HEEDAYA CHAPTER 35 BY By Khaleesat Haiydar

HEEDAYA CHAPTER 35 BY By Khaleesat Haiydar

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Abba ya dafa Asp a hankali yace “Sir, isn’t it good mu fara jin abinda ke tafe da shi tukun…” Asp ya girgixa kai 

strictly yace “That will be at the station not here, a suspect??? Noo” Handcuffing din hannun Khaleel dake ta kallon 

Shuraim ta gefen ido yyi in both hands, yana pointing dinsa da pistol din hannunsa Incase he should make any 

attempt of wanting to escape, ba musu Khaleel ya nufi motar da Asp din ke nuna masa yana biye da shi bayansa, nan 

yyi instructing din Shuraim ya biyo su, Khaleel ya sake kallon Shuraim kafin ya shiga motar da Asp ya bude masa, 

kawai he just don’t want to escape ne banda haka pistol din Asp bai bashi tsoro ba, minti nawa ne xai yi guduwan sa 

kuma bullet dinsu baxai ta6a shi ba, but he can’t just run without knowing if Heedayah is home or not, ynxu bai san 

ko Zayyad ya kawota gidan ko bai kawota ba, Junaid dai har sannan yana tsaye bakin gate tare da Abba, Abba ya 

dafasa yace “Let me go with them, Kai kuma ku taho station din tare da Barrister yanxu….” Junaid ya gyada masa 

kai snn ya juya ya koma cikin gidan. Khaleel na xaune yana facing wani d’an sanda dake masa tambayoyi yana 

rubutu a report book dinsu, su kadai ne xaune wajen, Shuraim na daga bakin kofa a tsaye looking directly at Khaleel 

dake magana calmly without any fear, he felt like shooting Khaleel ko xai ji saukin abinda xuciyarsa ke yi masa, bai 

ta6a jin he wants to use his gun on someone ba irin Khaleel, Mami dai na xaune ita ma a sanyaye tana kallon 

Khaleel, gaba daya ta dawo kamar warce ta tashi ciwo sbda damuwa, wnn dalilin yasa Abba bai bata fault ko kadan 

ba duk da without knowledge dinsa Heedayah ta taho Abuja which isn’t right but he never blamed her even for a 

second, Abban ma dai da Junaid na xaune wajen, sai Mijin Dinar da ya dawo a ranan shi ma yana gun a xaune, Dpo 

na xaune shima yana ta rubuce rubucensa shi ma a gurin, police officer din na kallon Khaleel yace “Bayan ka tafi da 

ita sai aka yi yaya?” Khaleel yace “A jiyan nace xan dawo da ita gida tace baxata dawo ba…” Police officer din yace 

“A daren still?” Khaleel yace “Eh” Police officern na gyada kai bayan ya gama rubutu yace “To sai aka yi yaya?” A 

takaice Khaleel yace “Sai na wuce da ita gidana” Hawaye ya shiga sakkowa Mami uncontrollably, Shuraim ya dauke 

kansa daga kallon Khaleel jin wani abu da ya tokaresa a kirji, Abba dai ya sauke kansa kasa, Junaid ya shafa kansa 

ya nemi waje ya xauna daga tsayen da yyi a wajen, Police officern yace “A gidan naka ta kwana kenan?” Khaleel 

yace “Ehh” police officern yace “Go on, sai aka yi yaya” Khaleel yace “Da safe after breakfast nace xan mayar da ita 

gida, tace min she isn’t going back home, I insisted and she ran away without me knowing” Police officern yace 

“She ran away from ur house?” Khaleel yace “Yes, but after 4 hours ta dawo gidan nawa, bana gidan ma lkcn da 

koma coz I was looking for her from the moment I noticed ta bar gidan, na dawo da yamma na ganta kwance parlor 

tana bacci, I have to make plans with my frnd kafin in basa ita ya mayar da ita gidan da na daukota” Dpo ya daga kai 

yana kallonsa yace “Wani plan kenan?” Khaleel yace “Na sa mata pill din bacci a lemo, bayan tayi bacci sai muka 

tafi da ita da abokina na nuna masa layin, na kuma gaya masa house number din snn na sauka motar nace ya karasa 

da ita” Dpo yace “Me yasa kai baka kai ta ba?” Khaleel yace “Because I remain a suspect a gidan, duk da I didn’t 

take her to my house intentionally, na tambayeta ko anyi mata wani abu a gidan ne da tace she isn’t going back, tace 

min nothing, she only want to stay with me” Kallonsa kowa na wajen yake yi, Mami dai sai kuka take don tasan ba 

training din da tayi ma Heedayah bane, something might be wrong somewhere” Dpo din yace “Toh abokinka bai kai 

ta gidan ba, and now tell us more about him, and where he stays….” Khaleel yace “I’ve been calling him but no 

response, shine ma yasa na tafi gidan to check if she is home…” Dpo din yace “Ya sunan frnd din naka?” Shiru 

Khaleel yyi, Dpo ya masa wani kallo yace “You Answer me….” Khaleel yyi kasa da idanuwansa yace “Zayyad” Dpo 

yace “Full name?” Khaleel yace “Zayyad Idris” Dpo yace “A ina yake xaune” Khaleel ya shafa kansa bai ce komai 

ba, dai dai nan wayarsa ya fara ring a pocket dinsa, xai ciro officern dake facing dinsa ya dakatar da shi ya mike ya 

ciro wayar da kansa, ya kalli screen din snn ya nuna ma Khaleel yace “Waye yake kiran ka?” Khaleel yace “Zayyad, 

shine ke kiran” Officer din ya daga ya sa handsfree snn ya mika ma Khaleel, lkci daya Khaleel ya ji gabansa ya fadi 

ganin handsfree d’an sandan ya sa wayar, daga Mami, Abba, Junaid da mijin Dinar duk kallon Khaleel suke, don 

Shuraim tun da ya fita bai sake dawowa ba, Daga daya bangaren Zayyad yace “Tell me Brainiac wacece wnn 

yarinyar da ka bani kace in mayar gida, for how long take wajen ka??” Khaleel yace “Why were you not picking my 

call?” Zayyad yace “No tell me yaushe ka fara rayuwa da yarinyar, how long??? coz ni na kawota gidan da kace and 

ban gane drama din da mutanen gidan suka yi displaying ba after seeing her, shekaranku nawa tare da yarinyar ni 

ban sani ba” Khaleel yace “Wani gidan ka kai ta??” Zayyad yace “Gidan da kace mana, I am even still at the house 

now, her father ya ki bari in tafi, it seems the girl have been away from home for long faaa” Gaba daya occupant din 

office din kallon wayar Khaleel suke listening to what Zayyad was saying, Khaleel yace “Are you sure layin da 

muka tsaya ka shiga?” Zayyad yace “Haba, shine wllh, and you know what Khaleel????” Khaleel yyi shiru, Zayyad 

yyi kasa da murya yace “Gidan Alhaji Ahmad ne, shine Mahaifin yarinyar, ka gane wani Alhaji Ahmad din?” Kittt 

Khaleel ya katse wayar, Officern dake kallonsa yace “Hey, Why did u cut the call??” Khaleel yace “Layin xa mu je 

da yace ya kai ta, sai a dubata a nan” daga Mami har Abba kallonsa suke keenly, Abba yace “But y did you end the 

conversation that way, when he is talking?” Khaleel ya kallesa bai ce komai ba, Abba ya kalli Dpo dake office din yace “I think ya kamata su gama maganan, he should call him back” officern na kallon Khaleel yace “sake kiransa” 

Mami ta sauke boyayyen ajiyar xuciya tace “Da dai mu fara xuwa mu ga halin da yarinyata ke ciki don Allah dpo, 

Ko xan samu nutsuwa” Dpo yace “Their conversation will take just few minutes Madam kiyi hakuri, xa mu je can 

din yanxu, ka sake kiransa” Dpo ya fadi haka yana kallon Khaleel, Khaleel ya sauke idanuwansa kan wayarsa ya 

sake dialing Number Zayyad, Zayyad na dagawa Khaleel yace “Be brave Zayyad…. where are you at now?” Wani 

kallo Dpo ya jefa ma Khaleel, ya tashi da kansa ya katse wayar yace “Maganar da yake maka daxu xaka ce ya ci 

gaba…. Keep on to that conversation” Khaleel yace “Ohhh, ohk” Daga haka ya sake kiran Zayyad, Zayyad na 

dagawa yace “Yauwa, Brave you, kace gidan wa kake?” Zayyad ya d’an yi shiru snn yace “Gidan Baban yarinyar…” 

Khaleel yace “Maintain… So waye baban yarinyar?” Zayyad yace “Uhn sure…, I just learnt that Alhaji Ahmad ne, 

wanda ke neman takarar gwamna na jihar kano, so I was surprise, ashe babanta babba ne… That’s all abinda xan fada 

maka, sai kuma ince why did she decide to leave home” murmushi kawai Abba yyi, Mami dai sai kallon Khaleel 

take, police officer ya katse wayar, Dpo ya mike yace “Xa ku tafi can anguwar tare da Asp Ina jin” motar yan sanda 

daya suka shiga, wanda Khaleel ne ciki da two police men, sai Shuraim dake motar shi ma, Mami da Junaid suka 

shiga mota daya, Abba da Mijin Dinar su ma mota daya suka hau suka bar police station din. Officer daya ya sa 

Khaleel ya sake kiran Zayyad ya tambayesa gida na nawa ne, Zayyad yace “Gida na biyar….” dai dai gidan Alhaji 

Ahmad duk motocin suka tsaya suka sakko, mijin Dinar yace “Wnn ai gidan makocina ne Honorable….” Asp ya 

bubbuga gate din, Yan sanda biyu na tsaye tare da khaleel, ba a dau lkci ba aka bude gate din, Dpo ya gaisa da sojan 

da ya bude gate din Snn ya nuna masa ID dinsa yace “Muna son ganin me gidan nan ne….” Sojan yace “Alright, bari 

ayi alerting dinsa” kulle gate din yyi ya koma, Jikin flowers Shuraim ya tsaya fuskarsa bbu walwala, ya ki yrda ma 

ya kalli direction din Khaleel kar xuciyarsa yyi explode, gaba daya he is just restless da bayanin da Khaleel yyi a 

station, su Mami da Abba duk suna tsaye bakin gate din, ita dai Mami fatan ta a ga daughter dinta kuma ko kwana ta 

dau ma kanta alkawarin baxa su yi a Abuja ba xata dauketa su koma gida, da ta tuna wai gidan namiji ta kwana jiya 

sai taji hawaye na mata xarya, bayan wani lkci Alhaji Ahmad ya bude gate din da kansa, da kallo ya bi dukansu snn 

suka gaisa da Asp dake kallonsa shi ma, Asp na murmushi yace “Sorry for the disturbance Honorable, amma daxu 

an shigo da yarinya gidan nan kuwa…. They mistook here for the girls home” Alhaji Ahmad ya d’an yi shiru duk 

yana kallonsu, can ya gyada kai cikin sanyi yace “Kwarai an kawo yarinya gidan nan daxu” Asp yace “Fatan tana 

nan gidan har yanxu?” Alhaji Ahmad yace “Sure, tana nan” Asp yace “To Alhmdllh, xa mu shiga mu tafi da ita 

ynxu” Mami bata san lkcn da ta sauke wani bayyanannen ajiyar xuciya ba, taji wani farin ciki ya lullubeta, Alhaji 

Ahmad dai bai ce komai ba ya basu hanya duk suka shiga gidan, k’in shiga Shuraim yyi ya nufi titi walking like the 

soldier he is, Khaleel dai sai kallon Alhaji Ahmad yake bayan sun shiga gidan, har suka isa building din Uwar gidan 

Alhaji Ahmad, Har sannan Heedayah na kwance parlon still sleeping heavily, Zayyad kuma na xaune saman kujera, 

Mum Islam na kusa da Heedayah da family Doctor dinsu da ya gama dubata, Mahaifiyar Heedayah kuma na xaune 

ta takure waje daya sai kallon Heedayah take ita a dole she is dreaming and can wake up anytime, Mami ta karasa 

gun Heedayah da ta fara gani a parlon da sauri ba tare da ta bi ta kan mutanen dake parlon ba ta durkusa kusa da ita 

ta fara kiranta tana girgixa ta, a rikice tana kallon likitan tace “Me ya sameta Dr??? what’s wrong with her” Mikewa 

Mum Islam tayi tana kallon Mami da mamaki bata son tabbatar da cewa Ita ce yarinyar da ake ta nema tun jiya a 

makotansu, Junaid dai na tsaye bakin kofar parlon sai kallon Mahaifiyar Heedayah yake, same goes to Khaleel that 

is shocked at the resemblance, Mami dai hankalinta gaba daya na kan Heedayah da take tadawa, Asp da Abba, da 

Alhaji Ahmad sai Mijin Dinar kadai ne waje basu shigo parlon ba har sannan, Heedayah ta bude ido a hankali, kana 

ganin yanda take bude idonsa kasan sun mata nauyi, murya can kasa tace “Mami” Rungumeta Mami tayi hawaye na 

sakkowa idonta tace “Ina kika tafi Heedayah, me yasa kika fita gida da daddare?? Where did you go to” A hankali 

Heedayah tace “I just felt like going Mami, Mami don Allah kiyi hakuri baxan sake ba” sai kuma ta fashe da kuka 

sosai, Mikewa Mahaifiyar Heedayah tayi daga inda take xaune hawaye na sakko mata ta wuce dakinta, Mami ta 

goge ma Heedayah idonta tace “It’s okay daughter, we are going back to Kaduna now, in sha Allah…” Heedayah ta 

d’an yi shiru, sai kuma da sauri tace “Mami where is he?” Mami tace “Who” Heedayah tace “Ya Khaleel, shi ya 

dawo dani gida ko?” Mami bata saurareta ba tace “I don’t know, we are going home now” Mami na fadin haka ta 

tashi tana dago Heedayah, Heedayah ta xame hannunta tace “Mami Ya Khaleel din fa? Da ya kawo ni wucewa yyi?” 

Sai a snn Mami ta juya ta kalli Khaleel bayan ta fahimci shi Heedayah ke tambaya, sosai gabanta ya fadi da suka 

hada ido da shi, don har sai da ta koma ta duka kasa, Heedayah ta shiga bin mutanen dake parlon da kallo, idonta ya 

fara sauka kan Zayyad, tashi tayi ta tafi gunsa da sauri tace “Ina ya Khaleel din, did he leave after bringing me 

home?” Zayyad ya nuna mata Khaleel da ke tsaye yana kallonta, kallon handcuffed hands dinsa ta dinga yi sai kuma 

ta tafi gunsa almost running tace “What’s this, waye yyi arresting din ka?” Komawa gun Mami tayi hawaye cike 

idonta tace “Mami wllh nice na bi sa ba shi ya tafi da ni ba, shi ba ruwansa, he only helped me, he is innocent, tell 

them not to arrest him plsss” Dai dai shigowar Asp tare da su Abba da Mahaifin Heedayah, Asp ya karasa gun 

Khaleel da makullin handcuff din ya bude ya cire handcuff din daga hannunsa, Heedayah ta tafi gunsa tana kallon 

wrist dinsa cikin sanyi tace “I am sorry I caused you everything” Mami ta nufeta ta dafata tana kallon Khaleel da ya sunkuyar da kai bayan ya hada ido da ita, ta kama hannunta za su fita parlon, Asp yana kallon Mami yace “Ku 

dakata Hajiya….” Kallonsa Mami tayi da sauran mutanen parlon, Asp ya kamo hannun Abba dake tsaye gefensa yace 

“Barrister Ahmad d’an uwan abokina ne da muka yi karatu tare, and we are still family frnds till date, 5 years ago 

Barrister ya xo station dinmu da wata yarinya da baxata wuce shekara 12 ba, a blind girl, lkcn Ina kano ba ayi 

transferring dina xuwa Abuja ba….” Very briefly Asp Usman ya bada wnn takaitattcen tarihin, Asp ya ci gaba yace 

“Shekarun baya, like 2 to 3 years back mu kan yi waya da shi in tambayesa how is this little girl kafin daga bisanni 

na watsar sanin baxai cuceta ba don a lkcn yace min har tayi regaining sight dinta, don har lkcn mu ba mu samu 

wani labarin iyayenta ba, but I must confess it’s a case we never took serious, ganin makauniya ce ita wnn yarinya 

kuma gata yar karama, nafi xaton daga less privileged home ya fito, ni Allah ya ga xuciyata kusan gata nayi mata na 

son in ga ta xauna gun shi wnn bawan Allah, nasan shi da iyalansa baxa su cuceta ba, xa kuma ta samu gatan 

karatu…” Yana nuna Heedayah yace “As at the time this lady got missing yesterday evening, d’an barrister ya kai 

report police station dinmu, but bana office then, sai daxu da rana abokina Dr Umar wato yayan shi barrister din ya 

kirani ya sanar min halin da ake ciki, and I immediately reported to office to see the needful we can do about the 

case…. Sai dai cikin hukuncin ubangiji bamu ga yarinyar nan a ko ina ba sai gidan biological parent dinta yanxu, and 

yanda ni nayi tunanin iyayen nata ba haka bane, sannan ba ayi masu adalci ba kwarai da gaske….” Asp ya nuna 

Alhaji Ahmad that is also by his side trying all possible mean to control his tears yace “Mahaifin yarinyar nan kenan, 

Honorable Ahmad, we saw pictures, resemblance, and concrete proofs, that’s just it, nan din gidan iyayen wannan 

yarinya ne” Heedayah ta juya tana kallon wanda Asp ke nunawa matsayin Mahaifinta, Khaleel couldn’t stop looking 

at him also, Abba ya karasa gun Heedayah yana kallonta ya kamo hannunta gently yace “That’s ur father Heedayah, 

I am sorry I never made any effort to take you back to them, I am sorry daughter” Rungume Abba tayi ta fashe da 

kuka sosai, almost whispering into his ears tace “You are always my father Abba, you remain my father” Mami taji 

ta kasa ci gaba da tsayuwa ta nemi waje ta xauna hawaye na sakko mata sosai, junaid dai ya dafe kansa kawai daga 

inda yake xaune, sai duk suke jin abun kamar a film, Mum Islam ta nufi Mami ganin yanda take kuka ta duka kusa 

da ita, ita ma tana share hawayen dake sakko mata tace “Mami nasan Dinar tun dawowarsu anguwar nan, mun shaku 

da ita sosai, har gaisawa mu kan yi da ke a waya in dai ta kira ki ina gidan ko kin kirata, amma duk bamu san ke ke 

rike da ‘yar Mai gidana da ta bace shekaru biyar kenan ba, wanda har yau duk muna rayuwa ne da ita a ran mu, ba 

tare da sanin ko tana raye ko ta mutu ba, Heedayah ‘yar kishiyata ce ta fari, wanda saboda bacewarta har yau ba a 

gane kan mahaifiyarta ba, but How can we pay for this great deed Mami? A blind little girl got lost, but we are 

seeing a sighted teenager now, baxa mu ta6a iya biyanku ba koda duk dukiyar Mahaifinta xa a baku” Mami bata iya 

ta ce komai ba sai share hawayen da ya ki tsaya mata take, sai take jin abun kamar a mafarki, so she is leaving 

Heedayah with them kenan yanxu, Abba dai na tsaye still holding on to Heedayah dake kuka sosai ita ma, shi kuma 

nan gani yake bai mata adalci ba bai ma iyayenta adalci ba, shi dai yasan ba da nufin komai ya banxantar da batun 

iyayenta ba, Abba ya kalli Alhaji Ahmad da ke ta kallon ‘yar tasa shi ma yana tunanin how is he going to pay 

barrister Ahmad and Barrister Rahinah, Abba yace “Ina mahaifiyar ta?” Alhaji Ahmad bai ce komai ba, can ya nufi 

dakin matar tasa, kwance ya sameta ta takure waje daya, ya xauna gefenta ya dagota yace “Aisha ur Daughter 

Heedayah is back home, my assurance to you always, didn’t go in vain, na sha gaya maki idan Allah ya amince 

Heedayah xata dawo garemu, and here she is today” Ta kamo hannunsa hawaye na bin fuskarta tace “Noo Ahmad 

kullum irin mafarkin nan nake, daga karshe sai kuma in tashi da wani ciwon, why is this dream taking long, don 

Allah ka tasheni daga wnn baccin, ni nasan ba gaskiya bane, irin mafarkin da nake yi kenan a ko da yaushe…. Daga 

karshe na tashi naga ba Heedayata, beside my Heedayah I know is blind….” kuka sosai take yi tana kallonsa, ya 

dagata suka fita dakin, suna fitowa parlor tayi ido hudu da Heedayah, kallonta kawai Heedayah ke yi, lkci daya ta 

xame hannunta daga na Abba, ta tafi da gudu ya rungume uwarta ta fashe da kuka, sai a snn mahaifiyarta ta tabbatar 

ba mafarki take ba, Heedayar tace ta dawo, but not blind Heedayah, ba mafarki bane, Cikin kuka tace “Heedayah” 

Heedayah bata mance muryar mahaifiyarta ba, har cikin ranta ta ji murya ta rungumeta sosai tace “Ammi I have 

missed you a lot, nayi missing din ki, you’ve always been in my thought, nayi missing din ki” Uwar ta kasa cewa 

komai sai hawaye, lkci daya Heedayah ta xame jikinta ta juya tana kallon Khaleel dake kallonsu, Bata san lkcn da ta 

nufesa da gudu ba ta rungumesa sosai, cikin kuka tace “You promised to take me to my parent, and u fulfilled ur 

promised, I love you dearly, and I will forever be grateful” Junaid ya sauke idonsa kasa daga kallonsu da yake, shi 

dai Khaleel na tsaye yana jinta har cikin ransa, but he is weak and breaking down, Baya yyi a hankali, ganin haka 

Heedayah ta sakesa tana kallonsa, ya dafe kirjinsa ganin xai kai kasa ta saki wani kara, tuni Zayyad ya mike ya nufo 

sa, haka ma Junaid da Abban Heedayah da Abba, with Asp, Mami ma ta mike tana cewa “Innalillahi wa Inna ilaihi 

raji’un” 

About AIS

Check Also

HEEDAYAH SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya}

HEEDAYAH  SHURIEM CHAPTER 17 BY Maryam sule koki {Maman khairiyya} Www.bankinhausanovels.com.ng  Dana ga Anty Meerah …

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *