JARIRI CHAPTER 6 BY AMEERA ADAM

JARIRI CHAPTER 6 BY AMEERA ADAM

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Daddy iya ƙarfinsa ya zage ya dinga ɗaukan Jariran duk wanda ya warta sai kaji tim ya buga shi da ƙasa, amma wani abun mamaki yana buga su da ƙasa sai ka ga sun girgije sun mulmula sun miƙe tsaye, Halifa ma ganin haka yasa ya fara yin yadda ya ga Daddy yana yi kusan lokaci ɗaya suka dinga ɗaukan Jariran suna wurgarwa ƙasa.+

    Jariran cikin haɗin baki suka dinga ƙyaƙyata dariya da an buga su da ƙasa sai kaji sun tuntsire da dariya, lamarin da ya sa Daddy da Halifa suka fara shan jinin jikinsu kenan. Daddy ne ya ɗan dakata yana raba idanu kamar almara haka yaji Jariri ya sure shi ta baya, daga Halifa har sauran mutanen zaro idanu sukayi suna kallan wannan lamarin, Halifa da sauri ya ƙarasa gurin da Jaririnsa ya sunkuci Daddy ya fara ƙoƙarin jan Daddy nan fa suka fara ja’inja, Jariri yana ja Halifa yana ja.

    Bai yi aune ba shima Halifa yaji ƙanƙanin hannu ya sureshi aikuwa ya ƙwalla ƙara yana neman agaji, Jariran nan haka suka mayar sa Daddy da Halifa kamar ƙwallo suka fara wurga su sama suna caɓewa.

  Inno da ke kwance cikin fitar hayyaci ita Goggo da ƙawayen ta fara cewa. “La’illaha’illahu, Innamal’a’amalu binniyati…” kafin ta ƙarasa faɗa Goggo ta ce. “Li’ilafikuraishin aniyar jiririn nan ta bishi…” Jin sun fara karaton ƴan ayoyi yasa Jariri ya damfara Daddy da ƙasa ya juyo gurinsu Inno haka ya dinga binsu da bulali yana cewa.

   “Ku rufe mini baki na ƙarajin kunyi karatu sai mayar da bakin ku ya koma ƙeyar ku” Inno da ƙawayenta haka suka yi shiru ban da ihu babu abun da suke yi.

   Daddy da ke gefe a yashe hannu biyu yasa ya dafe bayansa cikin azaba yace. “Wash! Jama’a nikam rayuwata ta zo ƙarshe na yafewa kowa nima ku yafe mini” Jaririn da ya sunkuci Halifa ne yaje bakin ƙofa ya juyo yace.

   “Shugaba ni dai na tafi da wannan kuma ku samo rabonku” Halifa yana jin ance an za’a tafi da shi ya rungumo ƙofa yana cewa. “Me gida dan Allah kayi haƙuri ka kyaleni karka tafi da ni” Jaririn yace. “Iyalaina suna cen suna jiran na kai musu kai babu abin da zai hana na tafi da kai” Jariri dake gurin su Inno ya juya gurinsu Halifa yace. “Kai Kuɗubale zo nan ba shi kaɗai za’a tafi da shi ba, kuma wannan babban kan ba naka bane nawa baka ganin Daddyna ne”

  Jaririn da ke ɗauke da Halifa ya ƙaraso ya sauke shi, Halifa da gudu yayi sufa ya shige cikin su Mummy da Nusaiba, Jariri ya kalli sauran ƴan uwansa Jarirai yace. “Kowa ya ɗauki rabonsa nida Daddy da Mummyna zan ɗauka” tun bai rufe baki ba Jariran suka buga uban tsalle suna cewa. “Yeehh Yau akwai shan lagwada” kowa ya tafi dan kama wanda yake san ɗauka, ɗakin banda ihu da kukan tsofaffi ba abin da yake tashi a ciki.

   Inno hawaye ta fara ta ce. “Yau wane irin la’ana ce ta samemu zuri’ar Me salati zatayi mutuwar wulaƙanci, wannan ɗiban albarka har ina ace wai makarai ne zasu cinye naman mu” tana rufe baki suka ƙara rushewa da kuka. Suna ji suna gani haka Jariran nan suka dinga sunkutarsu suna fitowa tsakar gida da su.

   Zuwan su tsakar gida kenan suka ji an turo ƙofar anshigo, bakinsa ɗauke da sallama ya ƙaraso. Jariran nan na jin haka suka buga tsalle suna suka wurgar da su Inno ƙasa nan take suka ɓace, a dai-dai lokacin ya shigo tsakar gidan yana shigowa ya hango duka mutanen gidan yashe a tsakar gida tsofaffin gabaɗaya zannuwansu ya cire daga su sai ɗan fatarinsu.

   Su Daddy na jin an watsar da su kamar haɗin baki gabaɗaya suka miƙe suka shige ciki da gudu har suna gware da juna, Abba da mamaki ya kallesu a fili ya furta. “Ikon Allah” idanunsa ya kai kan Jaririn da ke yashe a ƙasa sai kuka yake yana cilla ƙafafauwa sama, da sauri ya ƙarasa ya yi bismillah ya ɗauke shi yana cewa. “To wai yau lafiya me yake damun mutanen gidan nan? Ko wani abu ya faru ne?” Jariri da yayi lakur yana satar kallansa ta gefe a zuciyarsa yace. “Bari dai ka tafi gabaɗaya sai na ci ƙwal ubansu.

  Abba takawa ya yi ya wuce ciki yana rafka sallama daga cen ɗaki yaji muryar Halifa yana cewa. “Abba ka wurgar da Jaririn nan wallahi ba mutum bane” Da mamaki Abba ya kai kallonsa kan Jariri yaga ya ƙura masa ido ko ƙiftawa baya yi, nan take yasha jinin jikinsa saboda ba yadda za’ayi ace mutanen gida gabaɗaya sun juyawa Jariri baya ba tare da wani dalili ba. Abba ya ce  “Idan ma ba mutum bane ni zanyi maganinsa.” Jariri na jin haka ya wage baki ya fara tsanyara kuka.Goggo na jin abin da Abba ya faɗa ta leƙo ta windowa tana nuna Jariri da hannu ta ce, “Nadabo Allah dai ya yi maka salawaitun albarka, wannan Jaririn da kake gani ba ƙaramin taƙadari bane. Wallahi da zan iya sai ha tsinke hanjinsa gida uku.” Nusaiba da ke gefe ta kalli Goggo ta ce. “Ummmm ummmm Goggo” Goggo ta yi mata kallon gefen ido ta ja guntun tsaki ta ce. “Ke rufe mini baki da Salawaitun ummmm ummmm ɗin ki. Haka kawai a nemi a hana bawa da bakin sa ya yi magana.” Inno ta karɓe zancen da cewa.+

   “Amma dai Nadabo Allah ya tattaro albarkar duniya ya afka maka, shi kuma wannan yaro maras ɗa’a Allah ya ɗebe masa albarka wuta-wuta, inda ka ga ɗiban albarka da Jaririn nan ya yi mana kare ma bazai ci ba, shiyasa ko haufi bana yi Ubangijin Sammai da ƙassai ya ɗebe masa jinginannun albarka, ya afka masa ɗiban albarka wafulan-wafulan a tsakar kansa.” Daddy ya kalli Inno ya yi gyaran murya ya yi ƙasa da murya yace, “Inno don Allah ku daina aibanta Jaririn nan bakwa tsoron  ya kuma aikata mana wani abun”

  Inno ta keɓe baki ta ce, “Kai raba kanka ɗiban albarka ta, bakaji me Nadabo ya faɗa ba tun shigowarsa, akan kunnenka yace zai ɗebewa yaron cen albarka.” Tarasulu ta yi caraf ta ce, “Ni kam yau na ga sababi wallahi tun da me cin ƙwal ubansa yazo mr muke jira da ba za mu yi ta kanmu ba? Ai nikam wallahi da ni zan samu sukunin da wannan Yaro Nadabo ya samu da idan na samu mazaunansa na dinga kafa masa cizo, har sai ya gane Annabi ya faku.” Halifa ya kallesu fuskarsa ɗauke da busassun hawaye yace. “Inno Ummmm ummmm fa” Uwani ta matso jikin window  har tana bankaɗe Inno ta ce, “Nadabo don Allah kayi abin da yake gabanka, kar su cika ka da hayaniya maza ka sa shi a turmi ka kirɓe kowa ya huta.”

  Abba mamaki ne ya kama shi dan ganin suna ta faɗar abunuwa marasa daɗi akan Jaririn,  Jariri ɗaya bayan ɗaya yake sauraronsu da mugun alkaba’in da suke ja masa. Abba ya gyara tsayuwa har lokacin Jariri na rungume a hannunsa yace. “Wai dan Allah me ya yi muku haka ne” Jariri da yake mutsuniya a fakaice ya juya ya ƙwalalo musu ido,  tsit suka yi aka rasa wanda zai yi magana. A hankali Abba ya taka ya ƙarasa cikin falom da babu kowa a ciki ban da ɗangwale da zannuwa, daga cen gefe harda ɗan gajeren wandon Inna Uwani. Zama ya yi ya kwantar da Jariri akan kujera yana rufeshi da wani zani da baisan ko na waye ba.

   Ɗayan bayan ɗaya suka fara leƙowa daga baya suka fara fitowa, Daddy shine ƙarshen fitowa yana tafe yana muzurai.

    Abba cikin girmamawa ya gaishe da Iyayen nasa da ƙawayensu, sannan ya ɗora da cewar, “Goggo kinsan yau ne fa tafiyar tawa yanzu haka na kusa makara a gaggauce nace bari na leƙo nayi muku sallama.”

   Goggo ta hangame baki lokaci ɗaya ɗebi salati tana tafa hannuwa sannan ta ce, “Nadabo yanzu tafiya zakayi ka barmu da salawatun hatsabibin yaron nan…”  tun bata rufe baki ba wayar Abba ta fara ringing yana ɗauka daga cen ɓangaren aka ce.

   “Saura minti arba’in jirginku ya tashi fa ba buƙatar ɓata lokaci.” da yake ya warware speaker wayar Inno na jin haka ta ce, “Aikuwa ƙafata ƙafarka Nadabo. Wallahi bazaka barni da wulaƙantaccen nan ba ya ƙara ɗebe mana albarka haka kawai ba.” Abba ya kira lambar Adam bayan ya ɗauka yace, “Son maza kaxo gidan Daddynku it’s urgent ni zan wuce dan Khalid na Nurain tuni sun wuce mini da kaya na.” daga cen ɓangaren khalid yace. “Ok gani nan zuwa Abba”

   Abba yace, “Banda ɓata lokaci case ɗin Jaririn nan ya isheni ” Adam yayi guntun tsaki ba tare da ya bari Abba yaji ba, a zuciyarsa yake mitar wannan case na Jariri ya ishe shi.” amma a fili yace, “Yanzu zan fito Abba” Abba yana gama faɗa ya zaro dunƙulen kuɗi kashi uku ɗaya ya fara miƙawa Inno sannan ya miƙawa Goggo, ɗayan kashin kuma ya miƙawa Tarasulu yace. “Baba ga wannan ayi mana Addu’ar nasara” ya ƙarasa faɗa yana miƙawa  tsaye, sannan yace, “Adam yana tafe zan sa ya taho da Ya sayyadi na ƙasan layinmu insha Allah koma menene za’a shawo kan matsalar, Yaya ni zan wuce ka wallahi naso zuwa da wuri wani uzuri ne ya hanani,  sai na je dai mayi magan insha Allah.” Daddy gyaɗa masa kai kawai ya yi saboda gabaɗaya yawun bakinsa ya ƙafe saboda fargaba.

   

   Su Inno murnar kuɗi sai ta sa suka manta da Jariri dake kwance a kan kujera, Abba a hanzarce ya tashi ya fice saboda gudun kar ya samu matsala a Airport.

    Su Goggo na cikin irga kuɗi suka ji Jariri ya bankaɗe zanin da aka rufeshi, ya yi wata irin tsayuwa ta gwamim jaki da alama wannan karan kamar yafi jin ƙwarin gwiwa akan wancen karan, Ido ya gwalala musu cikin tsawa yace,

“Waye yace zai kafawa mazaunai na cizo da haƙoransa?” Jikin Daddy na rawa ya fara ɗaga hannu sama yana cewa, “Wallahi bani bane Inna Uwani ce…” a zabure Inna Uwani ta katseshi da cewar, “Bani bace sam kada ka sa a zalinceni bi gairi haƙƙina Tarasulu ce ta faɗa” Tarasulu tai tsilli-tsilli da idanu tana matsar ƙwalla.Jariri ya juya yana kallon Tarasulu cikin tsawa yace, “Ke ce kika faɗa ko?” Tarasulu ta ɗan ja da baya ta ce, “Ranka ya daɗe bani bace aljanuna ne suka  faɗa.” Jariri ya yi tsalle caraf ya ɗafe kafaɗar Halifa, nan take cikin Halifa ya kaɗa. Jariri ya fara mulmula kan Halifa yana lasar baki, yawunsa har yana ɗiga a tsakiyar kan Halifa. Leƙo kansa ya yi ta wajen fuskarsa yace, “Daddy wallahi yawuna ya tsik…” Tun Jariri be gama maganar ba Halifa ya katseshi hankali a tashe yace, “Da me yawun naka ya tsinke?” Jariri ya kuma shafo ƙetar Halifa yana sunkuyar da kansa da niyyar lasar ƙeyar, a zabure Halifa ya yi tsalle cikin muryar ban tausayi yace, “Dan Allah kayi haƙuri wallahi kaina ɗaci gareshi” Jariri ya gungura ya sauka yace, “Wasa nake yi maka Daddy ba kanka zan gwaguya ba, kan waɗancen zan gwaguya” Jariri ya ƙarasa faɗa yana nuna su Inno.+

    Lokaci ɗaya gumi ya fara wanke musu jiki, jikinsu ban da karkarwa babu abin da yake yi. Jariri ya nuna Tarasalu yace, “Matso da ke zan fara na cire miki aljanun kanki” Tarasulu ta tsugunna gwiwa bibbiyu ta fara roƙonsa idanu cike da hawaye.

  Jariri ya ɗare kujera yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yace, “Idan baki zo ba kika bari na ƙaraso idan na turmusheki sai na ɗaɗe mazaunanki dan babu abin da zai hanani yagarsu na cinye su tas” Tarasulu wage baki ta fara yi tana bin su ɗaya bayan ɗaya da jemammun idanuwanta, kallo take musu me ɗauke da ma’anar nikam tawa ta ƙare ku gafarceni, tana zuwa kan Inno ta ce, “Rakiya duk duniya ke kaɗai kike bina bashi kuɗi bayan na mutu ki kira su Ɗalha kicr su biya mini kar akaini da kuɗinki na faɗa hannun mala’iku, kinsan dai me Malam me haɗiyar alƙami ya taɓa sanar damu tun yarinta akan haƙƙin wani.” Inno ta sharce tata ƙwallar tana fyace majina ta ce, “Yanzu haka zamu yi mutuwar wulaƙanci muna ji muna gani, to Allah shi yafe mana amma nikam tsinke banzan amsa ba dan duniya da lahira na yafe miki, yanzu idan na karɓe na yi wa amintaka ɗa’a kenan?” Jariri ne ya buga musu tsawa yace, “Ke me karɓar wasiyyar basai  kin fita da rai ba” aikuwa ko rufe baki bai yi ba gabaɗaya tsofaffun nan suka yage baki suna kuka me nuni cewar ta su ta zo ƙarshe, gurin banda rawar murya da makyarkyatar tsofaffi babu abin da yake tashi.

   Daddy ma da yaga basu da wata mafita da sanin makomarsu, janyo gefen rigarsa ya yi ya fara goge ƙwallah. Halifa da su Mummy ban da ido babu abin da suke bin su da su na jikin a sanyaye kamar marasa jini a jika, Jariri tsalle yanyi ya ƙarasa gurinsu Inno ya yi ƙerere yana kallonsu sannan yace, “Maza ku shanye kukanku idan ba haka ba wallahi jikin ku ya gaya miki dan babu abin da zai haɗa na yi lugu-lugu da namanku.” Kamar anyi ruwa an ɗauke haka gurin ya yi tsit su Inno suka ja bakinsu suka yi shiru suna sauraron hukuncin da zai yanke akansu.

    Jariri wata miƙa ya yi yana dafe cike wanda ya kasance tunɓur dan ko wando babu a jikinsa, yamutsa fuska Jariri ya yi sannan ya kalli Nusaiba da take lungu kamar munafuka , tsalle ya fara yi yana buga ƴar ƙafa kamar ta sauro yace. “Mummy zan sha” cikin Nusaiba ne ya karta nan take gumi ya fara keto mata ta basar kamar bata ji shi ba.

    Juyawa ya yi yace, “Ko da yake kafin nazo sha bari na fara rage hanya da waɗance. Tafiya ya fara yi yana wata rangwaɗa yana dafe ƙeya haɗe da wurga ƙafa ɗaya, da sauri ya juyo ya kalli ƙofa yace, “Ku rufo mini ƙofar” tun bai ƙarasa faɗa ba suka ji ƙofofin ɗakin na bankowa da ƙarfi suna rufewa.

    Cikin kitchen ya wuce cen saman drowaer ya ɗare ya zaro wata silleliyar wuƙa, sabuwa tana sheƙi ya fito gurin da ya bar su Inno a tsaye, suna ganin Jariri da wuƙa suka ƙanƙame juna  suna kurma ihu.

   Jariri ɗaga wuƙar sama ya yi ya kalli Tarasulu yace, “Maza ƙaraso na fara da salsale gashin kanki kafin naje kan sauran, idan kuma kika bari na ƙaraso da kaina sara ɗaya zanyi na fille kanki ƙasa. Gara ki bari na fara bi gaɓa-gaɓa” Tarasulu bata da zaɓi haka ta ƙasa jiki a sanyaye ta tsaya gaban Jariri ta ce, “Gani nazo” Jariri ya buga tsalle ya ɗafe kafaɗar Tarasulu ya kalli saitin kumatunta yawun bakinsa na tsinkewa har yana ɗiga ƙasa, ya fara lasar kumatunta.

Ilahirin jikin Tarasulu rawa yake yi hawaye da majina sai ambaliya suke a fuskarta, kallan bakinta ya yi yace, “Buɗe bakinki na gwagwiya naji ko da daɗi.” Tarasu cikin kiɗima ta ce, “Ummmmun” yace, “Afke  ashe fa kece me aljanu ko?” Da sauki Tarasu ta gyaɗa kai yana jin haka ya zabura ya zame gashin kanta ya fara askeshi, Tarasulu ban da kuka da ihu babu abin da take yi saboda azabar yadda yake kankar kanta kamar yana fafe ƙwarya.

Su Inno tun kafin yazo kansu suka yanke ƙauna suna kuka da barin wasiyya, kafin wani lokaci tuni Kan Tarasulu yayi ƙwal kamar bayan silba, gashin Tarasulu ya fisga ya dinga cusawa a baki yana haɗiyewa, gabaɗaya ido suka zaro suna ta’ajibin wannan lamari na Jariri, kamar ya shiga zuciyarsu haka ya dinga damƙar farin gashin Tarasulu yana wurga musu yana cewa, “Maza kowa ya ci rabonsa, duk wanda bai ci ba sai na yanke kunnuwansa na bashi ya cinye” Kallan kallo aka fara tsakanin su Daddy da su Inno, kowa na tunanin wanda zai fara wannan lamarin a tskaninsu.

   Jariri na haɗiye gashin ya fara shaƙuwa da sauri ya ɓingere a ƙasa yana kukan jarirai yana cilla ƙafa, Inno ce tw fakaice shi ta raɗawa Goggo magana a kunne.

  “Kai amma wanna ɗan ƙwal uban jariri anyi hatsabibi, dubi ɗiban albarkar da yake gwadawa mutane” kome suka faɗa lokaci ɗaya suka bushe da dariya Inno harda kwanciya a gurin tana ƙyaƙyatawa.

   Jariri da ke kwance yana ta kuka haɗe da ciccila ƙafa sama ya ɗan jiyo a fakaice, ya saci kallonsu da wutsiyar ido sai ya kuma kwara ihu haɗe da cewa, “Inno! Wayyo Inno kizo ki ɗauke ni ki kaini gurin Mummy zan sha” Inno da ke jin ƙwarin gwiwa sakamakon tattaunarwa da suka yi da Goggo ta ce, “Sai dai ka mutu a wurin tambaɗaɗɗe maras ɗa’a” Tarasu  gefe ta ja ta zauna daɓar tana shafa kanta cikin baƙin ciki. Halifa wani tunani ne ya faɗo masa har sai da farin cikinsa ya bayyana a fili, cikin fakar ido ya fara takawa a hankali har ya faɗa cikin kitchen, yana shiga ya ɗauko taɓarya da sauri ya ɗaga ta sama iya ƙarfinsa ya bugawa Jariri a tsakiyarsa jikinsa da niyyar datse shi gida biyu.

Halifa na saukewa Jariri taɓaryar yaji kamar sauka dukar a jikinsa, nan take ya sulale ya baje a gurin saboda azaba sai gani suka yi fitsari na gangarawa ta ƙafafuwansa. Jariri bushewa ya yi da wata mahaukaciyar dariya yace, “Shege Daddy ya iya saiti” sai ya kuma bushewa da dariya lokaci ɗaya kuma ya murtuke fuska ya kalli ya kalli Goggo yace, “Maza zo ki ɗauki Daddy ki goyashi” Goggo cikin fargaba ta ce, “Da ni kake yallaɓai?” Jariri yace, “A’a da kaina nake” jin haka yasa Goggo ta ƙarasa gaban Halifa da ke baje a ƙasa ta ce, “Da ka taimako min da salawaitun ɗauki amma ni kaɗai bazai iya ba ina ni ina salawaitun Halifa yaro a murɗe kamar ƙarfe.” kallon da ya wurga mata ne yasa Goggo ta haɗiye abin da yake bakinta nan ta sunkuya ta fara cicciɓar Halifa sai kake ɓurrrr daaaaarrrrr Goggo na sakin tusa ta ko ina.

About AIS

Check Also

JARIRI CHAPTER 4 BY AMEERA ADAM

JARIRI CHAPTER 4 BY AMEERA ADAM Www.bankinhausanovels.com.ng  Adam da ke riƙe da Inno gyara mata …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *