki Mazwan. Www.bankinhausanovels.com.ng
Idan kuma ya yi wa sarki wata bakar
magana take za a yanke masa hukunci kisa za a buga
yanke masa hukunci daurin rai da rai a gidan maza.
Don haka a tarihin masarautar Hindu tunda
aka kafata, ake yin sarakuna tsawon dubunan shekaru
ba a taba yin azzalumin sarki kamar mazZwan ba.
A shekarun baya da suka gaba akwai ranar
da sarki mazwan ya taba fita ran gadi da kansa ya saka
aka saka masa hemomi a bayan gari ya zauna yana
shan iska fadawa suna fadanci.
Suna zaune sai ga wani matafiyi da matarsa
suna tafiya cikin nutsuwa da kamala tana haye akan
rakumi shi kuma yana kasa yana janye da ita.
Koda sarki mazwan ya gansu sai ya yi duba
zuwa ga dakarunsa ya basu izinin maza su gabato
masa da wannan matafiyin ai kuwa kafin ya kammala
rufe bakinsa harma sun cika aikinsu sun karasa gaban
matafiyin suka dakatar da shi.
Ya daga kai yana kallonsu daya bayan daya
kamar ba zai yi musu magana ba zuwa can yace musu
“Mene ina kan hanyata ta tafiya za ku dakatar da ni
Dakaru suka kalli juna suka bushe da dariya.
Mu ‘yan aike ne daga sarki mun zo amsar
harajin hanya” mutumin mai suna sham ya kalli
dakarun su duka cikin alamun jarumtaka yace musu.
Ku koma ku fadawa sarki mazwan cewar
ni sham ba zan biya haraji ba sai dai ya yi amfani da
karfin dakarunsa ya amsa” Jin wannan kalamin ya
saka dakarun suka zare makamansu suka. saka shi a
tsakiya suna kewa ya shi.
“Ahir dinka dan saurayi giggiwa ba taka
bace ba a fadar gaka a gaban mashahurin sarki daka
biya haraji ka wuce daya fi maka tsayawa yin taurin
kai Wani kato yace masa lokacin guda yana tunkarar
shi cikin alamun fushi na zuciya yana karasawa ya kai
masa sara da zumar raba kansa da jikinsa amma ga
mamakinsa sai yaga ya yi zamiya cikin sauri yabar
Ya zare takobinsa shima take ya yi wa
wajen saran ya wuce. Www.bankinhausanovels.com.ng
wannan katon tsargen kadanya ya rabashi biyu ko
wani sashe ya fadi kasa jini ya soma kwaranya kasa.
Ganin irin wannan mummunan kisan daya yiwwa
wannan katon sai ya fusata sauran dakarun suka yo
dauki kansa su duka nan fa kasuwar yaki ta. Soma ci
cinikin rayuka ta soma wanzuwa.
Duk wajen da sham ya saka kai.sai dai kaga
kawuna suna tashi sama kamar tsintsaye jini yana
famtsama a wajen kafin wani takin lokaci ya yi wa
dakarun sarki mazwan kaca-kaca, amman hakan bai
tsorata su ba yana kashe su suna kara danowa haka ya
rika dauki babu dadi da su shi kuma sarki mazwan
yana zaune a cikin hemomin da aka saka.mishi yana
kallon wannan jarumtaka da wannan sadaukin yake yi.
Ganin yanda yake masa barna jama’a kuma
yasan idan ya barshi zuwa wasu dakikai babu shakka
zai masa barna dakaru hakan yasa ya juya ya-kalli
dakaren dake kusa da shi ya mika masa hannu alamo
ya bashi takobinsa cikin gagawa ya zare takobin ya
mika masa.
Ya tashi tsaye yana juyata a hankali a
hannunsa lokaci guda kuma ya yi wata fitar burtu a
guje ya yi dauki akan sadauki sham yana zuwa ya kai
masa sara akaikaice sham baiga zuwan shi ba hakan ya
saka kafin ya Ankara sarki mazwan ya yi maså wani
wawan sara a hannu take wajen ya bude jini ya soma
gudana.
Saran sai daya saka sham ya yi baya can ya
fadi kasa sarki mazwan ya dube shi cikin kaskanci
yana ci gaba da juya wukar da take hannunsa.
“Bana son daukar makami a fagen fama don
haka yana nufin rayuka da dama za su salwanta idan
na fito da makamina Sarki Mazwan ya. karasa
magana, da kyar sham ya dafa ya tashi saboda saran ya
galabaita shi.
Ai tsoro shi yake sawa ‘yan maza suna bin
cikin duhu, daka san kai jarumi ne sai ka bari muyi
gaba da gaba da kai Sarki mazwan ya shafa goshinsa.
Kai yaro ne ai kuwa babu shakka yaro bal
san wuta ba sai ya takata don haka kai yanzu ka zama
ribatace sai wani Ya yi nuni ga dakarunsa
Maza ku kamo shi cikin sarka Sham
yanzu bashi da wani kuzari saboda saran da sarki
sarki
mazwan ya yi masa irin saran da babu shiri ya so
tirjewa amman babu ikon yin haka
dakarun kasar Hindu suka kama shi suka sakashi cikin
sarka. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sarki mazwan ya koma cikin himarshi ya
zauna yana kallon sham da aka kama, ‘wasu suka kama-
rakumin aka kwantar da shi aka kamo macen dake kai
aka gabatar da ita gaban sarki mazwan
fuskarta ya ganta kyakkyawar mace ta gaban kwatance
tunda yake bai taba ganin kyakkyawa kamartaba.
Ya sunanki? Ya tambayeta.
Ta daga kai cikin nuna tsana da kyamarsa
tace “Mene amfanin sanin sunana bayan banu amfanin
da zai yi maka” Sarki mazwan ya bushe da-dariya ya ci
gaba da kallonta can ya tashi daga kan karagarsa-ya
karasa har zuwa wajen da take ya dubeta karo na biyu
Ya sunanki? Ya kara tambayarta.
“Wahala da ukuba ba zai saka ka ji sunana ba da ba zai maka wani amfani ba Ya dubeta.wannan
karon babu fara’a akan fuskarsa.Idan kin ki fada min ni sai na baki suna,daga yau sunan ki Hasma kuma na maida ke maidakata
shi kuma mijinki zan saka a daure shi
daurin rai da rai kuma kullum sai an gana masa azaba
Sham ya dago kai cikin sauri jin abinda
ya fada take idanunsa suka kada ya dubi
mata.”Kinga yanda Allah ya maida mu kenan
muyu tawakali akan wannan kaddarar da Allah ya
jarrabemu da ita da ikon Allah wadan nan ba za su
samu nasara akan mu ba” Itama daga kai tayi
cikin idanunta tana kallon mijinta hawaye ya soma
gangarowå sham tace masa.
“Ai na yarda da ikon ubangiji musulunci
kuma ina da yakinin ba zai bari wannan AZzalumin ya
samu nasara akan muba, kai ka san cewa sun kashe
Maciji ne basu sare kan ba Sarki Mazwan ya bushe da
dari game da abinda ta fada.
Kina da matakin da za ki dauka kenan
akan wannan abun dana yanke akan ku? Ya karasa
maganaana mai dora hannunsa daya akan daya.
.Na yi imani da abin bautar mu, na kuma yi
imani yanzu da za ku zagaye wannan duniyar zan biku
har a kamo ku sannan zan daina farautar ku Tayi
murmushi tana kallonsa wannan karon cikin jarumta
tayi magana. Www.bankinhausanovels.com.ng
Ka yi sani babu makawa sai na kubuta
daga hannunka, ba zan dauwama a karkashin
makaskánci kamar ka ba, koman daren dadewa sai na
dawo. Sarki mazwan ya bushe da dariya ya dubi
dakarunsa yace.
Kunji fa wai zata kubuta daga hannuna, sai
na ji maganar kamar tatsuniya” Dakarun suka bushe da
dariya.
Shi lokaci
baya karya,
mashahuran jarumai ba a taba kama su a hannu su
dauwama, don haka duk daren dadewa sai mun kawo
karshen zalluncinka” Sarki Mazwan ya dubeta da
kananun idanunsa ya taka a hankali ya matsa zuwa
wajen da take ya tsuguna ya kamo gashin kanta yace
Ba irin mu ake yiwa barazana ba ya
Cizga sumarta yace mata. Duk
duniya babu daula mai girma da daukaka kamar tawa,
babu wani sarki daya kai ni karfin iko da isa da kuma
fadin kasa Ya saukar da ajiyar zuciya yana kallon
Dakaru.
Kafin ya gama kallon su Hasma tayi wuf ta
zare takobin da take jikin kuben ta a jikin damtsen
sarki mazwan ta yi wani ihu na nuna tsantsar jarumta
ta ture shi ya fadi can gefe guda ta kai masa wani sara
cikin gwaninta da zumar tsarge shi gida biyu amma
cikin tsananin zafin nama ya janye jikinsa duk da haka
sai sai data yanke masa rabin kunne jini ya zuba kasa.
Dakarun da suke Www.bankinhausanovels.com.ng
makamansu aka tsaya carko-carko ana kallon juna
Sarki mazwan ya shafi wajen data sare shi
ya ji rabin kunnensa ya fita, nan take ya saki wata kara
ta fusatar rai da kunar zuciya ya dubi dakarunsa ya
daka musu tsawva.
Kafin kace wani abu tuni sun yi dauki kanta
tayi dauki itama kansu kaifin takobinta ya hadu da su
walkiya da kara mai tsanani suka cika wajen, kasuwar
yaki ta dawo sabuwa.
Kafin kace wani abu tuni har ta karar da
dakarun da suke gabanta tayi wuf ta kaiwa sham dauki

HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG

About AIS

Check Also

JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 1 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI

JARUMI DAN BAIWA CHAPTER 1 BY ABDUL’AZIZ SANI MADAKIN GINI Www.bankinhausanovels.com.ng  JARUMI DAN BAIWAYaro ne …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *