JARIRI CHAPTER 9 KARSHE BY AMEERA ADAM

 JARIRI CHAPTER 9 KARSHE BY AMEERA ADAM

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Goggo ta kwaɓe baki ta ce, “Kinga Rakiya idan zaki zauna gara ki faɗa mini na kama gabana dan naga har tsayawa kike sauraron su.” Daddy ne ya shiga lallashin ana cikin haka sai ga Adam ya shigo shi da wani Malami, ganinsu ya yi carko-carko a tsaye yace, “Daddy dama Abba ne yace a kira Malami game da Jariri.” Daddy zai yi magana Inno ta ce, “Sai yanzu ya ga damar turo shi bayan anci ancinye komai.” ta juya tana kallam matashin Malamin ta ce, “Kaima ka ɗebo tsawo kamar daren mutuwa ka biyo shi zugwi-zugwi kamar robar wando, to tuni an gama da taƙadirin.” Adam yace, “Inno wallahi tun ɗazu ya gaya mini mantawa nayi na tafi Ball Bichi.” Takaici ne ya kama ya kama Inno ta ce, “Da kai da Ball da Bichin idan ban ɗebe muku albarka ba kace na bijirewa Mai salati lokacin da yana raye.”

   Adam ya ɗaga kaɗa yace, “Yooo wa ya sani tun da dai lokacin bana nan idan ma kin bijire masa ai bazan musa ba” Inno da Goggo lokaci ɗaya suka rushe da kuka suna komawa cikin Goggo ta ce, “Allah na tuba Rakiya ina zamu a wannan salawaitun rayuwar, naka na jininka ma yake cin zarafinka ina ga mun shiga duniya.” Inno ta sharce majina ta ce, “Ban da ɗiban Albarka Hansai wai ni Adamu yake gayawa haka? Wallahi bari Nadabo ya dawo inji ko shi yake karanta masa wannan halin.” suna gama faɗa suka shige ciki, Daddy faɗa ya yiwa Adam akan yadda ya yi wa su Inno sannan suka wuce cikin gida.

BAYAN SHEKARA ƊAYA DA RABI

    “Inno to dama har yanzu ba’a samu wanda zai zauna mata ba nace ko ke da Goggo ne zaku je tun da Halifa yace yafisan ta zauna a gidanta…” A hassale Inno ta ce, “Idan naje uwar me zanyi da tsufa na tsofai-rsofai, kinga ni da ƴar uwata babu inda zamu je.” Goggo ta shigo tana cewa, “Wai salawaitun masifar me kike yi Rakiya?” Inno ta ce, “Wai kiji ni da ke muje zaman daɓaro wajen nusaiba, ta manta iya shegen da wancen Jaririn ya yi mana” Mummy ta ce, “Allah ya baku haƙuri Inno dama dan kar kuce an kai wata ba a gaya muku ba shiyasa.” Mummy na gama faɗa ta fice.

   Goggo ta kalli Inno ta ce, “Anya wannan matar nan gaba bazata sa hannu ta dake mu ba kuwa? Dubu salawaitun maganganun da take gaya mana” Inno ta ce, “Barni da ita katuwar banza tana tafe da lafceciyar ƙafa kamar doyar Zariya” gabaɗaya suka bushe da dariya Goggo har da kwanciya, Inno ce ta kalli Goggo ta ce, “Oh ni ɗiyar Mai salati wannan karan ko Tarasulu zata zo mana suna kuwa?” Goggo ta yi mata wani sakaran kallo ta ce, “Kema akwai ki da salawaitun ban haushi, Tarasulu dai kinsan ko kina shure-shure bazata zo ba” Inno ta taɓe baki ta ce, “Ke ta sha zamanta yanzu idan muka gayyace ta kinsan kwaso mana gayyarsu Uwani zata yi su ishe mu da warin ɗiban albarka.” gabaɗaya suka kwashe da dariya.

ALHAMDULILLAH

About AIS

Check Also

RUFAFFAN SIRRI CHAPTER 1 BY SADNAF

Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *