INDA RAI CHAPTER 3 BY FADILA SANI BAKORI

INDA RAI CHAPTER 3 BY FADILA SANI BAKORI

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Khadija na kwance tana tunanin tafiyarta gobe, kira ya shigo wayarta. Khadija cikin fad’uwar gaba ta amsa kiran, ganin Mahaifiyarta ce mai kiram, tasan tafiyarta gobe za tai ma ta magana. 

Khadija cikin fad’uwar gaba ta kanga wayar akun nan ta tana sauraran abin da Mahaifiyarta zata ce mata”. 

Daga can b’angaran kuma, Mahaifiyar Khadija ta ce, “Hello Khadija ya karatun? “. “Lafiya k’alau Mama Alhamdulillah “. Cewar Khadija. 

“Goba ne hutun naku ko? “. Mama ta tambayi Khadija. “Eh Mama”. Khadija ta ba Mahaifiyarta amsa. 

Shiru Mahaifiyar Khadija ta yi, sannan ta ce, “Tom Khadija gashi wannan karan da Abbanku zamu tafi, dan ban san da tafiyar ba sai yau yake fad’amin, shine na ce idan kin dawo ko gidan Aisha kawai zaki zamanki?,  inda hutun naku ma kad’anne, ko kuma ki zauna Gidan su Maryam”. 

Shiru Khadija ta yi, dan ita ko haka nan bata son zaman gidan Aunty Aisha bare kuma yan zu da ta ke acikin halin nan, dabara ce ta fad’oma Khadija cikin jin dad’in dabarar da kuma tafiyar Mahaifiyarta,  ta ce, “Mama inda bakya nan Kawai na fasa dawowa, dama friend’s d’ina da dama ganin hutun kad’ane duk wa inda suke nesa basu tafiba, nima kam kawai zan yi zamana anan”.

Shiru Mahaifiyar Khadija ta yi, tana tunanin barin Khadija nan ta yi hutu, sannan ta ce, “Shikenan, amma Khadija ban da biyema k’awaye ana yawace-yawacan banza”.

 “Insha Allah Mama, babu abin da zai faru”. Cewar Khadija”. 

Mahaifiyar Khadija ba tare da shakkun ko mai ba, na barin Khadija tai hutun anan ta kashe wayarta”. 

Khadija sosai ta ji dad’in haka, Mahaifiyarta na kashe kiran, ta kira Hafsat tai mata albishirin ba za ta koma hutu ba, anan za tai hutun ta. 

Hafsat sosai ta yi ma Khadija murnar haka, duk da ita awajan ta bata ga dabarar hakan ba, ita aganinta gara Hafsat ta koma gidansu Iyayanta su san halinda ta ke, bataga amfanin b’ab’b’oyewar ba. Haka dai suka yi fira da Hafsat sannan Khadija ta kashe wayarta tana mai jin dad’in rashin zuwanta Gida”. 

Haka Khadija tai ta Rayuwarta, ita kad’ai , ad’an ma dai-dai cin d’akin ta, babu abin da ke fitar da ita sai sayan abinci. Idan ta gaji da zaman kad’aici ta d’akko wayarta ta yi fira da friend’s d’in ta a WhatsApp. Akwana atashi babu wuya, ahaka hutun su Khadija ya k’are. Ta ci gaba da zuwa School d’in ta, kullum sai sun gaisa da Iyayanta idan basu gaisa ta waya ba, zasu gaisa ta WhatsApp”. 

Kwana kai sunja, satittika sun yi nisa, inda su Khadija ma suke kan gab’ar karatu sosai, sai dai yan zu karatun na nai man gagararta, dan cikin nau yi ya ke mata, sosai, gashi yan zu dole ma ta aje zuwa School d’in dan cikinta ya yi wani irin girma. Hakan yasa gudin maganar muta ne, ta aje zuwa, dan ko Hafsat aminiyarta ta goyi bayan hakan, dan yan zu har abinci Hafsat ke zuwa ta siyo mata, dan so da dama wani lotun Hafsat anan ta ke kwana, dan Khadija nai mata k’orafin da kyar ta ke d’aga k’afafunta sun mata nau yi sosai, hakan yasa Hafsat yan zu ta dawo da kwana gaba d’aya wajan Khadijar , dan kayan Hafsat ma gaba d’aya ta dawo da su d’akin Khadija”. 

Watan Khadija biyu kenan rabanta da zuwa School. Yau Khadija da ciwan mara ta tashi, dan mararta sosai ta d’aure mata, ciwo ta ke mata sosai, gashi ita kad’ai ce agidan Hafsat na School. Haka Khadija tai ta malelekuwa awajan tana cije baki, tun tana daurewa har ta fara kuka. 

Hafsat ko da wowarta kenan, da sauri ta k’arasa wajan Khadija ganin yadda ta ke ciccije baki tana kuka. Hafsat hankalinta tashe ta k’arasa ta rik’e Khadija tana fad’in Khadija lafiya ko haihuwar ce? “. Hafsat ganin Khadija ba iya magana za tai ba, hakan yasa ta fita da sauri tana ce ma Khadija, “Ina zuwa Khadija bari in je in dawo”. 

Hafsat da sauri gudu-gudu ta k’arasa private Hospital d’in da ke kusa da su, inda suka je azubar ma Khadija da cikin”. 

Hafsat na shiga Allah ya had’ata da likikitar da suka samu lokacin da suka je azubar da cikin Khadija. Hafsat cikin alamun rud’ewa ta idasa wajan likitar tana kallanta ta ce, “Assalamu alaikum,barka da aiki, dan Allah kin gane ni? “. Hafsat ta fad’i maganar cikin k’osawa. 

Likitar  kallan Hafsat ta yi tana mai son tuna inda ta santa, amma ta manta, hakan ya sa ta ce ma Hafsat, “A’a na manta, tuna min? “. Hafsat cikin k’osawa ta ce, “Ni ce wadda muka tab’a zuwa da Friend d’ina azubar mata da ciki, ki kai mana wa’azi akan ba kyau, mu yi hak’uri, tom yan zu haka tana can bata da lafiya, dan Allah ki tai maka kizo muje ki duba ta, tana can bata da lafiya”. 

Likitar kallan Hafsat ta yi tana mai tuna ranar da suka zo azubar ma k’awarta  da ciki ta ce, Allah sarki ashe bata zubar, da cikin ba . Kallan Hafsat ta yi, ta ce,”Ayyah tana ina ne? “. “Tana nan kusa da ku, babu nisa”. Hafsat ta fad’i maganar cikin garaje. 

Likitar  kallan Hafsat ta yi, ta ce, “Muje”. 

Shingid’e likitar ta tadda Khadija tana cije baki, ta daina kukan da ta ke yi. Likitar zuk’unnawa ta yi, kusa da Khadija tana mamakin girman cikin Khadija. 

Likitar cikin tausayama ma Khadija ta ce, “Sannu ko, hannu ta kai tana matsa marar Khadija, sanan ta kalli Hafsat ta ke tsaye ta ce, bari in duba ta ko? “. 

Hafsat fita ta yi, sannan likitar ta sa handgallop ta sama Khadija hannu. Bayan ta gama duba Khadija kiran Hafsat ta yi, ta ce, “Haihuwa ce, ki je ki siyo kayan Haihu”. Hafsat cikin zaro ido da mamaki ta kalli likitar ta ce, “Haihu kuma!?, dama cikin ya isa Haihuwa!?”. 

Kai likitar ta d’agama ta,  ta ce, “Haihuwa ce ki yi sauri ki yi abin da na ce, kafin in dawo”.

 “A’a bari in baki kud’in sai ki siya dan Allah kizo da shi”. Cewar Hafsat”. 

Hafsat tambayar likitar ta yi ta fad’a mata yadda zasu isa ta bata. Likitar ta tafi ba da dad’ewa ba ta dawo, tana zuwa tai ba Khadija wata ‘yar k’aramar tablet ta ce ta sa ta aharshenta ta rik’a tsotsa kad’an-kad’an “. 

Khadija na fara tsotsan tablet d’in nan, nan fa ta fara jin wani irin azababban ciwo, Wan bata tab’a jin irin saba, dan kukan ma gagararta ya yi. 

Hafsat ko ganin Yadda Khadija ta ke yi, Kuka ta fasa, dan gani ta ke kamar mutuwa Khadija za ta yi, yadda ta ga ta na yi”. 

Wani irin kakkarwa jikin Khadija ya fara yi,  lokacinda Haihuwar ta zo.

Likitar ganin hakan cema Hafsat ta yi ta fita ta basu waje. Hafsat fita ta yi, ta na mai yi ma Khadija addu’ar sauka lafiya”. 

Cikin ikon Allah Khadija tana mai rirrik’e likitar. 

Hafsat cikin mamaki ta baza kunne jin kukan Baby”. 

Likitar d’auke ya rinyar ta yi tana mai yi ma Khadija sannu,  ta ce, “daure ko Khadija Uwa ce zata fad’o”. 

Khadija ko cikin rinrintse ido tana mai rirrik’e Likitar,ta kuma Sak’o wata Baby. 

Likitar cikin al’ajabi da mamaki ta ke cewa, “Alhamdulillah!  Alhamdulillah!!, Alhamdulillah!!!, Khadija kin haifi twins “. 

Khadija ko rakub’ewa ta yi tana mai nishin wahala, tana share hawayan da ke ta zuba a idon ta”. 

Likitar fita ta yi ta kira Hafsat da ke zau ne rakub’e .Hannun Hafsat ta kama suka shiga ciki. 

Hafsat da mamaki da al’ajabi ta ke kallan jarire biyun da aka kwantar , cikin mamaki ta kalli likitar ta ce, “doctor twins? “.Hafsat ta fad’i maganar tana share hawayan da ke zubar mata, Wanda bata san kona meye ba, shin farin ciki ta ke ko ko, tausayin k’awarta ta ke, ita kanta bata san halinda ta ke ciki ba. Jin shashshek’ar kukan Khadija ne, Hafsat ta waiga  tana kallanta..

Hafsat k’arasawa wajan Khadija ta yi, ta rungumata suna kuka tare”. 

Gyaran murya likitar ta yi, ta ce, “Dan Allah ku yi hak’uri da kukan nan, da ace zai yi magani na tabbata da Yaran nan basu zo duniya ba, ke kuma ai kece zaki k’arfafa mata gwiywa ba wai ki taya ta ba, inda kukan ba bu naganin da zai yi muku”.

Hafsat da katawa da kukan ta yi, ta ta shi ta ta ya likikitar suka gyara wajan tas.

 Bayan sun gama gyara wajan ne Likitar ta juyo ruwan zafin da ta d’ora a  cooker gas d’in Khadija, ta kama Khadijat ta kaita toilet ta ce ta yi tsarki da shi, inda bai da yawa. 

Khadija cikin daurewa da zafin ruwan ta yi abin da Likitar ta ce”. 

Likitar kallan Hafsat ta yi, ta ce, “Tom kinga gas d’inku k’arami ne, zan baku nawa aro da tukunyata,  yan zu zo muje gidana sai ki taho da su”. 

Hafsat bin Likitar ta yi ta d’akko gas d’in da tukunyar. Tana zuwa ta aza ruwa kamar yadda likitar ta ce ta yi kafin ta zo”. 

Kayan jarirai kala uku-uku iri d’aya likitar ta siyoma jariran, sai rubar wanka da towel shima guda biyu. Lokacin da ta dawo dai-dai ruwan ya ta fasa, yaran kuma sai kuka suke, Hafsat ta rasa yadda za ta yi da su, su kuka uwarsu kuka”. 

Likitar na zuwa ta juye ruwan za fin ta mai da wani, sai da ya d’an huce sanan ta d’auki d’aya daga cikin yaran ta tana mai wanka, sai da ta wanke shi adadin yadda ake wanke yaro, sannan ta d’akko d’ayar”. 

Hafsat kallan Babyn da akema wanka  ta yi, ta ce, “Doctor wai Maza ne ko mata? “. “Duk mata ne”. Likitar ta bata amsa. 

Bayan likitar ta gama shirya d’aya daga cikin Yaran ne ta mik’ama Hafsat. Hafsat cikin zumu d’i da tsantsar kyan Babyn ta amshi jaririyar, tana rungume ta cikin jikinta”. 

Cikin k’ank’anin lokaci likitar duk ta gyara yaran, d’ayar ma haka ta shirya ta cikin kayan sanyin da ta saima Yaran. 

Masha Allah kallo d’aya idan kai ma Yaran dole ka k’ara kallan su, dan kyawawan Yara ne na bugawa a ajarida. Ita kanta likitar rungume d’ayar ta yi, tana mai kallan Yarinyar yadda ta yi shiru tana baccin jin dad’in wanka da akai mata”. 

Hafsat da ke rungume da d’ayar Baby’n, Kallan likitar ta yi, ta ce, “Doctor cikinsu Wacece babba? “.”ina ganin alamun twins ne na d’aurama ta farkon zare a hannunta, ta hannunki ita ce babba”. Likitar ta ba Hafsat amsa. 

“Aiko gobe zan siyo azurfa a sama babbar ahannu yadda za arik’a ganewa”. Cewar Hafsat”. 

Likitar kwantar da ta hannunta ta yi, sannan ta kalli Khadija, da tun d’azu su ke bata hak’uri ta ki hak’ura sun gaji sun rabu da ita. Likitar cikin tausayama Khadija ta ce, “Khadija dan Allah ki yi hak’uri da kukan nan haka nan, ki rungumi Yaranki, yan zu tashi mu je in Miki wanka inzo in tafi gida kinji ana kiran sallar Magriba. 

Da tai makon likitar ta kama Khadija ta kaita toilet”. 

Wankan towel likitar tai ma Khadija, sosai ta wanke Khadija, sannan ta kamata suka fito toilet d’in. Ruwan zafi likitar ta d’ebo ta had’ama Khadija tea mai kauri ta mik’ama ta”. 

Khadija ba batare da musuba ta amsa ta sha dan Yunwa ta ke ji sosai. Likitar kallan Hafsat ta yi, ta ce, “Ki je restaurant d’in nan ki siyo mata tuwo ta ci, dan tea d’in nan ba zai ma ta ko mai ba”. 

Hafsat kwantar da Baby’n hannunta ta yi, ta je ta siyo ma Khadija tuwan shinkafa miyar kub’ewa”. 

Hafsat na dawowa likitar tai masu sallama ta tafi ta ce sai gobe da safe  zata dawo. 

Hafsat godiya sosai tai ma likitar “.

Likitar na tafiya Hafsat ta yi alwallar magriba ta tada Sallah. Hafsat na cikin Sallah ne d’aya daga cikin Yaran ta tashi sai kuka ta ke, innya-innya, d’ayar na tashi d’ayar ma ta ta shi, haka suka rud’a d’akin da kuka. Khadija ko da kukan Yaran ya isheta ta kuma rasa yadda za ta yi, dan tunda aka haifi yaran ko kallan inda suke bata yi ba. Khadija jin kukan ya yi yawa, ita ma kawai sai ta sa kuka”. 

Hafsat sauri-sauri ta yi ta idar da sallar, tana idarwa cikin sauri ta zo ta d’auki d’aya daga cikin Baby’s ta mik’ama Khadija, ta ce, “Khadija ki amsheta ki bata abincinta, kinga tunda Yaran nan suka zo duniya ban da ruwa babu abin da aka basu har yan zu”. 

Khadija ko d’agowa ba ta yi ba ta kalli Hafsat, bare Hafsat ta sa ran zata amshi Yaran gashi kuma dukkan su har yan zu kuka su ke basu fasa ba. 

Khadija ko har yan zu bata d’ago ba,  kanta ak’asa sai wani rin kuka ta ke kamar zata sik’e. Hafsat dafa Khadija ta yi, ta ce, “Khadija tun d’azu mu ke baki baki muda likitar nan, amma kin k’i yin Shiru, dan Allah inda ba zaki shiru ba ki amshi Yaran nan ki shayar da su kar Yunwa tai musu illah”.

Stil Khadija bata d’ago ba ta kalli Hafsat bare Hafsat ta sa ran zama ta amshi Yaran bare kuma ta shayar da su, kuma har yan zu Khadijar kuka ta ke kamar ranta zai fita, dan har ta fara ba Hafsat tsoro ganin yadda ta ke jan numfashi”. 

Hafsat cikin tsoran ganin yadda Khadija ta ke yi, ta ce, kamar za tai kuka, dan ita kanta arud’e ta ke ga kukan Khadija ga na Yaran sai ta rasa da wanne zata ji, ga Khadija tsabar kuka numfashinta na nai man sark’ewa. 

Hafsat da sauri ta kwantar da yarinyar da ke hannunta ta yo kan Khadija ganin yadda ta ke jan numfashi da kyar tana rirrik’e k’irji. 

Hafsat cikin tsoro da tashin hankali ta kamo Khadija tana kuka ta na cewa, “Dan Allah Khadija ki yi hak’uri haka nan karki kashe kanki da kukan nan da kike yi, dan Allah Khadi… “. Hafsat shiru ta yi da fad’in abin da ta ke fad’a tana girgiza Khadija, ganin Khadijar ta fad’i k’asa gaba d’aya numfashinta ya tsaya cak”. 

Hafsat cikin tsanin furgita, ta ke girgiza Khadija tana kuka, tana ambatar “Innalilahi wa inna ilaihirraju’un, Khadija dan Allah ki tashi, ya zan yi da yaran nan, dan Allah Khadija”. 

Haka Hafsat keta girgiza Khadija tana kuka”. 

Kukan sai ya had’e da na jariran. Hafsat ganin haka cikin rawar jiki, dan jikinta ko ina rawa ya ke, ta lalibi wayarta ta kira doctor da ta amshi Haihuwar Khadijar, dan ta amshi number ta d’azu”. 

Hafsat na kira likitar na d’agawa. 

Cikin kuka Hafsat ke cewa, “Dan Allah ki zo Khadija ta…….. ✍️

Hafsat na kiran likitar, likitar ta d’aga. Cikin kuka Hafsat ke cewa, “Dan Allah ki zo Khadija ta dai na numfashi, baki  d’aya numfashinta ya tsaya cak”. 

Cikin razanar jin abin da Hafsat ta ce,  likitar ta ce, “Innalilhi wa Inna ilaihirraj’un, ba ri in zo yan zu”. 

Da sauri ta doctor Ruk’ayya ta d’auki mayafinta, ta tafi”. 

Hafsat na nan tsaye rik’e da d’aya daga cikin babyn tana kuka, dan har yan zu Khadija kwance ta ke bata farfad’o ba. Da sauri doctor Ruk’ayya ta shiga ta na yin kan Khadija da ke kwance babu alamun rai ajikinta. Doctor Ruk’ayya kamo Khadija ta yi, tana mai shafa mata ruwan mai sanyi afuska. 

Dogon Numfashi Khadija ta ja, amma bata bud’e idon ta ba. Doctor Ruk’ayya k’ara shafa mata ruwan ta yi, tana mai jingina Khadija ajikinta, dan ta gane Khadija doguwar suma ta yi. Ruwa Doctor Ruk’ayya ta ba Khadija ta sha. 

Doctor Ruk’ayya kallan Hafsat ta yi, ta ce, “Ta ci tuwan da kika siyo mata ne? “. “Eh taci”. Cewar Hafsat”. 

Doctor Ruk’ayya allurar bacci taima Khadija. Aiko ba afi minti goma ba da yin allurar bacci ya kwashe Khadija. Bayan Khadija ta yi bacci ne, Doctor Ruk’ayya ta kalli Hafsat da ke tsaye rik’e da d’aya daga cikin baby’s tana jijjigawa, dan ma Allah ya sa sun yi shiru. Doctor Ruk’ayya kallan Hafsat ta yi, ta ce, “Hafsat kawo Babyn “. Hafsat mik’a mata Babyn hannunta ta yi”. 

Doctor Ruk’ayya ko gyarama Khadija kwanciya ta yi,yadda Yaran zasu iya shan mama,  sannan ta d’aga rigar Khadija sama,  ta kanga Babyn yadda zata iya shan Maman. 

Allah sarki ana ba Yarinyar ko ta rik’e ta ci gaba da sha. Allah ko ya tai maka ansamu ruwan nono Masha Allah. 

Sai da Babyn tasha sosai sannan Doctor Ruk’ayya ta cireta, ta amsha d’ayar ma ta bata kamar yadda tai ma d’ayar”. 

Allah sarki ana cire su ko suka Kama bacci. Doctor Ruk’ayya sallama tai ma Hafsat ta tafi.

Bayan Doctor Ruk’ayya ta tafi ne, Hafsat ta fita ta siyo ma kanta abinci,  tana ciki ta tada Sallar Issha’i sannan ita ma ta kwanta”. 

Cikin dare kukun Yaran ya tada Hafsat a bacci. Cikin bacci Hafsat ta jiyo kukan Yaran, Hafsat tashi tai da sauri, ta d’auki d’aya tana jijjigawa,inta jijjiga wan nan sai ta aje ta jijjiga d’ayan. Hafsat ganin sun k’i yin shiru, zuwa tai ta bud’e rigar Khadija kamar yadda ta ga Doctor Ruk’ayya ta, zata ba Yaran Mama. Ta d’akko d’aya daga cikin Baby’s kenan zata dangana ma Nonan, Khadija ta yunk’ura ta tashi da sauri suna kallan kalo da Hafsat”. 

Hafsat d’aurewa ta yi babu alamun lallashi, ta ce, “Yau wa inda kinma tashi amsarsu ki basu Mama”. 

Khadija kallan Hafsat ta yi, tana mai kauda kanta gefe, alamun bazata amshi Babyn da Khadija ke mik’a mata ba. 

Hafsat babu yadda ba tai da Khadija ba ta amshi Yaran ta basu Mama amma ta k’iya. Khadija ganin ran Hafsat ya b’ace sosai ya sa ta mik’a hannu tana kuka ta amshi d’aya daga cikin Yaran, amma kuma babu alamun zata bata Maman, gashi har yan zu Baby’s kuka suke. 

Ana cikin haka ne aka kira Sallar Asuba. Hafsat ta shi ta yi ranta b’ace ta je ta yi alwallah, ta zo ta tada Sallah. Har Hafsat ta idar da Sallar Khadija bata ba Yarinyar da ke hannunta Nono ba, hasalima itama kukan ta ke yi,  dan dai ita kad’an-kad’an ta ke yi”. 

Hafsat tashi ta yi tana had’a Kayanta da sauri da sauri, Hafsat sai da ta d’auke duk abin da ya ke ma zaunin na ta ne, sannan ta kalli Khadija babu alamun wasa ta ce, “Khadija Allah ya had’amu da alkairi, zan koma Hostel da zama dan gaskiya ba zan iya zama nan ba ke kuka Yara kuka, gashi kin k’i basu Mama, sai watarana na tafi”. Hafsat na fad’in haka ta juya zata tafi”. 

Khadija cikin tashin hankali ta yi sauri ta aje Babyn da ke hannunta ta kamo hannun Khadija da sauri, cikin kuka tana cewa, “Yi hak’uri Hafsat dan Allah karki tafi ki barni, Wallahi bazan sake yin kukan ba, dan Allah karki ta fi ki yi hak’uri na bar kukan”. Khadija ta idasa maganar tana goge hawayanta. Hafsat kallan Khadija ta yi, ta ce, “Khadija ba wai kuka kawai zaki bari ba, ya zama dole ki shayar da Yaran nan inda basu da abin da zasu ci, idan ba haka ba gaskiya ba zan iya zama ba ina ganin abin tausai, ace Yara k’anana jarirai suna kukan Yunwa, gaskiya in dai kina son in fasa ta fiya tom ki yarda zaki rik’a ba yaran nan Mama duk lokacin da suka buk’ata?”. 

“Eh na yar da zan rik’a basu”. Khadija ta fad’i maganar tana goge hawayanta”. 

Hafsat mai da kayanta ta yi, ta aje, sannan ta Kama hannun Khadija ta zau nar da ita, ta d’akko d’aya daga cikin Baby’s ta mik’a mata”. 

Khadija amsar Babyn ta yi, tana goge hawayan idonta. Khadija rik’e  Babyn ta yi, ta kasa bashi Maman. 

Hafsat ganin haka ta ce, “Khadija dan Allah ki kau da ko mai aranki, ki rungumi Yaran nan, idan baki basu abincin su ba, tom mutuwa kike so su yi?, haba Khadija, ki ka Sa ni ko daga kansu Allah ba zai kuma baki Haihuwa ba, kin san abin da zasu zama nan gaba?, haba Khadija kefa ba jahila ba ce dan Allah ki bar aiki irin na jahilai, zuwan yaran nan kad’ai duniya ya kamata ki fahimci haka Allah ya tsara Rayuaarki da kuma su Yaran, da Allah ya nufa ta haka za asame su. Idan kika yi hak’uri Khadija sai kiga Allah ya saka komai yazo miki da sauk’i, yadda kike tunani sai ki ga haka bai Kasan ceba, dan Allah ki basu Mama Khadija su sha, kafin alhakinsu ya kamaki”. 

Khadija goge hawayanta ta yi, sannan ta d’aga rigarta sama ta na sakama Babyn Maman abakinta”. 

Allah Sarki da ya ke Yarinyar Yunwa ta ke ji sosai, ta ke taci gaba da shan Maman ta.

Hafsat sai da ta tabbatar Babyn ta k’oshi, sannan ta amsheta daga hannun Khadija ta aje ta ta bata d’ayar. Amsar d’ayar ta yi itama ta bata ta sha ta k’oshi”. 

Khadija Kallan Hafsat ta yi tana goge hawayanta ta ce, “Hafsat ya zan yi da Yaran nan?, Ina zan kai su?, ki ban shawara dan Allah, dan Wallahi ba zan iya zuwa gidan mu da su ba”. 

Shiru Khadija ta yi, sannan ta ce, “Khadija idan kin ce ba zaki je Gidan ku da su ba, tom ina zaki kai su?, ko wurgar da su zaki yi? “. Hafsat ta tambayi Khadija tana k’ureta da ido”. 

Khadija kallan Hafsat ta yi, ta ce, “Hafsat kifa tuna gidan mu babu wanda ya san inada cikin yaran nan, yan zu kawai sai in koma musu da Yara?, Kai ina Wallahi ba zai yuwu ba, Mahaifina korata ma zai yi Wallahi “. “Tom Khadija shine ni yan zu nake tambayarki ai, yadda su za ki? “. Hafsat ta tambayi Khadija “. 

Shiru Khadija ta yi, sannan ta ce, “Ni ma Hafsat ban Sa ni ba, abin da kawai na sa ni ba zan  iya zuwa gidan mu da su ba”. 

Sallamar Doctor Ruk’ayya ce ta katse musu maganar da suke. Doctor Ruk’ayya da mamaki ta ke kallan Hafsat ta ce, “Hafsat biki d’ora ruwan ba? “. “Wallahi Doctor na shafa ane,  kin ga wadda duk ta rud’ani ta k’i ba Yara nono da kyar na samu ta basu. Murmushi Doctor Ruk’ayya ta yi, ta wu ce d’an ma dai-dai cikin kitchen d’in ta d’ora ruwan. Tana nan zau ne ruwan ya tausa yana tausa ta kwashe ta kai toilet d’in Khadija ta je tai mata wankan towel kamar jiya. Tana gama ma Khadija na Yaran ma ya ta fasa, bayan ya d’an sha ne, ta yi musu wankan, ta shirya su cikin kayan da ta sai musu, dama Doctor Ruk’ayya ta zo da gawayin hausa, da shi tai ma yaran gashin cibi, tana gamawa ta mik’ama Hafsat su, ta ce, “Hafsat kin ga dai yadda ake gashin cibin ko? “. 

Kai Hafsat ta d’aga mata. 

Doctor Ruk’ayya ta ce, “Yauwa tom amsa ki musu”. Hafsat amsar d’ayar ta yi tana mata kamar yadda taga doctor Ruk’ayya na yi”. 

Tun daga wannan rana Doctor Ruk’ayya daga ta yi ma twins wanka zata tafi, ta ba Hafsat tai musu gashin cibin. 

Masha Allah cibin ta samu gashi dan kwana uku ta faffad’i. 

Doctor Ruk’ayya ko sai da ta yi sati tana zuwa yi ma Khadija wanka. Aranar da Yaran suka cika sati d’aya da Haihuwa bayan Doctor Ruk’ayya ta zo ta kalli Khadija da ke zau ne, daga gani ta yi nisa a duniyar tunani. Doctor Ruk’ayya dafa Khadija ta yi, ta ce, “Khadija,an yi ma Yaran nan hud’u ba ma kuwa? “. Kai Khadija ta girgiza. Doctor Ruk’ayya ta ce, “Tom wana suna za a sama Yaran sai ni in musu hud’ubar inda ba Namiji? “. 

Khadija kallan doctor Ruk’ayya ta yi kamar za tai kuka ta ce, “Doctor ki tambayi Hafsat “. Doctor Ruk’ayya mai da kallanta ga Hafsat ta yi, ta ce, “Hafsat wana suna za a sa musu? “. Shiru Hafsat ta yi kamar mai nazari, sai cewa ta yi, “Ni sai inga kawai a barsu da sunan su, Hassana da Usaina”. “Ai kam haka ya yi sosai, dan nima ra’ayina kenan”. 

Doctor Ruk’ayya bayan ta gama duk abin da ya kamata tai ma su Khadija ne, ta kalli Khadija ta ce, “Tom Khadija zan tafi, daga Yau ba zan sake zuwa ba, sai in na zo duba  su Hassana, ai kinga yadda na ke miki wanka, tom haka zaki rik’a yi, dan Allah Khadija ki kauda damuwar komai aranki ki rungumi Yaranki, ki sa addu’a agaba Allah zai sa ko mai yazo miki da sauk’i”. 

Godiya sosai Khadija tai ma Doctor Ruk’ayya, sannan ta tambayeta na wa za abiya ta. 

Murmushi Doctor Ruk’ayya ta yi, ta ce, “Babu komai Khadija ki barshi kawai na yi miki duka dan Allah ne, ni dai fatana karki wasa da Yaran nan”.

Godiya sosai Khadija ta kuma yi ma Doctor Ruk’ayya, su kai sallama ta tafi”. 

Tun gada wannan ranar ya zamana kullum Hafsat zata tashi ta d’orama Khadija ruwan wanka, Hafsat ita kema Yaran wanka kullum, saboda so d’aya ake masu arana,  doctor Ruk’ayya ta ce ya ishesu, inda ba da k’una su ake ba”. 

Yau Hafsat da wuri ta tashi ta yi shirin shiga school, dan yau 7:30Am zasu shiga lecture. 

Hafsat tada Khadija ta yi, ta ce, “Khadija ki tashi ki yi wanka Ki ma Babyna”. Khadija bud’e ido ta yi tana kallan Hafsat ta ce, “Aiko Yau basu da wanka mamarsu bata nan, in kin dawo da wuri tom”. 

Murmushi Hafsat ta yi, ta ce, “Kut kin isama, in tafa ruwan da kai na, ki ce ke kad’ai zaki yi ba zaki ma Yarana ba, tom aiko sai dai kema in kar ki yi, in ba haka ba Yau ni da ke ne agidan nan”. Hafsat na fad’in haka ta je ta sumbaci yaran ta tafi da sauri, dan ta kusa makara”. 

Khadija shiga wanka ta yi, tana cikin wankan ne Yaran suka tashi kusan atare, suna kuka.

Khadija sauri-sauri ta yi ta gama wankan jin yadda yaran ke kuka, ta fito. Tana zuwa ta juyo ruwan zafin ta saka d’aya daga ciki, amma yadda yarinyar ke kuka dole Khadija ta tsameta a ruwan, ta ba ta Mama sannan ta samu ta yi shiru,tana mai da ta aruwan ta kuma fasa kuka, sauri-sauri Khadija ta yi ta yi mata wankan ta tsameta, dole Khadija sai dai ta goyata, saboda yadda ta ke kuka. Sanan ta d’auki ruwan ta zibar ta d’ebo wani ta saka d’ayar, bayan ta gama mata wankan,  Zama ta yi ta yi mata shafa ta saka mata kaya,  sannan ta kwantar da ita, ta kwanto ta bayanta ta yi mata itama. Khadija sai da ta gama shirya yaran sanan ta yi shafa itama, ta kwanta kusa da Yaranta ta na kallan su, tana mai al’ajabi cikin ranta, wai yau ita ke da Yara har biyu ba tare da aure ba, kuma ba tare  da sanin wani na Gidan su ba. Khadija d’aukar Usaina ta yi ta kwantar da ita akan k’irjinta ganin tana mutsu-mutsun tashi, ta na mai d’an jan tsaki kad’an ta ce, ” ke fa kin fiye rigima, Hassana sai ta wuni bacci amma ke sai dai ki ta takura mutane da shegan kukan ki”. Khadija na maganar tana d’an jijjigata saboda ta fara kuka. ana cikin haka ne kuma wayar Khadija ta fara ringing, Khadija ko da ta duba taga number Mahaifiyarta ce, aje wayar ta yi, saboda badamar ta d’auka saboda za ta ji kukan da Usaina ke yi. Khadija na ji nagani wayar ta tsinke har wani kiran ya k’ara  shigowa shima ya katse,Khadija naji nagani ta ki d’aga kiran, tashi ta yi  ta na mai tsakin yadda Usaina ke nai man ta kura mata,  sa ta abaya ta yi  ta goyata tana d’an yauwo da ita tana jijjigata”. 

Hafsat ko ba ita ta dawo ba sai gaf da magriba, tsaye ta iske Khadija da goyan Usaina tana jijjigata”. 

Hafsat da sauri ta k’araso tana mai k’ok’arin b’alle goyan ta amshi Usaina. Hafsat amsar Yarinyar ta yi, ta kallli Khadija ta ce, “Wai lafiya? “. k’aramin tsaki Khadija ta ja, ta ce, “Haba Wallahi Yarinyar nan yau tun da kika tafi muke aikin abu d’aya, kuka-kuka tun d’azu “. “Tom ko dai bata da lafiya ne? “. Cewar Hafsat. 

“Ba wani nan lafiyarta k’alau, idan zaki lura dama tafi Hassana rigama”. khadija ta idasa maganar tana mai samun gu ta zau na”. 

Haka kwana kai suka ci gaba da tafiya, Khadija in dai za tai waya sai dai tafita waje gudin kar cikin Yaran wani ya tashi aji kukan jariri. Sosai Hafsat ke d’awai niya da Yaran, dan indai bata je School ba tom ita ke rainon Yaran. Azufar mai tsada Hafsat ta siya ta sama Hassana a hannu ta cire zaran da aka sama Yarinyar na shaida, duk da yan zu suna ban-banta Yaran saboda Usaina tafi rigama, ta nan kawai suke shaida Yaran”. 

Akwana atashi babu wuya ahaka har su kai arba’in, Yaran sun yi wayau sosai Masha Allah. 

Sai dai hankalin Khadija sosai ya ke atashe saboda yan zu haka cikin satin nan za su samu hutu, wannan shine abin da ya yi mugun d’aga mata hankali, gashi tuntuni Mahaifiyarta ta dawo Nigeria”. 

Hafsat da ke k’ok’arin shigowa da sauri ta k’araso jin Khadija na kuka, abin da ta rabu taji, dan tunda ta ce ma Khadija in dai ta k’ara ganin ta tana kuka tom zata ta fi ta barta, tun daga ranar bata k’ara Kama Khadija tana kuka ba, sai yau, yau kuma tasan bai wuce maganar ta tafiyarta gida ba, inda gobe ne zasu yi hutu”. 

Hafsat kallan Khadija ta yi, ta ce, “Khadija dan Allah ki yi hak’uri da kukan nan, tun jiya da daddare ina jin kukan ki, haba ya isa haka nan mana, inda dai shi kukan nan tunda kike yin shi har yan zu babu wani magani da ya yi mi ki”.

Khadija kallan Hafsat ta yi, ta ce, “Hafsat ba zan je da Yaran nan ba Wallahi”. 

“Baza ki je da su ba!?, tom ina zaki bar su? “. 

Shiru Khadija ta yi, sannan ta ce, “Nima abin da ban sani ba kenan, kawai dai nasan ba zan je da su b…… ✍️¹¹ ¹²

About AIS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *