JARIRI CHAPTER 7 BY AMEERA ADAM

JARIRI CHAPTER 7 BY AMEERA ADAM

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Jariri na jin haka ya tattakura ya yi tsalle ya ɗaɗawa Goggo a mazaunanta, gantsarewa tayi tana rafka ihu ta ce, “Kai jama’a wai babu me taimakona daga salawaitun azabtar wannan ne” Jariri bai bi ta kanta ba hannu ɗaya yasa ya ɗaga Halifa sama da yake sakin numfashi da ƙyar,  tsawa ya bugawa Goggo yace, “Maza kinga yadda na yi masa haka? To haka nake san ki yi ɗauka ɗaya idan ba haka ba ni da ke ne” Goggo sharce majina tayi tana wurgawa su Inno mugun kallo saboda taso ace tare ya dinga saka su aikin wahalar aiko ba komai tasan sa sha wahalar tare.+

   Ƙarasawa tayi waje Halifa dake sharɓe cikin jin haushi ta make shi da ƙafa sannan ta yunƙura da ƙyar ta ɗago hannuwansa, sama wajen hannuwansa aikuwa batayi aune ba sai ji kake jigijib ita da Halifan sun  kife ƙasa, Goggo kuka ta saka tana dafe baya tana faɗin, “Wayyo Allah kwankwaso na waini wai jama’a ku agaza mini ƙuguna zai ɓalle” Jariri gefe yaja ya wani tuntsire da dariya harda dafe ƙugu sannan yace, “Wallahi idan baki tashi ba zan raba kwankwason naki gida uku” Goggo ɓingerewa tayi ta ce, “Wallahi na gaji da salawaitun rashin imanin nan, idan gida ɗari zaka rabani sai dai kayi ja’iri hatsabibi, sai fiƙi-fiƙi kake da idanu yana karuwar akuya.”

   Jariri ba ƙaramin bango ya kai Goggo ba, da alama wannan karan ta tuƙe ƙarshe a zuciye ta yunƙura tsaye tana ɗingisa ƙafa, Silbar dake gefe wacce suka sha farau-farau a daren jiya ta ɗauka ya fusace ta ƙarasa gurin Jariri, sai da ta saita tsakiyar kansa ta bashi raaaal saboda baƙin ciko ta ci gaba cewa.

“Shegen abu ƙanƙaninka da kai gajarta kamar inuwar Alli sai azabtar damu kake da salawaitin azaba” wannan karanma tana gama faɗa ta kuma ɗaga silba ta bashi ƙwaaaal a tsakar kansa.

   Gabaɗaya shiru suka yi suna kallonta cikin tsoro don sun san kamar bashi ne Goggo take ɗauka a wurin Jariri, zaninta dake cen gefe ta janyo ta ɗaura muryar Goggo har dacewa take saboda faɗa ta ci gaba da faɗin,

   “Tsabar tsiya da wasali tun da nake riga ban taɓa cirewa gaban yara ba amma dubi salawaitun iskanci da wannan ƙudul ɗin ya sani, wai ni ce da yarda zani a gaban ƴaƴa da jikoki Allah ya isa tsakanina da kai la’ananne” Goggo na zuwa nan a zancenta cikin baƙin cikin abin da ya yi mata ta kuma ɗaga silbar hannunta sake bashi raaal aka.

   Jariri da ke tsaye ko gezau bai yi ba tana sakar masa silba ta uku, da sauri ya fisgi silbar haɗe da wartar hannun Goggo ya nufi ɗakin da suke a ciki kafin zuwan Abba. Goggo na ganin haka ta ɓingere a gurin tana ƙwalawa Inno kira, Jariri bai bi ta kanta ba ya fisgi ƙafarta ya fara ja da ƙarfi Goggo na ganin haka tayi caraf ta riƙo ƙafar Tarasulu dake tsaye da sillallen kai, Tarasu bata yi wata-wata  ba ya janyo Nusaiba dake suka da ita. Jariri juyowa ya yi yace, “Au rakiya zaku yi mata gabaɗaya zan ci ƙwal ubanku kuwa har Mummy” Yana jan Goggo tana jan sauran har ya saka su a cikin ɗakin, silabar hannunsa ya ɗaga ya dinga tsalle akansu yana raɗa musu, Goggo da Tarasulu kusan sumansu biyu a kwance, yadda zafin silba yake sumar dasu haka zafinta yake farfaɗo da su, sai da ya ga sun yi lugub sannan ya fito ya rufe su a ɗakin.

   Adam na gama waya da Abba ya ja guntun tsaki yace, “Haka kawai na shirya zuwa Bichi Ball a dakatar dani waɗannan tsofaffin kamar virus haka suke, idan Allah ya kaimu yamma na dawo na ji da su tun da dai Abba ba ya gari.” yana gama faɗa ya goya jakar goyansa wacce take cike da kayan ƙwallonsa ya fice daga ɗakinsa, daga cen nesa yaji Hajiyar na yiwa Halima magana aka suyi su wuce cen gidan Daddy, bai bi ta kansu ba ya rufe ɗakinsa ya fice daga gidan gabaɗaya.

   Jariri na dawowa ya kalli su Inno dake ta raba ido kamar marasa gaskiya, Mummy ya kalla yace ta fito. Mummy cikin ne ya kaɗa ta tako a hankali ta fito tana kallansa ta ce, “Ranka ya daɗe gani” Wayar Cajar Laptop ɗin Daddy ya nuna mata yace, “Maza ɗakko ta” ba musu ta wuce jiki na rawa ta ɗauko wayar Cajar.

   Kallan Inna Uwani ya yi yace, “Kece kika ce zaki kiɓe ni a turmi ko” Uwani ta ce, “Ba ni bace” Jariri ya ce, “Madalla haka kika ce ko?” ya juya ya kalli Mummy yace, “Su zauna kowanne ya miƙe ƙafuwansa ki fara wanke musu ƙafafuwa da bulalar” Mummy ta zaro ido ganin haka yasa Jariri ya fisge wayar ya zuba mata a jiki, nan take ta hau sosa wurin.

  Wurga mata ya yi ta karɓa sannan ya nuna mata su Inna Uwani, nan take Mummy ta hau shinfiɗa musu wayar baj da ihunsu babu abin da yake tashi a wurin.

    Bayan wani lokaci ya dakatar da Mummy daga dukan da take musu, dan kamar yadda suke kuka itama kuka take fargabarta ɗaya batasan ita tata kalar azabar ba.

    Kallansu ya yi yace, “Gabaɗaya ku tashi” jikinsu na rawa suka tashi ƙyam suna jiran umarninsa, kallansu ya yi sai kuma ya wuce gaba ya fara ƙobarewa yana zungura kai gaba, sai kuma ya ɗage ƙafa ɗaya yana yi yana tafa hannuwa yama waƙa.

“Sai ni limaninsu! Sangandale sangandale, sangandale ina shuka tsiya yadda nake so…” Bai ƙarasa faɗa ba ya juyo yace, “Kuyi yadda nake yi” Haka suma suka ƙobare suna rawar sangandale, idan Jariri ya yi gaba sai kuma ya dawo baya-baya.Su Inna Uwani ba dan sun so ba haka suka bi bayan Jariri yana rawar sangandale suna mara masa baya, su Daddy ban da gumi babu abin da suke yi saboda gajiya, da ka dubesu gabaɗaya zaka gane sun jigata rawar ba ta daɗi suke yi ba. Su Inno dake cikin ɗakin sai numfarfashi suke da alama ma basusan wanda yake kansu ba, Halifa na sharɓe a ƙasa yana sauke numfashi da kyar yana jin duk abin da yake faruwa.+

    Wani nazari ya yi kamar wanda aka zabura haka ya miƙe zaune yana huci, tafin hannunsa ya kalla sai kuma ya fara motsa baki yana karanta ayatul kursiyyu haɗe da amanarrasulu, tofawa ya yi a tafin hannun nasa ya miƙe tsaye cikin ƙwarin gwuwa ya ƙarasa gurin su Jariri.

   Jariri na gaba kamar Liman ɗan ɗugul da shi wucewa Halifa ya yi, ya saita tsakiyar kan Jariri ya bashi taaal, Wata irin jijjiga Jariri ya yi sai ji kake kiriif ya faɗi cen gefe. Mutsu-mutsu yake yana yage baki yana kuka, carko-carko suka yi suna kallan ikon Allah. Nan Halifa ya wuce kitchen ya ɗebo ruwa a kofi yazo ya tsaya ya yi bismilla ya fara karanto addu’o’in tsari. Sai da ya gama karanta addu’ar sannan ya ƙarasa ya fara yayyafawa Jariri ruwan tofin nan jikinsa.

    Kuka yake sosai sai da ya jima a haka sannan ya yi shiru idanuwansa duk sun shanye, a hankali yake juya idanu yana kallansu ɗaya bayan ɗaya da alama bai so yadda Halifa ya yi masa ba, dan a yanayin kallon da yake musu kallo yake yi musu na ku taka a sannu zaku shigo hannuna.

    Ganin sun yi galaba akansa yasa suka fara ficewa daga ɗakin ɗaya bayan ɗaya, Halifa ne ya leƙa ɗakin da su Nusaiba suke ciki ya yi musu magana, da alama sun jigata dan sai sauke ajiyar zuciya suke kawunansu da goshinsu duk ya yi molo, sai da ya yi da gaske sannan ya samu ya dinga taimaka musu suna fita daga cikin ɗakin.

   Cen ɗakin su Salim ya shiga da sauri ya ɗauko wayarsa dan ya kunna karatu sai dai gabaɗaya babu sura ko ɗaya a ciki, Tsugunnawa ya yi kan Jariri ya dinga karanto addu’a yana tofa masa. Su Inno dake tsakar gida sai raba idanu suke Daddy cen gefe ya zauna yana sauke ajiyar zuciya.

   Tarasulu da su Inno kuwa kawunansu babu Ɗankwali babu zannuwa a jikinsu suka dinga bin hanyar gate zasu fita, sai Nusaiba da su Mummy suka dinga janyo su suna zaunar da su sannan aka samu suka haƙura, dan acewar Inno har abada ta yafe zamanta a cikin wannan gidan.

   Ana cikin haka Halifaya kira wani abokinsa Malam Muddasir me harkar Islamic chamist a take ya sanar da shi duk abin da yake faruwa, ba’a ɗauki lokaci me tsawo ba ya ƙaraso gidan wanda kusan tare da Ƙannen Nusaiba da matar babanta suka ƙaraso cikin gidan, da niyyar zuwa taron suna.

   Ɗakin da Jaririn yake aka shigar da Malam Muddasir, Jariri kwance yake a sharɓe jikinsa duk yayi laushi. Malam Muddasir zama ya yi ya ɗauki wasu kwalaben turare ya ciro habbatus sauda yace akawo masa garwashi, nan take aka kunna garwashi da yaje mummy tana da irin gawayin nan na kwali.

   Malam Muddasir bismillah ya yi ya fara karatu bayan ya zuba turaren habbatus sauda a cikin wuta, Jariri dake kwance sai mutsuniya yake hankali a tashe. Bayan wani lokaci sai ji suka yi ya ƙwalla ƙara yana cewa, “Malam ka barni dan Allah karka ƙone ni” Malam Mudasir ya jinkirta da karatun yace, “Waye kai kuma me yasa zaka shiga jikin bayan Allah nan ka dinga wahalar da su?” Jariri yace, “Maganar gaskiya Mahaifiyarsa ce ta bani lasisin shiga jikinsa kuma Allah ya sani nayi ɗaras na ji daɗin zama cikin wannan ahalin bana jin zan iya fita.” Yana gama faɗa ya bushe da dariya sannan ya ci gaba da cewa, “Yooo dama tuni mun riga da mu ɗauke mata nata ka ga kuwa ina naga gurin zuwa.”Malam Muddasir ya fusata yace, “Kai ni kake gayawa haka wato dama ba nadama kayi ba ko? Ai kuwa babu abin da zai hana babbake ka da ayar Allah” Jariri ya tuntsire da dariya yace, “Ai aramma idan ka mutu na suma dan dama nasan wannan ranat tana tafe, sai dai naso a ce na jima ina more waɗancen mutanen kafin su farga, wai kai Malam basai ka tambayi yadda akai na ƙwamushe mata ɗa ba, sai falau-falau kake da kunnuwa kamar na zomo” Malam Muddasir ya haɗiyi yawun baƙin ciki yace, “Kayi na ɗan lokaci sai dai wani ba kai ba, mu je ya akayi ka zalince su ka musanya musu ɗansu.”+

   Jariri ya karkace kai yana kallon Nusaiba sannan ya kalli Malam yace, “Ɗan tashe ni zaune” Malam Muddasir ya ɗaga Jariri zaune, ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya ya yi ya fara da cewa,

   “Nusaiba ta kasance tana da wata ɗabi’a lokacin da take ɗauke da tsohon ciki, tana yawan fita fitsarin dare kuma idan zata fita babu mayafi bare hijabi take fita kai wani lokacin da wata ƴar figigiyar riga zaka ganta ta fito turtsi-turtsi, haka zata banka ƙofa ta shiga ta kwara fitsarinta ta fito ta koma ɗaki.” Jariri na zuwa nan ya zarowa Nusaiba idanu yace, “Ko nayi miki ƙarya? Ai ina ankare da ke ƙarfe ɗayan dare har wani munafikin cin abinci kike tashi to dan Allah Malam me zai hana banyi wuff na faɗa ba. Na tabbata ko kai kake ganinta cikin yanayin nan sai dai fa kayi eh yaneehh” Malam Muddasir ya tsuke fuska yace, “Zaka bamu labari ko islkanci zaka yi wa mutane? Ko angaya maka kowa ɗan iska ne kamar kai?”

   Jariri yace, “A’a ai ko ko cikin dabbobi akwai na gari amma kai ɗin dai ban tabbatar ba ko da kuwa a tazugen liman kake kwana.” Wani mugun kallo Malam Muddasir ya watsa masa sannan Jariri ya ci gaba da cewa.

   “To yau da gobe ta fi ƙarfin wasa, tun ina ganinta ina ɗauke kai hai nayi sha’awar ɗauke ɗanta na maƙale ta haifo ni, haka kuwa nayi tuni na ɗauke jaririnta na wurgawa iyalaina suka yi habzi da shi ni kuma na ci gaba da zama a cikinta ina sharɓar romon damakwaraɗiyya, kuma ni dai dani da zuri’armu gabaɗaya ƴan ruwa ne dan haka ma yasa na dinga ninƙaya a cikinta san raina.” Yana rufe baki Inno ta ɗebi salati tana tafa hannuwa ta ce, “Amma dai wannan ja’iri anyi tambaɗaɗɗe dai Allah dai ya ɗebe masa albarka ruwa-ruwa.” Jariri ya wurga mata harara yace, “Bari wannan falalun ya tafi zan nuna miki tambaɗa shiyasa dama na so tsotseki tass a mota Allah ya ceceki. Malam Muddasir ya ɓata rai jin Jariri ya kira shi da falalu, bai yi ƙara ba dan duk cikin hallitar fuskar Malam Muddasir babu inda yakai kunnuwansa girma.

   Malam Muddasir A’uziya ya ƙara da niyyar fara karatu Jariri na jin haka ya ɗame ƙafarsa,  da gudu ya nufi Inno yana bankaɗa zaninta.

About AIS

Check Also

JARIRI CHAPTER 4 BY AMEERA ADAM

JARIRI CHAPTER 4 BY AMEERA ADAM Www.bankinhausanovels.com.ng  Adam da ke riƙe da Inno gyara mata …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *