JARIRI CHAPTER 3 BY AMEERA ADAM

JARIRI CHAPTER 3 BY AMEERA ADAM

Www.bankinhausanovels.com.ng 

A firgice Ɗan Karota ya ja da baya saboda cikin shammata Inno ta warce katakon da dukan da ta kai masa, sai da ya kuma yin nesa da Inno sosai sannan yace. “Iya lafiya me yake faruwa?” Inno ta kuma tsuke fuska tana gyara tsayuwarta ta ɗaga katakon sama ta kuma cewa. “Ubanka kayi mini! Ni zaka gwadawa ɗiban albarka ido biyu? Uban me jikana ya yi maka da zaka tsayar da shi ko hassada kawai da ƙyashi saboda ka ganshi da shirgegiyar mota, kai kuma kana fama da maras ɗa’ar tsalan wando kamar tazuge. To ahir ɗin ka jikana ya fi ƙarfinka ya sha tabara ya sha yasin kurwarsa kur aniyarka ta faɗa kanka sakarai maras ɗa’a” Ɗan Karotan sai a lokacin ya waiga ya hango motar Halifa da yake ƙoƙarin fitowa, haushi ne ya fara kama shi ganin yana bakin aikinsa ana shirin yi masa karan tsaye, matsowa ya yi gabda ita yace. “Me zanci da jikan naki ko ce miki akayi ni maye ne, kece baƙuwar mota wayasani ma ko duk zuri’arku shi kaɗai ne me mota, amma wallahi ina gargaɗin ki idan kika ƙara buga mini wannan katakon sai na shemeki a gurin nan, sai dai duk abin da za’ayi ayi shi. Ban da ma an rainawa

ma’aikacin ɗamara hankali har wata figaggiyar tsohuwa ta isa ta kai hannu jikina.” Inno na jin haka ta ɗaga katakon ta kuma sauke masa a ƙeya tana cewa. “Kaci Mai garinku ko uwarka ta isa ta ce mun figaggiyar tsohuwa bare kai saboda rashin ɗa’a, kai wallahi da ba dan ina da zuri’a ba da na kwashe maka albarka kowa ya huta. Amma wallahi bari a kira mini Salisu sai ya kira maka hukuma sun kwashe har danginka”  a hassale Ɗan Karotan ya taso da niyyar sheme Inno da sauri Halifa ya shiga tsakani, dukan da Ɗan Karotan ya kai masa ba ƙaramin shigar Halifa yayi ba har sai da ya yi taga-taga kamar zai faɗi, da gudu Inno ta jefar da itacen hannunta ta faɗa kan Halifa tana kuka tana cewa.+

  “Jama’a  ku kawo mini agaji Ɗan Farota zai kashe mini jika ba gaira babu dalili saboda ɗiban albarka. Wayyo Allah Halifa dan Allah ku ceto mini shi tun kafin na kwashe Ɗan Farota albarka ya bi duniya ya ɓalɓace”

  A dai-dai lokacin Nusaiba da Goggo suka ƙarasa wajen, Goggo kutsawa ta dinga yi cikin mutane har ta isa wajen da Ɗan Karotan yake cikin masifa ta ce. “Kai Ɗan Tayota kake kowa? Wani sabon salon salawatin rashin imani zaka gwadawa ƴar uwata, wallahi me rabani da kai yau sai ya shirya duk kuwa salawaitin haƙurin da za’a bani.” Goggo kamar wata ƴar dambe haka ta ɗage hijabi, kicici-kicici ta fara kaiwa Ɗan karota duka har wani nishi take tana ja da baya, ita a dole zata rama abin da aka yi wa ƴar uwarta. Ɗan Karotan na ganin haka ya  wawuri Goggo ya cukwikuyeta cikin hijabinta ya turata ciki ɗan gidan da suke shiga idan zasu bayar da haannu. Goggo cikin tashin hankali ta fara rafka salati tana cewa. “Jama’a ku kawo mana ɗauki zai halaka mun nida ƴar uwa da Salawaitin rashin imaninsa, ku agaza mana mutane ko bakwa ji na ne? Ku zo ku fiddani zafin ƙarfe sai gasani yake”

   Kafin wani lokaci tuni titi ya kacame da mutane yara da manya, wani mutum ne ya ƙaraso ya fito da Goggo da take nannaɗe a Hijabi a cikin ɗan akurki, tana miƙewa ta fara raba idanu tana neman Inno domin su gudu, banda gumi babu abinda take sharɓawa saboda wahala. Mutanen da abin ya faru akan idanunsu suka fara bawa Ɗan Karotan baki suna bashi haƙuri, waɗanda basu san yadda abin  ya faru ba suna ta zaginsa.

    Duk sun yi carko-carko sai hayaniya ce take tashi sama-sama, Inno na gurin Halifa tana ta subuaɗiɗin zance. Halifa bai bi ta kanta ba ya fisgi hannunta ya wuce mota da ita, Nusaiba da Goggo ma suka rufa masa baya suka koma mota, Goggo saboda sauri har tuntuɓe take yi, suna shiga cikin Motar ya saka maka lock. Da gudun gaske ya figi motar suka wuce sai da sukayi tafiya me nisa sannan Halifa ya yi parking ɗin motarsa a gefen hanya.

   Da ka kalli fuskar Inno zaka fahimci tana cikin ɓacin rai saboda fuskarta ta yi murtuk, Halifa ne ya fara magana cikin ɓacin rai. “Saboda Allah Inno yanzu abin da kuka yi kun kyauta kenan? Wai dan Allah wacce masifar ce tasa bazaku barmu mu kaɗai mu kai Ɗanmu asibiti mu dawo ba? Yanzu  ki duba abin da kika yi mana da banje na shiga tsakaninki da Ɗan Karotan nan ba wayasan iya abin da zaiyi miki? Sai kace yau kika fara fita maganar gaskiya ni na gaji wani ne yake auran mata ta da za’a dinga mun bita da ƙulli haka kawai, ni mahaukaci ne bansan hukuncin da addini ya gindaya ba game da matar da bata da tsarki ne? Gaskiya na gaji zan yi wa su Daddy magana idan mun dawo, haka kawai tsofaffi ku dinga kaja mun kai, yanzu da ya lahanki wa kika jazawa idan ba su Daddy ba su yi da kuɗinsu da aljihunsu amma ku komai aka faɗa mutum baisan me yake yi ba sai ku.” Inna na gama jin haka bata furta komai ba ta rushe da wani irin matsanancin kuka harda majina.

   Halifa haushi ne ya kuma kamashi ya kalleta da gefen ido yace. “Ba kuka ba ko kukan jini zakiyi Inno sai kun bar mini gidana ke da Goggo.” Goggo leƙowa tayi da niyyar yi wa Halifa masifa suna haɗa ido da Jaririn Nusaiba dake hannunta ya washe mata baki yana gyaɗa kai,  ganin ya miƙo hannu yana niyyar taɓa haɓarta Goggo da sauri ta ja baya tana faɗin.

    “Wayyo Allah ku agaza mini yau zai mini sabon salon salawaitu a haɓar baki na, dan Allah ku buɗe mun zan fita kar ya sauke mini haɓa na rasa bakin tauna” A hargitse suka jiyo dan ganin abin da yake faruwa, Halifa dafe kai ya yi ya tada motarsa da gudin tsiya a fili yana furta. “Innalillahi wa’inna’ilahirraji’un.” da ƙarfi ya daki sitiyarin motarsa sannan ya ce. “Wallahi Goggo idan kuna alaƙanta Ɗana da wata manufa zaku ga ɓacin raina. Kuma ba haɓa ba idan fuska zai sauke miki sai dai ya sauke amma tunda na rufe motata bazan ƙara buɗewa ba.

   Jaririn na jin haka ya washe baki yana zaro idanu ya kuma ɗaga hannu da niyyar shafo haɓar Goggo Inno dake gefe tana matsalar ƙwalla ta hango dan gudil ɗin hannu, Inno gefe ta ja tana dafe ƙirji tana shirin kurma ihu ta hango hannunsa yana miƙowa caraf taji ya sa hannunsa cikin rigarta.

    Inno kallan Goggo tayi ta rushe da kuka ta ce. “Dan Allah ku taimaka mini zai nuna mini rashin ɗa’a wallahi wannan ɗiban Albarka ya yi yawa nikam yau naga ta kaina zai ɗaye mini ƴan matana biyu” Kamar alamara taji Jaririn yace. “Inno zan sha Mama”

  Inno ciki kuka ta ce. “Banda shakiyanci da ɗiban albarka me zaka yi da ƴan mata na abu duk fata, yooo Allah na tuba yaushe rabona da shayarwa sama da shekara talatin idan ba fatar zaka ɗaɗɗayemun ba…? Inno bata ƙarasa magana ba taji Halifa ya kashe Motarsa ya buɗe  yana yiwa Nusaiba magana akan ta fito su nifa ward ɗin da ake alluran yaran. Nusaiba rungume da Jaririnta ta fice tana fita ya sawa ƙofar mukulli.

   Goggo waro ido waje tayi ta na gani Jaririn dake hannun Nusaiba da wanda ya maƙale a hannun Inno, tana shirin yin magana Jaririn yace. “Inno ki bani Mama ko na fisga ta karfi na sha”Inno cikinta ne ya karta take hankalinta ya tashi hannuwa bibbiyu ta naɗe a ƙirjinta tana tura ƴan yatsunta ƙasan hammatarta, da ƙarfin gaske Jaririn ya buga tsalle suka fara kiciniya shi da Inno, Inno sai maƙale hannuwa take Jaririn yana ƙoƙarin fisge hannuwa yana faɗin, “Ai dama nace sai nasha ko da tsiya ne” Goggo da ke gefe jikinta banda tsuma babu abinda yake yi ganin halin da ƴar uwarta take ciki yasa ta fara ihu. “Jama’a ku kawo mini salawaitun taimako kar ƴar uwata ta ɓalɓalce a hannun wannan salawaitun hatsabibin, wai babu me ji na ne ku kawo mana salawaitin taimako Jariri zai hallaka mini ƴar uwa.” Goggo tana yi tana waigen gurin da Jaririn yake dan kar itama ya kawo mata farmaki.+

    Inno banda kokawa babu abin da suke yi gabaɗaya ta haɗa uban gumi, tun da ƙwarinta har ta fara gajiya gabaɗaya ta saddaƙar da Jariri zai turmushe ta, yaye Hijabinta tayi tana banƙaro masa ƙirji ta ce. “Kai kaci ƙwal ubanka wai ba ɗiban albarka ce zaka gwada mini ba, Indai fata ce gata kayi ta sha idan ma cinyewa zaka yi ma kayi gabaɗaya, yooo dama me yayi saura Allah na tuba banda fata abu kamar ledar nafkin, ka ƙarasa ni kawai ka huta ƴaƴana kuma suyi ta ɗebe maka albarka har ƙarshen rayuwarka ja’iri maras ɗa’a…” Inno tun bata rufe baki ba Jariri ya buga tsalle kansa har yana buga saman motar, dafe ƙeya yayi ya fara wata irin rawa yana tura ciki gaba yana cewa. “Ta bani dama ehh! In tsinke abubuwan ehh! Ƴan matan Inno in zuge su ehh! Intatse su ehh! In haɗiye su ehh” yana rufe baki ya warto Maman Inno yana shirin kaiwa baki Inno tayi ta maza ta hankaɗe shi ta fisge rufe idonta tayi ta dinga kai duka ta ko’in.

   Yadda Inno take  kai duka hannunta sai wurgi take da Jaririn yana sama yana ƙasa kamar wani tamola, Goggo mutuwar tsaye tayi tana kallon Ikon Allah ace wai Jariri sabuwar haihuwa ne ake wannan ɗauki ba daɗin da shi. Goggo tana san taimakawa Inno tana tsoron karya dawo kanta, haka dai tayi ta maza itama ta runtse ido ta dinga kai masa duka har da ɗan ihunta. Jaririn na ganin haka ya ja da baya ya ɗare kan sitiyarin motar, ya wara ƙafafuwansa akai yana wani irin rangaji haɗe da zaro musu idanu  yana kaɗa harshe, yana nan daga tsaye sai ga fitsari tsiiiii tun dana inda yake tsaye har zuwa kujerar baya gurin da su Inno suke, haka fitsarin nan ya tarar da su.

STORY CONTINUES BELOW

   Cikin haɗin baki suka rafka salati Goggo harda tafa hannu Inno tace. “Yau naga abin da ya tsone idon kakata Laure mu kam mun gamu hatsabibin aljani maras ɗa’a, banda ɗiban albarka ya za’ayi ka fitsaremu kamar waɗanda aka ɗebewa albarka.” Goggo ta rushe da kuka tana fyace majina sannan ta ce. “Tun da ubana Me salati ya haifo ni ban taɓa ganin salawaitin siddabaru irin wannan ba, anya wannan Jaririn bazai kashemu ba kafin mu koma gida ba, ji yadda yake salawatun fitsari ido biyu kamar ɗan Kafirai. Kai amma wallahi ancuci jikata Nusaiba wallahi da biyu wannan Ɗanƙundalon da ta haifar mana badai tayin Nusaiba ba sai dai a tayin Halifa cen, daga ni har ƴaƴa da jikoki babu mai irin wannan salawaitin sheɗancin…”

    Tun Goggo bata rufe baki ba Inno ta ce. “Aniya bi aniya. Aniyarki ta koma kanki badai jikana ba wallahi cen sai dai daga jikin Nusaiba aka kwaso wannan ƙamayamayar, ai wallahi anyi ɗaya ba ƙari baza’a ƙara wannan ɗiban albarkar dani ba, haka kawai jikana ya dinga haifar ƴaƴa marasa ɗa’a irin wancen. Babu ko tantama idan muka koma dole nasa Salisu ya raba auren nan ko na ɗebe masa albarka kowa ma ya huta.”

   Goggo tana tafa hannuwa ta ce. “Ahayye tafi nono fari wallahi ko baki faɗa ba sai Halifa ya miƙo salawaitin takardar Nusaiba, kuma babu inda zata je da wancen Ƙunduss ɗin dan bazamu iya da salawaitun iskancinsa ba, dama kuma ba da shi muka aura masa ba sai ku riƙe tsiyarku cen ku ƙarata da salawaitun hatsabibancinsa.” Goggo ta ƙarasa faɗa tana nuna Inno da ɗan yatsanta.

   Inno ta rushe da kuka ta ce. “Hansai yau ni kike yiwa ɗiban albarka da rana tsaka saboda rashin ɗa’a, to wallahi indai nina haifi Uban Halifa auren Nusaiba da Halifa kamar ankashe shi ya mutu, zan nuna miki rashin ɗa’a da ɗiban albarka. Ke wallahi ba dan ina duba zumuncin Allah ba da tuni na ɗebe miki albarka kowa ma ya huta, to ina duba wasiyyar Me salati shiyasa kai Allah ya dai ya gafarta musu amma kedai Hansai albasa batayi halin ruwa ba.”

   Goggo ta ƙara shewa ta ce. “Sai dai mu ɗebewa juna dai, dan nafi ƙarfin ki mun salawaitu ina kallonki, sannan kuma ai…” Wata uwar ƙara Jaririn ya ƙwala wacce tayi sanadiyar katsewar maganar Goggo ba dan tayi niyya ba.

    Gabaɗaya nutsuwarsu suka shiga nan take jikinsu ya hau tsuma. Jaririn yana kan sitiyarin motar suka ga ya zura hannunsa cikin ƙwayar idonsa ya ƙwaƙwulota sai ga ƙwayar idonsa a tafin hannunsa. Sama ya dinga jefata yana caɓewa. Inno da Goggo nan take cikinsu ya fara ƙugi saboda tashin hankali har ana iya jin sautin ƙugin cikin nasu.

    Buɗe bakinsa yayi ya jefa shi ciki ya fara taunawa, Inno wani irin ihu tayi ta janyo Goggo suka rungume juna kowacce jiki sai karkarwa yake. Wata uwar tsawa ya buga musu yace. “Maza-maza ku saki juna ko na ƙwaƙwale idanuwanku na haɗiyesu yanzun na” tun bai rufe baki ba suka saki juna Goggo ta ce. “Kayi mana rai Ɗan nan karka yi mana salawaitun abin da ka faɗa…” da ƙarfi ya katse ta da cewar. “Ta kanki zan fara bani salawaitin na cinye kafin nazo kanki”

    Goggo ta zaro ido waje ta ce. “Ita salawaitun zan baka?” Jaririn yace. “Ita zaki ban ko na fara karyar gaɓa-gaɓar jikinki ina cinyewa.” Goggo ta fara matsar ƙwallah ta ce . “Yaro wannan salawaitun tun da ƙuruwaciya na wayi gari da ita bansan ya zan fasalta maka salawaitun bayanin ba”

   Inno ta kalli Goggo da tayi jage-jage da hawaye da majina ta ce. “Banda abin ki ba sai kiyi masa bayani dalla-dalla ba kya yi masa rashin ɗa’a ai sai ki ja ya ɗebe miki albarka” Jariri ya kalli Inno yace. “Kema ina tafe gurinki ki bani ɗiban albarkar da rashin ɗa’ar” gabaɗaya shiru sukayi kamar wanda ruwan ya shanye.

   Tsalle ya ƙara bugawa yace. “Naji kunce iyayena sai kun raba aurensu to naga wanda zai fita daga motar.” Yana gama faɗa ya murza sitiyarin motar da ƙarfi nan take mota ta tashi ya fara tuka ta da gudun gaske, Inno da Goggo banda gware da kawuna babu abinda suke yi da ya fisgi motar zaka ji kansu ya bada ƙwal sai kaji sun rafka salati, tun baiyi tafiya me nisa ba Inno ta sume a cikin motar.

Halifa na fitowa harabar gurin ya nemi motarsu ya rasa gabansa ne ya faɗi, suka kalli Juna shi da Nusaiba da take jijjiga jaririnta saboda kukan allurar da yake yi,  Halifa da sauri ya ɗauko wayarsa ya fara kiran Inno amma ba’a ɗauka ba, ya kira yafi a irga sannan ya kira ta Goggo sai da ta kusa katsewa ta ɗauka, cikin  fargaba Halifa yace. “Goggo lafiya naga babu motar kuna ina” Goggo muryar ta da ƙyar take fita saboda wahala ta ce. “Halifa ku kira ƴaƴa da jikoki ka sanar da su mutuwarmu ataru ayi mana addu’o’ domin tamu tazo ƙarshe” Halifa yace. “Waye ya ɗauke ku ne wai?” Goggo murya a shaƙe ta ce. “Jaririnka ne ya ɗauke mu yanzu haka sai fafara salawaitun uban gudu yake, ni da kake gani nayi salawaitun suma yafi a irga babu me tayar dani wahala ce kawai take farfaɗo da ni. Ga Inno dai yanzu kam nasan matambaya har sun dira kanta…” Tun bata gama maganar ba Jaririn ya fisge wayar ya kasheta gabaɗaya.Halifa ji ya yi jikinsa ya yi sanyi tun daga tsakiyar kansa har zuwa tafin ƙafarsa, ji yake kamar ƙafarsa bazata iya ɗaukansa ba. Kiran wayar ya ƙara yi nan take ya ji ta a kashe, Nusaiba ta tambayeshi me yake faruwa. Sai da ya ɗan jingina da bango sannan yace. “Wai kinji Jaririnmu ya tafi da su a mota” zaro ido waje tayi tana daɗa kallan Jaririnta ta ce. “Banda wanda yake hannuna yanzu? To a ina na taɓa ji Jariri yayi tuƙi idan ba aljani ba” Halifa yace. “Gaskiya lamarin ya fara bani tsoro wallahi, anya kuwa babu shafar aljanu a jikin su Inno amma ta yaya su kaɗai a mota za’a neme su a rasa alhalin babu mukulli a hannunsu.” Halifa ƙarasawa ya yi gaban wata kwantaina ya yi wa ma kwantainar sallamar sannan yace. “Dan Allah Malam ka lura da wata mota fara bakin glass a gurin da nayi parking, ko ka ga wanda ya buɗe ta?” Me kwantainar yace. “Gaskiya Abokina ban lura ba tunda ka ga nima a bakin neman kuɗina nake” jiki a sanyaye Halifa ya yi masa godiya ya koma gurin da ya bar Nusaiba a tsaye. Jigun-jigun sukayi aka rasa me magana Nusaiba tayi ƙarfin halin cewa. “Habibi me zai hana ka kira su Daddy ka sanar da su wannan fa ba ƙaramar magana bace.” Fuska ɗauke da damuwa yace. “Wallahi ina fargar sanar da su saboda Abba da Daddy kinsan kowanne  na da hawan jini bansan ma ta ina zan fara sanar da su ba, kinsan dai kowa zan gayawa abin da Goggo ta faɗa bazai yarda ba  to ni me ma zan ce musu? Cewa zan Jariri ya ɗauke su a mota ko me?” Nusaiba ta sauke ajiyar zuciya ta ce. “Habibi tafasar tukunya fa ba ta gefe ɗaya bace wannan ba maganar da zamuyi shiru bace, ya zama dole su Daddy su sani.+

    Hannu ya zura a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kira lambar mahaifinsa, sai da ta kusa katsewa yaji anɗauka. Kamar me ciwon baki haka ya buɗe baki a hankali yace. “Daddy barka da safiya” daga cen ɓangaren Daddy ya amsa sannan Halifa yace. “Daddy dama nace dama… dai..” Daddy yace. “Halifa lafiya kuwa duk naji ka wanj iri” Halifa ƙarfin hali ya yi ya sanarwa da Daddy halin da ake cikin, cikin tashin hankali Daddy ya dinga maimaita, ” Innalillahi’wa ilahirraji’un” Daddy ya ci gaba da cewa. “Yanzu kuna asibitin ne?” Haliha yace. “Eh muna cen Daddy” Daddy yace. “Ka nemi securities ka sanar da su abin da ya faru dan suyi gaggawar sanarwa da hukumar asibiti yanzu zan kira Yusuf na sanar da shi halin da ake ciki daga nan zanje Bompai nayi report, inyaso sai ku wuce gida” Daddy bai jira cewar Halifa ba ya katse wayar.

   Kamar yadda Daddy ya gayawa Halifa haka ya samu securities ya sanar dasu nan take maganar ta zagaye cikin asibitin, Halifa da Nusaiba adaidaita sahu ya tarar musu suka wuce cen gidan Mahaifinsa, lokacin da suka je suka samu mutanen gidan duk sunyi jigun-jigun saboda tashin hankali.

   Lokacin da Jaririn ya fisgi wayar hannun Goggo kusan mutuwar zaune tayi, gashi sai fafara uban gudu yake dasu kamar zai tashi sama. Goggo tun tana iya ihu har tayi laƙwas ga kanta da ƙeyarta duk ta gwabje da jikin motar, daga gefen goshinta har kumbura gurin ya yi.

    Kai tsaye bai wuce ko’ina da su ba sai gidan Halifa yana yin parking da sauri ya sauka ya fita, Goggo bata iya komai sai ido da take binsa da shi tana kallan ikon Allah, yana zuwa bakin ƙofa ya kallin kwaɗon da aka rufe gate ɗin yasa baki ya fisgoshi memakon ya wurgar dashi sai kawai ya haɗiye, Cikin Gwaggo ne ya hautsine, nan take ta fara sakin fitsari jikinta na karkarwa.

    Daga gurin da yake ya buga tsalle kamar ƙwallo sai gashi a cikin motar yana shiga ya fisgi motar ya wuce cikin gidan da gudu, wannan karan Goggo kan Inno ta faɗa saboda yadda ya fisgesu da ƙarfin gaske, yana shiga ya yi parking ya yi tsalle ya fito daga motar hanyar falon Nusaiba ya nufa yana dafe ƙeya haɗe da tura ciki gaba yana wata irin shakiyyar rawa, kamar wani ɗan ƙwaya haka ya dinga layi sai ya yi gaba sai ya dawo baya har ya shige gida. Goggo duk yadda taso buɗe motar abin yaci tura wayarta ta hango a cen gefe da sauri ta ɗauka ta kunna ta, sashen kira ta nufa tana danna labar tayi dace da lambar Halifa, bugu ɗaya taji an ɗauka.

    Goggo ƙasa tayi da murya kamar me raɗa ta ce. “Dan Allah ko waye a layi ya gaggauta zuwa gidan Halifa ya ɗauke mu nida ƴar uwata” Halifa yasan dai Goggo magana take yi amma sam bayajin me take faɗa. Da sauri yace “Goggo ce? Yanxu kuna ina?” Goggo satar kallan ƙofar da Jariri yabi tayi cikin raɗa ta ce. “Halifa ba sanya zakuyi ba kuzo ku fitar dani dan ƴar uwata tuni nasan matambaya sun dafe ta” sai a lokacin Halifa yaji shima sai da yasa a speaker.

  Da murnarsa yace. “To kuna ina yanzu zan zo” Goggo ta ce. “Gamu a gidanka idan kuka yi jinkiri nima sai dai ku ɗauki mushe dan Rakiya kam tuni tayi mushe” Halifa na jin haka ya katse wayar da murna ya fara sanarwa da mutanen gidan, Halifa da Adam ne suka taho gidansa.

    Halifa na zuwa ya tarar da ƙofa a buɗe da sauri suka shiga gidan, Halifa na zuwa bakin motar ya sa key ya buɗe da sauri Adam ya zagaya ya buɗe murfin motar ya tallafo da ta jima a sume. Goggo na ganin an buɗe murfin motar ta fito da sauri ko bi ta kansu batayi ba ta nufi bakin gate da guje, Halifa ne ya biya yana kira ta waigo ta ce. “Har abada na bar salawaitun gidanka da motarka gwara na shiga duniya na yi mushe a hannun ɗan iskan salawaitun gidanka.” Tana rufe baki ta bazama waje a guje Halifa ya rufa mata baya.

????  KU TARO GOGGO KAR TA FAƊA SALAWAITUN RAYUWA A ƊEBE MATA ALBARKA

About AIS

Check Also

JARIRI CHAPTER 5 BY AMEERA ADAM

JARIRI CHAPTER 5 BY AMEERA ADAM Www.bankinhausanovels.com.ng  Jariri na ganin haka ya tuntsire da dariya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *