JARIRI CHAPTER 1 BY AMEERA ADAM

 JARIRI CHAPTER 1 BY AMEERA ADAM

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Fuskar Halifa ɗauke da damuwa yace, “Inno gaskiya zuwa gidan Nusaiba da matsala saboda ko kaɗan banasan tayi nesa dani, na shaƙu da matata banasan ko nan da cen taje kawai kuyi haƙuri ku barta a nan” Inno ido ta zura masa tana ganin rashin kunyar ƴaƴan zamani ido biyu, kafin tayi magana Goggo ta karɓe zancen da, “Ka ji mun yaro da sabuwar salawaitun  fitsara ido biyu, mu zaku gwadawa fitsara da rashin kunya? Munga tantabaru ma wajen soyayya yaran yanzu da komai sai sun nuna rashin kunya a ciki, mun ƙi mu bar maka ita sakarai kawai” Inno ta ce, “A’a barshi Hansai ya nuna mana ya kusa haɗa kafaɗa da mu, tunda ya kusa ajje ɗa kinga mun haihu shima ya haihu ai mun zama ɗaya da shi, fitsararre mai idanun marasa ɗa’a dubi yadda yake fiƙi-fiƙi saboda ɗiban albarka” Nusaiba da ke gefe ta zumɓuri baki gaba ta ce, “Ni dai gaskiya Inno ku ƙyaleni a nan inyaso wani a cikinku yazo ya zauna mun”+

    Nusaiba na rufe baki Goggo ta ce, “La’ilaha’illallahu Muhammada ɗan Abdullahi, Inno kinji ɗibar albarka da yarinyar nan zatayi mana irin ta yaran zamani, kinji Nusaiba ta zaɓi miji akan gidan ubanta, ke dan Ubanki ni zaki nunawa rashin kunya ido biyu, idan ban kwashe miki albarka ba kice bani bace?” Halifa ya ce, “Goggo abun fa bai kai haka ba, saboda Allah zuwa gidan nan yayin haihuwa ba fa dole bane ku barmun matata a gida mana, ina jin ɗumunsu ita da abinda zata haifa amma kunzo sai kwashe mana albarka kuke, a haka zan barta taje wanka gida kuna kwashe mata albarka? Haba ina dalili.”

   Wannan karan Inno ce ta kuma rafka salati ta ce, “Tir da wannan halin naka na rashin ɗa’a amma dai Halifa na sai na kwashe maka albarka, wato jarabar taka ido biyu har agabanmu dan rashin ɗa’a? Wato mu bar maka yarinya inyaso ko arba’in bazatayi ba ka nuna rashin ɗa’a mujita da wani cikin ko?” Halifa hannu biyu yasa ya rafka tagumi saboda tsofaffun ba ƙaramin caja masa kai suke yi ba, cikin damuwa ya ce, “Inno wai dan Allah me yasa kunfiya matsala ne? Ni fa shiyasa wani lokacin ko ziyararku banaso saboda ba’a kwashewa ta daɗi da ku”

    Inno daƙuwa ta watsa masa ta ce, “Ubanka Salisu shine me matsala, kuma wallahi kamar a kunnensa zan kira uban naka a waya naji ko shi ya baka lasisin da zaka ɗebe mun albarka”  tashi yayi ya fice daga falon dan yasan indai ya cigaba da biye musu to tabbas zai hau sama da su.

    Nusaiba da sauri ta tashi tabi bayan mijinta bisa tsautsayi ta harɗe ta faɗi, nan take ta fara naƙuda ba shiri suka fara ƙwala masa kira, hankali a tashe ya dawo suka kamata suka sakata a mota suka wuce asibiti.

   Zuwan su asibiti da awa guda Allah ya sauki Nusaiba lafiya ta haifo ɗanta namiji kyakkyawa da shi, Nurse ɗin data karɓi haihuwarce ta fara goge jaririn amma wani abu daya ɗaure mata kai, yadda jaririn ya ƙura mata idanu ba kiftawa har hannu tasa ta rufe masa ido amma ƙir idanunsa a kanta, idan ba musu idanunta suke yi mata ba kamar ma harararta ta ga jaririn yana yi. A haka ta samu ta gama gyarashi da gurin aka sa masa kaya Nusaiba ta rungume abinta suka koma bacci, kafin wani lokaci tuni ƴan uwa sun cika asibitin kowa xai zo hannunsa ɗauke da kullar abinci yake shigowa, gudun hayaniyarsu yasa nurses suka hanasu shiga ɗakin da Nusaiba take saboda karsu hanata bacci.

    Bayan wani lokaci, Nusaiba ce ta tashi gabaɗaya yunwa takeji cikinta kamar anmata yasa, batasan da kawo abincin da akayi tana bacci ba dan haka ta ƙwalawa Nurse kira, tana zuwa tace ta kira mata su Inno da sauri ta fita ta sanar musu da saƙon Nusaiba, su Inno tare da sauron ƴan uwa ne suka shigo ɗakin fuskarsu ɗauke da farinciki, wasu daga ciki ne suka ɗau jaririn, Nusaiba a shagwaɓe ta ce, “Inno yunwa fa nake ji ku haɗa mun ruwan tea” Inno ita da goggo da ƙarfinsu suka nufi wajen kullar amma tunkafin su buɗe sukaci karo da tsottsatssen ƙashi da wanda aka taune akan murfin kular, suna buɗe ƙatuwar kular abinci yace ɗaukeni inda kuka ajiye.

    Ledar ƙaton buredin ma cen ƙarƙashin gado suka hangota, da alama anciye biredin iskar fanka ce ta tura shi cen ƙasan gadon, mamaki ne ya kamasu amma babu wanda ya magantu a cikinsu, Inno ce ta ɗakko flask ɗin shayi shima ta jishi shafal ba komai a ciki, a hassale ta fara magana. “Yau naga rashin ɗa’a ido biyu ni za’a gwadawa ɗiban albarka. Waye ya cinye abincin da shayin gurin nan?” Goggo ta ce, “Gane mun hanya yarinya ta haihu madadin taci ta ƙoshi gashi wasu ƙarti sun cinye”

    Da mamaki Mahaifiyar Nusaiba ta ce, “Inno duka abincin kulolin aka cinye? To Nusaiba ko kinci abinci ɗazu?” Nusaiba ta girgiza kai, Inno ta ce, “Banda rashin ɗa’a Nusaiba duk cinta ai bazata iya cinye cooler uku ta abinci ba, maza kiramun masu fararen kayan cen gabaɗaya sai na kwashe musu albarka banda su babu me aikata wannan rashin ɗa’ar, yara sai rashin ɗa’a da ɗiban albarka kamar ƴaƴan mayunwata.” Mami mahaifiyar Nusaiba ta nufi mazaunin Nurses ɗin ta kira suka taho tare dan su a tunaninsu wani abun ne ya samu Nusaiba, suna zuwa Inno ta kalle su ɗaya bayan ɗaya ta ce, “Ina kuka kai abincin gurin nan saboda ɗiban albarka yarinyar nan ko loma ɗaya batayi ba, idan sha’awa ya baku basai ku tambaya a baku ba amma zaku nuna mana halin rashin ɗa’a wato sai kunci na Allah ya isa ko?” kallan juna suka farayi kamar haɗin baki suka ce, “Wane irin abinci ana zaune ƙalau kamar wasu mayunwata” Goggo kulolin ta janyo tana cewa, “Gasu naga ɗazu ke kika taya ni shigo da wata” ɗan zaro Ido sukayi suka ce, “Duka abincin cikin kular aka cinye” Inno ta ce, “Kiji mun shakiyyan yara marasa ɗa’a tambayarmu ma kuke yi, wallahi ko ku fito dashi ko na ɗebe muku albarka ku bi duniya”

    Ɗayar nurse ɗin ce ta ɗan fara ɗaukan zafi ta ce, “Iya wai me kuka ɗauke mu ne saboda kuma muna ma’aikatan jinya duk wata ƙura aka ɗebo sai a watsa mana…” Inno a hassale ta katseta. “Amma kedai wannan yarinyar anyi maras ɗa’a wallahi idan baki rufen baki ba zan kwashe miki albarka ki ɓalɓalce ” ganin abun na nema zama faɗa Mami ta sasanta tare da yin waya gida akan a ƙara kawo musu wani abincin.

     A yammacin ranar aka sallami Nusaiba ita da Jaririnta, tun a asibiti ake taƙaddama akan zaman Nusaiba a gidan ita Mami ma shiru tayi saboda yadda su Goggo suke ja’ina da Halifa amma fir yaƙi yarda. A hassale Goggo ta ce, “Rakiya wai dole sai mun bi ta yaron nan ne? Shi da ita duk jikokinmu ne me zamu zauna muna bi ta tasu, ni idan ya bari idanma bai bari ba zan ɗauke ta na wuce gurina da ita.” Inno sheƙeƙe ta ce, “Hansai au ke zaki tafi da Nusaiba? Wallahi bazan yarda da wannan ɗiban albarkar ba nice na haifi Uban Halifa ni nake da iko da wannan maganar” Goggo ta ce, “Rakiya wallahi baki isa ba nina haifi Uban Nusaiba dan haka nina fi dacewa da tafiya da ita” Inno ta ce, “Ahayye Allah na dawo inji kishiyar me yaji, wallahi baki isa kizo mun da wannan rashin ɗa’ar ba,  ninan gurina zan wuce da ita.” Halifa ne ya shigo yaji yadda suka fara hawa sama a tsakaninsu dukda sun kasance ƴan uwa kuma aminan juna, Halifa ya fahimci sarai inda maganarsu ta dosa yace,”Nifa gaskiya babu wanda zai ɗaukarmun mata wai magana ɗaya ayita yinta har a asibiti ina dalili, idan fa kuka takura zau ɗauke matata na kaita wani gidan nawa inyaso na samu wacce zata dinga kularmun da ita ” Inno ta ce, “Oh La’ilaha’illallahu muhammad rasulillahi sallallahu’alaihi wasallam, oh ni ɗiyar mutum huɗu ba ko ɗaya naga abinda ya tsirewa kakata Laure ido, yanzu ɗibar albarkar da zaka mun kenan Halifa wani bari ubanka ya zo ya shata mun layi da kai, kai anya ma wannan ba’a sauyawa Salisu kai a asibiti ba?”  Mami ce ta ce, “Inno dan Allah kuyi haƙuri ku bar masa matarsa tunda har yace bayasan taje gida wanka, shawara ɗaya zan bayar gabaɗaya kuje ki zauna mata ai ina ga hakan yayi?” gabaɗaya sun aminta da shawarar Mami, Inno ta ce. “Hansai kinga gwara da akayi hakan dan kinsan ni yanzu bana iya aiki a bakin wuta, na dinga kula da aikin cikin gidan kina ɗora garwan wankan mejego da jaririnta idan ba haka ba kar naxo na aikata rashin ɗa’a” Goggo ta ce, “Eh kuma fa hakane Rakiya kinga zamanmu bibbiyunma zaifi.”

   Da wannan shawarar suka tarkata zuwa gida tare da ƴan uwa da abokan arziki.

     A daren ranar da suka koma da daddare kimanin karfe biyun dare Inno ce ta fito fitsari ahanyarta ta dawowa, ta hango ƙaƙanin abu na tafiya idan yayi gaba sai ya dawo baya ya rangwaɗa kai gefe. A ɗan tsoroce Inno ta ce, “Toooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da tsohon daren nan” ta ƙarasa magana tana haskashi da ƴar fitilarta.

    A zabure ta ja baya ganin jaririn Nusaiba ne tumɓur ko wando babu, washe mata baki yayi ya dafe ƙeya yana wani irin layi kamar wanda yasha ya maku, cikin wata irin murya ya cafe irin maganar Inno yace, “Tooo yau wacce irin ɗiban albarka nake gani da tsohon daren nan” tana faɗa yana wani irin tsalle kamar zai faɗo kan Inno, wurgar da butar tayi saboda tsoro ta fara gudu. Tsalle yayi ya caɓe zanin Inno har ya taɗe ta ta faɗi da rarrafe ta dingan rarrafawa tana ƙwala ihu, lokacin da ta ƙarasa ɗakinsu tuni ta daɗe da wurgar da zani daga ita sai ɗan fatarinta.Inno kan katifar da Goggo take kai ta faɗa jikinta na ɓari tana ƙoƙarin fisgar bargon saboda ceton  ranta, Goggo wani uban salati ta rusa wanda yasa Nusaiba miƙewa zumbur ta tashi zaune, Inno banda ihu babu abinda takeyi tana kabarbari.+

   Cikin magagin bacci Goggo ta ce, ” Oh nikam na shige su yau me nake ji kwarto da tsohon daren nan, yo ni Allah na tuba banda lalacewar kwaratan zamani  me zai yi  da tsohuwa? Gabaɗaya komai ya saki kamar robar wando…” bata ƙarasa faɗa ba Inno ta ruƙunƙumota sakamakon buɗe bargon da tayi sukayi ido huɗu da jaririn da yake ta washe mata wawulan bakinsa yana ƙara dafe ƙeya, haɗe da wata irin tafiya me tafe da rangwaɗa.

   Goggo ta kuma mirtsike idanu ta ce, “A’uzubillahi minasshaɗanirrajim Rakiya tashi kiji yau za’a nuna mun salawaitun iskanci ido biyu, oh ni ɗiyar Mahammadu ka rasa wacce zaka afkawa sai ni tsofai-tsofai da rai wannan ai sai dai ka kasheni da raina.” Nusaiba ce ta janyo wayarta da ke ƙasan fulo ta haska gurin su Inno. Ganin Goggo da Inno kaɗai a gurin Nusaiba taja tsaki ta ce, “Dan Allah Goggo da tsohon daren nan zaku dinga mana ihu ba sai a zaci da gasken kwarto bane ya shigo” Firgigit Goggo ta mirje ido raɗau ta kai kallanta kan Inno, a hassale ta fisge bargon ta ce. “Rakiya wani sabon salawaitun kika samo zaki hau wani fisge-fisge cikin dare?” Inno tana ƙoƙarin ƙara danna kanta cikin bargo ta ce, “Karki buɗe ni Hansai yana nan bina yake wallahi aljani ne ba mutum ba” Goggo ta ce, “Yo nikam yau na gode Allah Inno wai ko gamo kikayi ne?”
  Inno ta gyaɗa kai har lokacin jikinta rawa yake ta ce, “Wallahi Jaririn Nusaiba ba mutum bane aljan ne shi ne ya biyo ni”  Da mamaki Nusaiba ta kalli jaririnta dake kwance yana shaƙar bacci ta ce, “Wai Inno ko dai mafarki tayi ne take mana magagin bacci har da sumbatu?” Goggo ta ce, “To gane mun hanya dai ƴar nan?” Nusaiba zata yi magana Halifa ya shigo sanye da jallabiyya da waya a hannu yace. “Nusaiba lafiya nake jiyo ihun Inno?” Goggo ta ce, “Ina fa lafiya gamu a zaune cikin taraddadi da salallami” zaro ido ya yi yace. “Me yake damunta?”
  Goggo ta ce, “Wai jaririn cen ta gani ya biyota shine ta zo ta shige bargo ni bansan wane irin salawaitu bane, ace jariri ya taka ƙasa kwana ɗaya da haihuwa.”  Halifa yace, “Ruɗewa ce kawai irin ta Inno amma wannan ko ɗan goye ai bazai yarda da abinda ta ce ba. Ku rarrasheta kunsan dai halinta da raki” Inno ta ɗago da kai ta ce.

   “Halifu wallahi wannan ɗiban albarkar baza’ayi dani ba, maza ka kira mun ubanka Salisu a daren nan yazo ya ɗauke ni mu tafi gida, wannan rashin ɗa’ar har ina?” Halifa yace, “Haba Inno kinsan me kike faɗa kuwa karfe biyun dare fa. Gaskiya ni bazan kira Daddy yanzu ba haka kawai a tayar musu da hankali, ki dinga abu da lissafi mana” Inno hawaye ta fara yi ta ce, “Halifa ni kake gayawa haka saboda nazo gidanka ko? Yoo wace uwa ce ma a gidan naka gida kamar akurkin kaji, kasan gidan Salisu ya zarce naka ɗari bisa ɗari har kake wulaƙanta ni saboda ɗiban albarka. Har abada bazaka ƙara ganina a gidanka ba, ai laifin Salisu ne da na dage zan zauna wankan jegon nan ba sai ya mun nasiha ba a matsayinsa na ɗana, Allah na tuba tsofai-tsofai dani banda rashin imani wane irin zaman wanka zanyi yanzu, ai Halifa kaine ma babban mara imani na tabbata da uwarka Halima ce ta kai shekaruna bazaka bari tayi wannan aikin wahalar ba, wallahi idan baka kira mun Ɗana ba sai na kwashe maka albarka a daren nan kowa ma ya huta.” Halifa ya tsuke fuska yace, “Inno dan Allah dare ne fa yanzu karki tashi moƙota ki bari zuwa safiya inyaso duk yadda za’ayi sai ayi, amma sai magana kike da ƙarfi haba dan Allah dama akwai wanda ya miki dole ki zauna ne?”

STORY CONTINUES BELOW
    “Hansai dan Allah ki ɗauko madoki ki bashi duka na kawai ya rage kayi Halifa, wallahi duk masifarka babu mai hanani tafiya a daren nan shima uban naka zan kirashi idan yace bazai zo ba nayi tafiya ta cikin duniya. Dama wa nake da shi Allah na tuba daga Allah sai ma’aiki” Nusaiba cikin ƙosawa ta ce. “Inno dan Allah kiyi haƙuri zuwa safiya idan fa aka kira Daddy yanzu sai ya ɗauka wani abun ne kinsan yana da hawan jini, kar a tayar masa da hankali a samu matsala”

     Inno sakin baki tayi lokaci ɗaya ta ɗauki wani salati gabaɗaya suka tsaya suna kallonta, sai da ta dire ta ce,”Nusaiba amma Allah wadaranki ke kam anyi gantalalliya bansan wacce irin yarinya bace me mugun alkaba’i, aniya bi aniya. Aniyarki ta biki Salisun kike ja wa wannan mugun ciwon saboda ɗiban albarka, to bakinki ya faɗa kanki muguwa kawai anya ke jinina ce kuwa kike nufina da sharri amma dai anyi maras ɗa’a” Halifa ya shigo ɗakin cikin takaici amma sai ya tausasa murya saboda yasan indai ta haka ne sai su kwana Inno bata daina musu sababi ba yace.

   “Inno waya hallicemu wa muke bautawa?”

   Inno ta kalleshi baki a sake ta ce, “Halifa kafurta ni zaka yi to wallahi ko Ubanka da addinin ya ganni bare kai gantalalle” Halifa bai kulata ba ya cigaba da cewa.

   “Ki dubi girman Allah Inno kiyi haƙuri zuwa safiya kinsan dai Allah yafi kowa, na haɗa ki da shi ki bari zuwa safiya mayi maganar”

   Inno ta ce, “Au Halifa haɗani zakayi da Ubangiji na? Wallahi ba dan Allah ba da adaren nan zan tafi kowa ma ya huta, tunda banida kowa babu mai ƙaunata.” Goggo ta fara matsar kwallah ta ce.” Rakiya karki mun haka saboda Allah idan kika shiga gari ina na kama ina zani wa nake da shi? Mu biyu kaɗai fa muka rage kema in kika tafi ya zanyi?” Inno ta taɓe baki tayi ta ce.

  “Hansai dama wace alaƙa garemu? To nasan dai uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya bayan haka fa? Da kinsan da haka kina ji Halifa na kwashe mun albarka kikayi shiru saboda rashin ɗa’a. Wallahi kunci daraja ɗaya amma zuwa safiya zanga uban da zai hanani tafi” Ta ƙara matsar kwallah ta ce.

  “Dama nasan Nusaiba ba ƙaunar zamana take ba waya sani ma ko ita ta turo ɗan ta ya tsorata dan na bar gidan jikana” Nusaiba zatayi magana Halifa ya ɗaga mata hannu yace.

   “Inno yanzu koma dai meye kiyi haƙuri badai Daddy kike so a kira ba? To Allah ya kaimu safiyar duk abin da kike so za’ayi.” Inno ta ce “Shikenan Allah ya kaimu kuma wallahi tas  a kunnensa duk ɗiban albarkar da kuka yi mun” tana gama faɗa ta koma ta kwanta.

    Goggo ma ta koma ta kwanta Halifa ya ƙarasa bakin gadon Nusaiba yana shafa jaririnsu cikin so da ƙauna, Goggo ta ɗago ta tafa hannu ta ce.

   “Halifa wata sabuwar salawaitun fitsarar zaka yi wa ƴar mutane a gabanmu, wallahi a hir ɗinka fita ka bamu guri ba nace maka yarinyar nan haramiyarka bace har sai tayi arba’in.” Halifa tsaki ya yi zai yi magana Inno ta ɗago ta ce.

    “Halifa wannan jarabar har ina kai amma gaskiya albasa batayi halin ruwa ba, lokacin da uwarka Halima ta haifeka sai da ta yi wata biyu cir a gidansu, zaka fice daga ɗakin nan ko sai na ɗebe maka albarka kowa ya huta?” Halifa kamar ya yi kuka saboda takaici Nusaiba zatayi magana ya mata alama da ido, cikin takaici ta gyara kwanciyarta ta kwanta Halifa ya fice yana ƙunƙuni.

    Washegari da sassafe Inno ta fito falo ta fara ƙwalawa Halifa kira, cikin bacci Halifa ya fara jiyo muryar Inno na kiransa. Guntun tsaki ya yi ya ƙara jan bargo ya rufa bai yi aune ba yaji ta fara buga ƙofarsa da ƙarfi tana cewa.

   “Halifa ka kira mun Ubanka kace ina nemansa maza-maza yazo” Halifa ba yadda ya iya ya fito fuska a tsuke ya karɓi wayar Inno ya nemo mata lambar mahaifinsa ya kira.

    Inno na jin an ɗauka babu ko sallama ta ce, “Salisu dan Allah maza kazo gidan nan ga ɗan ka sai tijara yake mun tun tsakar dare, kazo ka bi mun haƙƙina dan maganganun da ya gaya mun ƙiris ya rage ciwon zuciya ya kama ni, wallahi ko maƙiyina bana fatan a gaya masa kwatankwacin abin da Halifa ya gaya mini” daga cen ɓangaren Daddy ya ce.

STORY CONTINUES BELOW
   “Gaskiya bai kyauta ba amma kiyi haƙuri Inno me ya faɗa miki inyi masa faɗa” Inno ta saki baki ta kalli Halifa cikin ƙufula ta ce.

    “Allah ya tsinewa faɗan da zaka yi masa Salisu” nan take ta rushe da kuka ta ci gaba  da cewa. “Yanzu duk ɗiban albarkar Ɗanka ya mun a iya faɗa kawai zaka yi masa saboda rashin ɗa’a. Kayi zamanka na yafe dama na lura ba ƙaunata kake ba kafisan Ɗan akaina, wallahi daga yau Salisu ko a mafarki kar inƙara ganinka a gaba na. Ƴar uwata Hansai ta isheni rayuwar duniya dama tare kuka ganni da ita, Allah na tuba dama wacce tsiyar kuke bani. Ƴar uwata dama ita ce rufin asirina”

   Daddy yace. “Ayi haƙuri gani nan zuwa yanzu…” Inno bata jira ƙarashen zancen ta ba ta kashe wayar. Halifa na tsaye ya cika fam banda harara babu abin da yake aika mata.

    Inno kallan sa tayi sheƙeƙe sai kuma ta wuce kitchen ta ɗauko muciya, dai-dai ƙafafuwan Halifa ta zauna ta ajiye muciyar tace. “Idan baka mun duka ba ka raina ubanka Salisu kuma wallahi bari ya zo gidan nan a gaba na sai na sa ya kwashe maka albarka kowa ya huta” Halifa ya ja dogon tsaki yace.

   “Wallahi bari Daddy yazo bazan iya ba dama kece dolensa, haba wannan wane irin abu ne tun farar safiya ki addabi mutane” ya ƙarasa faɗa yana wucewa ɗaki. Inna baki sake tabi bayan Halifa ta ce. “Wallahi zaka maimaita a gaban ubanka bari ya zo.” miƙewa tayi ta wuce kitchen zata ɗora ruwan shayi.

    Bayan ta dafa shayi ƙatuwar tukunyar farfesun kaji ta ɗauko da niyyar dumamawa, amma sai jin tukunya tayi fayau. A razane ta buɗe tukunayar farfesu yace ɗauke ni inda kika ajiye, babu abinda ta gani sai taunannun ƙashi da romo ɗan kaɗan. Ture tukunyar gefe tayi ta fito ta rafka wani uban salati, gabaɗaya suka Fito hankali a tashe. Inno kallan Goggo tayi ta ce, “Oh ni jikar mutum huɗu yanzu Hansai ki rasa me zaki aikata sai wannan ɗiban albarka da nuna halin rashin ɗa’a” Halifa fuska ba walwala yace.

“Me ya faruwa kuma” ƙanƙance ido Inno tayi ta ce. “A hir ɗinka da shiga tsakanin zumunci, mara ɗa’a bada kai nake ba. Idan kuma na ƙara jin bakin ka wallahi sai na kwashe maka albarka, sai idan Ubanka yazo duk abinda zai yi ya mun” tana gama faɗar haka ta wuce kitchen ta ɗauko tukunyar kajin da ƙarfi ta direta a gurin ta ce. “Duba mun nan kajin da ka kawo jiya da yamma gasu nan Hansai ta cinye.” Gabaɗaya zaro ido waje sukayi Halifa cikin mamaki ya ce. “Kaji biyar ɗin dana kawo jiya sune aka cinye tashi ɗaya.” Goggo rushewa tayi da kuka ta fara ƙoƙarin ɗauko wayarta da ke cikin kajarta, tana ɗaukowa tace. “Halifa maza kara mun Uban yarinyar nan” Halifa jiki ba ƙwari ya karɓa ya nemo mata lambar mahaifin Nusaiba, yana ɗauka Goggo ta ce.

    “Nadabo duk abinda kake yi maza ka bari kuma ka taho da hukuma wallahi me rabani da Rakiya sai kotu tunda ni zata laƙawa sharrin maita.”
Yawan comments yawan typing ɗin ku. Har yanzu ƙofa a buɗe take ga masu san siyan littafin ANYA BAIWA CE? karku bari a barku a baya.
_UMMOU ASLAM BINT ADAM_
*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
*ANYA BAIWA CE?*

             Na

*AMEERA ADAM*
         
_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624, DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
FREE PAGE 2

          Da daddare Bayan sallar Isha’i Jakadiya ce tafe tana lalube har ta ƙarasa sashen Fulani Maryama, da sallama ta shiga  ta russuna tana cewa, ” Barka da hutawa Uwar ɗakina ance kina san ganina yanzun nan “
STORY CONTINUES BELOW
     Fulani Maryama dake tsaye hannunta ɗauke da  Salman miƙawa Jakadiya shi tayi ta ce, ” Jakadiya inasan muyi tafiyar sirri kamar yanda muka saba da ke a shekarun baya, ayau basai gobe ba zamu kai ziyara ga Boka Marduska, saboda bazan iya kwana da maganar da kika sanar da ni ba, batare na nemi mafita ba “
      Riƙe Salman Jakadiya tayi tsam kamar wani zai ƙwace shi sannan ta ce, ” Duk abinda kika ce haka za’ayi, bani da ikon bijirewa umarninki, da kai da kaya duk mallakar wuya ne “
        Fulani Maryama na gama jin haka ta juya ta shiga cikin ɗakinta, cen ƙasan adakarta ta buɗe ta ɗauko wani kurtu tasa hannu ta ɗebo waɗansu irin wuri guda biyu da wani ɗan ƙaramin zobe, maida kurtun tayi sannan ta dawo gurin da tabar Jakadiya ke tsaye.

      Miƙawa Jakadiya Wuri ɗaya tayi sannan ta fara karanta waɗansu irin ɗalasiman tsafi, ba’a ɗauki lokaci ba sai wani haske ya mamaye gurun atake suka ɓace daga cikin ɗakin.

       Tsaye suke abakin wani kogon dutsen dake cikin wani surƙuƙin daji mai matuƙar duhun gaske, Fulani Maryama runtse idanunta tayi ta fara ƙwalawa bokan kira har sau uku, ” Marduska! Marduska!! Marduska!!! ” tana gama faɗa ta buɗe idanunta.

       Ji sukayi ankece da wata mahaukaciyar dariya sai da aka ɗan ɗauki lokaci anayi sannan aka tsagaita, sannu a hankali haske ya mamaye gurin, cikin wata irin murya aka fara basu umarni, ” Ku sanya ƙafafunku cikin waccen ƴar ƙoramar sannan ku tako ku shigo ciki.

     Kamar yanda aka gaya musu haka suka bi umarnin mai magana sannan suka shiga cikin kogon dutsen, daga cen nesa suka hango shi zaune akan buzun damisa, gaba ɗaya jikinsa lulluɓe yake da gashi tamkar ba bil Adam ba, Fulani Maryama na gaba Jakadiya na biye da ita a baya.
  
        Zama sukayi sannan Fulani ta kalli bokan zata fara magana ya ɗaga mata hannu sannan ya kuma kecewa da dariya, sai da yayi mai isarsa sannan ya fara magana,

        ” Ai duk wanda ya bamu iska dole kwaɓarsa tai ruwa, Maryama kin ɗauke mana ƙafa na wasu shekaru sai da buƙatarki ta tashi zaki waiwayo mu “
      Fulani Maryama ta russunar da kai ta ce, ” A gafarceni sarkin bokayen duniya, nayi kuskure awancen lokacin amma yanxu baza’a sake ba “
       ” Na amshi tubanki kuma nasan abinda yake tafe dake, kalli nan ” ya janyo wata ƙwarya mai cike da jini yana nunawa fulani.

       Tana leƙawa Fulani Zaliha ta gani kwance akan gadon ta tana baccinta hankali kwance, jinjina kanta tayi ta cewa Murduska, ” Ya babban boka sarkin bokayen duniya so nake a salwantar da cikin da ke jikinta inda hali ma akashe su gaba ɗaya, domin bayan Salman bana san kowacce matar sarki ta sake haihuwa acikin su saboda bansan gaba mai zasu haifo ba kuma bansan mai hakan zata haifar ba “
    Ƙwala-ƙwalan idanunsa ya kafe ta dasu yana ce, ” Daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaƙi, badan kinzo ayanxu ba da tuni sauran damar data rage miki ta ƙare gaba ɗaya ” A zabure Fulani Maryama ta ce, ” Ban fahimce ka ba Marduska “
     Wani mudubin tsafinsa ya ɗauko yasa wata jelar ɓauna dake hannun sa na hagu cikin ƙwaryar ya yarfawa mudubin, inuwar wani ɗan ƙanƙanin Yaro ce ta bayyana na ɗan wani lokaci sannan ta ɓace, maida mudubin yayi gefe sannan ya maida kallonsa ga Fulani Maryama ya ce, ” Alƙalami ya riga da ya bushe, duk duniya babu wani ko wata da zai iya dakatar da cikin jikinta har sai ta haifeshi, Zata haifo Ɗa namiji Mai kama sak da Mahaifinsa kuma koda baki ci wannan Alwashin ba haihuwa ta dakatawa Sarki Aminullah, duk wacce kika ga ta kuma haihuwa sai dai in wani ne  mahaifinsa ba Aminullah ba “
     Cikin damuwa Fulani Maryama ta ce, ” Yanxu babu wata mafita da zaka bani ya Shugaba na?? “
     Wani Allon jar ƙasa ya ɗauko ya jingine ya na faɗan waɗansu irin kalmomi, yana watsa wani tafasashen jini dake cikin wani ƙoƙon kan Ƙwarangwal, yana cikin haka baiyi aune ba sai gani sukayi Allon jar ƙasa ya ruguje wani irin hayaƙi mai wari na fita daga jikinsa.

      A tsorace gaba ɗaya suka ja baya Marduska ba ƙaramin tsorata yayi da ganin faruwar haka, cikin yanayin firgici ya fara magana, ” Tabbas Ruhin wasu ababen hallita na katange da shi, idan na matsanta halaka shi ba mu ba hatta Aljanun da suke taya ni aiki sai sun halaka, maganin kar ayi kar afara inba haka ba wanda baiji bari ba yaji woho “
       Fulani Maryama jikinta ne ya gama sanyi amma duk da haka zuciyarta bata karaya ba ta ce, ” Marduska abar batun Halaka shi tunda ni kaina ganau ce ba jiyau ba, amma bayan haihuwar sa ba damar a aiwatar da wani aiki akansa ko a nakasa shi? “
     Matsawa yayi bakin wutar dake ci ya ɗebo wani garin magani mai haɗe da garin naman mage da haƙoran jemage ya zuba aciki, take wutar ta kuma tashi sama sannan wata ƴar ƙaramar ƙorama ta bayyana aciki, daga cikin ƙoramar wasu litafan tsafinsa ya ɗebo guda biyu ja da baƙi, baƙin ya fara jefawa cikin wannan jinin dake cikin ƙwarya sannan ya zura kansa yana karewa Ƙwaryar kallo dake ta zaɓalɓala.

         Sai da ya gama kallo tsaf sannan ya ɗago da kansa da yayi gumi sharkaf ya fara mata bayani, ” Tabbas cikin biyun za’a iya gudanar da ɗaya amma biyun bazasu iya wanzuwa akanshi ba, zamu iya nakashi ta kowacce siga haka nan zaki iya sawa a fitar dashi daga cikin masaurautar, amma shi ne kuskuren da zaki fara tafkawa a rayuwar ki, domin kuwa ta wannan silar dukkan asiran da kika binne za’a binciko domin kuwa allura ce zata tono garma”

      Fulani Maryama harta fara jin daɗi ƙarshen maganarsa ya sa ta shiga damuwa, kallansa tayi cikin rashin fahimta ta ce, ” Bangane mai kake nufi ba? ” mayar da ƙwaryar yayi cen gefe ya ce, ” Abinda na gani kenan zaɓi ya ragewa mai shiga rijiya…, kowanne zaɓi kika ɗauka yana da nashi ƙalubalen da zaki fuskanta ki nutsu da kyau ki saurare ni inba  haka ba zakiyi gudun gara ki faɗa gidan zago “
       Jakadiya dake gefe tayi tsuru sai raba idanu ta ke cikin zuciyar ta ta ke faɗin, ” Lallai Fulani Maryama kema ba ƙaramar makira ba ce, amma ajuri zuwa rafi…, Ay bahaushe ya ce inzaka gina ramin mugunta gina shi gajere, amma lallai wannan Ɗa na Zaliha ya zama kainuwa dashen Allah, wata ƙila shi ne zai zama magajin mulki muga ta tsiya, dama ance kayun Ɗan ƙwarai ya gaji Ubansa “
       ” Ina sauraren kowacce kalma da zata fito daga bakinka kuma kowacce zan saka ta amazaunin da ta da ce ” Fulani Maryama ta faɗa.

     Miƙe ƙafafunsa yayi da gaba ɗaya gashi ya rufe su sannan ya fara mata bayani, ” Zabi na farko zamu iya baki garin maganin da za’a zuba masa a ruwan wanka ina nufin wankansa na farko a duniya kuma ko yaya ne asamu a bashi wannaa maganin ya sha, sai kuma na turare wanda ita Zaliha tana fara Naƙuda zaki turara mata, karki bari yaro ya faɗo ba tare da kin turara shi ba, to idan kika yi haka bazai iya gani da idanunsa ba, har tafiya da magana ke komai da kika sani sai dai ayi masa, saboda zai kasance a kwance sai dai duk abinda za’a furta zai ji shi babu abinda zai iya wanzarwa “
      Murmushin jin daɗi Fulani Maryama tayi ganin haka yasa boka ya ce mata, ” Sai dai akwai sharaɗin da zaki kiyaye,  akwai ruhin wata da na gani tana jingine da shi, zata  shigo cikin gidan masarautar ku tana ƙasƙantacciya muddin kika bari ta shigo cikin gidan sarautar, abubuwa marasa daɗi zasu fara faruwa gareki kuma duk ranar da tayi tozali da shi suka haɗa ido, a ranar aljanun dake riƙe da ƙafafunsa zasu tarwatse alƙadarinsu zai karye, idan kika yi sake ta ɗau wani abun ci ko abin sha ta bashi da hannunta to a ranar suma aljanun da ke riƙe da bakinsa zasu gushe zai fara magana, sai dai aranar zai fara wani irin ciwo kamar zai mutu zai yi ta amai ba ƙyaƙyƙyautawa kamar zai amayar da ƴan hanjinsa, hakan zai ɗaga hankalin Mai martaba har yasa anemo wanda ya bashi wani abu tunda shi zaiyi tunanin guba ce aka bashi, amma ba haka bane amayar da gubar da take jikinsa yake ta tsawon shekaru “Daga cen ɓangaren Mahaifin Nusaiba yace. “Subhanallah Goggo lamarin har yayi tsamari haka? Me zai hana ku daidaita ina Halifan?” Goggo ta ce. “Na rantse da Allah Nadabo sai anbi min haƙƙina ni za’a kawowa sabon salawaitin cin mutumci daga nazo gidan jikata” Abba yace. “To kiyi haƙuri Goggo insha Allah anjima zan zo” a hassale Goggo ta ce. “Idan har sai anjima zaka zo ka bari Nadabo na yafe tunda kai baka damu da martabar mahaifiyarka ba, zan tafi gurin hukumar da kaina ai na Allah basa ƙarewa tunda baka ƙaunata…” da sauri Abba ya katse ta yace, “A’a kiyi haƙuri ina nan tafe yanzu” tana jin haka ta katse wayar gabaɗaya.+

  Inno shewa tayi ta ce. “Ahayye Allah na dawo inji kishiyar me yaji to wa zai cinye naman idan ba ke ba, kinsan dai tun muna yara ke kura ce to kuma kya nuna mun ɗiban albarka ki kira Nadabo. Wallahi idan bai zo da majalisar ɗinkin duniya ba sai na kwashe masa albarka.”
  Haushi ne ya kama Halifa cikin ƙunci yace. “Dan Allah kuyi mana shiru haba dan Allah? Tun ɗazu sai abu ɗaya akeyi nikam gaskiya na gaji wallahi, Allah idan su Daddy suka zo tasaku zasuyi a gaba ku tafi ni bazan iya ba kwana ɗaya kacal kunƙi ku barmu muyi bacci cikin nutsuwa.” Nusaiba ta ce. “To wai ku dan Allah banda abinku me akayi muku na kiran su Abba? Idan zaman nan ɗin ne bakwa so basai ku koma mazauninku ba?” Inno kallan tsaf ta yiwa Nusaiba sannan ta mata daƙuwa ta ce. “Gidan ku ja’ira mara ɗa’a korar mu kuke yi nida ƴar uwata? Wacce uwar muke ci a gidan naku da har kuke korarmu” Halifa yace. “Inno yanzu mu dawo maganar nama wannan fa ba abin wasa bane wallahi tsoro ya kamani ace kaji biyar babu daga yamma zuwa safiya” Inno ta ce. “Gane mun hanya jikana ni kaina na fara zargin anya babu wata a ƙasa kuwa?” Halifa na shirin magana suka ji ƙarar fashewar abu a ɗakin Nusaiba, da sauri suka nufi ɗakin zanin Inno har yana niyyar faɗuwa, suna zuwa suka samu kwalaben turarenta ne a ƙasa. Baki suka saki suna mamaki Goggo ta ce. “Halifa kuna da ɓeraye ne a gidan nan?” Nusaiba ta ce. “Gaskiya bamu da ɓeraye amma nayi mamaki ya akayi har kwalabe suka farfashe haka?” Inno ta waiga ta kai kallonta ga Jaririn Nusaiba dake kwance kan gado ta ce. “Halifa kasan Allah wannan ɗan ƙundalon na fara zarginsa saboda naga ɗiban albarkarsa ido biyu, anya jinnu basu shafeshi ba kuwa” Halifa ya tsuke fuska ya ce.

    “Gaskiya banasan irin wannan Inno ya zaki dinga alaƙanta mun ɗa da aljanu ba naso kawai daga kwalaben turare sun zubo sai ki ce ɗana ne, wai me yaron nan ya tsare miki” Inno ta riƙe baki ta ce. “Ubanka ya tsare mun Halifa ka kiyayeni fa ina nuna maka Annabi kana runtse ido tam, wallahi duk ranar da ya nuna maka ɗiban albarkarsa zakayi bayani da bakinka”

     Goggo haushi ya isheta ta ce, “Rakiya wai wannan sabon salawatin ruɗewar meye ya sameki, anya aljanu basu buɗe miki idanu ba? Ke Nusaiba ɗauko mun shi ma inyi masa wanka kar wannan ruɗaɗɗiyar ta ƙara ruɗa mu” Goggo na faɗa ta fice haɗa ruwan wankan Jariri” Halifa ma ficewa yayi aka bar Nusaiba da Inno, Nusaiba cire masa kaya tayi ta wuce ɗakin da Halifa yake dan ta ɗebo kayan Jaririn. Inno na zaune ta ga Jaririn ya buga tsalle ya miƙe tsaye, dafe ƙeyarsa yayi ya fara wani irin zagaye yana yi yana gwalalo mata idanu. Sai yayi gaba kamar zai hau kanta sai kuma yayi baya ya buga tsalle. Ihu Inno ta farayi tana tafe a guje fitsari na bin ƙafafuwanta. Da gudu duk suka fito dan ganin abinda ya faru gabaɗaya suka fara jero mata tambayoyi kala-kala, Inno ji tayi bakinta yayi nauyi kallan ƙofar ɗakin Nusaiba take tana nunawa, da sauri Nusaiba ta shiga dan ɗauko Jaririnta.

STORY CONTINUES BELOW
   Ana cikin haka suka ji bugun gida da sauri Halifa yaje ya buɗe ƙofar Motocin Daddy dana Abba ne kusan tare suka ƙaraso, suna shigowa falon suka gaishe da su Inno sannan  suka zauna.

   Daddy ya ce. “Halifa Inno ta gaya mun abinda kayi mata meyasa kake yiwa mahaifiya ta haka ne? Yanzu idan ɗanka ya girma zakaji daɗi ya wulaƙanta mahaifiyarka” Inno ta ce, “Gaya masa dai wallahi Halifa bashi da ɗa’a sam, Albasa dai batai halin ruwa ba wallahi da niyyata inkwashe masa albarka kafin kazo” Halifa yace.

  “Insha Allah za’a kiyaye Daddy, kuma idan babu damuwa ku wuce da su kawai zuwa gida” Daddy yace. “Dama ai kiran da Inno ta mun kenan to ita Nusaiba wazai zauna da ita?” Inno ta tattakura ta rafka salati.

  “La’ilaha’illahu Muhammadur Rasulillahi Sallallahu Alaihiwasallam yanzu Salisu iyaka zaka mun da gidan Ɗanka saboda nazo zaman daɓaro, idan ka tafi dani gidanka wacce uwar zaka bani, Meye bana ci a gidan nan? Wallahi Salisu duk cikin jikoki banyi sa’ar jika kamar Halifa ba, baƙin cikin cin kazar kake mun? Ahir ɗinka wallahi ko a mafarki na kuma jin wannan zancen sai na kwashe maka albarka sakarai maras ɗa’a kawai. Yo idan ban zaunawa jikata ba wa nake da shi da zan zaunawa, kai nifa nazo kenan zuwa sojan badaskare kuma ka ɗebomun kayana tas ka kawo mun gidan nan” Daddy dafe kansa yayi zaiyi magana Halifa ya ce.

   “Maganar gaskiya nikam bazaki zauna mun a gida ba, tun da kuka zo gidan nan baccin kirki bama samun isasshe” Abba ya masa daƙuwa yace. “Gidanku Halifa su Inno kake gayawa hakan?” Daddy yayi gyaran murya ya ce.
   “Inno ta kiran da kika mun me kike so ayi” Inno ta ɗaga kai sama kamar me nazari ta ce.

   “Ɗanka nake san kamun iyaka dashi karya ƙara shiga sabgata, ai inace jikata ce ta haihu ko?” Daddy da Abba suka gyaɗa kai Inno ta cigaba da cewa.

   “To kuce ya haɗa ya nasa ya nasa ya bar gidan nan idan mun tafi ya dawo” Halifa ya watsawa Inno harara suna haɗa ido ta rushe da kuka.

    Goggo ta kalli Halifa ta ce, “Li’ilafi ƙuraishi aniyarka ta faɗa kanki ƴar uwar tawa kake yiwa wannan mugun kallon to kurwarta kur, oh yau naga sabon salawaitun mugun hali ido biyu anya Nadabo wata rana Halifa bazai rufemu da duka ba a gidan nan kuwa?”  Halifa tsaki yayi ya miƙe zai bar gurin da sauri Inno ta riƙo gefen rigarsa ta ce. “Dawo-dawo wallahi sai ka zane mu gwara ka dake mu a gaban iyayenka kar sai sun tafi ka kwashe mana albarka” Sai kuma Inno ta fashe da kuka ita Goggo kamar haɗin baki suke share kwallah. Abba ne ya kalli Halifa yace. “Dawo ka zauna.”
   Halifa ya cika fam kamar zai fashe ya zauna Abba ya sauko daga kan kujera ya dawo ƙasa yace. “Goggo dan Allah kuyi haƙuri kunsan yaran nan sai ana haƙuri da…” A hassale Inno ta katseshi ta ce. “Allah ya tsinewa haƙurin albarka mun dinga haƙurin kenan har sai ciwon zuciya ya kamamu nida ƴar uwata, wato baƙin cikin rayuwar kuke mana ko Nadabo kuzo ku kashe mu kawai ku huta” Abba dafe kai yayi yai shiru bai ƙara furta komai ba. Daddy kallan Abba da Halifa yayi ya ƙifta musu ido sannan ya fara cewa.

   “Halifa yanzu abinda zaka dinga mun kenan kana tayarwa da mahaifiyata hankali, to maza ka fice daga gidan nan ka shiga duniya kowa ya huta  gwara nayi rayuwar farinciki da mahaifiyata ya fi mun komai.” Halifa miƙewa yayi bai ce komai ba ya wuce ɗakinsa, wata jakar goyonsa ta zuwa gurin aiki wacce yake sa uniform ya ɗauko ya goya ya fito.

   Tsugunnawa yayi a gaban Daddy yace. “Shikenan Daddy tunda haka ne ni bari na tafi zan fita daga rayuwarku tunda Inno da Goggo basasan gani na” yana gama faɗa ya mike zai bi hanyar ƙofar.

   Inno ɓingirewa tayi a ƙasa ta zuba wani uban salati tana kuka, Goggo ce ta ɗagota zaune itama tana share nata hawayen. Inno kallan Daddy tayi ta ce. “Salisu wallahi idan Halifa ya shiga duniya sai na ɗebe maka albarka, yanzu dama baka ƙaunar Halifa ban sani ba a gabana zaka koreshi ya shiga duniya saboda rashin ɗa’a” Daddy yace. “Inno ke fa kika ce ya fita daga rayuwarki nikuma duk abinda bakya so nima bana sanshi…” da sauri Inno ta ce.

   “Ittaƙillah ittaƙillah wallahi karka mun sharri oh na shige su ni jikar mutum huɗu, yanzu haɗani zakayi da yaron nan da uwarsa, jikan nawa na cikina zaka ce bana ƙauna?” Wallahi Salisu idan baka dawo da yaron nan ka fice daga gidan nan ba sai na kwashe maka albaka, ni bansan wacce uwar ma zakuyi mana ba muna zaman lafiya nida ƴan jikokina da farar safiya kuzo ku kawo mana tarzoma”
STORY CONTINUES BELOW
   Goggo ta karɓe zancen da. “Wallahi Rakiya barni dasu Allah yaran nan hukuma ce zata rabamu da su” Abba ya kalli Halifa yace. “Ka wuce cikin gida ka ajiye jakar nan” Halifa murmushi yayi saboda yasan dama Daddy da biyu yayi haka sai yace. “Abba ku bari kawai na tafi gwara na shiga yawon duniya” ya faɗa yana murɗa kofar.

   Inno ta kuma matso ƙwallah tana jan majina ta ce. “Allah ya tsinewa yawon duniyar ni ɗin banza da wofi wallahi kanasa ƙafarka ka fita daga gidan nan sai na kai ƙarar Ubanka gurin hukuma, ni zaka tozarta ka ɗebewa albarka ku tashi ku bar gabana kuma ko a mafarki karna ƙara ganinku a gabana, yo dama me kake mun Allah na tuba ba Halifa ne yake mun komai ba, badan shi ba da nashiga wani hali tunda shine uwata shine ubana.” Daddy na shirin magana suka ga Inno ta miƙe zata fita da sauri Halifa ya dawo yana sauke jakarsa.

   Goggo tsuke fuska tayi ta kalli su Abba ta ce, “Ku fice daga gidan jikana tun kafin na ɓata muku rai da sabon salawaitun rashin mutumci, haka kawai zaku zo ku hargitsa mana gida muna zaune lami lafiya.”
   Su Daddy miƙewa sukayi suka fita suna murmushi ƙasa-ƙasa Inno ta ɗaga murya ta ce. “Kuma ko a mafarki kar na ƙara ganinku idan ba haka ba na ɗebe muku albarka marasa ɗa’a kawai.” Suna fita Goggo ta rufe kofa ta wuce ta ɗauko ruwan wankan Jariri ta wuce ɗaki dan tayi masa wanka. Goggo ta fara yiwa Jariri wanka ta ga ya ƙura mata ido yana kallo hura masa idon tayi da bakinta, nan take yayi tsalle ya ɗafe bakinta tana shirin kurma ihu ya saketa ya dinga tsalle a cikin ruwan kamar ana wulla ƙwallo, daga cikin robar tsalle yayi ya fara ɗafe labulewa daga kan wannan ya faɗa kan wannan, yana faɗowa daga kan labule ya fara fisgar zanin gado yana bankaɗawa yana shigewa yana fitowa, fitowa yayi daga cikin zanin gadon ya hau kan ƙafafuwan Goggo yana tsalle, daga ƙarshe zaninta ya bankaɗa ya shige ciki, wani uban ihu Goggo ta zunduma ta ce. “Ku dubi Allah karka shige mun oh na shigesu yau ga sabuwar salawaitun rashin ɗa’a da iskanci jama’a kuzo zai illata ni.”

FANS BA ZAN DINGA POSTING KULLIN BA SABODA LITTAFIN KUƊI DA NAKE YI, ZAN DINGA SAKAR MUKU KO SAU HUƊU A SATI NE.
_Ummou Aslam Bint Adam_?
*FIRST CLASS WRITERS ASSO*☀️
*ANYA BAIWA CE?*

             Na

*AMEERA ADAM*
         
https://chat.whatsapp.com/DgpHYMMtvIeCjKQQDbsBPN

_LITTAFIN NAN NA KUƊI NE DA NAIRA 200 ZAKI KARANTA SHI CIKIN KWANCIYAR HANKALI, GAME BUƘATAR VIP POSTING SAU BIYU A RANA ZAI BIYA 400, GABAƊAYA ZAKU BIYA TA WANNAN ACCOUNT ƊIN, FIRST BANK 3090957579 AISHA ADAM, ZA’A TURO DA SHAIDAR BIYA TA WANNAN LAMBAR 0706 206 2624,DAN GIRMAN ALLAH IDAN KINSAN ZAKI FITARMUN DA LITTAFI NA YAFE CINIKINKI._
FREE PAGE 3
       Ajiyar zuciya Fulani Maryama ta sauke sannan ta ce masa, ” Wace ce yarinyar? Kuma daga wane gurin zata xo? Babu damar dakatar da zuwan nata? Ya za’ay na gane ita ce dan na ɗauki matakin daya dace akanta?? “
      Boka ya ce, ” Daga ni har sauran matsafan duniya babu wanda ya isa ya ja da yarinyar domin ita ɗin FILSIFI ce, abinda muke kira da FILSIFI kuwa aharkar bokan ci, tarraya ko haɗakar shuɗaɗɗun ruhika mabanbanta daga jinsi Mabanbanta, zo ki duba nan ” ya ƙarasa faɗa yana buɗe mata wannan jan littafin da ke gefensa.

        Zanen  wasu matasan mata ta gani guda uku sai dai duk cikinsu babu wacce zanen fuskarta ya fito sosai daga ƙasan kowacce anrubuta wani irin gwamammen rubutu, ta farko ya fara nuna mata yace, ” Wannan da kike gani ita ce Muhaibish ita ta rayu ne tsawon dubbannin shekarun da suka gabata, Ƴar Sarkin jinsin Fararen Aljanun ƙarƙashin ƙasa ce, tunda take bata taɓa taka doron ƙasa ba “

        Zaro idanu Fulani Maryama tayi tana mamakin abinda ya faɗa, ta biyu ya nuna mata ya cigaba da cewa, ” Wannan kuma sunan ta Kalimsiyat Ƴar sarkin fararen Aljanu ce amma ta nan doron ƙasa itama ta rayu atsawon dubbanin shekaru, acikin wani littafin bincike na karanta cewar ta yi rayuwa ne tun bayan zuwan Annabi Yusuf (A.S) ita kuma tunda ta ke bata taɓa nutsawa ƙarƙashin ƙasa ba a matsayinta na jinsin aljanu, kuma ita Kalimsiyat mace ce mara haƙuri mai faɗan gaske, kuma abinciken da nayi dukkan su biyun kashe su akayi bisa doron zalinci, kuma abinda zai baki mamaki kusan duka ruhinsu guda ne, sai dai banbancin nahiya da zamani.
     Sai ta Ukun su ita ce aka ce zata xo aƙarshen zamanin nan, sunanta Rayzuta ita ta haɗa dukkan abubuwan da waɗancen suke dashi harma da wanda suka rasa, ƴar baiwa ce me ɗauke da ɓoyayyun al’amura, ita kanta batasan da wannan baiwa tata ba.”
STORY CONTINUES BELOW
      Yana rufe baki cikin azarɓaɓi Fulani Maryama ta ce, ” To itama ta ukun nasu Aljanar ce? kuma meye alaƙar su da junan su? Kuma meye alaƙarta da gidan masarautarmu? “

      ” Maryama kenan azarɓaɓin me kike yi? Ai duk gaggauwar asara ta jira samu, kuma duk gaggawar unguwar zoma ta jira a haihu, mai kike ci ne na baka na zuba inkinyi haƙuri sannu-sannu bata hana zuwa sai dai adaɗe ba’a je ba “
     Murmushin tayi sannan ta bashi amsa da, ” Hmmm Marduska ai Ranar biyan buƙata rai ba’a bakin komai yake ba, na ƙagu na ji matsayin Yarinyar da ka ce da kuma ya alaƙarsu ta ke? “
    Marduska ya cigaba da cewa, ” Har zuwa wannan zancen da nake miki ruhin su  na nan ya wanzu a dora ƙasa, sai dai babu inda zasu ya da zango sai akan cikon ta ukunsu, kuma ba kowa bace cikon ta ukunsu sai Yarinyar da nace miki karki sakankance har ta shigo Masarautar ku, har yanxu mudubin tsafi na ya gagara gano mun mutum ce ko kuma itama tana cikin jinsin Aljan, sai dai bincike ya nuna akwai wani ɓoyayyen al’amar dake bibiyar jinin zuri’ar sarki Aminullahi “

       Damuwa ce ƙarara a fuskar Fulani Maryama ta kuma jefo masa tambaya, ” Ita yarinyar ba dama ka nuna mun hoton fuskarta yanda zan gane kamaninta? “
     Mudubinsa ya janyo ya fara wasu surutai yana watsa masa wani ruwa mai yauƙi, wata irin ƙara suka ji ta tsagewar mudubin har sai da suka tsorata, cikin damuwa Bokan ya ce, ” Gaskiya gaba ɗaya aikin da kika zo dashi akwai damuwa da tashin hankali, haka kawai banci nanin ba nanin zata ci ni, na dakata akan binciken Yarinyar nan saboda ceton rayuwa ta “
      Abin duniya gaba ɗaya ya dami Fulani Maryama amma duk da haka ba ta gushe ba tana faɗin, ” Ka taimaka mun kayimun wani abu, ni da kai kaɗai na dogara “
       Wani mugun kallo ya bi ta dashi sannan ya ce, ” Baki da hankali ne a gabanki munanan abubuwa suka faru amma zaki ce na taimaka miki kinga idan kinganni a lahira kaini akai, babu uwar da zan iya taimaka miki, bincike na biyu da zan gaya miki shi ne, idan kika sa aka fitar da shi tun yana jariri to ba makawa acikin ƙasa da makwanni goma zai faɗa gurin da zai gamu da ita wannan yarinya kuma dawowarsu shi da ita bazai miki daɗi ba, dabara ta ragewa mai shiga rijiya…”

         Zufar dake goshinta ta goge sannan ta ce masa, ” Marduska wai dole sai akaina wannan masifun  yarinyar zasu sauka? Kaina ya kulle fa, dan Allah ka bani mafita…” katse ta yayi da ƙarfin gaske yana cewa, ” Da alama kin manta dokar kogon dutsen, azaba ta gaggawa zata iya wanzuwa agareki ” sunkuyar da kai ƙasa tayi ta ce, ” Tsafi ya dafa tuba nake bokana Sarkin bokayen duniya, ina gwanin wani ga nawa Aljani Garbunsa ya ƙara ja da zamanin ka “
     Motsa bakinsa yayi alamar jindaɗi sannan ya ɗauko wani ruwa dake cikin tukunyar ƙasa ya ɗaga shi sama da hannunsa ya fara surutunsa na tsafi, ya jima ahaka sannan ya sauko da shi ya leƙa wani tiriri ne yake fitowa, sai da ya gama kallon ƙwaryar ya ce, ” Akwai wasu ɓoyayun al’amura mai tafe da sarƙaƙiya, da alama shuɗaɗɗun abubuwan baya ne zasu iya dawowa wata ƙila Tarihi ne zai kuma maimaita kansa, amma bani da tabbas harsashe ne nayi,  ƙarɓi wannan ” Ya miƙa mata wata manyan layu sannan ya cigaba da bayani.

     ” Ita wannan layar ki saƙaleta aɗakinki zata taimaka miki na bunnuwar wasu sirrika na ki, wannan kuma ki binneta akan ƙofar shiga gidan masarautarku, bance zata Hana faruwar komai ba sai dai wannan layar zata hana tonuwar muhimmin sirinki musamman akan wance yaran, kinfi kowa sanin dai ba jinin Aminullahi ba ne hasalima ba jinin masarautar Kano bane, to ki saƙale ta gun da kikasan bazata faɗo ba, ita wannan ta ƙofar gidan wasu aljanune zasu miki gadin bakin ƙofar don hana ta shigowa, amma banda tabbaci yaƙini nake watakila shigowar Rayzuta gidan ya sa ta faɗowa wata ƙila kuma bazata faɗo ba, kuma na lura da faɗuwar gaba a duk lokacin da zaku haɗu da ita wannan yarinyar, sai ki riƙe wannan duk lokacin da kikaji faɗuwar gaba ki dinga lura da waɗanda suke tare da ke, ni nayi iya yi na ku tashi ku bani guri “
      Jakadiya dake gefe tsumu tayi najin kalaman boka cikin zuciyarta ta ke faɗin, ” Au dama Salman ba jinin Takawa bane? Lallai duk inda makirci ya je Fulani Maryama ta kai cen, babu ko tantama ɗan wajen Fulani Zulaiha shi zai zama magajin Izza, muje zuwa mahaukaci ya hau kura na tabbata akwai ranar da Ya zata ɗakin Ƙanwa, Fulani Maryama kinyi shuka a idon makwarya, lokaci na nan zuwa da kwaɓarki zatai ruwa, tafiya sannu-sannu kwana nesa. “
    Kamar Fulani Maryama tasan abinda yake ran Jakadiya aikuwa ta juyo cikin tsuke fuska ta fara mata magana, ” Jakadiya duk abinda kika ji agurin nan ki tabbata da ya zama sirri banasan kowacce magana ta fito daga bakinki, bakinki ƙanin ƙafarki, kinsanni sarai kinsan wacce Fulani Maryama bani da kyau banida daɗi, idan na sake naji wata magana ta ɓilla waje to daga gareki ne, kuma insa a hallakaki ba abu ne mai wuya agurina ba “
      Jakadiya sarai ta san Fulani Maryama zatayi abinda yafi haka ma ta rissinar da kai ƙasa ta ce, ”  Wane ni da wannan ɗanyen aikin ya Shugabata indai wanda ya mutu zai dawo to maganar nan zata tashi, ai duk wanda ya ƙona rumbunsa yasan inda toka take tsada, ina ni ina bayyana sirrin Uwar gijiya ta idan nai haka ai kamar na daɓawa kaina wuƙa ne “
    Fulani Maryama ɗauke kanta gefe tayi tana faɗin, ” Ki tabbatar da kin kiyaye abinda kika faɗa domin ni ginshiƙin dutse ce kowa yayi karo dani shi ka faɗi, idan kunne yaji gangar jiki ta tsira ” Jakadiya haɗiye yawu tayi mai ɗaci saboda jin haushin maganar Fulani, cikin zuciyarta ƙwafa tayi ta ce, ” Tunkafin ahaifi uwar mai sabulu balbela ta ke da farinta, Fulani Maryama dani kike zance wallahi duk wannan wulaƙancin da kike mun akwai lokacin da zan farke miki laya. “

      ” Muna godiya Ubangidana maganin kuka na dukda yau ce rana ta farko da zan fita daga kogon dutsen bada biyan dukkan buƙata ba, amma  ni mai bin umarnin ka ce akan duk abubuwan daka gindaya mun, tsafi ya dafa hatsabibancin ka ya cigaba da wanzuwar har ƙarshen zamani ” Fulani Maryama ta faɗa tana karɓar layun da ya bata.

      Cikin jindaɗin kirarinta ya ce, ” Taɓewa ta tabbata ga mai yin shirka kije tukwicin aikinmu na ga cikin bayin Masarautar ku kamar yanda muka saba duk lokacin da kuka ziyarce mu, zan ƙara miki tuni idan kun wayi gari da mutuwar wani bawan babu ku babu cin kayan sadakar inba haka ba zaku bishi, ku fice daga kogon dutse kuna masu ambatan sunan mu ” yana gama faɗa ya ɓace daga gurin, Jakadiya da Fulani tashi suka yi suka fita, suna zuwa bakin kogon dutsen Fulani ta kuma runtse idonta tana karanta ɗalasiman tsafin, atake haske ya kuma mamaye su suka ɓace daga gurin.

        Lokacin da suka koma cikin Masarautar tuni dare ya tsala babu motsin komai sai kukan tsuntsaye da ƙananan dabobbi, Fulani karɓar Salman tayi dake hannun Jakadiya sannan ta ce mata, ” Ƙuda wajen kwaɗayi akan mutum ina fatan baki manta maganar boka ba ” rissunawa Jakadiya tayi ta ce, ” Ina ankare ya shugaba ta “

About AIS

Check Also

JARIRI CHAPTER 5 BY AMEERA ADAM

JARIRI CHAPTER 5 BY AMEERA ADAM Www.bankinhausanovels.com.ng  Jariri na ganin haka ya tuntsire da dariya …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *